Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

GIDAN GANDU Complete Hausa Novel Document by GIDAN GANDU


GIDAN GANDU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 88561



GIDAN GANDU

Reading Time: 7 Hours

Added On: 08, Sep 2023

Author: Biebee Isa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 464.26 kb

File Type: txt

Views: 1728+

Download: 1999+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: GIDAN GANDU
Biebee Isa
Hausaebooks
Creat:- Shuraih Usman

Ku shiga shafinmu na facebook domin samun wasu kayatattun littatafan ta hanyar bibiyar wannan
adireshi na yanar gizo www.fb.com/hausaebooks

GIDAN GANDU
1⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕
Tsaki Haneefa ta qara bugawa a karo na biyu,
yanzu mu kullum haka zata dinga samu latti?
Bilqeesu tace Aifah, inda sabo ai ya ci ace mun
saba, ta cika nawa, Hanifa tace wlh baxa ta sabu
ba, bari mu dawo daga makaranta wlh mu samu
Tsoho mu gaya mishi, Islahulkhair da ke gefen
su ba ta tanka musu ba, cikin damuwa Fadila
tace Mallam Audi donAllah ka qara mata horn,
kafin Mallam Audi ya qara Horn suka hangota
tana sauri cikin yanayinta na sayih ta fada cikin
mota qirar bus, Mallam Audi Ina kwana, ya

amsa mata cikin murmushi, tace kayi haquri
wlh banga Socks dina bane, yace ba komai shigo
muyi ta tafia kar mu bata wani lokacin. Ya ja
mota ya bar haraban wakeken gidan da ke
qunshe sashe sashe..
Kusa da Islahulkhair ta zauna gefenta Fadila ce
riqe da keypoint tana karatu, Ta ce hey Sisters,
sorry i kept u waiting, Fadila ta dago ta kalleta,
cike da zolaya tace Allah ya nuna mana ranar da
zamu daina jiran Maysah, kin cika nawa, tace
wlh banga safata bane ta kalli Islah tace yadai
sisi? Murmushi ta mata tace lafya u will never
change will u? Daria ta mata ta kama kunnenta
tace sorry, ta kalli su Hanifa da bilkis a gefe
tace duk ina kwananku, a tare suka buga tsaki
tare da hararta, ba ta damu ba don idan da sabo
ta saba. Mazan da ke zaune su hudu a chan baya
tace Whatsapp bro, daya kawai ya amsata
sauran 3 hararata sukayih. Ta kalli Na'imah da
bakinta ke sake tana jalalar da miyau tace
Nimcy a rufe bakin mana, kar ki bata gaban
hijabinki, cikin tsiwa nimcy tace anqi a rufe din,
sa'idawa masu bacci da ido daya, tace Allah baki
haquri ta ciro littafinta ta shiga dubawa don yau
suke fara NECO exams...
Jikokin Alhaji Musbahu Zailani kenan masu
rubuta Jarabbawar qarshe ta makarantar
Sakwandire na TopOnwards Science College
Maiduguri, Su 10 cif zasuyi graduation bana...
***************
Assalam Alaikum tsoho me ran qarfe, Tsohon
da ke zaune kan Sofa kyakyawan gaske ne,
kadan ya rage ya cika shekaru chasa'in cif a
duniya, tsufansa me kyau ne, gyara zaman
gilashisa yayi yace Hanifa ce da Balki? Eh mune,
amma bilkisu nake ba balki ba, yayi daria yace
ja'ira, ya jarabawar? Suka ce toh Alhamdulilahi,
duk suka yi shiru, Tsoho yace me bakin shan
qwai menene? Naga magana a bakin ki, Hanifa
ta zumburo baki, tace kaga dai tsoho ka bar ce
man me bakin shan qwai, yace toh ai naga kun
kasa magana, ku fada matsalarku a magance
maku ita, Ke Me Gadon zinare menene? Bilkisu
tace daman Tsoho qara muka kawo ma,
Haneefa tayi charaf tace tsoho mu dai mun gaji,
wao kullum sai Maysah ta samu latti, gashi mun
fara jarabawa, wlh idan bamu bi a sannu ba
wata rana sai an hana mu zana harabawa saboda
latti, Mu gaskia da sakel, a san yadda zaayi
damu, ko a sama mata me kaita ta qarata chan
da lattin ta, Tsoho yayi jimm yace kuyi haquri,
kunsanta da Nawar tsiya, zan mata fada, amma

maganar raba tafiya duk bata taso ba, tun
lokacin yayyunku da sukayi aure tare ake kaisu
makaranta kunga lokaci guda ba za a bar
wannan qaidar ba, Hmm ai daman munsan baka
san laifinta ka fi sonta cikin jikoki, da sauri yace
haba yan jikoki na, wlh duk daya na dauke ku,
ku bari zanyi shawara da iyayenku, ku saurareni
kunji? Sukayi godia suka mai Sallama.
*******
Ta kalleshi tace Tsoho tunda nagama karanta
ma Jaridar bari naje nayi karatu dukda bamu da
paper Gobe sai Jibi, yace RUMAISA'U Meyasa
kike sa 'yan uwanki latti? Kullum ke kadai suke
jira, ko so kuke a hanaku shiga makarantar! Duk
cikin lallabi yake mata magana, ta yi raurau da
fuska tace, kayi haquri InshaAllah zan daina,
yauma don safata ta shige wani gurin ne ai da
bansamu latti ba, yacr donAllah ki daina kinji?
Tace InshaAllah, yace yauwa idan kin shiga cikin
gida ki kiramin Hajia Babba, tace toh Tsoho ta
miqe ta fita, a ranta tace InshaAllah sai na riga
kowa shirin makaranta jibi, ba za a qara jirana
ba sai dai na jira...Tayi Sassan Matan tsoho
domin kiran Hajia Babba, da Sallama ta shiga
dakin Hajia babba ce da Abida (Maman Hanifa)
a dakin, suna ganinta sun ka bata fuska, ta gaida
su ba wanda ya amsata, tace Hajia Babba tsoho
na kiranki, ba ta jira ta ce komai ba, ta fice don
bata son jin zagin da za a jefi kakar ta dashi ba.
Anty Abida ta buga tsaki tace jikar Mayu kawai.
Hajia Babba taja tsaki tace wanda suka gaji tsiya
game da miqewa don ansa kiran mijinta Tsoho.
*******
Gidan Alhaji Musbahu Zailani, wanda yan
unguwa da sauran mutane ke ma laqabi da
GIDAN YAWA, gida ne katon gaske gari guda ne,
me qunshe da sashe sashe, su biyu kachal
mahaifan su suka haifa, shida Qaninshi me suna
Rabi'u iyayensu asalin yan qasar Chadi ne yan
Shuwa Arab, Shekara 2 kachal ya ba qanenshi.
İyayensa sunyi hijira zuwa qasar Nigeria garin
Maiduguri inda suke sana'ar sirfani da
dinki,Bayan Rasuwan Mahaifansu Musbahu ya
rungunmi qaninsa suka cigaba da wannan
sanaar dinki, har Allah ya buda musu, sun samu
İlimi me inganci na arabi da boko. Kafin suka
fara habaka Sanoin su ta wani sigar.. Har suka
zama matasan Attajirai.
A kasuwan da suke Sanaarsu, Akwai Wata
yarinya Karime da ke kawo musu tallan fura
fura, yau da gobe ya sa suka saba da Musbahu
har suka fara Soyayyah, ba ayi wata wata ba ya

kai gaisuwa gun iyayenta, yace ba su da kowa a
Qasar nan sai qaninshi. Mahaifin karime yace
bakomi an bashi karime, ana haka ne diyar
kishiyar Maman karime ta shigo daga tallan
Goro, ta gaidasu, Baban yace sannu Hajjo kin
sha rana shiga kan kabad ki dauko samira na
nan da abinci kici tace to, Rabiu ya bi bayanta da
kallo chan yace Baba wannan fa? Yace hajara
kenan, qanwar Karime ce, amma ba uwarsu
daya ba, uwarta ta rasu, sukace Allah ya ji
qanta, Baban ya miqe yace ina zuwa, ya shige
ciki, Musbahu ya lura Akwai magana bakin
qanenshi, yace yaya dai Rabiu? Yace Yaya
wannan yarinyan ta man, bansan ko babanta ze
ban ita ba, Musbahu yace bari yazo a kwatanta
daman gwara kayi auten kaima, ko da baban ya
dawo Musbahu ya sanar dashi buqatar qaninsa,
Mallam yayi shiru yace baqi taku ba, amma
Hajjo bata da kowa sai Allaj sai ni, Hajjo tasha
wahalar kishiyar uwa, ta na kan sha, Zan baka
hajjo amma sai kayi man Alqawarin cewa zaka
riqe man ita da amana, da sauri Rabiu yace
wallahi na amince baba, zan riqe maka ita da
amana. Yace toh shikenan na baka ita bayan Sati
2 kuzo a daura aure. Sunyi murna gaba ki dayan
su...
*******
Da daddare Mallam ke gayama maman karime
yadda sukayi da meson Karime, murna fal
ranta, Allahu Akabar, ashe zan ga Auren Karime
nah, kai madalla madallah, yace ai ba auren
karime kadai zaki gani ba, harda na hajjo, take
Annurin fuskarta ya dauje dif, tace bangane ba,
yace Qanin Musbahu ke son Hajjo kuma har na
bashi ita, maman karime ta daka tsalle ta re da
riqe qugu tace Kam babban balaeen chan....
2⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Sai kuma ta
fashe da kuka, yanzu mallam ni zaka tona wa
asiri? Eyi? Yace bangane tona miki asiri ba, dan
ka ga ba ni na haifi hajjo ba shine zaka aurar da
ita ko neman shawara bakayi? Ynx idan tayi
aure wazai na kai mun talla? Ko ni kakeso na
fita tallan da kaina? Takaici ya hana mallam
magana sai kawai ya fice ya bar dakin...
*****
Tadihn su sukeyi irin ta masoyan da, Hajjo ta
shigo da Sallama a fuskarta, Musbahu ya amsa
da murmushi, yace Amaryarmu, nan da nan
karime ta hada gabas da yamma, tace wato
Rabiu ba xai janye ba koh? Me zaayi da wanda
ba a san asalinsu ba? Hajjo ta shige cikin gidan
da sauri tana matsar qwallah, Musbahu ya bata

rai yace haba karime me yasa kike haka neh?
Sai kace ba Mahaifinku daya ba? Charrr uban,
Allah ya sawwaqe, daman wayace ma baban mu
daya? To tsaya kajih yanda abun yake, da ita
kishiyar maman mu ta shigo gidan nan, Agola
ce, kuma da ta rasu, shine babana ya riqeta, ni
kadai ral mahaifana suka haifa, Musbahu yace
najih dai, be kamata kina nuna qyamarki gareta
a fili ba, ko kina kishi ne don ta fiko kyau, wani
mugun ashar ta lalayo ta dinga zage zage da
qyar ya lallabata tayi shiru. Ya shaida mata gobe
zasu je Chadi don sanar da kawunninsu auren
su, ta mai Allah ya kiyaye
******
Ko da Su Musbahu suka isa qasar Chadi suka
tarar da Kanin Mahaifinsu Ya rasu me dakinshi
batafi wata 2 ba itama ta rasu, Musbahu ya kalli
Rabiu yace kaga Rabiu inaga mu tafi da su
Mudassir da labaran Nigeria, yara ne ba su fi
shekaru 10 ba su da kowa yanzu sai mu, yace
Yaya duk yanda kace hakan zaayi...
Haka kuwa akayi Washegari suka kama hanyar
Nigeria. bayan kwana 2 aka daura auren
Musbahu da Karime, da kuma Rabiu da Hajjo.
Dan madaidaicin Gida ya kama musu, suka
zauna tare da yanuwansu Labaran da Mudassiru,
Musbahu yace Karime ta riqe su, fir taqi ita
bazatayi bautan yara ba tun kafin ta fara samun
nata, haka Rabiu ya kwashe su ya kaima Hajjo
su, ta amshe su hannu bibiyu.
*****
Bayan Shekara daya.
A daddafe ta
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download GIDAN GANDU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album