Join Our WhatsApp Group

A SANADIN KUSKURENA Complete Hausa Novel Document by A SANADIN KUSKURENA


A SANADIN KUSKURENA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 53110



A SANADIN KUSKURENA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 29, Dec 2023

Author: Zaynerb Muhammad kabeer ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ????AINUWA ????RITER'S✍????* *????SSOCIATION

Author Phone : 09066386347

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 324.37 kb

File Type: txt

Views: 466+

Download: 253+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: ο»ΏπŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡

*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡

πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.09066386347

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
*PAGE 1 & 2*

Zaune suke cikin katafaran fallansu me daukeda da had'add'un kayan daki , kamshi ne ke tashi ko ta ina .

Can na hango Hajiya luba zaune da katan cikinta da ya matukar yi mata kyau , sanye take cikin wata lafiyaiyar shadda, tasha daurin ture kaga tsiya .

Alhaji mansur dayake zaune kusa da ita yace," Hajiya , ta amsa cikin sanyin murya tace ," na,am gameda mai da idanshi kanta .

Cikin murmishi yake fadin," gaskiya a duniya bani da burin da yawuce ace in ga Allah ya rabaki da cikinki lafiya , ina matukar San ganinin kin haifamun yarinya ko Yaro kyakyawa mai kama dake.

Dariya tayi hade da sunkuyar dakai daga bisani ta dago tace,"kai Abban suhail wallahi maganganunka suna bani dariya , kai dai kawai miyi Addu,a Allah ya saukeni lafiya , inshallahu zaki haihu lafiya yayi saurin fada, dariya tasa tace, " humm Allah yasa ya amsa da Ameen .

Suhail ne ya shigo da gudu , yana fadin ,"mommy",mommy"saurin Amsawa tayi tace,"na,am suhail ya akayi??,dan shagwaba fuskarshi yayi yace," mommy ki fada Fahat ya daina tabamun a buna yaje ya batarmun da moto na, yafada hade da cuno baki .

Cikin Bacin rai tace," kiramun fahat din , da to ya amsa ya juya dan kiranashi.

Tare suka taho da fahat din , mahaifin nasu yayi saurin cewa ,"fahat meyasa bakajin magana ne , ba mun hanaka daukan mishi abun shi ba ba bakajin magana koh??.

Shuru yayi yadanyi kasa da kanshi yace," I,am sorry .
Harara ta galla mishi tace," Ku bace Ku bani guri , kai kuma suhail inshallahu gobe daddyn Ku zai siyo maka wani , maza kuje Ku shirya lokacin madarasah yakusa , kuma kuje kufadawa baba driver ya je ya daukko husna a school lokaci ya kusa , da toh suka amsa daga bisani suka fita .


Family gidan Alhaji mansur Suleiman mai tala kenan haifaffen garin gombe ,babban dan kasuwane, , ba laifi yanada kudi , suna zaune da matarshi da 'Yan yanshi cikin kwanciyar hankali.

Sulaiman shine babba Inda suke mishi lakabi da suhail ,kasancewar yaci sunan mahaifin Alhaji mansur , yanada shekaru goma a duniya sai Al_amin mai shekara bakwai , inda shi yaci sunan mahaifin Hajiya luba , suna yi mishi lakabi da fahat , sai kuma Asma,u husna tanada shekaru 5 a duniya ,inda itakuma taci sunan mahaifiyarta Hajiya luba .

Tunda Hajiya luba ta haifi Asma,u tsawan shekaru Biyar haihuwa ya tsayamata , sai kuma yanzu datake daukeda da tsohon cikin watanni tara, Alhaji mansur ya dauki San duniya ya daura ma cikin domin kuwa ji yake tamkar a kan cikin za,a fara haifa mishi yara .

Familyn Alhaji mansur kenan .


Bayan kwanaki goma Hajiya luba ta haifi santaleliyar 'yarta mai kama da ita, murna a gurin Alhaji mansur ba,a magana , ranar suna anci ansha , yarinya taci sunan mahaifiyarshi , zuwaira , amma zasu dinga yi mata lakabi da juwairriya ,da haka har taro ya watse kowa ya kama gabanshi .

Kulawa sossai baby juwairriya take samu a gurin Alhaji mansur da Hajiya luba .

Wasa wasa kimanin watanni shida kenan.

Juwairriya tayi waiyyo sossai kullum kara kyau takeyi domin kuwa duk tafi sauran yayunta kyau , soyaiyyar da Alhaji mansur ke nuna ma juwairriya a kullum mamaki take ba mutane domin kuwa duk yafi kaunarta cikin yaranshi .

Duk Inda zaije matukar yana gida to fa baby juwairriya na makale a jikin mahaifinta .

Hakan yasa husna tadan fara kishi , tana fadin_" dady yaa daina Santa sai dai juwairriya , watarana yayi dariya watarana ya bata hakuri yace yana santa itama .

Su suhail da fahat kam ba,a magana dan tun suna jin haushi har sun daina .

Wani lokaci Hajiya luba takan yi kokari ta fadawa Alhaji muktar cewa," yadaina nuna fifiko akan sauran yaran ,kullum cikin yimishi magana take , amma Sam bai canja ba , hakan yasa tayi shuru ta hakura ta zuba mishi ido ta daina mishi magana a kan San da yake ma baby juwairriya .

Shi kanshi yarasa dalilin da yasa yake matukar San juwairriya , amma a cewarshi dan dai sunan mamanshi ne da ita , wannan tunanin ne yayi rinjaye a cikin zuciyarshi .

Bayan shekaru uku .......✍️✍️✍️✍️

*Muje zuwa*


*Toh masu karatu ,ayimun hakuri nayi short page , amma inshallahu gobe zaki jini a long page , naso in yi typing yafi haka amma busy wlhy fatan zaku mun uziriπŸ‘πŸ‘πŸ‘*.

*Kubiyoni dan jin wainar da za,a toya a gidan Alhaji mansur hummm muje zuwa*.

*I NEED MORE COMMENTS*😎

*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


*BY MUM FU'AD*

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡

*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*
*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 3&4*


Bayan shekaru uku baby Juwairriya tayi wayyo sossai, ta kara kyau, soyyaiyyar da mahaifin ta ke nuna mata kullum kara yawa take , hakan yasa yarinyar ta sangarce , dan yariga ya shagwa'bata , baya bari mahifaiyarta tayimata koda tsawace bale yakai ga duka.

Juwairriya ta raina kowa ciki kuwa harda mahaifiyarta , duk abun da zatayi sai dai a zuba mata ido, dan matukar kayi wani abu da zai bata ran juwairriya to fa Alhaji mansur yayita fada kenan , dan da ran juwairriya ya baci gara nashi ya baci.

Hakan yasa Hajiya luba tayi shuru da bakinta , duk abun da Juwairriya zatayi matukar a gabanshi ne to fa sai dai ta zubamata ido .

Matukar Hajiya luba nayima Juwairriya fada , kullum shima sai ya mata fada a cewarshi wai ta tsaneta , ganin hakan na yawan hadasu fada , ta daina mata fada bare duka .


Shekarunta hudu a duniya mahaifin ta yasata school, badan yaso ba, sai dan matsawa da Hajiya luba tayi akan hakan , a cewarshi batayi girman da za,a sata a school ba , dan bayasan abun da zai takura mata , dakyar Hajiya luba ta shawo kanshi.

Tunda juwairriya ta shiga school ta addabi kowa ta raina duk mallamansu dan kuwa matukar malami yayi Mata fada ko yayi kuskuren dukanta to fa tabbas sai ya je makaranta yayita masifa .

Yasha canjama baby Juwairriya makarantu .

Ganin bata karatu sossai yasa dakyar Hajiya luba ta lallabeshi ya barta a makaranta d'aya, badan yaso ba haka ya hakura , amma bisa sharadin cewa ba duka ba zagi .


Kullum soyaiyyar juwairriya kara yawaita take a zuciyar Alhaji mansur , abun dai ba,a cewa komai .



Kwana a tashi ba wuya a gurin Allah , zuwa yanzu Juwairriya nada shekaru goma sha Biyar a duniya , Inda suhail Nada shekara Ashirin da biyar, sai fahada Nada shekaru Ashirin da biyu ,sai husna tanada shekaru goma sha tara a duniya .

Juwairriya ta zama budurwa ba laifi , sai tsantsar rashin kunya da rawar kai , kasancewar mahaifin ta ya take mata .

Kullum fadan da mahaifiyarta take mata shine ta daina rigima da rashin kunya da rawar Kai , amma Sam juwairriya bataji .

Husna ma kullum cikin yi mata fada take amma Sam bataji.

Suhail da fahat kam ma basa Shiga harkarta dan gudun rashin kunyarta .


Zuwa yanzu tana S.S two a school , makaranta kuwa tana Aji hudu .

Tun a wanan lokacin samari sukayi mata caaa mai Santa da aure da kuma akasin haka , amma Sam samari ba sa gabanta , dan kuwa duk Wanda yazo gurinta da sunan soyaiyya to sai ta mishi rashin muntunci , dan ta tsani taji ance ana sallama da ita.


Juwairriya kyakyawa ce Ajin farko fara ce sol tana da dan kiba kadan , baza,a cemata doguwa ba ba kuma za,ace siririya ba , baza,ace mai kiba ba , Shiyasa tun yanzu da take da shekaru goma sha bakwai samari sukayi ca akanta .

A kullum burin babbanta shine tayi zurfin karatu dan yasha Alwashin bazai yi mata aure a karancin shekaru ba , sai ta zama cikakkiyar mace , kuma itama Juwairriyan tayi na,am da hukuncin da mahaifin ta ya Yanke sabanin mahaifiyarta , dan ita mahaifiyarta a san samun ta tayi ma juwairriya aure dan kuwa rawar kanta yayi yawa , kar tazo ta ja musu abun kunya , amma ganin mahaifinta bai goyi baya ba yasata yin shuru ta bar zancan a cikinta .

Husna da Juwairriya Sam basa shiri , dan matukar husna zata fadawa Juwairriya gaskiya to sai sunyi fada .


Kwance take a daki tana danne _dannen waya kasancewar anyi hutun school da madarasah .

Anisa ce ta shigo , da sallama , wani ihu tasa tace," shegiyar kaya daga Ina??.
Dariya Anisa tasa tace," hummm wallahi daga gida mana kinsan har na kwanta barci mutumin ki ya kirani wai dan Allah in zo gidanku yanasan jin muryarki wai kwana biyu da bakya zuwa makaranta baya ganinki ya missing dinki , kuma yasan da zaizo gidanku ba zaki fito ba .

A zabure ta tashi tace," kinsan bana San rashin mutunci , dan kin rainamun hankali shine zaki wani zo kice zai kira yaji muryata , nifa tun wuri ki fadamishi wallahi bana sanshi yaje ya nemi wata amma ba juju ba ehee, ni juju nafi karfinshi ehe garama tun wuri kisameshi ki fada mishi , tafada hade da galla wata uban harara hade da murguda baki .

Murmishi Anisa tasa tace," humm lallali juju , kina hauka ne ?, ace mutum kamar wanan yazo yace yana sanki amma ki watsa mishi kasa a ido ki 'ki yarda wallahi da ana canjan soyaiyya to ina me tabbatar miki da na canje ki a gurinshi , ina ma ace ni yace yana so ke bakya ganin inda'Yan mata suke sanshi suke rubibi akanshi amma ke kice bakyasansh.... saurin dakatawa tayi da zancanta tayi saurin fadin," wai ma wa kikeso?? da har kika kasa bashi dama , waye Wanda ya kanainaye zuciyarki kika kasa ba Wanda yake matukar kaunarki dama??.

Wata Uwar harara Juju ta wurgama Anisa tace," ke tunda Mike dake kintaba ganin na Amince da soyaiyyar wani ?? Kuma kin taba gani wani yazo gurina da sunan hira ??

Toh wai ke miye nufinki , daman duk samarin da kike hulda da su kawancene kawai ba soyaiyya ba ?? nufinki bazaki kula kowa ba kenan ?? Anisa ta fada cikeda mamaki .

Cikin fad' a juju tace," wai ke Anee miye damuwarku dudu nawa nake , just fa kawai girman jiki ne I am only seventeen years , shine duk zaki daga mun hankali da maganar wasu samari , ni wallahi duk wa inda kike gani muna tare dasu duk basa gabana Sam adaiyi sha,ani kawai amma wallahi ba soyaiyya Mike ba .

Shigowar husna ne ya katse musu zancan su ...

Kallan juwairriya tayi rai a bace tace," wai ke Juwairriya meke damunki ?? meyasa bakida kirki ne , kullum sai a dinga miki magana ba kyaji , in kin ga dama ki tashi kije wa inda kika gaiyyata gashi sinzo suna nemanki sai ki tashi kije ki sallamesu ai Koh, Tana fadin haka ta fita Rai a bace.

Cuno baki juwairriya tayi tace," sai kiyi , ta gala uban harara .

Kallan Anisa tayi tace," tashi ki rakani .

Tashi tayi batareda tace komai , ta dauki gyalenta itama juwairiyan ta dauki nata gyelen suka fita a tare.

zaune ta samu mahaifiyarsu a falo kallanta tayi tace, " juwairiya meyasa bakyaji ne , Ke kullum kidinga kwaso Mana tarikice kofar gida , naga ke kikace ba aurena a gabanki ,to miye dalilin ki na gaiyyatar Samari kofar gidanan, in auren kikeso ki fada sai a miki , amma kar ki Kara kawo saurayi kofa gidanan matukar ba auren ne a gabanki ba , ke ko Kadan bakya koyi da halin 'yar uwarki husna, kin dauki bazanzar rayuwa da rashin kamun Kai , ke haka kika ga yafi Miki?? ko dan kina ganin mahaifinki ya daure miki gindi Shi ya baki damar yin duk wani abu da Kika ga dan'ma , to tun wuri ki farga kinji na fada miki in ba haka ba kuwa wallahi Zan Bala,in Bata Miki rai kuma lallai zamusa kafar wando daya dake a cikin gidanan kinji na fada Miki .

Tunda mahaifiyar juwairiya ta fara magana , juwairiya ke kallanta , tana gamawa kuwa taja hannun Anee suka fita batareda da tace komai ba .

Mamaki sossai Abun Yaba mahaifiyarsu , cikin ranta take fadin wani irin tarbiyya Juwairiya ta dauka tayi...


Read / Download A SANADIN KUSKURENA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album