Join Our WhatsApp Group

LADIDIN KAUYE Complete Hausa Novel Document by LADIDIN KAUYE


LADIDIN KAUYE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38876



LADIDIN KAUYE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 14, Apr 2023

Author: Mom Islam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08141799224

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 222.34 kb

File Type: txt

Views: 1667+

Download: 612+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: *LADIDIN KAUYE*



_funny & love story._




*Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa*


*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*_


*AND NOW*


*LADIDIN K'AUYE*


~MALLAKAR~ ZAINAB HABIB (mom Islam ).

*GODIYA* ina ƙara miƙa godiya ta ga Allah maɗaukakin sarki Wanda yabani ikon sake rubuto muku wanan ƙayatacen labarin cikin hikimar sa da iyawarsa Allah nagode maka.


*GARGƊi*_wanan labarin ƙir ƙirane ban yishi dan wani ko wata ba nayi shine dan ni shaɗii da ban dariya in yazo dai dai da rayuwarki /ratuwarka to hasa shene kawai._



🤏ban yarda wani ko wata su juyamin labari ba duk Wanda yayi yinkurin yin hakan to shida rabil izzati🤙.

08141799224

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




*EPISODE 1&2.*


📖____Yarinya ce ƴar kimanin shekara goma sha biyu da aihuwa sanye take da rigar atamfa da wandon yadi.

Tafiya takeyi tana waƙa da zabgegiyar bulala a hannun ta me rake ta hango da gudu ta ƙarasa gurinshi yana ganin ta ya washe jajayen haƙoransa kana yace "LADIDI daga ina kika fito haka"¿. Ɗaukar rake ƴan hamsin tayi kana ta ce "daga gida mana".

Ganin LADIDI ta kusa shanye rakeb hannunta tana shirin ɗaukar wani ido ya zare mata kana yace "ke baki da hankali ne kin ɗauki raken hamsin banyi miki magana ba yanzu kuma zaki kuma ɗaukar wani". LADIDI dake ta shan raken ta yawu nazuba a bakinta tace "wlh ko kabani raken in daɗa ko kuwa yanzu kaci najaki".
mai raken da aƙalla yayi sa,an baban ta dubanta yayi kana yace "yarinya ki wuce kitafi sabgar ki , LADIDI daketa juya bulala tana dariya tana kallonsa.

mai rake ne yace "yarinya ni natafi kiyimun addu,a yau inyi ciniki LADIDI ce tadubi mai rake tace "karka damu".

Mai rake ya juya zeja baron rakenshi yaji saukar bulala dur ƙusawa yayi yana ihu yana sosawa juyawa yayi yaga babu LADIDI babu samatan ta .


Gudu takeyi har ta isa gidansu , gidane ma dai daici kewaye yake da katangar kara.
YADIKKO na surfen dawa ko sallama batayi ba tashige ɗakin data ke kwana tarufe ƙofa YADIKKO tarasa abinda zatace ta girgiza kai ta ɗaga hanu tana rokon Allah yashir yamata LADIDI.

Kayan wasanta ta ɗibo kai tsaye gurin bishiyar kukar data mamayi filin tsakar gidan tanufa YADIKKO tana wanke dawar data surfa ta dubi Ladidi kana tace "bana ce ki dena zuwa gurin bishiyar nan ba¿.
LADIDI ce ta turo baki tana ƙananun maganganu YADIKKO ce ta riƙe haɓa kana tace "to kodai kin kwaso aljanu ne tunda kin nace da zuwa gindin kuka ita dai LADIDI bata kula YADIKKON ba taci gaba da wasanta .





YADIKKO ce take ta ƙwalawa Ladidi kira tasowa tayi tana bubuga kafa nera goma ta miƙawa LADIDI kana tace "ki ɗauki waccan dawar ki kai ingin Shafi,u kice ya miki yanzu .

Ɗauko mayafinta tayi ta ɗaure a kwan kwasonta kana ta ɗora markaɗen a kai .


Tana cikin tafiya taci karo da me awara ajiye nikan tayi kana ta kirashi tunda yaron ya tabbatar LADIDI ce me kiran har ze kwasa da gudu ta riƙoshi kana tace "ina zaka dan uwarka kasanni kuwa¿".



Dur ƙusawa yaron yayi kana yace "LADIDI kiyi hakuri talle mai ƙeya tayi kana tace "nawa nawa awaran¿

"Biyu biyar yaron yace saboda a tsorace yake Ladidi ce ta haɗa guda huɗu a guri ɗaya tacewa yaron naci biyu ƙara ɗibo huɗu takumayi tace naci na kuɗina saura ala koro nan yaron yadu beta yace "wlh LADIDI goggo na ta hanani LADIDI ce ta buge mai baki ta ɗiibi biyu.

Seda yaron yayi nisa sanan yace LADIDI bogaza Allah ya isa LADIDI tayi ƙwafa tasan ko ba komai taci awarar goma a talatin.

Nikan ta ɗauka tana zuwa dai dai ingin ɗin Shafi,u tace nakawo niƙa Shafi,u daketa nikan shi be kulata ba magana taƙarayi amma yaƙi kulata ramin cinnaka tagani kusada ƙafar shi ɗaya ta ɗauka tasamai a takalmin ƙafarshi takuma ɗaukar ɗaya tasamai a gefen rigarshi ragowar ɗayan tasa mai gurin da taga ya yage a rigar komawa gefe tayi kana tahau waƙe waƙenta .

Shafi,u ne yafara jin cizo ta kafa ze sosa yaji cizo ta kanshi yakai hannu ze Sosa kan yakuma ji ta jikinshi a she cinnaka har cikin wandon shi ya shige da gudu ya fice a ɗakin niƙan yana ihu LADIDI babu abin da takeyi in banda dariya shafi,u ne yayi hanyar gidansu yaje tsallaka murhun girkin gidan yataka tsakiyar murhun a she da wuta kwanciya yayi yana birgima an rasa meke damunshi sedai yasosa nan ya Sosa can LADIDI kuwa tunda Shafi,u yafice take gurin ingin niƙan dama ta iya tana gama niƙan ta daura a kanta tana tafiya tana dariya tana faɗin "dama nakashe goman YADIKKO gashi nasami niƙa a sabill.


Tana tafiya taci karo da wani me rogo dafaffe tsareshi tayi kana tasauke nikan ta dubeshi tace "mai rogo akwai ala koro¿." mai rogon nne ya galla mata harara yace "dan uwarki wanne kora dazan baki ala koro LADIDI ce tazaro ido kana tace "uwata fa kazaga mai rogo ne yace me kika isa kiyi jibeki kamar buhun alabo .

Be Ankara ba LADIDI ta ɓarar da tiran rogon kasa takwashi wanda zata kwasa tazo guduwa mai rogo ya riƙota faɗawa tayi kanshi tahau ruwan cikin shi tadinga kai mai duka baji ba gan.


Hakuri yashiga bata ɗagashi tayi kana ta ce "baka ganni yar ƙarama ba shine kakeson cin uwata a banza me rogo ne ya miƙowa LADIDI na ashirin ya zura da gudu .


Cigaba tayi da tafiyar ta har ta isa gida YADIKKO ce tace "LADIDI baky ajin faɗan da nake yi miki ko ¿.

sauke nikan tayi kana tace "YADIKKO zansha ruwa.

YADIKKO dake ɓarar gyaɗa tace "wlh ke da yar kishi yace kin shiga uku LADIDI ce kamar an tsikareta ta zabura a guje tafice waje.


Ƙarar mota ,
taji gurin masu motar tanufa ɗaya daga cikin su ne yadubi Ladidi kana yace "baiwar Allah tambaya muke yi" Murguɗa musu baki tayi kana tace "nifa banason kinin bibi zakayi magana kana wani tsari ɗaya daga cikin motar ne yace kiyi hakuri yammata dama muna neman mallam Adamu ne.

ta6e baki tayi kana tace "nasan gidan amma saidai inzaku sani acikin wanan akori kurar.

Wani daga cikin motar da tunda ɗayan yafara magana shi beyi ba leƙowa yayi ta cikin motar kana ya ce "ubanwa kika gani a akori kura¿.


Murguɗa mai baki tayi kana tace "karka ƙara zagina na kusa da shine yace Humaid mu lallaɓata ta raka mu .


Buɗe mata murfin motar Humaid ɗin yayi shigowarta keda wuya sukaji motar ta game da wari kamar anyi tusa Jalal ne yace "Humaid bakaji wani wari ba dede lokacin da warin ya iso hancin Humaid sun rasa meke wari a motar LADIDI ce ta dube su tace sewani toshe toshen hanci kukeyi sekace wasu malaman.

Duban tsafta Humaid ne ya ce wlh ga meyin warin nan hatta bakin ta wari yakeyi LADIDI data tabbatar da ita akeyi ciro alurar ɗinkin hannu tayi kana ta waiga taga Humaid ɗin yadena kallonta murmushi tayi kana tayi gefe da hannun ta sokawa Humaid alurar ihu Humaid yakeyi ba k'a kau tawa Jalal ne yafaka motar kana yazo gurin Humaid ɗin dake faman ihu LADIDI ce ta dubeshi kana tace "meyasa meka ne ɗan gayu¿

cikin su babu wanda ya kulata bare su waigo ta Humaid ne yace ja motar Jalal muyi sauri mu isa gidan .


Sun zo dai dai k'ofar gidan LADIDI tace "to munzo seku fito Humaid dake ɗin gisa ƙafarsa yace "to ai seki koma tun da kin rako mu. Zaro ido waje tayi kana a zuciyarta tace lallai wannan besan ko wacece LADIDI ba .


Duban ƙafar Humaid ɗin LADIDI tayi kana ta fashe da dariya Humaid da babu halin gudu ya dura mata zagi Jalal ne yace "tunda ta nuna mana ƙofar gidan to muje ka kyale yarinyar nan .


Hango wata zabge giyar sanda tayi ta ɗauka kana ta gyara bakinta seda tabari Humaid yazo dede saitin shiga gidan ta zula mai a kafar da tayimai allura zubewa yayi a ƙasa yana ihu da gudu ta ƙasa...

Malam adamu ne yaj ihu kuma na babban mutum da sauri ya ƙaraso Jalal ne yace "barka malam , malam adamu ne yace a,a wana ke gani kamar yan birni¿

Jalal ne yace "malam mune wata yarinya ce tara komu gidanka gashi ta bugawa Humaid sanda a ƙafa ta gudu ,malam yajin jina zancen kana yace "nasan ba wata bace illa LADIDI wannan aikin seita .


Humaid ne yayi ƙarfin halin magana yace "Jalal kaje kane momin yarin yar nan senaga waye ubananta.
Malam adamu ne yace "wlh gara ka hakura saboda wanan yarinyar ana tunanin tana da aljanu ......✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽.





*_~MOM ISLAM CE✍🏽.~_*

*LADIDIN ƘAUYE.*



_funny & love story._

*Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa*


*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:ZAINABU ABU*


*_AND NOW *_

*LADIDIN ƘAUYE.*



*BIMILLAHEER RAHMANIR RAHEEM.*


*EPISODE 3&4.*


___malam adamu ne yayi musu nuni dasu ƙarasa cikin gidan inna Hauwa matar malam Adamu ta na ganin su ta shiga yi musu sanu da zuwa d'akin malam Adamu suka wuce kai tsaye Humaid ne yayi rau rau da ido kamar me shirin yin kuka yace "Jalal please help me jalal da shima hanka linshi ya fara tashi yace "sorry brother anjima ka d'an zakaji jikin naka ya koma normal Humaid ne a ts,wace ,ya dubi Jalal kana yace "baka san azabar da nake ji bane shi yasa .

Jalal ne ya mik'e jiki babu k'wari yanufi gurin da inna hauwa take tambayar ta yashiga yi akwai asibiti anan kusa¿ inna hauwa dake dama fura da nono ta ce "eh akwai amma fa akwai tafiya sosai Jalal ne yace indai akwai barin yiwa Humaid magana mutafi inna hauwa ce ta kwala wa malam adamu kira shigowa yayi d'auke da ledar lemu da ayaba da kankana ajiye ledar yayi ganin yanayin Jalal malam Adamu ne ya ce har yazu jikin humidun ne eh Jalal ya ce asibiti nakeso mu kaishi ko aliura ayi mai .

Shiga d'akin sukayi suka temaka mai ya mike suka sa shi a mota seda suka yi tafiya me nisa kana suka shiga asbitin .

Wani likita ne yazo gurin malam Adamu hannu ya mik'awa malam Adamu suka gaisa kana likitan yace "baba waye babu lpy ¿.
malam Adamu ne ya nuna Humaid da zazza6i yarufeshi ri rik'eshi sukayi yanuna musu d'akin kwantar da marasa lpy ruwa aka fara samai kana aka yimai allurori bacci ne ya d'auke shi me nauyi Jalal ne yaji cikin shi na kukan yunwa mik'ewa tsaye ,yayi kana yace mala barin d'an fita yanzu zan dawo.

Malam Adamu ne yace ina kuma zaka¿ Jalal ne ya ce wlh am feeling Hungary malam Adamu ne ya zaro ido kana yace naji kamar kace kwan giri Jalal ne ya tun tsure da ,dariya kana yace .

"Cewa nayi ina jin yunwa malam Adamu ne ya ce au to ko in koma gida ne in taho muku da fura da nono ¿".

Jalal ne yace a,a ai dazamu taho naga masu saida abinci malam Adamu ne yayi mai Allah ya tsare Humaid ne ya farka d'auke da salati a bakin shi.

Malam Adamu ne yace sanu Humaidu,, humai ne ya dubi malam Adamu kana "yace yauwa sannu ina Jalal yayi ?".

Malam Adamu ne yace Jalal yaje siyo abinci yanzu ze dawo .

Likitan d'azu ne yashi go d'auke ta ,takaddar salama mik'awa malam Adamu yayi kana ya tambayi Humaid ya,,ya kejin jikin nashi Humaid ne ya ce wlh yanzu babu inda yake ciwo hamdala malam Adamu yayi .

Jalal ne yashigo da ba bbar leda a hannun shi kifi yasiyo soyayye da kuma kaza guda biyu gasassu malam Adamu ne yace duk wanan kayan ina za,a kai su lemun kewalba ya mik'awa Humaid da kifi domin Humaid d'in ma,abocin son kifi ne jalal ne ya d'auke kaza guda daya ,ya mik'awa malam Adamu .


Malam Adamu ne ya e a a ni bazan ci ba ,dole dai seda ya kar6a tukun ya d'an sha lemun ya barsu a gurin ya nufi masalaci.

Suma bayan sun gama sallah sukayi kana suka biya likita kud'in shi ,suka hau mota suna cikin tafiya suka hango Ladidi tana jifan mangoro abishiya Humaid ne ya dubi jalal yace tsaya ga mahau kaciyar ,yarin yar nan .


Malam adamu ne yace kufa kiyayi Ladidi kotayi lefi babu me d'aukar mataki Humaid ne a zuciye ,yace wai malam wanan yar gidan waye ¿malam adamu ne ya ce yar gidan amini na ne malam musa.


Humaid ne ya ce dan Allah malam kabari ,inkoya mata hankali malam adamu ne ya ce jalal kawuce mutafi na gaya maka kar katsaya .

Humaid ne ya lek'a ta window yace ke Ladidi wlh kinci bashi zanga uban daya tsaya miki a fad'in a kurkin k'auyen nan .

Ladidi ,da kamar jira takeyi ta sami abokin fad'a dagudu tayi ,yo gurin motar amma ina jalal ya k'ara gudun motar duwatsu tasamu tanata kai jifa amma babu sa,a jifan data kai na k'arshe se a bayan wani bafula tani yana tsugune a wata gona yana kashi yaji ,jifa a bayan sa dasauri yaja wandon sa ya rik'e yana ihu Ladidi data lura tayi mugunta tazo guduwa bafula tani yace yau k'aryar ki takare kamota yayi kana ya dunga dukan ta .


Yana saketa ,ta mul mulo zagi shikuwa bafula tani dayaga Ladidi tafi k'ar fin shi ya shemeta da sanda ko motsi bata yi .




*_FARKON LABARI*_
Malam musa shine ma haifin Ladidi ita kad'ai Allah ya basu tun tana k'arama bata ji ko,kad'an bare duka shima be dame taba abota ce me k'arfi ta shiga tsakanin malam musa da malam adamu mutanen kirki .


Malam Adamu shine k'anin mahaifin su Humaid da jalal ma haifin su Humaid wato alhaji abdullahi tun bayan rasuwar mahai finsu wato kakan su Humaid kenan da mahai fiyar shi. ya had'a kayan shi yatafi neman ilimi shi kuwa malam adamu be bi d'an uwan ,nasa ba ya zauna ,yana koyar da almajirai .


Shigar dadyn su Humaid garin jos ya had'u da wani bawon Allah ya d'aukeshi zaman shagon atamfofi suna samun alkairi sosai saboda alhaji abdullahi akwai amana baya cin kayan da bana shiba shiyasa yake zaune lpy da mutane.

K'watsam wata rana uban gidan shi yabashi kyautar wani katafaren shagon da yagina had'i da bashi kaya masu yawa acikin lokaci k'alilan kud'i suka bunk'asa uban gidan nashi ne ya cire kud'in shi kana yabawa alhaji abdullahi ribar halak d'inshi ne yana juyawa...


Read / Download LADIDIN KAUYE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album