Join Our WhatsApp Group

ZAINABU ABU Complete Hausa Novel Document by ZAINABU ABU


ZAINABU ABU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14019



ZAINABU ABU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 11, Apr 2023

Author: Zainab A Barde ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ALƘALAMI YAFI TAKOBI ????️ WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 07048614405

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 75.91 kb

File Type: txt

Views: 1560+

Download: 297+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: ✨✨ ZAINABU-ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE


🖊️ALƘALAMI YAFI TAKOBI 🗡️ WRITER'S ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)


Free page 1 nd 2

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM, DA SUNAN ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI, MAI RAHAMA MAI JINƘAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU KARA TABBATA GA FIYAYYAN HALITTA SUGABAN MU ABIN KOYIN MU, SHALELEN UBANGIJI, NA KHADIJA ANGON AISHA, DAN AMINATU RASULILLAHI ANNABI MUHAMMAD S.A.W, YA ALLAH INA ROKON KA, DA SUNAYENKA MASU TSARKI, DAN ANNABIN KA, DA ALKUR'ANIN KA, ALLAH KA JIƘAN MAHAIFINA, (ALHAJI ADAMU BARDE) DA SAURAN IYAYEN MU DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA, IDAN TAMU TAZO ALLAH KASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI, AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM...
YA ALLAH YADDA KA BANI IKON FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI LFY, ALLAH KASA NA GAMA SHI CIKIN NASARA DA KOSHIN LFY.


****


Juyi kawai takeyi, saboda hayaniyar yaran da suka hanata bacci, bargon ta jawo ta tura kanta a ciki wai ko zata daina jiyo hayaniyar yaran, amma ina kamar a cikin dakin suke hayaniyar, dagon tsaki taja tana fitowa daga ciki bargon, fitowa waje tayi inda yaran suke zagaye da wata tsohuwa, "Anna ni ta hamsin za'a bani","Anna ni kuma ta ashirin","Anna wllhi ni za'a fara bawawa, ai na rigasa zuwa","wllhi baku isa ba ni za'a fara sallama","duk kuyi hakuri za'a sallami kowa yanzon nan" bayan ta karewa yaron kallo da kowa burinsa a sallame sa, wani takaici ne ya rufeta na tashinta daga daddadan bacin da takeyi, tsaki taja a karo na farko, ai da sauri yaran suka jiyo ganin wacce ta fito yasa sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su, lokaci daya suka natsu saboda ganinta, Anna kuwa jin shirun yayi yawa yasata dagowa, murmushi tayi ganin ashai dodonsu ce ta fito, daya daga cikin yaran ne yayi tsuru tsuru, irin na mararsa gaskiya.




Shako masa wuya tayi, "dan buhun ubanka wana kama, dama na gaya maka zaka shigo hannu, wato ranar saboda kaga a gaban uwarka ne harda zagi na ko aiko yau zaka gayawa yan garinku" marinsa tayi aiko yaro ya fashe da kuka, wani marin ta kuma kifa masa, aiko nan yaro ya fadi kasa yana kuka, duk da haka bata kyalesa ba saida ta kuma marinsa, hakan ma ta kyalesa ne saboda maganar da Anna takeyi mata, aiko yana ganin ta kyakesa ya zura a guje yana fadin "Wllhi saina gayaki da mamana" dariya ta barke da ita, "yoo uwar takama in tayi lakada mata na jaki zanyi banlantana kai karankada miya, ku kuma kallon mai kukeyi min" ai dandanan suka sunkuyar da kai kasa, "kuma bari kuji na fada muku wllhi daga yau, in kukazo siyan waina kuka cikamu da surutu, wllhi sai naci uwar mutum kai harda uban ma, ko bakuji mai nace ba" ta daka musu tsawa,


A firgice yaran suka hada baki wajan fadin, "munji","karma kuji jikin mutum nai dai zaiyi tsami, ehhe","kekam Allah ya shirya min ke, na kula so kike ki korar mun yara, su daina zuwa suna siyan waina ta","yoo dan ubansu su daina zuwa mana, suga yadda zanje har gaban uwar yaro inyi kuli kulin kubura dashi" girgiza kai kawai Anna tayi, tama rasa abinda zatace, nan dai ta sallami yaran, hada kwanikan tayi, ta kaisu wajan wanke wanke, daganan ta share gidan sab, wanke wanken tayi, tare da sharo dakunan, saida ta gyara gidan sab sannan tazo ta zauna a kusa da Anna,



"Jikalle ta maza kici abincin in aike ki wajan Hannatu ki karbo min kudina, kusan sati kenn taƙi ta bayar","ai Anna bar karyawar nan bari naje na fara karbo miki kudin, yoo mu har akwai wanda zaici mana kudi a kwayen nan ya zauna lafiya ne","aa jikalle ki fara karyawa tukunna","sai kiyi kuma, saina amso kudin sannan hankalina zai kwanta, kinsan ni fa masifa har cina take in ban samu abokin fada ba" tana gama fadin haka ta zuba sudaddun silifas dinta tayi waje,



"Ya Allah ina mai tawassali da sunayan ka tsarkaka ya Allah, Uban giji ina rokon ka da fiyayyan halitta Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam ya Allah, Allah ka shirya min yarinyar nan" ta daga hannu tana rokon Allah, saboda kullum abubuwan nata gaba gaba suke karayi, saidai shiriyar Allah kawai,



Tun daga naisa yake kwala mata kira, amma ko gaizo batayi ba, ta ci gaba da tafiyar ta, bawai kuma dan bata jisa bane, ta jisa tsarai yan wulakancin ne a kanta, "Zainabu Abu" ya kuma kiran sunanta a ɗai ɗai lokacin da yake karasuwa, "haba masoyiyata Abu, inata kwalla miki kira amma baki jini ba","waya gaya maka cewar ban jika ba, najika sarai gadamar tsayawa ne banyi ba, koda akwai wani abu" ta fada tana jijjiga jiki tare da yin fari da ido, "haba masoyiyata Zainabu Abu mai tagwayen suna","kaga dakata Bala, kalle ni da kyau" kallonta yayi tundaga sama har kasa, "ka kalle ni ko?","ehh na kalle ki","nayi maka kala da wacce zata kula ka, ko wani daga cikin kwauyen nan, duk kanku banga sa'ana ba a ciki, dan haka ni kaga tafiyata" tsororo ya tsaya yana kallonta, kamar wani soko, dan dama ba yau ta fara masa rashin M ba, dandai bazai iya rabuwa da ita bane, saboda duk tafi matan kyauyen kyau, Zainabu Abu kenn, ga kyau ga diri, ga rashin mutunci ga rashin kunya, duk ta hada,




"Haba masoyiyata Abu, wai mai yasa kike min hakane?","mtwss sai kayi kuma, mutum sai kace maye, ance ba'ayi dashi amma bazai hakura ba, ni kaga tafiyata, kai kuma sai kayi ta tsayuwa a nan tunda bakada aikin yi, nikam ina dashi" tana gama fadin haka ta bugawa bujenta iska, shi kuwa kasa cewa komi yayi, badan soyayyar da yake mata ba, ina zai tsaya tana fada masa bakaken maganganu,


"Assalamu Alaikum, Salamu Alaikun ta fada tana bubbuka kofar langa langar, ko mutan gidan basa nan ne? inma basa nan ina nan babu inda zanje, in kuma sunanan su fito yau yan rashin mutunci ne suka kawo ni, ehhe" hannatu da take kashi a bayi, tunda taji sallamar Zainabu Abu, hantar cikinta ta kada, tasan duk lokacin da akaga Zainabu a waje to ba mutunci ne ya kawo ta ba, ko gama kashi batayi ba, ta wanke ta fito,



"Aa yausu Zainabu Abu ne a gidan namu","kinga dakata Hannatu, miko min kawai, kudin Kakata Anna na tafi, dan ba wani dogon zance ne ya kawo ni ba","dan Allah Zainabu kice mata tayi hakuri, wllhi zan kawo mata har gida inna samu","kutumar uba, ai wllhi baki isa ba, inkinga na bar gidan nan to kin bada kudin nan","dan Allah Zainabu, wllhi banida su, dan Allah kiyi hakuri, dana samu zan kawo" Hannatu ta fada tana marairaice fuska ko Zainabu zata tausaya mata ta kyaleta, murmushi Zainabu tayi tana fadin "toh shknn, amma fa ki kawo mata, nace kifa kawo mata kudin ta","insha Allah zan kawo" ta fada tana murmushi, ai Zainabu Abu harta kai bakin kofa, ta dawo a guje ta dauke waken dake cikin kwarya, da akalla zaikai kwano daya, "ke a ganinki zanyi zuwan banza ne, to na dauki waken nan a madadin kudin, inkin gadama ki biyoni da kudin gida ki karbi waken ki, inko kika bari yakai gobe wllhi bazan bayar ba" ta fada tana zurawa a guje .


"Na shiga uku ni Hannatu" da gudu itama ta biyo ta kofar gida, amma ina hartayi nisa, "keee! Zainabu dawo ki karbi kudin ki, ki bani wake na, akan dari biyu zaki dauke min waken dubu da dari biyu","ba kince bakida kudi ba, to kije ki rike kudin ni kuma in rike waken" ta fada da karfi yadda Hannatun zata iya jiyota","ni wai maima yaja min na ciyo bashi a gidansu Zainabu, gashi yanzo ta dauke min waken Alalata.



Koda ta baro gidansu Hannatu bata zarce ko ina ba, sai shagon Dan Liti, tunda ya hangota ya fara mata kirari "kaga Zainabu Abu, jika a wajan Anna, mutum ya tabaki ya tabowa kansa masifa","fadi ka kara fara Dan liti mai kwalelen kai" turbune fuska Dan Liti yayi, dan ya tsani ta kirasa da mai kwalelen kai,"wake na kawo maka ka siya","yoo banda abinki Zainabu, ai bama siyan wake saide mu siyar","aiko dolen mutum ya siya ehhe","haba Zainabu ina dole a nan, nida zan siya, lallaba nifa ya kamata kiyi in siya"



"Kan uba, nabi lallabawa da gudu dan ubanta, dan Allah dan Liti karka siya kaji" ta fada tana ajiye kwaryar, dan kwalin kanta ta kwance ta dora shi a kugu, jiki ta fara girgizawa tana fari da ido, "zaka siya, ko kuwa mu raba dan halin","kinga Zainabu zan siya, ni banason fitina, ke bakijin kunya wani yazo wucewa yaga kinci damara haka","yoo aini abin kunya gaba na basa ba baya ba, kaga nifa banma san maine wani abu waishi kunya ba, danma ka sani","niko nafi kowa sani Zainabu, nawa zaki siyar da waken","nawa kake siyar da wake?","dubu da dari biyu","to nima haka zan siyar maka","to ai nima zanci riba ko, saide ki siyar min dubu daya" wani banza kallo ta watsa masa, "kaga nayi kala da wacce za'aci riba a wajanta?" ta hayayya ko masa, "naji zan siya a hakan", "da dai yafi maka" kudin ta ya lissafo mata ya bata, waken ya karba ya juye sannan ya bata kwaryar ta, harta kai bakin kofa sannan ta juyo tayi masa kallon shatara saura kwata, "da baka siya ba ai, da kaga yadda zanyi maka","jike dai jarababbiya kawai" harta fara tafiya taji abinda yace ta juyo, "mai kace","aa ni bance komi ba" ya fada yana zazzare ido, "daka maimaita ai".





Shere Fisabilillah
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



🖊️ALƘALAMI YAFI TAKOBI 🗡️ WRITER'S ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)




Free page 3 nd 4


Arewa Book @Zainababarde1



****

Akan hanyarta ta komawa gida ta hadu da Safara'u ta debo ruwa, ita bama ta kula da ita ba, kudin hannunta ta daure a habar zani, sannan ta cakwali gaban rigarta, "ubanwa na kama","dan Allah Zainabu kiyi hakuri, kinga inna tace ta aike ni na daibo mata ruwa zata duro girki","cha cha cha, dalla rufe min baki kafin in fasa shi a nan wajan, dama gashinan kamar na biri, kinga sai na kara tabar dashi, sauke ruwan kanki","dan Allah kiyi hakuri","zaki sauke ne ko Aa" ta fada tana kankance ido, sauke ruwan Safara'u tayi, idonta na tara kwalla, ai tana sauke ruwan Zainabu batayi wata wata ba, ta dauki ruwan ta shaika mata shi, tundaga kanta har kasa, kuka Safara'u ta fashe tashi, ganin wannan wulakanci da Zainabu tayi mata, "gobe ma ki kara tsokanata kiga yadda zanyi maki" ta fada tana jefa mata bokitin tare da karawa gaba, durkushewa safara'u tayi ta fashe da kuka.




Tana dab da shiga gida tayi cilli da ƙwaryar tare da shigewa gida, sallama ta rangada tana kwala kiran sunan Anna, "ni wai lafiyan ki kike kwalla min kira haka?","lafiya lau Annata, dama kudin ki na karbo maki, gasu ma" ta fada tana ciro su daga habar zani, dari biyu ta bata, "ahh ni Anna yau wace rana Hannatu tayi biyan bashi ta dadin rai" ai bata gama rufe baki ba saiga Hannatu ta fado gidan kamar an jefota daga sama, "Anna ga kudin ki, ki bani wake na","wana wake kuma?","waken da Zainabu ta kawo maki mana","ni bata kawo min wani wake ba, kudine ta kawo min kuma gasu" ta fada tana nuna mata dari biyun,



"Kee! Zainabu ina wake na?","ban gane ba wana wake kike magana akai, kin bani wake ne?","waken da kika dauka a cikin ƙwarya na alalata","kinga malama ni ban daukar maki wani wake ba, kinje chan wani ya daukar maki wake zakizo ki lakabamin, banji ba ban gani ba" ta fada tana murtuke fuska a dole ba ita ta dauka ba, Hannatu zata sake magana Anna ta dakatar da ita, "kinga Hannatu tun muna shaidar juna ki fitar min daga gida, baza kizo har gida kice jikalleta ta daukar maki wake ba, bayan kuma bata dauka ba, dan kinyi biyan bashi, kuma shine harda sharri, to wayace kici bashin?","wllhi Anna wake ta daukar min da nace mata banida kudi, kuma Alalar siyarwa fa zanyi","kinga ki fitar min daga gida tun muna shaidar juna, kije ki naimi wanda ya daukar maki wake tun lokaci bai kure maki ba","Anna dan Allah kisa baki ta fada min inda wakena yake","Anna bari na fitar da ita tunda bazata fita ba" nan ta fara tura ta harta kaita kofar gida sannan ta hankadata, "gobe ma ki kara cin bashin Annata, kuma kiƙi biya kiga yadda zan maki" ta fada tana shigewa ciki,



Hannatu kuwa hannu ta dora a ka, tama rasa ihu zatayi ko kuka, a dakeka sannan a hanaka kuka, amma bataga laifinsu ba laifinta ne, da bataci bashin su ba, da duk haka bata faru ba, garama ta tashi tasan inda dare yayi mata, dan tasan kaf garin nan babu wadda ya isa ya karbar mata waken ta, har mai gari da kansa, saboda masifar Anna da jikarta Zainabu, tashi tayi ta kara gaba tana matsar kwalla.



Koda Zainabu ta koma cikin gida abincin ta taci tasha ruwa, ta godewa Allah, "Anna bari naje gidansu siyamah kafin lokacin dora abincin rana yayi, saina dawo na tayaki","sha zaman ki jikalle ta, dan nasan ma ba dawowa zakiyi da wuri ba, karki min wani dadin baki, in kuka hadu da ciyama ai baƙu sanin lokaci yayi","nace maki Siyamah ake cewa ba ciyama ba, ina gyara maki ne dan kar wataran ki kunyata mu","naki na fada yadda kikace din, yadda na iya haka zan fada, yar bantan uba" dariya tayi tana ficewa daga gidan.



Koda taje gidansu Siyama, tararwa tayi innarta batanan, ita kuma tana wanki, "ƙawata ashai dai zakizo","kin manta wace Zainabu Abu ashai, bata saba alkawari, tunda nace miki zanzo to zanzo" murmushi Siyamah tayi, nikam ai nafi kowa sanin ƙawata, kinji labarin anjima da daddare za'ayi babban wasa a dandali","wasan mai?","kin manta gobe ake aurar da yar gidan mai gari" tabe baki tayi "kinsan fa ni abinda ya dame ni nakeyi, ban shiga abinda bai dame ni ba","amma dai zamuje ko?","gaskiya ba zanje ba, amma in kinga kinason zuwa zaki iya zuwa","dan Allah ƙawata ki bari muje" zata sake magana, siyama tace "dan abotar mu fa" girgiza kai Zainabu tayi dan tasan abinda zatace kenn dama, "shknn inkin shirya ki biyo min sai muje","yauwa ƙawata ko kefa","ina Inna ko batana?"," eh taje gidansu wasila","ki gaishe min da ita in ta dawo","zataji sai mun hadu anjima"



Tana fitowa daga...


Read / Download ZAINABU ABU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album