Join Our WhatsApp Group

MUGUN ALBISHIR Complete Hausa Novel Document by MUGUN ALBISHIR


MUGUN ALBISHIR

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28948



MUGUN ALBISHIR

Reading Time: 2 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gidan Littafi

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 148.78 kb

File Type: txt

Views: 606+

Download: 201+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: Mugun albishir
.
Page 1
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
Na dade ina ganin kyawawan 'yan mata a duniya. Wadanda ke da kyawawan halittu da Kuma kyawawan fuskoki da kowa zai gani ya yaba ya yi sha'awarsu. Sau da yawa irin wadannan taurarin 'yan mata wasu da zarar mun rabu bana sake tuna su a xuciyata, sai ka ce tun fil'azal ban ta6a ganin su ba. Wadansu Kuma a cikinsu jefi-jefi su kan fado mani a rai, da zarar na tuno da kamanninsu sai in yi murmushi ni kadai in sake mancewa dasu. To amma Kuma duk da haka Akwai wata fitacciyar taurarruwa guda daya, wacce duk lkcn da na dubi xuciyata sai naci karo da hotonta dake maqale a ruhina shekara da shekaru.
.
Sunan ta zubaida!
.
Ba zan ta6a mance ranar da na fara ganin ta ba. A ranar wata litinin ne wacce ta xo dai-dai da goma sha hudu ga watan takwas alif dari tara da casa'in da tara miladiyya. Ita ce rana ta farko da na fara karatu a kwalejin ilimi ta tarayya dake a birnin zaria.
.
Ina zaune ni kadai a gefe guda akan doguwar barandar ajin da zamu dauki darasi, ina sanya da farin Wando da Kuma farar riqa mai ruwan qwai dake da jajayen rubutu sirara a gabanta. Sauran dalibai kowa yana ta harkar da ta dame shi. Ana ta kaiwa da komowa da kuma surutai da kuma if-iden matasa 'yan bana bakwai sabbin dalibai.
.
Kamar daga sama, sai na dago kai na hangeta, tana tahowa kai tsaye xuwa gare ni. Tana sanye da shudin leshi da Kuma baqin takalmi. Ta rungumo takardun karatunta a cikin fayil, sannan Kuma ta maqalo baqar jakarta kalar takalminta.
.
Zubaida kyakkyawace!
.
Kada ka zargeni don nayi mata wannan kirarin tun a karon farko. Don kuwa rude wa nayi tun a gani na farko da nayi mata. A rayuwata koda ace bani da qwarewa akan komai, to akwai wani abu daya da na tabbattar na qware akan sa. duk lkcn da na ga kyakkyawr mace ko daga nesa ne, na san a layin da zan ajiyeta, don kuwa na dade ina ganin su. Don haka Zubaida kyakkyawa ce fiye da duk yadda zan kwatanta maka ita a cikin wannan labarin.
.
Ku biyo ni. jimawa kadanmugun albishir
.
Page 2
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
.
Zubaida kyakkyawa ce fiye da yadda duk zan misalta maku ita a cikin wannan labari.
.
Akwai wani yanayi dake tattare da ita, Wanda ke sa mutane su kasa tantance doguwa ce ko Kuma gajeruwa ce? Sannan Kuma yanayin dake tattare da kyakkyawar fuskar mai annuri irin sa ne yanayin da duk lkcn da wani Sauran ya kalleta sai yaga kamar murmushi take yi masa, Wanda na tabbatar hakan ya sha tilastawa daruruwan samari fadawa a cikin kogin qaunarta kamar dai yadda nima na fada tun a karon farko.
.
Na ci gaba da kallon ta lkcn da take tahowa sannu a hankali kamar wata dawisu. Ba ni kadai ba hatta Sauran daliban dake a wajen kama daga 'yanmata har samari yawanci ynx duk hankalinsu a kanta yake, kowa yana so yaga a inda zata yada zango. To amma Kuma abin mamakin ga alama har ynx wurin nawa take tahowa.
'na shiga uku!'
.
Shin damar can ta ta6a gani na ne? Na ji gabana ya fadi. sannan Kuma tsoro ya kama ni. Ban yi mamaki ba don kuwa ta haka nake gane mace kyakkyawa a cikin mata masu al-alfahari da xunxurutun kyau. Da ace ban ji tsoro ba a lkcn da na fara ganin ta, da tun farko ban saka maka ita a cikin layin kyawawa ba, don kuwa ba don ta tafi da hankalina ba da wannan fuska tata mai annuri da duk abubuwan da zasu faru basu faru ba.
.
Ta qariso inda nake ina ta kallon ta ko qiftawa bani yi, ina ta mamakin wannan mace mai qyalqyali kamar tauraruwa sai ka ce ita ta qera kanta a duniya.
.
Ta zauna a kusa da ni muka hada ido, muka yiwa juna murmushi, tuni qamshin turaren dake fita a ji6anta da Kuma daddadan qamshin daya-sayen da ta shafa sun mamaye iskar safiyar da ake busawa. Ta sa hannu ta gyara dogon igiyar kitsonta da ya kusa rufe mata ido a cikin dogayen igiyar kitson da suka warwatsu a kafadarta, Suna ta sheqi da daukar ido. ta ce da ni a cikin sassanyar murya.
.
'sannunka.'
.
Sannan ta kashe mani fararen idanunta dake motsawa tarwai dara-dara kamar gilashi. Na biyata murmushi sannan nima na ce da ita.
.
'ke ma sannunki.'
.
Ta kai ganin ta inda Sauran dalibai ke zazzaune fululu a ko'ina, ta dawo da hankalinta kaina ta ce mani.
.
Qq

"ga alama kai ma irina na ce, baka son yawan surutu shi yasa ka ke6e gefe guda ka xauna anan ko mallam?"
.
Na sake cewa da ita.
.
"gskyrki, Wlh ban cika son yawan surutu ba."
.
Muka yi dariya a lkc guda, sannan ta tambayeni.
.
"ya sunan ka?"
.
Na ce da ita cikin farin ciki.
.
"Suna na mansur. Ke Kuma Fa ya sunan ki?"
.
Ta ce da ni.
.
"ni Kuma Suna na Zubaida
.
Ga al'darmu ta qasar hausa, duk lkcn da irin wadannan hirarrakin suka faru a tsakanin saurayi da budurwa, to ana sa ran soyayya ta qullu. Don haka nima ban yi mamaki ba da naji cikin dan lkc qanqani nkamu da ciwon son wannan 'yar talika mai Suna Zubaida ba." muka dauki lkc zaune a wurin mu biyu muna ta hira gwanin ban sha'awa. A lkcn ne ta sanar da ni cewar ita ma sabuwar daliba ce irina.
.
Duk lkcn da zata sanar da ni wata magana sai in ji bana son tayi shiru, don kuwa daddadan muryarta tafi kama da sarewa, yana matuqar tasiri a dodon kunnena. Bana son in rabu da wannan sabuwar masoyiya tawa, to amma Kuma anyya kuwa ta san cewar na kamu da ciwon son ta? Ban yi tsammanin hakan ba."
.
.
Lp=3Mugun albishir
.
Page 3
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
Madugun taska
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI"bata amince da daukar shafin ba, yin hakan kuskure ne a kula
.
.
Ban yi tsammani ba!
.
Bamu dade ba mallamin da zai yi mana darasi ya xo, nan da nan muka shiga tare da Sauran dalibaI aka soma karatu. Ba wuri daya muka zauna ba." a tsakanina da Zubaida Akwai mutum bakwai, sai dai duk da haka hankalina yana kanta. Wani lkcn kamar a jikinta ta san wani yana kallonta haka kawai sai ta waigo inda nake mu hada idanu. Duk lkcn da zata waigo sai ta same ni ita kawai nake kallo ba mallamin ba, Kuma duk lkcn da zamu hada idanu sai ta yi mani murmushi da tattausan le6enta dake sheqi. Nan da nan naji duk na qosa a tashi darasin, na qosa mu fita waje ni da masoyiyata Zubaida. addu'ar da nake yi a lkcn da muke cikin ajin ita ce. Allah ya sa Zubaida ta fahimci ina son ta, kuma allah yasa ita ma ta amince ta so ni.
.
To amma Kuma a lkcn da aka tashi karatu abin yaxo minn a bazata. Na dauka cewar Zubaida zata tsaya ta saurare ni, mu tafi tare muna hirarmu ta soyayy.
.
Maimakon haka sai ta ce da ni a lkcn da ta fahimci ina son tsare ta da surutu.
.
"to mansur, lkcn xuwa gida yayi, ni zan tafi sai gobe Kuma idan mun sake dawowa."
.
Nayi mata murmushi, kafin in sake cewa da ita wani abu har ta tafi ta bar ni. A haka na tsaya wurin ina ta wasi-wasi da tunane-tunane har daliban da suke a sashen mu suka watse suka bar ni ni kadai A tsa.
.
Me yasa ban sanar da ita ina sonta ba? Na zargi kaina, don kuwa abin da xuciyata ta gani tana so, bai kamata in yi shiru in 6oye a raina ba." bai kamata in yi kawaici in kasa sanar da ita ba." a ranar ban iya cin abinci ba, sannan Kuma barci ma qaurace min yayi kwata-kwata daga idanuna. Muryar Zubaida ta ci gaba da amsa kuwwa a xuciya. A lkcn da ta xo wurina ta zauna. Ba zan manta lkcn farko da ta fara yi mani magana ba."
.
"sannun...yaya sunan ka?"
.
.
** ** **
.
.
Tun ranar da wannan al"amarin ya faru na kasa samun sukuni a xuciyata. Don kuwa duk lkcn da naxo makaranta har qosawa nake yi in nemo ta in ganta don hankalina ya kwanta. to amma Kuma sbd tsananin fargabar da nake yi tun farko da Kuma razana, har aka dauki lkc mai tsawo ban sanarwaa kowa ba a cikin Abokina dake a makaranta. Ina matuqar jin tsoron in sanar da ita, daga Bayani Kuma ta nuna mani rashin goyon bayanta. Shi yasa na 6oye a xuciyata. To amma Kuma a haka zan ci gaba da son wacce bata san ma ina yi ba?"
.
kullum bani da wani aiki da ya wuce tunanin wannan kyakkyawar budurwa zubaida. Gashi kuma ko ho hotonta bani dashi, ballantana idan naje gida in riqa dubawa yana debe mani kewa. Don haka idan naje gida sai dai in kwanta ni kadai a daki in rufe qofa ina ta tunaninta, don Kada wani tunanin yaxo ya katse min hanzarina. Kullum idan ina tunanin Zubaida sai in riqa aiyanawa a xuciyata cewar waigo gashi nan har mun yi aure, muna zaune tare zaman soyayya da qauna a wani qayataccen gida na alfarma. to amma Kuma ni na san cewar Zubaida ba ta ni take yi ba, don kuwa ita a tsammaninta mutunci kawai muke yi irin na dalibai, bata yi tsammanin na kamu da matsanancin sonta ba tun ranar da na fara ganinta.
.
Sannu a hankali da ciwon sonta yayi qarfi a jikina wani lkcn haka kawai bana sanin sanda nake ambaton sunan ta. Sauran da yawa idan nayi shiru ina tunani sai in kira sunantta ba tare da na sani ba." abokaina da basu san me ke faruwar ba idan irin haka ta faru sai su tambayeni ni.
.
"mansur wacce ce zubaida?
.
Duk ranar da Zubaida bata xo makaranta ba, bana iya karatu bana iya magana da kowa, don kuwa duk ranar da na wayi gari ban ganta ba, wunin nake yi da zzazza6i mai zafi. Sai na ganta washe gari sannan nake warkewa. Gashi Kuma Kullum kamar qara kyau take yi. Kullum ta xo makaranta sai in ga tafi lokutan baya haske da Kuma annuri, da zarar na jiyo muryarta ko daga nesa ne, sai in ji gaba na ya fadi , xufa tana kwararo min, kai! Abin dai ya zame min kamar masifa. Wannan wacce irin soyayya ce ta same ni?
.
Kullum muka hadu a makaranta Bayan mun gaisa bana yarda Zubaida ta fahimci irin kallon da nake yi mata, don haka idan tana tare da qawayenta, sai in raku6e a jikin bishiya ina hangenta daga nesa, ko Kuma in 6oye a jikin tagar ajinmu. Ina matuqar sha'awar in hangeta tana dariya cike da farin ciki, sannan Kuma ina sha'awarsu in hangeta tana tafiyar tana rausaya cikin bunqasa da qima da kwarjini kamar wata sarauniya, ina sha'awar in saurari sassanyar muryarta, koda kuwa ace ba da ni take magana ba." duk lkcn da ta aback sunana da daddadan muryarta a ranar da farin ciki nake komowa gida. Shi yasa na haddace duk wata magana mai dadi da na san ta ta6a sanar da ni.
.
"....yaya sunan ka?"
"...sannunka mallaam..."
"...mansur kaxo lfy?"
.jiya ban xo ba Wlh yaya schl din?"
"....yaya schl din mansur....?"
.
To amma Kuma ni duk wadannan maganganun basu gamsar da xuciyata ba na samu kwanciyar hankali, don kuwa bani kadai bane dalibin da Zubaida take gaisa wa irin haka ba, kasancewar tana gaisa da samari da dama, don haka ba lallai bane don mun gaisa ni da ita in gani cewar ta fahimci ina son ta, Kuma ita ma tana sona ba.
.
Nayi son ta ce min.
.
"ina son ka mansur, kamar yadda im na tabbatar kana sona."
.
Ko Kuma ta ce min.

.
"allah yasa muyi aure in zama maTarka."
.
Sai yaushe Zubaida zata sanar da ni wannan kyakkyawan albishir na so da qauna a duniya?
.
.
.
** **
.
.
Sannu a hankali sai na fahimci Zubaida tana da matsayin da aji da ko kusa ni ba Abokin rayuwarta bane, don kuwa da xuqa-xuqan motoci take xuwa na milyoyin kudade, sannan Kuma da wahala ta sanya kayan a jikinta ta sake maimaita su.
.
.
Lp=4Mugun albishir
Page 4
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
Madugun taska
"TASKAR GIDAN LITTAFI"
bata amince da daukar wannan shafin ba."
.
.
.
Kullum kayan da take xuwa dasu kala daban ne na alfarma, wadanda yawancinsu lesuka ne na manyan mata da Kuma manyan atamfofi masu tsadar gaske. na san cewar ko sarqoqin da take yawa sun ishe ni hidimar karatu a rayuwata. don haka Zubaida ta fi qarfin, amma Kuma Kullum qara son ta nake yi, Kuma Kullum ina addu'ar ta zama matata, idan so samu ne.
.
Kwanaki suka yi ta xuwa Suna wucewa, watanni Suna biyo Bayan su, shekara daya Bayan daya har muka yi shekara uku a haka tare da Zubaida Kullum da sonta nake kwana nake tashi a xuciyata. Amma Kuma ita bata sani ba." wani abin takaici Kuma shi ne a cikin shekaru uku da muka yi tare da Zubaida an samu raguwar alaqar mutuncin da muke yi ni da ita. Sau da yawa sai mu hadu da ita a wani lkcn ma ko kallon inda nake ba zata yi ba, sai dai ni da nake binta ina yi mata magana, don kuwa na fadi maku duk ranar da ban ganta ba, Babu Sauran kwanciyar hankali a xuciyata
.
Sannan Kuma a cikin shekaru uku da muka yi ban san takamaimen gidansu ba, Kuma Babu Wanda nake tsammanin ya sani a cikin daliban ballantana in tambaye shi. Don kuwa Zubaida bata cika baiwa mutane fuska Suna doguwar magana ba." Babu Wanda zai ce ya san gidan su, ko Kuma ya ce ya san ko ita "yar wace ce a birnin zariya.
.
Rayuwata bata sake fadawa a cikin xullumi da tagayyara ba sai da lkcn jarrabawarmu ta qarshe ya xo. daga ranar Kuma shi kenan mun yi bankwana da juna, mun gama makaranta, ba zamu sake xuwa mu hadu da junanmu ba, sai dai Xiyara. Dalibai 'yan kwana Suna ta farin ciki da xuwan ranar qarshe, zamu gama jarrabawarmu amma Kuma ni baqin ciki nake yi, don kuwa lkcn rabuwa da masoyiya ta yayi.
.
Na san cewar idan muka rabu shi kenan, wata qila Kuma har abada ba zan sake ganin Zubaida ba." me yiwuwa ma ba zamu sake ganin juna ba." idan Zubaida tayi kwana daya bata xo makaranta ba, ranar rashin lfy nake yi sbd ban ganta ba, gashi Kuma ynx zamu rabu rabuwa ta har abada. Anyya kuwa zan iya rayuwa ba tare da wannan masoyiya tawa ba?"
.
Da ranar kammala jarrabawarmu ta zo ban yi barci ba, kwana nayi a zaune ina xullumi
Wata xuciyar tana raya mani cewar ya kamata in cire fargaba in sanar da ita cewar ina sonta. Don kuwa idan muka rabu ban sanar da ita ba, ban san inda zamu sake haduwa...


Read / Download MUGUN ALBISHIR

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

7 months ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album