Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Mugun albishir
.
Page 1
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
Na dade ina ganin kyawawan 'yan mata a duniya. Wadanda ke da kyawawan halittu da Kuma kyawawan fuskoki da kowa zai gani ya yaba ya yi sha'awarsu. Sau da yawa irin wadannan taurarin 'yan mata wasu da zarar mun rabu bana sake tuna su a xuciyata, sai ka ce tun fil'azal ban ta6a ganin su ba. Wadansu Kuma a cikinsu jefi-jefi su kan fado mani a rai, da zarar na tuno da kamanninsu sai in yi murmushi ni kadai in sake mancewa dasu. To amma Kuma duk da haka Akwai wata fitacciyar taurarruwa guda daya, wacce duk lkcn da na dubi xuciyata sai naci karo da hotonta dake maqale a ruhina shekara da shekaru.
.
Sunan ta zubaida!
.
Ba zan ta6a mance ranar da na fara ganin ta ba. A ranar wata litinin ne wacce ta xo dai-dai da goma sha hudu ga watan takwas alif dari tara da casa'in da tara miladiyya. Ita ce rana ta farko da na fara karatu a kwalejin ilimi ta tarayya dake a birnin zaria.
.
Ina zaune ni kadai a gefe guda akan doguwar barandar ajin da zamu dauki darasi, ina sanya da farin Wando da Kuma farar riqa mai ruwan qwai dake da jajayen rubutu sirara a gabanta. Sauran dalibai kowa yana ta harkar da ta dame shi. Ana ta kaiwa da komowa da kuma surutai da kuma if-iden matasa 'yan bana bakwai sabbin dalibai.
.
Kamar daga sama, sai na dago kai na hangeta, tana tahowa kai tsaye xuwa gare ni. Tana sanye da shudin leshi da Kuma baqin takalmi. Ta rungumo takardun karatunta a cikin fayil, sannan Kuma ta maqalo baqar jakarta kalar takalminta.
.
Zubaida kyakkyawace!
.
Kada ka zargeni don nayi mata wannan kirarin tun a karon farko. Don kuwa rude wa nayi tun a gani na farko da nayi mata. A rayuwata koda ace bani da qwarewa akan komai, to akwai wani abu daya da na tabbattar na qware akan sa. duk lkcn da na ga kyakkyawr mace ko daga nesa ne, na san a layin da zan ajiyeta, don kuwa na dade ina ganin su. Don haka Zubaida kyakkyawa ce fiye da duk yadda zan kwatanta maka ita a cikin wannan labarin.
.
Ku biyo ni. jimawa kadanmugun albishir
.
Page 2
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
.
Zubaida kyakkyawa ce fiye da yadda duk zan misalta maku ita a cikin wannan labari.
.
Akwai wani yanayi dake tattare da ita, Wanda ke sa mutane su kasa tantance doguwa ce ko Kuma gajeruwa ce? Sannan Kuma yanayin dake tattare da kyakkyawar fuskar mai annuri irin sa ne yanayin da duk lkcn da wani Sauran ya kalleta sai yaga kamar murmushi take yi masa, Wanda na tabbatar hakan ya sha tilastawa daruruwan samari fadawa a cikin kogin qaunarta kamar dai yadda nima na fada tun a karon farko.
.
Na ci gaba da kallon ta lkcn da take tahowa sannu a hankali kamar wata dawisu. Ba ni kadai ba hatta Sauran daliban dake a wajen kama daga 'yanmata har samari yawanci ynx duk hankalinsu a kanta yake, kowa yana so yaga a inda zata yada zango. To amma Kuma abin mamakin ga alama har ynx wurin nawa take tahowa.
'na shiga uku!'
.
Shin damar can ta ta6a gani na ne? Na ji gabana ya fadi. sannan Kuma tsoro ya kama ni. Ban yi mamaki ba don kuwa ta haka nake gane mace kyakkyawa a cikin mata masu al-alfahari da xunxurutun kyau. Da ace ban ji tsoro ba a lkcn da na fara ganin ta, da tun farko ban saka maka ita a cikin layin kyawawa ba, don kuwa ba don ta tafi da hankalina ba da wannan fuska tata mai annuri da duk abubuwan da zasu faru basu faru ba.
.
Ta qariso inda nake ina ta kallon ta ko qiftawa bani yi, ina ta mamakin wannan mace mai qyalqyali kamar tauraruwa sai ka ce ita ta qera kanta a duniya.
.
Ta zauna a kusa da ni muka hada ido, muka yiwa juna murmushi, tuni qamshin turaren dake fita a ji6anta da Kuma daddadan qamshin daya-sayen da ta shafa sun mamaye iskar safiyar da ake busawa. Ta sa hannu ta gyara dogon igiyar kitsonta da ya kusa rufe mata ido a cikin dogayen igiyar kitson da suka warwatsu a kafadarta, Suna ta sheqi da daukar ido. ta ce da ni a cikin sassanyar murya.
.
'sannunka.'
.
Sannan ta kashe mani fararen idanunta dake motsawa tarwai dara-dara kamar gilashi. Na biyata murmushi sannan nima na ce da ita.
.
'ke ma sannunki.'
.
Ta kai ganin ta inda Sauran dalibai ke zazzaune fululu a ko'ina, ta dawo da hankalinta kaina ta ce mani.
.
Qq

"ga alama kai ma irina na ce, baka son yawan surutu shi yasa ka ke6e gefe guda ka xauna anan ko mallam?"
.
Na sake cewa da ita.
.
"gskyrki, Wlh ban cika son yawan surutu ba."
.
Muka yi dariya a lkc guda, sannan ta tambayeni.
.
"ya sunan ka?"
.
Na ce da ita cikin farin ciki.
.
"Suna na mansur. Ke Kuma Fa ya sunan ki?"
.
Ta ce da ni.
.
"ni Kuma Suna na Zubaida
.
Ga al'darmu ta qasar hausa, duk lkcn da irin wadannan hirarrakin suka faru a tsakanin saurayi da budurwa, to ana sa ran soyayya ta qullu. Don haka nima ban yi mamaki ba da naji cikin dan lkc qanqani nkamu da ciwon son wannan 'yar talika mai Suna Zubaida ba." muka dauki lkc zaune a wurin mu biyu muna ta hira gwanin ban sha'awa. A lkcn ne ta sanar da ni cewar ita ma sabuwar daliba ce irina.
.
Duk lkcn da zata sanar da ni wata magana sai in ji bana son tayi shiru, don kuwa daddadan muryarta tafi kama da sarewa, yana matuqar tasiri a dodon kunnena. Bana son in rabu da wannan sabuwar masoyiya tawa, to amma Kuma anyya kuwa ta san cewar na kamu da ciwon son ta? Ban yi tsammanin hakan ba."
.
.
Lp=3Mugun albishir
.
Page 3
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
Madugun taska
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI"bata amince da daukar shafin ba, yin hakan kuskure ne a kula
.
.
Ban yi tsammani ba!
.
Bamu dade ba mallamin da zai yi mana darasi ya xo, nan da nan muka shiga tare da Sauran dalibaI aka soma karatu. Ba wuri daya muka zauna ba." a tsakanina da Zubaida Akwai mutum bakwai, sai dai duk da haka hankalina yana kanta. Wani lkcn kamar a jikinta ta san wani yana kallonta haka kawai sai ta waigo inda nake mu hada idanu. Duk lkcn da zata waigo sai ta same ni ita kawai nake kallo ba mallamin ba, Kuma duk lkcn da zamu hada idanu sai ta yi mani murmushi da tattausan le6enta dake sheqi. Nan da nan naji duk na qosa a tashi darasin, na qosa mu fita waje ni da masoyiyata Zubaida. addu'ar da nake yi a lkcn da muke cikin ajin ita ce. Allah ya sa Zubaida ta fahimci ina son ta, kuma allah yasa ita ma ta amince ta so ni.
.
To amma Kuma a lkcn da aka tashi karatu abin yaxo minn a bazata. Na dauka cewar Zubaida zata tsaya ta saurare ni, mu tafi tare muna hirarmu ta soyayy.
.
Maimakon haka sai ta ce da ni a lkcn da ta fahimci ina son tsare ta da surutu.
.
"to mansur, lkcn xuwa gida yayi, ni zan tafi sai gobe Kuma idan mun sake dawowa."
.
Nayi mata murmushi, kafin in sake cewa da ita wani abu har ta tafi ta bar ni. A haka na tsaya wurin ina ta wasi-wasi da tunane-tunane har daliban da suke a sashen mu suka watse suka bar ni ni kadai A tsa.
.
Me yasa ban sanar da ita ina sonta ba? Na zargi kaina, don kuwa abin da xuciyata ta gani tana so, bai kamata in yi shiru in 6oye a raina ba." bai kamata in yi kawaici in kasa sanar da ita ba." a ranar ban iya cin abinci ba, sannan Kuma barci ma qaurace min yayi kwata-kwata daga idanuna. Muryar Zubaida ta ci gaba da amsa kuwwa a xuciya. A lkcn da ta xo wurina ta zauna. Ba zan manta lkcn farko da ta fara yi mani magana ba."
.
"sannun...yaya sunan ka?"
.
.
** ** **
.
.
Tun ranar da wannan al"amarin ya faru na kasa samun sukuni a xuciyata. Don kuwa duk lkcn da naxo makaranta har qosawa nake yi in nemo ta in ganta don hankalina ya kwanta. to amma Kuma sbd tsananin fargabar da nake yi tun farko da Kuma razana, har aka dauki lkc mai tsawo ban sanarwaa kowa ba a cikin Abokina dake a makaranta. Ina matuqar jin tsoron in sanar da ita, daga Bayani Kuma ta nuna mani rashin goyon bayanta. Shi yasa na 6oye a xuciyata. To amma Kuma a haka zan ci gaba da son wacce bata san ma ina yi ba?"
.
kullum bani da wani aiki da ya wuce tunanin wannan kyakkyawar budurwa zubaida. Gashi kuma ko ho hotonta bani dashi, ballantana idan naje gida in riqa dubawa yana debe mani kewa. Don haka idan naje gida sai dai in kwanta ni kadai a daki in rufe qofa ina ta tunaninta, don Kada wani tunanin yaxo ya katse min hanzarina. Kullum idan ina tunanin Zubaida sai in riqa aiyanawa a xuciyata cewar waigo gashi nan har mun yi aure, muna zaune tare zaman soyayya da qauna a wani qayataccen gida na alfarma. to amma Kuma ni na san cewar Zubaida ba ta ni take yi ba, don kuwa ita a tsammaninta mutunci kawai muke yi irin na dalibai, bata yi tsammanin na kamu da matsanancin sonta ba tun ranar da na fara ganinta.
.
Sannu a hankali da ciwon sonta yayi qarfi a jikina wani lkcn haka kawai bana sanin sanda nake ambaton sunan ta. Sauran da yawa idan nayi shiru ina tunani sai in kira sunantta ba tare da na sani ba." abokaina da basu san me ke faruwar ba idan irin haka ta faru sai su tambayeni ni.
.
"mansur wacce ce zubaida?
.
Duk ranar da Zubaida bata xo makaranta ba, bana iya karatu bana iya magana da kowa, don kuwa duk ranar da na wayi gari ban ganta ba, wunin nake yi da zzazza6i mai zafi. Sai na ganta washe gari sannan nake warkewa. Gashi Kuma Kullum kamar qara kyau take yi. Kullum ta xo makaranta sai in ga tafi lokutan baya haske da Kuma annuri, da zarar na jiyo muryarta ko daga nesa ne, sai in ji gaba na ya fadi , xufa tana kwararo min, kai! Abin dai ya zame min kamar masifa. Wannan wacce irin soyayya ce ta same ni?
.
Kullum muka hadu a makaranta Bayan mun gaisa bana yarda Zubaida ta fahimci irin kallon da nake yi mata, don haka idan tana tare da qawayenta, sai in raku6e a jikin bishiya ina hangenta daga nesa, ko Kuma in 6oye a jikin tagar ajinmu. Ina matuqar sha'awar in hangeta tana dariya cike da farin ciki, sannan Kuma ina sha'awarsu in hangeta tana tafiyar tana rausaya cikin bunqasa da qima da kwarjini kamar wata sarauniya, ina sha'awar in saurari sassanyar muryarta, koda kuwa ace ba da ni take magana ba." duk lkcn da ta aback sunana da daddadan muryarta a ranar da farin ciki nake komowa gida. Shi yasa na haddace duk wata magana mai dadi da na san ta ta6a sanar da ni.
.
"....yaya sunan ka?"
"...sannunka mallaam..."
"...mansur kaxo lfy?"
.jiya ban xo ba Wlh yaya schl din?"
"....yaya schl din mansur....?"
.
To amma Kuma ni duk wadannan maganganun basu gamsar da xuciyata ba na samu kwanciyar hankali, don kuwa bani kadai bane dalibin da Zubaida take gaisa wa irin haka ba, kasancewar tana gaisa da samari da dama, don haka ba lallai bane don mun gaisa ni da ita in gani cewar ta fahimci ina son ta, Kuma ita ma tana sona ba.
.
Nayi son ta ce min.
.
"ina son ka mansur, kamar yadda im na tabbatar kana sona."
.
Ko Kuma ta ce min.

.
"allah yasa muyi aure in zama maTarka."
.
Sai yaushe Zubaida zata sanar da ni wannan kyakkyawan albishir na so da qauna a duniya?
.
.
.
** **
.
.
Sannu a hankali sai na fahimci Zubaida tana da matsayin da aji da ko kusa ni ba Abokin rayuwarta bane, don kuwa da xuqa-xuqan motoci take xuwa na milyoyin kudade, sannan Kuma da wahala ta sanya kayan a jikinta ta sake maimaita su.
.
.
Lp=4Mugun albishir
Page 4
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
Madugun taska
"TASKAR GIDAN LITTAFI"
bata amince da daukar wannan shafin ba."
.
.
.
Kullum kayan da take xuwa dasu kala daban ne na alfarma, wadanda yawancinsu lesuka ne na manyan mata da Kuma manyan atamfofi masu tsadar gaske. na san cewar ko sarqoqin da take yawa sun ishe ni hidimar karatu a rayuwata. don haka Zubaida ta fi qarfin, amma Kuma Kullum qara son ta nake yi, Kuma Kullum ina addu'ar ta zama matata, idan so samu ne.
.
Kwanaki suka yi ta xuwa Suna wucewa, watanni Suna biyo Bayan su, shekara daya Bayan daya har muka yi shekara uku a haka tare da Zubaida Kullum da sonta nake kwana nake tashi a xuciyata. Amma Kuma ita bata sani ba." wani abin takaici Kuma shi ne a cikin shekaru uku da muka yi tare da Zubaida an samu raguwar alaqar mutuncin da muke yi ni da ita. Sau da yawa sai mu hadu da ita a wani lkcn ma ko kallon inda nake ba zata yi ba, sai dai ni da nake binta ina yi mata magana, don kuwa na fadi maku duk ranar da ban ganta ba, Babu Sauran kwanciyar hankali a xuciyata
.
Sannan Kuma a cikin shekaru uku da muka yi ban san takamaimen gidansu ba, Kuma Babu Wanda nake tsammanin ya sani a cikin daliban ballantana in tambaye shi. Don kuwa Zubaida bata cika baiwa mutane fuska Suna doguwar magana ba." Babu Wanda zai ce ya san gidan su, ko Kuma ya ce ya san ko ita "yar wace ce a birnin zariya.
.
Rayuwata bata sake fadawa a cikin xullumi da tagayyara ba sai da lkcn jarrabawarmu ta qarshe ya xo. daga ranar Kuma shi kenan mun yi bankwana da juna, mun gama makaranta, ba zamu sake xuwa mu hadu da junanmu ba, sai dai Xiyara. Dalibai 'yan kwana Suna ta farin ciki da xuwan ranar qarshe, zamu gama jarrabawarmu amma Kuma ni baqin ciki nake yi, don kuwa lkcn rabuwa da masoyiya ta yayi.
.
Na san cewar idan muka rabu shi kenan, wata qila Kuma har abada ba zan sake ganin Zubaida ba." me yiwuwa ma ba zamu sake ganin juna ba." idan Zubaida tayi kwana daya bata xo makaranta ba, ranar rashin lfy nake yi sbd ban ganta ba, gashi Kuma ynx zamu rabu rabuwa ta har abada. Anyya kuwa zan iya rayuwa ba tare da wannan masoyiya tawa ba?"
.
Da ranar kammala jarrabawarmu ta zo ban yi barci ba, kwana nayi a zaune ina xullumi
Wata xuciyar tana raya mani cewar ya kamata in cire fargaba in sanar da ita cewar ina sonta. Don kuwa idan muka rabu ban sanar da ita ba, ban san inda zamu sake haduwa ba."
.
Ka shaida mata kana sonta mansur, ko banza dai yafi ace ka bar abin a iya xucyarka ba tare da ta sani ba." koda kuwa ace ba zata amince ba, ta san cewar dai kana sonta, Kuma duk inda take a duniya ita ma zata riqa tunaninta a matsayin masoyinta.
.
Da wannan shawarar na tafi makaranta a raina, ina ta mamakin irin wannan soyayya da ta cafi xuciyata.tun a ranar farko da muka fara karatu na fara sonta, gashi Kuma ban sanar da ita ba sai ynx a ranar mu ta qarshe da zamu rabu. Shekaru uku cur ina tfama da ciwon son ta a raina, Babu Wanda ya sanin ballantana ya taimaka mani ya jefi-jefi ya sanarwa kyakkyawa Zubaida
.
Bayan mun fito jarrabawarmu dalibai Suna ta gaisawa da juna, kowa yana neman dan uwanshi don a yawa juna Tunda dai rabuwa ta zo, ni Kuma sai nayi sauri na garzaya na bi Zubaida a guje, da na hangeta ta kama hanya ta tafi inda motarta take zata tuqa ta tafi. Na sha gabanta ina numfashi da qyar kamar raina zai fita. Muka hada ido ta yi mani murmushi sannan ta ce da ni.
.
"mansur ban ganka ba sai ynx, yau Kuma ranar rabuwa ta zo, mu yawa juna sai wata rana."
.
Na tuno ranar da muka fara haduwa a makaranta, shekara uku da suka wuce, sannan na sake tuno magana da ta sanar da ni da ke 6oye a dodon kunnena tsawo lkc.
.
"sannunka. ga alama kaima irina ce baka son yawan surutu, shi yasa ka zo ka zauna...."
.
Na ji hawaye sun tarar mani a idanuna, qwalla ta cicciko mani, nayi sauri na share hawaye na ce da ita cikin qarfin hali.
.
Yawan comment dinku shi ne kuzarina wajen sanqamo
Page 5mugun albishir
Page 5
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
.
Naji hawaye sun taru a idanuna, qwalla ta cicciko min nayi sauri na share hawaye na. Na ce da ita cikin qarfin hali .
.
"haka ne Zubaida yau ce ranar mu ta qarshe a makarantar nan, daga yau Kuma sai yaushe kenan zamu sake haduwa, ko kina nufin mun rabu kenan har abada?
.
Zubaida tayi dariya, ga alama bata fahimci irin matsanancin halin da rayuwata ta shiga ba." tayi mani farin da fararen idanunta sannan ta ce da ni.
.
"gsky mansur bana tsammanin zamu sake haduwa har abada
.
Tayi shiru tana tunanin wani abu. A yayin da ni Kuma na qarawa kyakkyawar fuskarta idanu. Wata xuciyar ta fara yi mani kururuwa.
.
"ka fadi mata kana sonta mansur, kayi sauri ka sanar da ita, sbd daga yau ta ce ba zaku sake haduwa ba a duniya har abada!!!
.
Kafin in dawo hayyacina in ce da ita wani abu ne, sai ta ce da ni cikin farin ciki.
.
"Akwai wani albishir mai dadi da zan sanar da kai mansur, Wanda ba kowa ne ya sani ba a makarantar nan, na san cewar zaka yi farin ciki, ina nufin zaka taya ni farin ciki.
.
Naji farin ciki ya kama ni.
.
...."wane irin albishir ne Zubaida fada min..."
.
Na ce da ita cikin zaquwa, don kuwa ni a shirme na tayi tsammanin ina matuqar sonta ne, shi yasa ita ma zata sanar da ni cewar tana sona.
.
Zubaida ta duba agogo sannan naga ta dan 6ata rai. ta ce da ni kai tsaye.
.
"kai kada in 6ata maka lkc mansur, nima sauri nake yi, dama ba wani albishir bane, so nake yi dama ka taya ni farin ciki, ina gayyatarka xuwa daurin aurena a wannan asabar din mai xuwa. Na sami miji zan yi aure."
,
Naji kamar ta watsa min garwashin wuta a fuska.
.
.
.
~~~~~~~{ mugun albishir }~~~~~~~~
.
.
.
Kowanne dan adam a duniya Akwai abubuwa da dama da suka fi bashi sha'awa a rayuwarsa. Alal misali wani shi a rayuwarsa yafi so yaga an yi ruwan an dauke, ni'ima ta wadaci ko ina a duniya, ana busa sassanyar iskar damina.
.
Wani kuma shi a nasa 6angeren yafi son ya ji ana zafi, don kuwa a irin wannan lkcn yafi walwala da nishadi tare da Sauran bani adamu. Wani kuma yafi son ya wuni yana yawo bashi a nan bashi a can. Wani kuma shi in har zai samu ya kwanta ya wuni yana barci, to duniya ta yi masa dadi koda kuwa bai samu abin da zai jefa a bakin salati ba."
.
Ni kaina ina da irin wannan buqata kamar Kowanne dan adam. To amma Kuma Babu mamaki ni a nawa 6angaren abin da nafi so ya banbanta da na Sauran mutane. Na san cewar mutane da dama zasu sha dariya idan na shaida masu cewa a rayuwata nafi so in zauna a daki ni kadai tun safe har dare ba tare da nayi magana da kowa ba."
.
A cikin irin wadannan ranakun da na samu wannan gara6asar ta zama ni kadai a yammacin wata lahadi ba zato ba tsammani sai naji sallamar wani yaro mai qirar wayayyu dan kimanin shekaru bakwai a dai dai qofar dakina. Tun kafin in amsa sallamar ya sa hannu ya yaye tsumman labulen dakina Wanda yayi fata-fata kamar kallabin mahaukaciya.
.
Muka hada ido ni da yaron, ina zaune ina gyaran wata tsohuwar rikoda tawa, wacce Kullum sai na dirka mata dundu Sau ba iyaka, sannan nake samu in ji labaran duniya.
.
:
"wai an ce ka xo ana kiranka a waje."
.
Na dubi yaron cikin damuwa, ganin irin kallon da nayi mashi naga ya dan jawo baya a tsorace. To amma Kuma wata qila ba kallon da nayi mashi bane ya tsorata shi, Babu mamaki tsohuwar rikodar tawa ya gani ya furgita, don kuwa ko ina a taskar dakina kayan cikinta ne falle-falle kamar an fede akuya. Amma Kuma duk da haka sai faman 6urari take yi da tsuwa a natalie tsammanin waqar fina-finan hausa take yi. Na ce da yaron.
.
"wane ne ke kira?"
.
Ya ce da ni.
.
"maman bose ce.
.
Maman bose? Na tambayeni kaina. Lallai Babu lfy. Don kuwa na san abin da ya kawota. na xurawa yaron idanu. Na ce dashi.
.
"ka ce da ita bani nan...ka ce da ita baka ganni ba."
.
A dai-dai lkcn da nake yiwa yaron burga ne, kakata ta fita daga dakinta dake kusa da nawa, tana dauke da bata zata yi alwala. Ta ce da yaron.
.
"kai je ka ce gashi nan xuwa ka ji ko?
.
Yaron ya garzaya waje da gudu bayan ya ce.
.
"to."
.
Nan da nan ta fara yi min sababin da ta saba tana cewa.
.
"sakarai, mutumin banza, kai dai mansur ba zaka ta6a jinjinawa nasiha ba." ace Kullum aka zo gidan nan yin sallama da kaI sai ka ce ace baka nan...ka ynx mutane ashe ba rahama bane mansur....ina amfanin wannan shashancin da kake yi a gidan nan?"
.
Na riqa na saba da halinta, in Sau dari za ayi sallama
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On MUGUN ALBISHIR
avatar
abdallah

8 months ago

Reply

Inason saya t coins

Please Login or Register in order to submit comment