Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ADALILIN YAYATA Complete Hausa Novel Document by ADALILIN YAYATA


ADALILIN YAYATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 34273



ADALILIN YAYATA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: Feedohm ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : _HASKE WRITERS ASSOCIATION_

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 205.01 kb

File Type: txt

Views: 932+

Download: 731+

Last download: 4 days ago

Description/Story: A DALILIN YAYATA
Na Nabila Rabi'u Zango
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]



馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA...._*馃崄馃崄
馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS_
1 to 2
_*Assalamu Alaikum ...na canza wannan littafin daga A
DALILINSU ...to ...A DALILIN YAYATA....Saboda naga sister
jannah tayi littafin mai irin Sunan.......馃崄*_
Duk da bana da wayau amma nasan duk lokacin da
wannan mai bakaken kayan yazo dole sae mamana tayi
kuka ranar ....baya da maganar da ta wuce ta babanmu
duk da yayi shekara daya da rasuwa...Mugun haushinsa
ya turnukeni ...ji nake da ina da karfi babu abunda zai
hana ban mashi jajjagen kasa ba abaki...
..Kai maman tamu bata nan kuma ba yanzu zata dawo
ba.....na saka hannu na tare bakin kofar ina mazurai ...
Yaushe zata dawo ...ya fada fuskar a murtake kamar
yarda yake kullun ...
Ohon maka ....kullun kai kazo sae ka saka mamanmu
kuka kai kana so kaga maman taka tana kuka ....na fada
tare da rike kugu...
Yayata dake cikin gida tana wanke waken da zatayi
awara ta kwala man kira ....
Na kalleshi duk na bata rai ina fadin ...matsa zan rufe
gidan saboda barayi.. ....ban jira komae ba na turo gidan
da karfi ...ina jin lokacin da ya sake tsaki mai karfi ....nayi
saurin dawowa na bude kofar ...lokacin har ya bude
motarshi zaya shiga ....
Da karfi na kwala mashi kira kamar yarda naji mamana
na kiranshi .....Lauya ...
Ya juyo yana kallona ....Maman tawa ta dawo Ashe ban
sani ba....na sake dariyar shakiyyanci ...
Karamin tsaki ya dan ja sannan ya dawo cike da bacin
rai ....na bashi hanya ya shiga ni kuma na koma kusa da
motarshi na tsaya ....
Ina ganin ya fito na tattare siket dina na kwasa a guje
...don nasan mamar tawa batta nan ...tsakin da ya man
ne ya bani haushi ...
Ban dawo lungun ba sae da na tabbatar ya bar unguwar
sannan naje kiran da yayata keman ...
markade ta bani na kai mata sannan ta tace awarar ta
daura saman wuta ...
Mamana ta dawo rike da ledar gari yayi zafi ....nayi
saurin karba ina dariya ....sae da ta dauko tabarma ta
shinfida sannan ta fito da kayan dake ciki .....
Irin kayan kwancen nan ne da ake bata inda take aiki
....ta miko man dae dae nawa sannan ta mikawa yayata
wanda zasu mata ...nan na dinga murna tare da godiya
.....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Tunda na fito daga gida yaron dake zagaye da kaskon
tuyar awarar yayata suka fara watsewa .....bana dagawa
kowa cikinsu ....don duk yawancinsu masu cima yayata
zalun ne ...basa bata kudinta idan sun dauka ita kuma ba
mai yawan magana bace ...sae dae ta kyalesu ....amma
idan ina gurin ko karkashin gadon uwarka ka boye sae
na bika na karbo kudina .....bana jin komae idan ka
daukar wa yayata awarar naira goma na je har gidanku
na kwanto akuyarku idan ma baku da ita zan iya dauko
tukunyar ku na taho da ita ..kuma idan duk duniya zata
hadu baran ce ga inda na kaita ba har sae anbiyani kudin
sannan zan bayar ...don bana ajeta gidanmu gudun kar
mamana tace na bayar ...
Shafi'u dan makwabtan mu na gani sae dauka yake
yana ci ba tare da ya kirga ba ....na kafe shi da ido har na
zauna bai san da zuwana ba ....sae da ya koshi sannan ya
mike yana kakkabe riga ya fito da naira goma ya aje bisa
kwandon yana fadin ...Saa ga kudinki nan kin biyoni sha
biyar ...
Kam ubancan ...Ashirin da biyar fa ...na fada tare da rike
kugu..
Yayi saurin kalloni yana washe baki kafin yace ...Haba
Hudata ina nufin saura naira Sha biyar aljihuna yanzu
zan fito mata da ita sae ta biyoni Hamsin ...
Nace ...owo ai na dauka ta ashirin da biyar kaci ...
Ya washe baki ...aa ina ni ....ai ina lissafi ...ya lalubi aljihu
ya fito dasu ya mika mata ...ya tafi yana kakkabe hannu
tareda kalloni ....
Gurin na koma na zauna ....Yayata ta Bini da kallo tana
so tace na tashi amma tana shakkata ...tasan in har na
zauna ba ciniki zatayi ba sossae ....Mutane na son zuwa
amma Ni suke tsoro ...
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA..._*馃崄馃崄
馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
3 to 4
Barister Shehu abunda kake niyar aikatawa sam bai
dace ba ...wannan zaluncine tare da yaudara ...matar
data amince da kai ta baka amanar dukiyar mijinta
yanzu kuma ta fito kana so ka zalumcesu ...idan har kai
baka taimakesu ba to bai kamata ka zaluncesu ba ....
Ya kife wayar tare da juyowa a firgice yana kallon
Mahmud daya kafeshi da ido harde da hannayensa a
kirji ...
Cikin borin kunya yace ...so what dan naci amanarta
kanwar babata ce ...kai Mahmud zan iya komae akan
kudi ...
Ni kuma Barister Mahmud nace indae har ina raye bara
ka taba wannan cin amanar ba ....
Wae me ya shafeka ne da rayuwata ....kaga ka fita
wannan maganar ...meyasaka tunda mijin nata ya rasu
baka je ka taimakesu ba sae yanzu zaka zo kana man
wani waazi ...
Sabida ta yarda da mutumin da bai kamata ta yarda
dashi ba....yana gama fadar haka ya matso kusa da table
din shi ya dauki takardun da zai dauka tare da briefcast
dinshi ya fita ...
Tsaki Barister shehu ya sake kafin shima ya tattara nashi
nashi ya bar office din ....daga nan gidansu Huda ya nufa
kai tsaye ...
Cikin lungun ya hango ana dambe da huda ...ta haye
ruwan cikinshi sae jibgarshi take yara sae kara zugata
suke ....yayi kwafa ...yana tunanin da itace ake duka haka
to babu abunda zai kaishi rabasu ...yafi kaunar a kasheta
kowa ya huta don da alamun yarinyar tana neman
shigar mashi hanci ....da wannan tunanin ne ya isa gurin
...tare da fincikota ya dagata daga yaron da karfi sannan
ya dauketa mari .......
Marin ya shigeta sossae ta dago tare da zuba mashi ido
kafin ta dauki katon dutse ta jefawa glass din motarshi ta
gama ......nan take glass din ya fashe ...ya juyo da azama
amma kamar walkiya ta bace .....yayi kwafa tare da sake
murmushin mugunta yayi sallama gidan ...da yake baida
katanga da gidan ya fada ciki ba tare da shamaki ba ....
Bayan sun gaisa yake fadawa mamanta cewa ....kudin
sallamar aikin babansu Huda malan Ibrahim sun fito
...yanzu haka gobe yake shirye shiryen fito dasu banki
sae ya kawo masu zuwa jibi ...
Tace ...ka barsu hannunka lauya ...idan ka kawo mana
ina zamu ajesu ...na tabbata bara ka cucemu ba ...don
haka ka barsu hannunka ..sae dae ka dan bamu abunda
zamu kara jari dashi dan Allah ..
Murmushi yayi yace ...aa hajiya zan kawo maki su ki
gani bayan kwana biyu sae nazo na karba ...don yanzu
haka ina shirye shiryen saya maku da gida wanda zaa
zuba yan haya a ciki duk shekara sae su dunga baku
kudin ...idan na kawo kudin jibi to wanshekare zanzo da
mutanen da zaku sayi gidan gurinsu sae a karbi kudin a
basu ....
To Amma ina tunanin inda zamu aje su Lauya ...
Murmushi yayi yana fadin ...Allah zai karesu Umma
....ya mike yana fadin zan tafi idan huda ta dawo a ja
mata kunne bata jin,magana yanzu daga rabasu fada ta
fasa man glass din mota ...
Ta hau sallallami tana bashi hakuri tare da fadin idan
kudin sun fito dan Allah ya sayi glass din dasu ...
Yace mata to ...tunda dama haka yakeso .....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Barister Mahmud indae kana bukatar wani abu cikin
kudin ka fada man bawae ka dinga man wani waazi ba
na daban ....
Wani kalan murmushi ya sake yana fadin ...nawa ne
kudin nasu ...
Yauwa dan gari ...10m ...ne ...zan baka 1m .....shikenan
ko ...
Dariya ya sake mai cike da maanuni daban sannan yace
...zan baka 10m ka bar masu nasu please
Barister Shehu ya sake dariya yana fadin ....Am not a kid
Barister baran taba cin kudinka na zauna lafiya ba
....nasanka sossae ...don haka kabar wannan uwar watsin
...
Suma wannan sae ka basu kayansu ...
Dariya yayi yana fadin gobe karfe biyar na marece zan
kiraka na basu agabanka barister ....ya juya ya shige
motarshi ...
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Karfe biyar dae dae ya kira Mahmud ya mashi
kwatancen gidansu Huda sossae yace yazo lungun gidan
ya iskesu ...ko minti talatin bai cika ba ya shigo lungun ....
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_*

Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ADALILIN YAYATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album