Join Our WhatsApp Group

FADAR BARCI Complete Hausa Novel Document by FADAR BARCI


FADAR BARCI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 2607



FADAR BARCI

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Yusuf Abdullahi A Jibaga ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08071051138

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 13.91 kb

File Type: txt

Views: 518+

Download: 111+

Last download: 1 day ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
FADAR BARCI

Wani Sarki ne da Sarauniyarsa suke mulki a wani
gari mai yawan mayu. Duk da cewa Sarkin nan da
Sarauniyarsa babu abin da suka rasa na dukiya da
jin dadin zaman duniya, amma Allah bai nufe su
da haihuwa ba tsawon shekaru, har tsufa ya fara
sallamo ma su.

Ana nan wata rana, Sarauniyar nan ta fita bayan
gari shan iska, ita kadai, har ta iso bakin wani rafi.
sai kuwa ta ga wani dan karamin kifi ruwa ya turo
shi bakin gaba, ya yi, ya yi, ya koma ciki ya kasa
har yana shirin mutuwa. Sarauniya ta ji tausayinsa
ta dauke shi ta mayar da shi cikin ruwa.
Bayan kifi ya yi nitso cikin ruwa, ranshi ya dawo,
sai ya dago kansa saman ruwa ya ce da
Sarauniya, "Na san abin da ke damun ku, ke da
mijinki, sakamakon taimakona da kika yi, za ki
haifi 'ya mace wadda babu kamarta a kyau duk
fadin duniyar nan, sai dai wani abin al'ajabi zai
faru gare ta." Yana gama fadin haka sai ya shige
cikin ruwa abinsa.
Shekara ba ta kewayo ba sai da Sarki da
Sarauniya suka haifi 'ya mace, wadda ba a taba
ganin kyakkyawa kamarta ba. Da ranar suna ta
kewayo, Sarki ya gayyato manyan Sarakuna na
duniya domin taya shi murna. Ita kuma Sarauniya
ta gayyato manyan mayun kasar su goma sha
biyu.

Duk baki kowa ya hallara, Sarakuna suka cika
fada, mayu kuwa kowace ta zo tana sanye da jar
hula da jajayen takalmi rike da fararen sandunansu
na tsafi. Bayan an ci biki har an kusa watsewa,
bakin Sarki suka bayar da kyaututtukan da suka
kawo wa abokinsu.

Su kuwa mayu sai suka fara ba wa jaririya
kyaututtukan sihiri. Ta farko ta nuna ta da
sandarta ta ce, "Za ki zama kyakkyawa." Ta biyu
ta ce, "Za ki zama mai arziki." Ta uku ta ce, "Za ki
zama mai ilimi." Ta hudu ta ce, "Za ki zama mai
tausayi da taimako."
Haka dai suka ci gaba da ba ta kyautuka har zuwa
mayya ta goma sha daya. Har mayya ta sha biyu
za ta mike ta bayar da tata kyautar, sai aka ji wuri
ya hargitse da kururuwa da hayaniya da iska.

Lokacin da wuri ya natsa, kamar daga sama sai
aka ga wata mayyar ta bayyana a cikin taron, tana
sanye da bakar hula da bakaken takalmi da bakar
sanda. Ashe an manta ba a gayyato ta ba wurin
biki, ita kuwa ta ji haushin wannan banbanci da
aka nuna mata. Sai ta nuna jaririya da bakar
sandarta ta ce, "Idan ki kai shekara goma sha
biyar za ki soke hannunki da kwarashin saka, nan
take za ki mutu!" Tana fadar haka sai ta yi wata
irin dariyar keta, ta zama iska ta bace.
Hankali Sarki da Sarauniya ya tashi a kan wannan
fata na mayya. Ga shi abin da suke nema shekara
da shekaru sun samu amma burinsu na barin
zuri'a a duniya ba zai cika ba, 'yarsu za ta mutu
tun kafin ta yi aure!
Nan da nan sai mayya ta goma sha biyu, wadda
ba ta bayar da kyautarta ba, ta taso ta ce da
Sarki da Sarauniya, "Hakika wannan mayya da ta
fita yanzu babbar matsafiya ce, babu mai iya tare
sihirinta a nan cikinmu. Amma ni, zan yi iyakar
kokarina in rage masa karfi." Sai ta nuna jaririya
da sandarta ta ce, "Idan ki ka cika shekara goma
sha biyar, tabbas za ki soke hannunki da kwarashi,
amma ba za ki mutu ba, za ki kwanta barci wanda
ba za ki farka ba sai bayan shekara dari."
Bayan an gama biki an watse, Sarki ya sa aka
sanar da dukan mutanen gari duk wanda ya san
yana da kwarashi, kai koda allura ce, a fito da su.

Aka tara kwarashi da alluran garin gaba daya aka
kona su. Sarki ya sa doka mai tsanani akan shigo
da kwarashi ko allura a cikin garinsa.
Da 'yar Sarki ta fara tasawa, dukan kyautukan da
mayun nan suka ba ta, suka fara bayyana tare da
ita. Ga ta dai ta zama kyakkyawar da babu
kamarta, ga hikima da basira, ga tausayi, dukan
abin da aka koya mata sau daya, shi ke nan ta
rike shi.
A kwana a tashi har ta kai shekara goma sha
biyar cif, a daidai lokacin ne kuma tafiya ta kama
Sarki da Sarauniya zuwa wani gari. Aka bar 'Yar
Sarki a gida, ita da masu kulawa da ita. Da ta gaji
da zama sai ta tashi tana bi lungu-lungu na gidan
domin ta mike kafafunta. Ta zo wani lungu, sai ta
ga wani daki da marikin kofarsa ta zinariya. Ta
kama marikin kofar ta tura, sai kofar ta bude. Ta
kutsa kai cikin dakin, sai ta ga wata 'yar tsohuwa,
tukuf da ita, zaune a kan kujera tana saka.

Ta kura wa 'yar tsohuwa ido, ta ga yadda take ta
surkulle da kwarashi, sai abin ya burgeta. Ta
matsa kusa da 'yar tsohuwa ta gaisheta cikin
ladabi, ta ce da ita tana so ta koyi yadda ake
wannan abu. Ashe ba ta sani ba, 'yar tsohuwar
nan ita ce mayyar da ta yi mata fatar mutuwa
bayan shekara goma sha biyar.
Tsohuwa na jin haka, sai ta mika wa 'Yar Sarki
kwarashi da kayan saka. 'Yar Sarki ta karba,
tsohuwa ta gwada mata yadda za ta yi. Ta fara
sakawa ke nan, sai kuwa kwarashi ya soke mata
hannu, nan take ta fadi kasa, sai barci. Ita kuwa
mayya ta dauka mutuwa ta yi, ta fita abinta tana
farin ciki, burinta ya cika.
Barci na dauke 'Yar Sarki, sai komai da ya ke cikin
gidan barci ya dauke shi. Dawaki a barga suka
soma barci, karnuka da tattabaru da suke kan
rufin fada duka barci ya dauke su. Wutar da take
a dakin dafa abinci, ita ma ta daskare. Ga mai
dafa abinci ta biyo kaza za ta kama ta yanka, ita
da kazar duk barci ya yi awon gaba da su. Wani
dogari ma ya daga bulala ke nan zai labtawa wani
bawa, duka barci ya kwashe su. Har wani dogari
can gefe ya daga kofin zai sha ruwa, shi ma barci
ya dauke shi. Hatta kudaje da kwarin da suke
cikin gidan nan duka barci ya dauke su. Sarki da
Sarauniya na dawowa daga inda suka tafi, suna
kutsa kai cikin fadar sai barci ya dauke su a kan
dawakinsu, duk da dawakin da 'yan rakiyarsu.

Labari ya watsu cikin gari, sai ya kasance babu
mai matsawa kusa da fadar nan. Shekara bayan
shekara, ciyayi da kayoyi da sarkakiya suka fito
suka zagaye gidan.
Duk shekara suna kara girma,
har ya zamanto ba a iya ganin fadar, duk kayoyi
da ciyayi sun rufeta. Labarin 'Yar Sarki mai barci
ya watsu ko'ina cikin duniya. 'Ya 'yan Sarakunan
duniya da sadaukai da dama suka ta yiwo tattaki
suna zuwa garin domin su ga 'Yar Sarki mai barci
da kuma irin kyawonta da suke jin labari. Amma
duk wanda ya zo shiga gidan sai ya ga babu
dama, domin kaya da sarkakiya sun rufe gidan,
dole ya koma baya. Wasu kuma sukan yi karfin
hali su kutsa kai ciki, amma sai sarkakiya ta
cukuikuye su, su kasa yin gaba su kasa yin baya,
har yunwa ta kashe su.
Ana haka, wata rana wani kyakkyawan Dan Sarki
ya shigo garin, ya sauka gidan wani dan tsoho. Ya
ce yana so dan tsoho ya kai shi fada su gaisa da
Sarki. Dan tsoho ya ce babu Sarki a wannan gari,
shi da fadarsa duka an sihirce su suna can suna
barci, har da wata 'yarsa wadda babu kamarta duk
duniya a wurin kyau, an ce kuma ba za su farka
ba sai bayan shekaru masu yawa, ni ma na ji
wannan labari ne daga kakana.

Ko da Dan Sarki ya ji haka, sai ya ce wa dattijo ya
nuna masa inda fadar take, yana so ya ga wannan
abin al'ajabi. Tsoho ya yi masa kwatance da fadar,
kuma ya gargade shi a kan kada ya kuskura ya ce
zai shiga ciki, domin mutane da yawa sun halaka.
Dan Sarki na isa wurin da fadar take, maimakon
ya ga ciyayi da sarkakiya da kayoyi, kamar yadda
tsoho ya fada masa, sai ya tarar da fadar zagaye
da furanni da ciyayi masu laushi. Ashe ranar ce
'Yar Sarki take cika shekara dari daidai tana barci.
Dan Sarki ya kutsa kai cikin fadar, ya ga dukan
mutane da dabbobin fadar barci suke yi.

Ya yi ta bi lungu-lungu, daki-daki, yana neman
inda 'Yar Sarki take, har Allah ya sa ya kai ga
dakin. Ya ganta kwance a kasa tana ta barci. Nan
take ya kidime saboda da tsananin kyanta da ya
gani, sai ya ga duk kyanta da dan tsoho ya yi ta
ruruta masa, bai fadi kashi ashirin cikin dari ba na
kyanta. Dan Sarki ya durkusa ya kura wa yarinya
ido, sannan ya sunkuya ya sumbace ta a kumatu.
Yana sumbatar ta sai ta bude idonta, ta yi
murmushi, nan take ta farka daga barcin shekara
dari.
'Yar Sarki na farkawa, sai dukan abin da ke cikin
gidan ya farka daga barci. Dawaki suka ci gaba da
kukansu, tattabaru suka ci gaba da fiffikarsu, mai
dafa abinci ta ci gaba da bin kaza za ta kama,
bawa ya gudu don kada a dake shi da bulala,
dogari ya ci gaba da shan ruwansa. Sarki da
Sarauniya da 'yan rakiyarsu suka sauka daga kan
dawakinsu. Rayuwa dai ta dawo a fadar kamar
yadda take a farko. Aka yi ta mamakin wannan
al'amari da ya faru.

Mutanen gari suka ci gaba da yi wa Sarkinsu
biyayya, da ma can ba su nada wani sabon Sarki
ba, saboda labarin adalci da taimakonsa da suka
samu daga kakanninsu. Sarki ya aurar da 'Yarsa
ga Dan Sarki, kuma ya yi murabus ya nada shi a
matsayin sabon Sarki. Suka yi zamansu cikin jin
dadi da kwanciyar hankali, har mai yanke jin dadi
ta zo yanke.

whatsapp number
08071051138
===| KARSHE |=== —

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
...


Read / Download FADAR BARCI

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album