Join Our WhatsApp Group

HATSABIBAN SADAUKAI Complete Hausa Novel Document by HATSABIBAN SADAUKAI


HATSABIBAN SADAUKAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 51261



HATSABIBAN SADAUKAI

Reading Time: 4 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Habibullah Muhammad Kabara ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 289.61 kb

File Type: txt

Views: 702+

Download: 314+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: **************HATSABIBAN SADAUKAI

***************CIGABAN ZUBAR DA JINI

***************1 PART A

LBR

***************HABIBULLAH KBR

Tace lallai na yarda cewa ke yarinya ce baki san menene mulki ba
Inaso ki sani babu abinda mutum baya iya yi indai yana da sarauta a hannunsa
Bayan haka hakika kin bani kunya tunda har kika nuna cewa
ni bazan iya biya miki bukatunki ba ke kinsan wacece ni da kuma irin karfin ikon da nake dashi

Kodajin haka sai marfuza ta mike tsaye yadda suna iya jin numfashin juna
Tace kwarai kuwa abindana fada daidai ne kuma wannan hukunci da kika yanke idan har bakiyi gaggawar barinsa ba to zaki tafka babban kuskure wanda nan gaba sai kinyi nadamar aikata shi

Domin har yanzu baki san wadannan mutane biyu ba wato sarki aryan da gimbiya walisa
Ina tabbatar miki cewa duk abinda kike takama dashi to suma suna dasu
Tana gama fadin haka saita wuce tabar sarauniya suzaila a tsaye tana kallonta

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A BIRNIN DURGAN
***** ****** ******* ******

Al'amarin yarima walisu kuwa lokacin daya kama hanya ya tafi neman gawar sadauki hassanul basari
Saidaya kewaye duniya acikin abinda bai wuce mako guda ba
Amma ko kadan bai sami koda labarin inda gawarsa take ba
Kwatsam wata rana yana tafiya kawai sai yaga zoben hannunsa
Yayi jajur sabanin yadda ainihin launinsa yake
Koda ganin wannan al'amari sai ya bushe da dariya yace
Tunda har ban sami ganin hassanul basari ba ai hakan ba wani abu bane
Domin komai kankantar makiyi ba'a raina shi
Ba komai ya gani ba face hoton gimbiya walisa tun daga lokacin data baro birnin shawana
Har zuwa sanda ta kwanta barci bata sani ba dokinta ya dauketa ya kaita can birnin durgan
Koda gama ganin wannan al'amari sai ya bushe da dariya yace
Amma wannan yarinyar ta yaudari kanta yanzu da wannan dan guntun karfin sihirin nata zatace zata iya hanani abinda naga dama
Tabbas kin tabka babban kuskure arayuwar ki
Amma kuma babu abinda nakeso a rayuwata kamar makiyi don haka bazan bari sarauniya suzaila ta sami nasara akanki ba dolene yau na cika alkawarin
dana daukarwa kaina na fara fita farautar rayuka tunda har walisa ta sami lafiya
Kuma dolene na farkar da ita daga wannan barcin da take inaso da idanunta ta dinga ganin jini yana fallatsi asama


Yana gama fadin haka sai take ya runtse idanunsa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi masu karfin gaske
Faruwar hakan keda wuya sai take wani farin haske ya fita daga cikin idanunsa ya tashi sama sannan ya tarwatse acikin iska kamar bai taba wanzuwa ba

Cikin dakiku kadan wannan hasken ya isa birnin durgan kai tsaye ya wuce zuwa cikin gidan kurkuku
Har cikin dakin da aka tsare gimbiya walisa
Koda zuwan hasken sai take ya shiga cikin kirjinta ya kewaya duk cikin jikinsa
Firgigit gimbiya walisa ta farka daga barcin da take a firgice
Kawai sai ganinta tayi acikin kurkuku daure cikin murtuka murtukan sarkoki
Kuma bata san sanda tazo wannan kurkukun ba ai kuwa nantake ta takarkare ta kwarara uban ihu
Sannan ta fara kokarin kwance sarkokin dake jikinta
Cikin mamaki sai taji kamar an zare mata dukkan jijiyoyin jikinta taji hatta hannunta ba zata iya dagashi ba
Koda ganin haka sai ta fara kokarin amfani da karfin sihirinta domin ta tsinka sarkokin dashi amma nan ma sai taji kamar an daure harshenta domin daga shi ma ta kasa bare ta furta kalaman tsafi guda daya

Da ganin wannan al'amari sai nantake wata kwallar takaici ta zubo mata
Kuma ta fara dana sanin barcin daya saceta akan dokinta
Domin ta tabbata shine silar zuwanta wannan kurkuku
Babban abinda yafi damunta shine rashin sanin inda take da kuma wanda ya kawota wannan wuri

Tana cikin wannnan hali ne kawai sai taga wani irin farin haske
ya ratso cikin ginin dakin da take ciki ya shigo cikinsa
Take fuskar dan uwanta yarima walisu ta bayyana acikin hasken
Yana kyakyata dariyar mugunta kuma daga hatta sautin dariyar tasa tana ji ba iya hotonsa take gani ba
Amma duk ragowar hadiman da suke cikin kurkukun da sauran fursunoni basa sanin abinda yake faruwa
Daga can sai yarima walisu ya murtuke fuskarsa kamar wanda aka turo masa da sakon mutuwa
Take ya dakawa walisa tsawa yace

Yanzu ke banda rashin kunya irin taki da wannan dan guntun sihirin naki kike tunanin zaki iya tunkarata?
Ke wacece kuma wanne mataki kika taka a tarihin rayuwar ki ?
Ni kuwa nine hatsabibin kuma tantirin boka wanda ba'a taba samun kamarsa ba
Fiye da shekaru dubu biyu baya nine wanda ya gagari manyan sadaukai da manyan bokaye
Sai da takai har bauta mini suke domin ni buwayar sadaukai ne
Nine wanda ganinsa yafi ganin mutuwa muraran agaba tashin hankali
To ke kuma tayaya kike tsammanin zaki iya samun galaba akaina
Bayan yanzu haka kin fada tarkon wata kankanuwar sarauniya…… .
Kafin ya gama fadin haka tuni tayi sauri ta tari bakinsa tace
Karya kakeyi, kamar yadda kake fada cewa kaga zamani mai yawa
To hakan bashi bane zai nuna maka cewa kai dauwamamme bane
Kuskuren da kake tafkawa a rayuwarka shine na cewa babu hatsabibin sadauki kamarka
Hakanne ma yasa a baya hassanul basari ya sami galaba akanka
Bayan haka ina shawartarka daka gaggauta fita daga cikin jikin dan uwana…… .
Kafin ta gama fadar haka tuni hoton komai ya bace

Duk wannan tattaunawa da suke yi yana tsaye a kan iska suke yinsa
Domin hoton fuskarsa kawai ya tura mata aikuwa koda yaji irin maganganun data fada masa sai
Take ya canja hanyar tafiyarsa ya nufi birnin durgan
Kasancewar shi ba karamin tantirin matsafi bane cikin dakiku kadan ya bayyana a birnin
Yadda abin ya kasance shine
A cikin tsakiyar yinin rana yayin da mutane suke tafiyar da harkokin kasuwancinsu
Akowacce rumfa kuwa zaka tarar da dakarun sarauniya suzaila a tsaye agabanta
Suna kallon duk irin cinikin da mai rumfar yake domin da zarar ya tashi daga kasuwar zai raba ribar tasa ne gida hudu ya dauki kaso guda ragowar kashi ukun kuwa ya baiwa dakarun sukaiwa uwar gijiyarsu
Idan kuwa har ya kuskura yayi gardama take zasu kamashi su tusa keyarsa wajen sarauniya anisa
Ita kuma da zarar an kaika gabanta take anan zata sa ayanke maka hukuncin kisa domin ko kadan bata da tausayi
Wannan dalilin ne yasa gaba daya suke matukar shakkarta kuma suke mata biyayyar dole domin sunsan cewa jayayya da ita daidai yake da sayen mutuwa da kudinka
Kuma ko kadan wadannan dakaru basa karbar cin hanci ko kuma tauye mata kudi
Saboda sun san sharrinta da kuma son dukiyarta

Suna cikin wannnan hali ba zato ba tsammani sai take
Suka dinga ganin kasar birnin tana darewa biyu
Gidaje suna ruftawa cikinta
Nanfa gari ya hautsine da guje gujen mutane da kuma iface ifacensu
Wata irin walkiya da tsawa suka cika birnin gaba dayansa
Ana cikin haka kawai sai gani sukayi wasu irin kananun kwari masu dan karen kyau suna fitowa daga cikin karkashin kasa
Koda mutane sukayi arba da wadannan kwari sai duk suka manta da tashin hankalin da suke ciki
Suka tsaya suna kallon kwarin
Koda wadannan kwarin suka gama bayyana sai kasa ta hade komai ya koma yadda yake da kamar babu wani abu daya taba faruwa
Yayinda mutane suka ga wadannan kananun kwari sai take sukaji sun kamu da tsananin sha'awarsu
Nanfa suka fara rububin kama kwarin domin su kai gida su ajiyesu saboda su kawata gidajensu dasu
Babu abinda zai baka tausayi face kaga mutum ya wahala kafin ya kama
Amma da zarar yazo hannunsa sai kaga dakaru sunje sun sa masa duka har sai sun kwace abinda yake hannunsa
Kafin adauki lokaci mai tsawo tuni mutanen sun kama kwarin da yawa a cikin hannayensu
Suna rububin tafiya su ajiyesu ai kuwa ana cikin wannnan hali ne kawai
Sai gani sukayi wadannan kananun kwari sun fara huda jikkunansu suna shiga ciki
Suna cinye naman jikinsu domin yawo suka dingayi acikin jikinsu kamar yadda jini yake yawo
Wohoho nan fa hankalin mutane ya kara dugunzuma suna ihun neman taimako amma babu damar hakan
Suna cikin wannan tashin hankaline kwatsam sai sukaga wata irin tsawa da walkiya ta taso daga sama
Acikin walkiyar ne kawai suka hangi wani mutum yana saukowa
Hannunsa ruke da wata iriyar sandar tsafi kallo daya zakayi masa kasan cewa ya cika hatsabibin gaske
Ba kowa bane wannan mutumin ba face yarima walisu ne da kansa
Ahankali har ya sauka atsakiyar birnin durgan alokacin da mutane suketa faman ihu da neman taimako sakamakon cin naman jikinsu da wandannan kwarin suke
Wani abin tausayin ma shine babu wanda yake da ikon taimakawa wani acikinsu domin kowa ta kansa yakeyi saidai kaga mutum ya fadi kasa yayita shure shure har ya mutu
Ai kuwa koda bayyanar yarima walisu sai take mutane suka fara tahowa gurin da yake domin ya taimaka musu
Abinda basu sani ba shine duk wannan abu da yake faruwa shine ya haddasa musu shi
Koda suka kusa zuwa. Dai dai inda yake sai nantake wani irin bakin duhu ya sauko ya mamaye birnin yadda hatta tafin hannunka ba zaka iya gani ba
wannan sandar ta hannunsa kuwa ta rikide ta zama wata iriyar sarka mai kaifin gaske kamar reza
Kawai sai ya fara cizge kawunan mutane da ita
Nanfa birnin gaba daya ya cika da ihun mutane da iface ifacensu
Babban abin tashin hankali ma a sannan shine mutane basa sanin lokacin da suke cusa kansu cikin hallaka
Duk sa'adda yarima walisu yayi cilli da sarkar hannunsa sai dai kaga tana fizge kawunan mutane kamar ana sassabe agona
Jini kuwa ya dinga kwarara ako ina na cikin birnin domin hatta kwatocin cikin kasar sai da suka rine saboda yawan jinin da yake gudana
Koda aka dauki lokaci ana cikin wannan yanayi sai gidajen birnin gaba daya suka fara rusowa suna fadowa suna danne mutane
Wasu mutanen ma su suke kai kansu inda zasu hallaka ba tare da sun sani
Wannan bala'in ba a guri daya ya tsaya ba harda gaba daya sassan birnin
Domin a wannan lokaci sarauniya suzaila na zaune acikin turakarta
Ta ajiye a binci agabanta tana ci kawai sai taji kasa ta fara girgiza burbushin bulo yana zubowa
Koda ganin wannan al'amari sai nantake ta zaro madubin tsafinta
Ta shafe shi domin taga abinda yake faruwa
Kawai sai gani tayi madubin tsafin nata yaki yayi aiki koda ta matsa abincike sai nantake yayi bindiga ya tarwatse
Da ganin wannan al'amari sai ta kwarara ihu wanda ya kara firgita sauran mutanen da suke cikin gidan sarautar
Cikin sauri ta shuri makamanta na yaki da kuma gurayenta ta falfalo da gudun gaske ta fito daga cikin gidan sarautar
Tana gama fitowa daga cikin gidan sarautar ne shima gaba dayansa ya rufto kasa ya ruguje

Ai kuwa da fitowarta sai ta tarar birnin gaba daya ya cika da gawarwakin mutane ko ina ka duba babu abinda zaka gani face jini yana ta kwarara kamar ruwan famfo

Ai kuwa cikin azababben gudu ta nufi can inda yake jiyo sautin ihu yana tashi
Wani irin gudu takeyi idan ka ganta sai ka zata akan iska take tafiya
Tafiya kadan tayi kawai ta iso cikin tsakiyar kasuwar garin kuma ta hango yarima walisu yana ta yiwa mutanen ta kisan wulakanci
Koda ganin wannan al'amari sai take ta daka tsalle ta tashi sama
Sannan ta runtse idanunta ta fara karanto wadansu irin dalasiman tsafi na musamman masu matukar wahalar karantawa
Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai wasu irin zabga zabgan kibiyoyin tsafi suka fara fitowa daga cikin karkashin kasa
Wasu kuma daga cikin sararin samaniya kamar ana ruwansu
Dukkan wadannan kibiyoyi sai suka taho kan yarima walisu da gudun gaske domin su shige jikinsa
Cikin matukar zafin nama shima ya karanta wadansu dalasiman tsafi irin nasa
Faruwar hakan keda wuya saiga wasu irin murtuka murtukan garkuwowi sun bayyana sun kewayeshi
Ai kuwa koda kibiyoyin suka sauka ajikin garkuwoyin sai take dukkansu suna narke tamkar ruwa
Adaidai lokacin ne sarauniya suzaila ta karaso daidai inda walisu yake
Ta daga takobinta sama cikin azababben karfi ta kai masa sara da nufin ta raba kansa gida biyu
Koda takobin ta sauka ajikinsa sai take ta kama da wuta kamar garwashin wuta
Saida zafin wutar ma ya kona tafin hannunta don haka bisa dole ta saki takobin tata ta fadi kasa
Kafin ta kara wani yunkuri tuni yarima walisu ya nunata da dan yatsansa
Take wata irin iska mai karfi ta fito daga cikin yatsun hannunsa ta shureta tayi sama da ita kamar takarda ta dinga wujijjigata
Koda ganin halin data shiga sai kawai yayi mata wani murmushi mai nuna tsantsar mugunta
Sannan ya juya mata baya ya cigaba da zaluncin da yakeyi tana ji tana gani amma bata ikon yin komai
Nanfa ya canja salon irin kisan da yake musu ba irin na da ba
Abin kuwa daya dingayi shine diban mutane,maza da mata yara da manya harda dabbobin garin ya dingayi da wata irin iskar tsafi mai karfi yana daga su sama da ita suna ta faman ihun neman taimako amma da zarar sunyi kololuwa a sama sai kaga iskar ta tsinkasu tayi musu filla filla
Saidai kawai kaga jini da sassan jiki suna zubowa kasa daga sama kamar ana ruwan sama

Dukda tsananin rashin tausayi irin na sarauniya suzaila a wannan rana saida taji tausayin mutanen ta yayi matukar kamata
Kuma ta fara nadamar zaluncin data dinga aikatawa a baya domin yanzu ta tabbatar da cewa mutuwa zatayi bata isa ta kubuta daga sharrin wannan azzalumi ba
Nanfa ta fara tunani acikin zuciyar ta kan labarin wani hatsabibin boka da iyayenta suke bata mai suna sahibul ukub
Da irin tsananin zaluncin sa da kuma labarin cewa masana sun tabbatar da cewa zai sake bayyana bayan shekaru dubu biyu
Kafin ta gama yin wannan tunanin da takeyi har ya gama kashe mutanen birnin gaba daya ba kajin sautin komai face iskar da take dauke da ita
Nan take ya fizgo sarauniya suzaila daga sama ya doka ta da kasa
sai da kura ta tashi sama sakamakon karfin dukan da yayi mata shatar alamun jikinta suka bayyana akan kasa
Kawai sai ya kara dagota sama fuskarsa a murtuke kamar wanda bai taba fara'a ba a rayuwarsa
Yace ke wacece a duniyar tsafi da har zaki hada karfin sihirinki da nawa?
Kuma wanne irin mataki kika taka a fannin sihirin tsafi ??
Ki sani na hadu da manyan matsafa da kuma sadaukai wadanda suka shafeki aduk fannin da kike takama dashi fiye da shekaru dubu biyu baya bayan haka inaso ki sanni hatta kakanninki suna daga cikin wadanda suke bauta mini a wannan zamanin saboda karfin iko na
Amma saboda rashin kunya kece zakizo da wan dan guntun tsafinki kice zaki tareni
Saboda...


Read / Download HATSABIBAN SADAUKAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album