Join Our WhatsApp Group

DAJIN DUHU book 1 Complete Hausa Novel Document by DAJIN DUHU book 1


DAJIN DUHU book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 24640



DAJIN DUHU book 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 128.12 kb

File Type: txt

Views: 1047+

Download: 422+

Last download: 5 days ago

Description/Story: An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

DAJIN MUTUWA
littafi na daya 1
Na Abdulaziz Sani M gini
Typing - Shuraihu Usman
Part 1A.
Awasu shekaru da dama da suka
A shude a birnin Farisa anyi wani
mashahurin sarki mai suna Hamaru ibini Salkuf.
Sarki Hamaru ya wadata da dukiya mai
tarin yawa gami da karfin mulki domin a
wannan lokaci akwai sama da manyan garuruwa
gudu dari bakwai a karashin mulkinsa. Haka
kuma yana da karfin mayaka bisa dalilin haka
ne ma dukkanin kasashen duniya ke shakkar
sarki Hamaru kuma ake yi masa biyayyar dole
da girmamawa.
Kash, duk wannan dukiya, daukaka da
mulki na sarki Hamaru sai suka zamo a banza
tunda sun kasa share masa hawaye bisa abin da
ya addabi rayuwarsa wato matsalar rashin
haihuwa.
Sarki Hamaru na da matan aure a kallah
guda arba'in da duriya kuma tun yana saurayi
dan shekara ashirin da biyu yayi auren fari
amma har shekara saba'in bai samu haihuwa ba,
wannan matsala ba karamin jefa sarki tayi ba
cikin mugun bakin ciki. Babu irin kokarin da
sarki Hamaru baiyi ba wajen neman maganin
haihuwa a wajen likitoci da bokaye amma ba'a Samu dace ba duk sa'adda sarki Hamaru ya tuno
da wannan matsala sai bakin ciki ya taru yayi masa katutu a zuciya harma ya boye kansa ya
kama kuka.
Ana cikin wannan hali ne wata rana wani
bakon boka waishi Shamakalu ya sauka a birnin
Farisa a cikin gari ya zamana cewa ya zo da
abubuwan al'ajabi wadanda suka firgita jama'a
domin kuwa yana iyayin abubuwa da dama
wadanda ake ganin cewa har abada ba za su
yiyu ba. Abu na farko da yayi wanda ya baiwa
kowa matukar mamaki shine akwai wata
tsohuwar rijiya a tsakiyar birnin wacce ta gagari
a budeta a debi ruwanta saboda tarewar wasu
bakaken aljanu a cikinta. Sai da ya zamana
cewa an gine rijiyar an kangeta, amma ko kusa
da wajen mutum ya je sai dai a dauki gawarsa,
kai hanyar da ta doshi wajen ma ba'abi sama da
tsawon shekaru talatin amma a ranar da boka
Shamakalu ya sauka ya banke kofar ginin, kuma
ya bude murfin rijiyar da karfin sihirinsa ya
fatattaki duk bakaken aljanun da ke wajen ya
debi ruwan rijiyar ya sha ya shayar da dokinsa
Harma ya mayar da dakin rijiyar masaukinsa wato ya rinka kwana a cikin dakin da rijiyar
take. Ko da faruwar wannan al'amari nan da nan
labarin Shamakalu ya cika gari sai ga jama'a
nata bulbulowa daga ko ina birni da kauye suna
zuwa neman biyan bukata. Duk wanda ya zo da
larura ta rashin lafiya sai Shamakalu ya debi
ruwan wannan tsohuwar rijiya ya bashi ya ce ya
sha. Ai kuwa da zarar mutum ya sha ruwan sai
ya warke daga cutar nan take ko da kuwa ya
shekara dari a cikin larurar.
Babban abin al'ajabi na biyu da
Shamakalu yayi shine akwai wata sihiratacciyar
Damisa wacce kullum daren duniya tana yawo a
cikin birmin Farisa. Duk wanda tsautsayi ya sa
ya yi arba da ita sai ya zama gawa ko kuma ya
hauka ce ko ya zama makaho ko ya nakasce. a
daren da Shamakalu ya shiga wannan birni yayi
arba da sihirtacciyar damisar suka yi gumurzu
ya kamata da hannunsa sai gashi tayi ladaf yana
sarrafata tamkar karen farauta ya zamana cewa
ko da yaushe tana durkushe a gabansa har ma
yana umartarta da yi masa wasu aiyukan. Ita dai
wannan Damisa duk mutumin da bai haura
shekara saba'in ba bai san farkon baiyanarta ba a Birnin Farisa sai dai kawai ya taso ya ganta ko
ya ji labarinta
Damisar takan fito ne kullum da tsakiyar
dare kuma idan tayi haniniya sai an jiyo sautin
haniniyar a ko ina cikin birnin kuma duk wanda
ya ji haniniyar sai ya firgita ainun wasu ma
asalin kamuwa da gudawarsu kenan.
Daga ranar da Shamakalu ya dira ba'a
sake jin haniniyar wannan Damisar ba sai ga
shima ana zuwa kallonta a banza da rana tsaka
ana ta al'ajabi.
Lokacin da sarki Hamaru ya sami
tabbacin wadannan abubuwan al'ajabi wadanda
boka Shamakalu ya yi sai ya aikamasa da
dukiya mai yawa kuma ya gaiyaceshi izuwa
fadarsa domin ya gabatar da bukatarsa a gareshi.
Yayin da yan aiken sarki suka jewa boka
Shamakalu da wannan sako sai yaki karbar
wannan dukiya kuma ya ce da su su koma ga
sarki su shaida masa cewa shi baya karbar
kyauta ko sadaka haka kuma baya zuwa wajen
mai neman biyan bukata sai dai a zo wajensa.
Nan take Shamakalu ya yi tsafi sai
dukiya ta baiyana ninkin wacce sarki ya aiko masa da ita. Kawai sai ya báiwa 'yan aiken sa
ya ce ku debi wannan dukiya na baku ita kyauta
domin ni ba'a zuwa wajena a tafi hannu banza
face an sami karuwa. Cikin tsananin farin ciki
da rawar jiki 'yan aiken sarki suka kwashe
wannan dukiya suka yi ta dogiya sannan suka yi
sallama suka tafi.
Lokacin da 'yan aiken suka koma fadar
sarki Hamaru suka kwashe labarin duk abin da
ya faru tsakaninsu da boka Shamakalu suka
zaiyane. Sai ran sarki ya baci zuciyarsa tayi
bakinkirin ya fusata ainun. Nan take ya tuno da
karfim,mulkınsa da kuma darajarsa a idanun
duniya amma ya za'ace boka guda daya ya shigo
har cikin birninsa ya nuna masa gadara.
Nan take sarki Hamaru ya ce "A shirya
dakarun yaki mutun dubu su je su fatattaki
wannan boka daga birninsa da karfin tuwo."
Ko da jin wannan danyen hukunci sai
fadawan sarki suka shiga rarrashinsa suna bashi
baki da kyar ya amince cewar a aikawa da boka
Shamakalu wasika cewar sarki na bukatar ya
kwashe komatsansa ya bar masa bininsa
Salin'alin ba da tashin hankali ba.
Nan take aka rubuta wannan takarda kuwa sai aka rasa wanda za'a baiwa takardar ya je ya kaiwa boka Shamakalu domin duk wanda
aka baiwa daga cikin bayin sarki sai ya kama
kuka yana neman ayi masa uzuri don kada ya je
fushin boka Shamakalu ya tabbata akansa.
Yayin da aka rasa wanda zai kai wannan
takarda sai sarki ya ce "aje kurkuku a fito da
wani mutum waishi Shafaru a bashi takardar ya
kai in ya so duk bala'in da zai same shi ya same
shin kuma da zarar ya dawo a sake damkeshi a
mai dashi kurkukun a kulle."
Asalin Shafaru kanine ga mahaifin sarki
Hamaru kuma shine ya cancanta ya hau karagar
mulki bayan mutuwar mahaifin sarki Hamaru
amma saboda kasancewar Hamaru sadauki
kuma azzálumi sai ya kama Shafaru ya kulle shi
a kurkuku kuma ya kori iyalansa daga cikin
gidan sarauta ya zamana cewa suna walagigi a
gari basu da makwanci basu da cin yau bare na
gobe, ma'ana suka wulakanta suka zama
Almajiran dole domin an rabasu da dukkanin
abin da suka mallaka.
A halin yanzu Shafaru ya shekara ashirin da daya a cikin kurkukun kuma tunda aka
kulleshi dai dai da rana daya bai taba fitowa ba
kuma bai sake saduwa da iyalansa ba. Shafaru
na da mata guda daya da kuma 'ya daya wacce
sa'adda aka daureshin bata wuce shekara uku ba
a duniya ana kiranta da suna
Humaila.
Mahaifiyar tata kuwa sunanta Amshira.
Wani babban abin takaici shine ba'a taba
barin Humaila da Amshira sun ziyarci Shafaru a
gidan kurkuku ba. Duk sa'adda suka je ganinsa
sai a koresu ayi musu mulakanci, wani lokacin
ma har dukansu ake yi a fatattakesu.
Da farko sa'adda Humaila take yarinya
karama kullum sai Amshira tayi bara ko kuma
tayi aikatau sannan suke samun abin da za su ci,
kuma komai ruwa komai rana sai dai su kwana a
kwararo ko a cikin rami sun sha jin giftawar
sihirtacciyar damisar nan daf da su amma wani
iko na Allah tsautsayi bai sa ta taba ganinsu ba
amma duk sa'adda Humaila ta ji haniniyar
damisar sai ta kwana bakwai tana a mai da
gudawa, dakyar take samun lafiya.
Lokacin da Humaila ta fara zama
budurwa, kyawunta da na siffarta suka fara baiyana sai azzalumai suka fara kawo mata
farmaki don suyi lalata da ita. Da kyar Amshira
ta rinka kwatarta. Ba shiri suka nemi aikatau a
gidan wani attajiri har ya basu makwanci a cikin
gidansa.
Shi dai wannan attajiri yana da mace guda
daya amma daga ranar daya kyallara ido ya ga
Humaila sai kwadayi ya kama shi don haka
wata rana matarsa bata nan ta tafi ganin gida sai
ya ribaci Humaila har ta debo masu ruwa takai
masa cikin turakarsa. Da shigarta cikin turakar
ya faki ido ya ga babu kowa a kusa sai ya shiga
ciki ya mai da kofa ya rufe, kawai sai ya afkawa
Humaila suka kama kokawa ya na son yayi
lalata da ita da karfin tsiya. A wannan lokaci
Amshira na can a cikin dakin da aka basu tana
ta sharar barci bata san abin da ke wakana ba.
Yayin da attajiri ya ga ya kasa biyan
bukatarsa sai ya mangare Humaila ta fadi kasa a
galabaice, har ya yunkura zai afka mata ashe
hannunta ya kai kan wata wuka cikin zafin
nama ta dauki wukar ta soka masa a ido , take
attajiri ya kurma ihu, jini kuwa ya kama
bulbula daga cikin idon nasa. Kafin bayin gidan Su iso tuni Humaila ta ruga dakin da mahaifiyarta ke kwance, cikin rudewa kuma ta
na kuka ta tashi mahaifiyarta ta sanar da ita duk
abin da ya faru tsakaninta da attajiri. Yayin da
Amshira ta ji wannan batu sai ta ce da ita.
"Shin wani ya ganki lokacin da ki ka fito
daga dakinsa?"
Humaila ta ce "A'a kafin bayin gidan su
kawo masa dauki tuni ta rugo nan."
Amshira ta ce "Da kyau yata kinyi farar
dabara, ki kwantar da hankalinki babu inda
Zamu tafi har sai. dare yayi sannan mu hada
namu ina mu mu sulale."
Wannan shine abin da ya faru tsakanin
Humaila da mahaifiyarta Amshira.
'al'marin attajiri kuwa lokacin da ya
kurma ihu sakamakon wukar da Humaila ta
caka masa a ido jini na ta zuba sai ga bayin
gidan sun rugo da gudu izuwa cikin turakar tasa.
Da zuwa suka iskeshi shi kadai yana ta birgima
a kas yana ihu, cikin gaggawa suka sa tsumma
suka daure idanun don tsaida jini sannan aka
ruga aka kirawo mai magani yayi masa magani.
Nan da nan 'yan'uwa da abokan attajiri suka cika gida. Yayin da aka tambayeshi yadda wannan
al'amari ya faru sai ya ce "Ai bisa tsautsayine ya
zame ya fada kan wannan wuka ta cike a
Idanunsa." Dalilin da yasa kuwa yayi wannan
karya shine zai ji kunya idan matarsa da jama'a
suka ji cewa yar almajira ya farwa ta yi masa
wannan aika-aika. Nan dai aka yi ta yiwa attajiri
jaje bisa rasa idonsa guda da yayi.
Lokacin da labari ya riski matarsa sai ta
baro gidansu da sauri tana kuka ta zo ta kama
aikin jinyarsa.
Yayin da dare ya raba sai Humaila da,
Amshira suka hada yan komatsansu suka sulale
suka bar gidan. Da fitowar sai suka wuce kai
tsaye izuwa gidan wata tsohuwa da ake kira
Shabiratu.
Tsohuwa Shabiratu ta kasance dillaliya a
gidan sarki kuma shekarunta a kallah za su kai
casa'in da motsi, ita dai Shabiratu ta kasance
mace mai tausayi da taimakon ma kaskanta.
Humaila da Amshira sun saba da wannan
tsohuwa tun suna kwana a kwaroro kuma tasha
yi musu tayin Su koma gidanta da zama amma
sai suka ki saboda gidanta a kusa da inda Tsohuwar rijiyan nan take mai kwankwamai.
Duk da cewa akwai tazara mai dan yawa
tsakanin gidan Shabiratu da wannan rijiya su
Amshira na matukar jin tsoron zuwa. Da yake
masu iya magana sunce idan kaga ki gudu to sa
gudu ne bai zoba kuma abin da ya koro bera
daga rami ya fada wuta, ya fi wutar zafi. Tabbas
Su Humaila sun san cewa idan suka ci gaba da
zama a gidan attajiri tabbas sai ya jefa
rayuwarsu a cikin bala'i bisa wannan rasa ido
guda da yayi. Haka kuma indai zai gansu a wani
wurin ma ba zai kyalesu ba. Bisa wannan
daliline suka yi tunanin cewa dole ne su nemi
wani gida inda zasu buya. Da suka yi dogon
tunani sai suka ga cewa ai basu da wani zabi
face su tafi gidan tsohuwa Shabiratu.
Cikin tsananin razani da fargaba kuma
jikinsu na kyarma suka tunkari gidan tsohuwa
Shabiratu. Abu nafarko dai suna tsoron
gamuwa da sihirtacciyar damisa sannan kuma
suna shakkar bin wannan hanya wacce zata nufi
inda muguwar rijiya take. Haka dai suka kama
hanya a cikin daren suka yi ta tafiya har suka iso
kofar gidan tsohuwa Shabiratu cikin sa'a bá tare da sun hadu da komai ba. Da zuwa sai suka
buga kofar gidan sau daya.
Bisa mamaki sai suka ji muryar tsohuwa
Shabiratu tana mai cewa Wanene nan yake
buga mini kofa da wannan tsohon dare?" Cikin
murya mai rawa.
Amshira ta amsa ta ce "Ni ce almajira
Amshira tare da 'yata Humaila. Yake dillaliya
kiyi mana rai ki bude mana mu shigo."
Ko da jin wannan batu sai dillaliya
Shabiratu ta mike da sauri ta fito daga cikin
dakinta taje ta bude kofar gidan.
Amshira da Humaila suka shige ciki
sannan ta mai da kofar ta rufe. Shabiratu ta yiwa
su Amshira kallon tsaf ta fuskanci cewa lallai
suna cikin tashin hankali kawai sai ta jasu izuwa
cikin turakarta tayi musu shinfida ta ce su
kwanta suyi barci bata bukatar ta ji komai da ga
bakinsu sai gobe da safe. Cikin tsananin murna
suka kwanta suna masu yi mata godiya. Ita dai
ba tace da su uffan ba har barci ya kwashesu. Ita
kuwa Shabiratu bata sami damar rintsawa ba sai
gefin Asubahi.
Yayin da Amshira da Humalla suka farka daga barci sai suka tashi suka wanke jikinsu,
sannan suka kama share-share da gyaran gida.
Kafin Shabiratu ta farka daga barci sun gama
kintsa gida har ma sun dafa abin kalaci.
Gamawarsu ke da wuya sai tsohuwa Shabiratu
ta farka koda ta ga yadda suka gyara gidan har
ma suka dafa abinci sai farin ciki ya lullubeta,
al'amarin da ya janyo idanunta suka...


Read / Download DAJIN DUHU book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album