Join Our WhatsApp Group

HUSSAIN MIJIN ALJANA Complete Hausa Novel Document by HUSSAIN MIJIN ALJANA


HUSSAIN MIJIN ALJANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8169



HUSSAIN MIJIN ALJANA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 04, Apr 2023

Author: Fatima Rabiu Ummu Affan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Adventure novels

File Size: 46.04 kb

File Type: txt

Views: 2134+

Download: 278+

Last download: 1 day ago

Description/Story: yarinyar nan ta rainani ko?tace"barni da ita yanzu dai ya maganar Zainab yace"mum mubar wannan maganar ni zan kawo muku mata wacce zakuyi fahari da ni."


To muci gaba ko mu tsaya?🤪🤪


HUSSAIN 80K MIJIN ALJANA idan kuna so naji ruwan comments hakan zaisa ku sami posting kullum.

More comments more typing,idan naji comments na k'ara muku yawansa akwai chakwakiya kuma labari ne na gaske aha🤣🤣🤣🤣🤣


Ummu Affan.✍️
*HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*

*Dedicated to*
_Hajiya Maryam Sakatare_
_Aisha Galadima_
_Wannan page naku ne,kuyi yarda kuke so dashi_ 😂

*Special Thanks*
_Ga masu goyan bayan ci gaba da suburbud'o wannan littafi,karku damu yanzu aka fara._ 😂

*Da k'yau 'yan Fcbk gaskiya kun burgeni musamman MIJIN KWAILA FANS gaskiya iya wuya ana tare.*


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 3-4*

Hajiya ta kallesa tace"to Allah yasa haka dai" yace"hakan nema domin ni matar da zan aura sai kowa yayi mamakinta" Hajiya tace" *HUSSAIN* Ba dai cika baki ba kar azo ayi za6en tumun dare" yace"haba Mum fatan alkhairi dai."

Murmushi tayi tace"a kullum muna cikin yi muku *HUSSAIN*",Kamar mai tunani sai tace"kai amma nafa mance da d'auko Hafsat kuma kai nace zan aika" *HUSSAIN* Wanda har ya fara danna wayarsa yace"haba Mum wacece kuma hakan?,tace"bana son shashancin banza har ka mance da Hassu 'yar wajen Baba k'arami dake k'auye?da sauri ya zaro ido kamar zasu fad'o yace"Haba Mum yanzu saboda Allah a rasa wanda zaije d'auko wannan mahaukaciyar yarinyar saini,bayan ga direba" tace"to ba direban da zashi kasan dai Baba k'arami da fad'a,idan ba kai kaje ba haka zai dunga mita ka sani" Kallon Mum yayi zai magana tace"kar kace komai kaje ka d'aukota duka tafiyar batafi awa guda ba zuwa KUJAMA."

Ba don yaso ba haka ya tashi tare da mata sallama,yana tafe a mota yana tunani,sarai yasan halin yarinyar bata da hankali sosai,matsalarsa d'aya da ita ALJANUNTA domin tana da Aljanu abin tashin hankalin babu abinda *Hussain* yafi tsoro irin aljanu.

Haka yana tafe yana tunanin nan har ya kai Kujama,kai tsaye gidansu Hassu ya nufa,kafin ya kai ya hango wasu matasan mata biyu suna fad'a,parking yayi tare da fitowa yana masifa"Ke!Ke!!,bazaku bari ba?,wacce ke kimar d'ayar da alama tafi k'arfi da rashin kunya ta taso da cewa"to Malam ina ruwanka sa'ido sana'ar banza" k'arasowa yayi cike da bala'i yace"ke wa kike fad'awa magana?d'aga hannu yayi zai mareta,ai da ta kurma wani uban ihuww tuni jikinsa ya fara rawa,wani mutum ne ya k'araso da gudu sai da ya iso gurin *Hussain* ya gane ashe Baba k'arami ne,ita kuwa yarinyar nan tana ganinsa ta k'ara sautin kukanta tace"Baba k'arami kaga wannan mutumin ko?cike da masifa ya juyo yana cewa"wanne mutumin?sai ganin Hussain yayi tsaye kansa yana mazurai,k'ara bud'e ido yayi yace"wa nake gani kamar *USAINI*?da sauri bakinsa na d'an rawa yace"eh Baba k'arami ni ne."

Baba k'arami ya fara tafa hannu yace" ehye USAINI kaine kake mugun Hassu,yanzu Hassun kake bugu?, *Hussain* aransa yace"kuji wannan tsohon kamar yaji ance ya daketa,nai sani ba ashe maganar zuciya ta fito fili saiji yayi Baba k'arami na salati yace"eh lallai USAINI ka girma ni kake fad'awa magana eh lallai wuyanka yayi kauri."

Girgiza kai da Shafa sumar kansa yayi tare da fad'in "matsala", muryar Hassu yaji tana cewa"Baba wai daman wannan Yaya WUSAINI ne?(Su wusaini manya😂😂🤣🤣🤪)yace"shine fa bakiga ya kawo girma ba abinda yake fad'a mini",turo baki tayi tace"Baba dama kace zaizo mu tafi binni ko?bari na ruga gida Iya ta had'a min kayana a leda,kafin ya bata amsa tuni har tasa gudu har tana take k'afar Hussain saboda sauri,ina ta sani ita dai tayi gaba da gudu,da sauri ya janye k'afarsa yana gogewa da fad'in "wash kai-kai yarinyar nan bata da hankali fa.

Baba k'arami ya tasa shi gaba har gida,suna isa k'ofar gidan sai ga Hassu ta fito da leda hannunta da tsummokaran kayanta tace"mu tafi,daga Hussain har Baba k'arami suka bita da kallo.


*MORE COMMENTS MORE TYPING*

*COMMENTS*
*AND*
*SHARE*

*MUJE ZUWA*
_FATIMA SUNUSI RABI'U._*HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*

_Wannan shafin naki ne Maman Imam comment d'inki na burgeni matuk'a_

_Hahhhhh_🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 _Yau ake yinta fa,wasu sunce wai ya zata kasance da Hussain da Hassu_ 🤣🤣🤣🤣🤣 _Ku biyoni muje zuwa._


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 5-6*

Hussain yace"wannan wanne irin hauka ne,ke haka ake tafiyar?. Da sauri Baba k'arami yace"tofa ni fa matsalata da kai rashin hakuri abun magana bai wuya agareka,yanzu ita Hassu me ta sani wallahi idan har masifa zaka dunga mata gara ma a hakura da zuwan."

Hussain aransa yace"da hakan yafi" sai ji sukayi Hassu tace"a fasa zuwa ina taf wallahi sai naje,Kai Baba kasan yarda nake mafarkin binni kuwa tabbb",Baba k'arami yace"tunda tana son zuwa ya zanyi,sai ka shiga ku gaisa da Talatu ka fito ku wuce" ciki ya shiga bayan sun gaisa ya fito,ya shiga mota Hassu ma ta shiga,Baba k'arami yace"uhmmm kai dai Hussain baka da halin k'warai yanzu kazo k'auyen nan ko 'yar tsaraba nan babu sannan kuma zaka tafi babu ko kyauta,ni kam wannan rowa taka da yawa take",sai lokacin yasa hannu aljihu ya zaro dubu daya yace"ayi hakuri Baba k'arami ga wannan" amsa yayi yana jujjuya gudar dubun yace"yanzu dubu guda zaka bani saboda tsabagen rowa irin taka to me 'yar uwata tace ka kawo min" a hankali Hussain ya furta"wallahi mutumin nan ya cika matsala,a fili kuwa cewa yayi"tace zata aiko maka saboda ina sauri yasa ban tsaya amsar sak'on ba" Zaro ido Baba K'arami yayi yace"amma kai USAINI anyi shiryayye bazan fad'i d'ayan ba,yanzu saboda Allah ni kakewa bak'in ciki saboda tsabar bak'in ciki irin naka ka tsaya ka amsa shine kak'i saboda saurinka na banza da wofi to na gode kace mata zuwa jibi zanzo da kaina" yace"to" tare da jan motarsa yabar gurin yana mita.

Sam ya mance da Hassu dake rashe gaban mota yana da mita da cewa"Baba K'aramin nan matsala ne" Sai ji yayi an kece da dariya da sauri ya juyo Hassu ke dariya ba sassautawa kallonta yayi kafin yayi magana yaga ta kalli saman motar tana cewa"Eh mana haka ne fa" sai ta saki dariya,cikin d'aure fuska yace"ke lafiya?bata kallesa ba taci gaba da surutunta.

Sun shugo garin Kaduna,zasu wuce ta gurin wasu masu kayan marmari tace"Yaya Hussain don Allah tsaya ka sayamin" yace"ni ba mahaukaci bane irinki" ganin bashi da niyyar tsaya ta fara k'ok'arin rik'e sitiyarin ai da yaga tana niyyar sa su fara layi a titi ba shiri ya tsaya yada daka mata tsawa,ina ta sauraresa ai da gudu tayi ta fita sai gurin masu kayan marmari,tana zuwa ta zari ayaba ta 6are ta fara ci.

Mai kaya ya bita da kallo cike da mamaki,gani yayi ta zauna saman benci tana cinye waccar ta zari wata tare da d'aukar lemu wanda aka fere ta dasa masa hak'ora,yace"Malama lafiya?tace"ka had'a komai da komai na dubu d'aya" jin ciniki da sauri ya fara had'awa domin da farko ya d'auka mahaukaciya ce.

Hussain ya fito yana wani takon isa,ya k'araso ganin abinda take ya zaro ido yace"ke baki da hankali ne" wai lemu ya fara washe baki yace"ashe tare take da Yayanta wannan yarinyar da gani 'yar gata ce" Mik'a mata yayi tace"yauwa ashe dai ka gane" gashi nan shi zai baka kud'in" ta nufi mota,mai lemu ya juyo da fara'a yace"oga na 1k ne kawai aka had'a" Zaro ido yayi yace"1k kai baka da hankali zaka bata kayan 1k ina laifin na d'ari biyu" yace"ranka ya dad'e ai ita tace a had'a mata" tsaki yayi yana mita ya basa domin shifa ya tsani kashe kudi ba gaira babu dalili.

Dawowa yayi mota,amma babu Hassu sai dai ga kayanta da lemukanta a ciki,yace"wannan mahaukaciyar kuma ina ts nufa" d'aga kan da zaiyi ya hangota gurin masu kaji,tana ci hannu baka hannu k'warya,da mugun tsoro ya zaro ido,ganin ana had'a mata guda uku cikin leda rik'e baki yayi da sauri tare da zaro ido.

Mota ya nufa da sauri domin ya yajin zai iya biyan wannan kudin sai dai idan basu gansa ba za amsa na ledar su yafe mata wanda taci ko su jibgeta babu ruwansa.

Yana k'ok'arin shiga har sun iso,amsar ledar tayi tare da cewa shi zai biyaku,ta shige ciki,suka ce"Alhaji dubu biyar ne" cikin masifa yace"ni kunga na muku kama da Alhaji ne?ko kuwa tsabar rashin mutumci?,mutumin yace"Allah yabaka hakuri Malam",cikin tsawa yace"waye Malam?kai kafa kikayeni",mutumin yace"koma dai menene fara biyana kud'in kazar na wuce" yace"ni naci da zakace na biyaka?,Hassu ta lek'o daga mota tace"wai Yaya Wussain ka basa mu wuce mana" wata harara ya buga mata tare dasa hannu aljihu aransa yana cewa Wallahi sai nayi maganin yarinyar nan tunda ta sani asara ba gaira babu dalili.

Biyansa yayi,mutumin na magana bai kukasa ba domin ji yaje kamar ya makesa wai ansashi asarar dubu shida lokaci guda me yakai wannan takaici🤪🤪🤪(Don a gurin Hussain dubu shida kamar Dubu dari shida take🤣🤣🤣🤣).

Shiga mota yayi yana mita da haka suka isa gida,yana parking ya fita cike da k'uluwa Hassu tace"Yaya WUSAINI kazo ka d'aukar min kayana mana.

🤣🤣🤣🤣🤣

*MORE COMMENTS MORE TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️*

*COMMENTS*
*AND*
*SHARE*

_MUJE ZUWA_
*FATIMA SUNUSI RABI'U.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*


*Marubuciyar👇*
*UWANIN QAUYE*
*CIKIN WAYE?*
*NIDA YAYA LAMEER*
*KAINE SANADI*
*NAYI GUDUN GARA...*
*IZGILI*
*K'URUCIYAR SAPNAH*
*MAHAD'IN RAYUWATA*
*SANDAR MAKAUNIYA*
AND NOW👇

*HUSSAIN*
_MIJIN ALJANAH_


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 7-8*

Wani kallo ya mata da cewa"waye d'an dakonki?sakkowa tayi tare da dire basa ledar kayanta gabansa sannan ta d'auki ledar kazinta da su lemunta tayi gaba.

Tsuwww yaja tsaki tare da d'aukar ledar yace"wallahi Mum ta kawo mana matsala gida" domin shi fa gani ya ke Hassu ba kanta guda ba.

Kasancewar Hassu ta ta6a zuwa gidan yasa ta gane hanyar domin duk idan Baba k'arami zaizo wato mahaifinta tare suke zuwa,hakan yasa kai tsaye parlourn gidan ta nufa HUSSAIN na biye da ita.

Fatima da ke zaune parlour tana ganin Hassu ta tashi da murmushi tace"Laaaah Hassu sannu da zuwa" tace"yauwa tare da dire kayanta tsakiyar parlourn ta zauna,Hussain da ya k'araso ya jefa mata kayanta kusa da ita ya haye sama,yana mita,Fatima ta dunga dariya k'asa-k'asa.

Fatima ta jata zuwa bedroom d'inta,tana cewa"Hassu wannan kaji haka ba dai daga k'auye aka saki ki kawowa Hajiya ba?cike da shiririta irin tata tace"Yaya WUSAINI YA sayamin a hanya" sosai Fatima ta zaro ido tace"kai da gaske Yaya Hussain mai mak'o wanda d'ari biyar kafin yabaka aiki ne shine ya saya miki kazi har uku?Sosai Hassu tayi dariya sai-dai bata ce komai ba.

Fatima tace"bari na d'auka a sake d'umamawa lallai yau zamuci tafarrakin uban 'yan mak'o,zata d'auki Kajin taga su lemu tace"wannan kuma fa?sosa kai Hassu ta fara tare da rank'washin kan kamar mai kwarkwata tace"duka duk ya sayamin. Fatima bakinta ya kasa rufuwa sosai take mamaki sai tayi murmushi ta had'a dasu tace"bari a wanko" sannan ta fita zuwa kitchen.

Ko da Hassu tayi wanka,wasu ko d'ad'd'un kayanta ta saka riga da zani da kallabi irin mai santsin nan,ta zana ja gira da wani jan gazar nata da ta taho dashi ta ranbad'a kwalli tayi d'igo-d'igo a kumatunta da goshi.

Sannan ta fito,lokacin Hajiya ta fito Hussain ma shugowarsa kenan ya dawo masallaci,gurin Hajiya ta k'arasa tace"ina wuni Inna" Hajiya tana murmushi tace"Hafsat lafiya k'alau,kun shugo ina sama na shiga sallah fatan kun sauka lafiya,ta washe hak'ora"lafiya k'alau Inna sai-dai Wallahi tallahi kinji na rantse kuwa wannan Yayan Wusainin yayi ta min fad'a wai zai dake ni"

Hussain wanda tun tahowarta yake harararta yace"nayi miki fad'an damma ban faffasa miki baki ba asarar da kika sani" da sauri tace"yauwa Inna kinji ko?,Hajiya da Fatima da babu abinda suke sai dariya Hajiya tace"kiyi hak'uri 'yata Yayan ne naku da bak'ar zuciya kamar tsohon kuturu" Kallon Hajiya yayi fuskarsa babu walwala yace"abinda zaki ce kenan Hajiya bayan na sanar miki duk kan abunda ya faru tun zuwana Kujama har dawowarmu" Hassu ta d'aure fuska tare da zama tana harare harare.

Hajiya tace"ni kuna rud'ani na rasa bayan wa zanbi to duka kuti hakuri yarana",tashi Hussain yayi ya wuce ciki Hajiya tace"Hassu haka yake da zuciya ga saurin fushi halinsa haka yake don haka ki iya zama dashi" Hassu aranta tace"ai kuwa haka wallahi zai ganene,bayana min kallon bagidajiya ba 'yar k'auye da wannan zanyi amfani na gyara masa zama.

Fatima ta kawo naman sukaci gaba d'aya suka k'oshi suka sha kankana lemu da ayaba sannan suka kora da ruwa mai sanyi,Fatima tace"yau wace rana munci ta farrakin Yaya Hussain sarkin 'yan mak'o.

Hajiya tace"wallahi babu ruwana idan yajiki ke da shine",Ranar basuci wani abinci ba saboda sun k'oshi da naman nan.

Washe gari da safe,Hussain ne ya sakko cikin shirinsa na fita kasuwa,kasancewar babban shago ne garesu na sayar da atamfafo shadda yadi les kai duk wani abu da ya shafi kayan sawa suna sayarwa shagon Yayansa ne (HASSAN ATK)Kasancewar shi Hassan yana cen k'asar India to shi Hussain ke kula da shagon🤪🤪🤣🤣tare da sauran amintattun Hassan d'in.

Hassu wacce tun lokacin da ya fara bud'e k'ofa ta fito da sauri daman tun asuba da tayi sallah taje kitchen ta kad'a omo da ruwa da mai kad'an cikin k'aramar roba,jin yana bud'e k'ofa yasata saurin sakkowa tazo saitin k'ofarsa ta juye ruwan omon sannan ta shige cikin labule,

Fitowar da Hussain zaiyi cikin shirinsa ya d'au wanka sai tsantsi ya jamesa timmmm ya fad'i k'asan tass saboda wahala sai da ya saki k'ara,Hassu ta fito daga cikin labure tana shek'a dariya da cewa"wohwohwoh ya fad'i kuzo kuyi kallo,Fatima ce ta fito da sauri tana tambayar lafiya?ganin yarda Hassu ke tun tsura dariya ta kalli gurin da take kallo zaro ido tayi ganin Hussain 80k zube a k'asa ya kasa tashi,gaba d'aya jikinsa ya 6aci.


*MORE COMMENTS MORO TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️*

*Yasin,Yasin WhatsApp ku gyara ina son jin comments idan ba haka ba kuji d'if ato.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*

_DEDICATED TO_
_My k'awar amana Rukayyat Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar) Allah ya bar amana,Ya kaimu ranar bikin amin,Sannan ya bawa jinin jikinki lafiya mai d'aurewa yasa kaffara ne,ina yinki over my K'awata_🥰

_SPECIAL GIFT TO_
_Hauwa S Zaria_
_Anty Hauwa Mmn Uswan,Alkhairin Allah ya kai miki har gadon barcinki,ina yinki over my Antyna._🥰


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 9-10*

Hussain wanda ji yake kamar ya karye k'ugu ya d'ago fuska murtuke yana dubanta,dai-dai fitowar Hajiya wacce ke cewa"K'arar me naji kamar abu ya fad'i?ganin Hussain k'asa warwas ta yi...


Read / Download HUSSAIN MIJIN ALJANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album