Join Our WhatsApp Group

BABBAN GORO Book 1 Complete Hausa Novel Document by BABBAN GORO Book 1


BABBAN GORO Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11095



BABBAN GORO Book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 21, Nov 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 63.54 kb

File Type: txt

Views: 932+

Download: 250+

Last download: 2 days ago

Description/Story: BABBAN GORO
-------------------------
Littafina daya
.
Part 1A
.
With shuraih 99%
Typing by :- Shuraih Usman
.
Zaku sha karatu har ku gaji
.in naga bakwa respond toh zan ajiye littafina agefe
.
.
Awani zamani can baya anyi wani attajirin sarki wai shi
abul dinar ,wanda matsafa da masu harsashe suka
tabbatarda cewa babu attajiri kamarsa a duniya ,saboda
tarin dukiyar da Allah yabashi wannan sarki yana da
matan aure guda goma sha shida kuma yana da kuyangai
tamanin gabaday wayannan mata nasa babu wadda ta
raba haihuwa sai guda daya ,
Wata mace da ake kira hauziya
Duk acikin matan abul dinar hauziyace yar talakawa
,domin duk sauran daga yayan sarakuna sai yayan mayan
attajirai na duniya
.
A ranar da aka fuskanci hauziya ta sami ciki ,sai sauran
kishiyoyinta suka cika da bakin ciki .
Batare da da bata lokaci ba suka shiga bin hanyoyin da
zasu tabbatar da cewa cikin ya zube ,masu tsafi nayi
,masu surkulle nayi, kai wasu ma kiri kiri a fili sukka ringa
yin abubuwan da zasu sa cikin ya zube amma ubangijin
musulunci shine mai yin yadda yaso ,sai ya kare hauziya
daga sharrin kishiyoyinta .
Shikuwa sarki abul dinar koda yaji cewar hauziya ta sami
ciki , sai yadauki son duniya ya kwallafa a akanta . Domin
zata share masa hawaye a bisa bakin cikin daya addabi
rayuwarsa ta duniya ,wato rashin magaji ,
Dayake ya tabbatar da cewa sauran kishiyoyinta bazasu
kyaleta ba, sai ya dauketa ya kaita wani gidansa dake
bayan gari .
Ya ajiyeta ita kadai ,
Daga ita sai bayi masu yi mata hidima .
Gidan ya zama ba'ashiga da fita ,in ba shi kansa ba .sarki
abul dinar ya tare wajen hauziya , tare suke ta rainon
cikin har wata takwas .
A ranar da cikin ya cika wata takwas da kwana shirin da
biyar .
Ciwon nakuda ya kama hauziya .
Cikin yan dakiku kadan ta haifi sankaceciyar 'ya,
Wadda atun tana jinjiniyar aka tsorata daganin kyawunta.
.
Sannu sannu akayi ta rainon yarinyar wadda aka sawa
suna Mabaruka ,har ta girma .
Ta zama cikakkiyar budurwa ,
Wadda saboda tsananin kyau labarinta ya cika duniya .
Jarumai da matsafa da dama sun hallaka junansu a kan
soyayyarta
.
.
Wata rana gimbiya Mubaruka ta fita rangadi , don
shakatawa cikin wata babbar gona ta mahaifinta ,kuyangi
da barade na take mata baya.
.
Kwatsam sai ga wata katuwar macijiya mai girman gaske ,
ta bayyana a gabansu .
.
Koda ganinta sai barade da kuyangi suka kwalla ihu, suka
ruga baya da gudu ,
.
Baraden nan suka yi ta rige rigen gudu ,sun mance da
aikinsu na tsare lafiyar 'yar sarki .
Ita kuwa mabaruka sai ta tsaya kyam ta kasa gudu , don
tsananin razana , hawayen bankwana da duniya suka
tsiyayo daga idanuwanta .
.
Katuwar macijiyar ta wangame baki zata hadiyeta , kawai
sai mabaruka taga wani bakin bawa yai tsalle ya rungumi
wuyan macijiyar
.
Nan fa suka kama kokawa shi da macijiyar su fadi can su
tashi can.(Ni kaina shuraih sai dana kusan....basai na
karisa ba)
.
Shi yana kokarin ya turmusheta ya rarumi wani icce dake
waje guda ya soketa ita kuma tana kokarin
kannannadeshi ta karairaya kasusuwan jikinsa . Haka dai
suka yi ta dauki ba dadi har tsawon rabin sa'a , macijiyar
nan tai masa fata-fata , duk jikinsa ya rune da jinin
raunuka
Amma hakan bata sa ya saketa ba ,
A hakan dai Allah ya bashi iko , hannunsa ya kai kan
wannan icen cikin zafin nama ya dauki icen ya caka
abakin macijiyar , ya bullo ta tsakiyar kanta .
.
Nan take macijiyar ta sulale ta fadi kasa matacciya,
Shi kuma bawan yafadi kasa a sume .
.
Koda ganin haka sai gimbiya mabaruka ta ruga gareshi ta
rungumeshi tana kuka ,
Gaba daya jikinta ya baci da jininsa .
Ahaka sarki abul dinar da dakarunsa suka zo suka sameta
.
.
Nan da nan aka ban bareta daga jikin bakin bawan , aka
tafi da ita shi kuma aka yayyafa masa ruwa ya farfado
daya ke shi bawa ne marar gata ,
Sai aka tuhumeshi da laifin rungumar 'yar sarki ,
Ba'ama duba sai da ran dayayi ba, dan ceton 'yar sarkin.
.
Saboda haka aka kaishi dakin tuhuma ,aka dauddaureshi
da sarkoki aka yita gana masa azaba iri iri.
.
A iya tunanin Mabaruka wannan bawa ya mutu wannan
dalili shi yasa tai ta kuka har hankalinta ya gushe ta suma
bayan ta farfado ta mike zaune daga kan gadon data ke
kwance ,
Inda tai arba da mahaifiyarta hauziya zaune a gefen
gadon idanunta cike da hwaye .
Koda ganin mikewar mabaruka sai farin ciki ya kama
hauziya.
.
"Mama ina gawar bawan daya ceci rayuwata?"
Mabaruka ta tambaya fuskarta cike da alamun bege
.
"Waya ce miki ya mutu? Ai dogon suma yayi kum, kuma
anzuba masa ruwa ya farfado ,yanzu haka yana can
daure a dakin tuhuma"
.
"Me yayi za'a kaishi dakin tuhuma?"
.
Batare da mabaruka ta saurari karin bayani ba ta mike
tayi waje da gudu ,
Mahaifiyarta tana kira amma taki dawowa , bata tsaya
ako ina ba sai a kofar dakin tuhuma,
Da zuwa ta dakawa masu gadin tsawa tace "su bude mata
kofa kofar "
.
Jikinsu na rawa suka bude kofar ta shiga , inda ta iske shi
kwance magashiyyan cikin jini .
Nan take tasa aka kwance sarkar dake jikinsa , tasa aka
kaisa gidanta inda taimasa wanka ta sama magani a
raunukan jikinsa sannan tasa aka kawo masa abincin
sarauta , ya cika tumbinsa ! Daga nan aka kaishi wani
dakin hutu ya kwanta yai barci, har sai da rana ta fadi
sannan ta shiga dakin ta tashe shi , duk su biyun suka
kurawa juna ido
.
"Yakai wannan jarumi menene sunanka"
.
Bawa yayi murmushi yace "ni sunana Ashwar "
.
"Ya akai kana matsayin bawa a gidanmu na sarauta
amma ban taba ganin kaba ?"
.
Ashwar yasake yin murmushi yace "yake gimbiya kisani
babu yadda za'a yi ki taba ganina , domin tun da aka
haifeni ban taba fitowa ba daga cikin lambun sarki na can
bayan gari sai ayau .
Mahaifina shine bawan dake kula da wancan lambu na
sarki , tun yana saurayi yake wannan bauta harya tsufa ya
mutu , nikuma na gajeshi
Mahaifiyata ma acikin wannan lambu ta rasu yanzu haka
kabarinta na cikin lambun
A yaune sarki ya aika mini naje daya lambun nasa nayi
aiki wanda shine kika ziyarta don rangadi
To ina cikin aikine na hango shigowarku keda kuyangi da
barade .
Kuma sai naga wannan katuwar micijiya ta tarwatsa
kuyanginki da baraden
Duk sun gudu sun barki shi yasa na sai da raina don ceto
rayuwarki".(Ni 99% nace lallai kacika sadauki)
.
.
Koda jin haka mabaruka tai ajiyar zuciya hawayen tausayi
kauna suka zubo mata tace "ya kai Ashwar kasani daga
yau bawani namiji da zan aura in ba kaiba
.
Cikin razana Ashwar yaja da baya ya takure jikinsa ga
bango yace" ranki ya dade ki rufa min asiri , ki tuna fa ni
bawane , bawan ma bakin fata ,ke kuwa gaki balarabiya
'yar sarki,ina ni ina aurenki"
.$
Mabaruka tayi murmushi tace "ai babu ruwan so da
matsayin jinsi ko launi ,idan duk duniya zata taru banga
wanda ya isa ya raba ni dakai ba , abu daya nake so na ji
daga bakinka kawai , kana sona ko baka sona?"
.
"Haba gimbiya ai babu wani namiji da zai ganki yace baya
so , amma ai wutsiyar rakumi tai nesa da kasa kuma
BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE"
.
"Kwarai kuwa"wata murya ta amsa daga bayan su.
.
Mabaruka da ashwar suka dubi bakin kofa a tsorace ,
sukayi arba da sarki Abul dinar fuskarsa a murtuke wasu
kartin barade shida na tsatsaye a bayansa suna muzurai
tamakar saci babu.
.
Cikin fushi ya dubi mabaruka yace "haba gimbiya shin kin
mance da martabar gidannanne ?kin manta da
matsayinki na 'yar sarki ne?har zaki wulakanta kanki ki
dauko bakin bawa ki shigo dashi har cikin gidanki mai
Albarka.
.
Maimakon mabaruka ta nutsu kota firgita da wannan
tambaya sai ta kyalkyale da dariya sannan tace "haba
Abba ka runa fa mahaifiyata ta fito daga dangin talakawa
,me yasa ka aurota har kuka haifeni? Shin baka
tsammanin zubar martabar sarautarka ne? Hakika sone
yasa idanunka suka rufe , tunaninka ya gushe ka manta
da matsayinta......"
.
Cikin hanzari abul dinar ya tari numfashin mabaruka
yace" yata kada ki yi la'akari da wannan , domin inki kai
tunani akwai alaka ta jinsi da jini tsakanina da
mahaifiyarki amma tsakaninki da wannan bakin bawan
babu alakar komai"
.
"Abba ni dai Ashwar nakeso"
(Shuraih 99% ke magana)
.
Wannan bayani ba karamin girgiza Abul dinar yayi ba ,
don tsabar takaici sai da yaji kwalla ta zo masa amma sai
ya juya baya yayi shiru yana tunani , daga can ya juyo ya
dubi mabaruka yace" na amince da niyyarki amma bisa
sharadi "
.
Cikin mamaki mabaruka tace "wane irin sharadi ne?"
.
"Zakiji sharadin gobe da a fada gaban dukkanin jama'a.
.
Nan take sarki ya juya ya fice daga dakin ,barade suka
take masa baya.
.
Ashwar da mabaruka suka dubi juna cikin tsananin
damuwa
.
"Ai daman na san wannan al'amari bazai taba yiwuba ,
nagaya miki cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE"
.
Mabaruka tayi murmushi tace "ashwar ina so ka kalli
cikin kwayar idanuna kaga ya mini abinda ka gani aciki "
.
Ashwar ya kura mata ido har tsawon 'yan dakiku kadan
sannan ya kawar da kai
"Me kagani acikin idanuna?"
"Banga komai ba face digon baki da zagayen fari"
.
"To wannan zagayen farin daka gani ba komai bane face
fadar zuciyata , wannan digon bakin kuwa daka gani guda
daya tilo ba komai bane face kai Ashwar Kai kadai nake so
bazan so wani ba yan kai ,idan kuwa aka aura mini wani
ba kai ba saidai ya zauna da gawata"
.
Haka dai Ashwar da mabaruka sukaci gaba mahawara
yana ta kokarin nuna mata matsala har zuwa gabannin
magariba ,sannan ya tafi gidan gona ita kuma taci gaba
da tunanin hanyar dazata bi ta shawo kan al'amarin .
Wannan shine abin daya faru tsakanin jarumi ashwar da
gimbiya mabaruka .
.
Shuraih ke magana
.
Al'amarin sarki abul dinar kuwa lokacin daya bar gidan
'yarsa mabaruka sai hankalinsa ya dada dugunzuma ya
rasa abinda yake masa dadi aduniya , har ya isa turakarsa
yana cikin wannan hali , ya kasa zauni ko tsaye sai da
dukkanin barorinsa da fadawansa suka fahinci lallai akwai
abin da yake damunsa .
Bayan yayi dogon tunani sai ya tura aka kirawo masa yan
majalisarsa cikin turakarsa daga cikin yan majalisarsa
sarki Abul dinar akwai waziri, galadima ,wambai da
Gulmanu sarkin matsafa na garin.
.
Bayan dukkaninsu sun zauna , sai sarki Abul dinar ya basu
labarin abinda ke faruwa tsakanin 'yarsa mabaruka da
kuma jarumi Ashwar, sannan yace
"Kunsani cewa abin kunya ne ace 'yarmu ta auri bakin
bawa ,tabbas idan akai martabar masarautarmu ta zube ,
sauran kasashe ma dake makwataka damu sai sunzage
mu sun raina mu ku sani idan muka sanar da mabaruja
kuru-kuru cewa ba zamu amince ta auri ashwar ba ,
tabbas zata iya hallaka kanta, nidai nace da ita zan bata
shi amma bisa sharadi ,sharadin kuma nace sai gobe da
safe zan tara jama'ar gari na fadi a gabansu .
.
Toh ku sani sharadin nan fa ni kaina ban san shi ba ,
wannan shine dalilin dayasa na tara ku anan, inaso muyi
tunani mai zurfi mu kafawa ashwar sharadin nemo wani
abu mai tsananin wuyar samu a duniyar nan, wanda a
sakamakon neman sa ma zai hallaka in yaso kun ga dole
mabaruka ta rungumi kaddara"
.
Yayin da 'yan majalisa suka ji wannan bayani na sarki
abul dinar sai duk suakayi shiru suka shiga tunani aka
rasa wanda zaice kala , har ya zuwa wani lokaci daga can
sai gulmanu sarkin matsafa ya mike yace
.
"Ya sarkin sarajkai hakika ni ina da mafita akan wannan
al'amari kuma na rantse da wata sharadin da zan dora
Ashwar akai bai is ya haye shi ba ina so ku yi hakurin jin
wannan sharadi har zuwa gobe da safe "
.
Koda abul dinar yaji wannan batu sai fuskarsa ta fadada
da murmushi yace na yarda dakai sarkin matsafan
duniya gulmanu , shikenan na sallameku, kowa ya tafi
gida sai gobe da safe mu hadu a kofar fada
.
Nan take 'yan majalisa suka watse batare da wani daga
cikinsu yace kala ba aka bar sarki acikin dumbin farinciki
.
Birnin sarwaliya babbar garine mai tsohon tarihi ,wanda
a halinm yanzu sarki abul dinar yake sarauta a cikinsa
gaba daya al'ummar farin ma'abota Addinin bautar wata
ne , duk sa'adda wata ya cikja kwana goma sha biyu gaba
dayansu maza da mata yara da manya sukan fito tsakar
dare , suyi sujjada ga watan suna masu fadin bukatunsu
da rokon gafarar kurakuransu, wannan abu ne wanda ya
yi matukar tasiri zukatunsu
.
Bayan sarki yagama shawara da yan majalisarsa sai yasa
akayita shela da yekuwa aka sanar da jama'ar gari cewar
gobe da safe ana gaiyatar kowa a fada ba ayafewa ko da
yara ba . Masu shela basu daina sanarwa ba har sai da
dare yayi , sannan suka je suka kwanta.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kashe gari jama'a sukayi ta tururuwa suna zuwa fada
kungiya kungiya ,ayari ayari ,har daga kauyuka,kai wasu
ma saga makotan kasashe sai da suka zo don son ganin
kwakwaf,saboda labari ya bazu cewa akan maganar 'yar
sarki ne da bakin bawan data nace tanaso.
A cikin wadanda suka halicci wannan taron akwai wasu
jarumai kimanin su shida masoya mabaruka , wadanda
suma ashirye suke dasu salwantar da rayuwars son ganin
sun sami aurenta.
.
Bayan sarki abul dinar da'yan majalisarsa sun hallara , sai
aka tura wani bafade yaje yakira ashwar daga gidan gona
. A sannan ne gimbiya mabaruka ta iso tare da kuyanginta
da baradenta , nan take taje ta zauna bisa kujerar dake
daf da karagar sarki ,
Sarki ya dubeta yai murmushi .
Hakan keda wuya kuma sai ga ashwar tare da da bafajen
da aka aika ya kirawo shi sun iso, da zuwa aswar ya fito
tsakiyar filin fada , ya fadi yayi gaisuwa ga sarki , bayan an
amsa gaisuwar ne aka yi masa izinin mikewa tsaye , yana
mikewa ne yayi ido biyu da abar begensa tana mai yi
masa wani irni murmushi mai tona asirin zuciya .
Cikin karfin hali ashwar ya yiwa mabaruka murmushi ,
sannan ya kau da kai ga barin kallonta don tsoron kada
tsananin kyawunta ya rinjayi zuciyarsa ya kamu da sonta
.
Tun daga ranar da ashwar ya fahimci cewa gimbiya
mabaruka na sonsa , tsoro da damuwa suka cika
zuciyarsa .
Badon komai ba sai don ya tabbatar mahaifinta ba zai
maraba dashi ba , wannan dalili yasa ya danne sha'awar
bege da so a zuciyarshi ,har a halin yanzu ashwar bai
yadda son mabaruka ya shige shi ba , kai in ba don ma
bin umarnin sarki ba da tabbas ba zaizo wannan kira da
akayi masa ba.
.
.
A cikin wannan gona ta sarki wadda ashwar ki aiki , akwai
wani dattijo abokin aikinsa wanda ake kira makabul.
Makabul tsohone sosai , domin shekarunsa sun kai
kimanin tamanin da doriya . Makabul aminin baban
ashwar ne , don asali ma tare aka siyo su a matsayin bayi
daga nahiyar kasar bakaken fata,
Tun suna samari yan shekara sha tara.
Tun ashwar na yaro karami ya taso yake ganin abotar da
ke tsakanin mahaifinsa da makabul, don haka bayan
rasuwar mahaifinsa sai ya rike makabul tamkar
mahaifinsa komai zaiyi sai ya shawarce shi . Yanzu
hakama makabul dinne yabashi shawarar yazo fada don
amsa kiran sarki kuma yace dashi kome aka bukaci da
yayi akan mabaruka kada yaji tsoron komai ya amsa
cewar zaiyi, komai wahalar al'amarin. Koda ashwar ya
tambayi makabul dalilin da yasa yace ya sai da ransa.
.
Sai yace dashi" tun mahaifinka nada rai mun taba zuwa
wajen wani boka wanda yayi bincike akan ka , bokan ya
sanar damu cewa zaka shahara a duniya , kuma zaka auri
'yar sarki, amma sai ka karbi Addinin musulunci
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yayi shiru yana tunani
daga can yace" kai baba makabul yanzu a ina zan sami
ma'abocin wannnan addinin daka fadi? Kasani cewa babu
masanan sa anan garin dakuma kasa shen kewayenmu"
.
Makabul yayi murmushi yace "kada ka damu akwai tafiya
da zakayi tabbas zaka hadu da ma'abota Addinin
musulunci,da zarar kun hadu ka karbi Addinin, in da
rabon mu ma zaka dawo gida ka sanar damu wannan
Addini mu karbe shi, don tabbas shine Addinin gaskiya ,
amma kiri kiri sarakunanmu sun ki shi don kwadayin
duniya , da son mulkinsu na kama karya "
.
,
Duk wannan...


Read / Download BABBAN GORO Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album