Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

SAIFUL MAUT Complete Hausa Novel Document by SAIFUL MAUT


SAIFUL MAUT

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 4083



SAIFUL MAUT

Reading Time: 0 Hours

Added On: 20, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 21.91 kb

File Type: txt

Views: 1848+

Download: 360+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN
GASKIYA: Part 1:
A wani zamani ne wanda ya shude a cikin birnin
kisra an yi wani azzalumin sarki mai suna Jawat
ibn Kafir shi dai wannan sarki Allah ya bashi
karfin damtse da karfin tsafi da mayaka na ban
tsoro dan kuwa kumin girman gari idan ya tura
mayakan sa to fa yan garin sun shiga balai da
kuma son mata ko yar wacece in dai ya hada ido
da ita to fa sai ya hada kwanciya da ita a haka
sai da ya tara mata wajen tamanin da biyar
kuma duk basu taba haihuwa ba saboda kafin ya
kwanta da mece sai yayi anfani da tsafin sa yayi
toshe mahaifarta toh a kusada garin akwai wani
karamin kauye mai suna Birnin Islama toh yan
garin kuwa musulmai ne fatake ne masu tafiye
tafiye toh su kuwa suna tafiyane da aladar
Musulunci suna da wani adalin sarki mai suna
Maut ibn Salim shi dai sarki salim Allah yayi
masa albarka da yaya biyu mace da namiji, masu
harshashe kuwa sun ce a wannan zamani ba
wanda yakai su kyau ballatana ita macen mai
suna Lasmina, shi kuwa namijin Allah ya bashi
jarumtaka da sa a don kuwa ba abin da yasa a
gaba idan yace sai yayi to kuwa ba wanda ya isa
ya tsai dashi don kuwa tun yana yaro yake yin
abubuwan alajabi don da akwai lokacin da ya tafi
dajin da akeyiwa lakabi da kauful jat a tarihin
dajin nan ba wanda yake shiga dajin nan ya fito
lafiya amma shi kadai ya shiga da zuwa kuwa sai
ya fara ganin abubuwan ban tsoro amma ko
gezau baiyi ba ya cikin dajin wajen dakika ashirin
sannan yaga wani babban zaki ya durfafo
wajensa maimakon ya gudu amma sai ya fara
shirin fada shi kanshi zakin yasan cewa ya gamu
da gomonsa ai kuwa sai zakin ya tahu a guje
kamar mayun waci yana zuwa kusa da shi sai ya
daka tsalle shi ko Saiful maut bai ko matsa ba
zakin na zuwa suka fara kokawa da yakushi har
wajen dakika talatin sai gashi saiful maut ya
kashe zakin da karfin damtse kawai sannan yakai
cikin gari totun daga ranar mutane suka fara
jinjina masa
zamu cigaba idan munga likes da comments
dinku to muna jira SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN
GASKIYA PART: TWO
A kasar sarki Jawat kuwa yana zaune a dakin
tsafinsa a gaban madubin tsafinsa inda yake
binciko kyawawon mata na duniya wanda zai tura
mayakansa su dauko ta koda da karfin yaki ne ko
tsafi yana nan dai a zaune akan wani turmin
tsagi
wanda aka rufe da wani jan yadi a tarihi ance ba
wanda y taba shiga cikin dakin tsafin ya fito da
rai
saboda irin hatsatsubin da suke cikin sa shi ko
sarki jawat yana ta kallon hotunan yan matan
kawai sai ya hango wani hoton wata kyakkyawar
mace wanda tunda yake duniya bai taba ganin
kyakkyawa kamar ta ba sai yayi binciken wacece
budurwar da kuma garin da take ai kuwa yana
dubawa yaga ai yar sarkin garin Islama ne kawai
sai ya fara dariyar mugunta dan kuwa shaawarta
yake tun bai ganta ba kawai sai ya tura wani
aljanun sa ya kira wazirinsa mai suna kafaru a
lokacin da wazirin yazo sai ya rusuna ya kwashi
gaisuwa yace a mai duniya naga ka turo a kira ni
lafiya kuwa sai sarki ya numfasa yanuna masa
hoto gimbiya Lasmina aikuwa da waziri yaga hoto
gimbiya lasmina sai da ya kusa zautuwa amma
sai
kawai ya share yace ya mai duniya yanzu kana
son inje garin Islam in tambayo ma hannun
gimbiya lasmina ka aure ta sai kuwa sarki jawat
ya dinka dariya kamar bazai daina ba amma sai
kawai ya tsuke baki yace ina son yanzu ka dauki
dukiya mai yawa ka kai wa sarki maut kuma ka
gabatar da bukata ta agareshi waziri yace
angama
ya mai duniya sannan ya tashi ya tafi baitul mali
don a hada dukiyar da sarki yace.
Acan garin islama kuwa ana ta fadanci sai kawai
aka ga su waziri kafaru sun shigo da kayyayaki
akan rakuma sai suka shigo cikin fada zasu
rusuna
amma sai sarki maut ya dakatar dasu yace ai ba
wanda ake rusunawa sai Allahu wanda ya halicci
sammai da kassai shi kuwa waziri ko damuwa
baiyi ba sai yace yakai sarki maut kasani cewa
sarkin mune ya aiko mu dan mu fada maka cewa
yana son yarka gimbiya lasmina da aure tun kafin
ya gama maganarsa Sadauki Saiful ya tari
numfashi sa yace ai bazai taba yiyuwa ba dan
ruwa da wuta basa zama waje daya ku fada wa
sarkin ku haka mu bamu da lokaci da zamu bata
akan ku dan zamu je mu bautawa ubangijin mune
idan kun gadama ku tafi idan kuma kun gadama
ku
tsaya sai sarki maut yace ga sakona ga sarkin ku
kuce masa bazai yu ba GASKIYA PART: 3
Alokacin da waziri kafaru yaga irin wulakancin da
sarki maut yayi musu shi da dansa sai ya ji wani
mugun haushi sannan ya cewa dakarun da yazo
dasu cewa su tafi a lokacin da ya isa birnin kisra
sai ya huce fada wajen sarki domin ya isar da
sakon da ya karbo daga garin islama alokacin da
ya isa wajen sarki sai ya kwashi gaisuwa yace
ya mai duniya ai tun danake a duniyar nan
bantaba ganin wulakanci irin wannan ba sai ya
kwashi labarin abunda yafaru ya fada ma sarki,
kawai sai sarki ya takarkare ya ringa dariyu
wanda ya bawa waziri matukar mamaki sai kuwa
ya tsuke baki yace yanzu anan duniyar da akwai
garin da zan tura ince ina son abu amma
maimakon abani sai a wulakanta ni toh kuwa
garin islama sun shiga bala in da basu taba koda
tunanin sa ba yakai waziri yanzu ka tura a kira
min sarkin yaki don a gobe nake son in gama da
garin islama alokacin da sarkin yaki yazo sai ya
kwashi gaisuwa sarki jawat yace ina son ka tara
min dakaru kamar dubu daya gobe da safe don
ina son kashe duk wani abu mai rai kuma in baje
garin islama sai sarkin yaki yace angama ya mai
duniya sannan ya tafi ya bar sarki da waziri suka
cigaba da tattauna yanda zasu bullo wa alamarin
gobe.
Da gari ya waye sai ga dakaru nan a cikin sulken
yaki na ban tsoro don idan ka dansu kuwa to
dole ne kasan cewa wannan su ake kira da bala i
sai ga sarki nan ya fito daga cikin fadarsa da
shigar yaki wanda baitaba yi ba kai idan wani
raggon yaga wannan shiga ta sarki jawat to
gaskiya zai iya mutuwa yana zaune ne akan
tabarmar tsafi wanda yake yawo akan iska yace
yaku dakarun masifa da bala i to yau ina son ku
sani cewa wannan yakin ba zamu tausayawa
kowa ba kisa ne kawai amma ina son akama mun
gimbiya lasmina a raye don itace makasudin
wannan yaki sai dakarun su kace an gama ya
mai duniya sannan suka fuskanci kofar fita daga
birnin suka nausa hanyar birnin islama.
Acan birnin islama kuwa sadauki saiful da ya
dawo daga masallaci sai ya tafi turakar
mahaifansa yayi gaishe dasu sannan yace wa
abbansa wato sarki maut cewa shi zai tafi
farauta suka sa masa albarka da kuma adduar sa
a sannan ya tafi dakin kanwarsa wato gimbiya
lasmina suka gaisa take cewa ya samo mata
inibi nunanne yace toh sannan yafi to cikin
bargar dawakin ya hau dokinsa sannan ya nausa
cikin daji abinda bai sani ba kuwa shine bazai
kara ganin garin ba alamarin su sarki jawat kuwa
sai gudu suke har dai suka karasa garin wajen
sallar azahar suna zuwa suka afka su fara # sara
da # suka suna kona gidaje suka kashe kuwa
abirnin har cikin fadar sarki maut suka shiga
suka kama shi da matar sa da gimbiya anan take
sarki ya fille kan sarki maut sannan ya fille na
mahaifiyar su sadauki saiful aka saka gimbiya
akan doki sannan suka tafi suka bar birnin wanda
aka baje shi.
Shi kuwa saduaki saiful yana ta farauta har ya
fara shirya taho wa gida sannan yatuna da inibin
da kanwarsa wato gimbiya tace ya samo mata
yana tafiyane ya hango bishiyar aiko bai bata
lokaci ba ya tsinko mai yawa ya taho dashi gida
tundaga nesa ya fara hango wani irin hayaki ya
turnike a sararin samaniya sai ya kara gudun
dokinsa domin yaga mai ya faru.
zamu cigaba SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN
GASKIYA PART: FOUR
Alokacin da sadauki saiful ya iso cikin garin su
yaga irin barnar da aka musu da kisa sai kawai
ya nufi fadar abban sa ai kuwa yana zuwa yaga
gawarwaki a ko ina burjuk yana shiga kawai sai
ya yi arba da gawar mahaifinsa da na
mahaifiyarsa amma kuma babu kawuna atare da
gangar jikin su kawai sai ya tsuguna ya fara
zubar da wasu zafafan hawaye wanda tun
lokacin da aka haife shi bai taba zubarda hawaye
ba sai yau sai ya nemu ruwa mai tsarki yayi
musu wanka yanda musulunci ya koyar damu ya
sallace su sannan ya binne su yana mai yin kuka
da bakin cikin abubuwan da suka faru alokacin
da bayanan ya dau lokuta kamar sa a daya
asannan ne kanwarsa ta fado mai a rai yayi ta
duba wa bai ganta ba yana cikin duba wa sai
yaga wani farin haske wanda tun da aka haife
shi baitaba ganin haske kamar sa ba hasken ya
tunkare shi kamar zai bankade shi sai ya sare
takobinsa daga cikin gidan ta yana dube duben
ta inda abin zai kawo masa farmaki amma
maimakon a kawo masa hari sai yaji wani murya
mai zaki tayi masa salama ya amsa...


Read / Download SAIFUL MAUT

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album