Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

MAKASHIN MAZA Book 1 Complete Hausa Novel Document by MAKASHIN MAZA Book 1


MAKASHIN MAZA Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 5502



MAKASHIN MAZA Book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 28, Jun 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 29.64 kb

File Type: txt

Views: 807+

Download: 326+

Last download: 1 day ago

Description/Story: MAKASHIN MAZA
Rubuta Labari
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
08137237071




Bayan shekaru dari takwas, zamani mai tsawo ya shude, an yi wani mashahurin sarki mai suna Lamisu a cikin birnin Ban nur. Wannan sarki ya kasance mai tarin dukiya, kuma ma'abocin son jin dadın duniya ne. A bisa wannan dalili yasa aka tara masa dukkanin magina na kasar, yace dasa yana so a gina masa kasaitacciyar fada wadda babu kamarta a duniya.


Ko da jin wannan batu sai sarkin magina ya mike yace "Ya sarkin duniya hakika ka zo mana da babban al'amari, don haka muna bukatar ka ba mu kwana bakwai mu je mu yi tunani"


Sarki Larmisu yayi murmushi yace "Na amince, kuma ina tabbatar muku da cewa komai yawan dukiyar da za'a kashe a kan wannan gini zan bayar"


Daga nan ya sallame su suka tafi.


Bayan kwana bakwai sarkin magina ya dawo yace da sarki sun gama shiri, nan take sarki ya bayar da duk abubuwan da ake bukata aka fara aiki.


Ana cikin yin haka sai aka tono wani irin ruwa a cikin karkashin kasa, wanda yai matukar tsorata wadannan magina. Shi dai ruwan mai kauri ne, kuma wani abu na motsi a cikinsa. Maginan suka yi iya kokarinsu akan su kwashe wannan ruwa amma sai abu
ya gagara, saboda tsananin santsinsa. Cikin tsananin razana maginan suka ruga izuwa fada suka sanar da sarki halin da ake ciki. Ko da jin haka, sai sarki Larmisu tare da bokansa Arjalu suka rugo izuwa wannan wuri. Da zuwa suka iske wannan ruwa, Boka Arjalu ya fiddo wata battar tsafi yayi wani tsafi, take wannan battar ta zude wannan ruwan gaba dayansa.


Arjalu ya dubi sarki Larmisu yace "Ya sarkin duniya, hakika akwai bayani mai hadari dangane da wannan ruwan, akwai bukatar bincike, zai fi kyau ka bini zuwa dakin tsafina"


Ba tare da wata gardama ba sarki Larmisu ya amince da shawarar boka Arjalu, suka tafi izuwa dakin tsafin su biyu kawai.


Daki ne wanda aka gina shi da duwatsun wuta, babu komai a ciki face tarkacen kayan tsafe-tsafe kamar kahunhuna, gashin dabbobi iri-iri, da kwalabe masu dauke da ruwa mai launuka da yawa. Da shigarsu cikin dakin sai boka Arjalu yai nuni ga wata kujerar karfe ga sarki Larmisu yace ya zauna.


Larmisu ya zauna, shi kuma sai ya fiddo battar nan wadda ya zuke ruwannan a ciki, wato ruwan da aka hako a wajen gini. Take boka Arjalu ya dora battar bisa wani farin gilashi ya fara surutai na tsafi tare da rufe ido. Jim kadan da faruwar haka, zufa ta lullube Arjalu, jikinsa ya kama karkarwa, al'amarin ya da ya firgita


sarki Larmisu, daga can kuma sai ya ga wani farin hayaki ya bulbulo ta cikin kunnuwan boka Arjalu.


Boka Arjalu ya kwalla ihu mai karfi tare da mikewa tsaye zumbur, sai da yayi dogon ajiyar numfashi gami da atishawa, sannan ya dubi sarki Larmisu yace "Ya sarkin duniya, hakika wannan ruwan ba ruwa ba ne mutum ne"


Cikin tsananin mamaki sarki Larmisu ya mike tsaye yace "Ban gane ba, me kake nufi?"


"Wannan ruwa, ruwa ne na masifa, ruwa ne na bala'i, hakika maginanka sun tono babbar jaraba ga dukkanin mutanen duniya. Wannan wani tsohon azzulumin matsafin sarki ne wanda ya gallabi mutanen duniya a zamaninsa, sunansa Marganu dan Jandanu jikan Gundukurki, ina tabbatar maka da cewa idan ya tashi kowa ya shiga uku. Ba zan iya ci gaba da tsare shi ba a cikin battar nan fiye da kwana arba'in, ka sani idan ya tashi karagarka tafi karfinka, ba kai ba ma gaba daya sarakan duniya da matsafan duniya mun shiga cikin mummunan bala'i"


Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki Larmisu ya kara dugunzuma, ya fara kai komo a cikin dakin tsafin, ya kasa tsaye ko zaune, sai ya kai gwauro ya kai mari. Daga can ya tsaya ya dubi boka Arjalu suka fuskanci juna sosai yace "Kai boka Arjalu! Ka tuna kai matsafi ne dan matsafa kuma jikan matsafa, maza ka






shiga aikinka! Ka bincika ko akwai hanyar da za mu bi mu samawa kanmu sauki, mu ceto rayuwarmu da ta sauran jama'ar duniya"


Yayın da boka Arjalu ya ji haka sai ya tuntsure da mahaukaciyar dariya har sau uku, sannan ya shafi gemunsa yace "Ya sarkin duniya, hakika ka zuga ni kuma na ji dadi, saboda haka zan yi aikina, na rantse da darajar tsafi sai na samo mana mafita, amma ina so ka ba ni tsawon kwana biyu"


Yayin da sarki Larmisu ya ji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya, sannan yace "To shikenan na amince zan kasance mai sauraronka"


Daga nan suka yi sallama sarki ya tafi.


Sarki Larmisu shi ne sarki na dari hudu da ashirin a jerin sarakan da suka mulki kasar Ban nur, tun daga zamanin sarki Hafis mahaifin Badiya, macen da ta daukaka a duniya akan baiwar fassara mafarki, kuma ita ce wadda ta bar babban abin tarihi a masarautar Ban nur wanda har yau yana nan a rubuce cikin kundin tarihin sarautar garin, a cikin wani daki na musamman a gidan sarautar.


A halin yanzu sarki Larmisu na da mata goma sha bakwai, kuma yana da 'ya'ya kimanin arba'in a da doriya. Shi dai wannan sarki ya mallaki dukiya mar tsananin yawan da shi kansa bai san iya adadinta be. Larmisu mutum ne shagalalle, babu abin da yake tsore


face mutuwa ko rabuwa da mulki, wannan dalili yasa hankalınsa yayi matukar tashi da ya ji cewa Marganu dan Jandanu zai dawo ya raba shi da karagarsa. Lokacin da Sarki Larmisu ya baro wajen boka Arjalu, sai ya dawo gida cikin matukar damuwa. Ko da yai arba da amaryarsa gimbiya Lamsiya, sai ta fuskanci hakika yana cikin damuwa.


Lamsiya ta tarye shi da sauri inda ta rungume shi, sannan ta zaunar da shi bisa wata kujera ta alfarma suka fuskanci juna sosai tace "Ya sarkin sarakai, me ne ne ya tayar maka da hankali na ganka a cikin damuwa?"


Larmisu yai gyaran murya yace "Ya ke sarauniyar taurari, kin sani cewa duk irin bacin ran da na shiga da zarar na yi ido biyu da kyakkyawar fuskar nan ta ki sai na ji zuciyata tai sanyi, amma kin ga yau an sami sabanin haka, tabbas ina cikin mummunan tashin hankali"


Nan take va kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da boka Arjału ya zayyana mata. Ko da jin wannan batu sai Lamsiya ta tuntsure da dariya, cikin matukar mamaki sarki Larmisu ya janye jikinsa daga nata yace "Me ne ne ya baki dariya?"


Lamsiya ta mike tsaye ta yi 'yar tafiya taku uku, sannan ta waigo ta dube shi tana mai murmushi tace "Yanzu kai akan wannan ne ka tayar da hankalinka? To tsaya ka ji, ni bana tsoron abin da zai zo muddin na san


da zuwansa, wanda ban san da zuwansa ba shi ke ba ni tsoro. Ka je ka saurari bokanka nan da kwana biyun idan har baka sami nutsuwa da mafita ba ka zo gare ni. ni zan baka mafita."


Ko da sarki Larmisu ya ji wannan batu sai yai shiru ya kura mata ido ya kasa cewa komai, ba dan komai ba sai don ya san cewa tana da babban abin dogaro. Mahaifin Lamsiya wani kasurgumin matsafi ne wanda ya shahara a duniya, domin a wannan zamanin ana kyautata zaton babu matsafi kamarsa a duk duniya. Shi ne matsafin da ya mayar da mutanen wani babban gari birai gaba dayansu, yau shekara ashirin kenan da faruwar al'amarin, har yau mutanen na nan a matsayin birurruka an rasa wanda zai warkar da su, har ma sun hakura sun rungumi kaddarar karasa rayuwarsu ta duniya haka, sunan wannan gari na birai Maduwal, shi kuma matsafin da ya mai da su biran wato mahaifin Lamsiya sunansa boka Zafaratu, a yanzu haka idan mutum ya je birnin Maduwal zai iske su a cikin rayuwa irinta bil'adama babu abin da ya sauya na daga al'adu da harkokin yau da kullum, matsala daya kawai basa magana kamar yadda sauran bil'adama ke yi, idan fatake suka shiga garin sai dai su yi harkar kasuwanci cikin bebanci.


***


aderbege


*shirya


Bayan kwana biyu sun cika sai sarki Larmisu ya koma gidan boka Arjalu yace da shi "Ya kai boka Arjalu, ka sani cewa yau ne ranar cikar alkawarinmu, dan haka na zo na ji daga gareka, me ne ne mafita a bisa wannan masifa da ta tunkaro mu?"


"Wannan zance haka yake, ya sarkin sarakai kamar yadda na gaya maka cewa zan yi bincike, to na yi kuma an dace, sai dai al'amarin ya zo da wani babban al'amari mai wuyar gaske. Inda zaka yi bincike a cikin littafin tarihin sarautar kasarka zaka ga yadda wadansu jarumai su biyu Sham'unal gazi da dan'uwansa Uzaifa suka narkar da Marganu dan Jandanu, ya zagwanye ya zama wannan ruwa da maginanka suka tono. Ka sani cewa su wadannan 'yan'uwa ma'abota addinin Musulunci ne, to kasa ni a...


Read / Download MAKASHIN MAZA Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album