Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

SARAUTAR MUTUWA Complete Hausa Novel Document by SARAUTAR MUTUWA


SARAUTAR MUTUWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30180



SARAUTAR MUTUWA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 20, Feb 2024

Author: Mansur Usman Sufi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137237071

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 161.28 kb

File Type: txt

Views: 955+

Download: 787+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: SARAUTAR MUTUWA
Haƙƙin mallaka
SUFI
Shekarar bugu
2023
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071




Babi na ɗaya

A ƙarni na biyu bayan yaƙin duniya na ɗaya, a yankin arewacin larabawa anyi wani kasaitaccen birni da ake yi wa laƙabi da zawatul-ifdar.
Birnin zawatul-ifdar ya bunƙasa a harkokin kasuwanci,noma,kiwo da ƙarfin tattalin arziki.
Sarkin da ke mulkin birnin yakasance gawurtaccen matsafi kuma mashahurin attajiri ana yi mashi laƙabi da Lazwar ibn kaulat.
A gaba ɗaya nahiyar larabawa babu mashahurin sarki tamkar shi bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamto GAGARABADAU a tsakanin sarakunan nahiyar.
Duk waɗannan abubuwan da sarki Lazwar ya tara da ya danganci ƙarfin sihiri da tarin dukiya gami da ƙarfin masarauta ya tashi a banza, domin a daren kowa ce rana sai na kulle ƙanshi a turakarshi ya yi ta kukan takaici da baƙin ciki, har sai kuyangin shi sun shayar da shi barasa sannan yake samun barci.
Ba komai ne yake sanya sarki lazwar wannan kuka ba face wani dalili guda ɗaya jal!
Dalilin kuwa shi ne bisa binciken da ya gudanar bisa halarar tsafin shi ya gano cewa har abada ba zai samun haihuwa da kowa ce ya mace ba face ya karya wani sihirin tsafi da a bokin gabarshi sarki darwazu ya yi mashi.
Matsawar kuwa ya yi ganganci ya sadu da wata ya mace koda da kuwa kuyangarshi ce take dukkanin sirrikan tsafinshi da duk abin da ya mallaka zai ƙare zai dawo talaka fakiri.
Tsawon shekaru biyar sarki Lazwar yana cikin wannan baƙin ciki dare da rana.
Kwatsam! Wata rana sai kawai aka ji ya ƙwalla ƙara sannan ya bushe da dariya, sautin dariyar tashi ya amsa kuwwa izuwa gidan sarautar baki ɗaya.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa kowa mamaki kenan, domin yau tsawon shekaru biyar ba'a taɓa jin shi ya yi hakan ba.
Abin da mutane ba su sani ba shi ne bakomai ba ne ya sanya sarki lazwar wannan dariya ba,
sai domin yau ne ya gano hanyar da zai lalata sihirin da abokin gabarshi sarki darwazu ya yi mashi.
Abu na farko da zai mallaka shi ne hawayen wani gawurtaccen dodo dake zaune a dajin Darul-shatir dodo murgazu yakasance hatsabibi wanda ya addabi fatake da biranen da maƙwabtaka da dajin Darul-shatir.
Abu na biyu shine tsumin tsafin bokanya lazira,
bokanya lazira ta shafe tsawon shekaru dubu biyu tana tsuma tsumin tsafin domin ta cika burin ta na tashin kakanta sarkin bokaye daga cikin kushewarshi domin ya sanar da ita waɗansu sirrikan tsafi da zata mulki duniya da su.
Abu na uku shine ruwan tekun Bahar-dawa'u, tekun Bahar-dawa'u na yamma maso arewacin duniya, yana ɗauke da waɗansu irin musifaffun kifaye da macizai da adadin su ya kai dubu biyar, tsananin ƙarfin damtsen ɗaya daga cikin kifayen yafi na bil'adama hamsin.
Abu na huɗu shine alkyabbar sarkin bokayen duniya na ɗaya boka Murkatul-azab, a halin yanzu alkyabbar na ajiye a fadarsho dake ƙarƙashin tekun Bahar-maliya, matsafa,bokaye da masu hasashe sun tabbatar da cewa a halin yanzu a duniya babu wani waje mai tattare da musibu tamkar fadar sarkin bokayen duniya.
Abu na ƙarshe shi ne wata jaruma da ake yiwa laƙabi da Sharifa bintu Usman.
A halin yanzu Sharifa na bauta ne a ƙarƙashin masarautar birnin Istanbul a matsayin baiwa, mahaifanta sun rasu ne a bisa KANGIN BAUTA a masarautar.
Baiwa Sharifa ce kaɗai zata iya taimaka mashi ya samu nasarar mallakar waɗancan abubuwa.
Sa'adda darki Lazwar ya ga wannan al'amari sai ya cika da matuƙar farin ciki, sai dai wani abu daya dugunzuma hankalin shi, shine halarar tsafinshi ta bayyana mashi cewa ba zai taɓa samun nasarar saduwa da baiwa Sharifa ba har ya bayyana mata buƙatar shi na son ta taimaka mashi ya samu nasarar mallakar waɗancan abubuwan da zai karya sihirin ba, face shi ma ya mayar da kanshi bawa ya yi bauta a ƙarƙashin masarautar na tsawon shekaru.
Sannan ma inda gizo ke saƙar shi ne, ba lallai ne Sharifa ta iya amincewa da buƙatar shi ba, tunda a halin yanzu ta rasa dukkan wani farin cikin rayuwar ta.
Kasancewar masu iya magana na cewa biyan buƙata yafi dogon buri, kuma inda rai da rabo.
Sai sarki Lazwar ya tsayar da ranar da zai fita farautar baiwa Sharifa.


Babi na biyu

Kashe gari tun da duku-dukun safiya sarki Lazwar ya fara shirye shiryen tafiya izuwa birnin Istanbul , a dai-dai lokacin da rana ta fara haske ne ya kammala shirin tsaf!
Tun daga kuyangi masu hidima, dakaru, gami da bayi.
A can fada kuwa jama'a sun cika maƙil babu masaka tsinke. Duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu saka tsinke tamkar dandazon kiyasai.
Kowa ya zuba idanu ana jiran fitowar sarki domin ganin wane zai baiwa riƙon sarautar shi.
Tsawon daƙiƙa latalin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura.
Daga can sai ga sarki Lazwar tafe tare da tawagarshi yana sanye cikin surutu na alfarma da sukayi matukar yi mashi kyawu, kai tsaye ya huce izuwa kan karagarshi ta mulki ya tsaya sannan ya fuskanci jama'a ya yi gyaran murya ya ce "ya ku mutanen wannan fada tawa mai albarka ku yi sani cewa a yau ne zan yi gagarumar tafiya izuwa nemo abubuwan da za su warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki Darwazu ya yi mini.
A bisa al'adar wannan masarauta sarki da kanshi yake zaɓar wanda zai bawa riƙon sarautar shi.
Bisa ga nazari da kuma hasashe da nayi babu wanda zai riƙe sarautar wannan birni da amana face magajin gari Yasiran".
Sa'adda sarki Lazwar yazo nan a zancen shi sai jama'a suka ruɗe da shewa da jinjina domin suna ganin shike nan sun huta da mulkin zaluncin sarki lazwar.
Kaico! Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce rashin sani yafi dare duhu, inda a ce jama'a sun san wane ne magajin gari Yasiran da sun gwammace gwara sarki lazwar sau ɗari.
Bayan an ɗora Yasiran a bisa karagar mulki sai kawai sarki Lazwar ya buɗe bakinshu ya ƙwala wa wani hadimin aljanin shi kira sau uku, yana gama rufe bakinshi sai kaga wata halitta shirgegiya na ketowa daga cikin gajimare tana sauka daga sararin samaniya. Nan fa suka ɗimauce suka fara guje-guje da ifice-ifice tamkar sun hango mutuwarsu, wasu ma saboda razani har sakin fitsari suke a wando basu sani ba.
Aljanin ya sauka a turba yana mai shimfiɗe fuka-fukanshi a ƙasa, shi dai aljanin ya kasance shirgege tamkar tsauni yana da rafkeken kai mai ɗauke da kwala-kwalan idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancinshu ƙato ne kofofinshi tamkar bututun shaƙar iska, bakinshi yana da girma tamkar bakin rijiya, maƙale a kwiɓin hamatarshi yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda huɗu.
Haƙiƙa wannan aljani yakasance mummuna kuma abin tsoro ga duk wata halitta mai numfashi.
Aljanin ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa ga sarki Lazwar.
Sannan ya ɗago da kanshi ya dubi sarki Lazwar cikin ladabi ya ce cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya mai duniya gani na amsa kiran ka me kake da buƙata ya shugabana?
Wani alfahari ya shiga kwanyar sarki lazwar jin aljanin ya ambace shu da mai duniya,
cikin BAƘAR IZZA Lazwar ya ce " ya kai Za'aratun-layal ka yi sani cewa bakomai ya sanya na kira ka nan ba sai domin ka ɗauke ni da tawaga ta domin gudanar da wata gagarumar tafiya mai matuƙar haɗari.
Sai dai ina so ka yi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zan 'yan ta ka ' daga ƘANGIN BAUTA a gare ni".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai aljani Za'aratun-layal ya bushe da dariyar farin ciki, dariyar tashi ta haddasa wata gagarumar girgizar ƙasa mutane suka fara halaka, sai da sarki Lazwar ya daka mashi tsawa, sannan ya tsuke bakinshi, a sannanne komai ya samu dai-dai ta.
Ba tare da ɓata lokaci ba sarki Lazwar da tawagarshi su ka hau bisa kan Za'aratun-layal da ya haɗar da sarkin yaƙin birnin da waɗansu zaratan bayi gami da kuyangi masu hidima suka zauna aka ɗora abin guzuri akai.
Sannan aljani Za'aratun-layal ya yunƙura ya tashi sama yana mai kaɗa fuka-fukanshi tare luluƙawa cikin gajimare yana mai tsala azababban gudu, tun jama'a na daga masu hannu har suka dai na hango su.
Sai da aka shafe tsawon sa'a bakwai ana tafiya a sararin samaniya ana keta gajimare cikin...


Read / Download SARAUTAR MUTUWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album