Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DARAJAR MUHALLI Complete Hausa Novel Document by DARAJAR MUHALLI


DARAJAR MUHALLI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 59041



DARAJAR MUHALLI

Reading Time: 4 Hours

Added On: 03, Oct 2024

Author: Nabila Rabi'u Zango ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08028525263

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 351.11 kb

File Type: txt

Views: 873+

Download: 460+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏑🏑🏑🏑🏑🏑🏑
DARAJAR MUHALLI
🏑🏑🏑🏑🏑🏑🏑

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]


Bismillahir Rahmanirrahim.
Ina farawa da sunan Allah me Rahma mejinkai.

GARGADI....... Banyarda wani ko wata su juyamun littafina ko su canzamun sunanshi ba. Wannan labari kirkirarre ne, banyi dan wata ko wani ba, zanyi shine domin yazama darasi ga kai, ke,ni, su da kuma mu baki daya. Allah yasa yanda zanfarashi lafiya in gamashi lafiya amin.

Season 1 πŸ”± 5

Zaune yake agefe guda yayi tagumi hawaye suna bin fuskarshi, idanu yazuba ma mutanen dasuke yi masu watsi da kaya.

Kallon dayan gefenshi yayi ganin yanda matarshi kuma abin sonshi, take kuka. Duk da itace sanadin fadawarsu wannan hali amma yana tausayinta sosai.

Kuma haryanzu duk da irin halin data sakasu bayajin digon sonta yaragu azuciyarshi. Wannan wulakanci na korarsu daga gidan haya shine na 3 tun bayan aurensu.

Goge idonshi yayi, wasu hawayen suka kara zubowa alokacin daya tuna magana mahaifiyarshi. Abbas kada kabiyema Son dakake ma wannan yarinyar, ze kai ka yabarokane, idan bazata iya zama da kai ayanda kake ba to kahakura da ita.

Kanshi yacigaba da girgizawa hawayen idonshi suna kara zubowa, yarasa inda zesa kanshi, gashi ta dalilin matarshi gaba daya sun bata da abokanshi, mutum daya ne, yarage mashi wanda yake temaka mashi.

Karar faduwar wani abu dayaji ne yayi saurin dawo dashi daga tunanin dayakeyi. Ihun matarshi yaji tana fadin dan Allah kuyi hakuri kada kuyi mana banna.

Saurin tashi yayi yanufi gurinta. Jawota yayi ya rungumeta yana bata hakuri, mutane dayawa yan unguwar harma da makota sun tausaya masu.

Wani daga gefe ne yace kai gaskiya abokina megidan nan beda mutunci, kamar ba musulmi ba, haba dan Allah yaza,a rika watsi da kayan mutane kamar besan darajarsu ba.

Abokin yace uhm abokina beda laifi, kama dena tausayin ABBAS ALEE, domin acikin rukunin unguwar nan mutane dayawa sun san halinshi,

Ace mutum beda tunanin kanshi sena matarshi. Haba wace irin rayuwace haka, ai so ba hauka bane, a iya sanina wannan shine gidan haya na 2 danasan ana mashi irin wannan korar wulakancin.

Kuma duk lokacin da aka tashi korarshi seyayi asara ba kadan ba. Yanzu kaduba kayansu, sekace wadanda suka shekara 10 dayin aure.

Duk sun kare ayawon haya. Wlh kaganni nan babu yanda za,ayi inyarda inyi aure batare dana mallaki MUHALLI na nakaina ba. Aishi MUHALLI DARAJA gareshi.

Maganar daya daga cikin mutanen dasuke masu watsi da kayan ne taja hankalin masu wannan maganar. Ina me tabbatar maku ko kukan jini zakuyi wlh kun gama zama acikin gidan nan.

Ai ko da kudin ubanku aka sayi gidan inde ance na haya ne, dole kubiya idan lokaci yayi, damma kunsami Oga mesauki ne har ya iya yafe maku na watannin da kuka kara.

Acikin kudinku na shekara har seda kuka kara wata 4, sannan duk da haka bakuga adalcin da megida yayi maku ba. Sa,a kukaci da besa aka daure kuba. Maza ku kwashe tsummokaran kayanku kubar kofar gidan nan.

Shide Abbas Alee yayi shiru bece komai ba, yana rungume da matarshi, yama rasa yanda zeyi, gashi ko sisi bashida ita bare yakira me mota yadaukar masu kayansu.


Yana kallo mutane yan kallo suka fara watsewa, da haka har gurin yazamto saura yara kanana, kama matarshi yayi yazaunar da ita gefe, tana ta faman goge kwallan datake zubo mata.

Aranta tana danasanin wannan hali nata marar kyau, da yanda tabiyema karyar zamani tasaka mijinta cikin wannan yanayin.

Matsawa yayi gurin kayansu yafara tattara akwatinansu yana kawosu gefe guda, sannan yakoma yahada sauran kayan daya bayan daya yatarasu suma agefe guda.

Kusa da ita yadawo yazauna, yace LABIBA dan Allah kidena wannan kukan haka, banason kina kuka domin kukanki yafi wannan hali damukeci, sakani cikin damuwa.

Kallonshi tayi tace dole inyi kuka Abbas, duk nice sanadiyar sakamu cikin wannan rayuwa, gashi yanzu duka shekararmu 4 da aure amma haryanzu babu gidan damukayi sama da shekara 1 acikinshi.

Tun muna zama gida me kyau, har muka fara zama marar kyau, yanzu gashi wannan dinma danake rainawa, shima ankoremu, yanzu kuma wayasan wane iri zamu samu? Kuka takara sakamashi.

Jawota yayi yace karki damu, Allah shine yasakamu acikin wannan halin kuma yana sane damu insha Allah bazamu tozarta ba, abinda nakeso dake ki kara hakuri dani aduk halin dazamu tsinci kanmu aciki.

Banason talauci yasa kijuya mun baya, nayi maki alkawarin zan zauna dake akowane hali nake ciki, inaso kema kimun wannan alkawarin Labiba.

Shan majina tayi takamo hannunshi tace nayi maka alkawarin zan zauna da kai koda acikin bukka zamu zauna matukar zan jika akusa dani, kuma nayi maka alkawarin insha Allahu bazan kara bijire maka ba aduk inda kasama mana domin muzauna.

Murmushin jin dadi yayi yakara rungumeta yana fadin nagode maki masoyiyata Allah yabarmu tare. Dafashi yaji anyi dasauri ya juya yana kallon bayanshi.

Murmushi yayi yace sannunku masoyan asali, wato kuna cikin wani hali amma kuna soyayya ko ABBAS ALEE?.

Murmushi Abbas yayi yace to abokina yakake so muyi, ai gara muyi soyayyar kozamu samu saukin abinda yake damun mu.

Zama yayi kusa da Abbas fuskarshi dauke da damuwa yace ina kasuwa ashago nasamu labarin abinda akai maku, hakan yasa na taho,kuma tundazu nasamu labarin.

Abinda yasa banzo dawuri ba, seda nabiya nafara sama maku wani gidan dazaku zauna sannan nataho da motar dazata dauki kayan.

Wasu hawayene suka zuboma Abbas dayaji bayanin babban abokinshi. Kallonshi yayi yace Jafar nama rasa dawane baki zan maka godiya, akullum bakada wani buri daya wuce ka kyautatamun.

Tabbas kai abokine nagari, Allah yayi maka albarka, yabaka duk abinda kake nema. Jafar yace amin. Dama kwana 2 banga kaje shago ba, shine naje gurin Alhajin na tamabayeshi,

Shine yake cemun wai ya sallameka, amma meyasa baka fadamun ba? Girgiza kai Abbas yayi yace haba Jafar yazanyi tasaka cikin damuwa, bayan kana kokarin temako na akowane lokaci.

Jafar yace koma menene yakamata kafadamun, ina da wani bayanka,ne? Kai wane irin temako,ne bakamun ba, seni yanzu inkasa temaka maka.

Wlh nayi bakin ciki da gidana be kasance me dakuna dayawa ba, da aciki zaka zauna har abada har kasamu naka nakanka, kai koda ace dakuna 2 ne, zan iya daukar daya inbaku daya.

Sede kash!!!, nima da kyar nasamu nagina ciki da falo da bandaki , kana ganin haryanzu kitchen dinma bankarasa ginashi ba. Abbas yayi murmushi yace Jafar ka godema Allah dayaba ikon mallakar MUHALLINKA na kanka.

Kuma babu komai, wannan abun ma dakamun kadai ya isa, nagode sosai, nima kaddara ce tafadomun harna rasa nawa MUHALLIN, se ayanzu nake gane DARAJAR MUHALLI.

Amma bakomai, tunda na tsira da abin sona hakan ma ya isheni. Girgiza kai Jafar yayi cike da tausayin abokinshi, yarasa wane irin sone yakema Labiba. Matar da itace silar shigarshi cikin wannan yanayin.

Kamar daga sama yaji muryar Labiba tace Jafar awace unguwa ka sama mana gidan, Allah de yasa tana da kyau, kuma babu kowa aciki?

Saurin kallonta Abbas yayi domin beji dadin maganar datayi ba, shiru yayi dan bayason yayi mata magana ranta ya baci. Jafar kuwa jiyayi kamar ya shakota.

Daurewa yayi yace acikin burget gidan yake, kuma abokina sede kuyi hakuri domin gidan dakuna 4 ne aciki guda 3 akwai mutane, dayan ne nakama maku, sede ciki da falo ne, amma babu bandaki aciki.

Yana waje, sede kuyi hakuri kafin Allah ya hore asamu wani se acanza maku, kasan yanayin da ake ciki, yanzu kasuwa tayi kasa. Abbas yayi murmushi yace haba abokina meye na bada hakuri sekace da kudinmu aciki.

Nagode sosai Allah yabar zumunci. Yace amin. Wata irin zufa ce tafara keto ma Labiba jin irin gidan da aka kama masu, yoko gidansu na da ai yafi shi daraja. Idonta ta kulle wasu zafafan hawaye suka zubo mata, tana kara tsanar kanta. Da haka aka saka masu kayansu acikin mota suka nufi sabuwar unguwarsu.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady )
08028525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏑🏑🏑🏑🏑🏑🏑
DARAJAR MUHALLI
🏑🏑🏑🏑🏑🏑🏑

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 5 πŸ”± 10

Labiba tana tsaye aka gama shiga da kayansu cikin gidan, wani irin bakin ciki ne ya turnuketa, tunda taga sun shigo cikin unguwar, gaba daya layin beda fasali,

Ko acikin Burget dinma yana daga cikin kazaman layi, har cikinta seda taji yana yamutsawa saboda warin kwata, kara kallon gidan dazata zauna tayi,

Ko kofar kirki babu agidan, hatta da simintin gidan duk ya karce, kwalla taji ta cika mata ido, tunawa tayi alokacin da Abbas yakama masu wani gida kafin su zauna a wanda
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DARAJAR MUHALLI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album