Join Our WhatsApp Group

KOWACCE KWARYA Complete Hausa Novel Document by KOWACCE KWARYA


KOWACCE KWARYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13015



KOWACCE KWARYA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 31, Jan 2024

Author: Yusrah Musa Abubakar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ANNURI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : +2349055273614

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 70.45 kb

File Type: txt

Views: 424+

Download: 108+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: TYPING 📲 {WED 20 DEC 23 8:43AM} YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

WHATSAPP NO: 234 905 527 3614

💞 KOWACCE 'KWARYA💞


DEDICATED TO
MY FATHER MUSA ABUBAKAR MUHAMMAD may Allah help u may Allah bless u may Allah protect u anywhere u are may Allah accept ur du'as amin.

STORY BY
🏵️👌 BATILAH ABDULLAHI)(Batul)(

✍️ WRITTEN AND EDITING
YUSRAH MUSA ABUBAKAR {maman Fatima Elham little Zaran aunty 🌹💕}

I'm here to make u happiness educated hhhhhh!😜 domin nifa I have no girman kai if u're fushi dani😠 to wallhi u're just 'batawa kan k lokaci🙉 ni ta kowa ce.

Godiya sosai sosai godiya masoya babu bakin da zanyi muku albarka dashi bisa kauna da kuke gwada min saidai nace Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa a duk inda kuke amin.
💕 Zarah Musa d'an Adam
💘Naja'at Musa Abubakar
😜Rakiya Abdullahi
🙉Ruwainah Abdullahi.
Ranar kuce masoya maza kada kuyi sanya muyi rausaya 'yan uwa mu taho da baya baya mune muke cashewa💃💃 a group.

In the name of Allah the most benefits and the most merciful we luv our nabi we like him he's the mirror of our life no success with out him he haven't limit peace be upon him amin.

#YUSI CE#
PAGE 0️⃣1️⃣👉0️⃣2️⃣
Parking yai da matukar 'karfi a cikin tabkekiyar babbar rumfar aje motocin dake 'katuwar harabar gidan su wanda da sauri wani mutum dake sanye da uniform yazo ya bude masa.

Yana cewa "u're welcome sir".

Fitowa yai cikin taku mai kyan burge mai kallon sa ya nufi kofar da zata kaishi cikin palor yana rike da rigar suits dinshi.

Yaji mamaki har yana d'an zaro kyawawan idanuwan shi waje ganin babu wanda ya kula da shigowar shi hankalin su naga kallo wasu naga waya.

Gyaran murya yai wanda a tare gabaki dayan su suka juyo suna maida hankalin su kansa.

Duk idanuwa suka zaro kamar zai fito waje dan tsoro da mamki lokaci guda suka rud'e kowa ya gigice.

Murje ido Afifah tai ganin da gaske shine yasa tace.
"Yaya kaine"😭?.

A yadda tai masa maganar yasa ya sake zaro mata idon ta gansu dakyau 'kila ko ta dawo hayyacin ta.

'Dora hannu tai aka da gudu tabar falon tai stairs tana cewa wayyo Allah shikenan discipline ya dawo zaman bedroom ya dawo jama'a ku fito".

"Hummm Afifah is so funny zan kama ki zaki baya ni" yai maganar a ransa ya wucewa.

Da kallo sauran suka bishi suna sauke ajiyar xuciya gashi 'kafafun su sunyi nauyi balle su tashi kafin ya dawo su gudu ita kam mummy lamarin su na bata dariya.

Shigowar Daddy kenan ganin yadda yaran nasa suke yasa shi dakatawa yana karantar yanayin su domin ya sani matukar suna halin lafiya yana dawowa zasu tare shi da farin cikin su sa'banin yau da yaga damuwa a fuskokin su.

Hannun karamar ya riko yana mikar da ita tsaye yace.

"Auta na miye yake faruwa ne"?.

Kafin tai magana Fati dake gefe tai wuf tace "Daddy ka taimake mu wallhi ya dawo".

Cikin rashin fahimta Daddy yace "waye ya dawo kuma"?.

"Yaya boss😂" Elham dake gefe tai maganar kamar zatai kuka.

Kallon ta Daddy yai da d'an mamki a fuskarsa yace "wai Aliyu Haidar d'ina ne ya dawo gida"? 'Dana ya dawo my son💘 is back 🙉".

Duk zaro ido sukai jin abinda daddyn yace ga kuma farin ciki ya bayyana a fuskarsa.

Kallon su yai yana murmushi yace "haba Koda naji shiyasa naga kun nutsu yanzu wace a cikin ku zata je ta kira min shi"?

😲Duk shiru sukai suna sunkuyar da kai aka rasa mai tari yar dariya Daddy yai yana girgiza kai yace.
"Ke Elham je ki Kira min shi".

Kallon Daddy tai hawaye ya kawo a idon ta lokacin data mike da d'an mamki Daddy yace.

"Wai duk maye hakan d'an uwan kune fa".

Goge hawaye Elham tai tana cewa "Daddy ba gudun shi muke ba lamarin yaya Aliyu sai shi".

"To kinga bar kukan je ki Kira min shi".

Wucewa tai yayin da Daddy ya bita da kallo yana murmushi kafin ya kalli sauran yaran nasa.

Tafiya Elham take tana tsara da yadda zata iya shiga dakinsa a hankali ta bud'a kofar falon ganin baya nan yasa ta wuce bedroom d'an kwankwasa kofar tai amma shiru ta sake ba amsa hakan yasa ta bude yana kwance a kan gado ya zubowa kofar ido yaga wanda zai shigo.

Tsayawa tai daga jikin kofa tane cewa "yaya kazo Daddy na neman ka".

Kamar tana tafe yana bin bayanta haka ta ganshi a falon daidai Afifah ta sauko ya jawota yana tuma mata dundu a bayanta 'kara tai da gudu tana yin bayan Daddy.

Elham kam tunda ya fito jikin ta yadau rawa bata farga ba ta ganshi a gabanta ri'ko hannun ta yai cikin fad'a ya soma magana.

"Ke dan uban ki ni sa'an wasan kine da zaki min magana ta kofa"?.

"Yau nake ganin ikon Allah a gurin ka to da ta ina zatai maka magana ta window"? Mummy tai maganar.

"A'a mummy yarinyar nan dan rainin hankali babu sallama taje tana min ihu harda gudu kamar taga mala'ika".

"To da meye kai mala'ikan yara ne mana kaga sakar min hannun yarinya".

Sakin hannunta yai yana bata ran'kwashi mai zafi wanda yasa da sauri ta dafe kanta.

Kallon Afifah yai yana cewa "ke discipline ya dawo Fati matsalar ki ya dawo Elham damuwar ki ya dawo Husnah kukan ki ya dawo mai hana ku shan iska mai dad'i kamar yadda kuka ce to kusa Allah a ranku ban canza ba ina nan yadda nake yadda kuka sani har nafi da kuma na dawo babu wacce zata sake jin dad'i a cikin ku".

"Nikam yau nake ganin wata 'kaddara ayi mutum fad'a kamar kububuwa dan Allah ka rika shan ruwan sanyi".

"Mummy yaran kin nan basa jin magana gabaki dayan su".

"Shikenan to idan ka gama fadan ka zauna mu gaisa daga dawowar ka duk ka hargitsa gida".

Zama yai suna gaisawa suna masa sannu barka da dawowa yana fad'a musu abinda ya cancata ya fad'a.

Daddy ne ya tambaye shi "yaushe zaka koma amma dai bada wuri ba fatan zaka dad'e"?.

"A'a Daddy karamin hutu na kar'ba maybe two weeks ma na koma".

Ya fad'a yana kallon Afifah da Elham lokacin da suka tafa cikin murna murmushi yai yana jinjina kai lallai yaran nan basu da hankali.

Maida hankalin sa kan Daddy yai jin yace "haba dai sati biyu fa Aliyu da wuri haka? Shekarar ka daya da rabi fa baka zo gida ba"?.

"Kuyi hakuri Daddy yanayin aiki ne".

"Babu komai munsan da haka Allah ya taimaka ya kuma albarkaci rayuwar ka da zuriyar ka".

"Amin Daddy na gode".

Kiran sa akai a waya ganin mai Kiran yasa yace.

"Ina son zan fita".

"Ok ba matsala".

Mikewa yai yana fita da sauri Afifah tazo gaban Daddy tana durkusawa tace.

"Dan Allah Daddy kasa shi ya koma yai hutun sa acan".

Kallon ta Daddy yai kamar zaiyi dariya ganin duk tabi ta burkice yace.

"Me kika ce Aliyun nawa zance ya koma d'ana nefa yaushe rabo na dashi"?.

"To amma Daddy kana ganin abinda yake mana daga dawowar sa".

"Eh na gani ai baifi gyara ba".

Tashi Afifah tai tana cewa "to wallahi zaman lafiya na kawai naje na hada kayana gara na tafi gidan su mummy kafin ya hutunsa ya koma dan na tabbata idan na zauna ko burbushi na baza'a samu ba".

"Kada ki soma had'o kayanki babu inda zaki je".

Tuntu'be ta kwasa jin abinda Daddy yace yasa ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya.

"Afifah idan baki tsaya kun fahimci juna ba a matsayin ku na yan uwa sai yaushe ko sai bayan mun mutu"?.

"Bana so na sake jin wata magana ki dawo ki zauna cikin yan uwan ki".

Dawowa Afifah tai tana zama batare da tace komai ba yayin da Elham ke mata dariya a boye.

Aliyu na fita yaga Samir yana sake gwada kiransa ganin ya fito yasa yace.

"Haba Aliyu tun dazu inata jiran ka".

"Eh kayi hakuri na tsaya gurin Daddy ne".

"Ok barka da zuwa gida bayan lokaci mai tsawo muje ka bani labarin inda kuke".

Wucewa sukai Aliyu na cewa "Amm Samir yaya ajiya ta take fatan tana lafiya right"?.

Murmushi Samir yai 'ai Marshall albishirin ka ajiyar ka tana lafiya ina kula da ita yadda ya kamata".

"Ka tabbata"?.

"Kwarai aboki na".

"Bana son wasa Samir".

"Ka yarda dani Marshall ba wasa abinda nake fad'a maka tsantsar gaskiya ne".

"Shikenan amma zan iya ganin ta"?.

"Mazai hana muje na nuna maka ita".

Fita suka daga harabar gidan suna tafiya wani gida suka shiga mai gate saidai ya tsufa har tsatsa yake kuma a hakan ta waje yafi ta ciki dama dama domin gidan a ru'be yake.

Magidanta uku ne a gidan kowa da kofar sa da iyalan sa da tsohuwar gidan tana nan a raye ita ta da part dinta.

Ba tsananin talauci ne ke damun gidan ba a'a ido ne yai musu yawa mazan gidan kowa bazai fidda kudi ya gyara shi kadai ba kuma a had'u a gyara rashin hadin kai ya hana.

'Daya headmaster ne na primary daya d'an sanda ne dayan shine baya da aiki saidai yana dan kasuwancin sa ba laifi.

Akwai gwarama a gidan akwai gulma munafinci yida wani hana zaman lafiya da akwai matan aure shida a gidan kowa macen shi biyu da yara.

Kofar tsohuwar gidan suka fara shiga da akwai yara da yawa suna zaune ganin tayi ba'ki yasa suka mike suna fita.

Zama sukai bayan sun gaisa kaka dake cin goro tace "Samar waye ne wannan din na kusa dakai"?.

'Bata rai Samir yai "kai hajiya dan Allah miye wani Samar kuma"?.

Aje goron tai tana masa dakuwa tace "naci gidan ku tun kafin a haifi ubanka nake rayuwa shima nice na raine shi saida ya taso na nuna masa komai zakai min wata magana".

"To hajiya ke dince da kayan haushi shi yasa ban cika shigo miki ba saboda fad'a muke idan ma nazo".

"Karka sake shigowa daga yau ai ba kai kadai bane jika na gasu nan da yawa saina za'ba".

"Basai kin za'ba ba kowa jikan kine".

"Nidai akwai wadanda ba jikanu na ba domin ni jikanu na suna da farin jini".

"To kuma waye mai 'bakin jini a gidan"?.

"Ban sani ba matse ni saina fad'a maka".

Zaro ido Samir yai "wa Nina isa nima da su Abba sun matse ni".

Kinga hajiya duk mubar wannan ga jikan ki yazo gaida ke".

Kallon sa hajiya tai "waye ne ban gane Shiba d'an nan daga ina"?.

Samir ne ya bata amsa "Aliyu ne daga gidan Daddy Ahmed".

"Tofa waye dad'i Ahmad kuma"?.

"Bafa dad'i Ahmad ba Daddy Ahmed nace".

"To ai ban gane ba kamin yadda zan fahimta mana".

"Hajiya nan kusa damu nake nufi gidan alhaji Amadu minister.

'Yar zabura hajiya tai tana zaro ido cike dake da son zuciya tace "ayya yaron daya tafi soja ne kaga marmari daga nesa ku ake wa kirari tuwon 'kaya Allah sarki yaro ashe ka dawo kullum saina yi sallar dare saboda kai da safe na sayo 'kosai nayi sadaka nace kuna can jeji ba gida ba gari fata na ka dawo lafiya sai kaga kwatsam kayya rayuwa" hajiya ta karasa maganar tana kuka.

Shiru Aliyu yai yana kallonta Samir na cewa "ki daina kuka hajiya ai tafiya ba mutuwa ce ba".

"Ka barni nayi Samar ka barni".

"Shikenan to hajiya zamu tafi" .

Mikewa sukai kudi Aliyu ya ciro yana bawa Samir ya Mika mata wanda dama tana goge idanu tana kallon shi ta tsananin yatsun ta da sauri ta karbe tana masa godiya suna fita ta daga fulo ta saka tana cewa.

"Haba malam zamanin nan Saida basaja Saida farauta ba gashi na samu kudin batarwa ba.

Suna fita daidai 'yan mata biyu zasu shigo gidan wacce tafi shishshigin da sauri tace.

"Yaya Samir waye wannan kamar yaya Aliyu na gidan su Afifah"?.

Daidai zasu fita Samir yace "ba kama bace shine".

Zaro ido tai tana dafe kirji tace "wow lokacin wanka yazo lokacin sa kyawawan kaya lalle akai akai zuwa gyaran jiki saloon ba kama hannun yaro zanyi bari naje gurin hajiya".

Daidai sun ci gaba da tafiya dayar da batai magana tace "ai bake kadai ba zaki nima haka mai rabone zai samu kusan mu biyar ne ke sonsa a gidan nan".

"Na sani amma ina ganin duk na fiku son sa".

"A yadda kike ji a ranki ba".

"Zance me kuke kuda kullum kuna tafe kuna magana kamar wasu ta'ba'b'bu"?.

Zama sukai Rasheedat na cewa "akan Aliyu ne dan gidan ministan nan alhaji Ahmed san kowa".

"To me ya faru" hajiya ta tambaya tana sake zaune fulon da tasa kudin.

Bilki tace "babu komai kawai son shi muke".

"Da gaske kuke yaran nan"?.

"Allah hajiya".

'kasa hajiya tai da murya tana cewa "yauwa yan albarka haka nake son ji kwanan nan zan jike da kudi idan dayar ku ta aure shi ku dage yasan daku".

Kudin daya bata ta dauko tana nuna musu tace.

"Kunga yanzu Samar ya kawo min kalli alherin daya min idan kuma akace yayi aure a gidan nan kullum jalaf din taliya🍝 da kifi🐟 ga zobo🍷 mai sanyi nasan shine abinci na dan Allah yaran nan kada kumin bakin ciki".

Kallon juna sukai suna shekewa da dariya suka ce "sai hajiyan mu muna yinki".

Washe baki tai yauwa ko kufa haka nake son ji".

Cikin wayo Bilki tace "amma hajiya kinsan bazai somu a haka ba dole sai muna kyawawan shiga irin ta 'ya'yan masu kudi muna kwalliya kuma bamu da kudi yanzu ni saurayi na yayi tafiya".

Dariya Rasheedat tai "nima nawa garan yayi tafiya shekaran jiya kuma banda ko sisi hajiya a cikin kudin daya baki zaki bamu ko dubu biyar ce".

Zaro ido hajiya tai "caf dubu me lallai yaran nan baku da hankali ko biyar bazan bayar ba balle dubu biyar".

Hada ido sukai suna 'kiftawa Rasheedat tace "shikenan hajiya zamu nema amma ki sani idan yazo yace yana son mu ya aure mu kada muga yar 'kafar ki a gidan idan ma kinje zamu sa securities suyo waje dake mu nuna bamu sanki ba daga mu sai iyayen mu".

Shiru hajiya tai jikin ta yayi sanyi ta dauko kudi tana cewa "saidai na baku Kowaccen ku dubu biyu nima fa dubu goma ne kawai".

"To shikenan munji bamu".

Mika musu tai suka mike suna fita hajiya data bisu da kallo tace " jimin shegun yara da wayon banza kodan idan dadin yazo tare zamu ci🤣.

Fita sukai suna dariya Bilki tace "wallahi dama yau haka na tashi ko sisi banda amma yanzu ga dubu biyu ziyau muje muyi wanka muzo muci uwar dubu hudun nan".

Fita sukai daga bangaren hajiya kowa yana shiga kofar su dan yin abinda suka ce.

Fitowar su waje Aliyu ya kalli Samir yana cewa "Kai Samir wannan wanne irin wulakanci ne ka nuna min"?.

"Eh da nai me "?

"Da kai ban sani ba cewa fa nai muje ka nuna min ajiyar dana baka"?.

"Oh sorry sorry my buddy kayi hakuri zan nuna maka ba yau ba".


"Sai yaushe"?.

Cikin tsokana Samir yace "tommorow morning"?.

Hade rai yai "tommorow morning kuma"?.

Shiru Samir yai kallon sa Aliyu yai ganin dariya yake masa yasa yadan daki kafadar sa yana cewa.

"You're not so kind mutumi na kana bani ciwon kai".

"Yi hakuri Marshall insha Allah gobe da safe zan baka magani zaka warke".

Amira na jin labarin cewa Aliyu ya dawo...


Read / Download KOWACCE KWARYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album