Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

BATUUL Complete Hausa Novel Document by BATUUL


BATUUL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 213593



BATUUL

Reading Time: 17 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Phartiemarhk ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.1 mb

File Type: txt

Views: 4247+

Download: 9457+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: Compiled by Umar Dalha
Copied by Princess Aysha Muhammad


💖💝BATUUL 💖💝


1




By phartiemarhk





All Thanks to Allah (SWT) for granting me d chance,ability , previledge and knowledge to write this story. I dedicate this book to *KHALEESAT HAIDAR* (Maijidda) ,you have been an amazing writer,you make time for it everyday. You have set realistic goals,embraced the ecstacy of writing. You followed your heart not the market and fame. You don't just Start stories,you finish them,you dream big. You learn the rules,follow the rules and break them because rules are meant to be broken😅.Constructive, Criticism,Solicit,Accept and Manage. Put your ego in your back pocket and sit on it. Writing is à Journey, not à destination. Enjoy the scenery and give back to the writing community. WRITE SCARED. Remember you are the master of inspiration, not its Slave. Set your stories Free. Send them into the world .
DON'T SLACK ON THE HARD STUFF.
*PHARTIEMARHK* LOVES ❤💝You😘






Sanye take da Abaya baqa da yasha aiki da Swarovski stones ta yafo qaramin gyalen abayar ba tareda da wrapping dinshi ba kafarta sanye da slippers din vinci shima baqi mai Swarovski Stones din à jiki .Siririyace sannan ba doguwa ba tana da shape mai kyau irin wanda ake kira figure 8 bata da haske kuma bata da duhu sosai, Irin dai mutanen da ake kira chocolate color ne ko kuma wankan tarwada, dan karamin fuskar ta zagaye yake da dan karamin baki, yayinda Dogon hancinta ya dace da mazaunin sa, Idan tai murmushi kuwa dimlpe dinta yake lotsawa ya Kara hasken annurin fuskar, idanun ta kuwa haka suke tamkar farin wata wajen haske yoh masu iya magana sukace Ga Wata 🌙👈 ga Zara 😀,hooo me kr2 Idan nace zan tsaya zayyano kyawun fuskar ta toh Lalle za'a dade ban gama ba, domin dai BATUUL mai kyau ce.




riqe take da iPhone dinta à hannun hagu yayinda dayan hannun take riqe da karamin yaro da bai wuce shekara uku ba, tafiya takeyi à hankali kuma cike da natsuwa sannan ga hadari da ya rufe ko ina, ruwa ko yaushe kan iya saukowa sai iska mai dadi dake kadawa à hankali à filin Idin Ramat square dake Maiduguri ,ta juyo sannan ta kalli yaron dake riqe da Hannunta sannan tace Babich kaga kasa su Mama Sun tafi Sun barmu ko ai shikenan in muka rasa sallah yaron yayi dariyarshi mai kyau yace ai zamuyi sallah har in roqi Allah ya bani irin CLS din Yaa Ahmad tace to kaga muyi sauri sai mu yi sallahn yaron ya dubeta sannan yace yaa Baatul ai kece bakya yin sauri inata Jan hannunki tace toh shikenan zanyi saurin muje mu samesu haka suka karasa har wajen Sallahn daga gefen mata suka samu har an shimfida musu abun sallah sannan suka zauna wata farar mata mai kyau da baza ta wuce shekaru 35 zuwa 38 ba tana riqe da jariri ta juyo ta dubesu tace a ina kuka sami hulan ? Baatul tace Aunty a mota ya bari matar da aka kira da Aunty tace ai ke kika biye mishi da kin barshi yayi sallah babu hula tunda da gangan ya cire, Batuul tayi murmushi tace Aunty ai da yanxu bamajin Khuduban nan da akeyi Aunty tace hakane Baatul ta juya ta kalli wata yarinya da bata wuce sa'arta ba tace Fa'iza kin dauko min jakata da nace ki fito min da ita dan inaso inyi sadaka in an idar da sallah yarinyar da aka kira da Fa'iza tace ehh yaa Baatul na dauko gashi nan ma ta dauko wata jakar Hermès mai ruwan toka da kana gani kasan an kashe naira ta mikowa Baatul ta amsa tayi murmushi sannan tace na gode Fa'iza haka suka zauna shiru suna sauraron khuduba har aka gama aka tada sallah Baatul ta dubi Fa'iza tace tunda ba kya sallah ki karbi Aabid à hannun Aunty tace toh Yaa Baatul ta sa hannu ta karbi jaririn daketa wasa sannan ta dan koma gefe su kuma sukayi kabbara suka nutsu dan su nuna godiyarsu ga Allah (swt) da yasa suka gama Azumi lafiya har yasa suka ga sallah.




Ahaka suke Zauna bayan idar da sallah har Imam ya gama hudubar bayan sallah da wa'azi da tunatarwa , nan Dubban jama'ar da suka hallaci sallar suka fara kokarin kama gabansu.
💖💝BATUUL💖💝






3






Dedicated to *KHALLESAT HAYDAR*






Tuki yake cike da nutsuwa da kwanciyar hankali kan titin Kashim Ibrahim Road ba a jin komai sai karar AC dake busa iska mai kanshi da dadi har suka karasa masallacin suna ta fadin (Allahu Akbar Allahu Akbar Laillaha illalah Allahu Akbar kabira wal hamdulillahi kasira wa subhanallahi bukratan wa asilaah wa sallalahu ala nabiyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi wa sallama tasliman kabira) Abinda suke ta maimaitawa har suka isa masallacin kenan suka samu waje suka yi parking sannan ya fito ya budewa Abui kofa Farida ma ta bude ta fito ta miko mishi Sallaya daga bayan mota sannan ta kalli Abui tace bari in karasa side na mata Abui yace okay mamana



Bayan idar da sallah ne Aunty ta dauko jakarta ta ciro rafar yan dari biyar sabbi fil ta mikawa Batuul tace gashi ki bayar sadaka ai baba ya baki naki ko ? Batuul tace ehh sannan Aunty ta sake cewa Ni zamu Je mota dasu dasu Yusra dan Aabid ya fara jin yunwa in kin gama ki samemu tace toh Aunty ta karbi kudin ta saka à jaka tace sai nazo su kuma suka tafi


....Hajiya Allah yasa anyi à sa'a Allah yasa muna da rabon ganin badi Hajiya à taimaka Fisabilillahi

Batuul ce ta karasa inda mutanen nan da Almajirai suke a zaune ta ciro kudi daga jakarta na bandir din dari biyar da na dari biyu ta fara rabawa bayin Allah dake wajen su kuma suna ta yi mata addua tana cikin rabawa ne wani iska mai hade da ruwa ya fara saukowa take ba tare da shiri ba ta zube musu kudin dake hannunta ta juya zata bar wajen kenan taji tayi karo da mutum, ta dago kanta da iska ke kokarin cire gyalen da sauri tana fadin Hey am sorry, bata samu karashe maganar ba sabida yadda taga mutumin ya tsaya yana kallonta dogo ne sosai dan sai da ta mikar da kanta sosai kamin ta karashe ganin tsawonsa , kyakyawa ne sannan ba fari bane baqi ne amma baqin shi mai haske ne, yana da side burns sannan yana da dogon hanci da mitstitsin baki dake zagaye da millionnaires belt duk da akwai hula akanshi sai da ta hango gashin kanshi kanannadadde da hulan bai rufe ba haka ma gashin gira da lashes dinshi bakake ne, cikin seconds da basu fi uku ta gama kare mishi kallo tayi sauri ta saukar da kanta kasa dan hawaye taf ya cika idonta, bugun zuciyanta ya karu kamar zai fito


ya bude baki kenan zaiyi mata magana cikin sauri ta matsa baya daga wajen bata tsaya yin komai ba ta juya cikin sauri sauri da dan gudu ta karasa inda tayi parking BMW 8 séries ta bude ta shiga ta jefa jakanta baya , tana zama tayi ajiyar zuciya Aunty ta juyo ta dubeta tace lafiya kike ajiyar zuciya ? Tace Aunty ruwan nan da nayi escaping bai jikani bane ya sani yin ajiyan zuciya Aunty tace toh ni yanxu karbi key mu tafi gida Yusra ta Ce min yunwa takeji, ga Aabid ma na rigima Batuul ta juya bayan motar ta kalli wacce aka kira da Yusra tace ba sai da nace kici abinci ba kamin mu fito ba kika ki wai ke sai kin dawo Batuul ta juyo ta dubi Aunty tace Janet fa har binta ta riqayi da abincin kamin ta saka mata kaya taqi shine yanxu zata cewa mutane wai tana jin yunwa bata ce komai ba Yusran sai zumburo baki da tayi Batuul din ta sake ce mata ki bude jakana akwai TWIX ki dauko kuci ke da Hafix (Babich) ki bawa Fa'iza ma sannan ta juya ta dauki tissue à gaban motar ta goge fuskanta da ya jike da ruwa, ta bude pidgin din motar ta dauko orbit mai flavor din pepper mint ta jefa à baki sannan ta gyara gyalen ta daura shi kamar dankwali sannan tayi igniting motar ta tada suka tafi


Tunda ta bar wajen yake tsaye yana kallonta har ta shiga motar suka tafi bai dena kallon wajen ba sai da yaji an taba shi ta baya ya
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download BATUUL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album