Join Our WhatsApp Group

GIDAN FATALWA Complete Hausa Novel Document by GIDAN FATALWA


GIDAN FATALWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8771GIDAN FATALWA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 19, Aug 2023

Author: Abdul King Article ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Horror novels

File Size: 48.05 kb

File Type: txt

Views: 1016+

Download: 207+

Last download: 2 days ago

Description/Story: An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

COMPILED BY
Abubakar Saleh Quyraemey Ne Mutumin ku
Admin @Top Hausa Novels
What@PP No: 08138873799


GIDAN FATALWA
Written by
abdul king article
A lokacin da matsanancin duhu ya zagaye ciki da wajen birnin, wasu halittu kan farka
domin gudanar da ayyukansu na yau da kullum, wannan farkawa tasu ya haddasa wata
kakkarfar guguwa, wannan guguwa ta fara tsiri sama tana wani irin karaji mai amo, da karfi
wannan guguwa ta fara gudu tana buge abubuwa, haka ta cigaba da shiga lungu lungu na
garin tana bannata kayayyaki.
Tafiya takeyi tana rangwada da taku dai dai sai kace marar jini da tsoka, juyawa tayi da
karfi sakamakon karar wani abu da taji, wannan abu data gani ya tayar mata hankali,
saboda haka ta fara gudu domin samun mafaka, amma ina, haka wannan guguwar ta
cimmata, a nan guguwar ta daga ta sama, ita kuwa sai ihu takeyi tana neman taimako,
amma ina, haka guguwar ta mata guntu guntu, wato kai daban, hannaye saban, kafafuwa
daban, anan matar ta fadi matatta.
Daga nan sai guguwar ta cigaba da tafiya har ta cimma wata mota, saurayi da budurwa ne
a ciki, yana shafa gashin kanta a hankali, ita kuwa yarinyar sai wani nishi takeyi tana
murmushi, suna cikin haka ne sai sukaji kamar motarsu na tashi sama, anan suka leko ta
taga domin ganin abinda ke faruwa, kuwa suka farayi domin guguwa ce ta daga motar
sama, anan guguwar ta jijjiga motar, daga baya kuma ta makata ga katangar wani gida,
take wadanda ke cikinta sukace ga garinku, a haka wannan guguwa ta cigaba da keta
gidaje tana gudu, saurayi da budurwa ne a saman titi, sun rungume juna suna tafiya,
budurwar bata ankara ba sai jin tayi saurayinta na kuwa, anan taga guguwa ta daga shi
sama tana juyawa, akwai wani dogon mashi mai tsini soke a saman wani gida, take
guguwar ta jefa shi saman mashin, a nan ya fadi matacce jini na fita a bakinsa, ita kuwa
budurwar gudu ta fara yi tana neman taimako, a cikin wannan gudu ne guguwar ta
cimmata, daga nan ta tsaga kanta gida biyu, daga nan itama ta fadi ba rai.
A haka wannan guguwar ta ci gaba da tafiya har ta cimma wani matsakaicin gidan sama,
tsiri tayi sama da nufin shiga wata taga.
FARKON LABARIN
Meenat na cikin dakinta tana wasa da laptop, kawai sai taji iska na damunta, da sauri ta
tashi da nufin kulle tagar dakin, cikin rashin tsammani sai taga an dagata sama an jefata
saman gado, wata guguwa ce ta shigo dakin, anan ta fara zagayar gadon meenat, ita kuwa
meenat take jikinta ya dau rawa, ba a dauki lokaci ba sai guguwar ta nufi kasan bene, to a
wannan lokaci duk fitilar dake dakin ta mutu, anan meenat ta fara lalube, dakyar ta lalubo
madubin idonta "eyeglass"
Bayan ta sanya, anan ta tashi domin fita daga dakin, tafiya taji ana tako benen da nufin
shigowa dakinta, anan ta rasa abunda zatayi, cikin tsoro ta koma saman gado tana
makarkata, a haka ta cigaba dajin wannan tafiyar, ana cikin haka ne sai taji tsit, kamar an
daina tafiyar, daga nan sai ta tashi tana laluben kofar dakin, tana ciki haka ne sai taji an
banko kofar da karfi, wata fitilar hannu aka cinna mata ana kiran sunanta, MEENAT,
MEENAT, MEENAT, ke aunty ce ke magana, wai ina kike?
Meenat najin haka take ta sheko a guje ta rungume aunty balkisu, lafiya naga idanunki
sunyi ja?
lafiya lau aunty, meenat ta amsa,
A haka aunty ta jata suka yi kasan benen domin cin abincin dare "dinner"
Meenat na cikin wani hali, duk da dai ta boye abunda ke damunta a lokacin da aunty
balkisu ta tambayeta, wannan abun ban mamaki ba shine na farko ba a wurinta, tasha
ganin ire irensu tun tana karama, abunda ke daure mata kai shine batasan abunda yasa
hakan ke faruwa a gareta ba, gashi kuma bata taba gayawa kowa ba.
Ummi wai me kikeyi ne haka? duk kin bata mana wuri da abinci, aunty balkisu ta tsawata
mata, anan ummi ta done kai alamar jin kunya, suna cikin cin abincin, kawai sai sukaji an
bude kofar falon, ashe bafferh ne ya shigo, bafferh dai shine saurayin meenat, wannan
soyayya ta samo asali tun suna yara, saboda haka iyayensu sun san da hakan, kamar dai
kowane lokaci bafferh kan shigo gidan yayi abunda yakesko kamar gidansu.
Ummi ce ta tashi da sauri ta rungumeshi, to bayan ya kusanto, cikin girmamawa ya gaida
su, anan meenat ta masa wani kallo mai bayyana tsintsar so, haka ya mayar mata da
martani kafin ya zauna, wow, amma wannan abinci yayi dadi, inaga bako shakka gimbiyata
ce ta dafa shi!!! ya fada, anan meenat tayi murmushi tana kallonsa.
uhmm, aunty balkisu tayi kaki tana mai cewa, wace gimbiya kuma, gimbiyar taka dako
shayi bata iya hadawa ba, wannan magana tasa su dariya gabaki daya, haba aunty... inji
meenat, gaskiya nifa..... anan ta juya musu baya tana ciccika cikin fushi, bazan ma ci
abincin ba........ta fada.
anan aunty balkisu ta fara lallashinta, haba yan mata, wasa fa nakeyi, gimbiya uwar
gimbiyoyi, kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, to yi murmushi mana, anan meenat ta
dan yi murmushi saboda jin dadin wadannan kalamai, haka su kuma sauran mutanen gida
sai suka fara mata tabi da jinjina, anan gida ya kable da sowa.
Tun da safe tayi wani wanka, bayan kammala break fast sai ga bafferh ya shigo gidan,
cikin jin dadi suka nufi mota, bafferh ne ke tukawa, to anan hira ta barke tsakaninsu, yau
kasan munada "EDS 201" inji meenat, anan bafferh ya kalleta, banason wannan course din
ko kadan, ni in badan keba dayau ko makarantar bazanjeba, anan meenat tayi dariya tare
da gyran madubin idonta, haba to idan kace haka mu muce kaka? inji meenat, juyawa yayi
da nufun bata amsa, amma cikin sauri ya juya matukin motar, anan suka fara ihu shida
meenat, a tsakiyar manyan motoci suke, sannan ga wata mota a gabansu tana shirin afka
musu, cikin sauri ya kara giya yana kokarin fita tsakiyar motocin, wani irin gudu ne yake
naban mamaki, yana fita babbar motar na kawowa, cikin ilimi ya murza matukin motar yana
kaucewa, wannan bajinta da yayi taba meenat mamaki, anan ta fara yi masa tabi, yaushe
ka iya mota haka? murmushi yayi ba tare daya amsa ba, haka suka cigaba da tafiya har
suka iso makarantar, bayan sun faka motar, kai tsaye suka shiga aji.
Bayan awa biyu da kare lecture, kawai sai suka fito suka nufi gida, to a wannan lokacin
tare suke da kawar meenat wato nabilat, itace a bayan motar, sai surutu kawai take rafka
musu, a haka suka cigaba da tafiya har suka zo wurin dazasu ajeta, daga nan suka nufi
gida, tun daga bakin gate sukejin hayaniyar mutane a gidan, da sauri suka shiga domin
ganin ko me ke faruwa, ashe daddy ne ya dawo, cikin murna meenat ta fada jikinsa, ahaka
ya riketa sai kace karamar yarinya, to bayan sun natsu, sai ya fara tambayarsu ya
makarantar, daga nan suka fara bashi amsa da cewa lafiya lau.
A cikin wannan dare dai meenat ta kasa bacci, saboda haka sai ta shigo falo domin ta
sarara, anan taci karo da daddy yana ba aunty balkisu labari, a gefe guda kuma kaka
zuwaira ce a kishingide, gaskiya akwai matsala a wannan gari, inji daddy, hala meke
faruwa? kaka zuwaira ta tambaya, wato jiya mutum dari biyar suka mutu sakamakon wata
guguwa ta anoba data bayyana, anan ya gwada mata labarin rubuce a jarida, ga kuma
hotunan wadanda suka nan birjik, meenat najin daddy ya fadi wannan guguwa, take
hankalinta ya tashi, domin kai tsaye sai ta tuno da abinda ya faru da ita a baya na guguwa,
a lokacin data fara zagayar gadonta.
Kaka zuwaira ta nisa kafin daga bisani ta fara magana, ai kaine sanadin kome, kasa
daruruwan mutane cikin halaka, kuma ka cuci muhibbat, ALLAH zai isar mata.
Haba kaka, ya kina irin wannan magana, ai abunda ya wuce bai kamata ace kina tunashi
ba, tunda yanzu dai komi ya wuce.
Wannan magana tasa meenat cikin rudani, anan ta fara tunani wacece muhibbat? sannan
kuma da gaskene mahaifinta shine sanadin mutuwar mutuwar mutum dari biyar din da
guguwa ta halaka, to yaya akayi haka? meenat ta cigaba da wannan tunani har daga karshe
bacci yazo mata, saboda haka ta tashi ta nufi daki.
Cikin wani kwaroro take mai duhu, gudu take iyakar gudu, tamkar wani abu na binta, tana
cikin wannan gudu sai taci karo da wata mata, juyawa tayi da nufin komawa inda take,
daga nan sai matar ta mata magana, haba meenat, ya kina gudun mahaifiyarki, ai nice na
haife ki da cikina, daga nan sai matar tace ki shiga dakin mahaifinki,zaki ga wani akwati
baki boye, inaso ki dauko akwatin ki duba abinda ke ciki, daga nan sai ta nuna mata wata
hanya, idan kikabi wannan hanyar ba mai iya cutar dake.
Firgigit, meenat ta farka, wai ashe mafarki ne takeyi, wannan mafarki ya bata mamaki, anan
ta fara tunanin wacece mahaifiyarta ta gaskiya, domin ita a tunaninta, aunty balkisu ce
mahaifiyarta.
Bayan safiya ta waye, sai meenat ta wuce kai tsaye cikin dakin aunty balkisu, haka zaki
shigo ko sallama babu, wai yi hakuri aunty, meenat ta amsa, bayan sun fuskanci juna,
daga nan sai meenat ta fara magana, dama inaso in miki wasu tambayoyi ne, wai don
ALLAH me kika sani game da maganar da kaka zuwaira ta fada jiya? gama fadin haka keda
wuya sai taga hawaye sun zubo a idanunta, kiyi hakuri aunty, ban fadi wannan magana ba
da nufin bata miki rai.
Ai ba shi nakema kuka ba, sai dai ina tunanin wani abu daya daya faru shekaru da yawa,
wato ki sani meenat, wannan tambaya taki sirri ce, kuma mahaifinki bazai so in gaya miki
itaba, saboda haka kiyi hakuri, to aunty wai da gaske bake kika haife niba? injiwa, ni na
haifeki da cikina in baki sani baki sani, to wacece muhibbat? meenat ta kara tambaya, haba
meenat, wadannan tambayoyi sunyi yawa, ya kina haka, to kiyi hakuri aunty zan fita, daga
nan sai meenat ta fita daga dakin, ita kuwa aunty balkisu ta bita da kallo har ta bace.
To bayan meenat ta fita ne sai taji ana busa sarewa, juyowa tayi taga ko su waye, anan
taga bafferh tare da kawayenta suna mata tabi, HAPI BIRTHDAY MEENAT, a guje suka
sheko wurinta suna tayata murna, daga nan sai ga daddy ya shigo da wani katon cake,
cikin gaggawa aka bata yuka ta yanka, daga nan sai suka fara shagali da murna.
Bayan an gama wannan shagali kowa ya watse, sai daddy yayi kiran meenat domin ta gyara
masa daki, anan taji dadi domin zata bincika ta gani in mafarkinta gaskiya ne, a haka ta
shiga dakin tana bincike maimakon gyara, lungu lungu sako sako, cikin wannan kazamin
binciken ne ta gano wani akwati karami, cikin sauri takai akwatin dakinta, hakan ya
tabbatar mata da cewa mafarkinta gaskiya ne, a cikin wannan dare ta bude akwatin, ga
mamakinta sai taga littafi, da wani zobe, sai kuma wasu kayayyaki wadanda batasan kansu
ba, a makarin littafin an rubuta MUHIBBAT, daga nan sai ta bude ciki, hoton wani gida ne
ta gani mai ban tsoro, domin anyi hoton a ciki dare, sai kuma ga hoton daddy da wata
mata, sai kuma gata a tsakiyarsu a lokacin da tana yarinya, wadannan hotuna sun bata
mamaki, ko wane irin gida ne wannan, it kuma wannan matar ko wacece, daga nan sai ta
kara bude littafin, a nan taci karo da wani labari, amma abunda ke bata mamaki shine, tana
fara karatun labarin sai taga wutar dakin ta dauke gaba daya, da sauri da kulle littafin tana
lalube, kulle littafin keda wuya, sai taga wutar ta dawo, anan cigaba da karatu, kuma sai
taga wutar ta kara daukewa, tana kullewa kuma sai ta dawo, sau biyar tana haka, daga nan
sai ta gane cewa littafin bai karantuwa, sabida haka ta aje shi saida safe.
Tun da sanyin safiya ta buda littafin, amma mamaki ba kome a ciki, daga nan ta buga ma
bafferh, shi kuma ya bata shawara cewa suje wani wuri mai nisa su karanta littafin, to a
cikin dare suka shiga mota, anan sukayi tafiya mai nisa har suka shigo daji, daga nan sai
suka bude akwatin, a hankali suka dauko akwatin, sunna budewa sai suka ga rubutun
littafin ya dawo, anan suka fahimci cewa lalle wannan littafin sihiri ne, zasu fara karatun
littafin kenan kawai sai suka ga ya tashi sama kamar tsuntsu, anan suka fara binsa da
nufin rikeshi, amma gudu yake tamkar mai kafafu, haka wannan littafi ya ci gaba da jansu
har sukayi nisa cikin dajin, cikin wani kogo nai matsananin duhu littafin ya shiga, anan
sukayi cirko cirko domin suna jin tsoron shiga kogon, juyawa sukayi da karfi saboda wata
kara da suka ji, anan sukaci da karo da itacen dajin na tafiya, suna kokarin kawo musu
hari, sannan a cikin wannan kogon wani gurnani ke fitowa.
MEYE KARSHEN WANNAN LABARI?
ZAMU CIGABA...............

GIDAN FATALWA 2
kashi na biyu
Written by
abdul king article
TUNATARWA DAGA NA FARKO:
A cikin na farko mun tsaya a inda meenat da bafferh ke kokarin karatun littafin sihirin da
suka sato,...


Read / Download GIDAN FATALWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album