Join Our WhatsApp Group

TARTSATSIN WUTA Complete Hausa Novel Document by TARTSATSIN WUTA


TARTSATSIN WUTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31417



TARTSATSIN WUTA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 06, Apr 2023

Author: Aliyu Ishaq First Class ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : AREWA WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Horror novels

File Size: 179.54 kb

File Type: txt

Views: 1573+

Download: 491+

Last download: 1 day ago

Description/Story: ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI



A wani zamani chan baya mai tsaho daya shude acikin daular larabawa kafin zaminin sarki fir'auna anyi wani azzalumin sarki a birnin kisra mai suna dizlan ibn kailur

Sarki dizlan ya shahara a fagen zalunchi gashi jarumi na gaban kwatance mai dakawa maza gumba a hannu kuma yana karfin sihirin da masana tsafi a wannan lkacin suna tabbatar da baida sa a indai a fagen tsubbu ne sabida haka ma yakeji da kansa kuma ko wacce kasa dake makwabtaka dashi ke tsoronsa suke bashi duk abinda ya bukata sabida sun San ba kyau dan shi kadai yake fita yaki ya yaki kasa guda ya kashe sarkin su matansa kuma yayi musu fyade y kashesu ya Dora magajin Sa akai



Sarki dizlan yana da wata al ada daya indai ya kyalla idanu yaga kyakykyawar mace to fah koh ta halin kaka sai ya mata fyade ya kashe ta wannan dabi'ar Sa ce ta yiwa mata fyade


Sarki dizlan yana da matar aure guda daya mai suma sima wadda sukayi auren soyayya tunda aka daura aura aurensu sau uku sarki dizlan ya taba kusantarta sabida shi a ka idarsa indai ya gama da gu to baya mai maitawa sai akanta ne ma ya mai mai ta takai t kawo har ta fara Neman bayinta batare da saninsa ba take cin amanarsa ita a ganinta hakan shine zai fiye mata



Acikin bayin sarki dizlan akwai wani bawa daya aminta dashi sosae ya bashi dukkan yaddar sa ana kiransa da suna rakib


Rakib shine mai kula da bangaren gimbiya sima wat rana yaje yana gyara mata gado ta sai da ta fuskan ci ba kowa a a cikin turakarta ta sai ta bishi dakin ba tare da ya sani ba saijin karan rufe kofah yayi yana juyowa ya ganta tsaye ajikin kofar ta kowa tayi kamar wata wahainiya tazo ibda yake ta zauna a gefen gadon tare da kallonsa taga yadda jikin sa ke tsuma tayi murmushi tare da fadin

Kwantar da hankalinka ya kai rakib kasani ba abinda nazo dan nama sai dai wani taimako danake nema agunka cikin matukar mamaki rakib ya kalli gimbiya sima tare da fadin

Keko gimbiya wani irin taikoma kike so haka a guna da kike tunanin baxan iya biya miki shima to idan banyi ba ma meye amfanina kenan



Murmushi tayi sannan tace "rakib kasan dai duk  abinda ke faruwa a tsanina da mijina baya kula da shimfidata ba ruwansa da bukatata kai in takai ta maka ma yau shekara daya kenan da auren mu amma sau uku ya taba kusanta ta ni kuma gashi INA da karfin sha awa haka xan zauna nayi ta kukan bakin ciki dan BA yadda xan nasan indai nayiwa sarki mgn karshenta ya Sa akasheni kataimaka min rakib nasan yanxun kasan irin taimakon Dana ke bukata agunka


Cikin matukar tsoro ya kalli ta yace haba yake gimbiya kinko San abinda ki ke cewa nayi kuwa idan wannan abun ya fito fili bama ni ba tattaba kunnena ma ya shafesu dan a zuri'ar mu koh kuda bazai saura ba Ni dai INA mai rokon ki da kimin afuwan wannan abun da kike cewa na aikata



Kuka tasa masa tare sa nuna masa cewa idan baiyi abinda tasashiba zata iya rasa ranta a banza shikuma ya nuna mata bazai iya cin amanar sarki ba da taga dai dgsk yakeyi saita chanxa salo tare da share hawayen ta kuma saita tintsire da dariya kawai ta kalleshi tace



Tunda nabika ta lallami kaki yarda to bari kaji akwai barorin da suka ga shiga ta dakin nan kuma sun San kana ciki idan bakayi abinda nasaka ba narantse da gunki da muke bautawa saina maka Sharrin da koh tattaba kunnenka ma bazasu so suxo duniya ba



Cikin kaduwa ya tsaya yin tunanin mafita yasan duk abinda gimbiya sima ta fada sai ta aikata tunda ya zauna da ita a zuciyar sa yace da amin sharrin da banji ban gani ba kwara na aika laifin da hujja idan an kama ni ma shikenan



Aiko anan ya afka mata ya biya mata bukatar ta duka ta kawo makudan kudi ta bashi yayi gdy to fah tundaga nan suke sheke ayarsu ba tare da wani ya sani ba dan a yanxun ma sunyi wata biyar suna cin amanar sarki dizlan ba tare da sanin sa ba har yanxun


Daya daga cikin abinda Sarki dizlan bayaso a rayuwansa shine magaji dan yayi bincike ya gano cewa dan sa ne nan xai kashe shi ya hate karagar mulkin sa shiyisa gaba daya ya daina shiga sabgar gimbiya sima ma kwata kwata



Wata rana sarki dizlan ya taso daga fada zai tafi turakarsa kawai sai ya hango turakan gimbiya a bude koh INA haske ya baibaye gurin kawai sai ya nufi turakar tata kai tsaye ya shiga bata cikin turakan sai ya nufi dakin baccin ta a kwance shame shame ya ganta bacci tayi dai dai ji yayi wata sha awarta ta kama shi ya nufi inda take kai tsaye tana baccin taji kamar ana taba ta bude idanunta tayi a hankali ta saukesu akan mijin nata dayayi nisa ma kawai saita gyaleshi yayi duk abinda yakeso ya fita a dakin wannan shine babban kuskuren da sarki dizlan yayi a rayuwansa dan da San abinda zai faru da bazai kusanci gimbiya sima ba Ashe ita tasan  dauke da cikin bawa rakib a jikin ta kuma gashi sarki baya kula ta shiyisa tasa akayiwa sarki kiranye kuma yaxo ya kusanceta kinga kenan tunda cikin sati biyu ne to kawai yazama dan sarki dizlan kuma magajin sa wani shu umin murmushi tayi tare da cije lebe kawai said ta tuntsire da dariyan farin ciki..................


TAP DI JAM LALLEKUWA A WATA MASARAUTA ANAN AKE YINTA KUDAI MUJE ZUWA COMMENTS KAWAI NAKE BUKATA A GURIN KU READERS


by fast class
🏤🏤🏤🏤🏤🏤
      🏤 🏤🏤🏤🏤
            🏤🏤🏤🏤

TARSTSATSIN WUTA
(adventure story)
            🏤🏤🏤
     🏤🏤🏤🏤🏤
🏤🏤🏤🏤🏤🏤

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
   (fast class )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
page 5to10


Achan yamma da birnin kisra akwai wani karamin kauye mai suna hairil salad a wannan zamanin sarki uklan ne ke mulkin wannan birni 

Sarki uklan ya kasance adalin sarki sabanin sarki dizlan kuma shi baya takurawa talakawansa a fagen jarumta kuwa shima ba kanwar lasa bane dan akab wannan nahiyar sarki dizlan shi kadai yake tsoron gwabza fada dashi dan sun gwabza yafi a kirga saidai sarki dizlan ya kwaci Kansa da kyar kuma akab nahiyar sarki uklan ne kadai yake yin duk abinda yakeso ya kwana lpy dan koh haraji sai ya ga dama yake biya kuma ba abinda aka isa ama sa sarki dizlan yayi binchiken yadda zai yi ya samu nasara akan sa amma sai ya rika ganin ba mafita dan idan baiyi da gsk ba mana acikin birnin Wanda zai kasheshi zai rayu sarki uklan yana da matar aure guda daya mai suna nasmin

Gimbiya nasmin ta kasance kyakykyawa ta gaban kwatance wadda akab nahiyar da akayi bincike aka tabbar da duk nahiyar ba mai kyanta face gimbiya sima sabida wannan dalili gimbiya taji ta tsane ta a rayuwa burin ta taga randa zata mutu nasmin nada da guda daya Wanda shekarunsa bazasu wuce bakwai ba ya kasance kyakykyawa na gaban kwatan ce kuma gashi jarumin maxa dan tun yana dan yaro yake iya gwabza yaki da karti majiya karfi Biyar kuma ya kaisu kasa sarki uklan yasaka duk wani buri akan wannan da NASA mai suna Aryan dan wani lokacin idan yana bawa Aryan boron yaki sai ya suma kusan sau bakwai amma yna farfadowa za a dora haka al amarin ya rika kasancewa


             BIRNIN KISRA

Bayan wasu watanni achan birnin kisra kuwa ba abinda ya ragu saima Wanda ya dadu cin amana kuwa kullum sai anyita tsakanin bawa rakib da gimbiya sima bayan wasu watanni gimbiya ta kwanta wata yar karama rashin lpy inda litanta ta gwada ta tabbatar da shigar ciki na wata daya ajikin ta murna a gurin gimbiya ba a mgn shikuma sarki dizlan bakin ciki kamar ya kashe shi amma ba yadda zai yi dan bazai iya kashe ta va jama a zasuyi masa wani kallo amma yayi alkawarin cikin bazai zo duniya ba ko ta halin kaka sai ya lalata shi da karfin tsafi



Ita kuwa sima ganin wannan cikin ya bayyana yasa ta fara bin bokaye kala kala dan Neman tsari daga mijin ta a yawan NATA ne ta hadu da wani kasurgumin boka daya fito daga birnin sin yawan duniya ne ya kawo shi birnin kisra aiko kai tsaye ya nuna shima indai ta aminche dashi to koh me za ai sai cikin jikin ta yazo duniya ko da jin hakan sima ba tayi wata wata ba gurin amin cewa dashi yayi lalata da ita sannan ya bata wani garin magani yace indai har ta yi turaren maganin turakarta to da kuma jikin ta to ba wani aljani dazai rave ta haka bawani tsafi daya isa ya shiga jikin ta da kwarin guwarta ta karbi maganin t koma gida tayi yadda yace din


Aiko da dare sarki dizlan ya shiga cikin dakin tsafin s dan ya lalata cikin jikin matar tasa amma duk abinda zai yi hoton ta yaki bayyana akan mudubin tsafinsa yayi yayi har ya gaji yace bari dai na gwada na karshe aiko yana yi mudubin tsafin NASA ya tarwatse haka ya tashi da bakin ciki dan ya kuma tabbatar wa wannan cikin sai yazo duniya haka yayi fuska kamar ba abinda ya faru dashi ya ci gaba da harkokinsa yana kula da cikin yadda ya kamata a gefe daya kuma ga rakib da duk hankalinsa ya tashi dan yasan ba cikin sarki ne ajikin gimbiya ba na shine kuma uban gijin su ya Sa masa San wannan cikin amma yasan wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa haka yasa idanu  dan BA yadda zai yi amma yayi alkawarin kome zai faru saiya dauke abinda zata haifah babban kuakuren da sarki dizlan yayi shine bai zauna yayi binchiken yadda akai cikin yayi cikin da ace yayi wannan binchiken daya gano cin amanar da aka masa wannan kenan




Achan birnin hairil salad kuwa lokacin da sarki uklan ya samu lbrn cikin jikin gimbiya sima sai shiga dakin tsafin sa yayi binchike sosae akan cikin dan yasan dai sarki dizlan ya tsani haihuwa anan yaga abin da ya girgiza shi wato gimbiya sima zata haihu amma abinda zata haifah yana cikin ukubar sarki a gefe kuma ga bawa rakib da San cikin sa ya mamaye zukatansa gaba daya da sarki uklan ya tsanan ta bincike sai ya gano cewa alhakin kula da abinda matar sarki uklan zata haifah ya rataya ne akan dansa yarima Aryan nan da shekara goma sha takwas abinda gimbiya zata haifah y girma kuma a wannan lokacin Aryan yana kan mulkin birnin hairil salad shine kadai zai iya shiga birnin kisra ya dauko gimbiya sima da bawa rakib d abinda suka haifah bayan gama wannan binciken ne y gano akwai babbar rigima a cikin wanan nahiya tasu dan ya gano cewa duk abinda aka haifah zai taso da sarki dizlan kuma shine zai zama ajalinsa  kuma yasan sarki dizlan yasan da sannan batun tunda shima matsafine.......................


To fah ana wata ga wata kudai kubiyoni a cikin wannan book nawa mai suna TARTSATSIN WUTA

By fast class


🏤🏤🏤🏤🏤🏤
      🏤 🏤🏤🏤🏤
            🏤🏤🏤🏤

TARTSATSIN WUTA
(adventure story)
            🏤🏤🏤
     🏤🏤🏤🏤🏤
🏤🏤🏤🏤🏤🏤

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
   (fast class )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
page 10to15

Dedicated to
ANTI HAUWA
UMMU INTEESAR
UMMU AFFAN
LAURAT M BELLO
DR MARYAM
SHAM'LAD
HALIMATU
MAMAN KHALEL
ZEEY
JANNAT
ZAINAB L SALIS
NANA KHADEE and all member in arewa writer's association

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI

Haka sarki uklan ya karaci binciken Sa ya gama sannan tace"na rantse da gunkin da nake bautawa saina raini dana da dukkan karfina ta yadda zaije har birnin kisra ya dauko jaririn da gimbiya sima zata haifa tare da uban jaririn na dawo dasu birnina haka kuma ni da kaina zan ba abin da ta haifa horon yaki ta yadda zaije har cikin birnin ya kashe min sarki dizlan ka shirya yakai azzalumi indai ni ne saina ga bayan ka akan ya rika yiwa kansa kirari daga bisani ya tashi ya fito a dakin tsafin nasa kai tsaye turakar dansa yarima Aryan ya nufah bacci ya sameshi yana yi cikin kwanciyar hankali ba abin da ya sha masa kai murmushi sarki uklan yayi tare da fadin yaro kenan da kasan aikin dake gaban ka dabaka kwanta bacci ba yanxun kallon dan NASA yake yi yna murmushi daga bisani kuma sai ya fara hawayen tausayin dan nasa a fili yace ya kai Dana kasani ina jiye maka ranar da zakayi gaba da gaba da sarki dizlan dan indai har kuka hadu dole sai daya ya mutu koh kai koshi nidai koh bayan raina abinnan zai faru ina maka fatan narasa ya fadi haka tare da shafa sunar yarima Aryan dake bacci cikin kwanciyar hankali



Abinda sarki uklan bai sani ba shine Ashe yarima yaji shugowarsa cikin turakar tasa da har zai tashi kuma daya ji uban yana mgn sai ya fasa bayan fitar sarki daga cikin turakar ne ya tashi ya shiga tunani a zuciyar Sa yake cewa to Wai waye shi wannan sarki dizlan din nan ne me yake takama dashi da har abbana yake shakkarsa to ni Aryan nayi alkawari koh waye shi wannan sarki dizlan din saina ga bayan sa indai ina numfashi a duniya yana gama fadin hakan ya tashi ya cire kayan jiknsa gaba daya kuyan gi suka masa wanka suka Shafa masa mai aduk jikin sa wai zo kaga jikin jarumta gadon sadaukantaka yarima Aryan tun yana dan shekara bakwai din amma jikin sa ya murde jijiyoyi sun tashi sabida karban horon yaki kayan yakin sa ya saka ya fita filin motsa jiki sabida ya shirya kansa tun kafin haduwar sa da sarki dizlan sabida shi a yanxun na Wanda ya tsana a duniya sama dashi din wannan kenan



                  Birnin kisra



Bayan wata takwas a yaune cikin gimhiya sima ya isa haihuwa tunda duku dukun safiya birnin kisra ya rikice yayi duhu hadari ya gangamo kamar za a tsuge da ruwa sai tsawa ake kwala wa aljanu sai shawagi sukeyi a saman garin a wannan loakcin gimbiya sima na daki rai a hannun Allah kamar ta mutu zuwa wasu yan mintina aka kwala wata Uwar tsawa said jin kukan jari rai akayi ya cika birnin gaba dayansa kuma adai dai wannan lokacin aka tsuge da ruwa kamar da bakin kwarya wata tsowuwa ce ta fito daga gidan sarautar rike da jariran mace da namiji  masu matukar kyau...


Read / Download TARTSATSIN WUTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album