Join Our WhatsApp Group

SIRRINSU Complete Hausa Novel Document by SIRRINSU


SIRRINSU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 12898



SIRRINSU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 26, Jul 2023

Author: Maje El Hajeej Hotoro ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 75.21 kb

File Type: txt

Views: 698+

Download: 259+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: SIRRINSU
Littafin Maje el hajeej hotoro
Shekarar bugawa:- 1999
Ebook creator and design by:- Shuraih Usman
Publish by:- Shuraih 99%
.
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 1
By♥ Shuraih Usman
A
A
3~4~'99
. *_ASABAR_*
Maryam!A'isha! Sai yaushe ?"
Kawata banga jakata ba
"Faruk ! Banda kwacen budurwa"
Boss ! Muhade a tropicana
Ka-ce-na-ce, rudu da kuma hayaniyar dasuka ringa
tasowa daga bakunan dimbin mata da mazan dasuka
halarci filin wasan kwallon kafar, datafi kowace girma
da kayatuwa a Nigeria (sulere). Bayan antashi daga
wasan costarica da nigeria agasar cin kofin duniya na
matasa
Cikin halin hargowa da matsananciyar bugun zuciya
kamar ta faso kirjina don tsananin bugu da takeyi tun
da nake Arayuwata. Ban taba tsintar. Kaina ahalin
danake ciki awannan lokciba
Domin aranar na hadu da wacce na kirawo mutumce
, Aljana ce ko kuma fatalwa , bayan an tashi daga
wasan. Anan ne. Na wadata idanuwana da abubuwa
da dama. Shuraih Usman
Shugaban askarawan nigeria janar Abubakar
Abdulsalami da tawagarsa. Sune suka fara ficewa
daga filin wasan 'yan jaridu da ma'aikatan gida jen
sadarwa nata daukar hotunansu. "Shuraih
usman"Alokacin da wasu ke shirye-shiryen tafiya ,
wasu ke shirin zantawa da sababbin 'yan matan. Da
sukayi Turawa kuma na ta daukar hotuna. Sai
idanuwanta suka hasku ga kyakkyawar fuskarta
Farace doguwa mai matukar yalwar bakin gashi, ta
mallaki dara-daran fararen idanuwa kamar madara
,sannan tana da dirarriyar cikar halitta da kan dau
hankalin dukkan da na miji
Dogon hancinta harbaka da dan karamin bakinta na
daya daga cikin abubuwan da suka tona asirin
kyawunta kallo daya zaka yi mata ka gamsu cewar
duk daga inda tafito tahada dangi da shuwa
Ina ganinta sai da wani abu ya taso daga kafufuwana
,har zuwa cikin kwalkwalwata,wanda hakan yasa
jikina yayi yarrr! Na wasu lokuta sannan ganinta ya
jefa zuciyata a cikin wani irin da tun dana. Shaki iskar
duniya ban taba tsintar kaina. A wannan yana yiba.
Shuraih Usmanbawai ina nace ban taba ganin macen
data fi ta tsarin kyan halitta ba,ko tsarin iya sa kaya
ba.
Haka kawai ina ganinta na ji kamar akwai wani abu
gare dayake fizgeta zuwa wajenta .
Babu abin da yafi bani mamaki game da ita, irin duk
cikar dakin wasan da yayi , da zunzurutun kabilu
daban-daban , maza da mata daga kowane bangare
na nigeria , da kuma kasashen ketare kowa na farin
ciki da nishadi .Amma ita tana can gefe guda jin gine.
Jikin bakar marsandi,ta sunkuyar. Da kanta kas ,
kamar.duk al'ummar dake wajen bata san da su ba ,
bata kuma damu da Suba. Hayaniyar kuma da sukeyi
bata dameta ba.
Wanda wannan na nuni da cewar shakka babu tana
cikin matsananciyar. Da muwa arayuwarta .
Na dada yin matukar mamaki lokacin dana fahimci
duk taron samarin dake wajen babu wanda yakula da
kowa. Shuraih Usman
bakar kwat da siket dinta da ke sanye a jikinta ,sun
mata matukar kyau,da tayi kama da gimbiya LAILA.
Kyakkyawan takalmi ne mai launi uku PRINCE sanye a
kafarta.
Kai tsaye na nufi inda take gabana na faduwa , jikina
na rawa kamar mazari,kuma bansan dalilin hakanba .
Sai dai abinda bansaniba. Shine ,zuwa wajenta
danayi,shine ya jefa rayuwata cikin gagrumin tashin
hankali,kamar mutumin daya bude dakin dake cike da
mayunwatan kuraye bai sani ba.
"Hello".na fada ina murmushin karfin hali a tunanina
bata yi kama da wanda ke jin hausa ba. Har nayi
magana dago kanata ba.
"Yau wa sannu".Ga mamakina naji ta fada ,lokacin
data daga kanta ta kalleni ,sannan ta mayar da
hankalinta. Ga hannunta. Sannnan ne na fahimci ba
hannun take kallo ba ,wani kyakkyawan zare ne mai
launin ja, baki da kuma fari, dake hannunta .ni kaina
nayi mayukar sha'awar zaren.
"Zanyi matukar farinciki idan har zuwana wata
matsala arayuwarkiba "
"Kwarai kuwa , domin ni kaina na ji dadin zuwanka
,wanda zai debe min kewa dama nake nima "shuraih
usman"wannan maganar tafi bani mamaki, fiye da
zunzurutun kyanda ta mallaka , wanda ita kanta ta
fahimci hakan.
"Maganar tabaka mamaki ko?"
"Shakka babau, tun ba ma da ta fito dagga bakin
mace irinki ba " nafada ina kallon fuskarata.
"Kamar yaya mace irina ?"
Tunda ta kalleni sau daya har yanzu hankalinta.
Nakan kyakkyawan zaren dake hannunta.
"Kinsan mu maza mun gama yarda. Cewar duk inda
mace take bata kasancewa ita kadai "
" To yaya aka yi ka sameni ni kadai"
"Ni kaina nayi mamakin hakan ,yanzun ma na dauka
wani kike jira" zaka iya sauke abun daka dauka don ni
bana mu'amala da da namiji "
Na kalleta kallon da ita kanta ta fahimci ban yarada
da abin data fadaba ." Shuraih Usman
"na san bazaka yarda da. Abin dana fada ma ba
,nikaina. Ba'a son raina hakan ya kasance arayuwata
ba saidai don babu yadda zanyi"
"Yanzun nan fa kikace kin yi farinciki da zuwana
,daman wanda zai debemaki kewa kike nema ,kuma
kince ba kya mu'amala da namiji"•
Nafada ina mai kwadayin fahimtar abinda take nufi
,yayin da ita kuma tayi daya mayar da fuskarta ,fuskar
data dace data wacce ,wani abu ke kuntata rayuwarta.
"Babu abin dana fiso arayuwata irin hira da da
namiji,sai dai bani dawannan daman arayuwata
.kasancewar. Takunkumin alakakai , data gindayawa
rayuwata .
Yanzu haka daza ta ganni da kai sai na dandana
kudata ,bata son ganina da namiji kwata-kwata
arayuwata .
Abin yana damu na saidai don babu yadda zan yi ne "
Tana rufe bakinata hawaye suka fara zuba daga
idanuwanta .
Wanda ba karamin bani mamaki yayi ba .
"Wace ce ke takura maki ?"
Na tambaya cikin mamaki.
Kawai saita cigaba. Da kuka tana kallon zaren dake
hannunta .
"Wai shin yaya sunanki?
Ni sunana HABIB?"
"FARIDA"
Cikin shisshikar kuka ta fada
Sirrinsu
Littafi na daya
Chapter 2
By Shuraih Usman
.
Babu irin magiyar da banyi mata ba don tafada min
amsar wacce ke takura mata .Amma taki bani amsa .
Kawai takurawa zaren dake hannunta ido,kamar tana
mamakin ganinsa ahannunta
"Shin dama Farida ke mutuniyar legos ce?"
Na tambaya don canja hirar.
Gyada kanta tayi alamar a'a ce amsar tambayata .
"Daga ina kikazo"
"Kaduna"
"Wacce unguwa a kaduna "
"Tudun wada "
"So nake ki kwatan tamin gidanku"
*Shuraih Usman*"kana zuwa tu dun wada ,kusa da
makarantar marigayi sheikh Abubakar gumi,duk inda
katambaya gidan Alhaji adam za'akaika, shine gidana
uku"
Tun data fadi wadannan maganganu,bata kara cewa
komai ba,sai kawai tacigaba da kukanta ,ga
kyakkyawan zaren, kamar aranta yake sainaji. Ina son
mallakarsa.
Sai naciro zoben azurfa dake hannuna,wanda fatima
yayata tabani
"Farida"
Nakira sunanta lokacin dana mika mata zoben tadaga
kanta ta karba ta saka adan yatsanta na hagu.sannan
taci gaba da kallon zaren.
"Farida"ina son kema kibani zaren dake
hannunki,don tunawa dake kafin mukara haduwa"
Nasamu dogon lokaci ina tambayarta Amma in da
kasan dutse nakeyiwa magana.ko kallon inda nake
bata yiba, bata dakuma niyyar kara yin magana .
kwata-kwta hankalinta na kan zaren,ganinyadda ta
tatattara hankalinta ga zaren saina mika hannuna na
rike zaren.
Inda kasan aranta yake ,domin ina tabawa ta daga
kanta ,sannan tayi wani irin ajiyar zuciyar da sai da
na tsorata ,Amma dauk da haka ban saki ba.* Shuraih
Usman*.
"Mene ne haka ?"
Naji wata irin murya mara dadin ji tafada daga
bayana , cikin sauri na waiwaya a tsorace ganinta ya
dada jefa tsoro da fargaba azuciyata.
Kodaddiya ce mummuna gajeriya kuma kakkaura
,mai wasu irin jajayen idanuwa kamar garwashin
wuta .
Sannan ta mallaki faskeken kai, da burgujejen
hanci.tun dana dora idanuna afuskarta ,naji kwata-
kwata na tsane ta ,na kuma tsani ganinta da nakeyi .
Sai na ji bana bukatar hada ido da ita ,domin da zarar
na kalleta sai wani irin kunci yakai farmaki zuciyata .
Lokacin dana. Mayar da hankalina ga farida ,sai na
fuskanci har yanzu ta daga kanta sama ,idanunta
arufe jikinta na matukar tsima kamar tsohon dan
taurin da tsiminsa ya motsa .
Kuma na fahimci zuwan kodaddiyra matar ce ,kuma
nafahimci ita ne ke takura wa farida'kuma na fahimci
shakka babu tana matu kar tsoron matar .
Saidai abin daya bani mamaki mene ne hadin farida
da wannan mummunar matar dako ta ina basu dace
agansu tare ba ba?* Shuraih Usman*
A fusace kodaddiyar matar takama hannun
farida,cikin sauri tabude motar da farida ke jingine ta
tura ta ciki da karfi sannantayi min wani irin kallo da
ya dada tsoratani sannan taci taya da karfin daya
tayar da kura awajen .
Kamar fitan harsashi daga bindiga motar ta bace
daga harabar dakin wasan .
Abin kamar aikin sihiri , awannan ranar babu abinda
ke zuciyata .
Sai yawan tunaninta ,duk abinda nake yi
kwatsam,saita fado min a zuciyata .
Sai dai ba zan taba mantawa da haduwata da ita ba
,domin rikirtaccen abin daya faru arayuwata .nakasa
gane shin farida ,MUTUMCE KO ALJANA KO KUMA
FATALWA
Sirrinsu
Littafi na daya
Chapter 3
By Shuraih Usman
B
*_SIR.AHMADU BELLO STADIUM_*
,na cikinjerin kayattattun dakunan wasa dake najeria.
Shakka babu wannan haka yake. Na yarda da hakan
ne don halartar wasan ghana fa crotia.
Amma kwata-kwata hankalina baya na kan wasan da
ake bugawa yake ba, burina kawai ata shi natafi
tudun wada neman gidan su farida .* Shuraih
Usman*Tunda jirginmu yata so daga legos ya dira a
kaduna ,na so na bincika amma kasancewar Ahmad
mijin yayata wanda shine ke daukar dawainiyarmu ni
dashi, halartar wasanin da ake gudanarwa.
Yabukaceni dana rakashi ziyartar kayatattun hotels,da
wuraren hutu,da kuma barikin sojoji.
Ana tashi daga wasan ko komawa masaukinmu
banyiba ,kai tsaye na wuce unguwar tudun wada .
Sai dai kash ban san cewar zan gamu da gawurtaccen
al'amarin da zai birkita kwalkwalwata ba .
Shadda ce launin ruwan kwai,sanye a jikina.
Kamar yadda ta kwatanta min ban sha wahala wajen
gane gidansu ba.
Babban gidane dayake da bakar kofa,ankuma yi masa
shudin fenti.
Banyi minti daya da zuwa ba kofa tabude ,wata
kyakkyawar yarinya wacce suka yi matukar kama da
farida ,sanye da shudiyar doguwar riga tafito daga
gidan.
Rike da Naira hamsin guda uku ahannunta .
A yadda na fahimceta zata kai shekara goma
shadaya.* Shuraih Usman*
"Sannu"nafada bayan nakirawota .
"Yauwa sannu"
"Yaya gida?"
"Lafiya ta Amsa tana yimin kallon rashin sani.
"Ko don Allah nan ne gidansu Farida?"
Tayi shiru kamar tana mamkin tambayar ,kafin ta
amsa min da cewa nan ne"
'Ke kanwarta ce ?"
"Eh"
"Yaya sunanki?"
"Meenat"Ta fada har yanzu bakon kallon na fuskarta.
Ko don Allah ta dawo?"
"Wa?"Ita ma ta tambayeni cikin mamaki.
"Ina nufin farida"
"Daga ina ?"
Wannan karon mamakin yafi bayyana afuskarta.
"Jiya muka hadu da ita a lagos ,shine ta kwatan ta
min gidansu ,idan kika ce habib wanda suka hadu
........
Ni kaina na fahimci matukar razana ,data bayyana
karara a fuskar meenat, atunanina kodon farida ta ec
bata mu'amala da maza shine take mamakin zuwana
.Amma bata tsaya saurarar ragowar abin dazan
fadaba , sai * Shuraih Usman*ta ruga gida a guje
,kamar wacce kare ke niyyar cizo.
A lokacin da nake tunanin kokirawomin farida ta tafi
yi,sai kofa tabude wata mace sanye da fararen kaya ta
leko,da farko na dauka farida ce don kamaninta dana
gani.
Sai daga baya na sauke ashe mahaifiyarta ce.
Ta yi min wani irn kallon matukar mamakn kamar
yadda meenat tayi min,shin ko tana mamkin nine
saurayi na farko da na taba zuwa wajen 'yarta ?
A dai de lokacin dana nufi inda take don mu gaisa
,saitayi sauri arazane ta mayar da kofar ta rufe .
Haka kawai sai zuciyata ta fara matsananciyar bugu
,jikina yayi wani irin sanyi.har na yi niyyar tafiya ,sai
kofar ta kara budewa .
Wannan lokcin nayi tsammanin ganin kodaddiyar
matar nan,ga mamakina sai wani dogon saurayi fari
kimanin dan shekaru goma sha takwas .
Sanye dafarar singileti da shudin wando jeans yafito.
Tun kafin ya karaso inda nake nafahimci irin kallon
mamakin da meenat da mahaifiyarta kemin,shine
shima. Akan fuskarsa.* Shuraih Usman*"ko kaine ke
neman farida ?"Yatamabye ni bayan ya miko min
hannu mun gaisa.
"Shakka babu"nafada bagun zuciyata na karuwa.
"Kuma kace itace t kwatan ta maka nan gidan"
"Shakka babu"
"Jiya kuma kuka hadu?"
"Shakka babu"
Na kara mai maitawa ina mamakin tambayoyin.
"A Lagos kuma kuka hadu?"Ya tambayeni cikin
shakkar abin dana ke fada
"Shakka babu"
Yayi shiru yanayimin wani irn kallon mamki,kamar ni
ne mutum daya taba gani arawursa.
Nikaina kallon mamakin da yake min sai yasa na rika
yi masa kallon mamaki.
"Ba wani abune yasa nake maka wadannan
tambayoyiba , Shuraih Usman saboda agaskiya wani
irin. Rikitaccen al'amarine ka zo da shi.
Hakika nan ne gidan su farida,saidai ina mai tabbatar
ma faridan dake nan gidan ta dade da MUTUWA"
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 4
By Shuraih Usman
Cikin matukar mamaki idona yazzaro,bakina a bude
na kalleshi kallon da ya karyata Abin daya fada.
"Shakka babu,zuciyata bata amince da abin daka fada
ba.
Na rantse da wanda raina ke hannunsa jiya mun
hadu da farida a Lagos ,kuma ita ce ta kwatan ta min
nan gidan har na bata zobena .shin ba farida ce
doguwa fara mai yalwar gashi ba?
Ina ganin meenat nasan kanwarta ce ,don kamar da
sukayi"
Kallon mamakin dake fuskarsa yai hijira sannan
kallon akwai matsala a kwalkwata ya ziyarci fuskarsa.
"Dankari! Agaskiya kazo da babban magana ,domin
ita meenat daka tambaya har tanzu a tsorace take,a
tunaninta kai mahaukacine, tabbas tasan farida ta
mutu"
Wani dattijo yazo zai wuce yana jan tasbaha , biye
dashi wasu almajiraine su uku
"Alaramma! Wai kaga wannan ne bai yarda cewa
farida ta mutu ba "saurayin yafada lokacin da
wannan dattijo yazo gabda mu zai gifta.
"Kamar yaya bai yarda. Ta mutu ba ?"
Ya tambaya
"Malam anshakka babu jiya na hadu da farida a
Lagos ,kuma itace ta kwatantamin nan gidan"
Shi da almajiran Shuraih Usman suka kura min
ido,suna yi min kallon anya ban tabu ba.
A gaskiya sai dai kowata faridar,amma wace kenan
gidan ta dade da mutuwa kuma mata tace ta wanke
gawarta.
*******
Na yi shiru ina birkitaccen tunani lokacin da saurayin
yashiga gida.
Wasu yara suna gara taya,suka zo wucewa na tsayar
dasu.
"Kai don Allah anan unguwar kuke ?"
"Eh"suka amsa
"Ko kunsan Farida tanan gidan?"
"Mun santa amma ta dade da mutuwa"
Adaide wannan lokaci sai saurayin yafito ,rike da
kundin adana hotuna (album).
"Duba sosai kaga ko wata kagani mai kamar
Farida"ya fada lokacin dana fara buda kundin
hotunan.*Shuraih Usman*
"Shakka babu faridan dake jikin wadannan hotunan
ita ce Faridar data kwatanta min wannangidan,kuma
ita ce ta karbi zobena a Lagos,wannan ko shakka
babu"
Narika fada lokacin dana ke nuna hotunanta.
Kamar na fita daga hayyacina .
"Shinyaya sunanka malam"ya tambayeni.
"Habib"
"Nikuma Nasir"~ Anya habib ba mafarki kayi kunhadu
da ita ba?"
"Jiya an yi ball tsakanin Nigeria da Costrica a Lagos?"
"Tabbas" yafada.
To shakka babu jiya na hadu da farida a Lagos,kuma
ita ta kwatantamin nan gidan"
"To ai ni abin dake bani mamki shine babu abin da
yada farida da Lagos ko da tana da rai domin bamu
da kowa aLagos"
Ya. Zura hannunsa a aljihun wandonsa ya fito da
kundin rubuta muhimman al'amura ,don tunawa
gaba(Dairy)ya miko min bayan ya budo inda yake so
naduba* Shuraih Usman*
RANAR ALHAMIS 1-2-96,RANAR BAKIN CIKICE
GAREMU.RANAR DA FARIDA TA KOMA GA
MAHALLICCINTA,ALLAH YAJI KANTA,YAYI MATA
GAFARA DA RAHAMA.
Cikin matukar fargaba da mutuwar jiki kwalkwalwata
ta kasa tabuka komai,namika masa littafin.
"Don na kara gamsar da zuciyaka,Farida kwananta
biyu a hafsat private Hospital ta mutu,zamu iya zuwa
can don su kara yimaka bayani ko ka sami cikakkiyar
gamsuwa"
Ban yi masa musu ba muka nufi hafsat private
Hospital.
Mun samu likitan dogo siriri wankan tarwada,mai
gashin baki sanye da kayan aiki na likitoci a
jikinsa.mutum ne mai fara'a wanda yafi dacewa da
malami akan likita .
"Ka shai dani?"Nasir ya tambaye shi.
Bayan mungaisa
"Kwarai kuwa. Bakaine kanen farida. Wacce ta mutu
anan asibitin shekaru uku da suka wuce ba.
SIRRINSU
Littafina daya
Chapter 5
By Shuraih Usman
"Tabbas nine,dama don Allah muna bukatar shaidar
cewar anan ta mutu,fatan dai kuna ajiye irin
wadannan takardun?"
"Hakika muna ajiyewa ,domin dokar asibitin ce ,ku
danyi min hakri mintuna biyar,ina zuwa"
"Yafada lokacin yanufi wani daki
Shakka babu wannan al'amari haka yake,na duba
wadannan takardu kuma na gamsu,sai dai har yanzu
mamakin al'amarin ya sa kwalkwalwata ta birkice .
Na hadu da mace jiya ace ,yau shekarunta uku da
mutuwa?"
Har zan tafi sai yace na tsaya ya kirawo babarsu,don
ita ma ta tabbatar min cewar farida ta mutu.
Babu abin da ya kara ba ni mamaki ,irin matukar
kama da farida ta yi da mahaifiyarta ,
Kamar ka tsaga kara gida biyu.
Kundin adana hotunan da nasir ya kawo min,har
yanzu shine a hannunta.
Bayan mun gaisa ta miko min kundin adana hotunan
,tace na kara dubawa,ko dai wata faridar ce .
Bayan na duba na kara gamsuwa, sai na zari daya
daga cikin hotunan batare da sunsani ba.
Sanye take da doguwar bakar riga ,data yi matukar
dacewa da jar fatanta.
Tasaki yalwataccen gashinta ya zubo har gadon
bayanta,sannan tayi amintaccen murmushi dakan
dau hakalin kowane namiji.
Sannan na mika mata kundin adana hotunan* _
Shuraih Usman _ *
"Shakka babu, wacce ke jikin hotunan nan ,itace
faridar dana hadu da ita a Lagos.
Kuma iace ta kwatantamin nan gidan,kuma har
zobena nabata .
Wannan ko shakka babu na rantse da wanda ya aiko
Annabi dagaskiya ,duk abin dana fada gaskiyane"
Tayi shiru tana...


Read / Download SIRRINSU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album