Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

DAGA TAIMAKO Complete Hausa Novel Document by DAGA TAIMAKO


DAGA TAIMAKO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16874



DAGA TAIMAKO

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Oct 2023

Author: Sadnaf ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 94.27 kb

File Type: txt

Views: 1478+

Download: 444+

Last download: 1 day ago

Description/Story: [9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*





PAGE 1




Wata matashiyar buduruwa na hango a zaune akan tabarma,tana ta guga,dagani kayan mijinta take gogewa Muhibba kenan,wacce bata fi wata Biyar da aure ba,gidanta madaidaicin gida ne,dan wanda take aure ba mai k'arfi bane,Palo d'aya ne da d'akuna biyu,sai kitchen da toilet,Mijinta Abdulmajeed Mallamin Makarantar primary school ne,dai dai gwargwado suna cikin rufin asirin Allah,auren soyayya suka yi,Muhibba tana da kirki sosai ga kyauta,tsafta awajenta ba a magana,Dan inka shiga gidanta kamar karka fito sabida kamshi da tsafta da gidanta ke dashi,kayan mijinta data wanke take gogewa taji ana kwankwasa gidan,d'aga murya tayi tace "Waye"? Ji tayi an k'ara kwankwasa wa batare da anyi magana ba,mik'ewa tayi ta nufi k'ofar Dan taga wa ke kwankwasawa,doguwar Riga ce a jikinta tayi parking ba dankwalli akanta,daga bayan k'ofar ta Dan tsaya ta bud'e k'ofar tana leko da kai Dan taga waye, wani irin fad'uwa gabanta yayi jikinta ya d'au rawa sakamakon tozali da tayi da wata farar mata mai tsayi,idonta manya manya girmansu ya wuce misali,tsayinta ma yayi yawa, farinta wani irin d'aukar ido ya ringayi,gashin girar ta jajaye,haka ma leb'enta,murmushi wanan matar tayi mata tace"kiyi hakuri na zo na takuraki da kwankwasa k'ofa Dan Allah fitsari ne ya matseni shine nakeso ki taimaka min inyi dan bansan kowa anan ba," Muhibba tunda tafara magana gabanta ya tsananta fad'uwa ta kuma kasa addu'a dan matar yanayinta abar tsoro,Dan zata iya cewa tunda take ba ta tab'a ganin mai irin tsayinta ba,d'aurewa tayi tace cikin rawar baki " lah bakomai shigo kiyi" da sauri matar ta shiga ciki,ta tsaya atsakar gida,Muhibba kuwa kamar tabar gidan da gudu Dan wani irin tsoro ne ya rufeta,gashi tana so tayi addua ta kasa,d'aurewa tayi ta shiga tayi hanyar da band'akin yake tace mata "bismillah ga band'akin akwai ruwa aciki" gani tayi matar ta nufo ta kamar ba tafiya take ba turota ake, ware ido tayi tana kallonta cikin tsananin tsoro da tashin hankali,dasauri tabi k'afarta da kallo taga babu alamar k'afa illa ma doguwar Riga dake jikinta kawai dake Jan kasa,jikinta ne ya d'au rawa kafin tayi yunkurin yin wani Abu wuf matar ta shige band'aki ta rufo k'ofar,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun" muhibba tace cikin tsananin tsoro da fad'uwar gaba hanyar waje tayi da sauri taje ta tsaya daga bakin k'ofar tana kallon band'akin shiru shiru matan nan bata fito ba,tsoro ne ya k'ara rufe Muhibba ta d'aga murya tace " Baiwar Allah har yanzu baki gama ba" shiru taji,ba ayi magana ba,hakan ne yasa tayi waje da gudu ta nufi gidan dake kallon gidanta,gidan surayya makociyarta ce suna mutunci sosai da ita,bubuga gidan taringayi da sauri tana kallon gidanta,Surayya kin bud'e k'ofar tayi sai data ce "Muhibba kin tabbata kece"? " nice mana yi sauri ki bud'e min"bud'ewa Surayya tayi ahankali ta leko da kanta itama kana ganinta kasan a firgice take,da sauri Muhibba ta shige kafin tayi magana surayya tace " kema kinganta ko" ? Cikin tsananin tsoro Muhibba tace wacece"? Cikin sauri tace " bakiga wata farar mata mai kama da aljana ba,gidan nan tazo wai na taimaka mata fitsari takeji tuni na rufo k'ofata dan wlh baki ganta ba kamar ba mutum ba" tunda surayya tafara magana jikin Muhibba yafara rawa gabanta in banda fad'uwa babu abinda yakeyi d'aurewa tayi tace " Innalillahi wa inna ilahi rajiun Surayya na shiga uku na lalace,wlh tazo gidana tunda ta shiga band'aki taki fitowa har yanzu, nashiga ukuna D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO zan janyo wa kaina balai Dan Allah zoki rakani inga mai take yi a band'aki tunda zu,Wani irin tsalle surayya ta buga tayi gefe tace " wa tab bazan iya rakaki ba,wane tsautsayine ya kai ki kika barta ta shigar miki gida,wlh wanan da gani ba mutum bace Aljana ce," ai tun kafin Surayya ta rufe bakinta,Muhibba ta d'ora hannu aka taringa kuka tana ta shiga uku ta lalace " Yanzu surayya ya zanyi wlh tana cikin band'aki har yanzu bata fito ba," sallati Surayya tayi tasa hijabinta tace "muje in rakaki Allah yasa ba aljana bace.
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭





*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*





PAGE 2




Rik'e hanun juna sukayi suka nufi gidan gabansu in banda fad'uwa babu abinda yake,Dan Muhibba har wani gumi take,suna zuwa k'ofar gidan,Surayya tayi sauri ta koma bayan muhibba,muhibba ita kuma taja da baya da sauri ta juyo tana kallon surayya "Haba Dan Allah surayya mai yasa kike min haka ne ko bazaki rakani bane"? Muhibba tace cikin rawar baki dan kiris take jira ta zuba aguje sabida tsananin tsoro,Surayya cewa tayi " kijiki da wani zance in bazan rakaki ba zan biyoki ne,kawai dai tsoro nakeji dan wlh Matan nan dak'yar in ba aljana bace kinga tsayinta kuwa",katseta Muhibba tayi da sauri tana k'ara ja da baya tace "haba Surayya ya kike kuma tsoratamu Dan Allah muje ki rakani insha Allahu ba aljana bace,muyi addua kafin mushiga ciki," na yarda zamu shiga ciki amma ke zakiyi gaba in biki abaya, Surayya tace tana k'ara lab'ewa abayan Muhibba,hanunta Muhibba ta rik'e gam, suka fara adduoi sai sun je zasu shiga sai su dawo aguje,sai da sukayi haka sau uku ana hud'u Muhibba ta d'aure suka shiga gidan,a bakin k'ofa suka tsaya suna kallon band'akin,yana nan arufe kamar yanda yake,cikin tsananin tsoro Muhibba tace " baiwar Allah Dan Allah ki fito har yanzu baki gama bane karki cuceni D🅰G🅰 T🅰IM🅰KA miki" motsi suka jiyo daga band'akin sukayi waje dagudu,
Surayya kuwa cikin kiftawar ido ta shige gidanta tana k'ok'arin rufo k'ofa Muhibba ce tayi saurin shigewa tace " Surayya wai mai haka ne mai yasa
Kika gudu kika barni ai da kin tsaya munga fitowarta inkece kinsan bazan miki haka ba ko" d'aga wuya Surayya tayi tana kallo k'ofar gidan Muhibba tace "kiyi hak'uri Muhibba wlh tunda naga wanan matar na rasa nutsuwata,wlh wani irin tsoro nakeji kinga bari mu samu namiji ya shiga ya dubo mana ita" kuka Muhibba ta fashe dashi tana " innalillahi wa inna ilahi rajiun nashiga uku ni Ummi( sunan da iyayenta suke kiranta dashi) D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na janyowa kaina masifa," tsayuwar lifan a k'ofar gidan Surayyan ne ya katse mata maganar da takeyi,Ayuba mijin Surayya ne ya dawo,da sauri Surayya tayi waje ta gayawa Mijinta abinda ya faru sallati yayi ya kalli Muhibba dake tsaye abakin k'ofa tana ta kuka,tambayarta yayi yanda akayi,ta kuma bashi labarin abinda ya faru, addu'a yayi aransa yace su biyoshi abaya,tsoron da sukeji ya d'an ragu sakamakon sun samu mai taimaka musu,Muhibba tana daga bayansa Surayya kuma tana daga bayanta ahaka suka shiga gidan,Band'akin ta nuna mishi ya nufi band'akin yana addu'a su kuma suka tsaya daga bakin k'ofa suna kallon band'akin,in banda fad'uwa babu abinda gaban muhibba keyi,"Auzibikalimati tamaaa•••••• Ayuba ya karanta har karshe ya tura k'ofar ahankali tura k'ofar yayi gabad'aya yaga ba kowa,juyowa yayi ya kalli su Muhibba dake Neman sakin Fitsari a wando sabida tsananin tsoro,durk'ushewa tayi a lokacin data ga ba kowa a band'akin kuka ta fashe dashi tana nuna band'akin " Wlh Aljana ce ta shiga band'akin nan,ta ina ta fita,oooo ni Ummi D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na Janyo wa kaina" Mijin Surayya rufo k'ofar band'akin yayi,yayi hanyar waje, suka bishi dasauri,Dan Surayya har tayi gaba,Ayuba tsayawa yayi yacewa Muhibba "ki kwantar da hankalinki babu kowa a gidanki watak'ila ma idonki ne yake gane miki kinga wata ta shiga band'akinki" dasauri Surayya ta katse shi tana "Wlh Ayuba Aljanace Nima naganta da idona Dan gidana tafara zuwa,Ina ganinta na rufe k'ofata Dan wlh Baka ganta ba kana ganinta kasan ba mutum bace,bansan tsautsayin daya sa Muhibba ta barta ta shigar mata gida ba"jikin Ayuban ne yayi sanyi daya ji abinda Surayya tace, Muhibba kuwa ta k'ara rushewa da kuka tana " Allah yasani T🅰IM🅰KONT🅰 nayi bansan Aljana bace ni yanzu mai zancewa Abdul,gashi ya kusa dawowa ko girki ban d'ora ba" Ayuba kwantar mata da hankali yafa yi yana "karki damu muhibba ai Allah yaga zuciyarki T🅰IM🅰KO kika yi niyyar yi,Insha Allahu Allah bazai bata ikon cutar dake ba",juyawa yayi ya kalli Surayya dake zare ido yace mata "jeki rakata ta d'ora abincin lokaci na tafiya,", da sauri Surayya taja da baya "Ayuba wlh ni tsoro nakeji Dan baka ga matar bane" wani kallo ya watsa mata taja bakinta tayi shiru,"wuce ki rakata bana San shashanci ke kin isa ki ga aljana da idonki" "Nima fa ban d'ora girki ba" ...


Read / Download DAGA TAIMAKO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album