Join Our WhatsApp Group

AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA Complete Hausa Novel Document by AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA


AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 91193



AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 04, Apr 2023

Author: Malik Al Ashtar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Horror novels

File Size: 483.68 kb

File Type: txt

Views: 2219+

Download: 1393+

Last download: 3 days ago

Description/Story: Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

A wata ranar alhamis bakin gabar kogi... Yanayi ne mai dadi a wurin, sama tayi baƙi kamar za'a yi ruwa, ga iska mai daɗi dake kaɗawa, igiyoyin ruwan kogin kuwa sai yawo suke daga gabas zuwa yamma wanda hakan yasa suka bayar da yanayi mai ban sha'awa. Sai dai duk da wannan yanayi mai daɗi, Zahra dake bakin kogin, bai wani sauya ta daga halin da take ciki ba. A kullum tana jin kamar bata da wani amfani a wannan rayuwar, yanayi mai muni da take ji tun lokacin da ta fara zama cikakkiyar budurwa. Da fara girman Zahra, ɗabi'unta suka sauya daga Zahra kamar sauran ƴan mata zuwa Zahra miskila, ita ce kullum shuru-shuru, dariya na yi mata wahala, kullum kai ƙasa, ga tsoron yin magana a cikin mutane da tunanin idan tayi magana za'a ce tayi laifi, ga yawan bayar da haƙuri koda kuwa ita aka yiwa laifi. Sanin balagar kowanne yaro da yanda take zo masa yasa, iyayen ta da sauran dangin ta suka yi tunanin zata daina wata rana. Gashi har yau tana da shekaru 22, ta idar da karatun ta har tana aiki a wani kamfani a matsayin sakatariya, alhali tun tana yar ƙarama take da burin zama yar jarida. Sai dai mafarkin ta bai cika ba, dalilin ƙarancin yarda da kai dake gareta. A ranar tantance shiga makarantar aikin jarida, ƙin zuwa tayi, domin tasa a cen cikin ranta koda taje ba zata ci ba. Makarantar da take son yin karatun, tana ɗaya daga cikin manyan makaratun garin wacce kowa yake da burin ace gashi a cikin ta. Da tunanin mutanen da suka fita kwarewa a rubutu zasu iya kunyatata a wajen yasa taƙi zuwa. Wannan aikin ma da taimakon mahaifin ta ne ta same shi, kuma tana ganin idan dai zata samu albashin ta ko ya yake toh ya wadatar da ita.
A hankali take kai komo bakin kogin, tayi nitso sosai a cikin tunani...

“Baiwar Allah baki duban gaban ki ne idan kina tafiya?...”

Dawowa hayyacin ta tayi, anan ta fahimci ta buge wata mata. Kyakyawar matashiyar budurwa ce sosai, dan Zahara bata taba ganin mace mai kyawun wannan ba, domin har wani ƙyalli take kai kace ita kaɗai rana ke haskawa. Rikicewa Zahara tayi da ganin wannan kyawun, dan tuni ta siffanta kanta da biri a gaban wannan kyakyawar halitta. Matashiyar budurwar tana sanye da doguwar farar riga, duk da kazantar rigar bai wani rage ko kaɗan daga kyan wannan mata ba. Siririn hancin ta, manyan fararen idanun ta da ɗan karamin bakin ta, yasa Zahara taji zata iya ƙarashe rayuwar ta tana kallon wannan matar. Zahara ta shagala da kallon budurwar da har bata jin masifar da take mata na buge ta da tayi.

“Dan Allah.. kiyi..hakuri..” Zahara ta faɗa dakyar tare da sunkuyar da kai, domin ba zata iya jure mugun kallon da matar take mata ba.

“Ke kurma ce ko me? Baki ji nace miki ni na bugeki ba? Kina cen kin lula wata duniyar, ni kuwa ina tsaka da fama da kaɗaici na.” Matar tace wa Zahara cike da fahari yayin da take fadar maganar ta ta ƙarshe.

“Dan Allah kiyi hakuri..”

Fuskar matar cike da mamakin wannan sanyin hali ko sakarci na Zahara. Ta faɗa mata ita ce ta bangaje ta toh me yasa take bata hakuri? Ita fa da mutum take son yin magana ba wai da mahaukaci ba.

“Wai meke damun ki ne? Gaki dai a shiga ta kamala amma kamar ba a daidai kike ba.” Cewar matar da ƙara jin haushin halin Zahara. Ita ma kuwa Zahra ta kasa fahimtar dalilin da yasa wannan matar take son dole sai ta janyo mata matsala. Abinda kawai take so shi ne a shafa mata lafiya.

“Shikenan, naji tausayin ki, yanzu faɗa min meye sunan ki?”

Zahra cen cikin makoshi ta fadi sunan ta, hakan kuwa ya baiwa matar nan haushi.

“Kin san dai Allah ya tsaga miki baki ko, kuma dan kiyi magana yanda za'a ji ne.”

“Sunana Zahara Usman.” Zahara ta sake maimaitawa, wannan karon ta ɗan ɗaga murya yanda matar zata ji.

“Yauwa Zahara, meye matsalar ki ne?” Matar ta tambaye ta.

Mamaki ne ya kama Zahara, domin wannan tambayar ita ya kamata ta yiwa matar nan ganin yanda ta takura ta, amma tsoro ya hana ta dan tana gudun kar ta ɓatawa matar rai. Yanke shawarar ta bata amsa tayi dan tana son su rabu lafiya.

“Ba wata matsala dake gare ni, kawai ina son naje gida ne.” Cewar Zahara da ƴar karamar murya.

“Amma wasa kike ko? Kina son kije gida alhali nazo ne domin mu kulla kawance.” Matar ta fada tana wani zunce baki da ya saka Zahara yin dariya bata shirya ba.

Suna fuskantar juna ne, kogi a bayan su. Duk da tsoron da Zahara take ji, na kasancewa a sararin subhana tare da matar da bata sani ba har suna musayar zance, wani yanayi ne take ji da ta kasa tantance shi, wani lokacin sai taji a jikin ta kirkin wannan matar, wani lokacin kuma sai taji gabanta na faduwa, taji wannan matar ba alkhairi a tattare da ita kuma babban abun ma shi ne lokaci na kara tafiya, tunanin zuwa gida na fita a ranta.

“Sunana AMRIYA.” Cewar matar tare da yin wani ƙayataccen murmushi da yasa Zahara taji ta dan sake da matar. Eh dan sakewa, domin tana ji a jikinta wannan murmushi yana boye da abubuwa da dama marasa kyau.

Dariya sunan matar ya baiwa Zahara, amma bata bari matar ta gane ba. Kasa sanin me zata ce yasa ta yiwa matar murmushi kawai.

“Toh faɗa mini Zahara, me kika zo yi nan? Ina yawan ganin ki kina zuwa nan.” Cewar Amriya, hakan ya daurewa Fatima kai, domin duk zuwa da take bata taɓa ganin ta, gashi kuma bakin kogin ba wasu rumfuna, ba wani shamaki wanda zai sa ka ƙi ganin mutum koda kuwa na wasu yan kilomitoci ne, dan haka ta kasa fahimtar yanda aka yi basu taɗa haɗuwa ba. Kokarin kauda tunanin tayi, tare da yin yanda matar tayi, wato yin zaune a kan yashi tare da tanƙwashe ƙafafuwa.

“Ina samun salama idan nazo bakin kogin nan. Shi kaɗai ne wurin da idan nazo shi bana jin kewar son zuwa gida.” Zahara ta bata amsa bayan wasu yan dakiku da ta kwashe tana nazari.

“Eh, muna lura dake duk lokacin da kika zo.” Cewar Amriya tana kallon Zahara da ta nuna alamar tsoro a fuskar ta.

“Ke da su wa?” Zahara ta tambaye ta, tare da ƙarawa kanta shakku akan wannan matar.

“Manta kawai! Yanzu dai naji dadin haduwa dake. Bani da abokanai mata da yawa dama, kuma hakan baya mun dadi. Zahara ko zamu iya kulla kawance?”

Zahara cen cikin kanta taji tambayar kuma tafi mata kama da umarni akan roƙo, sai dai wannan karon ta yanke ba zata biyewa tunanin ta ba kuma ta amince da tayin ƙawancen da Amriya tayi mata. A ranta tace, kuma dama ba kawaye ba gare ni, wata kila wannan karon abubuwa su canza.

Mika hannun ta tayi ga na Amriya da ta miko mata, suka yi musabaha domin nuna sun zama ƙawaye. Zahara tunani take tunda sun zama ƙawaye, kamata yayi ta tambaye ta shekarun ta da kuma gidan su. Da wannan tunanin tace mata :
“Ina ne gidan ku?”

“Kinsan ɗan Dauda Hospital?”

“Ta Dr. Mustafa Dauda?” Zahara ta tambaye ta.

“Eh ita...”

“Ah ai kusa da gidan mu ne! Nasan wata Mami anan. Ko ita ce maman ki?”

“Eh kusan haka.”

“Abun da mamaki, ban taɓa ganin ki a cen ba. Ina yawan zuwa gidan, domin maman ki kawar mama ta ce. Tana yawan aike na gidan. Ko ke ba a gidan kike ba?”

Shuru Amriya tayi na kusan wasu yan mintuna, da alamar tana tunani kafin ta maido hankalin ta ga Zahara.

“Kin ga mu bar wannan maganar kawata.” Ta fada tare da mikewa tsaye. “Ni zan barki ki cigaba da hutawa, amma idan ni ce ke barin wurin nan zan yi tun yanzu. Domin wannan wurin ba inda ke da salama bane kamar yanda kike tunani, ba ma zaki iya kwatanta abubuwan dake faruwa anan ba. Da ni ce ba zan sake dawowa nan ba. Ni zan tafi, ki huta lafiya.” Cewar Amriya kafin tayi tafiyar ta.

Kamar kullum, bayanin sai da yayi latti kafin ya kai cikin kwanyar ta, tuni Amriya tayi nisa kafin Zahara tace wani abu. Miƙewa tayi ta shiga dube-duben inda zata ganin ta amma babu alamun ta. Zahara a ranta tace Amma matar nan taji sauri. Tana cikin bitar shawarar da sabuwar ƙawar tata ta bata, ba tare da lura da farin gyale mai kwalliyar fulawowi dake ta shawagi a kusa da ita. Ɗaukar shi tayi, a ranta tace duk yanda aka yi na Amriya ne ta manta. Lallai wannan haɗuwa tasu da ban al'ajabi take, domin bata taɓa haɗuwa da mutum mai ban mamaki irin Amriya ba. Mamaki.. wannan kalmar ce taji tayi daidai da kwatanta Amriya, har ma da haɗuwar su.

Komai ya dagule mata a ka, yanke shawarar idan taje gida zata yi tunani akan abinda ya faru yanzu, amma yanzun zata biya ta gidan su Amriya ta kai mata gyalen ta.

Tafiya take tana sauri, domin tuni gari ya fara duhu. Bata lura da lokaci yaja har haka ba, duk kwanar data shiga sai ta dinga waiwaye taga ko wani bai biyo ta ba. Duk da dama cen matsoraciya ce ita, amma kalaman Amriya sun ƙara mata wani tsoron, domin har yanzu su suke mata yawo a kai. Tunani tayi, ko dama cen akwai wasu masu haƙon ta da kullum suke ganin ta tana zuwa bakin kogi, suna jiran su samu dama suyi mata wani abun. Cikin ikon Allah, ta ƙaraso kofar gidan MAMI, mahaifiyar Amriya. Bubbuga gidan tayi sannan ta jira a buɗe mata. Bayan wasu ƴan mintuna sai ga MAMI tazo ta bude. Ita kuwa Zahara taso ace Amriya ce dan ta miƙa mata gyalen, ta ƙarasa gida.

“Ah ƴata ce, shigo kin tsaya daga waje.” Cewar MAMI tana mai sakarwa Zahara hanya domin ta wuce.

“Ina wuni Aunty?” Zahara ta gaishe ta da ƴar siririyar murya, kamar kullum kai a ƙasa.

“Lafiya ƙalau ƴata, ba zaki shigo ba? Ina maman ki tana nan lafiya?”

“Lafiya ƙalau take, a'a ba sai na shigo ba Aunty sauri nake, daman na biyo ne na bawa Amriya gyalen ta.” Zahara ta bata amsa tana mai miƙa mata gyalen, sai dai ganin matar bata da niyyar ƙarba yasa, Zahara ta ɗago kai, nan ta lura yanayin ƙawar mahaifiyar ta ya sauya. Fuskarta ta sauya zuwa damuwa, idanun ta sun wani fito waje, baki buɗe. Zahara bata fahimci komai ba, amma taji a jikin ta akwai abinda ba daidai ba. Idan har Zahara tana cikin mamaki, toh wannan matar ta ninka ta.

“A..a..ina kika samu wannan?” Da i'i'na Mami tayi mata wannan tambayar, tana kokarin amsar gyalen amma hannuwan ta dake rawa sun kasa.

“Ƴar ki ce Amriya ta yar dashi bakin kogi, shi ne nazo na kawo mata. Me yake faruwa ne?” Zahara tayi ƙarfin halin tambayar ta, da duk tsoro ya kama ta na ganin yanayin da Mami ta shiga.

“Ta yaya hakan zai yiwu, wannan gyalen ƴata ce Aisha! Kuma ta rasu a hatsarin mota lokacin tana da shekaru 17 kuma ni bani da ƴa mai suna Amriya. Wanne zance ne wannan ƴata?”

Zahara ta rasa me zata ce. Damuwa taji a cikin muryar matar nan da ta kara mata mugun tsoro. meke faruwa kenan?

“Amma.. Ita tace min anan gidan take, ni ban gane ba..” Cewar Zahara da ta iya baiwa Mami amsa da ƙyar.

“Ni ƴa daya gare ni, kuma sunan ta Aisha. Ni na siyo mata wannan gyalen, kuma ni na saka mata wannan fulawowin da kaina... Innalillahi me yake shirin faruwa ne?” Mami Ta faɗa tana toshe bakin ta, ganin kuka na shirin kubce mata.

Ita kuwa Zahara tuni ido sun rena fata, kamar wacce ma ruhi ya bar jikin ta. Nan take kwalwar ta ta fara tuno mata da littafan ban tsoro da take karantawa, masu kama da irin wannan yanayin da ta shiga. Tambayar kanta take ko dai mummunan mafarki ne take, amma hannuwan Mami dake rike da nata sun tabbatar mata da idon ta biyu. Mami ce ta kama hannun Zahara ta jata da ƙarfi zuwa cikin gidan. Zahara tayi kokarin ƙwatar kanta amma da yake ba za'a haɗa karfin ta da na Mami yasa ta kasa. Numfashi daƙyar take yin sa, daga karshe da kokawa da komai, Mami tayi nasarar shigar da ita cikin wani daki dake cen cikin corridor falon gidan. Da shigar su Mami ta sake ta, tare da nufar drawer ta buɗe ta ɗauko wani hoto. Sai da ta ɗauki lokaci tana shafa hoton tana kuka, kafin ta mikowa Zahara shi da ta fita rikicewa dan tsoro. Zahara ji tayi ƙasa ta kasa ɗaukan ta, bugun zuciyar ta ya ƙaru.

Amriya ta gani kan hoton cikin farar rigarta wadda take sanye da ita ɗazun a bakin kogi da kuma gyalen da ta manta rataye a wuyan ta. Da sauri ta saki hoton ya faɗi kasa, ta fita da gudu daga gidan a rikice.

______________________________________

Kafin na cigaba naga comments idan kun ga alamun labarin zai yi dadi.


AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 1


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

Rufe idanu Zahara ta sake yi da sa ran ko zata samu yin bacci sai dai da ta tuna fuskar matar nan sai baccin ya gagare ta. Ji take duk inda ta duba ita take gani, tana bibiyar ta duk inda tayi, har ma a cikin mafarkan ta.

Sake juyi tayi ta canza kwanci bisa gadon, wannan karon zura kanta tayi a karkashin pillow, numfashi dakyar take yin sa, amma tafi gwammacewa yin hakan idan dai har ta samu yin bacci. Kokarin yin baccin tayi karo na barkatai, amma sai kwalwar ta shigo nuno mata hoton abinda ya faru kwana biyu da suka wuce. A yammacin nan da ta fita da gudu daga gidan MAMI, bata ma samu lokacin tsayawa gaishe da fuskokin sani da tayi ta haduwa dasu a hanya ba kamar yanda ta saba yi. Ita kawai a lokacin ba abinda take so kamar ta ganta a gida, kamar gidan shi zai mata maganin mummunan mafarkin ido biyun da take yi. Abin ma dariya wani lokacin yake bata, wai ita da da take guduwa daga gida domin ta kan ji kamar an takure ta. Amma gashi a ranar ba inda take ganin ya fiye mata tsaro irin gida. Tafiya-tafiya sauri-sauri take dan kar ta jawo hankalin mutane, amma ji take kamar idanun kowa a kanta suke.

Lokacin da ta samu ta isa gida, ta...


Read / Download AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

12 months ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album