Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

RUHI BIYU Complete Hausa Novel Document by RUHI BIYU


RUHI BIYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 19463RUHI BIYU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 04, Aug 2023

Author: Fateema Rabiu ,Khadija Kanwar Soja ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Royal Star

Author Phone : 08130479973, 08101235739

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 112 kb

File Type: txt

Views: 1064+

Download: 312+

Last download: 4 days ago

Description/Story: *☠️💀 RUHI BIYU☠️💀*
*Littafin had'aka*💪


MALLAKIN
*©Fateemah Rabi'u (ZAHRA R noOYAL STAR)*
&
*K'ANWAR SOJA*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*
PAGE 1️⃣➡️2️⃣


__________________✍️ Wani daji ne mai cike da yawan shuke-shuke da yalwar iska dajin cike yake da firanne masu kyan gaske, yanayin dajin sai ki rantske kice ba kowa a cikin k'arar motoci naji da sauri na waiga bayana dan na shagala da kallon dajin,


Da sauri na idasa inda wannan motocin suka tsaya dan in d'akko muku rahoto,
Wasu gidaje ne guda biyu a cikin dajin duk girman dajin kuwa masu matuk'ar kyawu yanayin gidajan sak irin na turawa,


Ahali ne guda suke sakkowa daga motocin tare da kayan su nik'e-nik'e suke d'aukar kayan tare suke da ma'aikatansu daga alama sabon gidane zasu tare gidan dake kallonsu suka nufa daga alama shine nasu, na kusa dasu kuwa dana waiga na kalli gidan da alama akwai wasu a ciki,
Daka kallesu kasan family ne guda dan kuwa a hankali suke fitowa daga motocin wani d'an dattijo ne ya fara fitowa sai wata y'ar tsohowa da alama basai ka tabbaya ba matarsa ce wani babban mutum ne yake fitowa shima sai matarsa sai yara guda biyu,


Da sauri y'ar yarinyar da bazata wuce shekara biyar 5 ba ke fitowa daga motar da d'an gudunta ta nufi yayarta ita kumah wadda zata kai Shekara sha takwas 18 zuwa tayi tana tsalle tana cewa "Aunty SAMIRA kinga gidan da Daddy ya siya mana mai kyau", tana fad'a cike da farin-ciki ita kuwa Samira d'an tsaki taja dan kwata-kwata gidan bai kwanta mata ba,
Da gudu yarinyar zata nufi cikin gidan matar daga alama mahaifiyarsu ce tayi saurin jawota tana cewa "ke ILIHAM ban hanaki guje-gujen Nan ba eyeee?", Cikin turo baki yarinyar tace"Mommy shigafa zanyi gidan yayi kyau", cike da yarinyata yarinyar ta idasa maganar,
Girgiza kanta kawai Mommy tayi tana d'aga kai tana kallon gidan time guda gabanta ya hanke ya fad'i itama dai na Samirar gidan saida sukazo kwata-kwata taji baiyi mata ba da yanayin wajan kansa ace ba gidaje koh d'aya amma ba yadda ta iya dan kuwa uwar mijinta wadda suke kira da INNEE tace ko zata mutu saifa d'anta ya tare a gidan danta lura wai bakin ciki take d'anta zai sake gida na gani na fad'a,


Dan girgiza ta Samira tayi tace "Mommy mu shiga koh", Innee dataji mi suke cewa tayi karam wajan cewa "yo karma ku shugo yara da uwarsu sai iyayin tsiya ga gida mai kyau da tsari da.... Kamin ta idasa Kaka wadda ya kasance mijinta ya katseta da cewa "kedai Aysha bazaki daina wannan sharmen ba wuce muje", ya nuna mata hanya ba yadda ta iya tayi shuru,
Rank'ayawa sukai gaba d'aya d'an kuwa Mommy k'ala batace ba danta lura yau Innee jan magana take shiga sukai gidane na gani na fad'a gidane babban gaske wadda kwata-kwata ginin ba irin namu bane k'ofa ce babba daga waje wadda daka shiga gidan k'aton falo zaka tarar wadda cike yake da kayan k'awa falon k'aton gaske ne wadda aka jera gujeru kala har uku saiya kasance kamar anyi falo uku ne sai wani k'aton dining table wadda sai yace mutum bakwai sai Kitchen wadda yake a bud'e kamar dai na turawa wadda yaji kayan buk'ata sai wata dogowar hanya ita kuma d'akona ne jire wajan guda takwas wadda suke cike da kayan k'awa babu abinda babu gidan wadda bayan gidan akwai k'aton lambu,


Kai komai dai na gidan da yanayin dajin sunyi matuk'ar kyawu amma yanayin dajin da kansa gidan saiya baka tsoro irin tsarin gidan da girmansa
Bayan sun zauna inda Mommy ta zab'arma Samira da Iliham d'aki d'aya dantace bazata rabasu ba dan kwata gidan tsoro yake bata sai Kaka da Innee d'aki d'aya sai ita da Daddy dan kuwa koh rabin d'ako nan basu cika ba sai y'an aikinsu guda biyu wadda suma akwai nasu d'akin,
Saida suka gama kimtsa gidan suka tsamtace sa sana suka zauna suna tattaunawa akan Daddy zai shirya wani shagali murnar tarewa, suna tattaunawa Iliham tazo da gudu ta fita da sauri Mommy ta kira Samira tace "ke bimin yarinyar can wllhy saina kyara mata zama ne", da sauri Innee ta amshe da cewa "wllhy ba wadda ya isa ya bigar min jika haka kurum yarinya a barta ta sake mana", ta idasa tana mai juya idanunta irin na tsofa Mommy dai bata ce komai ba illa d'an murmushi da tayi Daddy ma d'an girgiza kai kawai yayi ya tashi dan yau da daddare za'a shagalin,
Samira ce tabi Iliham da sauri dan taga ta nufi wannan d'ayan gidan wadda yake kallon nasu, yarinyar kuwa harta isa ta danna k'araurawar gidan da sauri Samira ta bige mata hannu tana cewa "wai ke dai bakiji koh?", Zata sake wata maganar aka bud'e gidan,


Wani matashin saurayine wadda bazai wuce shekara 30 koh fiye da haka kyakkyawan gaske ne kamar bature da sajansa wadda ya zagaye fuskarsa wadda saiya k'arawa fuskar tasa kyau da kwarjini da haiba murmushi ya sakar masu mai kyan gaske kamin yayi magana wata matashiyar budurwar ta fito itama mai kyau da ita da sauri ta kalli yaran da time guda suka birgeta tace "ya zaku tsaya waje ku shugo mana", da sauri Samira tace "a'a Aunty wllhy kinga yarinyar danazo Kira nan", da sauri Iliham tace "Aunty Samira abu nane ina halbawa shine ya fad'o gidan fa", ta idasa tana turo baki,


Da sauri Matar tace "haba ku shugo mana ba kune kuka tare ba yau? ku shugo sai a bata koh", d'aukar Iliham tayi tace"ya sunanki?", Da sauri Iliham tace "Iliham", matar tace "Wow Masha Allah",


Shugowa sukai gidan shima kamar dai tsarin nasu Iliham dan dai nasu Iliham yafi girma, mijinta ya kira sunan ta yace "Bilkisu kirana son yara gaskiya", murmushi tayi dan kuwa Allah bai tab'a basu ba duk da basu wani dad'e da yin auran ba amma kam tana son yara kodan yanayin wajan da suke mijin mai suna Aminullah tace "bari na d'akko miki abin wasanki tashi tayi ta d'akko har abin taba baki sadda zata dawo sunata labari da Aminullah dan shima akwai saurin sabo da kyar ta samo suka d'an taba abinda ta kawo tashi Samira tayi tana yabawa da mutumcin wannan mutane tace "Aunty zamu wuce amma dan Allah zuwa anjima da daddare za'ai shagalin tarewarmu ina gayyatar ku please", da sauri Bilkisu tace "inshallah zamu zo" cike da farin-ciki suka bar gidan


DARE
Shirye suke ko ina na dajin ya d'au haske waddae a wasu mutane suka gayyata ba y'an tsiraro ne a inda Bilkisu da mijin ta Aminullah suma sun halacci taron Samira ta gabatar dasu ga Mommy tarbarsu tayi cike da mutumtawa shagalin ya k'ayatar sosai,


Zaune Samira take tayi nesa da wajan mutane kanta a k'asa kamar ance ta tashi ta tashi zunbur ta fara tafiya ta dushi wata rijiya dake kusa da gidansu dai-dai kan rijiyar ta tsaya kanta a k'asa, kamar ance ma Aminullah kalli can ya hango ta da sauri ya tashi yana kiranta daga nesa amma ina bata waigo ba bare yasa ran amsawa ya kusa k'arasowa wajanta ya kirata da k'arfi waigowa tayi da kanta da saurin da ya fi k'arfin tunanin d'an Adam yayi arba da fuskarta idonta ya rine ya kuma bak'ikkirin gaba d'ayansa ga wani ruwan hawaye baki na zuba a kuncinta wata irin dariya ta b'ab'b'ak'e da ita gaba d'aya dajin ya amsa wadda hankali jama'an ya dawo kanso Aminullah kuwa da yayi mutuwar tsaya kamin yayi aune ta tafi ta fad'a rijiyar a yanayin yadda ta fad'a rijiyar da saurin daya wuce misali daka kalla kae kasan badae mutum ba,
Da sauri Innee ta d'ora hannu a kai ta fashe da kuka tana cewa "wayyo jikanyata innalillahi yaune naga tsiya ba wadda zai iya taimakonta ne?", Ta idasa maganar ta zazzare idanu Mommy kuwa da Daddy da Kaka ba abinda suke sai an baton Allah wadda Mommy da Iliham hawaye duk sun wanke masu fuska,
Kamin suyi aune Aminullah ya fad'a cikin rijiyar dan ceton ta Bilkisu kuwa zuciyar ta ce ta tsinke runtse idanuwanta tayi, a cikin rijiyar kuwa baisha wahala dan kuwa ya iya ruwa nemanta yake a cikin ruwan can ya hango ta ta juya baya da sauri ya nufi wajan dafa yayi ya juyo da ita da sauri ya saketa zuciyarsa na tayi wata mahaukaciyar bugawa saka makon tozali da yayi da fuskarta tayi jage-jage da jini ga wasu idanuwa yanzu sun koma fari gaba d'ayan su da sauri kuma ya k'ara koma ya tallafo ta sai dai abinda ya k'ara bashi mamaki da tsoro yanzu fuskarta normal ba wani abu a kanta, kauda tunanin yayi ya fito da ita a sume da sauri Daddy ya kinkime sai cikin...


Read / Download RUHI BIYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album