Join Our WhatsApp Group

AL HUBB Complete Hausa Novel Document by AL HUBB


AL HUBB

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 75066



AL HUBB

Reading Time: 6 Hours

Added On: 29, Jul 2023

Author: Aisha B Naseer ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 405.59 kb

File Type: txt

Views: 1207+

Download: 712+

Last download: 3 days ago

Description/Story: 💍 *AL_HUBB* 💍
The love💘

By Aysha b. Naseer

Episode 01: ASSIDDIQUE RESIDENCE

Bismillahir Rahmanir rahim
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala daya bani ikon fara wannan littapi ubangiji Allah yasa mu karu mu amfana da darusan dake ciki ya yafe kurakurai..


Its another bright saturday weekend dukda ma a gurinta ba weekend din bane, tunda har saturday ma setaje aikin, tana jin dadin aikin ko ba komai yana dauke mata kewar zama cikin wannan tangameman gidan da sam babu dadin zama ba kuma dan babu ba sai dan yawan yayi mishi yawa, ga rashin Albarkar mutane,
Satinta daya ne kadai yanxu da zuwa,
Ta janye hijab din dake kanta ta miqe daga kan dardumar da tun sallar asubahi take kai tana jero bukatunta gurin wanda shi kadae tasan ze biya mata su, a hankali ta karasa bakin mirror ta kalli kanta, yes yau ne kadai ta yarda ta rame tunda taji ana cewa ta rame din, tai azamar juyawa mirror din baya saboda ruwan hawaye dataji sun soma taruwa a idanunta, hakan ya baiwa idanunta damar sauka kan tamfatsetsen zanen frame din na fuskarta, tai azamar shiga bandakin dake cikin dakin, mintina 30 suka isheta gama shiryawa, a hankali ta tura kofar bedroom dinta, ya sadata da corridor din dakuna, sannan ta karasa fita sarari kafin wani tangamemen falour ya bayyana a idanunta, da farko kafin tazo gidan ta ayyana dole dama ze zama super unique amma datazo se taga gabadaya an karar da tunaninta, babu abinda ya hana ta zama er kauye a lokacin, ta sauke numfashi ta gangara kasan benen dashi kanshi ya isa abin kallo, (picture din falourn is on wattpad)
Motar da aka ajiye domin kaita gurin aiki ta shiga already driver na jiranta, ta lumshe ido tana jin sanyin A.C na ratsata, a hankali take rewinding abubuwan da suka faru cikin kankanin lokacin komi ya sauya
Gama jami'arta, Auren minnatullahi, barin gidan Anty siyama zuwa nan Abuja gidan As_siddique, fara service dinta,
She recalled the day she was posted to camp in Abuja, she was confused, tasan battada kowa a Abuja, ta fadawa dai Abbah jabir da Anty siyama inda akae posting dinta, haka ta tattara ta tapi dan tama mance a nan Abuja minnatullahi take aure, sae bayan sun kusa gama camping tana shirin relocating kawai Anty siyama ta kirata tace kar tayi relocating ta zauna nan *gidan As_siddique* ...
Wani katon mall driver ya karasa da ita, it was beyond expectation of a mall, yayi girma, a yadda a ke fadi ma shine the first biggest mall cikin garin Abuja babu kamarshi,
Har kofar inda zata shiga driver yyi parking ta fita batareda ko hasken rana ta tabata ba,
Mall ne mai different shops and places, cikin wani hadadden gurin cin abinci ta shiga, wani kamshi mai saka kasala ya ratsa ta, bata tsaya ko ina ba ta wuce direct inda nata aikin yake, duka anyi desserts din safiyar, ita daya ake jira tazo tai tasting,
Tayi sterilizing hannunta dukda a tsaftace suke, sannan ta fara da samosa, sau daya ta tauna ta zubar, angrily ta kalli chef din da yayi girkin ta nuna mishi barin hannun damanta, ya ja tray dinshi ya koma,
Sai tea cikin transparent disposable, ta karba tayi sipping shima din bata karasa hadiya ba ta zubar rai a bace,
Gabadaya 11 dishes din da suka kawo saida tayi disqualifying 10 dishes, sandwich ne kawai yayi shima yana buqatar ingredients to look more enticing and stimulating... Thats about *zainab* she loves to cook its in her blood..

Meeting na kusan 1hr sukai itada manager din data tarar a gurin sanda tazo wanda ke kula da restuarant din(SALEEM), atlast suka karkare kan zasu rufe gurin for some few weeks, a weeks din kuma zatayi training cooks din...
A ranar akayi shutting down restaurant din, a daren ta tsara yadda classes din duka zasu tapi ba tareda wani takura ba. kashegari kuma suka dinga zuwa gida daukan courses, cikin kwanaki 3 aka kammala duk wani dessert sannan suka shiga main dishes gadan gadan, she taught them everything su kansu sunji dadi sosai
In a week suka gama aka bude resutuarant din aka faraa girkuna,
And a wannan ranar ne masu gidan suka dawo daga doguwar tapiyar da suka dauka
Tana daki a zauna tana duba Al'quranin ta, karfe 8 harda mintuna bata jima dayin sallar isha'i ba,
Er hayaniya taji irin daga can nesa dayake gidan nada zurfi ta miqe ta fita bolcony din dake cikin dakin, daga inda take tana iya hangen kasa, hadaddun motoci ne a jere guda 5, black with dark tint, sun jima da tsayawa, duk securitues sun gama fitowa sannan a hankali ta zuro fararen kafafunta, ta fito tana kallon komai a yatsine, ta dayan bangaren ya fito, looking calm as ever, AS_SIDDIQUE,
Ya zagayo suka hade hannayensu, they look perfect, zainab ta fada tana murmushi
She will love to see their kids, ohh damn cute
Kafin su karaso cikin falourn kasa ta rigasu sakkowa, tana sanye da blouse da skirt, sanann gyale a kanta,
Tana tsaye a falourn aka bude musu kofa, suka shigo and everything seems like a dream to her, this is the second time data kasance gata ga As_siddique, amma sai taji da banbanci sosai, wancan karon batasan shi ne ba, wancan karon bata damu da sanin ma waye shidin ba, kuma wancan karan be cikin zuri'arsu, but today, tasan shi ne As_siddique, the billionaire's heir, the most beloved child a cikin family, kuma mijin minnatullahi wacce take kalla kamar yayarta dukkuwa da ba wani shirin kirki sukeyi ba
She couldn't say a word,
"Zainab how re u?" Shine kalmomin da suka fito a bakin minnatullahi, zainab ta dauke idonta daga kallon datake mishi, ta dubi minnatu tace "Ya mint am good and okay" sai ta dubeshi kadan tace "u're welcome"
Minnatu ta subale hannunta cikin nashi sannan tazo ta wuce ta gaban zee ta soma hawa stairs din kamin tace "pls zainab zan dan huta a dakina banason disturbance,
Zaianb ta gyada kai, sannan ta dawo da dubanta gareshi, shikuma ya juya yana sallamar securities din, cikin dumbin mamaki maimkon ya hawa sama shima ya huta sai ya sule takalmanshi a nan ya zauna kan couch din falourn ya miqe kafa,
Ganin haka yasa zee juyawa, and for the first time taji muryarshi yace
"Hlo zainab right"
Ta juyo ta gyada kai tana fata gaske ne
Ya yafito ta da hannu ta karaso kuwa amma sai ta zauna kan capet din dayake, yace noo pls tashi ki zauna kan couch, batayi musu ba ta miqe ta zauna kan kujerar
"He's nice" ta fada a ranta "gaskiyar Anty hawwer (her only sister)"
So tell me meke gudana a FC (food_court, restaurant dinshi da take aiki)
Tai shiru tana tunanin "shi bae gaji bane?"
Am all ears ya katse tunaninta
Tai gyaran murya sannan ta dora hannayenta kan kafarta (cinyarta) tana facing dinshi a karkace ta soma da fadin "well i thought saleem updates you, buh i ll say it all since u ask, actually most of the chefs re not well trained, so i had to give them a classes,,," ta fada mishi duk yadda sukai da achievement din da aka samu"
Beyi smiling ba but he's impressed, okay i will test u too"
Ta dago ta dubeshi, wai itane zeyi testing a fannin girki? Oh wow she'll love that
U ll prepare a coffee now, tai nodding sannan ta miqe ta tapi cikin kitchen din dake kasa wanda a cikin shi akwae bene daze kaika har kitchen din sama

She prepared the coffee dama batayin bacci sai ta sha coffee dan haka tai two cups ta dauka ta miqa mishi daya, amma se yaqi karba yace tai tasting tukunna ta zauna tayi sipping ta kuma miqa mishi kuma ya karba at once ya shanye tas
Zee ta zuba mishi ido, ya miqo hannu ta miqa mishi na hannunta shima ya shanye,
Ya zuba mata ido sai ya lumshe idanun kuma, ba tareda ya bude ba yace
"So u're hawwer's sisster...?" Wayarshi tai kara ya bude idanunshi yayi picking
"Okay mom sai kunzo" yayi dropping call din
"Muzakkir's wife?" Ya karashe tambyar, zainab ta tsaya kallonshi "how comes ya ganeta da wuri haka, tasan yazo gidan Anty hawwer sanda tana nan amma ai basu hadu ba"
Kamar yasan tunanin datake kenan yace "i don't forget taste, i remember how all the dishes tasted plus the tatse of ur coffee"

Muje zuwa..🥰
💍 *AL_HUBB* 💍
The love💘

By Aysha b. Naseer


Episode 02: His personal cook

Ranar aiki ce dan haka tayi shirinta da wuri, ta fito and everywhere was quiet, har zatayi descending downstairs, sai ta koma bangaren data tabbatr na minnatu ne, ta karasa bakin wata kofa ta kwankwasa amma shiru dan haka ta murda kofar, falour ne mai girma amma baikai waiting falourn kasa girma ba komi shiru sai karan na'urori, dispenser nata aiki, aircon na nata,
"I hav told you to hire a cook but u refuse"
Shine abinda taji minnatu na fadi har muryarta na tashi,
Zee ta dan daga murya tace "ya mint zan fita" minnatu tace "karaso"
Ta karasa dakin babba ne sosai dakin, yana zaune kan sofar dake dakin ya dora kafa daya kan daya looking calm as always saedae daga shi sai singlet da shots,
Itakuma minnatu na kwance kan gadon dake facing sofa dukda akwae tazara tsakanin gadon da sofar tana aika mai da harara, ganin zee yasa ta dan mata murmushi, pls STAR zaki hadama abin kari zae fita ne da wuri" zee tace to
Sannan ta fita, zee na juyawa minnatu ta aikamata da harara,
Ya dubeta muryarshi calm yace "wai kekam mene matsalarki, ni kin harareni dan nace kimin abin kari, itakuma mene nata laipin da kika harareta"
Muryarta kamar zata dokeshi tace "kai wlh kana da matsaala star, nipa ba wani son zuwanta gidana nakeyi ba, dan kawai karka takuramin da aikin girki ne yasa nace tazo, nasan zata dafa maka duk abinda kakeso"
Zee tayi diff
"Dama shine dalilin dayasa Anty Siyama tace tazo kenan, tun ba yanxu ba tasan halin Anty siyama da son kanta, wato ta moreta ta kawo wa kanwarta ma ta moreta, me suka maidani ne? Baiwarsu?"
Ta matsa daga bakin kofar a hankali dama tazo ta tmbyi me za'a dafa mishi ne, kunnunwanta sukae mata wnn jin
And everything became clear to her, ko a da basa shiri d minnatu balle kuma yanxu da ta auri Nigerians billionaire,
Ta shiga kitchen din smaa tayi preparing simple dessert for him, ta koma ta kai mishi, a falour ta sameshi shi kadae ta ajiye ta juya ta fita tana maijin haushin kanta na zuwa gidan minnatu saedae ynxu kam aikin gama ya rigada ya gama

Ayyukan zee a FC ya ragu dan duka cooks din suna kokari gurin inganta abinci kuma ga salim shima wanda diman daeman yana gurin yana kulawa da harkokin
Karfe 2 ta iso gidan, akwae karuwar motoci... Ta alakanta hakan da en sannu da zuwa ne
Takai kofar faloyrn kenan aka banko kofar duk nauyin kofar nan da fadinta zee tai baya da sauri ganin za'a lahantata, manyan mata su uku ne suka fito jikinsu yasha adon gwala gwalai, kai da gani kasan masu arziki ne, dukkansu babu wacce ta kula da zee kowacce taje ga motarta drivernta yaja ta suka fita, zee ta sauke ajiyar zuciya ko sudin su waye kuma,
Tana shiga taga minnatu tana ta taunar cingam abinta babu wani abinda ya dameta "ya mint sannu da hutawa" ta fada tana kokarin wuceta" yawwa ta amsa a takaice
Ta taka steps uku kenan ya shigo falourn, bai lura da zee ba yake fadin
"Whats ur problem please sune fa yayye na, kinsan sarae irin en ubancin da akeyi cikin gidan nan amma kikae ignoring komai kika musu rashin mutunci" minnatu ta miqe "mukayiwa juna dae, ai kasan en uwanka basu da kirki nikam bazan juri iskanci ba wlh ai basu nake aure ba," ta haye sama abinta
Ya zauna a nan din yana lumshe ido, zee ta juya ta cigaba da hawan steps dinta
"What's wrong with them both?" Ta tambayi kanta, and minnatu is like she dont respect him, shikuma ya fiya sanyi a yadda ta gani...

Karfe 6 na yamma
"Pls dear kiyi mata mgana mana" minnatu ra kalleshi, "aikin ta ne tasani karka damu zatayi maka" ya futa daga dakin nata ganin bata niyyar yin abinda ya sakata din, da kanshi ya karasa bangaren zee ya wuce falour ya shiga corridor din ya karasa bakin kofar dakin dayasan anan take ya kwankwasa, ta bude ta bashi hanya ya shiga ya zauna itakuma ta tsaya tana mamakin shigowarshi har cikin dakinta baze turo bane? Amma dae tai shiru
" in bazaki damu ba, anjima by 10pm inada important meeting kuma kece zaki dauki nauyin abinda za'ayi serving, zan turo Rafiq yazo ya tayaki,... kamar mutun nawa? Ta katseshi,
"Just 10" tace is okay basae an tayani ba i can manage" ya tsura mata ido yadda take mishi magana with lots of respect yayi nodding sannan ya miqe har ya kai kofa yace "Ammm please add that coffee to the menu" idanunta na kasa tace okay sir...

Ta dauki wayarta tai dialing number favourite cousin sis dinta, babu dadewa ta dauka "mutanen Abuja ya garin"
"Zakiyya wae barrister baisan Assiddique ya dawo bane? Wasu abubuwan fa duk da kanshi yakeyi" zakiyya tai murmushi "ya sani mana zee, shima barristern baya kasar kuma Assiddique ne ya aikeshi kinsan role biyu yake mai playing role din personal Assistant da role din barrister shiyasa aikin ke mishi yawa, kuma yaqi appointing wani P.A din kinsan beda yadda"
Zee ta zauna tana tinani "can u imagine duk girman gidan nan duk yadda matsayinshi yake babu cook, ma'aikata 5 ne masu share share suma suna ida aikinsu suke koma quaters dinsu, nice dae meyi musu girki se meyiwa ma'aikata da security girki a can quaters din"
Zakiyya tace "ai baki sani ba, yana da personal cook da, duk tafiyar dazeyi da ita yake kafin yayi auren, kuma Mami (qanwar mamanshi) ce ta bashi cook din saboda matsalolin tsaro, amma yanayin aure ya maidawa mami ita, shi yana tunanin minnatu zatana mishi girki, nan kuwa besan buhun uban girman kanta ba, yanxu kuma baze koma gurin mami yace mata ta maida mishi ba"
Zainab ta jinjina kai
(Barrister shine mijin Zakiyyan shiyasa take sanin wasu abubuwan dake gudana a gidan)
Sunyi hira daga baya suka katse kiran...

Karfe 9 da rabi na daren ranar, zee ta kammala abubuwan datasan zasu bukata har ta yi wanka ta fito a wanka, wayarta tai ringing, ganin bakuwar lamba ya saka ta mishadi sosai ta dauka da sauri, amma sai taji yace Yusuf Assiddique here, zee ta hadiye ruwan hawayenta sannan tace "good day sir, everything is ready" yace ze turo azo a tayata dauka sai tayi arranging kafin time ya cika...


Read / Download AL HUBB

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album