Join Our WhatsApp Group

ARMAN MALEEQ Complete Hausa Novel Document by ARMAN MALEEQ


ARMAN MALEEQ

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23619



ARMAN MALEEQ

Reading Time: 1 Hours

Added On: 30, Aug 2023

Author: Yar Lelen Royal Star ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 07033371851

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 136.66 kb

File Type: txt

Views: 1338+

Download: 540+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼


*DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE

Sadaukarwa ga Aminiyata Sadiya Abbakar Maru (Ƴar gatan royal star)

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*



PAGE 1.



Cikin Natsuwa jerin gwanon Motoci kusan guda biyar kirar Mercedes Benz , farare ne sol gwanin sha'awa, suke tafiya, duk in da motocin suka wuce ɗaga musu hannu da jinjina ake, wanda hakan ma ya isa ya shaida maka, ba ƙaramin mai daraja da ake ganin mutuncin shi bane a motar, sai da suka zo gurin wani Babban hospital kafin su fara rage gudu, a hankali suka fara sulalawa cikin Asibitin, sai da suka shiga cikin tafkeken parking space din cikin Asibitin kafin su tsaya.


duk fitowa mutanan da suke cikin motocin suka yi, sai wata mota daya da go budeta ba'ayi ba, a hankali aka bude murfin motar, kamshin turaren Huge Boss da ya daki hancina ne ya tilasta min ɗago da idanuna, hankan kuma yy dai-dai da zuro fararen ƙafafunshi fararw tass, wanda suke cikin takalmi half cover fari mai kyau, yana yin zubin takalmin kawai zaka kalla kasan cewar na Sarakai ne.



tun daga ƙafafunshi na fara ƙarewa kallo, har izuwa kwaurinshi wanda farar Alƙyabba mai torch din Golding da ta mammaye gaba daya jikinshi, wanda har fuskarshu ba'a iya gani, sai dai hannayenshi da ya zuro, wanda ya ke gyara igiyar Alƙyabbar jikinshi.


A hankali ya sanya kyawawan fararen hannayenshi, ya dan jaaa hular Alƙyabban da yake jikinshi, Masha Allah, kyakyawa ne sosai, duk kuwa da ban ga fuskarshi da take nannaɗe da rawanin da yake a kanshu ba, idanubshi kawai da gefen fuskarshi na samu nasarar gani, idanunshi manya ne dan kai tsaye za'a kiransu da Lu-lu Eyes ko ace Oil Eyes, dan har wani mai-mai ko in ce ruwa-ruwa ne a cikin idanun nashi, farare ne tas, sai dai maimakon back eyes ball , sai nashi y kasance royal blue.


lumshe idanun nashi yy, wanda hakan yy nasarar bayyanar da zara-zaran Eyes lashes dinshi, da suke baƙaƙe sidiƙ, idanunshi y bude tare da dan juyasu a hankalin, kafin ya fara tafiya, cikin yalwatacciyar natsuwa da kamalarshi.


Sauran Fadawan da suke bayanshi ne suka fara take mishi baya, cikin natsuwa duk suka nufi cikin Hospital din.
shigarsu kuma tayi dai-dai da shigowar motar Ambulance da take ta ihu, cikin gaggawa gaba daya nurses din da suke cikin Asibitin da Drs duk suka nufi waje in da Ambulance din ta tsaya.

cikim gaggawa aka fara fitowa da Majiyatan da suke cikin Ambulance din wanda kallo daya zaka musu kasan cewar Haɗarine Hadarin ma mugun haɗari wanda baya kalluwa, daga gaba dayan su bb wanda bai rasa wani sashe na jikinshi ba, duk jini jikinsu bb kyan gani, masu rauni zuciya ma daga cikin nurses din sai kuka suke, Drs din kuwa dama su sun saba gani, hakan yasa abun bai wani ɗaɗarasu da ƙasa ba, sun damu amma bawai kamar nurses din ba.fiffito dasu aka yi, amma sai suka yi cirko², ba'a shiga da su ciki ba.

Mutanan da suka shiga ciki ne suka fito , gurin da mutanan suke tsaya suka nufa,
abin ya mugun ɗaga musu hankali, wanda yasa da damarsu suka fara zubar da hawaye,daya daga cikin Drs din ne ya ce "wannan sai dai ku shiga dasu Amma bb alamar rai a jikinsu", ya fada yana niyyar juyawa, hannunshi mutumin ya kama, idanunshi da dago tare da tsurasu akan mutumin da sauri cikin ƙanƙan da kai yace "Allah ya taimaki Sheikh Arman wannan Haɗarin ya munana, bashi da kyan gani, bana tunanin za'a iya fitar da mai a ciki", ya fada cikim zallar jimami.


sakin hannunshi yy ya ƙarasa gurin motar, yana zuwa idannshi ya sauka akan wata Yarinya da take sharɓe gaba daya jikinta jini ne, wanda yasa bama a iya ganin fuskarta sa boda jinin da ya wanke gaba daya illahirin jikinta, ga wani farɗeɗan ciwo da ya zagayo tun daga kanta har tsagin fuskarta ɓangaren haggu, gaba daya Yarinyar ba zata wuce 7years ba, royal blue eyes din shi, ya juya a kam Yarinyar da kallo daya yy mata ya gane tana numfashi, a hankali ya furta "Yah Subhanallah", ya fada yana kutsa kanshi cikin tarin Jama'ar gurin.

yana zuwa bai ɓata lokaci ba ya dauketa chaak tare da nufar cikin Asibitin da ita, cikin wata Golden Voice mai dadin gaske, wadda kamar ana busa sarewa ya fara kiran "Doctor! Doctor!! Doctor!!!", ya ƙarasa faɗa cikin gajiyawa da rashin son magana, Dr din da ya mishi mgn Ɗazun ne y fito da sauri jikinshi na rawa, miƙa mishi Yarinyar yy , da ido ya mishi alama da a duba ta, da sauri ya karɓi Yarinyar da bb alamar rai a jikinta, Accident and Emergency room ya nufa da ita da sauri.


Yana shiga ya shimfiɗeta kan gadon da aka tana da domin masu rashin lpy mai tsanani ko haɗari, gaba daya gadon yana kewaye da na'u'o'i , na ceton ran Dan Adam, da sauri Dr din ya dauki
stethoscope da yake ajiye a saman wani dan table in da anan ne ake ajiye duk wani abu mai muhimmanci da Drs suke buƙat amfani da su domin ceto ran marar lpy.

cikin Sauri ya juyawa Yarinyar baya tare sa zage zip din yar rigar jikinta, ya ajiye a gefe, kwantar da ita yy tare da daura stethoscope din a kirjinta ɓarin dama, domin jiyo sauti bugun numfashinta, a hankali ya jiyo bugun numfashinta da yake chan ƙasa sosai wanda in baka saurara ba ba zaka iya jiyowa ba, da sauri ya dauki ya matsa gurin Ventilator, (Na'urar hura iska ita ce injin da ke shaka wa mutum yayin da huhu ke samun waraka. Yana aika iskar oxygen ko iska zuwa cikin huhu ta cikin bututu mai bakin ciki kuma yana ba da damar carbon dioxide ya tsere. Ana sanya bututun a cikin bututun iska ta hanci ko baki), cikin Jaddada wannan lamari ya ci gaba da gyara mata jikinta, sai dai irin manya-manyan rauni kan da suke jikin Yarinyar ya bashi tsoro, domin raunika ne wanda ba lallai in mutum ya jisu a jikinshi ya iya rayuwa ba.

jinin da yake ta zuba a tsakiyar kanta ya fara tsayar mata, ganin wani kwasheshen ciwo yasa, ya dauki scissor ya fara iske mata gurin da taji ciwon, tsorata yy lokacin da yy arba da ciwon da yake kanta, wanda yasa har ya matsa ba, yanka ce sosai wadda ta shiga cikin kanta, wanda har naman kanta ana iya hangowa.

bai san lokacin da kwalla ta zubo mishi ba, sa boda zallan tausayin Yarinyar, a hankali ya shiga mata ɗinki a kan, har ya gama yana hawaye, duk in da ta ji ciwo ya wanke mata, ya gyara mata karayar da tayi, kafin ya fara gofe mata jinin fuskarta, bayan ya gama da ya kalli fuskarta, sai da zuciyarshi tayi wani kyakywan bugawa, sa boda ganin yarda fuskar Yarinyar take, wadda jini duk ya dan bubushe mata, Fara ce sosai, yana yin zubin halittar fuskarta da farin fatar jikinta kaɗai ya isa shaida maka cewar ba cikakkiyar yar Ƙasar Nigeria bace, dan tafi kama da Larabawa ko Turawa.


bayan ya gama ya shiga duddubata, domin ganin in ta samu wani Internal Injury, abun da ya gani yy bala'in girgiza mishi tunaninshi, wanda yasa sai da ya dago ya kalleta,na wasu minutes kafin ya ci gaba da aikinshi, bayan ya gama, ya fidda sakamakon Gwaje-gwajen da aka mata, tare da fitowa yana goge idanunshi da fuskarshi da suka yi jaaazir tsabar tashin hankali.


ko da ya fito wayam yaga ƙofar, ko ha'a faɗa ba yasan Sheikh Arman-Maleek Abdul-azeez Sarki ya tafi , domin lokacin Sallar Juma'a yy wanda kuma yana da tabbacin duk lokacin da ya shigo Ƙasar shine yake Limancin Central Mosque din da yake cikin Abuja .

da sauri ya shiga cikin Office dinshi domin shirin tafiya shima, sai da ya gama kafin ya fito, kiciɓis yy da wata nurse cikin harshen turanci ya fada mata ta kula da Patient din da take ER(Emergency room), jinjina mishi kanta tayi, kafin ya wuce
, yana hawa kan titin da sai kai shi Asokoro Central mosque da yake cikim Abuja, ya fara jin daddar muryar Sheikh Arman-Maleek tana tashi ta cikin abun ƙara karfin saurin maganar da yake cikin Masallacin wanda ya ƙaraɗe gaba daya Unguwar ta Asokoro, cikin dadda kuma sanyayya tattausar muryarshi yake huɗuba , tare da nusar da jama'ah da baiwar da Allah ya bashi ta iya magana.

har ya ƙaraso harabar tankamemen Masallacin da yake cike da Al-umman Annabi yana jin Muryar Sheikh din na ratsa cikin kunnuwanshi, a hankali cikin natsuwarshi shima ya nufi cikin Masallacin in da ya fara tara jama'a, sosai wanda da ka kalli yawansu ma zaka san ba mutane ne kawai ba, dole ma akwai ƙarin wasu jama'ar.


Cikin Masallacin da ya kusa cika ya shiga, kusan gaba daya Masallacin ta kusa cika da mutane, hakan yasa sai kusan sahun karshe ya samu , yana shiga bai fi sa 2 minutes ba aka kabbara Sallah,cikin tsari da tausasa harshe yake karatun Al-qur'ani mai girma a cikin Suratul Khafi, cikin zaƙi da dadin muryarshi yake karatun har aka idar da Sallah, mutane ne suka fara fita, bayan idar da Sallah Juma'an, kusan kowa da yake cikin Masalacin sai da ya fita, kafin Sheikh Arman ya fara takowa domin fita, ta wata ƙaramar kofa da take gefen kusa da gurin da Liman yake, bakishn dauke da Tasbhi yake tafita, yana yi yana lumshe idanunshi, har ya fito daga cikin masallacin.

Escort dinshi da suke a waje suna jiranshi je da Fadawa suka take mishi baya, har gurin motarshi,, bude mishi akayi, sai da ya tattare Alƙyabbar jikinshi kafin ya shiga, rufewa aka yi,bayan duk tarin mutanan da suka rakoshi sun shiga mota , kafin aka fara tafiya , a jere cikin tsari.


Direct Hanyar Garin Gombe suka nufa, idanunshi na lumshe bakinshi bai gushe da Ambaton Allah ba har suka yi nisa sosai suka raba dai-dai tsakanin Abuja da Gombe, A hankali ya fara bude Royal Eyes dinshi, tare da kallon wayar da take gefenshi wadda take ta vibrating , ga kuma haske da take kawowa.

a hankali ya kai zara-zaran fararen yatsun hannunshi, ya dauki wayar tare da yin Receiving call din, a hankali ya kara wayar a kunnenshi ba tare da sanin mai kira ba, Wata Muryar ce mai sanyi da dadi ta daki dodon kunnenshi wadda tasa ya dan lumshe ido, yarda ya dan saki jikinshu ne kawai zai fahimtar da kai wanda yake kiran nashi yana da matuƙar muhimmanci a gareshi,a hankali cikin halin rashin son magana yace "l'll call you late ",yana fadar haka ya kashe wayar .

ko Ajiyeta a in da take bai yi ba, wani call din ya ƙara shigowa cikin wayar tashi, ```Jaddi``` sunan Mai kiran nashi ya bayyana a kan screen din wayar, sai da ya lumshe idanunshi kafin ya dauki kiran, A hankali yace "Assalamu alaika", daga cikin wayar muryar wani tsoho ta fara magana cikin harshen turanci , sai da na ƙarewa fuskar wayar kallo kafin na gane ashe number bata Nigeria bace, number ƙasar waje ce.

shi din ma da ya dauka ba wata maganar kirki ce ta haɗashi da shi ba, daga uhmm sai uhumm, shi kenan abun da yake ce mishi, har suka yi Sallama.


4hours ne ya kai su Gombe daga Abuja, direct titin Abdul-azeez Arman-Maleeek Sarki roaud suka nufa, basu tsaya ko ina ba, sai gaban wani tankameman get din gidan Sarauta wanda gaba daya gidan fenti ne irin na daɗɗiyar masarauta, fentin da ba'a samunshi a ko wace Masarauta sai masarautar da ta Haura shekara ɗari biyu da wani abu, tsarin gini da shigar mutan gidan ma ya isa kara tabbatar maka da dadewar Masarautar, a hankali ya bude idanunshi da suka dan zurma sa boda wahalar tafiya, dan tunda ya shigo ƙasar bai samu ya huta ba.


Get din gidan aka bude, in da motacin suka fara shiga a hankali, suna shiga ƙaramin get wanda zai sadaka da cikin gidan in da mutane suke, aka saki wani Algaita da busa wanda ba ko wace Masarauta ake yinshi ba, sai Masarautar da suke da Kambun Sarauta, sanan Algaitar nan da Busar ba wani ne yake yinsu ba, suna busa kansu ne a duk lokacin da wani wanda yake da Haƙƙin Mulkar Sarauta idan ya biyo ta ƙofar wanda bama kowa ne ake budewa ita ba.

matse idanunshi yy sosai, dan baya son busar nan da Algaitar dan a duk lokacin da za'ayisu to gaba daya tsikar jikinshi na zubuwa ne, sai ya rasa Natsuwarshi har sai yata Addu'o'i, yanzun ma hakan ce ta kasance, har suka ƙarasa parking space aka bude mishi mota bai bude idanunshu ba, kuma bai yi wani abu da zai nuna cewar zai fito daga motar ba.



kusan 10 minutes da bude mishi ƙofar motar kafin ya fito, A hankali, cikin kamala da cikar Zati yake tafiya, yana babbazar Alƙyabbar da take jikinshi, hannun na rike da wani dan sada irin na sarakai ko kuma wani gawurtacce a cikin gidan Sarauta.


Ƙofar Fada da ta fi ko ina tsaruwa...


Read / Download ARMAN MALEEQ

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album