Join Our WhatsApp Group

MARYAMA SARAUNIYA Complete Hausa Novel Document by MARYAMA SARAUNIYA


MARYAMA SARAUNIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 60937MARYAMA SARAUNIYA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 14, May 2024

Author: Ummi Aisha ,

Ebook Compiler : Princess Aysha Muhammad (Humaira)

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 352.95 kb

File Type: txt

Views: 189+

Download: 125+

Last download: 23 hours ago

Description/Story: ο»Ώ
Compiled by Princess Aysha Muhammad


_*MARYAMA SARAUNIYA...!!*_
*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*


_Dedicated to Maryam Qaumi_πŸ’ž


_Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai_*_1_*


K'arar usur da na kararrawa ne suka taru suka cika mata kunne wanda har hakan yayi sanadiyyar farkawarta daga baccin da take yi cikin kwanciyar hankali,

Juyi ta sake yi ta mika hannunta ta dauko pillow tayi gaggawar toshe kunnuwanta sai dai duk da hakan da tayi bai hana karar sake cika dodon kunnenta ba,

Juyi tayi cikeda takaici ta tashi zaune gamida kallon window bayan ta yaye blanket din dake lullube ajikinta, ko shakka batayi yau anyi posting din sababbin sojoji zuwa barikinsu domin dama kusan duk lokacin da aka turo sababbin sojoji barikin nasu na Victoria island dake cikin garin Lagos to hakace take faruwa duk da dama kullum haka barikin yake idan da sabo har ta saba,

Ahankali ta sauka daga kan gadon nata wanda ya kasance tafkeken gaske kirar Italian bed, takalminta silifas dake ajiye agaban gadon ta zira akafarta ta nufi hanyar fita daga ita sai wata yar karamar rigar bacci light purple marar nauyi wacce tsayinta bazai wuce iya gwiwarta ba, kanta babu ko dan kwali sai gashinta dake atufke a tsakiyar kanta yana kwance luf yayinda wani yake luf luf har gaban goshinta,

Ahankali take sauka daga kafar benen domin zuwa downstairs,

Mahaifinta ta hango zaune akan kujera yana sanye da farin medical glass yana singing ajikin wasu takardu, gefenshi kuma wani matashin saurayin sojane yana sanye cikin uniform dinshi na sojoji, kamar bazata kalleshi ba sai ta dan dubeshi, farine tas dogo marar rama, fuskarshi dauke take da dan siririn saje wanda ya sake fito da kyawun fuskar tashi, yanada dogon hanci mai tsini da manyan idanuwa masu dauke da bakin gashin ido da gashin gira,

Dauke idonta tayi daga kansa ta nufi mahaifinta tana yamutsa fuska,

"Good morning dada..." Tafada tareda zama akusa da mahaifin nata kamar zata koma cikin cikinsa, barin rubutun da yake yi yayi ya juya gareta yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi,

"Mai sunan mama kin tashi....?"

"Na tashi dada amma ni sam ba yanzu nayi niyyar tashi ba, wallahi wannan karar dake tashi ce ta tasheni"

"Ayya sorry mai sunan mama"

Jingina tayi da jikin kujerar falon tana yiwa wannan matashin sojan kallon tara saura kwata, shi kuwa baima san tana yiba saboda tun kallon farko da yayi mata yaji bata burgeshi ba sannan jininsa bai hadu da nata ba sam musamman ma yanzu da yaga yanda taketa wani yayyatsina tana zuba shagwaba kamar wata yarinyar goye,

"Mai sunan mama yau baza kije asibitin ba ne?" Muryar mahaifinta takatse ta,

"Dada zanje saboda nasan yanzu hakama suna can suna jirana"

"Yakamata mai sunan mama, Allah yabada sa'a, ya kuma baki lada.."

"Amin dada"

Sai da ta mike tsaye sannan mahaifin nata yaci gaba da rubutun da yake yi,

Tsayawa tayi tafara kiran kuku cikin karamar muryarta wacce ta hadu da yanga da iyayi,

"Kuku...., kuku....,kuku...."

Shiru taji bai amsaba saboda dama sam bazai iya jiyota ba kasancewar akwai rata sosai tsakanin falon da take da kuma kitchen din,

"Ssssssssss..." Tace da wannan sojan dake tsaye, ko kallonta bai jiyo yayiba balle ta saka ran cewar zai saurareta,

"Heeyyy,pls kira min kuku a kitchen.." Tace dashi,


Cikeda mamakin rainin hankali irin nata ya daga idonshi ya kalleta a karo na biyu tun shigowarta falon, ganin rigar dake sanye ajikinta yasashi saurin sauke idonshi kasa domin bazai iya cigaba da kallonta ba sai dai kuma mamakin abinda tace masa ya kasa gushewa daga cikin zuciyarsa, in banda rashin kunya da rainin wayo shi zata kalla tace zata aika ya kira mata kuku?

"Yes madam.." Muryar kukun ya katse musu tunsninsu su duka,

"Kuku, ka dafa min black tea empty sannan ka soya min egg guda biyar, yanzun nan kayi kagama saboda wanka kawai zanyi nazo natafi office"

"Yes ma.." Kukun yafada tareda juyawa da sauri ya nufi kitchen,

Juyawa tayi ta nufi upstairs bayan ta dauke kanta ta kaishi gefe guda, tana shiga dakin ta duba taga ko mai aikinta ta ajiye mata kayan da zata saka yau, tana dubawa taga bata ajiyeba dan haka ta sake juyawa ta fita zuwa kasa,

Tana sauka tafara kwalawa mai aikin kira,

"Blessing..., blessing...., blessing.."

Da gudu mai aikin ta fito tana amsawa,

"Blessing yau ni kike son na dauko kayan da zan saka ko me??"

"Kiyi hakuri anty namanta ne shiyasa"

"Naji, wuce kije ki fito min da kayan sannan baki kunna turaren wuta acikin dakin ba"

"To anty, zan kunna yanzu"

Har lokacin wannan sojan yana tsaye yana jin duk abinda suke cewa, juyawa tayi tabi bayan blessing zuwa dakinta wanda yake shirye da kayan ado na kyalele, ko ina nacikin dakin frames ne manya manya akafe masu dauke da hoton butterfly ajiki, saboda a rayuwarta tana kaunar wannan kwaron,kan gadonta kuwa cike yake da manya tedy kala kala wanda sune ma suka cika kan gadon, komai na dakin kalarsa pink & blue ne, hatta bed sheet din dake shimfide akan gadon da blanket din duk kalarsu pink & blue ne,

Towel taja ta wuce cikin toilet tabar blessing tana kiciniyar ciro mata kayan da zata saka,

Wanka tayi ta fito tana kallon agogo, karfe 12 narana daidai, katon hijab tasa ta shimfida abin salla domin batayi sallar asuba ba, cikin sakannin da bazasu wuce goma ba ta duddungura ta mike ta isa gaban mirror ta tsaya tafara tsarawa jikinta da fuskarta kwalliya....

*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»


*_MARYAMA SARAUNIYA...!_**_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*_Dedicated to maryam Qaumi_πŸ’•*2*

Zama tayi agaban mirror tafara tsarawa jikinta da fuskarta ado, akalla saida ta shafe jikinta da mayuka fiyeda kala biyar masu kamshi da taushi gamida gyaran fata,

Pink din janbaki tashafa tayi jagira ta saka kwalli acikin idonta take ta fito a maryaman ta sak mai ji da kyau gamida takama da baiwar da Allah ya bata, wani dan karamin roba ta dauko mai kamada maganin ciwon ido ta bude ta diddisa acikin idonta lokaci daya idanuwanta suka sake zama farare tatas yayinda digon blue din dake ciki yasake zama blue sosai amaimakon bak'i,


Tashi tayi takarasa wurinda blessing ta ajiye mata kayan da zata saka, bakar skirt ce doguwa yar kanti hadeda pink t shirt mai botira da dogon hannu sai dan siririn mayafi wanda zata yane kanta shima kalarsa pink,

Anutse ta saka kayan ta koma gaban mirror ta bude drewar din dake jiki ta ciro wasu barima na gold guda hudu kasancewar kunnenta kowanne huda biyune, bayan ta kammala sakawane ta sake ciro wata siriryar barimar ta gold wadda take dauke da wani dan zare ajiki da yan kyawawan flowers ta zira acikin hudar dake kan hancinta wanda ke gefen hagu,

Yar karamar sarka siririya ta sake daukowa ita dinma dai ta gold dince, kafarta ta hagu ta dora akan stool ta daura wannan sarkar ajiki tare da wani dan karamin zobe na gold shikuma a dan yatsanta natsakiya dake kafarta ta saka,

Hatta agogon da ta daura da sauran zobunan data saka a hannunta duk na gold ne, siririn mayafinta ta dan yafa akanta wanda ana iya hango gashinta dake kwance akanta musamman ma tagaba kasancewar taja mayafin baya ta kaishi tsakiyar kanta wannan dalilin ne yasa gashin ya bayyana afili tagaba,

Turaren cute lady da sauran turaruka tabi ta feffesa ajikinta wanda suka haura kala goma nan da nan ta dauki kamshi jikinta ko ta ina kamshine ke tashi,

Blessing ce ta bude kofa ta shigo tana dan rissinawa,

"Anty kin gamane?"

Juyowa tayi kamar bazata yi magana ba ta kalleta,

"Nagama, miko min phone dina a kan bedside drewar"

"Ok anty"

Cikin sauri takarasa ta dauko mata wayar ta kawo mata,

"Kashe a.c dinnan" tafada tana touching din wayar dake hannunta, Dr Naz tafara kira tareda kara wayar ajikin kunnenta,

"Hello kana inane?" Tafada bayan taji ya daga wayar,

"Gani nazo daukarki ki fito mutafi ina waje.."

"Kamar kuwa kasan yanzu banida driver wallahi,amma dai tunda ankawo sabbin sojoji nasan dada zai bani driver acikinsu.."

"Ai laifinkine tunda kece bakya son driving ban san dalili ba koda yake may be kina jin tsoron titine"

"Hakane wallahi ban fiya son ganin motoci dayawa akan titi ba, bari nafito.." Tafada tana murmushi hadeda katse wayar,

"Blessing bani shoes din mana..."

Da sauri blessing ta debo wasu pink colour din cover shoe masu shegen tsini tazo gabanta ta tsugunna tafara saka mata,

Tana rikeda wayarta tana yin waya da Dr Sameer tafita daga cikin dakin yayinda blessing kuma taje ta dauko mata laptop dinta ta saka acikin jaka ta rufe sannan ta dauki handbag dinta yar karama pink colour tafita da sauri tabi bayanta,

Tana sauka ta iske Dada a inda ta tafi tabarshi yanata signing ajikin takardu har time din bai kammala ba, wannan guy din shima yana nan atsaye,

"Bari nayi sallama da dada, i will call you back dr.." Tace da dr sameer tacikin wayar tareda katse wayar,

"Dada nashirya.."

Dagowa dada yayi yana kallonta cikeda kaunar yar lelen yar tashi kwallo daya a duniya,

"Gashi kuma driver din naki har yanzu ba asamu ba, ko zakiyi driving da kanki?"

Girgiza kai tayi "no dada, dr naz yazo daukana.."

"To shikenan insha Allah ma ayau zan samo miki wanda zai rinka kaiki tunda gashi ankawo mana sojoji sababbi"

"Ok dada thank you, i love you, bye"

Tace dashi bayan taje tayi kissing dinshi akumatu, murmushi yayi yabi bayanta da kallo cikeda kauna, shi kuwa sojan nan yana tsaye yana kallonsu ganin irin kwalliyar da maryama taci kamar wata aljana yasashi mamaki mutuka aranshi yafara tunanin to ko gasar sarauniyar kyau zata tafi?,ga wani irin rikitaccen kamshi da ya cika falon sakamakon shigowarta ciki, sannan ko yaya ta gifta ta kusa da mutum sai kamshinta ya bugi hancinshi yayi barazanar toshe masa kofofin hanci,

Cikeda yauki take takawa acikin barikin tana tafe tana waya da mutumin nata dr sameer, sojojin dake harabar wurin kuwa ko kallo basu isheta ba, da haka ta karasa wurin da dr naz yayi packing gaban motar ta bude ta shiga yayinda ita kuma blessing ta bude bayan motar ta ajiye mata jakar laptop dinta da handbag dinta sai dan madaidaicin basket wanda ke dauke da kayan breakfast dinta aciki.

Rufe kofar tayi bayan dr naz yayi sama da glasses din motar wanda sanyin kamshi ke yawo aciki,

"Maryama sarauniyar mata..." Dr naz yafada yana kallonta, ita dinma kallonshi tayi da juyayyun idanuwanta wanda suke kamar an diga zaiba aciki, ganinshi tayi sanye cikin kananan kaya t shirt da jeans blue colour, dr naz yarone sosai bawani babba bane amma yanace adole shi ita yake so,

"Dr naz ya office din?"

Murmushi yayi tareda jan motar suka nufi gate din fita daga gidan,

"Dr maryama kenan ai kece yar gata bakya zuwa office sai lokacin da kika gadama, amma ni tun 10 nagama ganin patients dina kawai dai dan ban ganki bane shiyasa nakasa tafiya"

Yatsina fuska ta danyi sannan ta dan saki murmushi irin murmushin nan na babu yabo babu fallasa,

"So kana so kace min kenan idan kayi dropping dina tafiya zakayi?"

"Ehh akwai wurinda zanje amma idan kika tashi just call me sai nazo na mayar dake gida.."

"Ok" tafada atakaice gamida kallon screen din wayar dake hannunta kirar galaxy 444,ganin me kiranta yasata yin dan guntun tsaki tareda kai wayar jikin kunnenta tafara magana ahankali kamar me rada koda yake gaba daya ma haka maganarta take ahankali kuma asanyaye,

Shidai dr naz kida yasaki yafara sauraren wakar d banj cikin wakarsa ta no be lie,

Final care specialists hospital suka nufa,har suka shiga cikin asibitin bata kammala wayarba,jiranta dr naz yayi har tagama sannan ta juya ta dubeshi tana dan murmushi,

"My guy ya akayi?"

"Nothing, sai nadawo.."

"Ok sai kadawo ko,bye bye take care" tace dashi tareda mika hannunta ta shafi kumatinshi daya,

Murmushi yayi yabita da kallo har ta bude kofar motar tafita, tana fita Joseph Massinger ya taso da sauri yazo ya bude bayan motar ya dauko laptop bag dinta da hand bag,da lunch box dinta yabi bayanta zuwa office dinta wanda shine office na hudu acikin jerin ofisoshin kwararrun likitoci dake girke a harabar asibitin,

Dr maryama, shine sunan dake makale asaman office din nata, tana budewa ta hango dr sameer zaune akan kujerarta ta aiki yana sanye cikin bakaken suit wadanda suka yi mutukar karbarsa,

Baki ta bude tana murmushi,

"Likita ya naganka anan, i hope dai lafiya?"

Murmushi yayi yana kallonta tareda karewa shigarta kallo wacce dama a ka'ida ita haka shigarta take daga riga da skirt yan kanti sai doguwar riga gown, tunda yake da ita bai taba ganinta da atamfa ko leshi ba kai hatta material sai dai kawai ta dinkashi dogawar riga, sannan tun lokacin data fara aiki a asibitin kusan shekaru uku da suka gabata bai taba ganinta da hijab ba koda kuwa talha ne, kai ko mayafi babba bai taba ganinta dashiba kullum sai dai tasaka riga da skirt wacce take kaiwa saman ciki, sai ko dan siririn mayafi marar kauri da girma, ko kuma tasa arabian gown ta yi rolling,

"Nariga da nagama ganin patients dinki, saboda tun 7 o'clock suke jiranki baki fitoba, yanzu kawai abinda zakiyi shine kije round ki duba patients dinki.."


Murmushi tayi bayan ta zauna akujerar dake gaban table din,


"Thank you dr..."

"You are welcome, kitashi kije kar kisake yin late"

Mikewa tayi tana lallon Joseph wanda shine Massinger dinta,

"Kaje ka siyo min lemon tsami saboda yakare jiya, idan ka dawo ka ajiye min acikin fridge..."

Tana kammala fadin haka ta juya tafita, kallo dr sameer yabita dashi saboda shidai a duniya yana tsananin kaunar maryama, komai tayi burgeshi take..

_Gaisuwa mai yawa ga masoyan maryama sarauniya..._

*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»


*_MARYAMA SARAUNIYA...!!_*
_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_πŸ’•*_3_*

Tamkar wata dawisu haka take takawa tana yin tafiya mai cike da burgewa gamida ban sha'awa, duk inda tawuce sai dai kaji ana fadin,

"Welcome antyn yara..!"

Murmushi kawai take danyi dan takaitacce tawuce da haka ta samu ta isa d'akin yara domin ita kwararriyar likita ce afannin, tun tana yar karama burinta kenan nazama likitan yara domin tana mutukar kaunarsu,tana sonsu ko kadan bata gajiya da wasa dasu,

Lokacin da tasaka kafarta ta shiga cikin ward din wanda ya kasance mai mutukar girma da fasali ko ina dauke yake da hotunan ababan sha'awa na yara harda manyan tedy zube a gefe daya sannan ga katuwar tv ankunna musu cartoon domin debe musu kewa,

Mikewa nurses din dakin sukayi suna yimata sannu da zuwa,

"Antyn yara sannu da zuwa.."

Bata iya amsawa ba ta nufi wani bed inda take jiyo kukan wani yaro, ko kadan bata son taji yara suna kuka,kukansu tada mata hankali yake yi,

Da saurinta taje wurinda yaron yake shida mahaifiyarsa wacce taketa kokarin dura masa abinci amma yaki ci sai faman kuka yake, matar na ganin dr maryama tafara murna tana cewa yaron,

"To kayi shiru ga anty mai chocolate nan tazo..."

Daukar yaron maryama tayi ajikinta tana kallonsa jikinsa yayi zafi rau,

"Sorry, zaka sha chocolate??

Kai ya daga, mayarshi tayi ta ajiyeshi akan gadonshi tajuya wurin nurses din,

"Aje store afara fito da kaya"

Tun kafin ta rufe bakinta suka fita, sai da ta rarrashi wannan yaron yayi shiru sannan tafara...


Read / Download MARYAMA SARAUNIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album