Join Our WhatsApp Group

ABINDA AKE GUDU Complete Hausa Novel Document by ABINDA AKE GUDU


ABINDA AKE GUDU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 101765



ABINDA AKE GUDU

Reading Time: 8 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Batul Mamman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 541.71 kb

File Type: txt

Views: 1560+

Download: 733+

Last download: 1 hour ago

Description/Story: ABIN DA AKE GUDU
Na Batul Mamman
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com

ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 1
Batul Mamman💖
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Daki ne cike da 'yan mata sai hayaniya suke yi. Wasu
suna saka kaya wanda ya kasance atampa ce ja mai adon
baki, wasu kuwa kwalliya suke yi a gaban madubi.
Wadanda basu sami wuri a gaban madubin ba da na
jikin hodarsu suke amfani ana ta fentin fuska cikin
nishadi.
Suna wannan hirar da shewa wata mace da bazata wuce
shekaru talatin ba ta shigo da katon cikinta ita ma irin
atampar jikinsu ta saka tayi kwalliya daidai gwargwado
cike da damuwa ta soma magana.
" don Allah kuyi sauri ku fito ku ake ta jira. Umma sai
fada take min babu amarya babu kawayenta. Kun dai
san tayi ta kashedi akan African time".
Wata cikinsu wadda da alama ta gama nata shirin tace
"kiyi hakuri Anti Shema'u yanzu zamu fito".
"Babu wani yanzu zaku fito. Ina Asma'un?" Ta fada tana
dube dube.
Can gefen gado ta hango kanwar tata ana rangada mata
kwalliya irin ta amare tayi kyau sosai. Kusa dasu Shemau
ta koma ta sake nanatawa mai kwalliyar tayi sauri ta
gama a fito da amarya. Ita dai Asma'u har yayarta ta
gama magana bata ce komai ba saboda kada ta bata
kwalliyarta. Wannan rana ce mai matukar mahimmanci
a rayuwarta. Ranar kamunta da mutumin da take ganin
tamkar babu irinsa a duniya.
Har Shema'u ta fara tafiya tayi saurin dawowa da sauri ta
sake kai idonta gaban rigar jikin amarya. Daure fuska
tayi " duk amaryar duniya idan ana bikinta rama takeyi
saboda zulumin barin gida da sabuwar rayuwa banda ke
Asmau. Dubi yadda rigar nan ta sake matse ki duk
kirjinki ya fito ta sama".
Hannu Asmau tasa ta rufe jikinta saboda yadda 'yan uwa
da kawayenta na dakin suka maido da kallonsu gareta.
Shemau ta cigaba da magana "ki tabbatar abinda zaki
yafa ya rufe miki kirji don bani da amsar bawa Umma
idan ta fara fada." Daga nan ta fice tana mamakin irin
wannan jiki na kanwarta. Dama can ita mai jikin kiba
ce....
******
Farfajiyar gidan ta gama cika da mata inda aka kawata
wani bangare da ado irin na gargajiya domin zaman
amarya. Ga kujeru da tebura wurin yayi kyau sosai
harda turaren wuta na tsinke da na garwashi aka kunna
sai kamshi ke tashi.
Mai gabatar da taron mace ce ta nemi kowa yayi shiru
saboda amarya zata fito. Mai kida ya canza salon kidansa
da wanda ya dace da amarya aka fara ita da kawayenta
suka fito suna taku daidai.
Sunyi matukar kyau da burge mutane da irin salon
fitowarsu. Aka dauki tafi, masu hoto kuwa na camera da
na waya suka fara aikinsu. Haka suka rinka tafiya har
suka karasa inda zata zauna. Autarsu ce Aina'u 'yar
kimanin shekaru sha uku a tsaye da mafici irin na kaba
yayarta na zama ta soma yi mata fifita a hankali. Hakan
ma ya kayatar da mutane.
Hajiya Bara'atu dake zaune cikin 'yan uwanta da kawaye
har 'yar kwalla sai da tayi. Gashi cikin ikon Allah karo na
biyu kenan da zata aurar da daya daga cikin 'ya'yanta. A
hankali tace " Allah Ka jikan Alhaji" bai rayu yaga auren
'ya'yansa ba bare yaga jikokin da suka fara tarawa.
Daga nan fa aka soma shagalin biki inda aka bukaci
dangin ango su fito domin kamun amarya. Suna tahowa
Asma'u ta bawa Walida aminiyarta wayarta ta rada mata
a kunne ta dauketa a hoto idan ana fesa mata turaren
kamun. Walida tace "uhmm su Asmau an iya soyayya.
Nasan sarai Abubakar zaki turawa".
Asmau ta juya ido tana fari "ke kuwa an hana bawan
Allah ganin iyalinsa dole na taimaka masa da hoto".
Dariya duk suka yi sannan aka cigaba da biki.
******
Ana soma kiran sallar magriba aka gama taron shiyasa
dama Haj Bara'atu ta rinka nanata musu banda African
time. Sallah aka tafi a gabatar harda amarya wadda ta
gaji sosai. Dakinta suka nufa ita da kawayenta suka yi
tasu sallar. Tana idarwa aka fara yi mata tayin abinci,
kafin a kawo ta dauki wayarta ta turawa Abubakar
hotunan kamu.
A lokacin yana tare da abokinsa Qasim. Shi dai Qasim
gani yayi Abubukar ya dan matsa ya fara waya.
Murmushi yayi don yasan da wa ake wayar. Hira suke yi
sosai yana fada mata yadda tayi kyau da kuma rashin
jindadinsa da aka hana shi zuwa wurin kamun.
Karshen gado ta koma ta rungume waya suna ta hira.
Tun ana cewa ta sauko ga abinci har suka gaji suka dena.
Ba su suka gama wayar ba sai da ya fara jin kiran sallar
isha daga masallacin gidansu wanda suma su Asma'u shi
din suke ji. Sallama suka yi tare da alkawarin zai kirata
anjima.
Tana saukowa daga kan gadon ta dafe cikinta "yunwa
nake ji kamar na kwana ban ci abinci ba"
Walida ta dan harareta "abincin ai ba jiranki zaiyi Juliet.
Ni nayi tsammanin a irin soyayyarki da Romeo din naki
baku san yunwa ko kishiruwa ba idan kuna tare".
"Nasan ba wani abu ke damunki ba sai tafiyar da rabin
ranki Babangida yayi gashi ba kya samunsa a waya sosai"
Asmau ta fada cikin tsokana ai kuwa Walida ta jefeta da
pillow tana fada. Babangida yaron gidansu Walida ne irin
almajiran nan marasa kunya gashi ya kware wurin kaiwa
matar babansu gulmar duk abinda take yi shiyasa ta
tsane shi. Har kusan daya na dare 'yan matan suka kai
suna hira sannan bacci ya dauke su. Wasu akan gado
wasu a katifun da aka shinfida a kasa.
Cikin bacci Asma'u taji wayarta na kara ta dauka cikin
magagi. Tana ganin sunan mai kiran ta wartsake.
Cikin taushin murya yace " Asmy na tasheki daga bacci
ko?"
Sai a lokacin ta kula karfe hudu da kwata na dare sunfi
wata daya yana tashinta a irin wannan lokacin dama.
Ta dan shafa idanu "babu komai Yayana yau mun so mu
makara ma".
"To a tashi ayi a nemi kusanci da Allah. I love you Asmy."
Murmushin da yake so a gareta tayi sannan tace "me too
Yayana".
Bayan ta ajiye wayar tashi tayi ta fita ta tafi bandaki ta
dauro alwala. Nafila tazo ta fara yi sannan ta dukufa
istigfari kamar yadda suka sabarwa kansu ita da
Abubakar har aka kira assalatu. Sake kira yayi ya
tabbatar idonta biyu sannan ya tafi masallaci ita kuma ta
tashi 'yan matan dakin ta tayar da tata sallar.
*****
Yau ta kama alhamis babu wani taro da za'ayi a gidan sai
karfe bakwai da rabi da za'ayi dinner da daddare.
Qasim yazo har gida ya sami Abubakar tare da takardar
da aka bashi ta canjin wurin aiki da karin matsayi. Abin
takaici ana bukatar lallai yaje ya gabatar da kansa a
sabon ofishin da aka tura shi a Zamfara kafin litinin mai
zuwa. Abubakar ya taya shi murna sai dai sunyi
bakincikin bazai sami dinner da daurin auren abokin
nasa ba. Abubakar duk ya shiga damuwa Qasim ya rinka
kwantar masa da hankali.
Abubakar yace "yanzu tunda ka zama ACP Qasim to sai
ka nemo mana mata musha biki."
Dariya Qasim yayi "wace mata zan nemo bayan kasan
albashin dansanda har yanzu bai taka kara ya karya ba."
"A dai rinka godewa Allah" Abubakar ya fada yana saka
takalmi. Har bakin mota ya raka Qasim. Dukkaninsu
basu ji dadin zuwan canjin aikin a wannan lokacin ba.
******
Kwalliyar Asma'u ta yau har tafi ta jiya. Kawaye da 'yan
uwanta kowa yayi irin nasa adon. Anti Shema'u, 'yarta
Mimi da Aina'u kayansu iri daya. Mazan gidan su biyu
suma shadda suka saka iri daya.
Suna gama shiryawa motar ango tazo daukar amarya.
Shima kayansa ya dace da nata. Tun a gida ake daukarsu
hotuna haka a wurin dinner din. Abin ya kayatar saboda
komai anyi shi cikin nutsuwa irin na 'yan boko. Duk
motsin Asma'u idon Abubakar yana kanta suna hada ido
sai suyi murmushi. Soyayya ce da ta samo asali tun
farkon tarewarsu Asma'u a unguwar su Abubakar
shekaru tara da suka wuce.
Sai wurin shadaya da rabi aka tashi daga taro kowa ya
tafi gida. Wani abokin Abubakar ke tuka motar suka
ajiyeta a gida sannan suka wuce.
******
Washegari Juma'a gidan commissioner kamar yadda
duk 'yan unguwa suka sakawa gidansu Abubakar sun
tashi a makare saboda gajiyar da suka kwaso a wurin
dinner da kuma sanyin da aka tashi dashi.
Mahaifinsu Alh Adamu Matawalle tsohon dan sanda ne
har commissioner ya taba yi. Da taimakonsa Qasim ya
sami aiki ma. Matarsa daya Yalwa wadda suke kira
Mama. Su shida ta haifa. Babban danta sunansa
Abdulhalim yana da mata daya da 'ya'ya biyu sai mai
binsa Nasiba itama tana gidan nata mijin. Abubakar ne
na uku amma kannensa mata biyu Sadiya da Suwaiba
duk sunyi aure. Su biyu suka rage shi da autansu Umar.
A gaggauce suka tashi domin baifi awa daya da rabi ya
rage musu ba lokacin daurin auren ya yi. Mata suka tashi
aka shiga kitchen saboda abokan Baba kamar yadda
suke kiran mahaifinsu a gidan zasu ci abinci idan an taso
daga wurin daurin auren. Ga samari 'yan uwa da suka
kwana a gidan su ma shiyasa aka yi ta layin shiga wanka
a bandakuna biyun dake bangaren maza. Da gangan
suka ki barin Abubakar ya fara shiga a cewarsu shi ango
dole a jira shi.
Baifi minti talatin ya rage ba Umar ya fito daga bandaki
kumfar jikinsa bata gama fita ba Abubakar ya shiga ya
rufe kofar da mukulli.
Sauran samarin babu wanda ya tsaya cin abincu suka
fita dama wurin daurin auren babu nisa daga gidan ko a
kafa zasu iya karasawa kofar gidan kakan Asma'u tunda
bayan layi ne.
Duk an gama taruwa iyaye suna daga cikin katon soron
gidan sauran mutane suna daga waje duk an cike layin.
Alh Adamu ya kira Abdulhalim yana tambayarsa ina
Abubakar. Abdulhalim yace "inajin yana waje kasan
halinsa da kunya karshenta ya ki shigowa."
A waje kuma abokansa ke tambayar juna ko ya shige ciki
ne domin basu ganshi ba.
Babu wanda ya saka damuwa a ransa har aka gama
daurin auren kowa yana tunanin yana wani wurin.
A can gidansu kuma Haj Yalwa ce ta kira wata yarinya
cikin 'yan uwansu tace ta duba mata kowane bandaki na
gidan ta dauko bota a cika su da ruwa a ajiye a waje
saboda abokan Baba. Idan sunci abinci zasu yi shirin
sallar Juma'a.
Yarinyar tayi ta zagaye tana dauko buta. Kofar bandakin
dake cikin dakin Umar ce ta kasa budewa sai ta koma
ciki ta fadawa Nasiba. Tare suka dawo suka yi ta kokarin
budewa suka kasa ga ruwa kuma ya fara fitowa ta
karkashin kofar bandakin. Nasiba ta saka kunne jikin
kofar taji alamun famfo yana zubar da ruwa. Mama suka
sanarwa tace a samo wani ya balle kofar saboda kada
ruwan bangaren ya kare tunda tanki ne. Abu ya hada da
mata suka kasa budewa ga ruwan yana yawa.
Dole suka hakura har Allah Yasa aka fara dawowa daga
wurin daurin auren. Lokacin duk sun tsince kayan dake
kasan dakin saboda ruwa. Umar na shigowa Mama ta
hau shi da fada shi bai ma san laifin da yayi ba sai da
tace yaje ya bude kofar bandakin shi. Yayi mamakin jin
kofar a rufe ya saka iya karfinsa ya soma dukanta. Babu
kowa a dakin sai shi kadai don Mama tace babu mai
taya shi gyarawa. A bugu na hudu kofar ta bude yayi
tozali da abinda yayi matukar razana shi.
Abubakar ne kwance cikin ruwan da ya hade da jini daga
kasan kansa ga sabulu can a gefen kafarsa ta hagu
alamun zamewa yayi.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 2
Batul Mamman💖
Lokaci guda Umar ya gigice jikinsa ya hau bari. Da sauri
ya shiga bandakin ya zauna cikin ruwan kusa da
Abubakar sannan ya daga kansa ya dora a kan cinyarsa.
Da kyar ya iya cewa "Yaya".
Babu wata alamar motsi a tare da Abubakar. Umar ya
shiga jijjiga shi yana kiran sunansa. Duk da haka
Abubakar bai motsa ba. Iyakar tsorata Umar yayi don ji
yake kamar zuciyarsa zata buga. Wasu zafafan hawaye ya
soma yi a hankali yace "Yaya Abubakar ka tashi an daura
auren."
Nan ma dai shiru yaji. Tunaninsa gabadaya ya kulle ya
rasa me zaiyi ya taimakawa dan uwansa. Da sauri ya
tashi ya fara kokarin daga shi ya fitar dashi daga cikin
ruwan, amma yayi masa nauyi domin duk jikinsa a sake
yake. Ya sake gwadawa yaji tabbas bazai iya ba sai ya
tashi ya fita tare da rufe dakin da mukulli.
Duk wanda ya ganshi da kaya a jike ga alamun jini a
gaban sabuwar shaddarsa da tasha dinki sai ya tambaye
shi ko lafiya. Babu wanda ya bawa amsa ya wuce dakin
Mama.
A tsaye ya ganta a gaban mudubi tana saka sarka. Kafin
yayi magana ta juyo da sauri saboda ganinshi da tayi ta
mudubin. Gaban rigarsa ta nuna tare da zuwa gabansa ta
tsaya "Umar me ya faru? Ciwo kaji garin gyaran
bandakin? "
Maimakon yayi magana kawai sai ya rungumeta yana
kuka mai tsuma zuciya.
*****
Duk akwatunan kayan Asmau an gama hadasu a wuri
guda. Daya daga ciki ta bude ta dauko wata atampa zata
saka Aina'u ta shigo dakin da gudu sai haki take yi.
"An daura auren. Daga yau dakin nan ya zama nawa ni
kadai" ta fada iyakar karfinta tana murna. Tana gama
fadar abinda ya kawota ta sake ficewa da gudu.
Su Walida suka soma guda suna yiwa Asmau tsiya. Harda
masu yi mata wakar ta zama dauko riga....ta zama dauko
hula....ta zama dauko wando....
Duk baki irin nata jikinta sai da yayi sanyi ta kasa biye
musu kamar yadda ta saba. Ji tayi zuciyarta tana bugawa
da karfi har abin ya bata tsoro kawai sai ta soma kuka.
Hankalinsu ya fara tashi. Walida ce ta rungumeta
maimakon ta bata hakuri itama sai ta fara kukan. Wata
'yar kanin baban su Asmau ce tace "haba Walida
maimakon ki bata hakuri sai ki biye mata. Yau ai ranar
farinciki ce ba kuka zakiyi ba. Ki tashi kiyi nafila ki
godewa Allah da Ya nuna miki wannan rana."
Jiki a sanyaye Asmau ta saka kayanta ta dora hijab ta
tayar da sallah.
*****
Gaban Mama ya fadi ta dan ture Umar daga jikinta. Ta
soma kokarin daga masa riga ta ga ko ciwo yaji ya zubar
da jini da yawa haka.
"Mama jinin Yaya Abubakar ne".
Jin maganar tayi har tsakiyar kanta. Jinin Abubakar
kuma? Abubakar din da ta tabbatar yana tare da
abokansa yanzu suna shirin zuwa wurin reception din da
zasuyi. Cikin rashin fahimta tace "wane irin jini? A ina
kaga Abubakar din?"
Umar yace "yana toilet dina ya suma".
Mama bata jira ya sake magana ba ta fita daga dakin da
sauri yana binta a baya. Matan dake cikin gidan suna ta
tambayar abinda ke faruwa. Ganin basu tsaya basu amsa
ba suka bi bayansu.
A kofar dakin Umar suka tsaya ya saka mukulli zai bude
kofar Abdulhalim ya shigo yana fadan Abubakar ya bar
mutane suna ta cigiyarsa har Baba sai da yayi ta fada.
Umar dai bai kula shi ba ya bude kofar Mama ta ture shi
ta shiga da gudu. Inda ya barshi a kwance suka sake
samunsa.
Abdulhalim ya karasa gabansa da sauri yana tambayar
Umar me ya faru. Da taimakon Umar suka dora shi a kan
gado daga shi sai dogon wando a jikinsa. Mama ta fada
kanshi tana jijjiga shi tana kuka.
Matan dake kofar dakin suma suka soma kukan. Nan da
nan aka kirawo 'yan uwansa mata. Abdulhalim ya kira
wani abokinsa likita da yazo wurin daurin auren ya
bukaci ya karaso gidansu da gaggawa. Dakin duk ya rude
da kuka duk da har yanzu basu san ainihin me ya same
shi ba. Sai da Abdulhalim yayi da gaske ya iya sawa suka
fita.
Cikin mintuna kadan likitan ya karaso. Yayi mamakin
ganin angon kwance jini har ya soma jika zanin gadon.
Umar ne yayi masa bayanin yanayin da ya tsince shi a
ciki. Abdulhalim yace "bari mu saka shi a mota mu tafi
asibiti. Bana so mutane su ganmu. Zanyi kokarin kawo
motata baya sai a fita dashi." yana gama magana ya fita.
Kabiru ya duba kan Abubakar...


Read / Download ABINDA AKE GUDU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album