Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ABIN DA AKE GUDU
Na Batul Mamman
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]

ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 1
Batul Mamman💖
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Daki ne cike da 'yan mata sai hayaniya suke yi. Wasu
suna saka kaya wanda ya kasance atampa ce ja mai adon
baki, wasu kuwa kwalliya suke yi a gaban madubi.
Wadanda basu sami wuri a gaban madubin ba da na
jikin hodarsu suke amfani ana ta fentin fuska cikin
nishadi.
Suna wannan hirar da shewa wata mace da bazata wuce
shekaru talatin ba ta shigo da katon cikinta ita ma irin
atampar jikinsu ta saka tayi kwalliya daidai gwargwado
cike da damuwa ta soma magana.
" don Allah kuyi sauri ku fito ku ake ta jira. Umma sai
fada take min babu amarya babu kawayenta. Kun dai
san tayi ta kashedi akan African time".
Wata cikinsu wadda da alama ta gama nata shirin tace
"kiyi hakuri Anti Shema'u yanzu zamu fito".
"Babu wani yanzu zaku fito. Ina Asma'un?" Ta fada tana
dube dube.
Can gefen gado ta hango kanwar tata ana rangada mata
kwalliya irin ta amare tayi kyau sosai. Kusa dasu Shemau
ta koma ta sake nanatawa mai kwalliyar tayi sauri ta
gama a fito da amarya. Ita dai Asma'u har yayarta ta
gama magana bata ce komai ba saboda kada ta bata
kwalliyarta. Wannan rana ce mai matukar mahimmanci
a rayuwarta. Ranar kamunta da mutumin da take ganin
tamkar babu irinsa a duniya.
Har Shema'u ta fara tafiya tayi saurin dawowa da sauri ta
sake kai idonta gaban rigar jikin amarya. Daure fuska
tayi " duk amaryar duniya idan ana bikinta rama takeyi
saboda zulumin barin gida da sabuwar rayuwa banda ke
Asmau. Dubi yadda rigar nan ta sake matse ki duk
kirjinki ya fito ta sama".
Hannu Asmau tasa ta rufe jikinta saboda yadda 'yan uwa
da kawayenta na dakin suka maido da kallonsu gareta.
Shemau ta cigaba da magana "ki tabbatar abinda zaki
yafa ya rufe miki kirji don bani da amsar bawa Umma
idan ta fara fada." Daga nan ta fice tana mamakin irin
wannan jiki na kanwarta. Dama can ita mai jikin kiba
ce....
******
Farfajiyar gidan ta gama cika da mata inda aka kawata
wani bangare da ado irin na gargajiya domin zaman
amarya. Ga kujeru da tebura wurin yayi kyau sosai
harda turaren wuta na tsinke da na garwashi aka kunna
sai kamshi ke tashi.
Mai gabatar da taron mace ce ta nemi kowa yayi shiru
saboda amarya zata fito. Mai kida ya canza salon kidansa
da wanda ya dace da amarya aka fara ita da kawayenta
suka fito suna taku daidai.
Sunyi matukar kyau da burge mutane da irin salon
fitowarsu. Aka dauki tafi, masu hoto kuwa na camera da
na waya suka fara aikinsu. Haka suka rinka tafiya har
suka karasa inda zata zauna. Autarsu ce Aina'u 'yar
kimanin shekaru sha uku a tsaye da mafici irin na kaba
yayarta na zama ta soma yi mata fifita a hankali. Hakan
ma ya kayatar da mutane.
Hajiya Bara'atu dake zaune cikin 'yan uwanta da kawaye
har 'yar kwalla sai da tayi. Gashi cikin ikon Allah karo na
biyu kenan da zata aurar da daya daga cikin 'ya'yanta. A
hankali tace " Allah Ka jikan Alhaji" bai rayu yaga auren
'ya'yansa ba bare yaga jikokin da suka fara tarawa.
Daga nan fa aka soma shagalin biki inda aka bukaci
dangin ango su fito domin kamun amarya. Suna tahowa
Asma'u ta bawa Walida aminiyarta wayarta ta rada mata
a kunne ta dauketa a hoto idan ana fesa mata turaren
kamun. Walida tace "uhmm su Asmau an iya soyayya.
Nasan sarai Abubakar zaki turawa".
Asmau ta juya ido tana fari "ke kuwa an hana bawan
Allah ganin iyalinsa dole na taimaka masa da hoto".
Dariya duk suka yi sannan aka cigaba da biki.
******
Ana soma kiran sallar magriba aka gama taron shiyasa
dama Haj Bara'atu ta rinka nanata musu banda African
time. Sallah aka tafi a gabatar harda amarya wadda ta
gaji sosai. Dakinta suka nufa ita da kawayenta suka yi
tasu sallar. Tana idarwa aka fara yi mata tayin abinci,
kafin a kawo ta dauki wayarta ta turawa Abubakar
hotunan kamu.
A lokacin yana tare da abokinsa Qasim. Shi dai Qasim
gani yayi Abubukar ya dan matsa ya fara waya.
Murmushi yayi don yasan da wa ake wayar. Hira suke yi
sosai yana fada mata yadda tayi kyau da kuma rashin
jindadinsa da aka hana shi zuwa wurin kamun.
Karshen gado ta koma ta rungume waya suna ta hira.
Tun ana cewa ta sauko ga abinci har suka gaji suka dena.
Ba su suka gama wayar ba sai da ya fara jin kiran sallar
isha daga masallacin gidansu wanda suma su Asma'u shi
din suke ji. Sallama suka yi tare da alkawarin zai kirata
anjima.
Tana saukowa daga kan gadon ta dafe cikinta "yunwa
nake ji kamar na kwana ban ci abinci ba"
Walida ta dan harareta "abincin ai ba jiranki zaiyi Juliet.
Ni nayi tsammanin a irin soyayyarki da Romeo din naki
baku san yunwa ko kishiruwa ba idan kuna tare".
"Nasan ba wani abu ke damunki ba sai tafiyar da rabin
ranki Babangida yayi gashi ba kya samunsa a waya sosai"
Asmau ta fada cikin tsokana ai kuwa Walida ta jefeta da
pillow tana fada. Babangida yaron gidansu Walida ne irin
almajiran nan marasa kunya gashi ya kware wurin kaiwa
matar babansu gulmar duk abinda take yi shiyasa ta
tsane shi. Har kusan daya na dare 'yan matan suka kai
suna hira sannan bacci ya dauke su. Wasu akan gado
wasu a katifun da aka shinfida a kasa.
Cikin bacci Asma'u taji wayarta na kara ta dauka cikin
magagi. Tana ganin sunan mai kiran ta wartsake.
Cikin taushin murya yace " Asmy na tasheki daga bacci
ko?"
Sai a lokacin ta kula karfe hudu da kwata na dare sunfi
wata daya yana tashinta a irin wannan lokacin dama.
Ta dan shafa idanu "babu komai Yayana yau mun so mu
makara ma".
"To a tashi ayi a nemi kusanci da Allah. I love you Asmy."
Murmushin da yake so a gareta tayi sannan tace "me too
Yayana".
Bayan ta ajiye wayar tashi tayi ta fita ta tafi bandaki ta
dauro alwala. Nafila tazo ta fara yi sannan ta dukufa
istigfari kamar yadda suka sabarwa kansu ita da
Abubakar har aka kira assalatu. Sake kira yayi ya
tabbatar idonta biyu sannan ya tafi masallaci ita kuma ta
tashi 'yan matan dakin ta tayar da tata sallar.
*****
Yau ta kama alhamis babu wani taro da za'ayi a gidan sai
karfe bakwai da rabi da za'ayi dinner da daddare.
Qasim yazo har gida ya sami Abubakar tare da takardar
da aka bashi ta canjin wurin aiki da karin matsayi. Abin
takaici ana bukatar lallai yaje ya gabatar da kansa a
sabon ofishin da aka tura shi a Zamfara kafin litinin mai
zuwa. Abubakar ya taya shi murna sai dai sunyi
bakincikin bazai sami dinner da daurin auren abokin
nasa ba. Abubakar duk ya shiga damuwa Qasim ya rinka
kwantar masa da hankali.
Abubakar yace "yanzu tunda ka zama ACP Qasim to sai
ka nemo mana mata musha biki."
Dariya Qasim yayi "wace mata zan nemo bayan kasan
albashin dansanda har yanzu bai taka kara ya karya ba."
"A dai rinka godewa Allah" Abubakar ya fada yana saka
takalmi. Har bakin mota ya raka Qasim. Dukkaninsu
basu ji dadin zuwan canjin aikin a wannan lokacin ba.
******
Kwalliyar Asma'u ta yau har tafi ta jiya. Kawaye da 'yan
uwanta kowa yayi irin nasa adon. Anti Shema'u, 'yarta
Mimi da Aina'u kayansu iri daya. Mazan gidan su biyu
suma shadda suka saka iri daya.
Suna gama shiryawa motar ango tazo daukar amarya.
Shima kayansa ya dace da nata. Tun a gida ake daukarsu
hotuna haka a wurin dinner din. Abin ya kayatar saboda
komai anyi shi cikin nutsuwa irin na 'yan boko. Duk
motsin Asma'u idon Abubakar yana kanta suna hada ido
sai suyi murmushi. Soyayya ce da ta samo asali tun
farkon tarewarsu Asma'u a unguwar su Abubakar
shekaru tara da suka wuce.
Sai wurin shadaya da rabi aka tashi daga taro kowa ya
tafi gida. Wani abokin Abubakar ke tuka motar suka
ajiyeta a gida sannan suka wuce.
******
Washegari Juma'a gidan commissioner kamar yadda
duk 'yan unguwa suka sakawa gidansu Abubakar sun
tashi a makare saboda gajiyar da suka kwaso a wurin
dinner da kuma sanyin da aka tashi dashi.
Mahaifinsu Alh Adamu Matawalle tsohon dan sanda ne
har commissioner ya taba yi. Da taimakonsa Qasim ya
sami aiki ma. Matarsa daya Yalwa wadda suke kira
Mama. Su shida ta haifa. Babban danta sunansa
Abdulhalim yana da mata daya da 'ya'ya biyu sai mai
binsa Nasiba itama tana gidan nata mijin. Abubakar ne
na uku amma kannensa mata biyu Sadiya da Suwaiba
duk sunyi aure. Su biyu suka rage shi da autansu Umar.
A gaggauce suka tashi domin baifi awa daya da rabi ya
rage musu ba lokacin daurin auren ya yi. Mata suka tashi
aka shiga kitchen saboda abokan Baba kamar yadda
suke kiran mahaifinsu a gidan zasu ci abinci idan an taso
daga wurin daurin auren. Ga samari 'yan uwa da suka
kwana a gidan su ma shiyasa aka yi ta layin shiga wanka
a bandakuna biyun dake bangaren maza. Da gangan
suka ki barin Abubakar ya fara shiga a cewarsu shi ango
dole a jira shi.
Baifi minti talatin ya rage ba Umar ya fito daga bandaki
kumfar jikinsa bata gama fita ba Abubakar ya shiga ya
rufe kofar da mukulli.
Sauran samarin babu wanda ya tsaya cin abincu suka
fita dama wurin daurin auren babu nisa daga gidan ko a
kafa zasu iya karasawa kofar gidan kakan Asma'u tunda
bayan layi ne.
Duk an gama taruwa iyaye suna daga cikin katon soron
gidan sauran mutane suna daga waje duk an cike layin.
Alh Adamu ya kira Abdulhalim yana tambayarsa ina
Abubakar. Abdulhalim yace "inajin yana waje kasan
halinsa da kunya karshenta ya ki shigowa."
A waje kuma abokansa ke tambayar juna ko ya shige ciki
ne domin basu ganshi ba.
Babu wanda ya saka damuwa a ransa har aka gama
daurin auren kowa yana tunanin yana wani wurin.
A can gidansu kuma Haj Yalwa ce ta kira wata yarinya
cikin 'yan uwansu tace ta duba mata kowane bandaki na
gidan ta dauko bota a cika su da ruwa a ajiye a waje
saboda abokan Baba. Idan sunci abinci zasu yi shirin
sallar Juma'a.
Yarinyar tayi ta zagaye tana dauko buta. Kofar bandakin
dake cikin dakin Umar ce ta kasa budewa sai ta koma
ciki ta fadawa Nasiba. Tare suka dawo suka yi ta kokarin
budewa suka kasa ga ruwa kuma ya fara fitowa ta
karkashin kofar bandakin. Nasiba ta saka kunne jikin
kofar taji alamun famfo yana zubar da ruwa. Mama suka
sanarwa tace a samo wani ya balle kofar saboda kada
ruwan bangaren ya kare tunda tanki ne. Abu ya hada da
mata suka kasa budewa ga ruwan yana yawa.
Dole suka hakura har Allah Yasa aka fara dawowa daga
wurin daurin auren. Lokacin duk sun tsince kayan dake
kasan dakin saboda ruwa. Umar na shigowa Mama ta
hau shi da fada shi bai ma san laifin da yayi ba sai da
tace yaje ya bude kofar bandakin shi. Yayi mamakin jin
kofar a rufe ya saka iya karfinsa ya soma dukanta. Babu
kowa a dakin sai shi kadai don Mama tace babu mai
taya shi gyarawa. A bugu na hudu kofar ta bude yayi
tozali da abinda yayi matukar razana shi.
Abubakar ne kwance cikin ruwan da ya hade da jini daga
kasan kansa ga sabulu can a gefen kafarsa ta hagu
alamun zamewa yayi.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 2
Batul Mamman💖
Lokaci guda Umar ya gigice jikinsa ya hau bari. Da sauri
ya shiga bandakin ya zauna cikin ruwan kusa da
Abubakar sannan ya daga kansa ya dora a kan cinyarsa.
Da kyar ya iya cewa "Yaya".
Babu wata alamar motsi a tare da Abubakar. Umar ya
shiga jijjiga shi yana kiran sunansa. Duk da haka
Abubakar bai motsa ba. Iyakar tsorata Umar yayi don ji
yake kamar zuciyarsa zata buga. Wasu zafafan hawaye ya
soma yi a hankali yace "Yaya Abubakar ka tashi an daura
auren."
Nan ma dai shiru yaji. Tunaninsa gabadaya ya kulle ya
rasa me zaiyi ya taimakawa dan uwansa. Da sauri ya
tashi ya fara kokarin daga shi ya fitar dashi daga cikin
ruwan, amma yayi masa nauyi domin duk jikinsa a sake
yake. Ya sake gwadawa yaji tabbas bazai iya ba sai ya
tashi ya fita tare da rufe dakin da mukulli.
Duk wanda ya ganshi da kaya a jike ga alamun jini a
gaban sabuwar shaddarsa da tasha dinki sai ya tambaye
shi ko lafiya. Babu wanda ya bawa amsa ya wuce dakin
Mama.
A tsaye ya ganta a gaban mudubi tana saka sarka. Kafin
yayi magana ta juyo da sauri saboda ganinshi da tayi ta
mudubin. Gaban rigarsa ta nuna tare da zuwa gabansa ta
tsaya "Umar me ya faru? Ciwo kaji garin gyaran
bandakin? "
Maimakon yayi magana kawai sai ya rungumeta yana
kuka mai tsuma zuciya.
*****
Duk akwatunan kayan Asmau an gama hadasu a wuri
guda. Daya daga ciki ta bude ta dauko wata atampa zata
saka Aina'u ta shigo dakin da gudu sai haki take yi.
"An daura auren. Daga yau dakin nan ya zama nawa ni
kadai" ta fada iyakar karfinta tana murna. Tana gama
fadar abinda ya kawota ta sake ficewa da gudu.
Su Walida suka soma guda suna yiwa Asmau tsiya. Harda
masu yi mata wakar ta zama dauko riga....ta zama dauko
hula....ta zama dauko wando....
Duk baki irin nata jikinta sai da yayi sanyi ta kasa biye
musu kamar yadda ta saba. Ji tayi zuciyarta tana bugawa
da karfi har abin ya bata tsoro kawai sai ta soma kuka.
Hankalinsu ya fara tashi. Walida ce ta rungumeta
maimakon ta bata hakuri itama sai ta fara kukan. Wata
'yar kanin baban su Asmau ce tace "haba Walida
maimakon ki bata hakuri sai ki biye mata. Yau ai ranar
farinciki ce ba kuka zakiyi ba. Ki tashi kiyi nafila ki
godewa Allah da Ya nuna miki wannan rana."
Jiki a sanyaye Asmau ta saka kayanta ta dora hijab ta
tayar da sallah.
*****
Gaban Mama ya fadi ta dan ture Umar daga jikinta. Ta
soma kokarin daga masa riga ta ga ko ciwo yaji ya zubar
da jini da yawa haka.
"Mama jinin Yaya Abubakar ne".
Jin maganar tayi har tsakiyar kanta. Jinin Abubakar
kuma? Abubakar din da ta tabbatar yana tare da
abokansa yanzu suna shirin zuwa wurin reception din da
zasuyi. Cikin rashin fahimta tace "wane irin jini? A ina
kaga Abubakar din?"
Umar yace "yana toilet dina ya suma".
Mama bata jira ya sake magana ba ta fita daga dakin da
sauri yana binta a baya. Matan dake cikin gidan suna ta
tambayar abinda ke faruwa. Ganin basu tsaya basu amsa
ba suka bi bayansu.
A kofar dakin Umar suka tsaya ya saka mukulli zai bude
kofar Abdulhalim ya shigo yana fadan Abubakar ya bar
mutane suna ta cigiyarsa har Baba sai da yayi ta fada.
Umar dai bai kula shi ba ya bude kofar Mama ta ture shi
ta shiga da gudu. Inda ya barshi a kwance suka sake
samunsa.
Abdulhalim ya karasa gabansa da sauri yana tambayar
Umar me ya faru. Da taimakon Umar suka dora shi a kan
gado daga shi sai dogon wando a jikinsa. Mama ta fada
kanshi tana jijjiga shi tana kuka.
Matan dake kofar dakin suma suka soma kukan. Nan da
nan aka kirawo 'yan uwansa mata. Abdulhalim ya kira
wani abokinsa likita da yazo wurin daurin auren ya
bukaci ya karaso gidansu da gaggawa. Dakin duk ya rude
da kuka duk da har yanzu basu san ainihin me ya same
shi ba. Sai da Abdulhalim yayi da gaske ya iya sawa suka
fita.
Cikin mintuna kadan likitan ya karaso. Yayi mamakin
ganin angon kwance jini har ya soma jika zanin gadon.
Umar ne yayi masa bayanin yanayin da ya tsince shi a
ciki. Abdulhalim yace "bari mu saka shi a mota mu tafi
asibiti. Bana so mutane su ganmu. Zanyi kokarin kawo
motata baya sai a fita dashi." yana gama magana ya fita.
Kabiru ya duba kan Abubakar inda ya fashe sannan ya
taba kirjinsa da tsintsiyar hannunsa. A razane ya dago kai
Mama ta kalle shi da jajayen idanu tace "ya cika ko?"
Yadda ta tsare shi da idanu bai isa yayi mata karya ba.
Sunkuyawa yayi ya sake bincika shi sosai sannan cikin
murya mai rauni yace "Mama sai dai muyi hakuri....".
A take ta zube a jikin Abubakar a sume. Su Suwaiba sai
kuka suke yi suka dagata. Kabiru ya fara kokarin taimaka
mata. Kuka kowa na dakin yake yi sosai. Tun kafin
Abdulhalim ya karaso yaji sautin kukan ya shigo a guje.
Umar ya fara hangowa durkushe yana kuka ya shigo ya
tarar Kabiru yana danna kirjin Mama. Wani irin
numfashi taja sannan ta bude ido da kyar.
Mikewa tayi tana kuka ta koma bakin gadon inda har
ansa gefen zanin gadon an rufe Abubakar. "Allah Ya
jikanka Abubakar. Na yafe maka duniya da lahira. Allah
Ya sa mutuwa hutu ce gareka."
Ana amsawa da amin kuka yana karuwa.
Duk dauriya irin ta Abdulhalim shima kukan yake yi ya
kama hannun Kabiru suka fita. Suna fitowa ya fara
hango kawunansa da sauran abokansa da na Abubakar.
Wurinsa suka taho suna tambayarsa ina ango. Bai iya
cewa komai ba sai hawayen da yake zubarwa. Kabiru ne
ya iya basu amsa ya sanar dasu halin da ake ciki.
Gabadaya farfajiyar gidan ta rude da addu'a. Tashin
hankali mara misaltuwa aka tashi dashi. Abubakar ya
rasu daidai lokacin daurin aurensa.
Maza sai kai kawo suke yi cikin dan kankanin lokaci
labari ya isa kunnem Alh Adamu wanda dama suna
hanyar shigowa gidan da abokansa. A gigice ya shigo ya
wuce dakin Umar inda su Yalwa suke da sauran
'ya'yansu. Suna ganinsa kuwa su Nasiba suka rungume
shi suna kuka. Duk wanda yake gidan sai ya tausaya
musu wannan tashin hankali da suke ciki. Shi kanshi Alh
Adamun da kyar yayi ta maza da taimakon dattijai
abokansa suka sa duka matan suka fita domin a yiwa
Abubakar wanka idan sun sauko daga sallar Juma'a sai a
kai shi.
*****
Jafar shine wanda yake bin Shema'u ita kuma Asmau
take binsa. A gabansa Kabiru yake fadar rasuwar
Abubakar. Saboda firgice bai san da yadda kafafunsa
suka kawo shi gida ba.
Masu kidan kwarya ya hango suna ta jera kayan kidansu.
Zuciyarsa ta sake tsinkewa da ya tuna halin da kanwarsa
zata shiga. Dama tun a bakin gate ya goge hawayensa
saboda gudun tambaya. Yana shiga falo aka fara
tambayarsa ko 'yan daurin auren sun watse ana son kai
Asmau wurin kakarta tayi mata nasiha kafin 'yan yini su
kara cika gidan. Jafar yace akwai sauran mutane sannan
ya nemi jin inda Umma take.
A bayan gida ya ganta suna magana da kanwarta Anti
Bintu. Umma na ganinshi tace "baban Yaya har kun
dawo? Ka ce zaku reception ko kaya ka dawo canzawa?"
Jafar ya ji kamar ya fasa fada sai dai kuma babu yadda
zaiyi. Idanunsa suka kada sukayi jazur yace "Umma Allah
Yayiwa Abubakar rasuwa".
Daga ita har Anti Bintu a tare suka ce "Me?"
Jafar yace "yanzu muka dawo daga wurin daurin aure
Yaya Abdulhalim yake fada...." maganar tasa makalewa
tayi saboda kukan da ya zo masa.
Suma kukan suka fara. Wannan tashin hankali da yawa
yake. Fuska sharbe da hawaye tana salati Umma ta shiga
ciki ta tafi daki. Anti Bintu ta daure ta leka dakinsu
Asmau ta kirata.
Tun da ta taso gabanta ke matsanancin faduwa tana ta
karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil.
Kafin ta shiga dakin Umman taji muryoyi suna cewa
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.....a razane ta shiga
Shema'u ta taso ta rungumeta. Kokarin ture yayarta tayi
bakinta har rawa yake yi tace "waye ya rasu?"
Bazata iya tuna muryar wadda tace "sai dai hakuri
Abubakar ya rigamu gidan gaskiya" ba.
Kamar saukar aradu haka Asmau taji zancen sannan
numfashinta ya fara kokarin daukewa. Daga nan bata
sake sanin inda take ba sai farkawa tayi a gadon asibiti.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽3
Batul Mamman💖
_Afuwan Qasim Inspector ya zama ba ACP please_
*GA MASU NEMAN BOOK IDAN AN WUCE KU SAI A
DUBA www.fikrahwriters.com.*
Kusan minti biyar kenan da ta farfado amma ta kasa
bude idonta. Tsoro take ji idan ta bude za'a sake fada
mata wannan mummunan labarin da take tunanin taji a
mafarki.
Kasakasa take jin muryar su Umma a dakin ana ta
tambayar ya jikin nata. Wannan ya tabbatar mata ba
mafarki take yi ba. Lallai ta rasa Abubakar har abada. Ji
tayi inama daga wannan kwanciyar itama mutuwar ta
dauketa. Ya zata yi da rayuwarta ba tare dashi ba? Ita da
Abubakar masu rikon sirrin juna ne. Mutuwarsa komai
daren dadewa zata fallasa sirrin da suka boye. Sirrin da
ya kara musu soyayya da mutunta juna saboda rashin
gudun juna da suka yi. Hawaye ne ya zubo ta gefen
idonta. Walida ce ta lura da hawayen tace "Umma ta
farfado".
Haj Bara'atu ta dawo gefen gadon ta zauna tare da rike
hannun Asmau.
"Ki bude idonki Asmau kinji. Ko ruwa ne ki tashi ki sha.
Kin dade a kwance gashi har la'asar ta wuce".
Subhanallah! Ta tabbatar ta rasa Abubakar kenan. Garin
yaya aka barta a kwance har ta kai yanzu ba'a bari ta
sake ganinsa ba? Ko bata tambaya ba tasan tuni
Abubakar yana makwancinsa. Sake runtse idonta tayi.
Gara ta cigaba da kwanciyar har nata lokacin ya yi.
Umma ta kalleta da tausayawa kwalla ta cika mata ido
tace "kiyi hakuri Asmau. Shima ba gaggawa yayi ba. Mu
kuma da kike ganinmu a nan ba jinkiri muka yi ba. Duk
mai rai yana da wa'adin da Allah Ya dibar masa na
rayuwar duniya. Mutuwa nada daci amma babu abinda
hakuri da tawakkali ya bari."
Maganganun Umma suka sake saka mutanen dakin kuka.
Asmau kuwa taki bude idon. Duhun da take gani ido rufe
ya fiye mata akan hasken da babu Abubakar a cikinsa.
Duk yadda aka rinka rarrashinta sam taki yarda ta bude
idonta balle ta tashi zaune.
Suna haka suka ji sallamar Haj Yalwa da Abdulhalim. Ita
da Umma suna hada ido sai kuka. Suka rungume juna
suna yi ana basu hakuri. Umma tace cikin kuka "Mama
Yalwa me yasa kika fito? Allah Ya jikan
Abubakar....Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"
Dakin ya sake rudewa da koke koke. Bayan sun dan
nutsu ne Mama ke tambayar ya jikin Asmau.
Umma ta dan tabe baki "tana jinmu tun dazu ta farfado
amma taki bude ido. Mama Yalwa ni dai banso fitowarki
yanzu ba. Mutane zasuyi ta cigiyarki a gida. Da zamu
samu ta tashi muma duk gidan zamu taho yanzu."
"Zamana a gidan bazai dawo dashi ba Umma. Komai na
gani ji nake kamar karya ne Abubakar yana nan."
Tashi Mama tayi ta koma gaban gadon da Asmau take
kwance tana hawaye. A hankali Mama ta tayar da ita
zaune ta rungumeta a jikinta tana shafa mata baya.
Abdulhalim yana tsaye daga bakin kofa zuciyarsa
cunkushe da bakinciki.
Cikin nutsuwa Mama ta soma magana "Asmau kuka ba
soyayya bane tsakaninki da Abubakar. Kiyi masa addua
da fatan samun rahmar Mahaliccinmu. Da iliminki
amma ace kin kasa karbar kaddara? Dukkanmu nan
jiran lokaci muke yi. Ki daure ki tashi indai ba kina son ki
nuna cewa kinfi karfin jarabta daga Allah ba."
Jin haka Asmau ta bude idonunta da suka kumbura da
kyar. Dai dai ta rinka kallon mutane kafin ta sake
fashewa da wani kukan mai shiga rai aka shiga tayata.
Babu mai bawa wani hakuri sai Abdulhalim.

Please Login or Register in order to submit comment