Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yake rufewa. Ko kallonta baiyi ba da zai wuce
tana ta masa magiya.
Washegari tun kafin yazo shagon ta iso. Yinin ranar da ta
ga babu mutane sosai sai ta shiga ta roke shi. Tun yana
mata fada ta fita har ya dena kulata sai ta ga wani zai
shigo ta fice a sanyaye.
Dansa Abba ya sake kawo masa abinci amma yau bai bi
ta kanta ba. Yana ciki yana cin abincin ne ya jiyo kakarin
amanta. Tun awarar jiya bata sake samun wani abincin
ba.
Kamar ya share sai ta bashi tausayi ya dauko flask din ya
mika mata. Idanunta sun kara fitowa waje sai hakora
gayau kamar ta shekara tana jinya. Kusan fizgar flask din
tayi ko wanke hannu bata yi ba ta soma cin abincin.
Abinda bata taba ji bane ya faru a wannan lokacin. Motsi
taji a cikinta wanda ya kara tabbatar mata lallai ba ita
kadai take rayuwa ba. Yanayin da ta shiga da jin motsin
yasa ta farinciki ta dafe cikin. Tunowa da Abubakar da
halin rayuwarta kuma yasa ta koma yin kuka. Abincin da
bata iya cinyewa ba kenan.
Da Sada zai tafi ta mika masa flask din yace ta rike ya bar
mata. Yana kallonta ta tafi har ta bace masa.
*****
Sau biyu kenan Rashida tana fadawa maigidanta ta kai
masa ruwan wanka sai yace to ina zuwa. A karo na uku
ta zauna kusa dashi cikin damuwa.
"Baban Abba me ya faru ne? Allah Yasa ba laifi nayi ba."
Dan murmushi Sada yayi yana kallon abar kaunarsa.
"Ko kadan Maman Abba. Bari nayi wankan dai."
Sai da ya gama cin tuwo sannan ya bata labarin Asmau
mai zuwa kofar shagonsa.
"Ni bansan daga ina take ba sai dai ta bani tausayi. Muna
ganin kanmu kamar marasa arziki amma wallahi cikin
rufin asiri muke akan wasu. Tsorona daya kada taje
wurin wani mara imanin ya bata maganin."
Rashida tace "to ai dama kaine kullum kake ganin kamar
shagonka kadai baya wadata mu. Amma gashi yara hudu
duk suna makaranta kuma bama rasa abinci.
Idan bazaka damu ba gobe sai na kawo maka abincin da
kaina na ganta. Kila idan na bata shawara ta hakura da
zubar da cikin ta koma gida".
*****
Asmau ta dauko robar da Uwargida ta bata. Tana son sha
kuma har ranta bata son zubar da cikin. Dama gudun
zubarwar yasa ta fito daga gida. Dan motsin nan da taji
ya sa ta kara son abinta. Robar ta dauka ta zubar da
kadan a bakin rariya sannan ta mayarwa Uwargida.
Bakin Uwargida a washe tace
" nan da wayewar gari ma yana iya zubewa. Kinyi kyan
kai 'Yar Da6as."
Yau ma ta riga Sada zuwa shagonsa. Ita kanta bata san
me ya dawo da ita ba. Da yazo har kasa ta durkusa ta
gaida shi. Ya amsa mata fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Yayi mamaki da ko sau daya bata sake batun maganin
ba. Tana dai zaune ne kawai a gefe guda.
Wuraren shabiyu wata mace ta sha katon mayafi ta iso
kafar shagon da flask din abinci. Matar tayi mata
murmushi Asmau ta gaisheta. Sada ya fito daga cikin
shagon yace "wannan ce yarinyar".
Rashida taji tausayin Asmau ba don komai ba sai don
yanayin da ta ganta. Har wani wari take yi saboda rashin
wanka. Sada yace su shigo ciki ya dan kara kofar alamun
ko anzo kada a shiga.
Asmau na zaune a kasa a gabansu Rashida tace ta fada
musu daga ina take kuma ina uban dan dake cikinta.
"Kada kiyi mana karya domin kuwa Allah Yana
kallonmu".
Karo na biyu kenan tana bada labarinta. Kafin ta gama
Rashida tayi ya6e ya6e da hawaye don tausayi. Mata da
yawa idan an tambayesu game da ciki a irin wannan
yanayin sai suce fin karfi aka yi musu. Amma wannan
yarinyar ta zabi ta fada musu abinda suka fi tunanin
gaskiya ne. Wato biyewa rudin shaidan da son farantawa
masoyi. Shi kansa Sada yaji tausayinta matuka. Lokaci
guda tarbiyarta ta wargaje a dalilin kawa da kafafen sada
zumunta.
Waje suka ce ta fita ta jira su. Muhawara sukayi inda
yace su mayar da ita gida Rashida tace kada ta koma sai
ta haihu ta yiwu iyayen su yafe mata idan suka ga dan a
hannu. Duk da suna tsoron halin Dan Adam yanzu. Kayi
masa rana yayi maka dare amma zukatansu sun amince
da taimakonta musamman ma suna jin tsoron kada ta
zubar da cikin ta fada sana'ar banza.
Sada ya rufe shagon suka ce ta biyosu. Babu musu tabi
bayansu tana adduar Allah Yasa alkhairi ne a tattare da
mutanen.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽22
Batul Mamman💖
Zahra 'yar Rabe ta biyu ke zaune tana waya da
mahaifiyarta Laraba wadda Raben ya dade da saki. A
hirarsu ne take fadawa Laraban zancen haihuwar
Shema'u wadda akayi kwanaki goma da suka wuce. Tun
ranar da akayi haihuwar Yassar yazo ya sanar sai akayi
rashin sa'a Rabe da Zahran ne kadai a falon. A wurin ya
ci mutumcin Yassar sannan yace da Zahra kada ta
fadawa Hajjo babu mai sake zuwa gidan Bara'atu.
Laraba duk ta gama sauraren 'yarta tace mata su kara
hakuri da babansu. Dama ita ta bata shawarar dagewa
taje bikin Asmau. Tace idan ta shigo Kano zata zo tayiwa
Umma jajen abinda ya sami Asmau da barkar Shema'u.
Hajjo tana tsaye a bakin kofa ta fahimci duk hirar Zahra
da Laraba. Ko kwanaki uku da suka wuce sai da ta cewa
Rabe wai har yanzu Shema'u bata haihu bane yace wa ya
sani ne. Bara'atu da bakin hali kuma. Ta rasa gane irin
wannan tsana da yake nunawa iyalin dan uwansa.
Dakinta ta koma jiki a sanyaye ta dauko mayafi ta fito.
Karnukan Garzali ne suka yo kanta ba shiri ta koma ciki.
Dakinsa ta je yana bacci ta daka masa duka a baya. Shi
babu arabi babu boko sannan auren ma ya gagara. Sai
dai yaje yawo ya dawo gida ya kwanta bacci.
A zabure ya bude ido ganin wace ke kansa ya turo baki
"haba Hajjo yau kuma me nayi zaki doke ni? Na rantse
jiya ban sha komai ba. Sansana bakina kiji".
Ta kau da fuska "Allah Ya tsareni na kai hancina bakinka.
Ni tashi ka daure karnukan ka fita zanyi. Ka mayar mana
da gida kamar dandalin 'yan daba. Motsi kadan sai
haushin karnuka."
Dariya yayi tare da zuro kafafunsa zai sauko daga kan
gadon. Daga bayanta taji ance "ina zaki je?"
Gabanta sai da ya fadi don firgici ta juya tana kallon
Rabe wanda bata san ya dawo gida ba. Murmushin da
bai kai zuci ba ta kakalo
"Yaushe ka dawo Alhaji?"
Ya basar da tambayar. "Naji kina cewa zaki fita".
Kamar ba mahaifiyarsa ba duk ta kidime tace "uhmm
dama gidan waccan mara kunyar zani. Ashe Shema'u ta
haihu shine ko ta aiko mana. Ai bata isa ta rabamu da
'ya'yan Shuaibu ba ko?"
Rabe ya soma jin tsoron yawan ambaton su Bara'atu da
take a kwanakin nan sai ya dan dake.
"Yanzu a kanta zaki fita cikin ranar nan? Ki kyaleta kawai
da halinta. A ce har 'yar dan uwana ta haihu bamu ji ba
kawai don bata daukemu a bakin komai ba. Ni daga
yanzu na kafa doka babu mu babu su. Tunda haka ta
zaba kowa yayi ta kansa."
Hajjo ta jinjina kai tama mamakin yadda yake gilla mata
karya haka. Ta tabbatar maganar da Zahra keyi a waya
ba karya bane. Ta sake gwada sa'arta ta hanyar cewa
"Wai dama nace muje ko tare da kai ne mu dan zagesu
mu huce haushi"
Juyawarsa yayi don kada ta sake jan zancen.
" Koma daki kiyi kwanciyarki ki huta Hajjo".
Tana kallo ya tafi itama ta juya zata koma dakinta.
Hawaye ne ya sauko mata wanda bata san dalilinsa ba ta
goge da habar zaninta sannan ta koma daki.
Garzali da bai tanka musu ba yaji tausayin mahaifiyarsa
ya ratsa shi. Ya rasa dalilin da yasa dukkansu har Yaya
Abu da Yaya Lami basu da katabus sai abinda Rabe yace.
Amma zaiyi kokari ko yaya ya kai Hajjo taga jikokinta
tunda wulakancin da suke musu yasa suka dena zuwa
gidan.
A daki Rabe ya kasa sukuni. Sagira na masa magana ya
daka mata tsawa. Dama ba wani matsayi gareta a
wurinsa ba. A duniya babu matar da yake matukar so
kamar Bara'atu duk da girma ya kamasu. Sai kuma
batun Malamin tsibbunsa. Dama lokaci lokaci yake sake
biya a toshe bakin Hajjo da 'yan uwansa. Yanzu idan
asirin ya karya yasan Hajjo cewa zata yi su tashi daga
gidan Bara'atu ta dawo. Matsalar idan suka tashi basu da
wurin zuwa. Ya riga ya sayar da gidansu na kofar
mazugal ya mutstsike kudin batare da sannin kowa ba.
*****
Baaba Ta Annabi tana zaune kofar wurin girki tana
tsintar wake taji sallamar yayarta Hassana wadda suke
kira da Yaya Tagwai. Farantin waken ta ajiye ta tarbo su
cikin farinciki.
Ta Annabi ta kalli 'yar daya yayan nata Usaini tace "auta
ba kya laifi kullum kina kuturin Yaya Tagwai. Naga alama
idan anyi bikinki tare za'a kaiku."
Yaya Tagwai tayi murmushi tana kallon Harira autar dan
uwanta . Ita Allah bai bata haihuwa ba shine ya bata
Harira take ruko duk da a gida daya ma suke da zama.
Tabarma Ta Annabi ta dauko Harira ta shimfida musu
suka zauna aka gaisa. Ta tambayesu ya suka baro
mutanen Misau.
Sai da suka ci abinci ne Yaya Tagwai tace ina sauran
yaran gidan. Ta Annabi ta fada mata sunje biki ne a
dangin Babansu. Ita ma girki zata karasa ta tafi.
Yaya Tagwai tace " gara da nayi sa'ar ganinki. Ke Harira
tashi ki tafi gidan yayarki kafin nazo na sameta ita ma."
Fitar Harira ke da wuya Yaya Tagwai ta kalli kanwarta rai
a bace "kin kyauta Ta Annabi, wato don ni ban haihu ba
shine kika kira Usani kina sanar dashi katobarar da
'ya'yanku suka yi. Allah Yasa ina labe a bakin kofa naji
duk abinda kika fadawa Ado ya sanar dashi. Don
shashanci sai ji nayi yana sanya musu albarka. Sai da na
kare masa tanadi na taho. Duk tsiyarku nice babba dole
kuyi yadda nake so daga ku har 'ya'yan naku."
Ta Annabi ta dukar da kanta. Yaya Tagwai akwai rikon
zumunci sai dai bata da hakuri. Hakuri ta bata sannan
tayi mata bayanin yarinyar da Sada da Rashida suke riko.
Sada da Rashida auren zumunci suka yi. Shi Sada dan Ta
Annabi ne ita kuma Rashida 'yar Kawu Usaini. Tun farkon
zuwan Asmau yayiwa mahaifiyarsa bayani a kanta kuma
ta nuna amincewarta. Daga baya ne ta yanke shawarar
sanar da Usaini don yasan me yake faruwa.
Bayan ta gama bayanin Yaya Tagwai taja dogon tsaki.
"Ina tsammani yarinyar dai da asirinta tazo gidan. Idan
ba haka ba waye zai ajiye mace mai ciki a gidansa ba
dangin Iya ba na Baba. Ni zanje gidan na same su. Lallai
ne su koreta ko don tsare lafiyarsu da ta yaransu. Wa ya
sani ma ko mayya ce ko kuma duk abinda ta fada musu
karya ne."
ABINDA AKE GUDU🙆🏽23
Batul Mamman💖
Hanjin cikin Rashida sai da ya kada da Harira ta gama
fada mata dalilin zuwansu.
"Bari na kira Baban Abba na fada masa kafin ta karaso
gidan nan."
Ta dauko wayarta sai dai tayi ta kira Sada bai dauka ba.
Harira tace "kema Yaya me zaisa ki amince ku ajiye
matar da baku sani ba. Wallahi yanzu duniya babu
gaskiya."
"Na sani Harira. Sai dai karki manta mu musulmai ne.
Idan har zamu biyewa halin mutane yanzu ko sadaka
bazamu bayar ba. Kamar yadda Baban Abba ya fada kayi
komai saboda Allah. Idan mutum ya cutar da kai yayiwa
kansa kuma dama faruwar hakan rubutaccen al'amari
ne. Asmau bata da matsala ko kadan,sai kin zauna da ita
zaki gane hakan".
Suna hirar Asmau su Abba suka dawo daga makarantar
boko. Dama jira tayi su dawo ta basu mukulli ta tafi
gidan bikin da su Baaba Ta Annabi zasu je. Yanzu dole ta
hakura tunda Yaya Tagwai ta zo gari.
Sai biyar da rabi Yaya Tagwai ta iso gidan tun daga bakin
kofa take fada.
Rashida tayi tsuru tsuru da ita har ta shigo ciki. Gaisuwar
ta ma bata amsa ba sai fadan rashin hankalinsu da ta
gani sun ajiye matar da basu san asalinta ba. Tana
wannan fadan Asmau ta shigo a gajiye tana jan kafa
saboda tsufan cikinta.
Sallama tayi ta shigo ganin baki ta durkusa da kyar ta
gaishe da Yaya Tagwai. Kamar gaske ta saki fuska
"maraba da tsintacciyar mage. Babu kunya kike yawo da
cikin shege a cikin gari."
Asmau tayi shiru tana kallon Rashida wadda kunya duk
ta lullubeta. Rasa abin cewa tayi ita kuwa Yaya Tagwai ta
cigaba da magana
"Rashida yanzu wannan mai kwalakwalan idanun kika
ajiye a gidanki da sunan taimako. Kina kallon yadda
jikinta ya mulmule babu mai cewa daga gidansu ta
gudo."
"Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Idan kika ji labarin
yarinyar nan sai kin tausaya mata. Kaddara ce ta afka
mata. Adduarmu Allah Ya kare 'ya'yan musulmi daga
fadawa makamancin halin da ta tsinci kanta a dalilin
sharrin waya."
Hannu Yaya Tagwai ta kai zata doke Rashida "yi min shiru
shashasha. Sai iya bayani rai-rai-rai kamar wata zabiya.
Zabgegiyar mace kamar wannan kika sani ko barauniya
ce, ko kuma rufeki Sada yayi cikin ma nasa ne".
Kukan da Asmau take yi ta tsayar ta dago kai da sauri
tana kallon Yaya Tagwai.
"Wallahi duk abinda na fada ba karya nayi ba. Kuma ban
taba ganin Kawu Sada ba sai a garin nan da ya taimake
ni. Kiyi hakuri don Allah idan zuwana ya bata miki rai".
Rashida ma hawaye take yi tace "na yarda dake Asmau
nasan amana ce a tsakaninmu.
Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Da zarar ta haihu
zamu mayar da ita gaban iyayenta".
Ta juya wurin Asmau da take ta zubar da hawaye.
"Tashi ki koma dakinki. Bani mukullin Kemis din nasan
ya kusa dawowa ya karba."
Su biyun Yaya Tagwai ta ke bi da kallo cike da mamaki."
Mukullin wane kemis din ne?"
Rashida tayi shiru ita kuma Asmau ta tashi ta tafi dakinta.
"Nace mukullin wane kemis din ne?"
Rai a bace Rashida tayi mata bayanin tsarin da suke yi na
zaman kemis da Sada.
Hannuwa ta shiga tafawa tana salati.
"Aahaf, ni nasan ba a banza ta barku ba. Yanzu hanyar
samun naku ma tare kuke yin komai da ita. To na rantse
sai ta bar gidan nan ko kunki ko kunso. Bazan koma
Misau ba sai naga abinda ya turewa buzu nadi."
Asmau tana daki tana jin fadan Yaya Tagwai da muryar
Rashida da Harira suna bata hakuri. Kuka take yi sosai
tana cike da fargabar abinda zai faru a gaba.
Har kusan magariba Sada bai dawo ba. Dole Yaya Tagwai
ta tashi ta koma gidan kanwarta saboda idan duhu yayi
sosai ba gani take da kyau ba.
Gidan shiru har Sada ya dawo Rashida ta fada masa
abinda ke faruwa. Ko zama baiyi ba ya wuce gidansu sai
dai shima babu sa'a. Fada yasha sannan tace ya tashi ya
bata wuri.
Haka suka kwana gidan kamar babu mutane. Asmau
tasha kuka ga wani ciwon kai da ya kama ta.
Da safe Sada ya kirata suka kara kwantar mata da hankali
yace zasu je gidan su sake bata hakuri. Har Kawu Usaini
sun kira yace yana hanya zai zo a taru a bata baki. Batun
zuwa kemis kuwa ranar babu ita.
Adaidaita sahun ya karbo bayan yaran sun tafi
makaranta sannan suka fita shi da Rashida da Harira da
ta kwana a gidan.
Ba suyi minti biyar da fita ba Yaya Tagwai ta shigo tare da
kanin Sada mai suna Habu. Asmau na daki taji
sallamarta. A tsorace ta fito ta bude mata kofa ta bata
hanya ta wuce.
Yaya Tagwai ta soma kiran Sada, Asmau ta fada mata sun
fita.
"To tunda saboda ke dama nazo ki fada min iyakar
gaskiyarki. Shin cikin nan na Sada ne ko wani wanda ya
sani?
Asmau ta girgiza kai tana hawaye.
"Alhamdulillahi tunda ba cikinsa bane ina so yanzu
yanzu kafin su dawo ki fita ki bar gidan nan."
Gwiwa a kasa Asmau ta durkusa tana rokonta. Yaya
Tagwai ta dubi Habu
"Kai da nazo da kai meye amfaninka ne? Ja min ita ka
datse kofar gidan. Wallahi idan kika sake dawowa gidan
nan sai na kirawo miki 'yan sanda. Haka kawai kin
tsaface min yara basa jin maganar kowa sai taki. Kin
gama karuwancinki zaki nemi bayin Allah ki hadasu da
wahala. In dai cikin nan ba na dana bane to ki kama
gabanki".
Asmau tana kuka tace "ki taimakeni don girman Allah.
Bani da wurin zuwa idan na tafi."
Yaya Tagwai ta harareta "daga bishiya kika fado da zaki
ce baki da wurin zuwa? Tun wuri ki koma gaban
iyayenki."
Ta sake cewa Habu yaja Asmau sai ya kasa saboda
tausayinta da yaji. Yaya Tagwai tace
"Idan baki fita ba zan sa iyayensu su zare hannuwansu
daga kansu. Idan baki sani ba ina so kisan cewa ina da
wannan ikon da kannena".
Jin haka Asmau ta juya zata shiga dakin ta debo 'yan
kayanta. Yaya Tagwai ta tsare kofar dakin. "Bazan bari ki
sake shiga ba bare ki kunna wani tsafin nima naji ina
sonki. Fita tun kafin nayi yekuwa a unguwar nan nace ke
mayya ce".
Habu ma sai da yasa baki akan ta bari ta dauko kayanta
amma taki. Haka ta ja hannun Asmau daga ita sai kayan
jikinta Allah Yasa da mayafi tayi waje da ita ko takalmi
babu. Kuka take yi sosai amma a haka Yaya Tagwai ta ja
hannunta har suka bar layin. Sai da suka yi nisa ta jefa
mata naira dari biyu.
"Matsiyaciya sai ki dauka ki kara gaba wasu masu
tsautsayin su dauke ki amma ba gidan 'ya'yana ba. Allah
Ya isa idan kika dawo."
Kukan Asmau ba karamin tausayi ya bawa Habu ba
amma yana kallo tayi gaba Yaya Tagwai ta kama
hannunsa suka koma gidan Sada.
*****
A gidansu Sada ne Baaba Ta Annabi ta fada musu tun
dazu Yaya Tagwai ta tafi gidan nasu. Suna jin haka suka
kama hanyar gida hankali a tashe. Suka yi rashin sa'a
titin da ya biyo wata mota ta lalace ta hada uban goslow.
Kusan tsalle Rashida tayi da suka iso gida ta fito daga dan
sahun. Tana shiga ta tarar da Yaya Tagwai tana yin boli
boli da kayan Asmau. Kuka ta saka tana tambayarta ina
take Habu yace ta tafi.
Sada na jin haka cikin fada ya tambaye shi hanyar da
tabi ya kwatanta masa. Tare suka bi hanyar ko zasuyi
sa'ar ganinta. Sai dai sunfi awa biyu suna nema daga
baya wani yace ta shiga wata bus amma bai san inda bus
din tayi ba.
Da suka dawo gida Rashida ya gani a tsakar gidan ta
rungume kayan jariran da Asmau take tarawa tana ta
kuka. Yaya Tagwai tace "idan kin gaji kya yi shiru. Irin
wannan kuka da kike yi sannan ace ba aikin asiri bane."
Ayatul Kursiyyu ta shiga karantawa tana tofawa Rashida
a ka wai maganin sihiri. Sada ya dagata ya shigar da ita
daki tana ta kuka. Habu da Harira kuwa sai kallo. Yaya
Tagwai ko a jikinta. Tasan komai daren dadewa zasuyi
mata godiya saboda ta rabasu da masifa.
*****
Yaya Babba ke bacci harda minshari Zubaida ta samu ta
lallaba da kyar ta fito daga gidan.
A iya watannin da tayi duk shegantakar karuwanci 'yar
tsohuwar nan ta koya mata. Tun tana nuna bata so har
ta hakura tana biye mata saboda a rage matakan tsaron
da aka saka mata. Bata taba yarda wani yayi amfani da
ita ba. Tace sai ta koma gidan Uwargida. Yaya Babba bata
damu ba ita dai aikin da aka sakata tayi.
Tunda tazo gidan sai yau ta samu damar fita. Kullum
tana tunanin Asmau. Bata sani ba ko ta haihu yanzu.
Gidan Uwargida ta tafi da niyyar idan Asmau tana nan su
gudu tare. Daga bakin kofa ta hadu da wata cikin matan
gidan.
"Zuby kin dawo?" Ta fada tana kallon irin shigar
Zubaidan da yadda ta kara cikowa.
Zubaida ta rage murya
"Shiga ki kirawo min Asmau bakuwar nan. Don Allah kiyi
sauri ga wannan kada ki fadawa Mama kin ganni." Dari
biyar ta bawa matar ta karba sannan tace "wannan
bakuwar baki dade da tafiya ba ta gudu. Har an sami
wasu bakin biyu bayan tafiyarta."
Zubaida tayi wani murmushi cike da
jindadi."Alhamdulillah nasan taji shawarata ta koma
gidansu."
Daga nan ta dauki jakar kayanta ta juya ita ma. Matar ta
biyota tana tambayar ina zata je Zubaida tayi gaba ko
kulata bata yi ba.
Daga nan bata zame ko ina ba sai tasha ta nemi motar
Kano. Basu dade ba motar ta cika suka hau titi. Indai
bata manta ba Asmau tace sunan umguwarsu Hotoro
layin kwamishina Adamu. Gidansu zata nema don tasan
in Allah Yaso yadda Asmau ke bata labarin Umma zasu
riketa har ta sami mijin aure. Ta dan yi murmushi "ko
me Asmau ta haifa" ko meye ma zata tayata raino tunda
dai taji shawararta ta koma gida. Allah Yasa dai ta gane
gidan.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽24
Batul Mamman💖
Zuciyar Asmau banda zafi babu abinda take yi. Ji take
kamar ta haye tsakiyar titi mota tayi gaba da ita kowa ya
huta. A tunaninta babu sauran mai kaunarta a duniya.
Tana wannan jan kafar ne taji kwandastan wata hayis
yace Hajiya zaki hau? Kai ta gyada tare da shiga motar da
bata san inda suka nufa ba.
Sunyi tafiya mai dan nisa wasu na sauka wasu na hawa
kwandastan nan yana ta tambayarta kudin mota
hankalinta baya wurin saboda kukan da take yi. Wata
mata ce a kusa da ita ta dan taba ta sai ta kula da yadda
kafafun Asmau suka yi futu-futu ko takalmi bata dashi. A
tsorace matar ta ja jikinta gefe ta karewa kodaddun
kayan jikinta kallo. Daga murya tayi iya karfinta tace
"mahaukaciya ce"
Nan da nan hankalin jama'a ya dawo kanta aka fara
cewa za'a sauka. Dreban hayis din ya hau yiwa
kwandasta fadan ya dauko musu mahaukaciya. Tsayawa
yayi suka janyo hannunta aka fitar da ita daga motar.
Bakincikin da take ji ya hanata magana. Wai yau ita ake
yiwa kallon mahaukaciya.
Tana kallo motar tayi gaba sannan ta kula da cewa inda
take ya danyi wajen gari babu gidaje sosai. Ga wani irin
ciwon baya da mara da ya taso mata lokaci guda. Runtse
idonta kawai tayi tana tafiya zafin kwalta yana kona mata
kafa sai ji tayi an taka burki da karfi motar tayi wata irin
kara.
A razane ta bude idonta. Wata mota ta gani mai kyau
ashe da tana tafiya ta dan hau titi bata sani ba. 'Yan
samari biyu ne suka fito suna ta zaginta ta uwa ta uba.
Dukkansu bata jin akwai wanda ya shekara ashirin sai
tsayin kafa kawai. Kayan jikinsu sun nuna yaran sun fito
daga gidan arziki sai dai daga yanayin maganarsu ta kula
a buge suke.
Wanda ya danfi tsahon yayo kanta kamar zai doketa
dayan yayi saurin rike masa hannu
"Haba Annur, duba da kyau mahaukaciya ce. Tunda
Allah Yasa bamu tabata ba kawai zo mu ware".
Mai suna Annur ya ja tsaki "da ka barni na mareta. Haka
kawai zata janyo mana makara a wurin party din. Sai an
gama zabe fine chicks din"
Ciwo ne ya sake kwasarta tayi kasa tana rike baya.
Jajayen idanunta da suka rine don kuka ta daga tana
kallonsu tace
"don Allah ku taimaka min"
Wanda ya hana a mareta yace "kai Annur it seems matar
nan haihuwa zata yi".
"Gaddafi bazan tsaya a wurin nan ba. Kaima kasan yanzu
haka an fara nemanmu a gida. Allah Ya kawo wani amma
ba mu ba. "
Da sauri yaja hannun abokinsa suka shiga mota. Gaddafi
ya leko da kansa ta taga yana kallon Asmau kwance a
kasan gefen titi. Motoci basu da yawa saboda har lokacin
goma na safe bata yi ba. Gashi titin fita gari ne.
Annur ya fizgi motar da gudu Gaddafi yana rokonsa da
su taimaka ko wane gari suka gani su sauketa a nan wani
ya kaita asibiti. Tsaki da zagi Annur ya rinka yiwa
abokinsa kafin ya juyo da motar suka dawo inda take.
Ransa a bace yace Gaddafi ya shigo da ita. Kuma ya
zauna a baya tare da ita saboda kada ta kai masa duka.
Shi duk saurinsa ya isa party din abokinsa da za'ayi a Jos
batare da sun sami matsala a hanya ba domin kuwa ko
license na tuki basu dashi.
Da sauri Gaddafi ya taimakawa Asmau ya shigar da ita
motar. Ciwo ya fara tsananta a gareta sai gumi take yi.
Annur ya soma yiwa Gaddafi magana da turanci
"Tun farko da nasan haka zaka yi min da ban ce ka raka
ni Jos dinnan ba. Amma babu komai zanyi maganinka.
Hmmm yau 'yan matan Jos suna da manyan baki" ya
karasa maganar yana wata shu'umar dariya.
"Kayi hakuri Annur ni kaina bansan meyasa ta bani
tausayi ba. Ji fa yadda take gumi ko magana bata iyawa.
Allah Ya tsinewa wanda yayi mata cikin nan dai"
Ciwon taji ya lafa mata ta kallesu tayi dan murmushi. Ga
dukkan alamu Yassar zai girmesu duk su biyun. Ita ma
turancin tayi musu wanda hakan yasa hankulansu
dawowa gareta
"Wanda yayi min ciki ya rasu fatana Allah Ya jikansa. Ku
kuma ina yi muku fatan shiriya daga Allah kada ku fada
mummunan hali nan gaba."
Annur ya juyo kamar ba shine yake tuki ba yana kallonta
da mamaki dan sauran mayen da yake duk ya tafi "wai
dama ke ba mahaukaciya bace. Gaddafi kaga ka dauko
mana masifa ko? Ke police ce ko 'yar mafiya?"
Kasa bashi amsa tayi saboda ciwo. Yana maida kansa titi
saura kadan ya bugawa wani. A haka ya cigaba da tukin
Gaddafi yana yi mata sannu. Sun isa wani gari yayi
kokarin tsayawa su sauketa sai ya kula da 'yan sanda a
gefen wurin. Dolensa ya sake taka mota yana ta sharara
gudu. Basu tsaya a ko'ina ba sai da suka shigo garin Jos.
A wannan lokacin ba karamin tausayin Asmau duka su
biyun suke ji ba. Wai dama hake ake nakudar gaske ba ta
fim ba. Idan taji ciwo tana addua sai taji suna tayata
suna yi tare. Idan ka matso kusa da motar sai ka zata duk
su ukun suke nakudar, sai sharba gumi suke yi kamar
babu AC a motar . Bakin gate din wani asibiti da yayi
musu kama da na gwamnati suka tsaya. Sai da Annur ya
taimakawa Gaddafi suka fitar da ita daga motar.
Tsoronsu daya kada a kamasu ayi tunanin ko sato ta
sukayi ko suna da alaka da ita.
Cikin tsananin jin ciwo Asmau ta tambayi sunansu suka
fada mata.
"Bansan daga ina kuke ba amma ina muku fatan alkhairi
da shiriya don nasan iyayenku ba rayuwar da suke yi
muku fata ba kenan. A duk inda kuke

Please Login or Register in order to submit comment