Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da murmushi "idan na riga me zaki bani?"
"Zan siya miki mota idan na giyma. Kuma zan kaiki
Makkah da Madina"
"Idan kuma kika rigani me kike so?"
Amatullah tayi dariya harda alamar tunani "zaki goyani
yau har nayi bacci."
"Kin girma fa Ama ga nauyi"
"to bazan ci abinci daye ba. Don Allah Ummi ki goyani"
ta karashe da buga kafa.
Asmau tace "naji shirya 1, 2....." kafin ta kai 3 Amatullah
ta kwasa a guje. Dariya tayi kawai tabi bayanta. Yarinya
sai son goyo bata san ta girma ba. Kyaleta tayi sai da ta
kusa shiga sannan ta bita da gudu. Tana sane ta bari ta
rigata.
Da dariyarsu shiga falon Amatullah tana cewa ta riga.
Asmau ma ta shigo da dariya sai tayi turus daga bakin
kofa. Kamshin turarensa ta fara ji kafin idanunta su
sauka akan Jikamshi. Shadda ce ruwan kasa a jikinsa ga
hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa
girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita
yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta a
kunyace. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a gidansu
ba. Balle da taji shiru bai amsa sakonninta ta hanyar
waya ko text ba.
Dan gyaran murya taji sannan aka ce "muna kusa fa" ta
kalli wurin da sautin ya fito. Subhanallah...
Umma, Hajjo da Ismail ne zaune a wurin. Daburcewa
tayi gabadaya tace "uhmm sauri nake banyi sallar
magariba ba."
Bata jira amsar kowa ba ta shige ciki gabanta na tsananta
bugu. Tana jiyo dariyar Ismail din yana tsokanar
yayansa.
*****
Bandaki ta fada ta watsa ruwa da sauri tayi alwala. Sai da
tayi sallah sannan ta koma gaban madubi ta shafa mai
da gyara fuska. Ba kwalliya ta tsananta ba amma tayi
kyau. Ta rasa kayan da zata saka kada su Umma suce
kwalliya tayi saboda ganin Jikamshi. Sannan kuma bata
son mayar da na jikinta don a gaskiya tayi suyar nama
dasu. Karshe wata jallabiya ta dauko baka mai adon
duwatsu pink. Tana son rigar sosai, Anti Bintu ce ta siya
mata da taje Zaria. Mayafin rigar tasa tayi nadi sannan ta
sami wuri ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta fita.
Umma da kanta ta shigo ta danyi murmushi ganin
Asmau na kallon kasa. Allah mai iko, sai Ya sanya musu
son juna duk da lalaurar dake tattare da kowanensu.
Wannan ma kadai ya ishi bawa aya. "Asmau kije ku gaisa
mana kin barmu da baki kuma kinsan naki ne"
A kunyace tace "ni bansan zasu zo ba."
"Bari na sallame su to. Ina jin gaishemu suka zo gara su
tafi tunda mun gaisa."
Dago kai tayi da sauri amma bata ce komai ba. Umma
tayi murmushi kawai ta godewa Allah. Cikin ikonSa 'yarta
ta sami farinciki a rayuwarta. "Gulma to tashi kada
waccan akun ta cika su da surutu"
Sai da Asmau ta jira Umma ta bar dakin sannan ta fito
falon. Da sallama ta shiga. Ai kuwa Amatullah ta gani
tana ta zuba zance tana bawa Ismail labari yana biye
mata suna dariya. Hajjo kuma da Jikamshi suke tasu
hirar.
Tana shiga Ismail yace "yauwa ga amaryar tamu. Hajjo
ke fa an sallameki. Daga yanzu duk abinda zaki fada ba
ganewa zaiyi ba"
Wayyo Allah, ji tayi kamar ta juya da gudu. Ismail na
tsokanarta shi kuma gogan ya wani zubo mata idanu
yana kallonta yana lumshe ido kamar mai jin bacci.
"Babu inda zani, ni har akwai masu nuna min soyayya
ne. Allah Ya jikan Malam amma muma a zamaninmu fa
ba'a cewa komai"
Ismail yace "Allah Hajjo?"
"Hmmm kaidai bari dannan." Ta fada tana jinjina kai.
Yau fa tunda ta tuno Malam to wanda bai sanshi ba zai
sha labari. Allah Sarki Malam Yahya. Hajjo baki shi kuma
shiru shiru. Shiyasa akayi zaman lafiya duk da rigimarta.
Daurewa Asmau tayi ta gaishe su. Ismail ne kawai ya
amsa, Jikamshi tashi yayi yana dubanta. "Muje na baki
amsa ko"
Hajjo tace "'yan nema kuyi a gabana mana."
Da muryarar nan tasa me sa Asmau jin tafi kowa dace
yace "ga Ismail nan ya fini iya hira da tsofaffi. Ni ga tawa
nan." Ya nuna Asmau.
Amatullah ta taso tana kumburi "Babana kace fa yau da
ni zaka yi wasa banda Ummi"
"Duk yau taki ce. Yanzu ma sako zan bata kinji princess.
Zauna a wurin sabon Baba kafin na dawo"
Asmau na kallonsa ya fita. Ismail yayi mata alama da
hannu tabi bayansa. Sai da tayi dariya a hankali sannan
ta fita. Hajjo tace "oh, yaran zamani baku da ta ido.
Wannan yayan naka Sama'ila yana wani mici mici da ido
sai kafirin iya saye zuciya."
Ismail sai dariya "ko dai za'a koma da ne ki zabe shi ki
bar Malam"
"A'a fa, Malam yafi kowa. Wannan alakoro ne Asmau ta
samu. Ni kuwa nawa shine gangariya"
*****
Wurin motar Ismail da suka zo da ita ya kaita. Barin
dreba ya bude ya nuna mata kujerar yace "zauna"
Zata tambaye shi ina zai zauna ta ga ya tafi hanyar kofa
inda wasu kujerun roba suke farare ya dauko daya. Sai a
lokacin ta zauna kafafunta a waje shi kuma ya dasa
kujerar daga gabanta ya zauna kafarsa daya kan daya.
Ji tayi kamar wadda aka rufe a cikin keji duk ya cike
wurin. Ta kasa kwakkwaran motsi.
Wayarsa taga ya dan turo gabanta ta karanta abinda ke
rubuce a ciki. Text dinta ne na biyun da ta tura masa
kafin su iso gida.
"Ina sonki Matar Jikamshi, don Allah kada kiyi kuka.
Hawayenki yana da tsada. Ba a gaban kowa zaki zubar
dashi ba. Amsar ta gamsar dake ko na kara wata?"
Murmushin da yake so daga gareta take yi amma ta kasa
dago kanta. Kunyarsa ke karuwa sosai a zuciyarta. Ga
wani nishadi da take ji kamshin turaren Jikamshinta ya
baibaye wurin gabadaya.
Dama yasan irin wannan kalamai sai a text. Tana ganinsa
take komawa bebiya. Ranakun da take ajiye kunyarta
kuwa sai taga alamun zata rasa shi ne.
"Dago kanki na baki amsar sakonki na farko. Shine
babban dalilin zuwana"
Dan kadan ta iya daga kan tana sauraronsa.
"Matar Jikamshi Allah Yayi miki albarka. Bani da wata
kalma da zan iya nuna miki matsayinki a zuciyata.
Sakonki ya shigo a lokacin da komai ya rikice min.
Haduwata dake zuwa yau hadi ne daga Allah. Har abada
nasan cewa kinyi min abinda mata da yawa bazasu yi ba.
Ni kuma saboda son kai na amince maimakon na dage
na rabu dake ki auri wanda zaki haihu dashi..."
Bude baki tayi zata yi magana ya sanya yatsansa a saman
lebensa "shhhh, kada kiyi magana. Text dinki yace
komai. Ki barni nima na fadi nawa. Banyi miki alkawarin
cewa idan munyi aure shikenan duk wani bacin rai da
damuwar da kike dasu zasu kau dari bisa dari ba. Amma
Matar Jikamshi zanyi kokari naga na kare hakkinki kuma
na kyautata rayuwarki har karshen rayuwata. Abinda
kike gudu tun farkon da na gabatar miki da soyayyata
bance bazai taba faruwa ba. Kowane mutum yana da
damar fadin son ransa duk da kiyaye bakin shi yafi akan
fadar magana mara alkhairi. Ki sani a dangina ko naki,
makota ko abokan arziki dole watarana sai anyi miki gori
a gabanki ko bayan idonki wannan bani da haufi akansa.
To ina so duk lokacin da aka fada miki maganar da ta
shafi rayuwarki ta baya kuma bana wurin bare na kare
miki ki sani cewa Ishaq yana son Asmau. Ki sakawa ranki
akwai wanda zaki zo kiyi kuka a gabansa ya rarrasheki,
akwai wanda yake kaunarki saboda Allah yake fatan
kasancewa abokin rayuwarki har a aljannah."
Ba sai na fada ba Asmau kuka take yi sosai saboda yadda
kalaman Jikamshi ke ratsata. Shi kanshi a raunane yake
idan ya tuna cewa duk su biyun suna da abin fada a
rayuwarsu.
"Abu na karshe Matar Jikamshi ina so don Allah kiyi
hakurin zama dani. A duk lokacin da kika ji anyi haihuwa
zuciyarki ta kwadaitu da son ina ma kece maijegon to ki
tuna cewa samu da rashi na Allah ne. Da kudi na bayar
da haihuwa da wasunmu sun sayar da komai nasu don
suji kukan jariri a gidajensu. Ki godewa Allah kina da
wadda zaki kalla a matsayin tsatsonki. Ni bani da wannan
kuma na yarda na karbi kaddarata. Ina fatan hakurin da
nake da wanda zaki zo ki tayani muyi ya zama silar
samun rahmarmu a wajen Allah"
Da gaske Asmau take kuka. Abinda ake gudu ya riga ya
faru. Allah Ya kara kare sauran 'yan uwa musulmi. Ji take
duk duniya idan ba da Jikamshi ba bazata taba iya
rayuwar aure da wani ba. Shi kanshi idonsa yayi ja
amma sai ya daure yace "kinsan dai ba'a daura mana
aure ba don Allah ki dena kukan nan. Nafi so ki tara shi
sai ranar da idan kinyi zan daukeki na...."
Da kukan nata da jikakkiyar fuska ta dago kanta tana
murmushi tare da dora hannunta irin yadda yayi a
lebenta "shhhhh Jikamshina kada ka karasa ko na gudu"
Yayi murmushi "ina sane na turaki cikin motar don kada
kice zaki gudu. Share hawayenki kinji Matar Jikamshi.
Kada Umma ta hanani aurenki, kullum nazo sai kinyi
kuka."
Tissue din gaban motar ta zara tana goge hawayen yana
fada mata wuraren da kwalli ya bata. Tace zata duba
madubin motar yaki yarda. Haka ta goge suna kallon
juna suna dariya.
Sun danyi hira yake ce mata sunyi magana da Umma
yana ganin nan da wata uku za'a saka musu rana. Umma
tace akwai bikin Dijan Anti Bintu wata biyu masu zuwa
wanda shima lokacin yaso ayi aurensu. Yasan kafin nan
ya gama gyaran gidansa.
"yanzu da Umma kayi zancen saka rana?"
"Na lura kin mayar dani mara kunyan karshen zamani.
To Ismail ne ya fada musu. Ni shiru nayi ina ta sunkuyar
da kai irin yadda kike yi"
Dariya take yi wanda hakan yake sanyaya masa zuciya.
Yana jindadin ganin ya faranta mata. Sun fi awa daya a
wurin batare da sun san lokaci ya wuce ba. Ismail ne ya
fito da Amatullah a bayansa. Haka nan Allah Ya dora
masa son yarinyar nan. Shi bai ki ba wallahi Asmau tace
ta bar masa ita.
Suna zuwa gaban motar Amatullah tace "Ummi kinga
sabon Baba ya goyani."
Col. Ishaq ya tashi tsaye ya sauko da ita daga bayan
Ismail sannan ya dorata a cinyarsa.
"Idan banyi da gaske ba naga alama zaka yi min kwacen
'ya"
"Colonel ai na gama da kai. Ka taho nan sace zuciyar
Umminta da dadadan kalamai ni kuma ina nawa yakin a
kanta da kayan kwadayi. A takaice dai yanzu nine baban"
Asmau ta rufe ido tace "Yaya Ismail kada muyi haka da
kai"
Jikamshi yace "gara ki kira Musaddiq yaya da wannan.
Shifa bai san ya girma ba. 'ya'ya biyar amma idan yana
barkwanci kamar mara iyali."
"Kada ka zubar min da girma mana soja. Yanzu dai
gaskiya Madam ta damu ban koma gida ba tun fitar safe.
Ummin Amatullah taimaka ki sallame shi mu tafi. Don
ma na fada mata Yayanta na rako zance yau da an
hanani tuwon dare"
Ta fuskanci da gaske Ismail mutum ne mai barkwanci.
Jikamshi ya katse mata tunani da cewa "haka suke daga
shi har matar tasa. Gidansu kamar gidan wasan yara"
"Allah Sarki kace ina gaisheta"
"Fada mata da kanki dai" Ismail ya ciro wayarsa ya kira
Aisha matarsa. Da gaskiyar Jikamshi kuwa don da gaske
Aisha tayi ta janta da hira da wasa kamar ta santa.
Karshe tayi ta jaddada mata ta rike amanar yayansu. Ita
dai Asmau sai dariya kawai. Bayan sun gama wayar
sukayi sallama dasu. Jikamshi kamar kada ya tafi. Ba don
dare yayi ba kuma dai yakamata Ismail ya tafi gida yau
da Umma sai ta koreshi da kanta.
A hanya ne ya dubi kaninsa yace "nagode Ismail da
yadda kake yiwa Asmau da Amatullah "
Idonsa na kan titi yace "Colonel nine da godiya da ka
yafe min maganar da nayi maka rannan. Duk da bana
ganinsa amma na tabbatar shaidan ne irin masu hada
fada tsakanin 'yan uwa ya murde min harshe na fadi
abinda banyi niyya ba"
Murmushi dan uwan nasa yayi "zaka fara ko, kada ka
damu komai ya wuce a wurina in sha Allah. Ka fadawa su
Dahiru idan zasu sami lokaci karshen sati sai muje
Jikamshi ayi magana dasu Kawu"
*****
Ranar Juma'a da yawancin ma'aikata ke tashi da wuri
Col. Ishaq da kannensa maza suka tafi garinsu, Jikamshi
a Katsina garin Dikko...Katsinawa kunya gareku ba tsoro
ba. Kafin tafiyarsu dama Hajiya ta riga ta fadawa Yayanta
da kuma kanin mijinta komai game da Asmau a waya.
Kamar yadda yayi tsammani bai sami goyon baya sosai
daga garesu ba. Wani kawunsa ma cewa yayi indai
saboda rashin haihuwa ne yasa zai auri karuwa, karuwar
ma mai 'ya to akwai zawarawa a gari masu yara ya zaba
a cikinsu don Allah Ya aura amma kada ya gurbata musu
dangi. Su da suka je yin kwana biyu basu sami dawowa
ba sai litinin. Col. Ishaq sai da ya taba rashin kunya aka
sami daidaito tsakaninsa da Kawunan nasa da manyan
Gwaggoninsu. Daga karshe ma dai harda wa'azi da
nasiha ya hada. To anyi sa'a da yake ana ganin girmanshi
gashi kuma da dan abin hannunsa sai suka gama
fadansu suka amince zasu taho Kano nan da sati biyu.
Kamar yadda ya saba ya hadasu da alkhairi kafin ya tafi.
Wannan karon harda kari don kada su bashi kunya ma.
*****
A bangaren su Asmau kuma washegarin da Jikamshi yaje
gidansu Qasim yazo. Ya nuna mata ya janye batun
aurensu kuma yana mata fatan alkairi a zamansu da Col.
Ishaq. Taji kunya sosai tace "Yaya Qasim kayi hakuri da
hukuncin da na yanke a matsayin zabin Allah. Bazan taba
mantawa da abinda kayi mana ba. Duk da kaine babban
abokin Yaya Abubakar amma hakan ba shine yake nufin
sauran su gujemu ba. Tun ranar da ya rasu ban kara jin
duriyar kowa ba sai taka. Nagode Allah Ya baka mace
tagari kamilalliya."
Yayi mata murmushi "babu wata godiya mata zaki nemo
min kawai."
Itama tayi murmshin ga dan hawayenta "to In sha Allahu
zan nema maka kuwa"
"Kada ki dauka wannan abin zai shafi zumuncinmu
Asmau. I am always here for you. Ki daukeni dan uwanki
wanda zaki iya fadawa matsalolinki. Shi kuma soja tunda
yayi min fin karfi ki fada masa aure bazai yiwu ba sai ya
kama kafa dani."
"An gama ranka ya dade" ta fada zuciyarta wasai.
Alhamdulillah dama bata so su rabu ana jin haushin
juna.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽50
Batul Mamman💖
Tun daga wannan lokacin tsakanin Matar Jikamshi da
Jikamshinta wata sabuwar soyayya ke tashi da shakuwa.
Duk wani labarin rayuwarsu da basu sani ba a da yanzu
sun fayyacewa juna. Komai nasu abin shaawa sannan
suna soyayya a tsaftace. Irin hirar nan da zata jawo
budurwa da saurayi su fara sakin layi har a kai ga jin
sha'awar kusantar juna sun nesanta kansu da ita. Kuma
duk da haka idan kaga yadda suke sai sun burgeka.
Wannan ita ce soyayya ta gaskiya. Duk wata hira mai
tado sha'awa sunanta batsa kuma tana cikin jerin
abubuwan da suka kusanci zina indai ba ga ma'aurata ba
wanda Allah SWT Ya umarcemu da mu nisanta
kawunanmu da ita. Allah Ya kara shige mana gaba.
*****
Bayan sati biyu kamar yadda suka yi alkawari kawunnan
Col. Ishaq suka zo daga Jikamshi. Haj Lubabatu ta shirya
musu tarba mai kyau sai da suka ci suka koshi sannan
sauran kannensa maza suka yi musu jagora zuwa gidan
Umma. A nan din ma tun safe ake shirin zuwan nasu.
'Yan uwa da abokan arziki sun taro. Alh Adamu ma da
tasa gayyar duk don a taru a rufawa juna asiri. Baki kam
sun ga karamci kuma sun yaba. Matsalar dai itace
haihuwar Asmau kafin aure. Amma tunda dan nasu yace
yaji ya gani dole su bi yarima su sha kida. Dubu dari suka
bada wanda yasa su Baba nuna a rage. Wani cikinsu dan
tsoho yace ko kwandala bazasu rage ba. Dansu yace lallai
abinda zaa bayar kenan ko sama da haka. Kawu Garzali
sai murna yake. Allah Yayi Asmau zatayi aure kuma zata
auri wanda yake matukar sonta. Adduarsu Allah Yasa
soyayyar ta zarce har gidan aure. Taro ya tashi cikin
mutunta juna aka yi sallama suka tafi.
*****
Asmau kuwa da wuri ta fita amma ta bar Amatullah a
gida. Hankalinta a kwance wannan karon kana ganinta
zaka san amarya ce mai murna da dokin lokacin
aurenta. Da kwatance saboda sababbin gine gine ta isa
gidansu Walida tsohuwar aminiyarta. Har kofar gidan
adaidaita ya kawota. Tana sauka a kofar gidan Walida ta
fito daga makotansu. Hada ido suka yi sai suka tsaya
kallon kallo kowacce tana zubar da hawaye. Duk su
biyun abubuwa da dama suke tunawa wanda suka
wargaza musu rayuwa. Asmau ce ta fara yunkurawa
kafin ta karasa itama Walida ta taho cikin sauri suka
rungume juna. A bakin kofar gidan suka fashe da kuka
sosai suka rike da juna. Mutane kuwa sai kallonsu suke
yi. Sai da suka dan nutsu Walida ta ja hannunta suka
shiga ciki. Antin Walida matar babansu na zaune tana
yankan farce suka shigo. Murna ganin juna suke sosai. A
firgice ta tashi tana nuna Asmau.
"Wa nake gani kamar Asmau?"
Walida tace "ita ce Anti"
Ta karewa Asmau kallo sannan ta tabe baki "to ina
abinda kika haifa. Ai na jima da jin labarin kin dawo
Kano da dane ko 'ya ni ban rike ba. An gama yawon ta
zubar an dawo gida."
Murmushi Asmau tayi, irin wadannan maganganun 'yan
uwa da yawa da Jikamshinta sun fada mata dole ko taki
ko taso sai tayi hakuri dasu. Kuma sanin halin Antin na
kwarewa wurin rashin mutunci yasa bata dauki abin da
zafi ba. Walida ma da a da tasan cewa bata shiru, idan
matar nan tayi mata ramawa take suyi ta cacar baki
kamar kishiyoyi shiru Asmau taga tayi. Ta kama
hannunta suka shiga dakinta. Kan wata kujera suka
zauna Walida tace
"Ashe rai kan ga rai 'yar uwa? Na fidda rai da sake
haduwa dake wallahi"
"Kiyi hakuri Walida. Na dan jima da dawowa amma na
rasa me zamu cewa juna idan muka hadu. Har ga Allah
abinda ya faru dani shekarun baya kika gujeni yasa ban
kara nemanki ba"
Walida ta share kwalla "ki yafe min Asmau, na cutar dake
da na zama sanadiyar koya miki dabi'un da ba naki ba.
Ba haka kawai na gujeki ba amma..."
Asmau tace "kada ki damu. Yaya Qasim ya fada min
kema duk abinda ya faru dake. Mu kuma haka Allah Ya
rubutu mana tama jarabawar" da kuka ta karashe
maganar. Suka taru su biyu suna yi babu mai rarrashi.
Asmau na tuna rasuwar Abubakar da cikin da aka gane
tare da ita a ranar da ya rasu. Ita kuma Walida tana tuno
ranar da mahaifinta ya kamata da saurayi ya zura
hannuwansa cikin rigarta. Wa'iyazu billah wadannan
'yan mata bazasu manta da sharrin social media ba.
Da suka gama kukan ne suka bawa juna labarin irin
gwagwarmayar da suka sha. Walida tayi murna da jin
zancen auren Asmau sannan tayi ta kallon hotunan
Amatullah a waya tana mita ba'a zo mata da ita ba.
Itama ta bawa Asmau labarin irin takunkunmin da
babanta ya saka mata saboda jin labarin cikin Asmau.
Karshe ma ko karatun jami'ar bai bari ta kammala ba
yace sai tayi aure. To gashi shekaru shida babu auren
babu karatun sai zaman gida da zuwa islamiyya. Matar
gidan ta sami yadda take so wurin fadawa Walida
maganganu sai dai ta dena ramawa saboda yanzu
babanta bai damu da lamarinta ba. Indai ba aure tayi ba
shi baiga amfaninta ba. A wannan zaman gidan kannenta
biyu 'ya'yan Anti sunyi aure har sun haihu. Bata yawo
daga islamiyya sai gida sai kuma abinda ya zama dole.
Samari kuwa kamar anyi ruwa an dauke. Babu mai zuwa
yanzu.
Asmau tace "dukkanmu munga irin abinda ake gudu a
waya da social media. Allah kara rufa mana asiri duniya
da lahira."
"Amin Asmau, amma ai kinfini ganin tashin hankali.
Kullum ina miki addua Allah Yasa kada rayuwarki ta
lalace da kika bar gida. Da farko a social media na fara
watsa hotunanki cigiya kafin Baba ya karbe wayar.
Rabona da wayar arziki na manta"
Yini suka yi suna hira sai bayan laasar lokacin da Asmau
ta tabbatar an gama taron gidansu tayi haramar tafiya.
Jikamshi yayi mata waya yace to ta fara shiri sauran
kadan fa ta karasa zama matarsa yana fatan za tayi shiri
mai kyau kafin zuwan lokacin. Yaso zuwa daukarta ma
da kansa amma kamar yadda suka faro da bin komai
yadda ya kamata sai ya hakura. Wani lokacin ko babu
social media idan budurwa da saurayi suka kebe su
kadai a mota sanyin AC yana dan ratsasu sai shaidan ya
fara kawo musu hari. Ko kadan babu burgewa kice wai
duk inda zaki saurayinki shine yake kaiki ya dauko ki. Ki
duba da kyau kiyiwa kanki adalci watarana ko dan yaya
sai anyi abinda bai dace ba ko da kuwa taba hannu ne.
Yau da gobe ai tafi karfin wasa.
******
A cikin wata daya Col. Ishaq ya dage sosai ana ta gyaran
gidansa. Duk inda yake bukatar canji kamar kayan cikin
toilet irinsu baho da sink an canza an saka komai sabo.
Haka ma a kitchen da su kofa. Ga fenti sai da ya kira
Asmau ta fadi irin kalar da take so. A bangarensu ma
Umma ta tashi tsaye sosai. Daga Asmau yanzu babu
kowa a gabanta sai Yassar. Su Shemau ne suka je suka
gano gidan aka zo aka fara siyayya. Dole ita ma ta dage ta
fito da 'yarta ta. Gado ma ready made ta siya guda biyu
tare da sauran kayan gida. Shemau, Jafar, Kawu Garzali
da gidan Mama duk ba'a barsu a baya ba. Kowa akwai
abinda ya dauki nauyi don ganin cewa Asmau ta sami
nutsuwa a rayuwarta. Ita kam sai son barka da yi musu
addua.
Saura kwanaki biyar su tafi Zaria bikin Dijah. Umma da
Anti Bintu basa zama kullum sai an fita siyayya saboda
ana gama na Dijah da sati hudu za'ayi na Asmau.
Jikamshi yazo yiwa Asmau sallama tafiya ta kamashi
Warri zaiyi sati uku. Zaune yake ya dora hannuwansa
akan cinyarsa sannan ya tallabi fuskarsa dasu yana
kallon Asmau. Kallon ya takurata tace "Jikamshina zan
tashi fa idan baka dena kallona na ba"
"Tashi ki tafi ban hanaki ba. Amma ki sani zan je na sami
'yan matan Warri na kalla son raina"
A shagwabe tace "don Allah ko da wasa ka dena fadin
haka. Kada kasa na kasa bacci yau"
"Shine kike son hanani baccin? Daga gobe fa zanyi sati
uku ban sakaki a ido ba. Ji nake kamar a daura auren
nan na tafi dake. Idan mun dawo sai ayi bikin, kada kice
wani abu nasan kema haka kike so ko Matar Jikamshi"
wannan lumshe idon yake mata. Ita kuwa ta soma
dariya.
"Wane irin aure ne amarya da ango zasuyi tafiya bayan
an dawo ayi biki."
Yace "to kawai idan mun dawo mu wuce gidanmu ko.
Tsayawa bikin duk bata lokaci ne."
Dariya Asmau take yi kawai. Jikamshinta yau sai wani
marairaicewa yake.
"Kada ka damu ni dama ba wani biki nake so ba. Zuwa
za'ayi ayi ta kallona. Na fadawa Umma ayi komai a rana
daya. Bayan daurin aure mata kadan su zo a kaini."
Col. Ishaq ya gane sarai dalilinta na yin haka. Yadda mata
ke son biki amma tace bazatayi komai ba saboda
surutun jamaa. Dena wasan yayi yace "Matar Jikamshi
ko me kika yi na fada miki dole za'a sami masu magana.
Bakiji ance Dan Adam mai wuyar gane hali ba. Idan kinyi
biki ace baki da kunya ko makamancin haka, idan kin ki
biki ace ko dan bikin nan batayi ba don kada mutane su
je. A wurin Dan Adam bazaka taba fita ba. Saboda haka
biki da akeyi abu na lokaci daya zukatan masoya suji
dadi na makiya su fashe...."
Da har ta fara kwalla sai yanzu tayi dariya. Shima biye
mata yayi.
"I am a soldier Matar Jikamshi. Dole nayi aure irin na
sojoji. Su Safiyya suna can suna tsare tsare kamar yadda
su Ainau suke yi. Zamuyi aure da biki kamar kowa kinji
ko. Duk wanda ya fada miki mara dadi ki rinka tuna
ranar asabar din da zaki tare a gidana. Ranar da
Jikamshinki zai nuna miki matsayinki a rayuwarsa.
Wannan ya isheki maganin duk wani bacin rai. Look
forward to being Mrs Jikamshi a zahiri." Gyara zama yayi
bayan ya gama maganar yana son ganin yanayinta. Kasa
take kallo tana wannan murmushin da ta saba idan tana
jin kunyarsa. Bai barta haka ba sai da ya tabbatar mata
lallai bikinsu za'ayi taro kamar na kowa. Masu farinciki
da 'yan saka ido kowa ana gayyatarsa. Addua zasu cigaba
Allah Ya kare duk wani tashin hankali da abin ki har ayi a
gama lafiya.
Da zai tafi Asmau harda kuka. Tana ta cika masa baki sati
uku ba komai bane zata iya jurewa ko basu hadu ba
akwai waya. Hoto ya rinka daukarta fuska a kumbure
saboda kuka. Da ya shiga mota ya tayar tace "Jikamshina
don Allah kada ka kalli kowace mace. Ai ni kadai na
isheka ko?"
Ya murmusa "anya kuwa? A haka kinsan bazan tabbatar
ba sai nan gaba. Idan rabon na hadu da kishiyar matar
jikamshi ne a can sai ki tayani addua"
Ranta a bace ta zamo dankwalinta ta kasan mayafin da ta
lullube kanta ta jefe shi dashi. Dariya yayi mata ya dauki
dankwalin ya dora akan fuskarsa tare da rufe idanu.
Muryarsa can kasa yace
"Ina son kamshinki"
Kunya taji ta mika masa hannu "don Allah ka bani"
"Haba yarinya, dama ba roka nayi ba kika bani. Yanzu
kuma yazo kenan. In sha Allah ke dashi sai a gidanki.
Love you, kiyi min adduar tafiya"
Tana kallo ya rataya dankwalin a wuyansa yaja mota
kamar baya jin magiyar da take masa. Dafe kai tayi tana
tunanin me zata ce idan aka tambayeta dankwalin. Tayi
sa'a babu wanda ya kula. Kafin ta kwanta ya turo mata
hotunansa ya ware dankwalin akan fuskarsa ya rungume
da hannuwansa. Ranar har tayi bacci shi take tunani.
Da sassafe ta kira shi bayan sun gaisa tayi ta jero masa
addu'o'in neman tsari da sa'ar tafiya. Dadi kamar me
haka ya rinka ji yana saka mata albarka. Haka suka yi ta
waya yana hanya har suka isa.
*****
Kwanci tashi sun je Zaria an sha biki lafiya. 'Yan uwansu
na Wushishi sun zo sosai suna cewa saura zuwa Kano
bikin Asmau. Bayan an kai amarya Kaduna da suka
dawo da daddare kafin su kwanta Anti Bintu ta kirata
dakinta. Ita dama bata je kai amarya ba kamar yadda
al'adar bahaushe take. Wata jarka karama ta dauko ta
bawa Asmau.
"Ga wannan zuma ce da aka yi mata hadi mai kyau.
Kullum a kalla kisha cokali biyu. Kada ki sakata a gaba
kiyi

Please Login or Register in order to submit comment