Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bude bakinki
ki karbi abincin...."
Sallamarsa ta sake ji cikin muryar da ta gama ganewa
yanzu. Amatullah na ganinsa ta matsa daga kusa da
Asmau har allurar da ake yi mata karin ruwa ta soketa ta
tsala ihu. Kukanta yaji har ransa ya matsa da sauri ya
gyara mata ya bi Asmau da harara, ita kuwa ta matsa
gefe rai a bace.
Rarrashin Amatullah yayi sannan ya bata abincin kamar
ba soja ba ya mayar da kansa yaro a gabanta. Ko sau
daya bai yiwa Asmau magana ba har sai da Amatullah
tayi bacci sannan ya tashi.
Wayarsa ya miko mata fuskarsa babu alamun wasa ta
dan ja da baya.
"Karbi mana, numbarki zaki saka min"
Tayi kicin kicin da fuska
"Na bawa Hajiya"
"Na sani, ina son karba saboda na kira 'yata anjima".
"Da ka barshi ma, saurin mantuwa gareta kana fita zata
mantaka"
Ya dan daga gira "ke kadai kike son faruwar hakan banda
ni da ita. Nasan bazata manta ni ba."
Duk da haka Asmau taki karbar wayar tana adduar ya
fita kawai. Tunda an biya musu kudin asibitin ba yau ta
fara ba, guduwa zatayi idan dare yayi.
Ya tsareta da ido "na fa san ba numbar daidai kika bawa
Hajiya ba. Kuma nasan baki kira kowa ba dazu. So ki bani
numbar tun girma da arziki kafin na fara bincike a
kanki."
Duk da ta tsorata harararsa tayi tana magana a dan
tsorace
"A wane dalili zaka yi bincike a kaina? Daga taimako, dole
ne na bada number?"
Yadda ya kalleta yasa tayi shiru. Wayarta ya dauka daga
kusa da Amatullah ya kunna sannan ya saka numbarsa
ya kira tasa wayar.
Mayar da wayar yayi inda take ya kama hanyar fita
"saura kuma kiyi tunanin cire sim din. Na bar sojoji biyu
zasuyi min gadin 'yata don kada ki gudu cikin dare".
Gabanta sai da ya fadi da ya fadi haka. Ji tayi kamar yana
karanta abinda ke ranta. Ba'a fi minti biyar da fitarsa ba
taji wayarta na kara. Da sauri ta dauko a tunaninta
Zulaiha ce sai ta sake jin muryarsa.
"Baban Safina ne, Colonel Ishaq Muhammad Jikamshi.
Na bugo ne don na tabbatar baki cire sim din ba." Bai
jira tayi magana ba ya kashe wayar yaja motarsa yayi
gaba.
Asmau ta tsaya tana kallon wayar cike da mamaki. Tsoro
ne ya kamata don da gaske ta yarda ya bar masu
tsaronta kada ta fita su bindigeta a banza. A hankali ta
sake maimaita sunan nasa. Dama a jikin rigarsa ta ga
inda aka rubuta I.M Jikamshi.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽30
Batul Mamman💖
Sau biyu Asmau na leka waje amma bata ga soja ko daya
ba. Ga tsoro kada sai ta fita su tsareta. Haka nan ta
hakura zata zauna don dole. Dadin dadawa tana so
Amatullah ta kara samun sauki.
Sallah tayi ta ci abinci itama sannan ta saka kati daya a
wayar ta kira Zulaiha ta fada mata inda suke. Sauran
ukun kamata yayi ta sayar dasu ta fada a ranta.
****
Col. Ishaq gidansa ya wuce dake Tudun yola. Gidan da a
yanzu baya son zama cikinsa saboda abubuwa da dama
da yake tuna masa dasu. Dakinsa ya shiga ya dauko wasu
takardu ya jira akayi har sallar isha sannan ya tafi gidan
Hajiyarsa.
Babu kowa a falon lokacin da ya shiga shiyasa ya wuce
dakin kaninsa wanda yayi aure kwanakin baya inda
yanzu ya mayar nasa. Yayi wanka ya saka kananan kaya
sannan ya hau gado ya kwanta. Tunanin Amatullah yake
yi yana dan murmushi. Yarinyar ta tsaya masa a rai. Sai
kuma ya koma tunanin mamanta. Ji yayi yana son sanin
ko ita wace ce. Tunani kala kala ya rinka yi game da ita.
Da ya gaji wayarsa ya dauko yana karanta sakonnin da
aka turo masa wasu ya share wasu ya bada amsa.
Sunan da baiyi tunanin gani bane ya dauki hankalinsa da
sauri ya bude sakon. Sallama tayi masa sai hoton baby
da ya biyo baya. A kasan hoton ta rubuta _Alhamdulillah
mun sami baby boy_.
Da kyar Ishaq ya iya hadiyar yawu don tashin hankalin
da ya tsinci kansa a ciki. Har wani guntun zazzabi ne ya
nemi rufe shi. Ya tashi ya fita zai je wurin Hajiya a daki
sai yaji muryarta a falo.
Labarai take kallo ita kuma Bilkisu tana zaune a kasa
suna hirar sanyin Jos da mai aikin gidan Hinde. Motsinsa
yasa Hajiya kallon kofa tace "yaushe ka shigo gidan ban
sani ba?"
"Dazu ne bayan Isha"
Ya zauna akan kujerar kusa da ita tare da mika mata
wayar. "Kin gani Badar ta haihu"
Hajiya ta kalli su Bilkisu "ku dan bamu wuri"
Tashi suka yi Bilkisu sai da ta waiwayo ta kalli Kawunta
tana mai tausaya masa.
Bayan sun wuce Hajiya ta karbi wayar ta kalli hoton
jaririn tayi guntun murmushi "Allah Ya raya" ta gyara
zama sosai tana fuskance shi
"Mai sunan Alhaji, nasan irin damuwar da kake ciki
amma ina so ka sani ba'a yiwa Allah dole. Duk yadda
kaso Allah bai nufa zaku kare rayuwarku da Badariyya
ba. Duk kuma yadda kuka nemi haihuwa kasan wani
baya haifar dan wani."
Kansa a kasa yace "na sani Hajiya. Yanzu na tabbatar
mun rabu har abada kuma kamar yadda Mami take
yawan fada ya tabbata nine bana haihuwa" a yadda yake
ji a wannan lokacin gara yayi kuka ko zaiji sauki a ransa.
Tausayi ya bata sosai.
"A matsayinka na musulmi ka sani cewa babu abinda
bawa zai samu a rayuwarsa sai wanda Allah Ya kaddara
masa. A bisa tsari da hikimarSa *Yake azurta wasu da
'ya'ya mata, wasu da 'ya'ya maza, wasu Ya hada musu
duka biyun, wasu kuma Ya barsu haka* duk inda Allah
Ya jarabceka da fadawa kasan babu wayo ko dabararka.
Ka zama mai hakuri wata rana zaka ci ribarsa".
Ajiyar zuciya yayi ya gamsu da bayananta wanda ya sani
dama.
"Nagode Hajiya, bari naje na kwanta"
"Abinci fa"
"Bana jin yunwa. Sai da safe"
Tasan halin da zai shiga kenan shiyasa tun tana Jos
shekaranjiya da maman Badariyya tayi mata waya ta
sanar da ita haihuwar bata fada masa ba.
*****
Sake kwanciya yayi yana tuno rayuwarsa ta baya. Auren
soyayya suka yi da Badariyya suna zamansu lafiya. Har
suka shekara biyu da aure ko batan wata bata taba yi ba.
Gashi Allah Yayi shi da son haihuwa tun bata fara
damuwa ba ya matsa su je asibiti. An duba su aka
tabbatar musu duk lafiyarsu kalau su jira lokaci.
A haka har suka yi shekara shida babu labari. Maman
Badariyya duk ta damu. Magunguna har da na gargajiya
kawo musu take yi amma shiru. Ishaq ya tayar da
hankalinsa sosai gashi ko ina suka je sai ace babu
matsala. A wani asibitin Jiddah ne ma aka ce kwan
haihuwarsa bashi da karfi. Ya shiga damuwa sosai sai
gashi Badariyya ke bashi baki.
Sun sami shekara goma da aure Mamanta taje har gidan
Hajiya ta roketa arzikin asa Ishaq ya saketa tunda anfi
tunanin matsalar daga gareshi. Hajiya Lubabatu tayi ta
rokonta akan tayi hakuri sai tace to nan da wata shida
idan ba'a saki canji ba dole ya saketa.
A wannan wata shidan Ishaq yaje asibitoci sunkai
takwas. Magani kuwa duk wanda aka bashi sha yake yi.
Lokaci na cika har gida Mami tazo ta bukaci ya saki
'yarta. Badariyya kanta tace ko waye da matsalar a
cikinsu zasu hakura tunda suna son juna. Mami ta dage
abu har kunnen manya a danginsu duka. Ganin
al'amarin yana neman lalacewa dole ya yi mata saki daya
suka rabu ba don suna so ba. Tana gama iddah da wata
biyu yaji labarin aurenta, gashi yanzu har ta haihu ko
shekara bata cika ba. Ya amince bashi da rabon ganin
dansa. Kannensa duka sun haihu hatta autansu matarsa
ciki gareta.
A haka bacci ya dauke shi zuciyarsa cunkushe da tunani.
*****
Da safe likita yazo ya duba Amatullah yace jikin da sauki
amma zasu barta sai gobe a sallamesu. Asmau masa tayi
godiya sannan ta tashi tayi wanka ta gogewa Amatullah
jiki ta canja mata kaya.
"Ama zan fita na siyo miki abinci kinji. Duk wanda ya
shigo ki ce masa ina bandaki"
"Ummi kayya ko, ashe kema kina yi kika ce na dena"
Kafin ta iya bata amsa taji tace "yeeey Babana ya dawo"
Asmau ta dago kai a kunyace. Karshenta yaji abinda
Amatullah ta ce. Yau ma kayan sojan ne a jikinsa sai dai
babu fara'a kamar jiya. Duk da haka yayi kyau ga cika
ido.
Gaishe shi tayi ya wuce bai amsa ba. Wani mutum ne ya
shigo da kwandon abinci ya gaisheta ya ajiye a gefe ya
fita.
Col. Ishaq yana zaune akan kujera yana yiwa Amatullah
wasa da tambayar ya jikinta. Asmau duk ta takura ta rasa
abin yi.
"Ki zuba mata abinci mana idan ke baki jin yunwa."
Wai mutumin nan ina ruwansa da ita ne. Me yasa ya kara
dawowa ma. Ta danyi tsaki a hankali sannan ta hada
abincin ta zauna a daya gefen zata bawa Amatullah ya
miko mata hannu alamun ta bashi plate din. "Kema ki
zuba kici".
Gefe kawai ta ja tana kallon ikon Allah. A baki ya rinka
ciyar da Amatullah tana ta yi masa surutu. Asmau tana
satar kallonsa.
"Abinci nace ki zuba ba kallona ba"
Ya Salaam! Ba karamar kunya taji ba ta tashi da sauri ta
zuba abincin ta dawo tana tsakura da cokali.
Ya tashi saboda ya fuskanci kunyarsa take ji. "Safina bari
na je naga likitan da ya dubaki na dawo"
Fita yayi ko waige babu. Asmau ta tuttura abincin kada
ya dawo ya sameta.
*****
Tambayoyi ya yiwa likitan game da ciwon Amatullah. Da
ya fito ya tsaya bata lokaci don ya bata damar gama cin
abincin. Gara da Allah Yasa yayi tunanin kawo musu
abincinsa da yake tafiya office dashi ba don haka ba don
ganganci fita zata yi ta bar yarinya ita kadai a daki. Wasu
na nema ido rufe ita ta samu bata rike da kyau ba.
Kafin ya dawo ta gama ta dauke plates din ta dauraye a
toilet. Ya shigo yayi mata alama da ta fito waje.
Darajar girmansa da take gani da tsoronsa da take ji a
yanzu yasa ta fita. Ta tsaya can gefe ta sunkuyar da
kanta.
"Da ban zo ba sai ki fita ki Safina ita kadai a daki? Kuma
shine harda koya mata karya. Allah kadai Yasan me kike
koya mata kafin yanzu"
Taji haushin maganarsa ta dago kai zata yi masa rashin
kunya "ina ruwanka da abinda nake koya mata".
Yanayin kallon da yayi mata kadai yasa ta kawar da kanta
gefe
"Ni kike fadawa haka?"
Da wadanda ke karkashinsa zasu ji abinda ta fada kila
idan ta fara tsallen kwado sai kafarta ta kumbura. Lallai
tana da tsaurin ido. idan kayan jikinsa basu yi mata
kwarjini ba ai shekarun da yake jin zai bata shabiyar ko
sama da haka ya isa yasa taji kunyar idonsa.
Da yake rashin kunyar ba dabi'arta bace sai taji babu
dadi "kayi hakuri wallahi nagode da taimakon da kuka yi
min. Abinda kaji na fada mata ma don babu wanda zai
zauna min da ita ne"
"Its ok, zan aiko muku da abinci anjima saboda haka
kada ki fita ki barta ita kadai."
"Nagode"
"Har yanzu baki kira kowa a gidanku ba?"
"Uhmmm sun ce zasu zo anjima".
"Maman Safina kin iya karya" ya fada yana shafa kansa.
Asmau taji kamar ta nutse a wurin. Kai wannan mutumi
da bin kwaf yake.
"Ance gobe za'a sallameku. Na fadawa likitan kada yayi
sallamar sai nazo"
Ta dan bata rai "saboda me"?
"Saboda na kamaki da kyau. Ina son sanin inda zaki kai
min 'ya idan kin fita daga nan"
Cikin dakin ya koma ya cewa Amatullah zai je office ya
dawo. Har da kukanta ita zata bishi. Asmau ta kalleta
bayan ya fita a ranta tace ki gama ganinsa da kyau kafin
ki dena ganinsa.
Da yamma Haj Lubabatu ta saje dawowa har take
tambayar Asmau ina iyayenta. Tace mata yanzu suka tafi
za'a kawo musu abincin dare. Hajiya tace "ai mun zama
daya nasan zamu hadu ko ba yau ba".
A zuciyarta tana kokonton ko da gaske sun zo. Babu wani
alamar kayan dubiya ga akwatunansu Asmau a gefe
wanda ya kamata ace an tafi dasu gida. Da Ishaq ya
koma gida da daddare sai da ta fada masa. Yace shima
yana son bincike ne a kanta ko don yarinyar da take tare
da ita.
*****
Sai wurin karfe tara na safe Col. Ishaq ya dawo
washegari amma sau biyu yana aika musu da abinci har
da kayan kwalama na yara. A lokacin aka basu takardar
sallama da magani. Sauran kudin da ake binsu duk yaje
ya biya mutumin da ya kawo musu abinci ya kinkimi
akwatunanta.
Asmau ta dakatar dashi yace Yallabai ne ya saka shi.
Dauka kawai yayi zai fita Ishaq ya shigo yace ya wuce
dasu gidan Hajiya zasu biyosu a baya.
"Bangane ba" Asmau ta fada a tsorace. "Nima namu
gidan zam wuce don Allah kace ya ajiye min kayana"
"Kinga ki wuce muje akwai tambayoyin da nake so nayi
miki daga nan nayi alkawari zan kaiki gidanku da kaina."
"Ni bazan bika ba, haka kawai na sani ko....ko..."
Yayi murmushi "karasa mana. Ko satar mutane nake yi.
Nima tsoron da nake ji kenan ko sato Safina kika yi".
Idonta har ya ciko da hawaye tace "wallahi 'yata ce, don
Allah ka barmi mu tafi."
Fita taga zaiyi daga dakin tace cikin kuka "zanyi maka
ihun barawo"
Col. Ishaq yayi dariya ya kalli Amatullah "Safina ina
babanki?"
Ta sake lafewa a jikinsa "ga ka"
"To kinji, idan kina son 'yarki ki biyoni. Taimakonki nake
son yi albarkacin wannan yarinyar"
"Bana son taimakon ka bani 'yata...." tafiyarsa taga yayi
dole tabi bayansa tana dan gudu gudu saboda yadda ya
soma yi mata nisa.
Gaban wata mota mai kyau suka tsaya baka ya bude
gaba ya ajiye Amatullah wanda dadi ya isheta sannan ya
zagaya ya zauna a wurin dreba. Babu yadda Asmau ta iya
dole ta bude baya ta shiga. Suna hada ido ta mudubi ya
kashe ido yana murmushi ita kuwa ta murguda masa
baki.
Shi da Amatullah suke ta hira tana bashi labarin gidansu
Umma Zulaiha. Gidan Hajiya ya wuce dasu zuciyar
Asmau tana ta daridari.
Duk kunya ta dameta haka tabi bayansa suka shiga
gidan. Haj Lubabatu ta tarbeta cikin fara'a aka kawo
musu abinci. Col. Ishaq yace Bilkisu taje ta yiwa
Amatullah wanka. Asmau tabi bayansu da ido yarinya sai
murna takeyi ta sake dasu.
Hannunsa ya dan kada a gabanta ta dawo daga tunanin
da take yi. Yace "Malama Asmau ina ganin ya kamata ki
sanar damu ko ke wace ce. Hajiya ma ta fahimci akwai
abinda kike boyewa shiyasa na kawoki nan ki fada mana
a gabanta."
Asmau ta soma hawaye "naso ace yadda muka hadu
cikin mutumci mun rabu a haka batare da na tonawa
kaina asiri a duk inda na tsinci kaina ba"
Hajiya tace "kada kiga kamar mun takuraki, rayuwar
Safinatu muke dubawa shiyasa. Idan har baki da wurin
zuwa ga yarinya mai lalura lallai kina bukatar taimako"
"Ina da iyaye da 'yan uwa. Kuma a garin nan muke"
Col Ishaq yace "to me ya rabaki da gida har kika kasa
fada musu kuna asibiti"?
Asmau tayi ajiyar zuciya sannan ta basu labarin
rayuwarta. Tun Haj Lubabatu tana kada kai ha[truncated
by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽33
Batul Mamman💖
Gidan suna dai ya koma wurin zuwa kallon Asmau da
'yarta. Bayan anyi sallar la'asar ne ta tuna da Col. Ishaq
da ya kawo su. Dafe kai tayi saboda tasan bata kyauta ba.
Ganin su Umma yasa ta manta da kowa. Shema'u ta
fadawa cewa dan matar da suka zo tare shi ya kawosu
kuma yana waje. Haj Lubabatu tana jinsu sai dai kunya
ta dan fari ta sanya taki tuna mata dashi. Kuma tasan yau
rana ce mai matukar mahimmanci a wurin Asmau. Ta
hadu da iyayenta da 'yan uwa bayan tsahon lokaci.
Shema'u ta sanar da Umma. Nan da nan aka samu food
flasks aka hada masa duk wani na'uin abinci na gidan
sunan. Jafar aka kira akan su wuce gidansa domin bako
ya samu yaci abinci ya huta.
Jafar da Sabira suka fito dauke da kayan abincin tare da
Asmau dake binsu a baya rike da hannun Amatullah.
Zaune yake a gaba ya kwantar da kansa a saman kujera
yana sauraron karatun Al'Qur'ani kira'ar Shiek Mishary
Rashid. Tausayinsa Asmau taji saboda kunyar abinda tayi
masa. Babban mutum kamarsa sun shanya shi a kofar
gida. Kuma ta tabbatar baici abinci ba kafin su taho.
Yana dawowa daga masallaci ko zama baiyi ba yace su
taho kawai.
Amatullah ta tafi da gudu ta fada jikinsa. Hakan yasa shi
saurin bude ido yana murmushi. Jafar ya karasa gaban
motar ya mika masa hannu suka gaisa.
"Kayi hakuri don Allah an barka a waje tun dazu. Duk
laifin Idon kuka ne da bata fada mana tare kuke ba"
Col. Ishaq yace "Idon kuka kuma?"
Dariya Jafar yayi kana ganinsa kasan yana cikin farinciki,
ya nuna Asmau "ai sunanta kenan."
Kyakkyawan murmushi Col. Ishaq yayi yana kada kai
"sunan ya dace da ita"
Duk akayi dariya sannan Jafar ya fada masa yana son ya
biyo shi gidansa domin yaci abinci. Da farko Ishaq ya
nuna baya jin yunwa sai da Asmau ta bashi hakuri tare
da rokonsa. Yayi yar dariya
"Haba Idon kuka, bayan ko introducing dina a wurin
yayanki baki ba?"
Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Jafar ya
sake mika masa hannu murmushinsa yana kara fadada
"nima da laifina, sunana Jafar ni Asmau take bi,wannan
matata ce Sabira. Idan kaci abinci zamu shiga ciki ka
gaisa da duk 'yan uwa."
Col. Ishaq ya dafa kan Amatullah "ni kuma sunana Baban
Safina"
Sabira ta kalli Asmau "kice kawai biki zamu sha kwanan
nan"
Da sauri Asmau ta daga hannuwa "ba haka bane, Ama ce
kawai take kiransa babanta. Sunansa...."
Shiru tayi duk suka zuba mata ido. Kunya taji ta kasa
fadin sunan sai ta wayance tace ya kamata su tafi saboda
kada abincin ya huce. Col. Ishaq ya nuna su shiga
motarsa.
Jafar ya shiga gaba, Sabira na baya sai Amatullah da ta
dage zata bi babanta. Asmau tana tsaye suka ja mota
suka tafi ta koma ciki.
Hira aka dora daga inda aka tsaya. Shema'u tana goye da
Abid din Sabira sai jijjiga shi take kafin Sabirar ta dawo.
*****
Mata kamar kara turo su akeyi gidan ana ta zuwa kallon
Asmau. Hajjo duk ta matsu su firfita don su samu ayi
hira yadda ya kamata da Asmau. Duk dakin da ta shiga
mata ne harda wadanda ma basu zo ba da farko. Su
Umma ma dai kara kawai suke yi amma duk a matse
suke da a basu fili suyi hira da 'yarsu. Da suka ga abu
yaki karewa Hajjo da kanta ta shiga falo rai a bace tana
mita yadda masu hankali zasu fahimta
"Kai jama'a ace anzo taron suna anci tatsotse dinnan
anci salak, anci tuwo anci wannan anci wancan amma
mata sai tururuwa suke yi. Fisabilillahi ko irin karar nan
ta a fita a bamu waje da jikarmu muyi hirar yaushe
gamo ya gagara".
Wasu nan suka fara jin kunya suka fara hada kayansu
suna fita. Sauran da suka yi biris kuwa Hajjo ta rufe
idonta ta sallamesu. Umma da Mama dai sunji kunya to
amma halinmu na mata wurin saka ido da bin kwaf ya
janyo musu.
Basu samu gidan yayi daidai ba sai bayan karfe tara. A
falo suka zazzauna. Duk 'yan uwan Asmau makusanta
suna wurin har da Kawu Garzali ga kuma Haj Lubabatu
da danta. A nan aka shiga bada labarin abubuwan da
suka gabata. Kowa jikinsa yayi sanyi musamman da suka
ga Asmau tana ta kuka da rokon a yafe mata. Suka yi ta
kukan wannan kaddara da ta riga fata.
Mama Yalwa tace "ai wannan bala'i na waya sai an dage
da addua sosai. Akwai alkhairi tattare da ita amma
sharrinta a bayyane yake. Kuma kullum kara samar da
sabuwa akeyi mai saurin hada mutane da barna."
"Haka ne" Haj Lubabatu ta amsa mata. " Sai kiga yara
kanana sun yini da waya a hannu ki rasa me suke
tattaunawa. Wani lokacin a haka ake haduwa da mutane
babu sanayya idan kika yi rashin sa'a ba nagari bane sai
su bata maka tarbiya ba tare da ka lura ba. Kwanakin
baya jikata dake karatu a nan wurina Bilkisu na fuskanci
ta soma nacewa waya fiye da yadda ta saba. Kullum suna
hira da wata yarinya da suka hadu a irin group dinnan
na waya. Kunsan yanzu tsakanin mace da mace ko maza
ma babu abinda ba'ayi. Na kula kawancen ya soma yawa
bata da zance sai nata. Abun ya fara bani tsoro. Shabiyun
dare sai kiji suna waya sai da nayi mata tas akan hakan."
Hajjo tace "ni idan babu hali ba sai a hakura da wayar
ba. An fara abu da gaisuwa da sada zumunci a hankali
waya ta zama tamkar kana dauke da duniya a tafin
hannu. Idan kaki bawa danka waya ma zai fita ya gani a
ta wasu."
Tattaunawa suka yi ta yi a game da tasirin waya ga
al'umma yanzu. Babu babba babu yaro kowa yana da ita
kuma ya iya amfani da ita. Jankunne sosai manyan suka
yi garesu akan su dubi yadda rayuwar Asmau ta kasance
su kula da kawunansu da na yaransu. Kasancewarsu
masu aure duk bashi bane domin yanzu hatta mata da
mazan aure suna fadawa tarkon waya. Daga group sai
kaga matar aure tana mu'amala da 'yar uwarta mace ko
namiji mai aure ko mara shi wanda a da ba halinta bane.
Sun jima suna hira har shadayan dare tayi basu kula ba
sannan Haj Lubabatu da Col. Ishaq suka tashi tafiya. Sun
sha godiya a wajen dangin Asmau sosai tare da neman a
cigaba da zumunci don yanzu sun zama daya.
Fitowa suka yi har bakin mota rakiya Amatullah na
makale jikin Col. Ishaq tana bacci. Tashin da yayi zasu
fito yasa ta farka ta soma rigimar binsa. Shi kan shi baya
son rabuwa da ita. Ana ta lallabata taki yin shiru sai da
Asmau ta karbeta ta karfi tana mata fada. Hakura tayi
amma bata dena kukan ba. Col. Ishaq ya bata rai sosai
saboda fadan da tayiwa Amatullah. Kallon da yake mata
ya nuna rashin jindadinsa sai kawai ta sunkuyar da
kanta.
Bayan tafiyarsu Umar ya tafi kai Mama Yalwa gida shi
kuma Abdulhalim ya dauki matarsa da yara suka wuce.
Dakin Umma suka koma Amatullah tana ta kuka har sai
da Asmau ta goyata duk girmanta don taki yarda da
kowa. Daga nan aka soma wata sabuwar hirar har aka zo
kan Kawu Rabe Asmau tace shi kadai ne bata gani ba .
Shema'u tace "hmmm Asmau mutum babu kyau. Ashe
duk tsahon lokacin nan Kawu Rabe wurin wani malami
yake zuwa ana rufe bakin Hajjo da su Yaya Abu. Bayan
tafiyarki Hajjo tazo ta nemi gafarar Umma har ta bukaci
lallai ta dawo gidannan dasu Aina'u idan har ta yafe
mata. Shi kuma tace ya soma gyara musu gidan kofar
mazugal su koma. A nan aka ji ashe ya dade da siyar da
gidan. Ya kuma dage wannan nasa ne. Sai ga ainihin
takardun gida Hajjo ta fito dasu, ke magana har za'a
shiga kotu don duk su Kawu Garzali sun ce sai ya biyasu
kudin gidansu da ya sayar. Wurin aikinsu ma suka kore
shi yaci kudin kamfani bai biya ba. Sai da yaga abu ya
kure masa ya roki gafarar Umma suka tashi. Yanzu haka
yana kauyen Dakasoye can ainihin kauyen babansu Anti
Sagira. A nan baban nata ya bashi gona da gida suka
zauna tunda bashi da wurin zama. Yanzu da wuya yazo
cikin Kano. Zahra dai tayi aure tana Jigawa"
Asmau tace "har ya bani tausayi. Da ma Umma ta barshu
kawai a nan din"
Aina'u tace "tabdi, ko yanzu fa ba wani rissina yayi ba.
Tsoron hukuma yaji don da gaske su Yaya Abu sunso a
kama shi sai ya biyasu kudin shiyasa ya bada hakuri ya
tattara yayi gaba"
"To Allah Ya kyauta" duk suka ce Amin.
Kan katon gadon Umma suka kwanta su uku sannan aka
shimfide yaran akan bargunan banda baby Asmau
wadda suke kira Husna.
Sai wurin daya da rabi na dare Umma ta baro dakin
Hajjo inda su Anti Lami suke. Su ma sum gama tasu
hirar. Wani hawaye taji yazo mata da taga 'ya'yanta mata
kwance su uku a wuri daya sun takure alamun daya
gefen nata ne. Kasa kuma ga yaransu duk sunyi bacci.
Maimakon ta kwanta alwala ta dauro tazo tayi sallah tana
mai mika godiyarta ga Allah tare da adduar dadin shiriya
ga zuri'arta da sauran musulmi.
*****
Col. Ishaq yana kwance amma ya kasa bacci. Ya rasa
abinda yasa yake ta tunanin Asmau. Can kasan zuciyarsa
yace tausayinta ne kawai da kuma son Amatullah. Sai dai
kuma ko rufe ido yayi murmushin da tayi bayan
komawarta gida yake tunawa sai kawai ya tsinci kansa da
yin murmushin shima.
*****
Washegari karfe takwas na safe sai ga Jafar da Sabira
dauke da kwanunkan abinci. Dankali ta suya da plantain
da kwai. Duk da tasan dai a gidan ma za'ayi. Umma ta
nuna jindadinta sosai. Shiyasa take son Sabira, barta dai
da surutu amma mace ce mai ladabi da sanin ya kamata.
Sauran matan masu jini a jika irin su Shemau da Rashida
suna kitchen ana ta soye soye. Aina'u ma ta tashi duk da
hanata aikin komai ita da Zubaida mai ciki. Asmau kuwa
kamar wadda aka saukarwa bacci tana yin sallar asuba ta
koma. Ji takeyi rabonta da bacci mai dadi cikim
kwanciyar hankali har ta manta.
Amatullah ce ta tasheta tana kiran Babanta. Cikin bacci
Asmau ta janyota jikinta ta soma rarrashi
"Ama nan ne gidanmu fa, na rasa inda kika koyi rigima.
Amma idan kika cigaba zan mayar dake wurin Zinaru"
Shiru tayi ta kwanta a jikin Asmau daga baya tace "Ummi
to zaki kaini naga Babana sai mu dawo?"
Asmau ta shafa kanta tana murmushi "in sha Allah zan
kaiki kinji. Tashi muje muyi brush a gaishe da su Hajjo"
Suna fitowa falo suka tarar da kowa a zaune har su Jafar.
Rike take da hannun Amatullah sai suka basu sha'awa.
Ita kuwa kallon da suke mata yasa taji kunya ta saki
hannunta. Yanzu tunda anzi gida sai ta koyi kara kada
ace bata da kunya. Suna zama suka gaishe da kowa Anti
Bintu ta cikawa kowannensu plate da abinci. Amatullah
ta ware ido sai ta tashi taje tayiwa Asmau rada a kunne.
Duk ana kallonta sai suka ga tana share hawaye.
Hankalinsu ya tashi Umma tace me ya faru.
Kunya tasa Asmau ta kasa fada da wayo Umma tace
"Safina zo ki fada min abinda kika fadawa Ummi. Kinga
gashi har kin sakata kuka"
Duk aka zuba mata ido ita kuwa tace "Ummi in fada?"
Murmushi kawai Asmau tayi tace "tambayata tayi taci ko
kuwa"
Amatullah ta cafe "idan naci Ummi zata ce nayi

Please Login or Register in order to submit comment