Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matukar son daya, dayan kuma take ganin
girmansa. Duk su biyun kuma tana jin kunyar nuna
musu bata sonsu a yadda take ganin ba karamin
darajata suka yi ba da suke sonta da aure.
Col Ishaq yana kallo yadda ta shiga rudani. Kamar yadda
ya fada mata da ace Qasim ya rigashi to zai hakura ne
indai ya tabbatar da gaske yake sonta. A yanzu kuwa
yana da yakinin shi Asmau take so kuma ya riga saboda
haka yana nan daram sai yaga abinda ya turewa buzu
nadi. Shi kishin kara masa so da kaunarta yayi ma.
"Kamar kwana nawa kike bukata na baki ki sallame shi"
Ji karfin hali ta ayyana a ranta. A fili tace "bangane ba"
"Kin gane, karin bayani kike nema dai. Bansan iya
matakin da kuka kai ba ke dashi shiyasa zan baki lokaci
kuyi rabuwar arziki. Shima don na fahimci kamar yana
da halin kirki ne."
"Ya kake so nayi? Kaima na fada maka babu zancen aure
a raina shima kuma hakan na sanar dashi"
"Idan babu zancen aure a ranki kin tanadi yadda zakiyi
da soyayyata wadda yanzu ma na fara nuna miki ita.
Idan bakiyi wasa ba nan gaba kadan saboda yadda zan
rinka yakin neman sonki da kanki zaki ce gobe a daura
mana aure"
Dariya tayi, shi a komai sai ya saka wasa tace"kai
Jikamshi"
"Allah kuwa Asmau" shima ya mayar mata da
murmushi.
"Ni da ban taba cewa ina sonka ba. Amma kana da
confidence a kaina"
Kansa ya shafa yana kallonta. Baya gajiya da kallon
Asmau ko kadan.
"Asmau kina sona. Nima ina sonki. So bana bukatar sai
kinyi ta maimaitawa da baki. Akwai lokacin da zaki rinka
fada da kanki"
Ita kam Jikamshi yana bata mamaki. Sai ya fadi magana
ya kuma dake abinsa.
"Ki shiga ciki bana son kina shakar kurar nan. Kada ki
manta da abinda nace. Idan kin sallame shi zan turo
iyayena a fara maganar aurenmu"
Magana taso yi ya sanya yatsansa akan lebensa alamun
tayi shiru.
"Idan rokona zakiyi akan Qasim kada ki bata bakinki.
Nan da sati biyu idan baki sanar dani yadda kuka yi ba ki
zaki ga magabatana sunzo. Ki kula min da kanki da
princess dina. Yau duk kin rikita min lissafi na kasa bata
kulawa yadda ya kamata"
"Ni babu ruwana."
"Harda tsakinki. Sai da safe"
"Allah Ya bamu alkhairi"
Tana kallo ya shiga mota ya zauna sannan itama ta juya.
"Matar Jikamshi"
Cak ta tsaya amma bata juyo ba sai murmushi da take yi.
"I love you"
Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cike da kunya tayi hanyar
gida a kunyace.
******
Daurewa kawai Col. Ishaq yayi har suka karashe hirar
cikin wasa. Da ya rage shi kadai yana tuki tunani yake
kada iyayen Asmau su bawa Qasim ita saboda sunfi
sanin shi sannan abokin Abubakar ne. Saurin kawar da
tunanin yayi daga ransa. A zatonsa ya gama soyayya
akan Badar sai gashi lokaci guda Asmau ta wargaza masa
tunani.
Yana zuwa gida dakin Hajiya ya wuce. Bayan sun dan
taba hira ya sanar da ita zancen Asmau. Tayi mamaki
sosai don bata taba hasko hakan ba. Bilkisu da tayi niyar
fada mata kuma ranar tun a hanya yaja mata kunne.
Shiru tayi na dan lokaci kafi tace
"Kai yanzu kana tunanin sai ka aureta ne kawai zaka iya
kyautata rayuwarta da ta Safina?"
"Hajiya nifa ba don in kyautata musu kawai nake son
aurenta ba. Ina sonta ne tsakani da Allah"
Ko kunyar yace yana son mace baiyi a gabanta. Tayi iya
kokarinta wurin nuna masa kunyar dan fari amma duk
baya biye mata. Yanzu me ya kawo zancen soyayya a
gabanta.
"Bazan zama irin iyaye marasa karbar kaddara ba
musamman da na san komai game da ita. Kai ba yaro
bane da zan ce baka san abinda ya kamata ba. Amma ka
jira nayi shawara da 'yan uwana dana mahaifinka. Kasan
zancen duniya baya buya. Gara su sani tun kafin ayi
auren sabo gudun gutsiri tsoma"
Murmushi yayi ya nuna mata tsantsar farincikinsa.
"Hajiya nagode da kika fahimce ni. Ina fata ko sun nuna
rashin amincewa don Allah kada ki hanani aurenta don
wallahi bakiji yadda nake jinta a zuciyata ba"
Haj Lubabatu ta kawar da kanta gefe a kunyace. Ya
cigaba da cewa "idan tayi murmushi ji nake kamar...."
"Kai tashi ka bani wuri zancen ya isa haka" ta fada amma
kafin ya tashi ita tayi gaba. Dariya yayi dama tsokanarta
yaso yi.
Sai da ya gama shirin bacci ya dauko wayarsa zai kira
Asmau yaga missed calls da bakuwar number har uku.
Ya kira numbar ga mamakinsa sai yaji muryar Qasim.
Sun sake gaisawa yace ya karbi numbarsa a wurin Yassar
ne don su rinka gaisawa. Hira suka dan taba cikin
mutunta juna. Suna yin sallama ya kira Asmau.
Ta dauka kafin tayi magana yace cikin muryar shagwaba
"Matar Jikamshi kin cuce ni"
Gyara zama tayi a dan tsorace." Me nayi kuma"?
"Wannan dan sandan saurayin naki wallahi yana da
mutumci. I feel guilty nace ki rabu dashi gashi har yana
min waya."
Ta dan murmusa "to ko na barshi kai ka janye"
"Ba haka nake nufi ba fa. Kawai dai naji babu dadi ne. Da
kin sani wani dan caburus kika nemo wanda zanji kwarin
gwiwar yiwa rashin....." ya dan toshe baki "wai
shekarunki nawa ne? Kinsan dole na kula da abinda zan
fada a gabanki saboda kada na bata yarinya"
"Nice ma yarinyar. Shekarata ashirin da takwas fa"
"Kai, kai ,kai...kada azo a kamani ina soyayya da 'yar
yarinya"
Asmau sai dariya take yi tana juyi akan gado, Ainau daga
gefe tace "love in Tokyo"
Pillow ta jefeta dashi ta cigaba da dariyarta saboda
yadda Jikamshi yake mata shagwaba yau "shiyasa nace
ka hakura ka janye kawai ka barwa yaro"
"Ai baki isa ba yarinya. Bayan duk kin gama kashe min
jiki da wadannan idanuwan naki. Na dai fada miki ina
tausayinsa ne amma bance ki tausaya masa ba. Ki
gaggauta sallamarsa kada ya janyo zuciyarki da kirkinsa"
"Jikamshi"
Sai da ya gyara kwanciya ya amsa mata "mene ne?"
"Babu komai, sunan kawai nake son fada"
"Shi mai sunan ba kya son shi?"
"Ina so"
Da sauri ta tashi zaune da ta gane abinda ta fada. Ta rasa
dalilin da yasa idan tana tare dashi take manta komai
tayi ta sakin baki. Ko dai ta fara zama irinsa ne???
*****
Washegari Malam Musa ya zaunar da iyalinsa ya fada
musu cewa nan da sati mai zuwa zai tura masu
wakiltarsa a nemawa Qasim auren Asmau. Ya gaji da
ganin dan nasa gwuaro. Da Qasim yace basu gama
shawara sa Asmau ba, Mal Musa yace babu komai sunyi
magana da Alh Adamu yace zaije ya sami Umma da
Kawu Garzali a tsayar da magana ayi aure kowa ya huta.
Murmushi Qasim yayi na jindadi don yasan Asmau
bazata bijerewa iyayensu ba.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽40
Batul Mamman💖
Washegari su Asmau basu sami zaman gida ba. Sun hadu
da Shemau, Sabira da su Nasiba an sake gyara gidan
Ainau kamar masu shirin kai amarya. Da yamma Umar
yaje ya daukota. Kana ganinsa kasan yau yana cikin
farinciki. Kusan wata uku bata gida don tun kafin ta
haihu aka bata bedrest shine Mama tace ya kaita gida
zata fi hutawa.
Ranar Jikamshi ya kirata yafi sau shida kuma sai anyi hira
akalla ta rabin awa. Yana kira sai ya tambayeta ko Qasim
ya kira kuma wayar minti nawa suka yi. Sai da ta gama
dariya sannan ta zolaye shi tace
"baya ajiye waya sai wata wayar ta shigo min."
Shima dariyar yayi mata kawai yace "ba zan damu ba
don nasan tawa hirar ce kawai take burgeki koda kuwa
ta minti daya ce. Amma zancen gaskiya ki dena kashe
masa murya yadda kike yi min. Kara sonki kawai zaiyi ni
kuma ba hakura zanyi na bar masa ba"
Tayi dariya sosai hakan ya sanya shi nishadi.
"Haba Yaya Ishaq, kai fa Yayana ne kuma Yayan Qasim.
Kaci girma kawai"
Kamar tana gabanshi ya dan daure fuska cikin wasa "ki
kiyaye ni fa matar Jikamshi. Ni ba yayanki bane na fada
miki. Kina magana da baban Safina mijin Asmau in Sha
Allah"
Ta danyi shiru tana jin inama hakan ya tabbata.
"Baki ce amin ba"
"Amin" ta amsa ba don yana tunanin ganin ranar
aurensu a gaba ba. Addua zata yi masa Allah Ya bashi
mace ta gari. Amma tasan bazata je komai ba a bikin.
Daga haka suka yi sallama kowannensu yana kara jin son
dan uwansa.
*****
Bayan sati daya kullum Col. Ishaq da Qasim sai sun
kirata a waya kowanne yana kara jaddada mata irin son
da yake mata. A wannan kwanakin da Jikamshi bai zo ba
ita kanta abin ba karamin damunta yayi ba. Har mamaki
take yi da take masa so irin wannan duk da tana kokarin
dannewa. Ranar alhamis ta kira Zubaida ta sanar da ita
zata zo yini washegari. Zubaida sai murna don tun
dawowarta sau daya ta samu taje gidan, basu zauna
sunyi hira yadda suke so ba. Ita kuma Zubaida saboda
cikinta ya tsufa babu batun fita.
Kafin shabiyun rana washegarin Asmau ta gama girkin
rana tayiwa Amatullah wanka sannan itama ta shiga.
Tana fitowa taga Umma ta dawo duk da ranar aiki ne.
Har daki ta bita tana tambayar ko lafiya.
"Babu komai yau dai na gaji ne. Kinsan kwana biyu
bamu huta ba. Kema da kin hakura da zuwa gidan
Zubaidan sai wani satin. Yarinyar nan kina ta yawo da ita
'yan kwanakin nan"
"Umma Yaya Jafar yace zai kaini ba adaidaita zan hau
ba."
"To kiyi maza ki karasa shiri kinsan baya son jira."
Asmau ta tashi ta koma daki ta karasa shiryawa sannan
ta zauna jiran Jafar. Ko rabin awa ba ayi ba ya iso. Suna
shirin fita taga Kawu Garzali shima ya shigo. Gaisawa
suka yi yace mata Zubaida tun asuba take jiranta. Yanzu
Kawun nasu kamar wani kaka haka yake musu wasa.
Shima dai tayi mamakin ganinsa don ance mata Umma
ce ta sama masa aiki a inda take wato MTN office.
*****
Suna fita Umma tayi ajiyar zuciya ta tafi dakin Hajjo ta
sanar da ita wayar da suka yi da Mama tun tana wurin
aiki. Shine ma dalilin dawowarta gida da wuri da zuwan
Kawu Garzali. Alh Adamu ne yake son ganinsu don yace
gidan zai zo idan ta taso aiki. Kasa hakura tayi saboda
Mama tace mata batun auren Asmau da Qasim ne zai
kawo shi. Shiyasa ta fada Garzalin suka dawo gida kawai.
A cikin satin da tayi magana da Asmau akan manemanta
biyun ta nuna mata ita karatu kawai zatayi duk zata
sallamesu batare da bacin rai ba. Sai dai kuma tuni
Umma ta gano inda zuciyar 'yarta tafi karkata. Matsalar
dai bai wuce abinda itama Asmau take jiyewa tsoro ba
na dangane da gori ko rashin amincewa daga dangin
mazan.
Bayan ta gama bayaninta Hajjo tace "yaron nan da gaske
yake da rike amanar amininsa. Allah Ya tabbatar da
alkhairi." Ta danyi shiru kamar mai tunani sannan tace
"Amma idan banyi kuskuren fahimta ba sai naga Ishaq
shima kamar fa sonta yake yi. Kinsan mu idonmu idon
soyayya. Muna ganinta muke ganewa"
Umma tayi dariya sannan ta fada mata wayarsu da Anti
Bintu da kuma yadda suka yi da Asmau
"Bazamu zuba mata ido ba duk da muna jin tsoron
surutun mutane auren shine rufin asirinmu. Duka su
biyun ni bana kin kowa amma Hajjo kinga Qasim muka
fi sani kuma gashi har maganarsa ta kai kunnen manya.
Garzali ma ya shigo ina tsammanin a falo ya tsaya. Shine
namiji dole ayi komai dashi "
"Kinga wancan mutumin banzan shi ya kamata ace zaiyi
komai akan lamarin yaran nan amma kafin a ganshi ma
aiki ne"
Umma ta fahimci da Kawu Rabe take. Murmushi kawai
tayi "kada ki damu Hajjo, Garzalin ma ai babanta ne
kuma na fadawa su Yaya Abu don su san me ake ciki.
Saura kuma sai yazo munji"
Kawu Garzali sallama zai shigo dakin yaji Hajjo tace
"Kinsan Allah Bara'atu kada ku yarda kuce kun amince
ba tare da munji ta bakin Asmau ba, bazan yarda kuyi
mata auren dole ba. Idan bata so ya hakura kawai"
Umma tace "Hajjo mu har mun isa muce bama so? Kada
ki manta duk abinda ya faru da Asmau. Yanzu duk
wanda yazo neman aurenta ai alfarma yayi mana"
Hajjo ta danyi shiru tana tausayawa jikarta "kuma fa
haka ne. Allah Ya rabamu da mummunar kaddara"
Tashi Umma tayi "dama yanzun ma ina jin shawara ce
dai yake son bamu a matsayinsa na uba gareta."
Kawu Garzali ya gaishe da Hajjo sannan tace su fito falo
Alh Adamu yazo.
*****
Sun zazzauna an gaisa da Alh Adamu da Mama Yalwa da
bata dade da shigowa ba itama.
Yayi dan gyaran murya wanda ya janyo suka fuskance
shi "Nasan Yalwa ta fara sanar dake dalilin zuwan nan.
Mal Musa ya kirani a waya ya sanar dani yadda suka yi da
Qasim akan auren Asmau. To shi a son ransa nan da
lahadi su zo ayi magana ta iyaye a tsayar da lokaci. Shine
ya bukaci lallai in fara sanar daku domin ayi shawara"
Hajjo ce ta soma magana "hakika Alhaji kai uba ne ga
dukkan 'ya'yan Bara'atu. Ka rikesu tsakani da Allah tun
lokacin da mu da suke dolenmu muka wofantar dasu.
Duk shawarar da ka yanke akan yarinyar nan muna da
tabbacin bazata cutar da ita."
"Duk da haka Hajjo me kuka gani? A basu dama su zo ko
akwai wani tanadi da kuka yi mata".
Kawu Garzali yayi saurin cewa "haba haba Alhaji akwai
wani tanadi ne da ya wuce aure. Amma Haj Bara'atu me
kika gani?"
Idanu suka koma kan Umma. Daga yadda Alh Adamu
yake magana ta tabbatar yana so su amince tunda har ya
zo gidan da da kansa. Mutumin nan yayi musu gata fiye
da tunanin mutane. Ta dauke shi tamkar dan uwanta
bazata iya bijere masa ba balle kuma Asmau.
"Nima dai bani da zabi sai abinda kuka yanke. Wannan
aure idan ya yiwu ba karamin dago mata martaba zaiyi
ba a idon jama'a sai dai muyi fatan alkhairi. Shi kuma
Abubakar Allah Ya gafarta masa" ta kare da guntun
hawaye. Da yana raye duk wannan abin bazai taso ba.
Mama ma sai ta soma kuka duk kuma zukatansu suka
raunana. Alh Adamu yace "zaku fara ko?"
Da yaga sun nutsu ya ce "tsakani da Allah ni naso nasa
Abdulhalim ya nemi aurenta domin kare martabarmu
gabadaya. Sai na bari ta dan kara kwana biyu ashe rabon
Qasim ce. Zan sanar dashi su zo jibin. Idan yaso sai mu
kira dangi na kusa azo ayi komai da wuri. Iyalin Mal
Musa sunyi mana abinda bazamu manta ba tunda suka
bari dansu ya nemi auren tamu 'yar."
Sunyi ta tattaunawa akan maganar karshe mazan suka yi
shirin zuwa masallaci. Aka bar su Mama suna kara
shawara akan kamar yaushe ya kamata asa auren idan
dangin Qasin sun nemi asa rana da wuri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽41
Batul Mamman💖
Asmau tana can gidan Zubaida suna hirarsu bata san
wainar da ake toyawa a gidansu ba. A cikin hirar ne ta
fada mata zancen Qasim da Col. Ishaq.
Zubaida taji dadi sosai "kinga yadda Allah ke juya
lamarinSa ko. Shawarar zan baki ki yarda kiyi aure
amma ki zabi wanda zuciyarki tafi so. Ni shaida ce akan
irin abinda Qasim yayi da kika bata to amma nafi
danganta hakan da rike amanar Abubakar da yayi.
Bansan gaskiyar lamari akan menene a zuciyarsa ba
yanzu. Ma'ana soyayya ce ko tausayi. Shi kuwa sojan nan
dole na yaba masa. Duka duka yaushe ya sanki amma
yake sonki da aure"
"Ba kya tunanin nan gaba matsala ta taso ko a kaina ko
akan Amatullah"
"Hmmm Asmau kenan, ke kike da goben da har kike
tunanin matsala? Yadda Allah Ya daidaita miki lamura
yanzu, idan har wani abin ya taso a gaba Shi din dai zai
mana magani. Kada ki manta nima ba 'yar aure bace
amma Allah Ya hadani daku gashi babu wanda ya taba yi
mim gori. Auren ma Hajjo ce ta hada. Zamana nake
lafiya na manta da kazantar da na taso cikinta. Yadda na
hadu daku da yardar Allah itama zata hadu da mutane
nagari a rayuwarta"
Asmau ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na taho mata.
Duk matar da tayi zina ta gama cutar abinda ta haifa. Sai
dai idan an hadu da mutane na kwarai. Kuma duk da
haka haifewar itace tafi akan zubar da ciki wanda yake
daidai da kisa idan an busawa jaririn rai. Mace sai ta
sami rahmar Allah idan ta rungumi kaddararta ta bawa
abinda ta haifa tarbiyar da ta dace da addininmu.
"Ki kara hakuri da rayuwa Asmau. Haka Allah Ya tsara
miki. Ke kika zama ishara ga masu hankali wadanda idan
sunji labarinki zasu san cewa biyewa sharrin yanar gizo
da son zuciya halaka ne. Uwa uba babu wani alkhairi da
yake tattare da shiga groups din nan na whatsapp ko
facebook masu yada alfasha."
"Nagode Antina ta kaina. Allah Ya raba lafiya mu sha
suna"
Dadi Zubaida taji da taga Asmau ta dan sake. Amatullah
tana tsakar gida suna wasa da yaran Zubaidan.
"Tashi mu soya wainar fulawa"
Asmau ta zaro ido "yaushe muka gama cin abinci?"
Cikinta ta shafa "bani nake so ba kaninki ne ko kanwa"
"To kala masa sharri saboda bashi da baki. Ina fulawar
take na hada?" Ta fada tana tashi.
Ranar dai sun wuni suna hira kuma taji dadin shawarar
da Zubaida ta bata. Duniya kenan, Zubaida da ta tashi a
matsayin 'yar magajiyar karuwai gashi Allah Ya sauya
mata rayuwa. Sai bayan magariba Asmau tayi shirin
tafiya. Dama Jafar yace zai dawo daukarta sai ya kira
yace ayyuka sun masa yawa. Nan kuwa bata san suna
can gidansu ana maganar aurenta bane.
Zubaida ta sake yi mata tuni akan lallai kada ta bari dama
ta kubuce mata. Ta amince tayi aure
"Ni na kula sojan nan ba dai iya nuna kulawa ba.
Zuwanki nan kunyi waya sau uku."
Murmushin Asmau ya tabbatar mata da zarginta na
cewa shi take so. Har kofar gida ta rakata suka tafi titi
suka shiga adaidaita sahu ita da Amatullah suka tafi gida..
Abin mamaki tana zuwa ta tarar da Anti Bintu tazo da
yaranta wai zasuyi weekend. Tayi murna sosai.
Amatullah ma ta ganesu saboda haka ta saki jiki ana hira.
Umma tace idan ta huta tazo dakin Hajjo tana son
ganinta. Anti Bintu Asmau ta kalla tana dan murmushi,
ko dai ta fadawa Umma zuwan Jikamshi Zaria ne.
Karshenta maganar aure ce. Ta riga ta kudiri niyar bin
shawarar Zubaida. Zata tsananta addua ta amince da Col.
I M Jikamshi.
*****
Ko kayanta bata cire ba da ta shiga daki Jikamshi ya
kirata kamar yasan tunaninsa take yi a wannan lokacin.
Daukar wayar tayi tare da yin sallama.
Shima lokacin yana gida ya tasa laptop a gaba yana
kallon wasu hotuna da ya dauki Amatullah. Yana son
yarinyar nan, ko babu komai ta dauke shi uba sannan
gashi tayi sanadiyar hadashi da Umminta. Safinansa
akwai shiga rai.
Sallamar Asmau ce ta katse masa tunani ya amsa mata
cikin daddadar muryarsa.
"Matar Jikamshi kun dawo gida lafiya?"
"Lafiya kalau"
"I miss you so much"
"Duk wayar da muke yi tun safe?"
Yayi yar dariya "yanzu ke hirar waya ta isheki. Ni nafi son
na ganki a gabana. By the way lokacin da na baki fa yayi.
Anyi sati daya ya kuka yi da Qasim?"
Shiru tayi domin kuwa bata sami biyan bukata ba. Tayi
kokarin nuna masa ya hakura da zancen aure sai ya
rinka danganta abin da ko tana gudun aurensa saboda
tunanin Abubakar ne. Karshe yace mata ta jira nan da
lahadi komai zai zo karshe.
Col Ishaq yace "ya kika yu shiru? Kada kice min bakiyi
komai ba."
Sautin muryarsa kamar baiji dadi ba tace "ka kara hakuri
yace na jira zuwa ranar lahadi idan yazo kamai zai zo
karshe"
"Ban fahimceki ba, komai zaizo karshe kamar yaya?"
Asmau kanta bata gane abinda Qasim yake nufi ba "nima
dai haka yace min"
Col. Ishaq ya tashi daga kashingidar da yayi "look Matar
Jikamshi, ni mutum ne kaifi daya. Idan kina jin nauyin
fada masa saboda kusancin families dinku ni zan fada
masa da kaina. Tunda naga ya cigaba da yi min text da
waya nasan bai san alakarmu ba. Kinga kashe wayar
kawai bari na kira shi na fada masa Ishaq da Asmau suna
son juna don Allah ka nemi wata"
Bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba "yanzu don
Allah sai ka fada masa haka"?
"Kin dauka wasa nake yi, yara ne suke da lokacin wasa da
soyayya."
Tace "kayi hakuri zuwa lahadin please"
Yadda take magana duk ya kashe masa jiki. Zai iya hakuri
amma zuwa sunday kawai. Daga nan kuwa to sai dai
ayita ta kare. Shi ba don yana ganin mutuncin Qasim din
ba tun ranar da ya gansu da Asmau da a lokacin zai fada
masa.
"Yarinya dake duk kin rikita min lissafi. Amma zan rama
ne, sai kin shigo gidanki"
"Nima fa ka rikita min"
"Me kika ce?"
Zancen zuci ne ya fito fili tayi saurin toshe bakinta. Ta
rasa inda zata sa kanta don kunya. Tana ji yana mata
dariya don yasan bata so yaji abinda ta fada ba.
"I love you Matar Jikamshi. Nasan bazan kara samun
nutsuwa ba idan ba aurenki nayi ba. Na riga na fadawa
Hajiya amsarki nake jira a fadawa iyayena maza. Idan
kika zabi Qasim zan tayar da yaki a zuciyarki"
Wani dadi ne taji yana ratsata. Ashe tana da rabon
samun farinciki a rayuwarta. Ita ma tana son shi kuma ta
shiryawa duk wani nau'i na gori da zai iya zuwa daga
danginsa. Abinda ake gudu ya riga ya faru sai dai a kiyayi
gaba.
" 'yarka da Yassar ma bazasu barni ba idan na zabi wani
ba kai ba. Da ka tashi sai ka hada da zuciyata data
Amatullah kuma harda ta kanina."
Da tasan irin yadda yake ji a ransa da ta rage yi masa
magana ko don ta sassauta masa. Ajiyar zuciya yayi har
tana jin sautin
"Say you love me please" ya fada cikin sanyin murya.
Yau daya zata sakaya kunyarta ta farantawa mai faranta
mata "I do love you _Jikamshina_"
Kafin ya kara magana ta kashe wayar gabadaya don
tasan zai sake kira. Kwanciya tayi akan gado tana juyi ita
kadai zuciyarta kamar an wanke mata.
Shi kuwa rike yake da wayar a hannu yana murmushi.
Hmmm bari dai ace an daura musu aure. Ranar Asmau
zata san tana da masoyi. Zaiyi iya kokarinsa wurin nuna
mata soyayya da cewar itama har yanzu tana da
darajarta a cikin mata. Abinda ya wuce a baya sai ayi ta
addua da fatan Allah Ya yafewa musulmi kurakuransu.
*****
Tana ta maimaita hirarsu a kwakwalwarta tana dariya
Amatullah ta shigo
"Ummina Umma tana kiyanki"
Ai da sauri ta sauko daga kan gadon. Shaf ta manta
Umma tace tana son ganinta.
Saurin da take yi yasa Amatullah tace "Ummi guduwa
zamuyi ne? Me nene akan gadon?"
Asmau tayiwa kanta dariya sannan ta dauki Amatullah
tana juyi da ita. Soyayyar Jikamshi ta zame mata wani
bangare mai mahimmanci a rayuwarta. Tana juyin tana
dariya.
Amatullah tana tayata duk da bata san dalilin murnar
Ummin ta ba
"Ummi abin dadi ne ya fayu?"
"Shine zai faru in sha Allah Ama, muma Allah zai bamu
rayuwa mai tsafta kamar kowa"
"In ce Alhamdulillah?" Amatullah ta tambaya
"Fadi kinji Aman Ummi"
Sai da ta gama murnarta ta kama hannun Amatullah
suka fito. A falo ta barta ta karasa dakin Hajjo. Kafin ta
shiga taji muryar Anti Bintu tana magana sama sama da
ji kasan ranta a bace yake
"Yaya Bara wallahi Asmau tana son Ishaq. Don ta fada
miki zata sallamesu duk su biyun kawaici ne kawai. Ita a
tunaninta bata da wata kimar da namiji zai aureta. Don
Allah kada ku shiga tsakaninsu. Hajjo kiyi mata magana "
Hajjo tace "Bintu nima ba wai naki Ishaq bane. Ki tuna
wacece Asmau, tana da tabon da babu ruwan da zai
wanke shi duk duniya. Qasim da iyayensa sun san komai
game da ita kuma dazu muke ji ashe saboda ita yaki aure
tuntuni wai kada kishiya tayi mata gori ko habaici"
Anti Bintu tace "to duk abinda yayi ai ba wai sunyi da ita
zata aure shi bane. A yadda na kula da irin son da Ishaq
yake mata ba zai hakura kai tsaye ba."
Umma kanta tasan wanda Asmau take so amma bazata
iya yiwa Alh Adamu musu ba kamar yadda shima yaji
nauyin Mal Musa. Idan ta biyewa Bintu jan zancen kawai
za'ayi ta yi azo zumunci ya sami rauni.
"Bintu don Allah ki bar zancen nan. Komai ya kure tunda
ranar lahadu zasu zo kawo kudi. Itama sai tayi hakuri ta
karbi kaddara"
A fusace Anti Bintu ta mike "ni bazan zuba ido ina kallo a
cuci yarinyar nan ba. Ba kwa tunanin kada *abinda ake
gudu* ya sake faruwa? Don kaddara ta fada mata
shikenan kuma bata da damar zabar wanda take so"
"Abinda ake gudu ya riga ya faru kumq shine yasa dole
duk muyi hakuri. Kina jin da hakan bata faru da
rayuwarta ba zan amince da auren nan ne? Yanzu kuwa
bamu da bakin magana tunda mu za'a taimakawa. Ki
dena bata bakinki akan maganar nan. An gama yanke
shawara tun dazu"
Hajjo ta rasa yadda zatayi da su biyun. Kowacce ta kafe
har suna neman yin fada "don Allah kuyi hakuri. Bintu
kece karama, mu taru kawai mu tayata addua."
Hawayene kamar an kunna famfo yake saukowa daga
idanun Asmau. Dama shiyasa Qasim yace ta jira zuwan
lahadi? Yanzu shikenan tun ba'aje ko'ina ba an datse
mata samun farinciki daga wurin Jikamshi. Duk maganar
su Umma kuma gaskiya suke fada. Ita din tana da tabo a
rayuwarta. Wannan yasa a komai shawararta zata zamo
ta karshe. Iyaye zasuyi ta ganin kamar komai suka yanke
shine alkhairi gareta.
A sanyaye ta shiga dakin ta zauna a kasa.
"Umma indai auren Qasim kuke gani shi yafi dacewa
dani na amince"
Anti Bintu ta taso ta tayar da ita tsaye.
"Asmau wace irin magana ce wannan. Ishaq kike so
kuma na shaida yana matukar sonki. In Allah Ya yarda
shine mijinki"
Umma taji tausayin Asmau har ranta amma yadda abin
yazo musu ne basu da yadda zasuyi "Bintu na dauka
mun gama maganar Ishaq dinnan"
"Yaya Bara'atu bazan bar maganar ba sai naji daga bakin
Ishaq ko shi din ya hakura"
Cikin kuka Asmau tace "Anti Bintu ki bar maganar kawai.
Allah Yasa hakan shine mafi alkhairi"
Tashi tayi ta fita jikinta duk babu kwari. Gobe in Allah Ya
yarda zata kira Jikamshi ta bashi hakuri. Bata san wace
irin rayuwa kuma zatayi da Qasim ba. Mutumin da bata
taba jin sonsa ko kadan a ranta ba.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽42
Batul Mamman💖
Sallar isha kawai tayi ta kwanta sai kuka. Ganin bazai
fishsheta ba yasa ta tashi ta dauro alwala ta soma nafila.
Yi take tana kuka tana kara istigfari. Rokon Allah

Please Login or Register in order to submit comment