Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sha da yawa. A hankali zata ratsaki." Ta hado mata
da wasu kullin magani duk na sha ne. Tace da kanta ta
hadasu kayan amfanin jiki ne.
Tunda ta fara bayani kan Asmau a kasa. Da farko kunya
take ji daga baya sai hawaye. Anti Bintu ta rude "menene
kuma Asmau?"
"Anti yanzu a matsayin budurwa fa zanyi aure amma
....."
Fadawa tayi jikin Anti Bintu ta rungumeta tana kuka.
Itama ta biye mata tana kukan tana rarrashi. Umma
dake bakin kofa tana jinsu itama da nata hawayen. Babu
wani abu a duniya da zasu bawa Asmau ya dawo mata
da budurcinta. Shi kam idan ya tafi ya tafi kenan. Shiyasa
ake so mata mu kiyaye. Kada ki sayar dashi a waje wasu
suci kudinki da sunan zai dawo. Halittar Allah da 'yan
dabaru na mutane basa taba zama daya.
"Ki dena kuka Asmau. Shima Ishaq din yasan komai ba
yaudararsa kika yi ba. Amma dole ki gyara jikinki saboda
rayuwar aure zakiyi yanzu. Ki cire yawan tunani don
Allah. Bashi da fa'ida. Yawan kukan nan tamkar baki
godewa Allah ba da ya ni'imtaki da samun masoyi. 'Yan
mata da zawarawa nawa ke kwadayin irin wannan sai
gashi ke Allah Ya kawo miki don Ya saukaka miki
matsalolinki na baya."
Haka ta dauki jakar da magungunan jiki a sabule. Yadda
'yan mata ke rawar kafar shan magani idan bikinsu yazo
sai gashi ita jin abin take kawai wani iri. Yanzu haka za'a
daura auren budurwa mai 'ya. Allah abin godiya.
*****
Sun fi sati da dawowa Kano sannan Col. Ishaq ya dawo.
Yana zuwa gida wanka kawai yayi tunda yayi sallah ko
abinci ya kasa nutsuwa yaci ya fice. Hajiya ta girgiza kai,
Allah Ya kara hada kawunansu su zauna lafiya.
Asmau ta zauna ta hada abinci mai rai da lafiya wanda ya
dace da tarbar bako. Bata taba yi masa abinci ba. Idan
yazo lemo kawai take bashi da snacks saboda tana
kunyar irin wannan. Yau ma Umma ce ta bawa Yassar
kudi akan a siyo abubuwa na abinci yau kwadayi take ji.
Tasan yau Ishaq zai dawo amma saboda kunya Asmau
bazata yi yunkurin yi masa wani abu daban ba. Itama
kuma hakan yafi mata. Bata taba bawa 'ya'yanta kofar
idan saurayi zai zo ayi ta girke girke kamar maigida ba.
Sai kaga 'ya'ya basa kunyar iyayensu. Bayan ta gama
Umma tace "ki dibarwa Ishaq mana kinsan matafiyi kila
yayi sha'awa." A kunyace ta diba ta ajiye masa nasa.
Da ya iso Amatullah ta dafe shi tana ta murnar ganinsa.
Yayi musu tsaraba ta doya da sauran abubuwan
kudancin kasarmu. Idonsa kyam a bakin kofa har Asmau
ta fito. Ji yake inama dai anyi auren. Yayi kewarta sosai,
ga wani haske da kyau da ta kara saboda mayuka da
sabulun gyara jiki da Zubaida ta hada mata da kanta.
Itama ganinsa ba karamin dadi yayi mata ba. Tana zama
yace
"Yi a hankali kada na narke da wannan kallon da kike yi
min"
Sam ta kasa boye murnarta shiyasa yake ta tsokanarta.
Da ta gaji da kunyar ta soma ramawa. Yaci abinci ya
kuma yaba da iya girkinta. Daga nan ne suka dasa hira
har ta fada masa cewa ita dasu Umma zasu je Azare da
Jos nan da sati daya.
"Wannan tafiyar dani za'ayi in sha Allah. Dole naje har
gida na godewa mutanen da suka taimaka wurin kare
min martabar iyali."
"Kuma har gidan Uwargida zamu je. Umma tace dole
Zubaida ta ga mahaifiyarta"
"Tabbas uwa komai munin halinta ba'a canja mata suna.
Kila kiga rabon shiriyarta ne idan taga 'yarta tayi aure
har da 'ya'ya. Ki fada min da wuri ranar da aka yanke yin
tafiyar sai na shirya da wuri."
Ta danyi ajiyar zuciya "Yaya Qasim ma yace zashi"
Murmushi Jikamshinta yayi "Matar Jikamshi bazan taba
rabaki da Qasim ba. Ina son halayensa kuma nasan
mutum ne nagari. Ko jiya munyi waya dashi. Yasan
Asmau matar Jikamshi ce wannan ya isheni kwanciyar
hankali. Ke dai Allah Ya kaimu muje mu dawo a fara biki
"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽51
Batul Mamman💖
Shirin tafiya sosai suke yi. Umma ta nemi Shemau da
Jafar su kawo abinda ya sauwaka wanda zasu kaiwa
mutanen Azare da Jos tsaraba. Duk da bata san Zulaiha
ba amma ta yaba da taimakon da tayiwa Asmau. Sune
suka rufawa 'yarta asiri ba don haka ba Allah kadai Yasan
irin rayuwar da zata tsinci kanta a ciki yanzu.
Shemau dai katan din taliya hudu ta kawo da maggi. Shi
kuma Jafar galan din mai da katan din macaroni bibbiyu.
Suna zaune a falo ana ganin kayan tana saka musu
albarka. Idon kuka sai da tayi sana'ar tata kafin tayi
godiya. 'Yan uwanta sun rufa mata asiri. Bata san mata
nawa bane irinta a duniya wadanda kyama da hantara ta
dangi ta kara tura su ga aikata sabo. Umma tace "na
bawa Yassar ya siyo min buhun shinkafa biyu sai a bawa
su Rashida daya ita ma Zulaiha daya."
Asmau ta kara yi musu godiya "nima zan duba cikin
kayan da kuka bani wanda ban dinka ba na daukar
musu."
"Hakan yayi kyau" inji Hajjo "kai Yassar ina naka ne? Ka
zauna sai washe baki kake yi ban ga wani abu daga
gareka ba"
"Hajjo ni da ban fara aiki ba ina ni ina gudummawa. Ai
ma na kyauta tunda zan tuka mota." Sai ya kara fadada
murmushinsa "ashe da Yayanmu za'ayi tafiyar."
Shemau tace "haka Umma ta fada min. Ni fa har kunyar
Qasim nake wallahi. Nutsuwarsa tayi yawa. Gashi dai
bashi zata aura ba amma ko kadan bai bari hakan ya
zama sanadiyar bacin zumunci ba"
Yassar ya dan tabe baki "au shima zuwa zaiyi? Ni da
mutumina nake yallabai baban Amatullah"
Umma ta rike haba "oh ni Bara'atu, nagode Allah a
namiji kazo Yassar da ina tsammanin sai kunyi fada da
yayarka. A take takenka da gani zaka iya kwacen saurayi.
Idan Ishaq yazo gidan nan aka yi rashin sa'a kana nan
kayi ta rawar kafa kenan. Jiya ina jin ku kana mita wai
Asmau taki fitowa da wuri"
Dariya suka yi, Yassar ya sosa keya "wallahi Umma
burgeni yake yi. Nifa gaskiya idan an gama bikin nan zan
nemi short service nima na zama soja. Baki ga ba idan
yana tafiya ko magana....kai"
Hajjo tace "anya Bara'atu kin tabbatar yaron nan namiji
ne ba mata maza ba?"
Su Jafar sai dariya Yassar ya tashi yana tura baki. Shi ba'a
kyauta masa ba. Yabonsa fa kawai yayi saboda ya burge
Asmau. Da taga anyi masa taron dangi sai ta koma
bayansa tana kare masa. Yace "rabo dasu sai sun ga
matar da zan aura ma sis. Kowa sai ya yaba harda
tsohuwa mai ce min mata maza" aka sake dariya.
******
Lokacin da Col. Ishaq ya fadawa Hajiya zaiyi tafiyar nan
dasu Asmau ta dage itama sai taje.
"Ke da kike fama da kafa Hajiya"
"Kada kaga laifina. Ba wai na karyata abubuwan da
Asmau ta fada mana bane amma ance gani ya kori ji. Kai
sonta kake da aure ni kuwa son 'ya nake mata. Ina so
idona ya gane min inda ta rayu kafin haduwarku. Ina son
samun hujja ga mutanen da tuni suka fara kawo min
sukar auren nan. Da yawa cewa suke karuwanci tayi
lokacin da ta bar gidansu. Bazan tura kowa a dangi ba
bare a sami na gutsiri tsoma. Kai dai kawai ka hadani da
dreba idan motarka ta cika"
Ji yayi jikinsa yayi sanyi. Mutum ba'a iya masa.
Mahaifiyarsa kuma da gaskiyarta. Da yana da yayye kila
su zata wakilta tasan bazasu yi mata karya ba. Kuma gara
taje din akan ta tura wani.
"Shikenan Hajiya Allah Ya kaimu. Bilkisu sai ta koma
gidan Safiyya ko su Dahiru"
"Tare zamu je kasan rabonta da gida tun haduwarmu da
Asmau. Ita ma gara taje ta kwana biyu kafin bikin tunda
ta gama jarabawa"
Da ya kira Asmau ya fada mata ko kadan bata nuna
damuwa ba. Har zuciyarta dadi taji ko babu komai idan
akwai wani zargi da yake ransu zasu ganewa idanunsu
cewa ba karya tayi ba.
Ranar da zasu tafi sammako suka yi. Yaran Shemau duka
ta kawosu gidan Umma zasu zauna da Amatullah da
Hajjo. Asmau da ita taso tafiya Shemau tace gara ta
barta ta fara sabawa da rashin ganinta saboda idan anyi
biki sai kamar bayan sati biyu ko uku za'a kawo mata ita.
Ta dai amince don babu yadda zatayi ne. Basu saba
rabuwa da juna ba. Wani abin ma sai sunje kwanciya ta
mayar da kanta yarinya ta biyewa Amatullah suyi ta hira
tana sauraron shirmenta. Burinta ta dasawa kanta
babban matsayi a zuciyar Amatullah yadda nan gaba
yarinyar bazata nuna mata kyama ba idan taji tarihin
haihuwarta. Soyayya kuwa zata nuna mata hadda wadda
take tunanin da Abubakar yana raye shima zaiyiwa
'yarsa. Allah Sarki bai ma san da cikin ba bare
haihuwarta.
Sun gama loda kayansu a motoci aka fara shiga. Asmau,
Bilkisu da Zubaida suna motar Jafar da yaran Zubaidan.
A motar Umma kuma kawu Garzali ne a gaba Yassar zai
tuka. Baya ita da Mama ne. Shi kuma Col.Ishaq drebansa
ne zai tuka su. Yana gaba a baya kuma Hajiyarsa da
Shemau.
Tun zuwansu gidan ya samu Asmau ta dan fito kafin a
fara shiga mota "yanzu ina kallo zamu je wuri daya
amma ba motarmu daya ba? Wannan tsarin baiyi ba
gaskiya ki dawo motarmu Shemau ta koma ta Jafar. Wa
zan rinka satar kallo ta madubi"
Zaro ido tayi "sai na zauna kusa da Hajiya don rashin
kunya kai kuma kana kallona?"
Yace "to meye a ciki? Naga auren danta zakiyi karewa."
Ta kawar da kai tana murmushi "ni dai kayi hakuri don
Allah kada a fito ka fara cewa na dawo motarku. Kada ka
sani jin kunyar da ban shirya ba".
"Dama kina da kunyar ne? Ana shirin tafiya kin kasa
hakuri kin fito ki ganni"
Asmau ta rasa me zata ce sai bude baki kawai da tayi
cikin mamaki. Shine fa yayi mata waya yana magiyar ta
zo ya ganta.
Dariya yake mata don yasan ya kureta "rufe bakin kada
ya makale a haka"
Ta dan juya ido "gara ya makale kowa ya huta"
"Tuba nake Matar Jikamshi, shi bakin nan naki da kike
gani ba karamin mahimmanci gareshi ba. Idan ya
makale an cuce ni."
Ta soma dariya ganin yadda ya kara marairaice fuska
"meye amfanin bakin banda cin tuwo. Idan ya zauna a
haka kaga na dena shan wahalar bude shi"
Yace "da gaske kina so na fada miki kadan daga cikin
mahimmancin bakin Matar Jikamshi"
Wani jan zancen yake yana kallonta kasa kasa. Ko baa
fada ba tasan ko me zai fada karshenta sai taji kunya
shiyasa ta saka hannuwanta biyu ta toshe kunnenta tana
ja da baya.
"Ka barshi kawai na yafe. Wani ilimin ba sai na sani ba"
Yayi murmushi mai kyau "kaji min yarinya. To ba abinda
kike tunani zan ce ba. Shiyasa nace kinfi karfina dama"
Sosai Asmau taji kunya ta koma ciki da sauri tana jiyo
dariyarsa.
Yanzu da suka shiga motocinsu zasu tafi ji yake ina ma
motarsu daya. Ko yaya suka juya su kama juna suna
kallon junansu.
*****
A titin Zaria road suka hadu da Abdulhalim da Qasim a
motar Qasim din. Daga nan suka mika sai Azare.
Tun fitowarsu Zubaida ana ta hira a mota amma jikinta
yayi mugun sanyi. Ba don Umma tayi mata nasiha sosai
ba ita ko kadan bata son tuna asalinta. Yanzu duk
mutanen nan kowa sai ya ga a irin kazantar da ta tashi.
Addua take Allah Yasa kada su je su tarar da irin tsofaffin
yan tashan nan da basa tsoron Allah masu zuwa wajen
Uwargida a dakin. Sai su zo suce wai banda tsufa ya fara
zuwar mata duk tafi yaranta iya aiki. Wani sa'in ma idan
taji kudi sosai komai kuruciyar mutum bata jin komai
take bashi dama. Koda yake ina wata kunya ga mace irin
wannan.
Motarsu ce a gaba Zubaida tayiwa Jafar kwatance. Su
Asmau ma jiki ya mutu suka dena hirar saboda ganin
yadda yanayinta ya canja. Asmau tana zancen zuci tace
kada Allah Ya kawo ranar da Amatullah zata kyamaceta
irin yadda Zubaida take yi a yanzu.
Gidan yana nan yadda yake ko fenti ba'a canja ba. 'Yan
bakin kasuwa suna kallon abin mamaki. Motoci irin
wadannan a kofar gidan Uwargida. Kuma gashi harda
mata bare ace wasu kadangarun barikin ne suka zo
neman 'yan matan gidan.
Asmau da Zubaida aka rasa me fara shiga. Ita Zubaida
ma hawaye take yi har Kawu Garzali ya gani. Da sauri
yazo ya karbi baby dinta mai suna Shuaibu suna kiransa
Aiman sannan ya rike hannunta suka fara shiga. Zuciyar
Asmau ta tsinke, yanzu haka Jikamshi zai shiga gidannan.
Allah Yasa kada shi ko Hajiya wani yace a fasa auren.
Zuga guda suka shiga da sallamarsu. Matan a gaba maza
a bayansu. Kaya ne tarkace kala kala a tsakar gidan.
Wasu matan na wanki wasu suna girki. Kowacce da
sabgar gabanta. Kadan a ciki Asmau ta gane. Duk barin
abinda suke yo suka yi kallo ya dawo kan baki. Daga
kofar dakin Uwargida Bulayi ya fito. Mutumin da ya fara
kawota gidan nan. Dama can a dattijo ta san shi. Yanzu
kuwa tsufa ya kara bayyana a tattare dashi. Yana kokarin
zura takalmansa ne idonsa ya sauka akan Zubaida.
Fuskarsa ba karamin mamaki ta nuna ba yace "Zuby???"
Ranta a dagule yake dama ta harare shi "Zubyn uwarka"
a duniya yana cikin mutanen da ta tsana. Duk yarinyar
da aka kawo gidan sai yayi amfani da ita kafin kasuwarta
ta bude.
Maimakon ta ga bacin rai a fuskarsa sai ya washe baki
cike da fara'a yace
"Shegiya ita ce kuwa, kina nan da bakinki kamar reza"
Cikin dakin ya koma da sauri har yana tuntube. Suna jin
muryarsa yana kiran Uwargida tazo ga Zuby ta dawo.
Zubaida ta ji muryar mahaifiyarta tana cewa "Bulayi
kada kayi min wasan da zai tayar min da hawan jini"
"Yasin da gaske nake, bari na kamaki muje wajen"
Kunya ta kara kama Zubaida, yanzu haka zasu fito hannu
da hannu kamar wasu mata da miji a gaban mutanen
nan masu daraja a idonta. Dukkansu kallon kofar suke
zasu ga wannan Uwargidan ga wadanda basu taba
ganinta ba. Bulayi ne ya fara fitowa hannunsa rike da
sanda yana cewa "yi hankali da matattakalar kofar"
Rike da sanda ta fito wacce Bulayi ya daga mata daga
waje yana mata jagora. Tana nan da tsayinta fuskar nan
tayi wani irin dabbara dabbara saboda mayukan
bleaching da taji a baya. Sanye take da tubarau baki
wuluk irin na makafi. Tana mika hannu cikin iska alamar
lalube tace
"Zuby kina ina?"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zubaida bata san lokacin
da ta saki hannun Kawu Garzali ba ta tafi wurin babarta
tana kuka
"Mama makancewa kika yi? Wayyo Allah na, kinga ni fa
jikokinki na kawo miki nayi aure. 'Ya'yana hudu. Mama
ki bude ido ki gansu don Allah"
Uwargida tayi dan murmushi tana rungume da 'yarta.
Hawaye ya zubo mata tana ta shafa fuskar Zubaida tace
"Ashe zamu gana kafin na mutu Zubaida. Allah nagode
Maka. Ina yaran? Wane dan albarkan ne ya rufa min asiri
ya aureki? Kinga yadda Allah Ya mayar dani ko. Karyar
karuwanci ta kare bani da wani mataimaki sai Allah sai
Bulayi da bai gujeni ba"
Zubaida ta kalle shi sai taji kunyar zagin da tayi masa. A
yadda taga mahaifiyarta ta kara tsufa da yankwanewa sai
ta godewa Allah da Umma ta dage lallai sai tazo. Bulayi
ne yace "Uwargida tare da baki take fa. Ina jin surukanta
ne mu shiga daga ciki ko kuma ina zuwa dai" dakin ya
koma ya dauko tabarmi gudu uku. Kamar hadin baki
Qasim da Col. Ishaq suka ki zama. In da sabo tsayuwa ba
komai bace wurin soja da dan sanda. Sai akayi dace
kyamarsu tazo daya basa son zama a tabarmar da ta fito
daga dakin matar.
Sauran dai sun zauna sannan Zubaida ta fara yi mata
bayanin kowa. Yaranta kuwa sai da Uwargida tabi tana
shafasu tana binsu da kiss a fuska. Manyan biyu mace da
namiji dai kyankyaminsu suke. Tana yi suna gogewa duk
ta yaba musu yawu. Da Zubaida tace tare suke da Asmau
Uwargida ta mika hannu zata kamata. Balayi yace "Yar
dabas kin canja Yasin. Jikinki duk ya murje kinyi fresh.
Dama naso naga kama to kuma sai naga ta yanzu tafi ta
da kyau da daukar ido."
Wani mugun kallo Col. Ishaq ya sakar masa wanda ya
girgiza har hanjin cikinsa. Ba arziki yayi shiru. Asmau ta
dan matsa gaba Uwargida ta kama hannunta.
"Nayi sanadiyar lalacewar 'ya'yan mutane da yawa Yar
dabas, iyayenki har nan sun zo nemanki. Nagodewa
Allah da baki kama sa'a kamar yadda naso ba. Hakkin
wadancan shegun kadai ya isheni. Ni shaida ce akanki
har kika bar gidannan namiji bai taba zuwa kofar dakinki
ba. Ke kam kinji dadi 'yan uwa basu kyamaceki ba har
Allah Yasa rayuwarki ta koma kan layi. Me kika haifa?
Tausayi Uwargida ta rinka basu. Asmau ta soma kuka
saboda yadda ta tuna Uwargida da iya gayu duk
girmanta. Yanzu kuwa sai da dauriya zaka iya zama kusa
da ita saboda warin jiki. Su Umma sun gama gaisawa da
Uwargida sai Haj Lubabatu ta dan yunkura zata tashi.
Col. Ishaq yace "Hajiya kafar ce?"
Bata bashi amsa ba sai matsawa da tayi gaban Uwargida
ta zauna kusa da Zubaida tana kare mata kallo. Kuka
sosai ya kwace mata tace "Habiba"
Uwargida ta fara mika hannu inda taji kira. Rabonta da
amsa wannan sunan tun ranar da ta baro garinsu.
Hannunta har rawa yake tana ta mika shi ko zata kama
mai kiran tace "wace ce don Allah, babu wanda yasan
sunana sai 'yan garinmu"
Hajiya sai kuka ta kara shigewa kusa da Uwargida. Col.
Ishaq ji yake kamar ya janyota. Me ya hadata da wannan
matar. Hannuwanta duka biyu ta rike
"Lubabatu ce, Luban gidan Sarkin dorin Jikamshi"
Salati sosai Uwargida ta saka kafin ta rungume Hajiya.
Babu kyama Hajiya ta rungumeta itama suka barke da
kuka. Kowa sai kallosu yake. Matan gidan sun fito ganin
kwaf Qasim ya daka musu tsawar da ta kidimasu suka
bar wurin suna karo da juna.
Uwargida ta share majina da kasan zaninta tace "Allah
mai iko, ashe zan sake ganin na gida. Luba ina Baba da
Inna, ina 'yan uwana?"
Cikin kuka Hajiya tace "Liman da Inna sun dade da
rasuwa. Yayarki Indo ma babu ita. Sauran 'yan uwanki
duk suna nan an tara 'ya'ya da jikoki"
"Allahu Akbar, Allah Ya jikanku Baba, Allah Yasa sun yafe
min kafin su rasu"
Tana kuka ta labarta musu yadda almajirin Liman yayi
mata ciki ashe ma fyade ne yayi mata kuma ya gargadeta
kada ta fada har ciki ya bullo. Babu uzuri ko neman
ba'asi iyayenta suka tsine mata. Wannan kuskure ne
babba. Yana da matukar amfani jurewa wajen kula da
yara idan sunyi kuskure domin a toshe kofar gaba.
Tunda ta fiti take aikatau da ayyukan wahala domin taci
abinci. A haka cikin ya bare tana yawo a gari. A wani
gidan aikinta ne a Bauchi maigidan ya kuma yi mata
fyade da ta fada matarsa tayi mata duka duk da lokacin
shekarunta sunyi gaba don da jima tana rayuwar kunci
da wahala. Maigida ya karyata kamar yadda aka saba ji.
Shine da ta fito ta sami uwardaki. Bata zubar da cikin ba
ta haifi Zubaida. Da girmanta ta fara sana'ar karuwanci
kuma tace ta gwada rashin imani kamar yadda mutane
suka gwada mata. Sai shekaru biyu da suka wuce da ta
kamu da lalurar ido tayu nadamar rayuwarta. Duk
matan gidan sun dena bata kudin haya ga rashin abinci.
Ta kare da bawa mutane shawara da su rinka taimakawa
masu raunin imani da wadanda ke cikin matsanancin
hali don gujewa samuwar karin mugayen dabi'u a cikin
jamaa.
Su Mama duk anyi kukan tausayin labarin Uwargida da
kuma dadin handala da Asmau tayi dacen haduwa da
mutane nagari. Wannan kuma zamu iya cewa harda
adduar da suke yi mata ba tsinuwa ko zagi ba. A gidan
aka bar Zubaida da Kawu Garzali. Sun yanke shawarar
idan zasu koma Kano a tafi da ita sai a kaita Jikamshi taga
'yan uwanta ko da basa maraba da dawowarta.
*****
Daga nan gidan Rashida suka wuce. Dama tasan da
zuwansu. Sada ma yana gida yana jira ga su Abba duk an
zama samari. Cikin gidan aka yi musu shimfida mazan
kuma suna dakin nan da Asmau ta taba zama. Tana shiga
gidan sai kuka da ta tuna lokacin da ta zauna ga ciki ga
rashin iyaye a kusa. A falo taga Sada ya kalleta fuskarsa
dauke da murmushi yace
"Asmau kece kuwa?"
Tana kuka ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Sada ne
mutum na farko da ya fara taimakonta a rayuwa sosai
bayan Zubaida mai bata shawarar kada ta zabi
gurbatacciyar rayuwa. Wurinsu Abdulhalim yaje inda
aka ajiye musu kayan abinci. Sai da suka yi sallah suka ci
abincin.
A ciki suma matan sallar suka yi aka ci abinci. Nan hira ta
barke ana tuna baya ana kuka da dariya. Rashida tace
"yakamata watarana muje kiga Yaya Tagwai fa"
Asmau tayi murmushi, Yaya Tagwai ai ta janyo mata kara
shiga garari. Cikin yaran kuwa babu wanda ya tuna ta sai
Abba. Sai da suka yi laasar a ranar dai suka kama hanyar
Jos. Rashida da Sada sai lokacin biki zasu taho Kano.
Sun sha tafiya jiki kuma ya fada saboda zaman mota.
Duka matan a gidan Mami akayi musu masauki sai gari
ya waye zasu gidan Zulaiha. Asmau ta damu sosai da ita
saboda dena samunta da tayi a waya. Col. Ishaq ne ya
samarwa mazan masauki a cikin barikinsu na sojoji dake
garin. Shi da Matarsa sai dare suka sami damar yin waya
aka biya bashin soyayyar da ba'a yi ba a ranar.
Mami da yaranta sunyi kokarin karrama bakin Kano.
Bilkisu sai murna anzo gida. Da safe wurin shadaya suka
gama shiri aka dunguma zuwa gidan Zulaiha. Motarsu na
tsayawa Asmau ta hango Humaira da karuwar roba a
kanta cike da ruwa. Da sauri ta fito ta kira sunanta. Ai
tuni Humaira ta saki robar ruwan ya kware a jikinta ta
rugo da gudu ta dafe jikin Asmau. Sai ga kannenta suma
duk ruwan suka. Yara sai murna suke suna tambayarta
ina Ama. Kusan janta cikin gidan suka yi tawagarsu
Umma suka biyo baya suna mamakin yadda yaran ke
murna haka.
A durkushe bakin murhu tayi tozali da Zulaiha tana ta
hura wuta tana tari. Tsaye a gefenta kuma Zinaru ce ta
harde kafa tana masifa "malalaciyar banza, tun dazu
hada wuta ya gagareki. Yanzu idan suka fito da me zasuyi
wanka. Kinsan Gidado baya son ruwan sanyi...."
Zulaiha tace "Zinaru kiyi hakuri itacen ne mai danshi"
Tun a bakin kofar Asmau ta soma hawaye. Rayuwarta ta
gyara ga Zulaiha cikin matsanancin kunci har yau. Duk ta
kara figewa sai dan wuya kamar kazar mayu. Cikin sauri
ta karasa shigowa tace "Zulaiha"
Tashi Zulaiha tayi da sauri itama ta nufo Asmau cike da
murna da mamaki. Rungumar juna sukayi suna kukan
yaushe gamo. Zinaru babu bakin magana saboda yadda
gidan ya cika da mutanen da Asmau tazo dasu. Borin
kunya ta soma da taga su Shemau na binta da mugun
kallo.
"Haka ake tarbar baki kin tsareta a hanya kuna kuka. Ke
Humaira maza shimfida tabarmar nan a rumfar
babanku. Kai kuma Ali jeka ka taso babanku. Yau
Asmaun da yake ta jira ta dawo"
Wata mace ce wadda da kadan zata girmi Humaira ta
fito tana yatsina fuska.
"Hayaniyar me nake ji haka? Zinaru wannan banzar ta
dafa min ruwan wankan ko kuwa?".
Zinaru ta galla mata harara zata bata musu harka. A
yadda taga mutanen da shigar Asmau tasan akwai
maiko. Har ta fara nadamar barin Gidado da tayi ya auro
'yar mutumin da ya bashi shago a kasuwa.
Zulaiha sai murna take ta shimfida musu tabarma da
zannuwanta wankakku biyu don babu abinda zata basu
su zauna. Basu zauna ba sai tausayinta da suka rinka ji.
Zulaiha tana cikin mawuyacin hali. Yaranta kaf babu mai
zuwa makaranta yanzu. Duk abinda ya rage mata dashi
Gidado yayi aure. Watarana ya sha giya ya bugu yayi
mata duka cikin jikinta ya bare. A yanzu haka babu irin
wukakancin da basa gani ita da 'ya'yanta a wurin Zinaru
da amaryar Gidado. Yi sukayi kamar basa ganin su
Zinaru suka shiga hirarsu da Asmau da yan uwanta.
Col. Ishaq ba karamin haushinsa yaji ba bare da ya fito
yana tangadi alamun mayen jiya bai sake shi ba. Ya dubi
Zulaiha da take gaishe da su Umma. Wahala ta mayar da
ita wata iri. Idan za'a bashi dama daga Gidadon har
uwarsa sai ya kullesu.
Zulaiha tace "Ummi kinji dadi iyayenki sun yafe miki. Ji
yadda kika koma nayi miki murna"
Hajiya ce ta ce "kema in sha Allah bazamu tafi ba sai
mun hadaki da naki iyayen. Asmau ta fada mana komai
game da rayuwarki"
Zibaru ta cafe "to tace muku tana bukatar taimako ne?
Yarinya tana zaman auren soyayya da mijinta zaku shiga
tsakani"
Qasim ya taso mata "idan baki kiyaye bakinki ba wallahi
idan nasa aka rufeki babu wanda ya isa ya fito dake"
"Kaiiiiii, babar tawa kake yiwa tsawa" Gidado ya fada.
Darajar 'ya'yansa tasa duk mazan nan su Jafar, Yassar,
Abdulhalim ga soja da dan sanda basu rufeshi da duka
ba.
Zulaiha tana kuka tace "nasam bazasu yafe min ba.
Shekarun da yawa. Kara na kaisu na zabi wannan
rayuwar akan su"
Asmau tayi ta bata baki ta amince da shawararsu ta zuwa
gida. Zinaru tace "idan kika fita a bakin aurenki"
Yau da Zulaiha ta sami masu tsaya mata bata ji maganar
Zinaru ba tayi gaba 'ya'yanta na binta. Tana ji Zinaru tace
Gidado ya sake ta. Dama me ya rage mata a auren nasa.
Suna kallo duk suka fita. Zinaru tasan sun gama yawo
domin kuwa korarsu zaayi daga gidan.
Zulaiha ke kwatance har suka iso bakin gate din wani
makeken gida. Gida ne babba na gani a fada. Asmau tace
cikin tsantsar mamaki "nan ne gidaku?"
"Nan ne Asmau" su Humaira ma duk mamaki suke wai
daga nan mahaifiyarsu ta fito amma suke ganin kuncin
rayuwa. Daga bakin gate kenan ma. Maigadi yayi musu
iso akan cewa bakin mamanta ne. Jikinta a sanyaye suka
shiga. Gidan ya kara fadi gashi ya dace da zamani. A
wurin ajiye motoci ta hango kaninta da Alhajinsu.
Zuciyarta tana dar dar Alhaji na hangota ya taho wurin
da suke yana kallon Zulaiha. Shekarunta sha bakwai
rabonta da gida. Ana jiran aji da wacce zai tarbi yarsa.
A hankali yace "sai yau uwata? Sai yau kika iya tunawa
kina da iyaye?"
Abin tausayi Zulaiha ta fada jikin mahaifinta. Saboda
yadda ta kode sai ka zata wa da kanwa ne ba uba da 'ya
ba. Farinciki yake ji mara misaltuwa. Allah Ya karbi
adduarsa 'yarsa ta dawo. Ba karamin fushi yayi da ita ba
a da amma daga

Please Login or Register in order to submit comment