Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwadayi.
A gidan Babana ma sai tace naci. Mu a gidan Zinayu koko
da kosai muke ci, ko byodi da tea, ko tuwon safe ko
Ummi"
Kasa cin abincin Asmau tayi ta fashe da kuka. Sunga
rayuwa ita da Amatullah. Dan kudin da take samu a
kudin makaranta yake tafiya. Abinci kuwa sai dai aci
garau garau. Su Umma suma kukan suke tayata. Abinda
tafi karfi a da shine yanzu yafi karfinta. Anti Bintu tazo ta
rungumeta "komai ya wuce Asmau. Kuka bazai dauke
shekarun baya ba sai dai ya tuna miki da bacin rai."
Hajjo tace "haka ne ki dena kukan haka. Rayuwace kowa
da irin tasa duk da dai komai yana da sanadi. Naji dadi
da kika koyawa yarinyar nan tarbiya mai kyau."
A haka suka ci abincin ana taba 'yar hira har Asmau ta
sake. Kafin su tashi Amatullah ta sake cewa "Ummi daga
yau a nan zamu zauna ne?"
"Eh mana ai kun dawo gida kenan" inji Shemau
Tare duk suka tashi aka kwashe kwanukan suka fara layin
wanka.
Wurin shadayan safe Asmau na saka kaya don kuwa
Mama Yalwa tace yau a gidanta zasu yini taji wayarta na
ringing. Ko da ta dauka bakuwar number ta gani har tayi
zaton ko Zulaiha ce tace "tuba nake maman 'yan biyu
ban samu na kiraki ba"
Shiru taji daga daya bangaren tace "Zulaiha ko kinyi
fushi ne. Ni da ke fa ba'a ji kanmu ba"
"Ashe kin iya hira Idon kuka" ji tayi gabanta ya fadi.
Muryar da ko cikin bacci yanzu tasan zata gane taji.
Kamar yana gabanta ta dan russuna a kunyace ta gaishe
shi.
"Har kin gane mai magana, ko kuwa dai wayancewa kika
yi?"
Tana murmushi tace "Na gane"
Col. Ishaq ya gyara kwanciyarsa. Shi bai ma san dalilin da
yasa yayi mata waya da safe haka ba.
"To waye?"
"Baban Amatullah"
"Uhmm uhmm, a wurinta kadai nake baba. It seems ko
sunana baki sani ba. Shiyasa jiya kika kasa fadawa
yayanki"
Asmau taji muryarsa kamar baiji dadin hakan ba tace
"na sani kuma na fada masa ma"
Magana yake kamar maganar aiki ce mai zaman kanta
yace "me kika ce masa? I am sure ba Baban Safina kika
ce ba".
Ita fa kunyarsa take ji. Ganinsa take yi babban mutum
mai matukar kwarjini da cika ido shiyasa bata tsawaita
hira dashi. Sake maimaita tambayar yayi tace "Col I. M
Jikamshi"
Wani iri yaji yadda ta fadi sunan a hankali kamar bata so
yaji.
"I. M Jikamshi yana rokon alfarmar ayi saving din
numbarsa saboda kada ki sake kirana Zulaiha. By the
way ina princess dina?
"Ana yi mata wanka"
"To zan sake kira anjima ki hadani da ita. Ina fata kinji
request dina. Idan kika sake kirana da sunan mata zamu
kulleki ni da Safina. Ki gaida da Umma."
Amsa masa tayi da to...tana 'yar dariya ta ajiye wayar.
Mimi babbar 'yar Shemau ce ta shigo tana kiranta
Umma tace tazo falo. Hijab ta saka ta fito daidai lokacin
da Qasim ya dago kansa. Suna hada ido nata ya ciko da
hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai.
Ya kura mata ido yana kallonta "Asmau ke ce?"
Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a
da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. A da Abubakar ya fushi
kumari. Gashi duk ya canja alamun yana da sukuni.
Kusa da Umma ta zauna a kasa ta gaishe shi tana dan
murmushi ga hawaye
"Yaya Qasim ai bazan ganeka ba"
Yau da Asmau namiji ce babu abinda zai hanashi
rungumeta don ya nuna mata tsantsar farincikinsa da ya
ganta. Jiya da ta tsaya a Shanono su Inna suka ce dare
yayi ya bari gari ya waye ya karaso Kano ji yayi inama bai
biya ya sanar dasu ba. Yau dai burinsa ya cika Asmy din
Abubakar ta dawo gaban iyayenta.
Amatullah ce ta shigo falon tana kira Asmau. Duk da ta
sake da mutanen gidan amma haka halinta yake da an
dan jima sai ta nemi Umminta. Tana ganinta kuwa zata
kama wata sabgar.
Gaban Qasim har faduwa yayi da ya ganta. Baya bukatar
wani karin bayani ya tabbatar wannan 'yarsu ce wadda
rabon haihuwarta ya jefa iyayenta da su kansu cikin
rudani. Tashi yayi ya durkusa a gabanta yana shafa
fuskarta, muryarsa na dan rawa yace "yaya sunanki"?
Tayi masa murmushi irin wanda yake tunawa Asmau da
Abubakar idan tayi shi "Safinatu Amatullah Abubakay"
Rungumeta yayi kawai hawayen farinciki na fito masa.
Muddin yana raye yayi alkawarin kula da ita har karshen
rayuwarta. Yana shafa kanta yace
"Safinatu nine babanki"
Ta dago kanta tana kallon Asmau "Ummi ni babana biyu
ne"?
ABINDA AKE GUDU🙆🏽37
Batul Mamman💖
Tana gama wayar Ainau ta tambayeta ko waye tace
baban Amatullah ne. Ainau ta kurawa 'yar uwarta ido
"Yaya Asmau zaki iya yin sati a garin nan kuwa ko kawai
mu bi Yaya Yassar mu koma Kano"
"Kada ki damu Ainau, irin wannan abubuwan nasan ban
fara ganin komai ba ma. Idan ya faru ne yake taba min
zuciya na dan lokaci har nayi kuka. Dama abinda ake
gudu kenan, ba wai yin a lokaci daya ba, abinda zai je ya
dawo bayan kayi. Kinga rana daya a rayuwata ta canja
akalar komai nawa." Kuka suke yi duk su biyun Ainau
tana bata hakuri
"Ku zan bawa hakuri ma da na janyo ake yiwa tarbiyar
da Umma ta bamu kallon gazawa. Don Allah kada ku bari
taji wannan labarin. Shima Yassar din zanyi masa
magana"
Anti Bintu tana bakin kofar tana jinsu. Tausayin Asmau ta
kara ji ta koma wurin maigidanta. Alfarmar kada su
fadawa Yayarta tazo nema sai gashi Asmau tayi wannan
tunanin.
Sun dauki lokaci a dakin suna magana kafin su dawo falo
bisa umarnin Kawu Yusuf. Rokonsu yayi da suyi hakuri
da halin tsufa irin na mahaifiyarsa kuma yana fata zasu
sake a gidan bazasu takura kansu a daki ba.
Sai da suka yi sallah aka zauna cin abinci. Babu wata
hirar kirki sai hayaniyar Amatullah. Kowa jikinsa a
sanyaye yake. Ganin haka Asmau ta rinka dauko hira duk
don ta nuna musu bata tare da damuwa.
Su Yassar sun dawo daga masallaci inda suka yi sallar
la'asar yace zai kama hanyar komawa. Anti Bintu ta
tsayar dashi ya jira a kawo sako da take son ya tafiwa da
Umma dashi. Yana zaune a falon Col. Ishaq yayi masa
waya yana tambayarsa kwatancen gidan da suke zai zo
ganin Amatullah.
Yassar ya tashi tsaye cike da mamaki, sannan ya
kwatanta masa inda zaije ya jirashi sai yazo ya kawo shi
gidan. Anti Bintu ta tambayeshi ko lafiya ya sanar da ita
bakon da zasuyi. Murmushi tayi "anya 'yar yazo gani ko
uwar 'yar"
"Nima tunanin da nake yi kenan Anti. Mutumin ba
karamin burgeni yake yi ba. Idan yace yana son Yaya
Asmau ai ya gama min komai. Wallahi binsa zan rinka yi
sau da kafa".
"To sarkin zumudi, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi
zaki" Anti Bintu ta fada amma itama tana fatan hakan ya
tabbata. Dan ganin da tayi masa ranar da suka dawo da
Asmau ta yaba dashi.
"Bari kiga naje bakin layin kada yazo yayi ta jirana"
"Ita yayar taku tasan da zuwansa?"
"Kai bana jin ta sani, kyaleta kawai Anti kada ta bata
lamarin. Ba karamin aikinta bane ta tura masa Amatullah
taki zuwa su gaisa. Kuma ai kinga bai dace ba mutum
yayi tafiya irin wannan saboda danka"
Wannan karon dariya sosai ya bawa Anti Bintu. Lallai
Yassar da yana da iko tuni zai bawa sojan nan auren
yayarsa. Yana fita ta shiga ciki suna daki ana ta wanka
saboda zafin gari. Ta tarar Asmau ta shirya cikin wata
doguwar riga mara nauyi shudiya ta yafa karamin
mayafi fari a kanta. Anti Bintu tace ta taso ta tayata
hadawa bako abinci don duk 'yan matan gidan suna
Islamiyya.
Tashi tayi tabi bayanta ta bar Ainau da yaran. Da yake
akwai sauran abincin rana salad kawai ta sake hadawa ita
kuma Anti Bintu ta hada zobo mai sanyi.
Tray din abincin ta dauka ta shiga falo, ko tsakiyarsa bata
kai ba taji sallamar Yassar da ta Jikamshi. Sai dai murya
ta biyun ce tafi daukar hankalinta har ta daga kai suka
hada ido. Sanye yake cikin kayan aikinsa da hularsa rike
a hannu. Yayi kyau sosai. _Innalillahi wa inna ilaihi
rajiun_ ta fada saboda tsabar kaduwar da tayi
hannuwanta suna rawa tana neman sakin tray din a
kasa.
Wani irin kallo ya bita dashi yana wani kashe ido. Sai
kuma ya karasa gabanta ya karbi tray din da yake tangal-
tangal ta kasa rike shi da kyau. Sai da ya ajiye shi a kan
centre table din falon ya sake dagowa yana kallonta
kamar wadda aka kafe a wurin yace
"Duk murnar ganina ce haka tasa kika kasa motsi?"
Juyawa tayi bayanta taga Anti Bintu tana murmushi,daga
bakin kofa kuwa Yassar ne bakinsa ya kusa zuwa keya
don dadi. Ji tayi kamar ta make shi.
Mamakin ganinsa ta yi sosai har ta kasa hada wata kalma
a bakinta. Shi kuwa ba karamin dadi yaji ba da ya ganta.
"Kinyi tunanin wasa nake yi da nace zan zo? Gashi ko
wurin zama baki bani ba sai aikin daukar miki tray daga
shigowata"
Da sauri Yassar ya nuna masa kujera. Anti Bintu ta
karaso ta zauna suka gaisa amma har lokacin idonsa na
kan Asmau da ta tsaya kawai tana kallonsa. Bata taba
kawowa da gaske zai zo ba kamar yadda ya fada a wayar.
Ji tayi ya sake shiga ranta har abin yana bata tsoro.
"Yaya hanya? Yassar na shirin tafiya yace ka shigo gari"
Sai sannan ya maida hankalinsa ga Anti Bintu yana
magana da alamar damuwa a fuskarsa
"Waya muka yi da Ummin Safina sai naji kamar tana
kuka kuma taki fada min abinda ya sameta. Shine kawai
nayi deciding na taho don ko na zauna bazan iya aikin
ba"
_Subhanallah_ ta fada a zuci. Shi kuwa me yasa yake
haka ne. Baya jin komai idan ya fadi magana a gaban
mutane. Kallonta Anti Bintu tayi sai taji kunya. Kada tayi
tunanin ko ta fada masa abinda ya faru ne. In'inar karfi
da yaji ce ta kamata
"Uhmmm...dama...da.....lokacin...kai" ta rasa karyar da
zata yi ma. Shi kuwa ya zuba mata ido kamar bai san da
mutane a wurin ba.
Anti Bintu tayi gyaran murya don ta kula hankalinsa yayi
gaba. Hasashensu ita da Yassar ya tabbata. Wannan kallo
da yake yiwa Asmau indai ba na soyayya bane to bata
san dame zata kwatanta shi ba. A iya saninta dai yasan
komai game da Asmau shiyasa ta fada masa magana ce
surikarta ta fada da batayi mata dadi ba shine dalilin
kukan.
Bata so aka fada masa ba tana tsaye a inda take tun dazu
ta soma hawayen da ta rasa dalilinsu. Karshe ciki ta shige
kawai ta koma daki. Sai da yaga shigewarta yace "ita
Asmau haka take ne da saurin kuka? Na zata a yadda
taga rayuwa by now ta zama jaruma wadda zata iya
daukar duk abinda yazo mata"
Yassar ya bi bayanta zai lallabata ta dawo wurin bakonsu
don maganar komawarsa Kano yanzu kuma tabi iska.
Anti Bintu tace "tun da can Asmau mace ce mai raunin
zuciya. Faruwar wadannan al'amuran sun sa ta kara
samun rauni dole ne sai muna binta a hankali har Allah
Yasa ta iya sakin jikinta kamar da. Dazu munyi mata
nasiha sosai akan toshe kunnuwanta game da irin
wadannan maganganun da zasuyi ta tasowa"
"Allah Ya kara rufa asiri. Kiyi hakuri I just can't help
myself when it comes to Asmau"
Tayi dariya "babu komai, mu hakan muke so ma. Allah
Ya tabbatar mana da alkhairi"
Da yake yasan bazata girmeshi sosai ba sai yayi
murmushi "ko Yayata? Kada kice kin gano ni "
"Na nawa kuma" tayi dariya.
Sai ya rufe fuskarsa da hularsa "amma kuwa har naji
kunya."
Anti Bintu me zatayi banda dariya ta tashi "haka kake da
abin dariya"
Dan dakewa yayi shi a dole babu wasa "don dai kawai a
gaban in-law nake. Amma ni serious mutum ne. Soja ai
baya abin dariya"
"Uhmmm naga alama, sai dai ban rike sunan wannan
sojan ba"
"Call me Ishaq"
"To Ishaq kanina Allah Ya bada sa'a. Bari na turo maka
ita. Ga abinci nan don Allah ka ci"
Daga shi har ita dariya suke yiwa juna sannan yayi mata
godiya ta tafi. Da taje dakin Yassar ta gani yana faman
bawa Asmau dake kuka hakuri tana yi masa fadan me
yasa ya kawo shi gidan.
Ta shiga dakin ta zauna a gefen gado "bana son shirme
Asmau, meye abin kukan ma. Idan mutum ya nuna kina
da mahimmanci a rayuwarsa bai cancanci wulakanci
daga gareki ba. Dan gyara fuskarki kije ku gaisa."
Ta tashi zata shiga bandaki ta wanke fuskar Yassar yace
"Antinmu kema kinyi mubaya'a ne. Naga kin shigo kina
dariya"
Ta kalli Asmau da ta juyo tana kallonsu " ina wasa da kai
ne. Tashi ka bani wuri kazo ka zauna a cikin mata" fita
yayi yana dariya kawai.
Asmau ta wanko fuskarta ta fito "mubaya'ar me Yassar
yake tambayarki?"
Ainau da tun dazu bata saka musu baki ba tace "nima
abinda zan tambaya kenan"
"Ku kyale shi shashancia ne kawai" ta bagarar da zancen
ta fita.
Ainau tace "ko dai baban Amatullah yana ciki ne"
"Kinga ki kiyayeni. Ya isheku daga ke har Yassar"
Tana jiyo dariyar Ainau har ta kai karshen korido din da
zai kaita falon.
A zaune ta same shi yana waya ta zauna a wata kujerar
daga can gefe. Yassar yana daga kusa dashi. Sai da ya
gama yace "Yassar dan bamu wuri ina son siye zuciyar
yayarka"
Ya tashi yana dariyar da ta soma bawa Asmau haushi ita
kuwa ta bata rai. Ya dan mike kafafunsa
"yunwa nake ji"
Fuskarta babu wata fara'ar kirki tace "ba ga abinci nan a
gabanka ba"
"Kince naci ne?"
"Au sai nace?"
Ya gyada kai yana murmushi wanda yasa ta dan saki
fuska.
"To ga abinci nan kaci"
"Nagode" ruwa ya fara sha sannan ya bude plate din da
aka hada masa abincin zai ci.
Asmau ta tashi "bari na baka wuri kaci abincin"
"No yi zamanki please"
Kasa kallonsa tayi yana cin abincin. Shima kadan yaci ya
rufe plate din. Haka yake abinci bai dame shi ba.
"Asmau kalleni nan"
Dan kadan ta iya daga kanta ta dube shi
"Ina so ki zama jaruma mai hakuri da dukkan abinda
zata ji ko ta gani a wurin mutane. Babu wani abu da
bazai wuce ba a duniya saboda haka yawan zubar da
hawaye akan magana ba naki bane. Ke uwa ce dole ki
jajirce wurin zama macen da ba raguwa ba ko don kada
'yarki tayi koyi da hakan"
Yana magana ta soma hawaye har ya kai karshe. Girgiza
kansa kawai yayi
"Don nace ki rinka barin kukanki kiyi a gabana shine zaki
yi kuma. To share hawayen ko na share miki da kaina"
Habar mayafinta tasa ta goge hawayen da sauri
"Ko ke fa...yanzu ace nazo tun daga Kano amma fuskarki
duk a kode"
Ta dan turo baki "don zaka zo sai nayi kwalliya?"
"Sosai ma kuwa, ko ba kya so ki kara samun karbuwa ne.
Yanzu haka zan kama hanya har na koma gida
kodaddiyar fuskar nan zanyi ta gani. Da na sani driver
nasa ya kawoni"
Asmau tace "nifa..."
"Ke fa me? Kinga mu bar wannan zancen sai kin koma
gida. Wai ina princess dina ne banganta ba"
"Sai yanzu ka tuna da ita? Tayi bacci"
Ya kwantar da kansa a saman kujera "duk laifinki ne. Kin
wani kasheni da ido kinsa bana tunanin komai sai naki.
Kije ki tasheta magriba ta kusa kada ki koya mata baccin
yamman nan"
Asmau ta tashi tana tafiya tana waigensa. Duk juyawa sai
yayi mata murmushi sai ta kawai da kai. A na ukun ta
kusa karo da bango ya soma dariya "yi a hankali ba
yanzu zan tafi ba sai kin koreni da kanki"
A kunyace ta shige tana mamakin yadda ya gama da
zuciyarta cikin dan kankanin lokaci.
******
Bayan tahowarsu Mama Yalwa taje gidan Umma. Suna
zaune harda Hajjo take fada musu yadda suka yi da
Qasim a daren jiya kafin ya tafi da kuma amsar da
Asmau ta bashi.
Hajjo tace "ki ji min yarinyar nan fa. Ita banda abinta ai
ba saka mata ido zamuyi ba. Kuma yaron nan Qasimu ya
cancanci yabo wallahi. Bari ta dawo muyi magana amma
aure ai shine rufin asirinta."
Umma tace "nima na yaba da halayensa sosai. Nasan
duk abubuwan da take tunani har yasa take tsoron yin
aure. Amma ko kadan ba hujja bace. In sha Allah zamuyi
mata magana. Ni kaina ban hango mata rufin asiri ba
kamar a gidan Qasim. Allah Yayi masa albarka".
"Amin" Mama ta amsa. "Kar kiso kiga yadda naji dadin
labarim nan. Yarinya ce mai biyayya nasan bazata watsa
mana kasa a ido ba.
*****
Da yamma ne bayan tafiyar Mama Anti Bintu ta kira
Umma tana bata labarin zuwan Col. Ishaq da hirar da
suka yi. Cike da murna tace "Yaya Bara wallahi na yaba
da yadda ya damu da Asmau. In Allah Yaso shine zai
share mata hawayen dukkan damuwarta."
Umma bata iya bata amsar kirki ba saboda tunani da ta
shiga yi akan maneman 'yarta.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽36
Batul Mamman💖
Ba karamin damunsa rashin daukar wayarsa da Asmau
take yi yayi ba. Sai dai kuma ya kuduri niyyar bazai barta
ba. Murmushi yayi....yana son mace mai jan aji, amma
bazai bari ta ja masa aji da yawa ba saboda yadda yake ji
da ita a zuciyarsa. Har mamakin kansa yake yi. Bai yarda
sonta yake yi har haka ba sai bayan 'yar hirarsu ta dazu.
Yana son muryarta, kunyarta, yanayinta....ya dan shafa
kansa yana murmushi ya tura mata da text
"Asmau Ummin Safina ki shirya, don Jikamshi da gaske
yake. Kiran wayarki kuma yanzu na fara. Gudnyt"
*****
Hannunta har rawa ya soma bayan ta karanta text din.
Wani abu taji ya ratsa jikinta gabadaya don dadi. Bayan
Abubakar bata taba tunanin sake jin wani abu
makamancin wannan akan kowane da namiji ba sai akan
Col I.M Jikamshi. Sai dai kuma wutsiyar rakumi tayi nesa
da kasa. Yaudarar kai ne ma ta yarda wani abu yayi nisa
tsakaninsu. Tafi kowa sanin ko ita wacece, bata cikin
mata da zasu sami rabon aure a wannan duniyar. Dadin
dadawa Jikamshi ba karamin mutum bane. Yana da wata
kima ta daban a idonta, sam bazata so suyi rabuwa mara
dadi ba. Gara tun ba'a soma ba kada a fara. Tana
wannan tunanin ne bacci ya kwasheta.
Washegari Umma ke fada mata su fara shiri nan da
kwana biyu zasu tafi Zaria da Aina'u. Sati daya zasu yi
daga nan zata zo ta same su su wuce Wushishi. Jin zata je
Zaria wurin Anti Bintu yasa ta farinciki har ta dan manta
da tunanin da ta kwana ta tashi dashi.
Shirye shirye suke yi daga ita har Aina'u sun hada
kayansu da komai. Yassar ne zai kaisu ya dawo
washegari.
Da yamma ne ta tafi gidan Jafar saboda yace yana son
ganinta tace ya bari zata zo da kanta. A gida ta bar
Amatullah tana bacci. Sun dan taba hira da Sabira ta
tashi ta basu wuri. Ba wani dogon abu bane maganar
karatu yayi mata wanda yace sunyi shawara ne da
Shemau zasu hada kudi su biya mata ta koma
makaranta. Kuka take yi sosai kamar yasan abinda take
son yi kenan.
"Yaya Jafar Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai, nima
abinda yake raina kenan don bana son nayi ta zaman
haka."
"Kada ki damu Asmau. Ina so ki manta da rayuwar baya
kiyi kokarin gina rayuwa mai kyau daga yanzu. Kada ki
manta ko ke wacece a duk inda kike. A yanzu da kika
dawo gida inda mutane suka sanki suka san labarin
rayuwarki ki zauna da shiri na fuskantar kalubale kala
kala. Dole duk inda kika shiga kiji maganganu marasa
dadi daga bakin mutane daban daban. Abinda nake
bukata daga gareki bai wuce ki toshe kunnuwanki ba.
Komai yayi farko yana da karshe. Ki mayarda dukkan
lamarinki ga Allah sai kiga kinyi nasara."
Tayi murmushin takaici "hakane, kuma nagode da
shawararka. Dole ne nayi hakuri da dukkan abinda
mutane zasu ce game dani da Amatullah. Irin labarinmu
dai da wuya yake zama tarihi. Duk wanda ya sanmu duk
sanda muka hadu sai sun tuna. Wannan kaddara har
jikoki idan da rabo nasan za'a goranta musu wata rana"
ta kare maganar da kuka.
Tausayin kanwarsa yaji sosai. Ya dade da sanin cewa illar
zina tana bibiyar mutum duk inda yaje. Musamman idan
akwai haihuwa tsakani. Fatanmu kawai Allah Ya tsare
mana imaninmu Ya karemu daga fadawa sharrin
shaidan da mukarrabansa.
"Ki tsarkake zuciyarki Asmau, daga nan ki barwa Allah
komai. Rayuwa ce kowa da irin tasa. Babban abin
dubawa dama shine tuba da komawa ga Allah. Idan kika
yi haka to babu ruwanki da zancen mutane. Duk wanda
ya fiye bibiyar kuskuren dan uwansa don tonon asiri to
Allah na kallonsa kuma Shine Yasan yadda zaiyi da
bayinSa."
Godiya ta sake yi masa har ta kira Shemau tace zata je
har gida tayi mata godiya. Dan uwa rabin jiki inji
bahaushe...banga mai kamarka ba. Abinda suka aikata ita
da Abubakar ba su kadai yake bi ba domin kuwa tasan
za'a nuna iyayensu da 'yan uwansu idan dalili ya kawo
suma a goranta musu. Kai zina laifi ce mai muni, kazanta
ce mai kaskantar da mai daraja. Ya Allah Kasa mufi
karfin zukatanmu. Masu neman aure maza da mata Allah
Ka basu abokan rayuwa nagari. Mu kuma Ka bamu
zaman lafiya da wadanda Ka hadamu dasu.
*****
ASP Qasim zaune gaban mahaifiyarsa ya gabatar mata
da zancen Asmau wanda ta dade da sanin kudurinsa
akai.
"Baba ni bazan hanaka aurenta ba. Babanku ma yace ya
amince da auren. Abu daya nake so da kai shine ka tuna
dukkan abubuwan da suka faru. Naso kwarai kayi aure
kafin yanzu ta yadda ko ka auri Asmaun zaka hadata da
wata matar"
"Inna kenan, kina gudun ita kadai ta kasance surika a
gareki saboda tana da 'ya kafin tayi aure?"
"Dan nan yau da gobe sai Allah. Mutane da bakinsu
bazasu fasa surutu ba"
"Amma Inna nasha fada miki ina gudun zamansu da
kishiya yaki dadi saboda gori. Da bata dawo ba kamar
yadda kika bukata a shekarar nan zan nemi aure. Ku
cigaba da yi mana addua."
Ta kada kai "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi. Haj
Yalwa tace zata zo dasu su gaishe da Malam. Allah Ya
kiyaye hanya"
Qasim ya tashi ya leka dakin mahaifinsa har lokacin
bacci yake yi. Shiryawa yayi cikin wani yadi mara nauyi
ruwan toka yayi kyau sosai ya kama hanyar Kano daga
Shanono.
Ana magariba ya iso. Gidan Mama ya fara zuwa suka
gaisa sannan ya kira Asmau ya fada mata zai zo idan an
idar da sallar isha. Umma taje ta sanarwa.
"Allah Sarki Qasim, gaskiya ya rike amana. Ji yadda yake
kokarin kula daku duk da ba a garin nan yake aiki ba.
Allah Ya biya shi da mafificin alkhairi."
Asmau ta amsa da amin tana gyara goyon Husna da tayi.
Suna cikin hira Qasim yayi sallama Umma tayi masa izini
ya shigo. Cike da ladabi ya gaisheta ta amsa fuska a sake.
Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma dakin Hajjo. A nan
ta sanar da Amatullah zuwan Qasim daya baban nata ta
fito gaishe shi.
Qasim ya ajiye kofin lemon dake hannunsa yana maida
hankalinsa Asmau.
"Asmau magana nazo muyi, ina fata zaki saurare kuma ki
fahimceni."
"Ina jinka Yaya Qasim"
"Asmau kinsan irin shakuwa da abotar dake tsakanina da
marigayi Abubakar"
Ta gyada kai tana tuno masoyin da bazata taba mantawa
ba a tarihin rayuwarta.
"Duk abinda ya gudana a rayuwarku na sani na kuma
san nima akwai sa hannuna a ciki. Bazan gaji da rokon
gafararki ba saboda ance karfe daya baya amo. Kamar
yadda kawa ta ribaceki haka nima nayiwa Abubakar, ga
kuma sakamakon hakan duniya ta gani. Asmau tun kafin
ki dawo na yanke shawarar aurenki ko a wane yanayi na
sameki. Cikin ikon Allah yanzu na tsinci kaina da tsananin
kaunarki"
A razane ta dago kai ta kalleshi ta mayar da kanta kasa.
Yayi sassanyar dariya
"Nasan dole kiyi mamaki sai dai kuma ki sani burina ba
wai na maye gurbin Abubakar bane. Ina so ki bani dama
a matsayin masoyi na sami kaunarki na kuma zama uba
ga 'yata Amatullah."
Wannan shine ana wata ga wata. Ita fa ko kadan bata son
maganar aure ma yanzu. Qasim wani babban jigo ne a
rayuwarta saboda yadda ya damu da lamarinta da na
Amatullah. Ya rike amanar Abubakar ba da wasa ba.
"Yaya Qasim bani da abinda zance maka sai godiya da
fatan alkhairi amma don Allah ka janye maganar aure a
tsakaninmu. Maganar aure ba ta mace irina bace. Duk
yadda zan so bani da wani mutumci da kima da zan kai
gidan aure. Amatullah ko naki ko naso 'yarka ce amma
don Allah mu bar maganar aure."
Dama yasan da wuya ta amince kai tsaye.
"Ba cewa nayi ki bani amsa yanzun nan ba. Zan baki
lokaci kiyi tunani. Amma ki sani kamar yadda aure yake
zama garkuwa ga kowace mace kema shine mutumcinki.
Zamanki a haka shine zai janyo miki duk abinda kike
gudu wato surutun mutane."
"Ni dai....."
Hannu ya daga mata alamun tayi shiru ya tashi tsaye
"kiyi tunani nace kuma kiyi shawara da duk wanda kika
san zai baki shawara tagari"
Rasa abin fada tayi kawai ta sanar dashi batun tafiyarsu a
washegari yayi mata addua sannan yace zai zo idan ta
dawo yasan lokacin tayi duk wani tunani da zata yi.
Bayan tafiyarsa Asmau ta shiga tashin hankali. Ko zata yi
aure ba dai da Qasim ba. Idan ta amince tamkar taci
amanar Abubakar ne. Kana ganinta kasan tana cikin
damuwa ta tafi daki da niyar kwanciya wayarta ta soma
kara.
Sai da gabanta ya fadi da taga sunan mai kiran. Kwana
biyu tun ranar da taki amsa wayarsa bai kara kiranta ba
sai yau. Zuciyarta ce ta rinka bugu da sauri da sauri
amma ta kasa amsa kiran. Text taga ya turo mata
_Idan Safina batayi bacci ba ki hadani da ita. Taki muryar
ma ina son ji amma ba a waya ba, so wayar ba taki
bace._
Wani dan murmushi ne ya subuce mata. Sai kuma ta
dan dake tana yiwa zuciyarta tuni da cewar ta manta da
maganar aure. Babu wani namiji da zai aureta a yanayin
da take ciki komai tsahon lokaci ace wata rana bai
goranta mata irin rayuwar da tayi a baya ba.
Dakin Umma taje ta bawa Amatullah dake aikin wasa da
Husna wayar da ya sake kira. Kusan minti ashirin tana ta
yi masa hira sannan mikawa Asmau. Da ta karba sakawa
tayi a kunnenta tayi shiru tana so taji ko ya ajiye.
Yanayin yadda take saukar da numfashi ne ya tabbatar
masa ta karbi wayar. Murmushi yayi kamar tana kallonsa
yace
"Ana so ana kaiwa kasuwa"
Da sauri Asmau ta kashe wayar tana dariya. Me ya kaita
saka wayar a

Please Login or Register in order to submit comment