Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take Ya
yafe musu kuskuren da suka aikata wanda har yau yake
bibiyar komai na rayuwarsu. Daga nan tayi adduar fatan
samun nutsuwa da dukkan wanda Allah Ya kaddara zata
aura. Tana sallar Anti Bintu ta shigo da niyyar sake bata
baki ta tarar tana sallah. Gefen gado ta samu ta zauna
tana jiran ta idar. Tunanin wannan al'amari ne ya rinka
damunta. Idan akace *abinda ake gudu*to ba faruwar
laifin ake ji ba. Abubuwan da zasu iya biyo bayansa.
Asmau ta dade tana ganin tasirin hakan a rayuwarta tun
ranar da Abubakar ya rasu. Miji ya rasu ranar daurin
aure sannan a sami amarya da ciki. Ai ko a iya nan aka
barta ta kafa tarihi a rayuwa wanda duk mutumin da ya
santa idan suka hadu sai ya tuna. Ga 'ya ta haifa itama
nan gaba tana kara wayo zata iya bukatar jin waye
ainihin babanta. Idan kuma marasa tausayi cikin mutane
suka goranta mata yanayin haihuwarta ko na sakan daya
ne sai ta tsani mahaifiyar da ta sha wahalar rayuwa don
ta haifeta. Babu dan da yake son jin shi shege ne. Sannan
ga soyayyar wani Allah Ya dora mata amma saboda
abinda ya faru a baya idan tace zata bijire ma kallon
mara kunya kuma mara godiyar Allah za'ayi mata. Allah
Sarki Asmau da matan da suka sami kawunansu a yanayi
shigen nata. Tuba da tawakkali shine kawai kwanciyar
hankali garesu.
Anti Bintu tana ta tunani har bacci ya kwasheta a zaune
Asmau bata idar da sallah ba. Itama sai gabanin asuba ta
soma baccin. Ana kiran assalatu ta tashi dama baiyi nisa
ba. Ta shi Anti Bintu da 'yan matan da suka shigo dakin
kwanciya tun tana sallah. Sai wurin bakwai na safe bacci
mai nauyi ya dauketa.
*****
A kitchen Umma ta rabawa kowa aikinsa na taron gobe.
Gidan Mama zasuyi meatpie da doughnut. Nan kuma
cake zasuyi da pepper chicken sai lemuka da za'a siyo.
Har dakin Yassar taje ta bashi kudin abubuwan da zai
siyo a fara aikin yace mata da zazzabi ya kwana. Yassar
da bashi da kyuyar aike yau kirikiri ya nuna mata bazashi
ba. Dama tun jiya ta kula yana wani cin magani ta rasa
dalili. Bata san Col. Ishaq yake tayawa kishi ba tun kafin
ya fara nasa. Dayake Shemau zata zo sai kawai ta kirata a
waya ta fada mata abubuwan da zata taho dasu.
Ta fito tana mitar tasan Yassar kalau yake Anti Bintu tayi
dariya.
"Indai Yassar ne ranar daurin auren ma yana iya kirkiro
ciwo. Don baki san irin shakuwarsu da Ishaq bane."
"Ke kuma naga alama abin yayi miki dadi. Ni duk a
yaushe ya tara masoya a gidan nan ne ban sani ba?"
"duk abinsa ai dole yaji kunyarki. Don baki ga yadda
mukayi dashi a Zaria ba. Hatta babansu Dijah sun sha
hira sosai. Tamkar 'yan uwansa haka ya dauke mu. Gashi
yanzu kun zo kun raba"
Umma ta rike haba tana kallon kanwarta. Da gaske Bintu
ta zama 'yar kamfen "kun mayar dani wata boss dai.
Gani kuke yi kamar bana son Asmau. Bari ayi auren ku
gani idan suka fara zaman lafiya. Yau fa ko gaisheni bata
fito tayi ba."
Anti Bintu tace "bacci take yi, jiya kwana tayi tana sallah
da kuka"
Hajjo dake tsaye a bakin kofa tana musu dariya tace "ta
kwana sallah kika ce, to ni dai babu ruwana Bara'atu da
Garzali ne suka yanke shawarar. Allah Yasa dai bata
ambaci sunana a adduar ba. Ko dai na tasheta na
tambayeta ne. Kunsan addua ba abin wasa bace"
Duk su biyun dariya suka yi. Daga falo suka ji shigowar
Zubaida da Sabira. Har kitchen din suka zo aka gaisa
suna yiwa Zubaiba fadan dalilin zuwanta tace "Umma
jiya banyi bacci ba tunda ya fada min gobe za'a kawo
kudin Asmau. Mu dan shiga ciki akwai wani sirri da nake
tsammanin bata fada miki ba"
Anti Bintu tace "fadi a nan kawai, ba zancen Ishaq bane"
Zubaida tace "wannan sojan ko. Ashe kun sani, to
meyasa za'a hadata da Qasim?"
Hajjo tace "kinga matar auta, jeki ki bawa 'yar uwarki
baki kawai. Maganar nan an gamata tun jiya. Allah Ya
sanya mana alkhairi"
Jikin Zubaida duk sai yayi sanyi. Mata nawa ta gani a
gidan Uwargida wadanda suka ce auren dole ne ya fito
dasu daga gidan iyayensu. Allah Yasa Asmau ta iya hakuri
dai.
Ko sau daya Asmau bata fito daga daki ba. Abinci ma
Dijah ce ta kai mata. Amatullah da bata iya komai idan
Umminta bata walwala itama a dakin ta zauna. Har su
Shemau suka zo yara sun cika gidan amma taki fita sai
nanikar jikin Asmau take yi. Col. Ishaq yayi ta kiranta ta
daure ta dauka tace masa baki ne a gidan yau duk ya
cika. Har su Anti Bintu sun zo.
"To bazan takuraki ba kije kuyi hira zuwa dare sai muyi
magana. Ki gaishe min da Yayata Bintu"
Tana ajiye wayar sai kuka. Yanzu da tasan za'ayi mata
katanga dashi tafi jin sonsa ma a zuciyarta. Duk bayan
dan lokaci kadan sai tayi mata text mai cike da kalamai
masu ratsa zuciya. Shemau tazo tayi ta rarrashinta akan
ta hakura ta karbi wanda Allah Ya zaba mata. Gudun
kada su dameta yasa ta dan sake tana amsa musu idan
an sakota a hira.
Sunyi aikinsu sun gama zuwa yamma. Washegari kawai
ake jira mutanen Shanono su iso. A daren ranar Ainau
da bata sami zuwa tayasu aiki ba ta kirata harda kukanta.
Ta kira Umma tana rokon kada a hana yayarta wanda
take so. Umma dai ta rasa yadda zata yi. Duk sun hade
mata kai. Jafar ne ma bai nuna ga wanda ransa tafi so da
Asmau ba.
Uban gayya ASP Qasim shima sai dare ya kira Asmau.
Kana jinsa kasan yana cikin farinciki yace
"Asmau kinga ikon Allah ko. Ina sanar da su Baba
maganarmu suka ce kawai azo ayi komai. Ina fatan
hakan zai karan kwantar miki da hankali kisan cewa
komai ya wuce."
Zuciyarta har wani zafi take yi don bacin rai ta daure
tace "babu komai Yaya Qasim, Allah Ya tabbatar mana
da alkhairi"
Yaji dadin furucinta "Amin Asmau, goben zanzo nima.
Idan sum gama nasu sai mu fara tsara bikin. Sai da safe
ko gimbiyata"
Ta kakalo murmushi tayi "to sai da safe" ta ajiye wayar
ido na cikowa da kwalla.
*****
Washegari da wuri gidan ya cika kamar masu shirin biki.
Yaya Abu da Anti Lami sun zo, Mama da 'ya'yanta mata
harda matar Abdulhalim. Sai Aina'u da Shemau da
Sabira. Falon aka share aka tura kujerun baya aka
shinfida wani kafet din ko da wurin zaman zaiyi kadan. A
bangaren maza ma akwai masu zuwa ta bangaren Hajjo
da maigidanta sai Kawu Garzali da abokansa biyu. Ga
mazansu Anti Lami da na Anti Bintu. Banda kuma gayyar
Alh Adamu. So suke su nunawa dangin Qasim suna son
'yarsu kuma ita din 'yar dangi ce.
Tun safe Asmau ta kashe wayarta don bata san me zata
cewa Jikamshi ba idan ya kirata. Adduarta kada yazo ana
tsakar taron. Yau ma a daki ta zauna sai dai 'yan uwanta
su shigo tayata hira.
*****
Ana la'asar mutanen Shanono suka iso gidan Alh Adamu.
Daga nan suka dunguma zuwa gidansu Asmau. Mota
biyu suka ciko da nasu 'yan uwan. Qasim dama ya rigasu
zuwa ya sai zauna a cikin gidan idan taro ya watse zaije
ganin Asmau gimbiyarsa.
Kafin su iso Umma tace Asmau ta tafi gidan Jafar tare da
wasu cikin 'yan matan tace kanta na ciwo bazata iya fita
ba. Umma tayi murmushi kawai ta rabu da ita.
Sauran suka tashi aka jera komai a falon sannan suka
koma ciki suna hira a dakin Hajjo saboda yafi fadi.
Asmau na kwance zazzabin dole ya rufeta taji hannuwan
Amatullah sun rike mata wuya ta baya. Tun jiya taki
sakewa itama. Idan ta korata tayi wasa bata dadewa take
dawowa wurin Umminta. Murmushi tayi tana kokarin
cire hannunwan don rikon ya danyi karfi
"Ama sake min wuya mana"
Jin tayi shiru yasa ta juyawa sosai. Amatullah ta gani tana
kokarin numfashi bakinta a bude.
"Subhanallah" ta fada a rude tana dagata.
"Ama ki rufa min asiri, wayyo Allah"
Gabadaya ta manta da inhaler din da aka basu a asibiti ta
dauketa sai dakin Hajjo. Kuka take yi sosai tun kafin ta
shiga su Umma suka fara fitowa saboda muryarta da
suke ji.
Ganin Amatullah na numfashi da kyar Shemau ta
karbeta Sabira kuma ta kira Jafar a waya. Lokacin Umma
har ta dauko mukullin tata motar. Yassar baya gidan shi
tun safe ya fice.
Sabira na fadawa Jafar ya tashi da sauri. Lokacin an
gama gaisawa da dangin Qasim kenan. Abdulhalim ya
tambayeshi abinda ya faru ya fada musu.
Kowa sai salati suka tashi don ta nan su Umma zasu
wuce.
Kafin kace meye wannan suna mota Asmau ta cire
dankwali sai hijabinta kawai tana yiwa Amatullah fifita. A
can gidansu kuma Alh Adamu ya gama gigicewa. Yana
matukar son jikarsa shiyasa hankalinsa ya tashi. Karshe
yace don Allah suyi hakuri zai bisu asibitin. Idan komai
ya lafa sai su karasa abinda ya tara su. Duk da wasu basu
ji dadi ba to amma lafiya tafi komai. Haka suma aka
samu wasu cikinsu suka bi bayansu aka tafi asibiti.
Ainau ce ta kira Yassar ta fada masa. Kafin ya karasa
asibitin ya kira Col. Ishaq ya sanar dashi da kuma sunan
asibitin. Shima hankalinsa a tashe ya tafi. Dama yayi ta
kiran wayar Asmau yau baya samu. Niyarsa bayan
magariba yaje gidan.
*****
Emergency suka kaita nan da nan likitoci suka fara
aikinsu. Sun tabbatar musu ba abin damuwa bane
asthma dinta ce ta tashi amma abin baiyi tsanani ba.
Ana ta rarrashin Asmau ta kasa shiru. Dama can
hankalinta ba a kwance yake ba. Suna nan aka canza
mata daki lokacin numfashin ta daidaita ta sami bacci.
Qasim ya shigo dakin aka gaisa ya duba Amatullah ya
fita. Bai dade da fita ba Jafar yace taje waje Qasim na
kiranta.
Bata son nunawa mutane rashin son auren shiyasa ta fita
ta same shi. Kokarin kwantar mata da hankali yayi tace
ta gode. Suna nan tsaye Col. Ishaq ya iso. Tunda idonsa
ya gano masa Asmau da Qasim yaji wani bacin rai sai dai
jikin Amatullah ne a gabansa. Daya karaso suka gaisa da
Qasim. Itama ta gaisheshi sai ya shareta kawai. Tana
kallo Yassar ya fito ya kaishi dakin ya duba Amatullah.
Kasa nutsuwa yayi ya fito ya dawo inda suke. Gaban
Asmau sai faduwa yake yi. Yana zuwa yace
"Naga dakin a ciki da mutane da yawa. Tun yaushe ta
fara ciwon ban sani ba?"
Qasim ne ya bashi amsa "ko awa daya ba'ayi ba.
Mutanen ciki 'yan uwana ne dana Asmau. Kayi hakuri
naso sanar da kai ma abin ne yazo a kurarren lokaci."
Idon Col. Ishaq akan Asmau yace "wane abu kenan?"
Da dan murmushi Qasim yace "kawo kudi aka zo sai
ciwon Amatullah ya tashi"
Guntuwar fara'ar fuskar Col. Ishaq tuni ta bace "kudin
aure??? Na wa?"
Kirjin Asmau sai bugu yake da karfi don tsoro. Gashi yq
tsareta da ido.
Qasim yace "kin barni ina ta magana ni kadai ko, wallahi
daga fadawa iyayena kawai sai suka yanke shawarar gara
ayi komai lokaci guda. kudin *aurenmu* aka zo
kawowa."
Sabanin bacin ran da tayi tunanin gani a fuskar Jikamshi
sai taga yayi dan murmushi
"Kasan mata da kawaici da kunya. Musamman ma dai
_Matar Jikamshi_. Asma'una baki fada masa muna
soyayya bane?"
Qasim ne yaji kamar an sauke masa guduma a kansa. Sai
ya kalli Asmau da tayi mutuwar tsaye sannan ya kalli Col.
Ishaq wanda yake binta da kallo mai nuni da tsantsar
soyayya kamar ya sanyata a jikinsa.
Daga bayansu Yassar ne yazo kiran Asmau ya fada mata
Amatullah ta farka. Jin abinda Col. Ishaq ya fada yasa shi
daka tsalle ba shiri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽43
Batul Mamman💖
Shiru suka yi gaba dayansu sai Col. Ishaq da yake
murmushi kamar bai san abinda yayi ba. Shi kuwa
Qasim nema yake maganar da yaji ta gama shiga
kwakwalwarsa. Ihun tsallen Yassar ne yasa duk suka kallo
inda yake. Baiyi wani dogon tunani ba don kada a gano
shi ya durkusa kasa tare da rike kafarsa ta hagu
"Wayyo Allah wani abu ne ya cije ni"
Asmau tayi kansa da sauri dama neman hanyar da zata
bar wurin take yi don ji take kamar idan ta kara minti
daya itama sai dai a bata gado kusa da Amatullah saboda
irin bugun da zuciyarta take yi.
"Mu gani a ina ne?"
Ya dago kansa yana kallonta, duk sai ta bashi tausayi.
Karyar kafar ma saboda ita yayi
"Barshi kawai bari na cire takalmin. Kije Amatullah ta
tashi tana kuka"
Kamar an harba walkiya haka ta bar wurin ko waigowa
baya bata yi ba. Qasim da Col Ishaq suka dawo kusa
dashi suna tambayarsa abinda ya sami kafar.
"Ji nayi kamar abu ya cije ni. Ku shiga ciki Amatullah ta
tashi."
Qasim ya dawo hayyacinsa daga abinda Col. Ishaq ya
fada har ya yiwa Yassar sannu harda kokarin cire masa
takalmin zai taya shi duba kafar. Yassar yayi saurin jan
kafar yana mai jin kunyar karyar da yayi "ya dena ciwon,
zan karasa motar Umma ina da silifas a ciki ina jin
cinnaka ne ya shiga."
Daga haka ya samu Qasim ya shige. Kafin ya mike tsaye
yaji an kama wuyan rigarsa an tayar dashi. Ba don yasan
wanda ya rike shi ba sai yayi ihun gaske. Col. Ishaq yayi
'yar dariya yana kallonsa "ka kyauta da ka taimakawa
yayarka don sauran kadan ta suma a wurin nan. Har na
fara tunanin me zan fadawa su Umma"
Shima Yassar dariyar yayi yana murza wuyansa "haka
kawai kun sata a tsakiya. Ga soja ga dan sanda da wanne
zata ji"
"Laifinta ne da tasa duk muka kamu da sonta. Allah Yasa
kada ta kwaso mana lauya ko alkali kuma."
Murmushi Yassar yayi tare da jin kunyar amsar da aka
bashi. Shi dai komai na Col. Ishaq yana burge shi. Ina ma
ace shi zai aureta. Ba kuma don baya son Qasim ba sai
dai wannan maganar aure ce.
*****
Asmau na shiga dakin Amatullah ta dena kuka. Kan
gadon taje ta zauna tana yi mata fadan dalilin kukan don
bata ganta ba kamar bata san sauran mutanen wurin ba.
Mama tace "kiyi mata a hankali Asmau. Yarinyar nan taji
jiki. Haka muka sha fama da Abubakar da yana yaro.
Idan ta kara wayo zata san yadda zatayi ta rinka
kiyayewa sai kiga attacks din basa zuwa sosai."
'Yan uwan Qasim suka ce zasu tafi sai dai su dawo wani
satin. Alh Adamu yayi ta basu hakuri yace tunda
Amatullah taji sauki suna iya komawa a karasa. Hakan ya
razana Asmau sosai ta shiga rarraba idanu taji me
Jikamshi zai ce. Sai tayi sa'a yayi kamar baya jinsu. Su din
ma sun nuna babu damuwa tunda yamma tayi zasu sake
saka rana.
Ita dai Asmau ko kallon Qasim din ta kasa. To da wane
idon zata kalle shi bayan abinda Jikamshi ya fada masa.
Shi a rayuwarsa ta kula baya jin shakkar fadin magana
ko a gaban waye indai yana tunanin akan gaskiyarsa ne.
Gashi yau ya fadi maganar da tasan dole Qasim ya
kullaceta a ransa.
Shima a nasa bangaren gani yayi gara ya kyaleta saboda
asibiti ba muhallin maganar bane. Sannan ga Amatullah
babu lafiya yanzu ko me zata fada masa zai zamto babu
nutsuwa a tare da ita. Tare da su Alh Adamu suka fita
raka 'yan uwansa zasu biya gidan Umma su dauko
sauran. Kayan ciye ciye da aka tanadar musu Umma tasa
Sabira da Shemau su bi bayansu sai su hada a basu su
tafi dashi.
*****
Suna zaune har akayi magariba sannan su Umma suka
tafi aka bar Hajjo da Asmau. Kayan kwana za'a hadu
musu sai Mama ta dawo su kwana tare. Col. Ishaq yana
dakin amma shima yaki kallon inda Asmau take, shima
bata da abin fada masa. Ba don ciwon Amatullah ba da
yanzu an gama magana tsakaninta da Qasim sai batun
saka rana. Biyewa Amatullah yayi tana ta shagwaba son
ranta, sai Hajjo dake dan yi masa hira itan ma kunyarsa
take ji tunda tasan komai. Duk yadda Asmau taso su
hada ido yaki. So take ta bashi hakuri tunda tasan yanzu
bata da sauran mafita. Karshenta kafin sati ya zagayo ma
mutanen Shanono su sake dawowa.
Shigowar Jafar da Qasim yasa shi tashi yayi musu
sallama ya fita.
Damarta kenan ta bashi hakuri a yau tunda wayarta tana
gida. Bai dade da fita ba tace zata je tambayar likita ko
zata iya bawa Amatullah abinci. Jafar yace ta bari yaje ta
wayance "barshi Yaya Jafar so nake na dan fita na gaji da
zaman wuri daya"
Shi kuwa Qasim tuni ya gane inda take son zuwa sai
kawai ya dauke kansa. Yana kallo ta fita cikin sauri don
kada ya bar asibitin kafin ta karasa wajen.
Tana fitowa ko alamunsa babu ta kara sauri harda dan
gudunta. Tsoronta bai wuce kila daga yau yaki dawowa
ba. Garin sauri tabi wata hanyar da zata kaita wurin ajiye
motoci ta kusa karo da mutum har sai da taji tsoro
saboda rashin wadatar haske a wurin. Tsaye yake ya
sanya hannuwansa a aljihun wando yana kallonta. Kallo
ne na tuhuma wanda har ranta sai da taji babu dadi don
bata kyauta masa ba. Bai motsa daga inda yake ba yace
"me yasa kika wahalar da kanki da yin gudu bayan
kinsan dole zan jira fitowarki. You have alot of explaining
to do"
Fuskarsa yau babu fara'ar nan da take kara saka mata
sonsa. Yau a sojansa ya fito sai ta daburce ta rasa ta ina
zata fara bayani.
"Kinyi shiru, na tafi ne?"
"A'a don Allah kayi hakuri" sai ta soma kuka.
"Matar Jikamshi" sai yanzu ta danji sanyi a ranta saboda
yadda ya kirata. A hankali ta dago ido ta kalle shi.
"Why?" Ya tambaya shima duk dakewarsa yana jin babu
dadi. Idan ya rasa Asmau gani yake bazai taba samun
madadinta ba. Yana mamakin irin wannan so da yake
mata wanda ya shige shi lokaci daya.
Idanunta cike da hawaye ta soma fada masa yadda abin
ya faru." Kayi hakuri da ban sanar da kai ba. Babu yadda
zanyi ne tunda duk iyaye sun amince"
Ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar ta "ki dena kukan
nan kinji ko. Idan nace miki everything is ok nayi karya
because it is not. Kinji kunyar sanar da Qasim da wuri
kinga abinda hakan ya janyo. Magana kuma tunda ta
hada da iyaye zan hakura kamar yadda kike so. Dazu ma
naga ya kamata ya sani ne shiyasa na fada masa."
Wani kukan ne yazo mata sai zubar da hawaye take. Tana
sonsa fiye da yadda take tsammani a baya.
"Jikamshi to yaya zanyi?"
Tausayi ta bashi. Asmau ta fuskanci abubuwa da dama a
cikin 'yan shekaru.
"Da ace babu ni a cikin manemanki sai na baki shawara.
Amma tunda ina ciki bana so a zargeni da son kai.
Shawara tana gareki Asma'una. Idan Allah Yayi Qasim ne
mijinki alfarma daya nake nema kada ku rabani da
Safina. Atleast ko school fees dinta ku bari ya zama
responsibility dina."
Meyasa Qasim bai sanar da ita iyayensa zasu zo da wuri
ba. Ji tayi gabadaya auren ya fice mata a rai. Kuka kawai
take yi mai ciwo. Muryarta a shake tace "To yanzu
shikenan?"
Murmushi yayi mata, sai da taji shi har ranta. "Shikenan
Matar Jikamshi. Maybe daga yau bazan kara kiranki da
wannan sunan ba. Ki rike duk abinda Allah Ya kaddara
miki da hannu biyu. Qasim mutumin kirki ne a yadda na
fahimce shi. Ban taba ganin mutum mai kokarin rike
amana kamarsa ba"
"Na sani wallahi, shiyasa na kasa fada masa gaskiyar
abinda ke zuciyata. Ina gudun bata masa rai saboda
nasan duk abinda yake yi don ya kyautata mana ne."
"Kada kiyi ja in ja da iyaye akansa. Idan shine alkhairin
rayuwarki bamu da zabi da ya wuce karbar kaddara."
Juya mata baya yayi zai tafi. Yana jin sautin kukanta ya
karu. Yasan yana sonta ba da wasa ba, amma duk abinda
aka ce iyaye sun shiga ciki a matsayinsa na babba bai
kamata ya nuna mata bijerewa alkhairi bane. Duk da
kuwa yana ji a ransa kamar gobe ya turo nasa iyayen.
Asmau ta wuce a kirata wani bangare na jikinsa. Shine
ita, itace shi. Da haka kawai zai iya kwatanta kaunar da
yake mata.
A sanyaye yaji muryarta yadda bata zaton zai ji tace
"Jikamshi ina sonka" a hankali
Wannan kalmar ta tsaya masa sosai a zuciya har ya fasa
tafiya. Sake juyowa yayi ya ganta durkushe tana kuka.
Shima durkusawa yayi a gabanta suna fuskantar juna
"Matar Jikamshi kina so na hakura dake"?
Girgiza kai tayi tana fitar da hawaye mai dumi.
"To bazan hakura ba. Jikamshi yana son matarsa. Ki tashi
ki koma ciki. Gobe in sha Allah zanyi magana ta fahimta
da Hajjo tunda ita ce babba. Zan fada mata bazaki iya
rayuwa da kowa ba sai Ishaq. Nima da ke kadai nake son
karashe rayuwata. Duk shawarar da ta bayar da ita zanyi
amfani."
Tana hawayen amma murmushi take yi tana kallonsa.
Yayi dariya "to dena kallona haka kada ki cinyeni kafin a
daura auren"
Ta sunkuyar da kanta kasa cikin kunya. "Ba fa kallonka
nake yi ba."
"Kallo na nawa kuma, a ciki ma ko kunyar Hajjo baki ji
ba kika rinka satar kallona. Anya yarinyar nan baki fi
karfina ba. Da ina yi miki kallon saliha amma yanzu
ajinki daban ne"
Murmushi kawai tayi ta rufe fuskarta da tafukan
hannuwanta tace "zama da kai ne"
"Indai nine baki ga komai ba. Kinga koma kada a fara
cigiyarki. An saba maza ke zuwa zance amma yau kin
kasa hakuri kin biyo ni. "
Sai da ya rakata har kusa da dakin sannan ya dawo. A
daidai inda suka gama magana yaga kamar alamar
mutum. Ya dan juya yaji shiru sai kawai ya tafi.
Qasim ne a wurin kuma duk yaji maganganunsu. Tun
bayan fitowar Asmau ya biyo bayanta a zatonsa Col.
Ishaq ya riga ya tafi. Rasa inda zaisa kansa yayi saboda a
yau ya tabbatar ko kadan bata yi masa soyayya irin
wadda yake fata. Duk wani tunaninsa ya kulle a yanzu
shiyasa kawai ya shiga motarsa ya bar asibitin.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽44
Batul Mamman💖A daren nan Qasim ya wuce Shanono. Abin duniya duk
ya ishe shi. Dama wani lokacin baka sanin kana son abu
sosai sai kaga alamun zaka rasa shi. Da gaske yake jin
kaunar Asmau a ransa. Tunani yake har me ta gani a
tattare da Col. Ishaq take sonsa haka. Yasan mutumin dai
ya hadu amma ko babu komai shi Qasim ya fishi
kuruciya. Duk da bai san komai game da Col. Ishaq ba
amma yana da tabbacin da wuya idan bashi da mata
daya ko sama da haka. Shi da yake da burin bata dukkan
kulawa ta yadda babu wata mace mai suna kishiya da
zata takura mata shine zata kai kanta cikin mutanen da
basu dade da sanin juna ba. Yanzu idan ta aure shi
danginsa suka wulakanta ta fa? Hawaye yaji yana neman
zubo masa. Duk laifinsa ne da ya zama mugun aboki ga
Abubakar. Ba don shawarar da ya bashi ba ai da haka
bata faru ba. Ko Abubakar ya rasu ya tabbatar duk inda
tayi aure zata tsira da mutunci da martabarta. Sai kuma
tausayinsu da yaji. Asmau tayi masa halacci da har bata
kalli tsabar idonsa ta nuna masa bata son shi ba. Yayi
dan murmushi, dole yasan yadda zaiyi ya janyo ra'ayinta
gareshi tare da nuna mata illolin da auren wanda basu
gama sani ba zai iya jawo mata. Idan kuma hakan bai
samu ba......kasa karasa tunanin yayi.
*****
Col. Ishaq yana zuwa gida ya kira Asmau. Jin wayar a
kashe yayi dan murmushi. Ya fuskanci tana cikin matan
da basa bawa waya mahimmanci. Yau ta kashe gobe tace
wayar tana daki ne. Sai da yayi wanka yaci abinci sannan
ya tafi dakin Hajiya.
A zaune ya sameta a kasa Bilkisu tana matsa mata kafafu.
Ya zauna a gefenta ta dan janye jiki ita a dole ga dan fari.
Dariya Bilkisu tayi ya rankwasheta a ka don yasan
tsokanar Hajiya take yi, sannan ya fuskanci Hajiyar.
"ciwon kafar ne ya tashi,akwai maganin ko ya kare?
"Na sha ma bayan naci abinci dazu. Yau ina ka tsaya
daga cewa zaka ganin abokinka"
"Asthma din Safina ce ta tashi suna asibiti an kwantar
dasu."
Cikin tausayawa Haj Lubabatu tace "Allah sarki, ciwon
yaro babu dadi bare ciwo irin wannan. Da ka fada mana
tun dazu ai sai Sabo ya kawo mu kafin ya tafi gida. Ya
kamata su hada mata da maganin gargajiya, zan tambayi
Kawunku suna masana a bangaren. Kasan ciwon yana
bukatar kulawa"
Yaji dadin yadda mahaifiyarsa ke nuna damuwarta akan
abinda yake so duk da bata son fada. Bilkisu yasa ta tashi
hado masa abinci ya samu ya sanar da Hajiyan duk
abinda ya faru a yau bayan zuwansa asibiti. Haj
Lubabatu ta kalle shi cikin damuwa
"Yanzu kai bazaka hakura da ita ba tunda iyayenta sun fi
son wancan yaron?"
"Hajiya itama bata son sa. Kuma don ban gabatar da
nawa magabanta bane da wuri. Kin sanar da su Kawun
kuwa?"
Ta girgiza kai tana mamakin wannan soyayya da danta
yake yiwa Asmau.
"Na fada musu don Yaya Auwalu ma yace zai kiraka kuyi
maganar. Ni dai bana so azo a sami matsala daga
iyayenta gara kawai tunda har an fara batun kawo kudi
ka janye."
Dan murmushi kawai yayi "Hajiya idan kina kyamar
aurena da Asmau ki fada min. Nasan hakan zai iya zuwa
ranki saboda irin yanayin data tsinci kanta a baya. Kin
sani duk yadda nake son abu bazanyi batare da izini da
neman albarka daga gareki ba"
Akwai shi da iya tsara zance da ladabi shiyasa take sonsa.
"Ko kadan bana kyamar aurenku. Kuma ni wacece da
zanki karbar kaddara. Ka sani babu wata uwa a duniyar
nan musulma da zata ji farat daya hankalinta ya kwanta
idan danta ya nemi auren macen da ta taba haihuwa a
wajen aure. To amma kowa da abinda Allah Ya tsara
masa. Yarinyar nan kana ganinta kasan ta fito daga gidan
tarbiya sai gashi tsautsayi ya fada mata ta tsinci kanta a
irin wannan yanayin. Bazan ki ta ba don da Allah Yaso da
daya daga cikin nawa 'ya'yan za'a buga misali. Idan
Asmau matarka ce fatana Allah Ya baku zaman lafiya da
hakuri da juna"
A take fargabarsa na kin amincewarta ta gushe daga
zuciyarsa. "Nagode Hajiya Allah Ya kara lafiya. In sha
Allah zan nemi Kawu Auwalun idan ya bukaci naje
Jikamshin sai naje. Ina so su zo da wuri ne."
Yanaa tashi Bilkisu ta shigo da abincin ta ajiye a gabansa
tana murmushi "Uncle albishirinka"
"Goro maigadon zinare"
Ta danyi tsalle kamar karamar yarinya "gobe Mami zata
zo"
Dena zuba lemon da yake yi yayi yace "da gaske"
fuskarsa na nuna

Please Login or Register in order to submit comment