Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guduma "Malam ya
zaka ce bamu da gado? Dukkanmu fa uwa da uba daya
muke. Ni nan da kake gani shi ya saki nono na kama ko
ba haka ba Hajjo?"
Malam yayi murmushi "Alh Rabe ai shi rabon gado ba'a
yi masa katsalandan. Allah SWT da Kansa Ya raba saboda
haka babu wani son zuciya a nan. Zan nemi 'yan uwana
malamai kamar mutum biyu sai muyi abinda ya dace.
Allah Ya jikan Alh Shu'aibu".
Malamin na fita Rabe ya soma fada ya dubi 'yan uwansa.
Babu wanda yace masa komai. Dama Garzali karamin
cikinsu baya shiga sabgarsu sosai shaye shayensa ne a
gabansa. Yaya Abu da Lami ma basuyi magana ba ganin
Hajjo tayi shiru. A haka taron ya watse Bara'atu na
mamakin wannan hali na Rabe.
Har daki Rabe yabi Hajjo tana daga kwance akan gado ta
tashi zaune.
Ya numfasa yace "Hajjo kina jin malamin nan. Yanzu
banda sharri yace bamu da gado. Nufinsa wannan gidan
da Yaya yake ta shirin komawa Bara'atu da 'ya'yanta ne
kadai zasu tare?"
Hajjo tace "banda abinka Rabe ai haka rabon gado yake.
Da so kake ace kaima ka shiga gidan ko yaya? Dubi fa
yadda ya sake gyara gidan nan. Ni bana son tashin
hankali. Kada na sake jin zancen nan ya taso". Da haka ta
kashe maganar.
Kwanaki biyu a tsakani Malamin ya dawo aka zo akayi
rabo daidai da sharia. Gida da mota duk sun fada rabon
Bara'atu da 'ya'yanta. Gonar Zaria an sayar aka fitarwa
Hajjo nata sauran duk na 'ya'yansa ne. Bakin cikin Rabe
baya misaltuwa. Ya kwallafa rai sosai akan gidan.
Bara'atu ta koma Zaria suka fara shirin dawowa Kano
gabadaya.
*****
Rabe zaune gaban wani malamin tsibbu ya gabatar masa
da bukatarsa ta son a toshe bakin Hajjo duk abinda ya
fada ta amince.
Dariya Malamin yayi sannan ya karbi kudin aikinsa.
"Indai wannan ne matsalarka an gama."
*****
Bayan sati daya Hajjo ta zaunar da Rabe fuskarta cike da
damuwa " idan baka fada min matsalarka ba wa kake
dashi wanda ya fini?"
Kansa a kasa yayi dan murmushin takaici "Hajjo ko na
fada bazaki amince ba. Gani kike yi kamar cutar da iyalin
dan uwana nake son yi".
"Ko kadan Rabe, fada min abinda ke ranka".
"Dama nayi tunani ne bai kamata na bar zuri'ar Yaya ta
wulakanta ba. Kinga matarsa tana da sauran kuruciya.
Idan tace zatayi aure waye muka sani da zai kula da ita
da 'ya'yan da zuciya daya? Ni a tunanina ta bani su tunda
mun rabo da Laraba sai na kara aure na rikesu
gabadaya. Ko kuma....."
"Ina jinka, ko kuma me?"
Dan murmushi yayi mai nuna yana jin kunyar abinda zai
fada "nace ko zaki yi mata magana ta amince na aureta.
Kinga sai mu zauna tare gabadaya da yaran. Babu zancen
a rabata da 'ya'yanta."
Shiru Hajjo tayi yana tunani.."yanzu matar da ko wata
uku batayi da haihuwa ba kana ganin ba'ayi wauta ba
idan aka bijiro mata da zancen aure?"
Dadi yaji batayi fada ba "nima ba wai yanzu yanzu zan ce
ayi auren ba. Kawai dai tasan da maganar ne".
Hajjo ta kada kai "shawararka tayi kyau , ranar asabar
zata zo su fara kawo kayansu sai kayi mata magana a
lokacin.
Asabar da yamma Bara'atu na shayar da Aina'u a tsohon
dakinsu Rabe ya shigo babu ko sallama.
Da sauri taja rigarta ta suturta jikinta rai a bace. Wani
kallon kasa kasa yake mata yana murmushi.
"Mutum da kayansa meye kike wani rufe jiki"?
Maganarsa ta bata mata rai tayi yunkurin tashi yace ta
zauna magana zasuyi. Zama tayi a nan ya sanar da ita
bukatarsa. Hade rai tayi tana kallonsa a wulakance.
"Rabe bahaushe yace in maye ya manta uwar da bazata
manta ba. Duk irin cin kashin da kukayi min a gidan nan
don rashin kunya zaka ce kana son aurena. To ni ba
shashasha bace, nasan sarai abinda kake nema a gareni.
Gida ne ya tsokale maka ido kake son mu koma daga
nan dani da yaran da abinda kake ganin sun samu mu
koma mallakinka. To wallahi kayi kadan. Ko mazan
duniya sun kare bazan aureka ba."
Hajjo ta shigo tana kallon yadda Bara'atu take fadawa
danta magana. Tuni ta rufe ido ta fara fada.
" yanzu saboda yana son rufa miki asiri kike masa
wannan rashin mutumcin? Idan har baki aure shi ba to
ki sani dole ki bashi yaran nan."
Fada sosai Hajjo tayi Bara'atu bata tanka ba. Washegari
ta koma Zaria suka karasa hada kayansu wata mai zuwa
zasu taho idan sun karbi takardun yara na makaranta.
*****
A nasa bangaren Rabe yayi ta zuga Hajjo akan ta bari ba
sai ya auri Bara'atu ba kawai ta amince ya zauna a gidan
da nasa yaran sai ya hada duka ya kula dasu. Itama
Hajjon ta zo a tare da ita tunda gidan akwai dakuna.
Yaci galaba domin Hajjo ta amince. Sannan tace ya nemi
mata yayi aure. Ita ya barwa zabi ta hadashi da 'yar
kanwarta. Bayan sati uku aka daura aure amarya ta tare
a sabon gida a Hotoro. Ba ayi mata kaya da yawa ba
saboda kusan komai na amfani Shu'aibu da Bara'atu sun
saka.
Kwanan amarya biyu su Bara'atu suka iso Kano. Kayansu
ta kwatantawa masu mota aka kai hotoro ta wuce kofar
mazugal. Makota ke sanar da ita su Hajjo sun tashi. Tayi
mamaki sosai to ina suka koma? hotoro ta wuce da sa
ran zata je gidan Lami a kwatanta mata inda suka koma.
Suna isa gate din gidan Jafar ya fita ya budewa mijin Anti
Bintu da ya tuko su a motar da yanzu ta zama ta Bara'atu
ya shiga. Yaran Rabe su biyu ta gani suna wasa a waje ga
Hajjo zaune karkashin bishiyar goba tana shan iska.
A sanyaye Bara'atu ta karasa kirjinta na dukan uku uku.
Hajjo ta washe baki tana yiwa jikokinta maraba. Bara'atu
ta gaisheta tana kallon kofar gidan a bude.
Hajjo tayi tsaki "ya naga duk jikinki yayi sanyi ne? Ki
kwantar da hankalinki nayi tunanin bai kamata na matsa
miki ki auri Rabe ba shine muka dawo gabadaya a taro a
kula da marayu. Kuka ne ya tasowa Bara'atu sai dai kafin
ya kai ga fitowa ta ga Sagira yar kanwar Hajjo ta fito
Garzali yana binta a baya yana tsokanarta.
Hajjo ta saki murmushi "ga amaryar Rabe fa
shekaranjiya ta tare. Bari tazo ta nuna miki dakunanku
ke da yara. Daki har biyu Rabe yace a baku. Su Jafaru
dakinsu yana nan kusa da na kawunsu Garzali"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Bara'atu ke fada
saboda tsananin bacin ran da take ji a wannan lokacin.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽16
Batul Mamman💖
Wannan karshen satin tun alhamis Abubakar yazo.
Kullum sai yaje wurin Asmau sunyi hirarsu yadda suka
saba. Ranar asabar ya wuce Shanono wurin Qasim suka
je daurin auren wani dan uwan Qasim din. Daga nan
suka koma gidansu sai zuwa yamma yayi niyar komawa
cikin Kano.
Zaune suke a dakin Qasim suna kallon ball wayar abokin
nasa tayi kara. Rage sautin TV din yayi ya amsa wayar. Ya
dan jima suna hira d wadda Abubakar ya fuskanci mace
ce sai daga baya yaji akalar hirar ta canja. Qasim yana
tambayar yarinyar wane irin kaya ta saka.
Murmushi yayi bayan ta bashi amsa "me kika saka a
ciki?"
"Ni kwance nake a daki da shorts(gajeren wando) ina
shan iska ina tunaninki" (karya yakeyi. Kufta da wando
ya saka).
Irin wannan hirar ya kusa rabin awa suna yi da
budurwarsa. Abubakar sai kada kai yake don takaicin
wannan hali na Qasim. Yayi fadan da nasihar har ya gaji
gashi ya kasa rabuwa dashi saboda shakuwarsu. In dai
hirar banza ce a waya to Qasim ya ciri tuta. Sai ance ya
fidda matar aure yace duk mata babu tagari.
Mugun kallon da Abubakar yake jifansa dashi yasa ya
katse wayar yana dariya.
"Ya Ustaz irin wannan harara haka. Ni fa bance ka tsaya
jin hirar ba duk ka wane hade rai."
"Yanzu bazaka dena wannan muguwar dabi'ar ba? Ina
jiye maka tsoron kada watarana kayi me gabadaya.
Kasan zuciya bata da kashi".
Kujerar kusa da Abubakar ya dawo ya zauna.
"Kaima kasan duk abuna bazan yarda nayi lalata da 'yar
mutane ba. Irin wannan hirar dai da dan abinda ba'a
rasa ba shi muke yi don mu rage yawa.
Sanin kanka ne yadda aure yayi tsada ni kuma ba wani
abu na tara ba. To kuma ga abu mu muna so suma
matan suna so. Sai a taimaki juna".
Runtse ido Abubakar yayi "ji yadda kake cewa a taimaki
juna kamar wani aikin kwarai. Kana dan malam har ka
manta haramcin taba jikin macen da ba muharramarka
ba? Ko ka manta inda Allah SWT Yake cewa : *WALA
TAQRABUZ ZINA INNAHU KANA FAAHISHATAW WA
SAA'A SABILA*
(ISRA' 32)
Ma'ana _KUMA KADA KU KUSANCI ZINA DOMIN ITA
ALFASHA CE KUMA HANYAR BATA_
Taba jikin budurwa da niyar gusar da sha'awa batare da
kunyi abin gabadaya ba yana cikin abinda Allah Yayi hani
dashi. Kallo wannan da irin maganganun nan da kuke yi
duk yana ciki. Wata rana sai kaga anyi abinda ake gudu
azo ana cizon yatsa."
Qasim yayi murmushi jikinsa ya danyi sanyi sai dai
shaidan bai barshi ba.
"Naji kuma duk nasani to amma ka manta cewa Allah
SWT mai yawan gafara ne da jinkai? Idan mutum ya
aikata irin haka tuba fa kawai zanyi a kankare min
zunubin. Haba Abubakar kaima kasan yadda zuciya take.
Ni a haka nasan ina kokari don ban taba ketawa kowace
mace haddi ba. Za'ayi abin sama sama gayyar ta watse."
Abubakar yace "Muna cikin wani zamani ne da hanyoyin
gurbata tarbiya musamman masu nuni da zina suke da
matukar yawa. Cartoon wannan sai kaga mage da bera
suna kiss. Duk a haka ake lalata mana zukata. Na dade da
sanin ina cikin maza masu karfin sha'awa shiyasa kaga
na dage da yawan azumin litinin da alhamis. Idan naga
abin zai dameni har sauran ranaku inayi. Manzon Allah
SAW yace a lokacin da mutum yake zina fa babu imani a
tare dashi. To me zaisa mu biyewa son zuciya haka kawai
kana kan wata mace mala'ikan mutuwa ya ziyarce ka".
Qasim ya dubi abokinsa. Tabbas Abubakar ba tun yau ba
baya cikin maza masu kallon mata. Shiyasa ake masa
kallon mai kunya sosai shi kuwa yana yi ne don ya kare
zuciyarsa.
"In Allah Yaso zanyi kokarin denawa sai dai fa abin sai a
hankali. Bazan maka karya ba wallahi na saba sosai. Allah
mun tuba."
Da haka hirar ta kare bayan la'asar Abubakar ya koma
gida.
*****
Washegari lahadi Umma ta tafi da Aina'u yinin 'yar wata
kawarta sai Asmau da Yassar a gida Abubakar ya kirata a
waya zai zo suyi sallama don yau da wuri yake son tafiya.
Sauri tayi ta karasa girki sannan tayi wanka ta canza
kaya. Kwalliya tayi sosai irin yadda take karantawa 'yan
matan littafi na yiwa samarinsu. Ta saka wata doguwar
rigar atampa maimakon ta daura dankwali tasa hijab ko
mayafi mai mutumci yadda ta saba sai ta dauko wani
karami a kayan Aina'u ta yafa rabin kanta da yasha
sabon kitso duk a bude ta gaba. Falo ta koma ta zauna
sai taji kunyar ya ganta a haka. Ta tashi ta koma zata
canza wata zuciyar tace tayi zamanta abinda sun kusa
aure kuma dai haka ake yi yanzu don ita duk abinda ta
karanta har ranta gani take yi daidai ne saboda a yadda
ta dauki marubuta masu buga littafi da online komai
suka rubuta basa kuskure.
Sake shafa hoda tayi ta dawo falon. Tana zama Abubakar
yayi sallama tare da neman izinin shigowa ta amsa masa.
Gabansa ne ya fadi da yaga Asmau. Tayi kyau sosai gashi
tana da 'yar kiba sai rigar ta kamata a kirji da kugunta.
Ba wai bai taba ganin yanayin jikinta ba saboda yau da
gobe yakan ganta babu mayafi amma sai bisa kuskure.
Yau kuwa shigar ta tsaya masa a kokon rai har ya kasa
dauke idonsa daga gareta.
Murmushi tayi na nasara saboda yadda taga yanayinsa
ya canza. Tunda ta fara karance karance da hirarsu da
Walida taji ta matsu ko hannunta ne ya dan rike itama
taji yadda ake ji.
Wani juya ido tayi duk sauran kunyar suka bace "Mine
ka zauna mana."
Wani jan numfashi yayi "Asmy kinyi kyau"
Tayi masa murmushi "nagode"
"Kaci abinci ko na kawo maka? Bana son ka tafi da
yunwa".
Abincin ya bukaci ta kawo masa. Ta tashi tana tafiya mai
daukar hankali. Har ta shige kitchen ya kasa dena
kallonta. Sai da ta bace yace _Astagfirullah_ tare da
kudurta niyyar zaice ta suturta jikinta sosai.
Tana dawowa kujerar gefensa ta zauna kamshin
turarenta ya bugi hancinsa sai ya fasa cewa ta rufe jikin.
Yana matukar son Asmau amma yau harda wata
muguwar sha'awarta ce ta taso masa. Yana cin abinci
suna hira kadan kadan domin duk hankalinsa ya koma
kan halittar jikinta.
A nata bangaren ta lura da canjawarsa kuma taji dadi a
ranta. Da ya tashi zai tafi dubu biyu ya miko mata kudin
motar makaranta. A da sai ya bata sau uku bata karba ba
har suyi fada wani lokacin. Amma yau kawai don taji
hannunsa a nata ta mika hannun a kunyace tana kallon
kasa. Tana sane tayi hakan hannunta ya kai kan nasa
maimakon kudin.
Saurin dauke hannun tayi saboda wani yanayi na daban
da taji (dama shaidan komai kankantar haram dada
mata dadi yake fiye da yadda take don kawai a cigaba da
aikata ta)
"yi hakuri ban kula ba"
Abubakar yaji dadi fiye da yadda taji domin tana taba
hannunsa ji yayi kamar ya janyota jikinsa. "Dama ina
zaki kula kina wani sunkuyar da kai kasa. Ni zan tafi sai
friday in sha Allah. Ki kular min da Asmy na".
Tana murmushi tace
" nima ka kular min da Yayana. Allah Ya tsare Ya kaika
lafiya."
Haka Abubakar ya tafi surar Asmau tana yi masa gizo.
Sawa yayi a ransa idan sunyi waya zai fada mata ta dena
irin shigar nan har sai sunyi aure. Sai dai yana isa bayan
sallar magriba wasu hotunanta suka shigo wayarsa. Duk
babu wanda tasa dankwali kanta wasu ma rigunan sun
dameta fiye da rigar dazu.
Bai iya yi mata maganar da yayi niyya ba ya rasa dalili.
A haka suka kwashi wajen wata biyu. Asmau ta dena jin
kunyar fita gabansa da shigar bayyana jiki indai tayi sa'a
yazo Umma bata gida. Mayafin nan kullum a kafada an
baza gashi ta kasan dankwali. Tun yana tsanar kansa idan
suka rabu har ya saki rai yana jindadin hakan tunda
yasan aurensu yana kusa. Kusa da juna suke zama yanzu
ana hira sai su rinka neman hanyoyin taba hannun juna
kowa yana nuna kamar ba hakan bane a ransa.
Sai yanzu Asmau ta yarda suna soyayya domin tafi
jindadin alakarsu. A zuciyarta ta kwantar da hankali
tunda tana da yakinin aure zasuyi kuma dai ana aure
komai ya wuce. Ita yanzu babban burinta yayi kissing
dinta ko sau daya ne yadda take karantawa. Ayi kiss
amma sai a nuna kamar bisa kuskure ne ko kuma a nuna
na komai yin hakan a addini da al'adarmu.
A nasa bangaren shima ya dena damuwa. Kullum
sha'awarta karuwa take yi a ransa hakan yasa ya soma
rasa nutsuwarsa. Bashi da aiki sai azumi kamar mai
kaffara amma wasu ranakun shi kansa yasan a irin
tunanin Asmau da yake yi na tsantsar sha'awa azumin
nan baya kaiwa ko ina.
*****
Su Asmau an gama jarabawa kuma wannan karon suna
dawowa makaranta idan aka sake hutu za'ayi bikinta.
Ko sati ba suyi ba da fara hutu Anti Bintu tazo Kano
ziyara. Kwananta biyu mijinta yazo da zasu koma tace da
Asmau zata tafi. Umma bata musa mata ba ta umarceta
da hada kaya. Murna tayi sosai Aina'u kuwa ansha kuka
gashi ba'ayi hutu ba.
Abubakar yaji dadin komawar Asmau Zariya wani satin
da ya zagayo ko Kano bai je ba. Mama Yalwa tace ta gane
dama zuwan ba nasu bane na Asmau ne.
A gidan Anti Bintu yake zuwa su sha hira wadda a hankali
ya fara rungumarta da sunan zaiyi kewarta idan ya tafi.
Su biyun duk sun san haramcin abinda suke yi amma
sunyi nisa. Suna haduwa duk yakin da suka shirya da
wannan sabuwar dabi'ar tasu sai ya rushe.
Anti Bintu ko kadan bata san me suke yi ba. Falonta take
bar musu idan yazo. Nutsuwa da tarbiya irin ta Asmau
da Abubakar babu wanda zai taba zargin haka
tsakaninsu.
Wata rana bayan asuba karamin dan Anti Bintu Haidar
yana toilet bayan ya gama ya fara kiran Asmau tazo tayi
masa tsarki. Lokacin ko bakwai na safe bata yi ba duk
baccin da take ji taki komawa saboda an turo cigaban
wani labari da take karantawa. Ko yunkurin tashi bata yi
ba tace masa tana zuwa.
Haidar ya kirata yafi sau biyar tana cewa gata nan har
Anti Bintu ta fito daga kitchen tayi masa tsarkin lokacin
har ya fara kuka. Duk abinda suke yi da Asmau ta ji.
Dakin nasu ta shiga Asmau tayi nisa a duniyar labari sai
ganin Antin tayi a tsaye a gabanta. Da sauri ta tashi a
tsorace zata fita.
"Dawo indai tsarki zaki yiwa Haidar nayi masa"
Duk sai taji kunya sannan ta gaisheta. Anti Bintu ta dauki
wayar da ta ajiye akan gado ta bude ta dan karanta wani
bangare na labarin. Tayi scrolling sama kuma irin sakon
nan ne na kwanciyar aure.
Jikin Asmau kamar mazari don tsoro ta gama rudewa.
Anti Bintu ta kama hannunta ta zaunar da ita a bakin
gado sannan taja kujerar gaban mudubi ta zauna.
"Kin bani mamaki Asmau. Wannan wane irin text ne kike
karantawa? Yanzu kwanciyar aure har sai wata can da
baki sani ba ta koya miki? Wannan abu halitta ce wadda
idan lokacin yinta yayi baka bukatar malami. Idan kuma
har akayi rashin sa'a mace ko miji suka matsala ta
fannin gamsar da juna to ba duniya zaki fadawa
matsalarki ba. Mutum daya zaki samu cikin 'yan uwa ko
abokan arziki wanda zaki iya bawa amanar sirrinki sai ki
fadi matsalar a baki shawara. Amma me ya kaiki karanta
irin wannan post din wanda ko matar aure ce ta karanta
da wuya idan bai karya mata alwala ba saboda yadda ake
bayani 6aro-6aro. Kada ki bari kawayen banza suce ya
kamata a koya miki irin wannan tunda kin kusa aure.
Komai yana da lokaci. Kodayake masu rubutawa sunfi
kowa laifi tunda kayi rubutu ne baka san iya idanunwan
da zasu karanta ba. Wayar nan yarinyar da bata fara jini
ba ma tana da ita kuma akan same su a groups din
manya suyi ta sakin baki a gaban 'ya'yan cikinsu. Wani
lokacin sai su tura yara masu karfin sha'awa su karanta a
tayar musu da hankali su fara neman mafita. Ki rufawa
kanki asiri ki dena karanta abinda bazai amfaneki ba.
Abu na biyu wannan novels din da kike karantawa. Nima
babarki ina karantawa amma ki sani akwai wanda har ki
gama babu wani darasi da zaki dauka sai bata lokaci da
tabarbarewar tarbiya. Uwa uba kuma wannan mugun
son da muke yiwa labaran yana sawa mu manta da
al'amuran da suka fi bukatar hankulanmu.
Tun zuwanki gidan nan na fuskanci kin canja sosai. Kina
idar da sallah ko azkar baki gama ba sai ki janyo waya.
Har akwai wani labari da zaisa ki kasa hakurin minti biyar
ki bautawa Allah cikin nutsuwa? Mata irinki da yawa gasu
nan. Sau nawa girki yake konewa ko mace ta yini cikin
kazanta saboda karatun labari wanda a ciki tsafta da kula
da miji ake koyarwa? Wata ma bata girkin akan lokaci sai
taji mijinta ya kama kofar gida zai shigo ta ruga kicin.
Wata ta bar yaro da kazanta har sai ta gama karatu. Wata
kuwa da wayar zata shigo bandaki tana biyan bukatarta
tana karanta labari. Idan hakane karatun labaran masu
dauke da darussa bai amfanemu da komai ba sai kasala,
ganda da kazanta.
Ki zama mace mai tsari a rayuwa komai kiyi shi a
lokacin da ya dace. Babu abin takaici sai kinga mace da
tsakar dare ko asubar fari tana cigiyar novel ga mijinta a
gefe bawan Allah kila yaso ta bashi hakkinsa na aure ma
amma ya hakura don kada ya takurata. Idan mara
hakuri ne ayi ta samun sabani.
Asmau nasan Yaya Bara tana kokarinta a kanku. Gashi
aiki yayi mata yawa duk don biya muku bukatu. Kada ki
watsa mata kasa a ido da dabi'u marasa kyau kinji ko".
An tuno da Idon kuka ana mata fada tana sana'arta. A
take tayi nadamar daukar shawarar Walida wanda yasa
take yin abubuwan da a da can tasan basu dace ba.
Kukanta ya tsananta da ta tuna tabbas irin yadda suke
gudanar da soyayyarsu yanzu yana da alaka da canjin da
ya fara tasowa daga gareta. Wai ita ce suke rungumar
juna da Abubakar. Abubakar dinta mai riko da addini ta
zama sanadiyar da suke munafuntar kawunansu da
iyayensu.
Anti Bintu ta cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya
sannan ta tashi. A ranar ta ga canji sosai a wurin 'yar
tata. Asmaunta ta da ta dawo.
*****
Abubakar na kwance a daki yana kallon wasu hotunan
Asmau. Tun daren jiya da ta turo ko baccin kirki ya kasa
yi. Yau da ciwon mara ya tashi irin wanda ake samu idan
sha'awa tayiwa mutum yawa. Ya rasa abinda yake masa
dadi ko office ya kasa zuwa. Shawara ya yanke zaije
Zariya a ranar ko dan yaya yayi dan abinda zai kwantar
da kwadayinsa. A yadda yake sonta bazai iya neman wata
matar a waje ba. Ita dinma bashi da niyar ayi mai
gabadaya ta bakin Qasim. Dan dai abinda ba'a rasa ba
yadda sai samu yaji dadi. Da wannan shawarar ya tashi
yayi wanka ya hau shirin zuwa Zariya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽17
Batul Mamman💖
Kafin ya fito ya kira Asmau a waya ya sanar da ita zai zo.
Jikinta a sanyaye ta amsa masa don ita yanzu kunyar
ganinsa take yi. Ko ba'a fada ba daga nasihar Anti Bintu
tasan cewa duk abinda ya faru laifinta ne.
Har daki taje ta sanar da Anti Bintun zai zo kamar yadda
ta saba.
"Ki dora abinci dashi amma ki bar dan waken sai gobe
don bazan bawa suriki dan wake ba"
Ita da Asmau duk dariya sukayi sannan ta wuce ta dora
shinkafa da miya.
Wuraren karfe uku ya iso Anti Bintu tazo suka gaisa
sannan ta basu wuri.
Yau Asmau hijab ta saka dogo har kasa fuskarta babu
kwalliya sai hoda da kwalli. Jikinta duk babu kwari tayi
nadama sosai. Abubakar kuwa tamkar ya hadiyeta da
kallo. Anyi sa'a yaran gidan suna ta gilmawa a falon. Da
laasar suka tafi islamiyya shi kuma yaje yayi sallah.
Ana idarwa ya dawo ya kalli Asmau dake zaune a can
gefe.
"Asmy dawo nan kusa dani nafi jindadi". Ya nuna kujerar
gefensa.
Tashi tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tana
zama ya kama hannunta ya rike yana lumshe idanu. Can
kasa take jin muryarsa
"I love you so much Asmy. Ina ma anyi aurenmu kiga
irin abinda nake nufi."
A kwanakin baya har so take ya rike mata hannu amma
yau sai taji ta tsani hakan. Tana son nuna masa kuskuren
abinda tasan ya fita sani amma dole tabi lamarin a
hankali kada yayi mata mummunar fahimta ko yace ta
mayar dashi dan iska.
Har lokacin tafiyarsa yayi bata iya sakin jiki dashi ba. Shi
kuwa gabadaya ya kasa samun nutsuwa. Bakin motarsa
da ya ajiye a wajen gate ta raka shi ai kuwa yana bude
motar ya rungumota jikinsa. Dama layin ba mutane
sosai saboda unguwar bata gama cika ba ga duhun
dare.
Wasu hawaye masu zafi Asmau taji sun taho mata ta
hadiye. Dole ta sami lokaci suyi magana da Abubakar
akan wannan abin. Rungumar da take jindadi daga
gareshi yau bata so. Tana wannan tunanin taji yayi mata
abinda bai taba yi ba. Abinda take ta mararin faruwarsa.
Bakinsa ya hada da nata yayi mata rikon da bazata iya
kwatar kanta ba koda tayi niyya.
Hawayen da take boyewa ne suka sakko ganin Abubakar
tamkar baya cikin hayyacinsa. Abubuwan da yake mata
sun fara wuce gona da iri. Ba shi ya saketa ba sai da don
kansa yaji hankalinsa ya fara dawowa gareshi.
Ganin tana kuka ya soma bata hakuri.
"Asmy kiyi hakuri please. Na rasa dalilin da yasa nayi
miki hakan. Ki sani ina sonki tsakani da Allah kuma in sha
Allah bazan sake kwatanta miki haka ba sai munyi aure".
Yadda yake maganar sai ya bawa mutum tausayi. Tabbas
baya son abinda yake yi sai dai karfin sha'awarsa da
tsananin rudin shaidan yasa ya kasa hakuri.
A hankali ta share idonta "Yaya Abubakar don Allah mu
dena irin wannan abin kaga babu kyau."
"Na sami Asmy, ni kaina na rasa gane yadda akayi muka
fada ga wannan masifar. Ki share idonki kinji matar
Abubakar".
Kafin ya tafi sai gashi ta sake sosai hankalinta ya kwanta.
Suka rabu zuciyar kowa tana nata sake saken.
*****
Abubuwan da suka gudana tsakanin Abubakar da Asmau
su suka rinka yi masa yawo a kwakwalwa. Yayi tunanin
zaiji saukin sha'awar dake damunsa sai abin yayi tsanani
sosai. Kullum cikin mafarkinta yake yi. Baccin kirki ya
gagare shi sai tunanin yadda zaiyi ko dai a matso da
aurensu ko ya kashe yunwarsa ko sau daya ne.
A nata bangaren hatta hirar da suke yi a waya yanzu tana
kame bakinta daga hirar da bata dace ba. Ta tarkarta
tunaninta kaf zuwa lokacin aurensu ko sa sami nutsuwa
da kwanciyar hankali saboda tasan duk su biyun yanzu a
matse suke da ganin wannan lokacin.
Bayan kwana biyu ya sake zuwa wannan karon ko waya
baiyi mata ba. A hirarsu da Anti Bintu ya nemi izinin
ranar asabar da Asmau zata tafi zai zo ya kaita da kansa a
cewarsa baya so ta shiga motar haya.
Anti Bintu tayi shiru na dan lokaci saboda ba haka sukayi
da yayarta ba. Dama tasha za'a kaita ta tafi saboda motar
Kawu Yusuf tana gareji wurin makanike. A duk dan
tunaninta bata hango wata matsala ba duba da irin siffa
ta kamala da suke dashi su biyun.
Asmau kanta bata ji komai ba saboda yau hirarsu duk
irin ta da ce. Cikin nutsuwa da kiyayewa. Soyayya mai
tsafta irin wadda masu yinta basa son rabuwa da juna.
Kwanaki ukun da suka zo kafin tafiyarsu Abubakar yaji
babu dadi. Har wani zazzabi ne ya kamashi saboda ji
yake tamkar ana hura masa wutar sha'awar kasancewa
da mace. A yadda yake ji ko ba Asmau bace wannan
karon zai iya nema.
Ranar da zasu tafi wurin karfe goma ya iso. Asmau da
yaran harda dan kukansu na rabuwa.
Suna mota ita da Abubakar babu wata hirar kirki don
basu taba kadaicewa a mota haka ba na tafiya mai nisa.
Hanyar cikin gari ya nufa ya kashe motar a gefen titi.
Asmau ta kalle shi zata

Please Login or Register in order to submit comment