Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi magana sai ta kasa ganin
idanunsa sunyi wani iri kamar wanda yake cikin tashin
hankali.
A raunane yake dubanta har sai da tsigar jikinta ta tashi
don tsoro da ya dora hannunsa a kan nata.
"Asmau"
Yaushe rabon da ya kirata da sunanta haka. Gabanta na
dukan uku-uku ta amsa.
"Idan na rokeki alfarma zaki yi min?"
Ita fa Yaya Abubakar tsoro yake bata da yanayinsa na
yau.
"in sha Allahu idan baifi karfina ba".
Gwauron numfashi ya ja.
"Asmy ina cikin matsala kuma ke kadai ce zaki iya yi min
maganinta. Ko sati ba'ayi ba da muka amince mun dena
taba jikin juna.."
Bugun zuciyarta ne ya karu tana ganin kamar ta fara
fahimtar inda zancensa ya dosa.
"Ni mutum ne mai yawan bukata, ina tsammanin baki
san me hakan yake nufi ba."
A ranta kuwa tace sai dai na fadawa wani. Rabe-raben
mutane ta fannin sha'awa tuni ta san shi a posts din
waya. Muryarsa wadda take rawa taji a kusa da ita.
"Ina cikin tashin hankali da son kasancewa tare dake.
Wallahi bazan iya kaimu Kano ba a yanayin da nake ji
yanzu musamman da kike zaune kusa dani. Ki taimakeni
ko sau daya ne na kawar da wannan masifaffen
tunanin."
Kofar motar ta kama a gigice hawaye na wanke mata
fuska jin ya saka lock. Sanyin AC bai hanata gumi ba.
"Yaya Abubakar ka rufa min asiri ka mayar dani gidan
Anti Bintu. Duk ni na jawo wannan matsalar da na rinka
saka kaya masu matse jiki ina zama kusa da kai. Sharrin
shaidan ne da na zuciya don Allah kayi hakuri nan da
wata hudu zamuyi aure fa".
Magiyar da take masa jin muryarta yake kamar tana
masa busa. Wannan wace irin masifa ce??? Shiyasa tun a
da yake nisanta daga duk abinda zai jawo masa sha'awa
tunda ya gane yanayinsa.
Hawaye ne ya zubo a idonsa wanda bai san dalilinsu ba.
"Ke kadai nake so kuma da ke kadai na amince Asmy.
Idan baki amince ba wallahi nayi miki rantsuwa zan
nemi wata. Bani da lafiya duk a dalilin sonki da son
kusantarki. Ko kinsan satin nan ko sau daya banje wurin
aiki ba saboda halin dana tsinci kaina a ciki".
Kuka Asmau take yi sosai gashi tausayinsa ya mamaye
zuciyarta.
" Yaya kada mu aikata haram. Kuma idan ka rabani da
abinda duk budurwa take takama dashi yaya zanyi?"
Hannuwanta duka biyun ya rike. "Asmy kinsan dai nine
mai aurenki ko? Kuma ni ba wai zanyi miki yadda zaki
tashi daga budurwa bane. Akwai yadda zanyi babu
wanda zai ce namiji ya kusanceki. Ki taimake ni.
Har bincike nayi wasu malaman sunce kudin aure daidai
yake da sadaki. Ko baki ga iyayenmu maza ke zuwa ba
ayi a gaban shaidu. Al'ada ce kawai sake taruwar da ake
yi a daura aure. Amma yanzu ma a haka ni da ke
matsayin mata da miji muke." Shi da yake fada mata
hakan ya tabbatar karya yake yi amma babu yadda ya
iya da zuciyarsa.
Roko da rarrashi haka ya rinka yiwa Asmau tana kuka
haka ta amince saboda tausayin da ya bata da tsoron
kada ya nemi wata.
Wani hotel ya sama musu kuma da yake duk sunyi
shigar mutunci babu mai cewa ba ma'auratan gaske
bane. Haka ya karbi mukullin dakin zuciyarsa tana
kwabarsa da abinda yake shirin aikatawa amma gangar
jikinsa bazata iya hakuri ba.
A kofar dakin da kyar Asmau ta shiga. Yana rufe kofar ta
kara fashewa da kuka. Abubakar yayi nisa duk da yana
tausayinta hakan bai hanashi biyan bukakarsa ba.
Alkawarin da yayi mata na yin dabara kada ta rasa
budurcinta tuni ya manta dashi.
Sai da komai ya kammala yaji kamar tashin hankalin
duniya duk ya kare a kansa. Gefen gado ya koma ya dafe
kai ya rasa inda zaisa kansa.
Asmau tana kwance sai sautin kukanta ke tashi. Ga ciwo
ga bakinciki.
Sun kusa awa daya sannan yayi wanka ya umarceta da
itama tayi. Wannan masifa da yawa take...Ya Allah Ka
tsare mana imaninmu.
Haka suka fito babu wanda yake yiwa dan uwansa
magana. Ya biya kudin hotel suka wuce Kano yana ta
zabga gudu a hanya.
A bakin gate din gidansu ya sauketa zuciyarsa tana kuna.
Ya rasa me yake ji game da Asmau. Ko kayanta bai
taimaka mata da dauka ba haka ta fito dasu ta shige gida
fuska a kumbure.
Su Umma sai murna suke yi ta dawo amma ganin
yanayinta Umman ta tsorata tana tambayarta abinda ya
faru.
Asmau ta fashe da kuka ta rungume mahaifiyarta. Yau
taci amanar addininta kuma taci amanar Umma.
Taruwa suka yi a kanta Jafar ya taba jikinta. Zazzabi ne
sosai a jikin hatta kanta ya dau zafi.
Ya danyi murmushi "Umma wannan 'yar taki ta fiye
shagwaba da raki. Daga zazzabi kuma sai kuka?"
Sai a lokacin tayi dan murmushi ganin cewa idan ta
cigaba da kukan zata tonawa kanta asiri.
"Yaya Jafar ji nake kamar kan zai tsage biyu"
Umma ta tasheta tsaye
"Ki dena tsorata ni irin haka Asmau. Baki ji yadda
gabana ya fadi ba. Muje ki dan watsa ruwa sai kici abinci
kisha magani. Ina Abubakar din?"
Har zuciyarta ta razana jin an ambaci sunansa.
"Ya tafi gida amma yace zai shigo ku gaisa anjima".
"Babu komai ai kun sha hanya ga rana. Allah Yasa ba
kukan nan naki kika rinka yi masa ba saboda baki
jindadi."
*****
Har washegari Asmau tana kiran wayar Abubakar saboda
bai zo ba kamar yadda tayi tsammani. Babu waya babu
text. Nata kiran kuma yaki dauka. Hankalinta yayi
matukar tashi. Yanzu idan ya fasa aurenta saboda abinda
suka yi yaya zata yi da ranta.
Shima a gida kwana yayi kuka. Idan yaga wayar Asmau ji
yake kamar yasa ihu. Zuciyarsa ta kasa rabe masa
haushinta yake ji don ta bashi kanta ko kuwa haushin
kansa da ya tilasta mata.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽18
Batul Mamman💖
Bacci barawo ne ya sace Asmau ba don taso ba. Ta raba
dare tana kuka wanda ya haddasa mata mugun ciwon
kai ga jikinta da yayi tsami. Washegari wurin karfe
takwas da rabi ta fito daga dakinsu zata shiga kitchen
dora ruwan tea ta tarar Umma har ta dama kunu tana
buga kosai.
Gaishe da Umman tayi sannan ta yunkura zata karbi
aikin ta karasa Umma tace ta bari ya jikin nata. Kafin ta
amsa Umma ta dakatar da ita
"Asmau ki fada min gaskiya meye yake damunki? Ji
yadda fuskarki ta kumbura ga wata tafiya kina yi kamar
me tatata".
A dan tsorace Asmau tace "zamewa nayi a toilet da zanyi
alwala."
Umma ta bita da kallo na rashin gamsuwa.
"To fuskar taki fa? Kinsan bana son boye-boye idan
rigima kuka yi da Abubakar jiya ki fada min tun wuri
ayiwa tufkar hanci."
Murmushi Asmau ta kalalo "Umma lafiya kalau muke.
Kaina ne har yanzu yake ciwo sosai kamar bansha
magani ba".
"Idan anyi breakfast sai Jafar ya kaiki asibiti tunda dai kin
sha magani jiya bai warke ba gara kiga likita sosai. Allah
Ya sauwake. Bari na soya kosan sai kici kiyi wanka."
Jikinta a sanyaye ta fita ta koma daki tayi wanka.
Zuciyarta ta gama raunana amma cigaba da kukan bazai
amfaneta da komai ba sai tonon silili.
Umma kuwa sai tattalinta take yi har daki ta kai mata
abinci tana ta sannu. Wannan ya kara sawa taji ta tsani
kanta. Ji yadda mahaifiyarta ke kula da ita bayan ciwon
nata baya bukatar tausayawa daga kowa.
Sunje asbiti tasha allurai saboda zazzabi sannan aka bata
magunguna.
Da suka koma gida Umma ta sanar da ita Abubakar yazo
amma ya wuce Kaduna ana nemansa akan wasu takardu
da ya kulle a office. Kai kawai Asmau ta gyada ba don ta
yarda ba. Daga dawowarsu zuwa wayewar gari tayi masa
text yafi goma banda waya da ba'a kirgawa. Gani take yi
kawai zai gujeta ne kamar yadda take yawan jin labarai
na samari da suke yaudarar 'yan matansu.
*****
Kafin azahar Abubakar ya isa Kaduna. Jiya ko kadan bai
runtsa ba sau tunani da ya addabi zuciyarsa. Ji yayi
Kanon tayi masa zafi shiyasa ya dawo saboda baya son
yawan tambaya akan me yake damunsa.
Kwanansa biyu da dawowa baya zuwa ko ina daga office
sai gida sai ko masallacin unguwar da yake. Rabonsa da
abincin kirki ma ya manta. Yana kwance ya kurawa fanka
dake juyawa ido wayarsa tayi kara.
Sunan Qasim ya gani shiyasa ya dauka. Qasim ya sanar
dashi wani aiki zai kawo shi garin yanzu zai kamo hanya.
Addua Abubakar yayi masa sannan ya dan gyara dakin
da ko shara baya samu.
Tun zuwan Qasim ya kula da canjawar da abokinsa yayi.
Yayi tambayar har ya gaji babu amsa. To me zai fada
masa?
A nata bangaren Asmau ji take yi kamar tayi hauka. Tayi
wayar har ta gaji. Hawayenta ma ya kafe jira take kawai
azo ace Abubakar ya fasa.
*****
Ranar juma'a da safe Abubakar ya gama shirin tafiya
office Qasim yace
"Karfe nawa zamu tafi Kanon?"
"Wannan satin bazan je ba ayyuka sunyi min yawa"
Abubakar ya bashi amsa.
Kayan da yake sawa a 'yar jakarsa ya ture ya koma
kallonsa "Abubakar nayi nayi ka fada min abinda ke
damunka kaki na rasa dalili. Ni mai sonka ne da alkhairi
idan ka fada min ko addua sai na tayaka".
Kwalla yaji ta cika masa ido ya dan dake "na fada maka
babu komai bari naje na dawo mu tafi. Shikenan ko".
Qasim dai bai gamsu ba. Yana nan zaune aka kawo wuta
ya saka wani CD na wa'azi da ya gani a kusa da tv din
dakin. Ko minti goma ba'ayi da farawa ba Abubakar ya
shigo lokacin shabiyu saura.
Zamansa ke da wuya aka yiwa malamin dake wa'azin
tambaya akan ZINA. Malamin yace
"Lallai zina tana daga cikin manyan kaba'ira da Allah SWT
Yayi hani dasu. Ban da lalacewar zamani yanzu da muka
dauketa ba a bakin komai ba zaka ga yawanci duk
addinin duniya yayi hani da zina saboda muninta da
kazantar dake cikinta. A cikin suratul Furqan ayoyi na 69
zuwa 71 Allah Yana cewa
*WADANDA BASA DAUKAN WANI BAYAN ALLAH A
MATSAYIN UBANGIJI KUMA BASA KASHE RAI BA BISA
SHARI'AH BA, KUMA BASA ZINA WANDA DUK YA AIKATA
HAKA ZAI SAMI ZUNUBI DAIDAI AKIN DA YAYI*.
*ZA'A NINKA MASA AZABAR RANAR ALKIYAMA KUMA ZAI
KASANCE A CIKINTA HAR ABADA*.
*SAI WANDA YA TUBA KUMA YAYI IMANI KUMA YA
AIKATA AIKI MAI KYAU, WADANNAN SUNE ALLAH YAKE
CANZA MUSU ZUNUBANSU ZUWA GA LADA. ALLAH MAI
RAHMA NE MAI JINKAI* Abin duba a nan shine an lissafa
zina da ayyuka masu matukar muni wato shirka da kisan
rai ba tare da hakki na shariah ba"
Haka malamin ya cigaba da janyo ayoyin AlQurani da
hadisan Annabi SAW wadanda suka yi hani da zina ko
azabar dake jiran masu yinta.
Ya kawo aya ta 32 a cikin Sural Isra' wadda Allah
Madaukakin Sarki Ya umarce wadanda suka yi imani da
kada su kusanci zina.
Sai aya ta 2 a cikin suratun Nur wadda Allah SWT Yake
cewa: *MAZINACIYA DA MAZINACI IDAN SUKA YI ZINA
KU BULALI KOWANE DAYA DAGA CIKINSU BULALA DARI.
KADA KUWA WANI TAUSAYI YA KAMAKU GAME DA
TABBATAR DA HUKUNCIN ADDININ ALLAH IDAN KUN
KASANCE KUN BADA GASKIYA GA ALLAH DA RANAR
LAHIRA. KUMA LALLAI NE WATA TAWAGA DAGA
MUMINAI SU HALARCI WURIN YI MUSU HADDIN*
Abubakar da Qasim duk hankalinsu yana ga bayanin
wannan malami. Duk su biyun jikinsu yayi sanyi
musamman Abubakar da yasan abinda ya aika.
Malam mai wa'azi cikin bayaninsa ya kawo hadisin
Bukhari wanda Annabi SAW yake cewa _MAZINACI BA
SHI DA IMANI A LOKACIN DA YAKE AIKATA ZINA...._
Da wani hadisin na Abdullahi ibn Mas'ud wanda yake
cewa _MUN KASANCE TARE DA ANNABI SAW MATASA
MARASA KOMAI NA DUKIYA_. _SAI ANNABI SAW YACE
DAMU_:
_YA KU SAMARI, WANDA YA SAMI IKO A CIKINKU YAYI
AURE DOMIN YAFI AKAN KARE KALLO DA MUTUMCI.
WANDA BAZAI IYA BA SAI YAYI AZUMI SABODA ZAI ZAME
MASA KARIYA._
Kallon kallo ne ya koma tsakanin Abubukar da Qasim a
lokacin da malamin ya soma bayanin lahira da tanadin
da Allah SWT Yayiwa bayi masu biyayya da masu sa6o.
Ya karanto ayoyin Suratul Haaqqa wurin da Allah SWT
Yake fadan irin farincikin da masu aikata aiki nagari zasu
shiga idan sun karbi littafinsu da hannun dama da tanadi
mafi kyau da Yayi musu a aljannah. Da kuma tashin
hankalin ma'abota sabawa Allah a lokacin da suka karbi
nasu littafin da hannun hagu(Ya Allah Kasa bama cikinsu.
Amin) da azabar da zasu tarar.
Duk da Qasim ya shiga tashin hankali da jin wadannan
bayanai saboda abinda yake aikatawa na shafa jikin 'yan
matansa saboda gusar da sha'awa, yayi matukar mamaki
ganin Abubakar ya fashe da kuka. Dafa abokin nasa yayi
yana cewa
"Ba kaine zaka yi kuka ba Abubakar. Ni ne ya kamata
nayi kuka saboda nasan na sabawa Allah sosai. Irin
wannan abin da na fada maka akalla nayi da mata wurin
biyar."
Abubakar ya kalle shi hawaye na kwararo masa." Qasim
nawa sabon yafi naka. Na cuci kaina na aikata zunubin
da bana hangowa kaina komai sai azaba."
A tsorace Qasim ya dago kan Abubakar dake kallon kasa"
ban fahimceka ba, kada dai kace maganarmu ta rannan
tasa kaima kaje kayi romancing wasu. Na shiga uku, ai ni
ne cikin matsala tunda duk wanda yayi umarni da
mummunan aiki yana da zunubi kwatankwacin na
wanda ya aikata kamar yadda yake ga mai umarni da
kyakkyawa".
Dafe kansa kawai yayi yana tunanin wannan sabon
tashin hankali da ya saka kansa a ciki.
Zuciyar Abubakar cike da danasani yace "Qasim zina
nayi"
"What??? Abubakar garin yaya? Da wa?"
Sai da ya hadiyi yawu da kyar ya iya amsawa "Asmau".
Qasim yana girgiza kai yana karanto La haula...
"Marainiyar yarinya, wayyo Abubakar ni ne sila ko? Tun
yaushe ne? Garin yaya ka aikata hakan kai da ka kusa
aure? Idan aka gane fa? Ga mahaifiyarta mutuniyar
kirki."
Tambayoyin da Qasim keyi shima Abubakar din sune
suke masa yawo a kansa. Yana hawaye ya sanar da
Qasim abinda ya faru da irin kunya da bakincikin da ya
sami kansa a ciki. "Yanzu shikenan nima da hannun hagu
zan karbi littafi na ranar lahira. Lallai Annabi SAW yayi
gaskiya da yace a hadisi na hudu cikin arba'una na
Annawawi wanda aka karbo daga Ibn Mas'ud yake cewa
..
_......Hakika dayanku zaiyi ta aikata aiki irin na 'yan
aljannah har sai ya kasance tsakaninsa da ita bai wuce
zira'i ba sai littafinsa ya rinjaye shi sai ya aikata aiki irin
na 'yan wuta sai ya shigeta...._
Qasim ya soma hawaye " in sha Allahu bazamu shiga
wuta ba. Ka manta Allah Yayi alkawarin yafe zunubin
masu tuba.?"
Sai da suka sha kukansu sannan Abubakar ya bawa
Qasim wayarsa ya karanta wasu cikin sakonnin text da
Asmau ta turo masa.
_Yaya Abubakar ka dubi girman Allah ka daga wayata.
Kada ka gujeni a wannan lokacin_
_Idan ka rabu dani rayuwata bazata kara wani amfani ba.
Me zan fadawa duniya nan gaba._
_Kai kadai ne zaka iya taimakona a wannan halin. Ka
daure kada ka fasa aurena._
_Na amince ko washegarin aurenmu ne ka sakeni wallahi
bazan yi korafi ba. Amma yanzu idan ka kini duk wanda
ya aureni zai iya tona min asiri._
Kasa kara karatun Qasim yayi saboda tausayin Asmau da
ya kama shi. Sun dauki wasu mintuna babu mai magana
sai muryar malamin nan kawai suke ji yana kara tsorata
mutane game da aikata zina.
Qasim ya tashi tsaye yana kashe kayan wuta na dakin
dake kunne "ka tashi mu tafi ka bawa yarinyar nan
hakuri sannan mu san yadda zamuyi su Baba su amince
a matso da bikin nan zuwa wata biyu tunda kace mai
hayar naka har ya gama ginin da wuri."
"Kana ganin zasu amince? Wata hudu ya rage da 'yan
kwanaki yanzu nace a maido shi baya?"
"A nawa ganin hakan ne zai kara kwantarwa Asmau da
hankali tasan cewa da gaske bazaka gujeta ba. Wallahi
Abubakar ban taba zaton zamu wayi gari mu ga rana
irin wannan ba. Ba don da bakinka ka fada min ba Allah
bazan taba yarda ba."
Rufe dakin suka yi sannan suka fita zuwa motar
Abubakar. Qasim ne zai tuka su. A hanya suka sami
masallaci sukayi sallar juma'a sannan suka wuce Kano
suna ta tattauna yadda zasu bullowa su Baba domin su
yarda a dawo da bikin baya. Kafin su rabu sai da
Abubakar yasa Qasim yayu masa alkawarin wannan
zancen zai zama sirri a garesu har mutuwa.
*****
Ko gida Abubakar bai shiga ba yana sauke Qasim ya
tashar unguwar kabuga zai wuce Shanono, gidansu
Asmau ya wuce kai tsaye. Lokacin Umma na wurin aiki
ita kuma tana daki tana sana'ar kuka. Ta gama sawa
ranta Abubakar ya gujeta kenan yanzu abinda ya faru
matsalarta ce ita kadai. Jafar ne ya buga mata kofar daki
ya sanar da ita zuwan Abubakar.
A zabure ta tashi ta lulluba mayafi ya rufe mata rabin
fuska ta fita ta same shi a wurin da Umma ke ajiye mota.
Tana zuwa gabansa bata yi la'ari da cewa wani zai iya
ganinsu ba ta zube gwiwoyinta a kasa tana kuka mai
sauti.
"Don Allah Yaya Abubakar kada kace kazo rabuwa dani.
Gara na mutu da in ga ka juya min baya a wannan
yanayin."
Waigawa yayi ya tabbatar babu mai ganinsu sannan yayi
mata alama da ta tashi. Shima hawayen yake shirin yi.
"Asmy kiyi hakuri ki yafe min. Naci amanarki na cutar
dake. Amma ina so kisan cewa bazan gujeki ba. Wannan
tsautsayin ni ne na tilasta miki saboda haka tare zamu
fuskance shi. Idan kin amince zanyi magana a gida a
dawo da bikinmu nan da wata biyu".
Wani hawayen ne ya sakko mata ga dariyar farinciki duk
a lokaci daya.
"Da gaske? Wallahi na amince. Na yarda. Nagode Yaya
Abubakar."
"Ki dena yimin godiya. Ni dake duk bamu fi karfin
kaddara ba. Kuma kowane bawa akwai irin jarabawarsa
a duniya. Dama Annabi SAW yace _Shaidan yana gudu a
jikin mutum kamar yadda jini yake yi._
Kinga ashe bamu fi karfin fadawa tarkonsa ba. Sai dai
Ubangijinmu mai rahma ne da gafara. Idan muka tuba
sai kiga kamar ba'ayi ba."
A sanyaye yake maganar ciki da nadama.
Daga wannan lokacin suka fara azumi da tashi cikin dare
neman gafarar Allah. Yaso samun matsala da su Baba
amma daga baya sun amince an matso da auren. Tun
daga lokacin Asmau take bashi girma fiye da na da, tsoro
take yi kada ta kuskure yace ya fasa asirinta ya tonu.
Haka lokaci ya tafi har zuwa bikinsu da abinda ya faru
bayan nan.
*****
*CIGABAN LABARI*
Asmau ta share hawayenta bayan ta gama bawa Zubaida
labarinta. Ita ma Zubaidan kukan take yi na tausayi ga
bakuwar da kwanansu daya da haduwa amma jininsu ya
hadu.
"Tabbas kinga tashin hankali a rayuwarki Asmau. To
amma abinda ya daure min kai shine yadda kuka tuba
amma duk da haka kika tsinci kanki a irin wannan
rayuwar".
Dan murmushi Asmau tayi "Zubaida kenan, tubanmu ba
shi zai hana faruwar kaddarar rayuwarmu ba. Komai da
kika gani ya faru ga bawa rubutaccen al'amari ne tun
kafin zuwansa duniya. Wani abin yana faruwa ne domin
ya zama darasi ga wasu don su kiyaye. Ni bana bakinciki
da ikon Allah. Nasan bazai barni na tabe ba albarkar
Annabi SAW."
Zubaida ta gyada kai ta gamsu da bayanin Asmau.
"Allah Ya jikan Abubakar"
Asmau tace "Amin " tana share kwalla.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽20
Batul Mamman💖
Wani mugun fitsari ne ya tashi Asmau daf da kiran
assalatu. Ta fito zata je bandaki amma ko ruwan tsarki
bata dashi. Haka ta koma daki tana ta matse shi da
adduar Zubaida ta fito da wuri ko dan yaya ne ta
sammata. Har aka idar da sallah a masallaci Zubaida bata
fito ba. Zuwa lokacin Asmau sai gumi take yi tana cilla
kafa. A hankali taji ya fara zubowa dole ta tafi bandakin
da gudu tayi batare da tayi tsarki ba. Haka ta dawo
dakinta ta shafi kura tayi taimama sannan tayi sallar
asuba.
Batun jin yunwa dama ba'a magana. Wannan yanayin da
ta tsinci kanta a ciki hakurinta ya fara karewa. Ace tayi
fitsari ko ruwan tsarki babu gashi tana gani amma gidan
nafsi nafsi (kowa na ta kansa)kawai ake yi.
Yau Zubaida bacci sosai take yi don har tara ta wuce bata
farka ba. Asmau ta gaji da jiran tsammami ta duba
hijabinta wanda yafi kowanne dauda ta saka ta fita bakin
titi. Ga rana ta kwale haka ta daure zuciyarta ta zauna
duk wanda yazo wucewa tace.
_Sadaka fisabilillah_
Mutumin farko da ya bata naira goma yana yin gaba ta
saka kuka. Wai ita da watanni kadan da suka wuce take
cikin rayuwar jindadi tare da masoyinta da iyayenta, ita
ce take bara tamkar mara galihu. Bara sana'ar da take
tattare da kaskanci da mutuwar zuciya. A ranta addua
take yi Allah Yasa mufi karfin zukatanmu Ya nesanta mu
da kaddara mai muni irin wannan.
Ita kenan ma da tayi nadama amma Allah Ya zabeta don
gwada imaninta da kuma nuna aya ga sauran mutane.
To ina masu aikata zinar duk da sun san laifine amma
basu dauketa a bakin komai ba. A ganinsu suna da
sauran lokaci. Ina masu bada muguwar shawara a baki
ko a rubuce batare da yin la'akari da tasirin da hakan
yake yi a zukata masu rauni ba. Da Abubakar bai tuba ba
shikenan haka mutuwa zata riske shi yana halin sabawa
Mahalicci.
Taci kuka har ta godewa Allah a wurin. Har rana ta take
naira hamsin da biyar ta hada. Ga jiri na dibanta saboda
tsabar yunwa. Tashi tayi ta kama hanyar gidan da yanzu
shine matsuguninta. A hanya ta sayi fanke na naira
hamsin din da pure water guda daya.
Dakinta ta wuce wanda ko jawo kafar batayi ba. To me
zata rufe bayan bata da komai. Fanken nan ta janyo tana
ci hannu baka hannu kwarya. Ko uku bata ci ba sai amai
ya taso mata. Dole ta hakura ta dan jingina da bango
tana adduar kada ya fito don ta dan ji kwarin jikinta.
Ba don tana gudun mutuwar kafirci ba gani take yi a
wannan lokacin gara ta mutu ta huta. Tana jin shigowar
Uwargida ta tashi ta bita daki. Bazata iya cigaba da bara
ba gara kawai tayi abinda zai fishshe ta a nata ganin.
" 'Yar Da6as yau tun safe kina ina?"
Asmau ta dan waiga bayanta tana dube dube.
Uwargida tace "indai Zubaida kike nema na kaita wurin
uwargijiyata a wannan sana'a. Girma ya fara kamani
dolenta ta nema mana kudi. Yaya Babba zata koyar da ita
ta karfin tsiya sannan ta dawo gidan nan ta taimaka
wurin dago darajarsa kamar da."
Tausayin Zubaida ya kama Asmau. Yarinyar da bata
kaunar zaman gidan ma bare sana'arsu ace wai
mahaifiyarta da kanta take son lalata mata rayuwa. Sai
dai babu taimakon da zata iya yi mata yanzu. Kanta a
kasa tace "idan kina da maganin zubar da cikin ki bani".
Wata shewa da tafi Uwargida tayi cike da murna. Tasan
za'a rina. Wannan yanzu idan ta fara bawa Asmau abinci
na sati tuni zata murmure ta fara caskar kudi da ita.
" kin taimaki kanki kuma na tabbatar bazaki yi dana sani
ba muddin kika fara jin jakarki da nauyi. Bari na dauko
miki wani jiko da na bawa Darling kwanaki."
Uwar dakinta ta shige ba jimawa ta fito da wata robar
swan da ta dafe da datti. Ruwan ciki kore ne fatau ga
wasu 'ya'yan ball suna ta shawagi a ciki. Asmau na ganin
robar taji amai na yunkurin fitowa. Toshe bakinta tayi ta
karbi robar ta fita bayan Uwargida tayu mata bayanin
yadda zata sha.
Tun da ta ajiye robar ko kallon wurin bata sake yi ba. A
matsayinta na wadda take da ilimi daidai misali tasan
shan wannan kazantar babbar illah ne gareta.
Washegari wurin karfe goma ta tashi ta shiga cikin
kasuwa. Tasha yawo sannan Allah Ya sa taga abinda take
nema wato chemist(kemis). Daga saman an rubuta
*SADA AND SONS CHEMIST*.
Mutane ne suke ta shige da fice a wurin ta rakube daga
can gefe tana jira suyi sauki ta je ta roki mai kemis din
ko zai taimaka mata da maganin zubar da ciki. Sama da
awa daya bata ga alamun mutanen zasu yi sauki ba har
ta gaji ta soma gyangyadi a gefen wani benci da aka ajiye
a wurin shagon.
Cikin bacci taji an soma kiraye kirayen sallar azahar ta
bude ido tana hamma sannan ta dan kalli kofar shagon
ta ga akwai mutum daya a ciki har yanzu. Daga can nesa
ta hango wani yaro da kayan makaranta da flask din
abinci ya nufo wurin shagon. Ta tashi ta kade jikinta da
niyyar idan ya iso zata roke shi ko ya rage abinci ya bata.
Yana zuwa kuwa ta dan sauke murya.
"Don Allah in ka rage abincin makarantar ka bani in ci".
Yaron da zai kai shekara goma yana da dan jiki ya kalleta
yayi murmushi
"Kwanon abincin makarantana na mayar gida. Wannan
na babanmu ne na kawo masa".
Daga haka ya shige cikin shagon. Ba dadewa suka fito
wurin 'yar rumfar kofar shagon inda bencin yake. Yaron
ya ce "Baba kaga almajirar da tace na bata abincin
naka".
Mal Sada mai kemis ya dan kalli Asmau. Tabbas babu
wanda zai mata wani kallo daban da na almajira. Dogon
mutum ne mai dan haske da kiba. Fuskarsa kadai zata
nuna wa mutum yana da kirki.
Da hannu ya yafito wata mai awara yarinyar ta karaso da
gudunta don kada 'yan talla 'yan uwanta su riga ta zuwa.
Ya zira hannu a aljihu ya dauko naira dari ya mika mata.
"Zuba wa matar nan ta sittin sai ki bata canjin. Abba
miko mata ruwa a cikin fridge dinnan guda biyu."
Mai awara da Abba suka yi yadda Mal Sada ya saka su.
Asmau na karba ta rinka yi masa godiya da fatan alkhairi
sai ka zata ta dade tana sana'ar bara.
Mal Sada ya dan daure fuska "nan ba wurin zaman
almajirai bane kinji ko. Idan kin gama ci ki tafi."
Ta gyada kai ta koma gefe ta zauna. Da ledar ruwa daya
ta wanke hannunta ta fara cin awarar cikin jindadi.
Rabonta da abincin kirki ta kwana biyu. Tana gamawa
tasha ruwa sannan ta dauki daya ledar ruwan tayi alwala
ta shimfida dankwalinta tayi sallah. Lokacin tuni Abba ya
tafi. Sada yana kallonta sai ta burge shi da bara bata
hanata ibada ba.
Bayan ya dawo daga masallaci yana bude shagon kafin
kowa ya shiga ta bi bayansa. Sai kuma kunya ta hanata
fadin abinda ya kawota.
"Kina bukatar wani abu ne?"
Kamar mai rada tace "nawa ne maganin zubar da ciki?"
Cak ya tsaya yana kallonta. Wato ban da bara har jikinta
take sayarwa. Ransa a bace yace "idan baki fice min daga
nan ba ranki zai baci. Ku baro gidajenku kuna bara
saboda mutuwar zuciya karshe almajirai da marasa
zuciya irinku su rinka yi muku ciki. Ko ina dashi bazan
bayarba."
Asmau ta soma kuka tana rokonsa ya taimaka mata.
Daga hannu Sada yayi kamar zai maketa shiyasa ta fita.
Amma a kofar shagon nan ta zauna har taran dare
lokacin

Please Login or Register in order to submit comment