Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya ya hakura sai dai yayi alkawarin
babu mai zuwa gareta idan bata kawo kanta gida ba. A
ciki ma wurin Innarta sai murna da kukan farinciki. Ga
'ya'yanta duk aka taru ana kallonsu. Duk 'yan uwanta
suka taru ana murna. Alhajinsu yayi ta godiya ga su
Umma da suka dawo da ita gida. Zama suka yi ana
jajanta irin wannan hali da yara ke jefa kansu a dalilin
soyayya sun yarda su rabu da kowa.
Asmau da Zulaiha sun zauna suna ta mayar da zancen
halin da suka tsinci kawunansu a ciki. Ta yanke shawarar
nema takardarta a wurin Gidado. Ita da aure kuma sai a
aljanna. Asmau tayi dariya tace "zaki yi ne tunda na sami
miji kema zaki samu in sha Allah" ta bata labarin
Jikamshinta da bikinsu da za'a fara nan da sati biyu.
Zulaiha tace biki kam da ita za'ayi komai in sha Allah.
Ranar ma a gidan Mami suka kwana washegari sai Kano
ta Dabo tumbin giwa. Biki ya gabato ana ta rabon kati
ABINDA AKE GUDU🙆🏽52
Batul Mamman💖
Daga 'yan uwan Asmau har na Col. Ishaq kowa shirin biki
yake yi sosai. Ita har mamaki suke bata. Hala sun manta
wace ce ita suke son yi mata biki irin wannan. Mutanen
da zasu zo karshenta duk 'yan kallo ne wadanda zasu tafi
da ita a baki. Sake yiwa Jikamshi korafi tayi akan haka
yace shi bai taba damuwa da biki ba sai yanzu. Idan suka
yi abin shiru shiru a gida shine mutane zasu sami na
magana ace dama ansan dole ayi abin kamar na marasa
gaskiya. Yanzu kuwa biki zasuyi su nunawa duniya
farincikinsu da ni'imar Allah garesu. Dama tasan tuni
yabi zugar su Shemau da Ainau shiyasa batayi mamakin
amsarsa ba. Kwanansu biyu da dawowa Walida tazo
gidansu har ta rakata karbo dinkunanta na fitar biki.
Kokari suke su ajiye komai su mayar da kawancensu na
da. Bata da niyar gayyatar sauran kawayen makaranta
don basu nemeta ba a baya kuma dama bata dasu da
yawa. Yanzu ma bata san ina yawancinsu suke ba. Duk
wadda tazo bazai wuce bawa ido hakkinsa ba. Dinkuna
sunyi kyau sosai. Kayan Amatullah ma ba'a magana.
Musamman da yake kayan yara akwai daukar ido. Ita da
su Mimin Shemau da Nanan Kawu Garzali mai sunan
Hajjo duk anko akayi musu.
A bangaren gyaran jiki da abinda ya shafi lalle kuwa
takanas Nasiba yayar Abubakar tayiwa aminiyarta ta
Nijar magana. Massouda kenan, matar da a Nijar din ma
ji suke da ita. Taji labarin Asmau kaf a wurin kawarta
kuma ta tausaya mata shiyasa tayi mata hadin kayansu
masu kyau da tsada sosai don tace Asmau dole a gyarata
a saya mata kima a wurin mijinta. Shi kanshi mijin wani
girmansa take gani. Duk mutumin da zai iya auren mace
kamar Asmau lallai ya cancanci yabo da jinjina. Dole a
taya shi da adduar Allah Ya saka masa da alkhairi bisa
wannan kyakkyawan aiki da yayi. A wannan lokacin idan
kaga Asmau zaka so sake kallonta. Duk da dama can ita
bata sahun farare amma fatarta ta kara kyau sosai tayi
haske. Kuma duk wahalar nan ta baya da tasa ta rame
yanzu cima ta canja ga kwanciyar hankali. Shiyasa jikinta
ya dan dawo ta ciko. Idan Umma ta kalleta sai dai tayi
godiya ga Allah. Bata ma so tayi tunanin halin da Asmau
zata fada da bata hadu da mutanen kirki ba ko ta dawo
gida.
A dan tsukun lokacin Col. Ishaq ya damu sosai da rashin
ganin Matarsa. Massoudan Nijar ta saba da irin wannan
aikin na gyaran amare ta taho har gida ta murjeki da
kyau. Saboda haka gidan Umma akayi mata masauki.
Safe, rana, dare daga wannan turaren sai shafa wancan
abin. Sau uku yana zuwa ana ce masa bazata iya fitowa
ba. Ransa a bace a karo na hudu yace da Yassar idan
bata fito ba wallahi bazai tafi ba komai dare.
Yassar yayi murmushi wannan soyayya tana daukar
hankalinsa sosai "ka bani dan lokaci zan fito da ita.
Umma da matar da Anti Nasiba ta kawo ne basa bari ta
fita. Yau kwana biyar ko kafar gidan nan bata fito ba"
Fuskarsa sam babu walwala yace "Ka fadawa matar zan
kara mata kudi amma gobe tayi shirin komawa garinsu
aikin ya isa haka"
Yassar ya kalli yadda yake magana kamar bashi yayi ba
ya wani hade rai. Shi dai ya sosa keya ya tafi. To Col.
Ishaq ba irin wanda zaiyiwa tsiya bane da ya sha tsokana.
Yana komawa dakin Anti Bintu tace "Allah sarki bawan
Allah, ya tafi kuwa?"
"Ya ce komai dare zai jira a gama"
Umma ta dan sha kunu "kaje kace ina wurin ka kasa
fadin sakon, haba yayi hakuri mana. Nan da kwana hudu
za'a fara bikin sai ya ganta. Kema da laifinki da baki fada
masa lokutan da kuke farawa ba"
Asmau ta rufe ido kawai. Ba karamin kewarsa take yi ba
ita kanta. Gashi tasan abubuwa sunyi masa yawa tunda
bikin ya matso amma kullum kokarinsa ya ganta ko yaji
dadi. Sai ake rashin sa'a idan yazo an fara shafe shafe ko
turara mata jiki. Da daga ita sai Massouda ne kawai
yadda suke wasa da matar ficewa zatayi ba'a sani ba.
Amma kullum ba'a rasa babba da take jin kunya.
Har Yassar ya juya Hajjo ta dakatar dashi. Tace a goge
jikin ta fita "gyaran nan ai saboda shi ake yi ko. Kwana
nawa kullum yazo amsa daya ai babu dadi, sai kun sa ta
fita a ransa. Ko dai ku barta ta fita ko kuma naje na kawo
shi har dakin nan muga karshen gyara"
Umma kunya ta kamata ta fice daga dakin su Anti Bintu
suna dariya. Auduga ake tsomawa cikin ruwan wani
humra mai bala'in kamshi ana goge mata jiki. Sai da aka
gama tas ta zura dogon hijab akan rigar jikinta ta fita
don ko kwalliya an hanata sai ranar kamu.
*****
Tayi zaton yana waje sai ta ganshi a falo yana waya ga
Yassar da Amatullah suma suna zaune. Cikin nutsuwa ta
shigo falon Yassar ya dauki Amatullah a wuyansa suka
fice.
Col. Ishaq ko sallama baiyi ba a wayar ya kashe yana
kallonta. Ya ciri tuta a iya kallo mai kashe mata jiki. Ashe
ita ma tayi missing dinsa sosai. Sai yanzu da ta ganshi taji
sauki a ranta. Ko hoda babu a fuskarta kuma iya abinda
yake iya gani kenan amma tayi masa kyau. Ga wani
kamshi mai sanyi da bai san da yadda zai fasalta shi ba
yana fitowa daga jikinta.
Kujeru biyu ne tsakanin wadda ta zauna da tashi ta
gaishe shi amma da kai ya iya amsawa babu magana.
Shirun nasa ya dameta tace "Jikamshina yaya, ko kayi
fushi ne?"
Yayi sassanyar ajiyar zuciya "Matar Jikamshi harda
muryarki ma gyarata ake yi? Tunanin nawa zan karawa
matar da take gyara min ke nake. I just love the way you
look. Matsalata daya ce hanani ganinki da ake yi"
Tayi murmushi "to kayi hakuri kaji _Jikamshina_ .
"Na fada miki idan zan tafi ki dena kirana da sunan nan
amma kinki ji ko?"
Wani kalar tausayi yake mata tayi dariya sannan ta fara
magana da shagwaba "haba Jikamshina yanzu fa na fito.
Ko rabin ganinka banyi ba kake zancen tafiya"
"Kina wasa dani yarinyar nan. Nace ki dena kin cigaba.
Kada kice banyi warning dinki ba dai. Bari na tafi, da na
sani ban matsa sai na ganki ba yau"
Gabanta taji ya fadi ko dai yayi fushi da gaske ne. Tana
ganin ya tashi itama ta mike tsaye jiki a sanyaye tace
"Me yasa kace haka"
Kallon da yake mata na ido cikin ido ne yasa tayi saurin
kawar da kanta. Rage muryarsa yayi yadda itama bata
jinsa sosai batare da ya bar kallonta ba yace "zan fada
miki nan gaba. I love you. Sai da safe"Gabanta taji ya fadi ko dai yayi fushi da gaske ne. Tana
ganin ya tashi itama ta mike tsaye jiki a sanyaye tace
"Me yasa kace haka"
Kallon da yake mata na ido cikin ido ne yasa tayi saurin
kawar da kanta. Rage muryarsa yayi yadda itama bata
jinsa sosai batare da ya bar kallonta ba yace "zan fada
miki nan gaba. I love you. Sai da safe"
Kasa amsa masa tayi tana kallonsa ya fita. Ta koma ciki
duk tana jin babu dadi. To me tayi masa haka da ko
minti shabiyar batayi ba da fitowa ya tafi. Ko dai yayi
fushi ne da gaske? Bazata iya jurewa hakan ba kwanaki
kadan kafin aurensu. Dakinsu ta koma ta dauko wayarta
zata tura masa text don bata son kira yana tuki. Hakuri
zata bashi idan ma tayi laifi ne. Tana dauko wayar ta ga
sakonni a whatsap dinta. Idan ba 'yan gidansu dasu
Rashidan Azare ba babu wanda take chatting dashi sai
Jikamshinta. Budewa tayi zata tura masa text sai taga
nashi ne a sama alamun yanzu ya turo sakon.
_Allah Ya kaimu ranar aurenmu Matar Jikamshi. Ranar
zaki san irin matsayin da Allah Ya baki a zuciyar Ishaq.
Kada ki fassara tafiyata da komai, idan na dade tare dake
*kamshin matar jikamshi zaiyiwa jikamshinta illah* Ji
nayi kamar na tafi dake._
Asmau ta karanta sakon yafi a kirga tana murmushi ita
kadai. Ko a yanzu ace zaiyi mata kishiya ta tabbatar
zuciyarta zata iya bugawa. Duk wannan kalaman nasa da
iya nuna kulawa ace ya nunawa wata matar bata san
inda kishi zaiyi da ita ba. Adduar son kai tayi a zuciyarta.
Allah Yasa Jikamshi nata ne ita kadai....
*****
Washegari da azahar sai ga Zulaiha a Kano ita da su
Humaira, Muhsin da sauran 'ya'yanta. A bakin kofa suka
rungume juna suna tsalle kamar wasu yara ita da
Asmau. Yara na murnar ganin Amatullah. Gida mai dadi
ba Zulaiha ba hatta yaranta sun dan murmure. Kayan
jikinsu kuwa ya isa ya fada maka cewa babanta wani ne.
Don ko gidan Mama da Asmau take yiwa kallon arziki
sosai bai kai na mahaifin Zulaiha ba. Kaddara da rabon
'ya'ya ya kaita auren Gidado. Dreba mahaifinta yasa ya
kawosu tare da kanwarta itama sunanta Asmau suna
kiranta Ma'u.
A tsarin bikin ranar Juma'a za'ayi Kamu da walima
wanda gidan amarya ne suka dauki nauyi. Washegari
asabar a daura aure sannan bayan magriba ayi Sword
Crossing sai kuma ranar lahadi ayi yini a kai amarya.
Yadda su Shemau suka ci burin kawata kamun ayi biki
mai kayatarwa wasu mata suka dauko masu shirya biki
da duk wani abu na bikin kamar abinci da harkar
decoration. Ya da kanwa ne Aisha da Zainab Maiturare.
Tunda suka ji sunan ango har ragin kudi suka yi musu
sun ce ai su kannensa ne wannan biki na yayansu ne
saboda haka zasu zage damtse wurin yin abinda za'a
yaba.
Rashida tazo itama da yaranta da kanwarta Harira. Yaya
Tagwai ma ba'a barta a baya ba. Da ta shigo gidan harda
kukata tana bawa Asmau hakuri da bata tausaya mata ba
ta koreta. Sai a lokacin suka daidaita da Hajjo. Mutanen
Wushishi da amarya Dijah wadda ta kafawa mijinta naci
duk sun zo. Gida kam yayi albarka don ya cika da 'yan
uwa da abokan arziki. Asmau gidan Jafar ta koma ita da
Zulaiha. Rashida tana tare da Zubaida a nata gidan inda
take kula da Uwargida. Sai bayan biki zasu je Jikamshi.
Sabira ce ta kai Asmau wani salon aka gyara mata kai
gashin nan yana ta kyalli sannan aka gyara kafa da
hannu. Ta kalli Sabira tace "yanzu banda iyayi har hannu
ma ana gyara shi. Na zata sai masu saka farce ake yiwa"
"Ummin Amatullah yanzu gyara ai ko'ina ake yiwa.
Matan da ake cewa suna kwacen miji a waje ba wata
tsiya suka fimu ba sai gyaran da rashin kunya. Mu kuma
Hausawa komai sai mu ce Allah Ya sauwake nayi kaza
bayan kuma gidan mijinki kike"
"Kuma fa gaskiya ne, shiyasa naga Yaya Jafar indai abu ya
shafeki wallahi baya kyashi ko kadan. Ashe gyara ne da
sauran sirrikan da zanzo ki bani. Muma Allah Yasa mu
dace"
Suka yi dariya, Sabira tace "ai dacewa dai kin gama.
Wallahi ki rike baban Amatullah tsakani da Allah. Irin
yadda yake sonki kadai ya isa ya nuna miki cewa Allah
Yana jin adduar bayinSa. Abinda ya rage kawai ki bi duk
wata hanyar kyautata masa yasan cewa shima ya auri
mai sonsa."
Ummy mai salon tana mata gyara tana nade shawarar
da Sabira ke bata itama zata gwada a nata gidan.
*****
Ranar da daddare Col. Ishaq ya dawo gida a gajiye
saboda ya tsaya karasa wasu ayyuka kafin hutunsa na
aure ya fara washegari. Har wani aiki za'a turo shi Liberia
ya samu aka bawa wani. Suna magana da Mami da ta iso
a ranar ne yaji waya. A zatonsa Asmau ce don yau aiki
yasha masa kai tun wayar safe bai kara kiranta ba. Da ta
kira ma bai ji ba sai daga baya ya gani ya aika mata da
text.
Bakuwar numba ce ya dauka tare da sallama. Muryar da
yaji ko bata fadi sunanta ba bazai taba mantawa da ita
ba.
Badariyya...
Ko aurenta ya mutu ne????
ABINDA AKE GUDU🙆🏽53
Batul Mamman💖
Amsa sallamar tasa tayi suka gaisa a mutunce. Shiru ya
biyo baya ya katse shi ta hanyar tambayarta ya
maigidanta da danta Nabil. Dan gyaran murya tayi tace
"Uhmm Ishaq dama dazu naje yini gida ne aka bani
katin bikinka. Ashe aure zakayi babu labari"
"Badar kenan, kina gidan mijinki ai bai kamata na kiraki
nace zanyi aure ba. Dama Hajiya tace zata aika cards
nasan zaki ji labari"
Rayuwa kenan, mutumin da suke matukar son juna
gashi yanzu akwai katanga mai karfi tsakaninsu. Tayi dan
murmushi. Wayar ma sai da ta nemi izinin mijinta dama
ta kira saboda kare hakkin aure. Zancen ba'a son ranta
akayi auren ba tuni ya wuce da ta sami ciki.
"Allah Ya sanya alkhairi na bugu inyi maka dama. Sai dai
naji wani labari a gida da ya tada min hankali...."
Katseta yayi wayar ta fara isarsa. Abokai da mutanen da
bai ba sani ba duk sun ishe shi da irin wannan maganar.
Ga kiran Asmau yana ta shiga call waiting.
"Cewa Asmau tana da 'yar da ta haifa babu aure ko?
Haka ne abu daya kawai zakiyi min shine adduar da kika
yi ta Allah Ya sanya alkhairi ki cigaba da yi"
Maganarsa batayi mata dadi ba "idan saboda rashin
haihuwa ne don Allah ka nemi wata mai 'ya'yan. Me
zakayi da wadda ta gama yawonta a gari?"
Runtse ido yayi ransa na kara baci. Haka ce zata yi ta
faruwa kenan ko bayan aurensu. Albakarcin zaman tare
da son da yayi mata a baya ya hana shi fada mata
maganar da zata dade tana mata ciwo a rai.
"Kema kinsan bazanyi aure irin wannan ba. Ina son
Asmau da zuciya daya. Anyway nagode da wayar taki. Ki
gaida mijinki"
Ya katse wayar Mami tace "kayi hakuri Yaya. Nasan bazai
wuce irin maganar da mukayi ba ita ma shi tayi. Sai an
sami mai zurfin tunani ne zai nemi jin ainihin labarin
Asmau kafin ya yanke muku hukunci."
"Gaskiya ne, Allah Ya kyauta. Babu mai iyawa mutane sai
Ubangijin da Ya haliccemu. Komai kayi a wurin mutane
baka iya ba a wurin wasu."
Dakinsa ya tafi ya kira Asmaunsa yana bata hakurin
rashin jinsa da tayi. Dayake tasan yana aiki tace babu
damuwa. Sunyi hira wadda duk akan abinda ya shafi biki
ce sannan ta kwanta.
*****
Ranar Jumaa gidan Umma tun safe ya cika da jama'a
duk da a katin an rubuta ba a gidan za'ayi kamun ba.
Mutane sun rasa daga inda wasu ma suke zuwa. Abin
mamaki sai ga Sagira matar Rabe da 'ya'yansu matan.
Duk ta yamushe rayuwar kauye babu dadi. Umma batayi
zaton zasu zo ba ganin da Asmau ta dawo an aika musu.
Hajjo ce ma ta hana Asmaun zuwa Dakasoyen ta gaishe
da Kawu Raben saboda shima ya dauke musu kafa. Gashi
dai shine da laifi amma yafi kowa fushi.
Su Anti Lami da Yaya Abu duk sun iso da safe da yaransu
har na gidan miji. Abu yayi kyau ko babu komai dai
dangi ba'a canza su.
Lalle aka zauna yi mata ja da baki wanda aka bata lokaci
wurin yinsa. Tasha zama kuwa don 'yan uwanta sun dage
bazata cire da wuri ba sai ya fito sosai yadda za'a jima
ana cin amarci.
Ana idar da sallar jumaa aka fara wanka don gidan
Umma, Mama da na Jafar duk babu masaka tsinke.
Itama Asmau kafin a kira la'asar tayi wankanta mai
kwalliya Najah tazo ya fara aikinta. Fuska ta dauka don
Naja ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi
mugun fentin nan na foundation ba da fuskar mutum
take canzawa gabadayanta. Ana gamawa ta tashi tayi
sallah aka sake gyarawa sannan ta saka kaya. Idan ka
ganta a lokacin bazaka ce Asmau mai wankin bandaki
bace a asibitin Jos. Tayi kyau ba kadan ba. A lokacin
yawancin matan dake gidan sun tafi venue din. Yaya Abu
ce ta kira Zubaida akan lallai su taho da amarya da wuri
mutane sun soma cika a wurin. Ita har mamaki take yi
wasu daga ina suka zo.
Wata mota ango Ishaq ya turo mai kyau ta daukar
amarya zuwa wurin biki. Da suka isa ita da Walida da
Zulaiha ne a motar. Safiyya tazo tace ta zauna domin
ango yana hanya sai ya iso zata fito. Ta saki wani
murmushin jindadi bayan Safiyya ta tafi. Zulaiha ta ce
"Hmm Asmau amare na dan kuka rana irin ta yau sai
fara'a kike yi."
Allah Yasa dreban motar ya fita sai AC da aka ware musu.
Walida tace "baki ga komai ba ita da Col. Ishaq nasu
salon daban yake"
Asmau tayi fari da ido kawai tana murmushi. Motar tasu
mai tint ce ta waje ba'a ganinsu sun jiyo kida daga wurin
bikin yana tashi ga mata suna ta shige da fice. Wurin
cike yake da sojoji masu gadi. Da farko ma taron ba'ayi
niyar yi da maza ba. Sai Mami ta roka akan cewa ango zai
zo da abokansa suyi hoto da amarya ya tafi. Shima da
kyar ya yarda da zuwan. Shemau ce ta fada mata kalar
kayan da amarya zata saka suka yi gaggawar nemawa
ango wanda zai dace.
Bugu zuciyar Asmau ne ya karu da ta hango motar
Jikamshinta. Wurin motoci bakwai ne suka shigo tare.
Wai bikin da akace babu maza kenan. 'Yan kashe
kwarkwarar ido da abokan arziki duk sun biyo shi.
Saitin motar da take Dahiru da ya tuko motarsa ya
daidaita tasu yadda zasu fito tare. Ya hakimce a baya
yana waya. Sai da ya gama ya fito ko'ina ya dauki
kamshi.
Kofar inda take zaune yaje ya bude suka hada ido. Babu
karya ya yarda yana son Matar Jikamshi. Duk abinda
kake so kuwa dole kaga kyaunsa. Indai haka ne Jikamshi
da Asmau sunyi kyau a yau ranar kamunsu. Wani
hadadden lace ne peach a jikinta da ta samu tela yayi
mata dinki na gani a fada. Doguwar riga ce amma tayi
kyau sosai mai dogon hannu. Dankwalin rigar aka hada
da wani yadi mai kyalkyali purple mara turowa akayi
mata dauri. Sai tasa mayafi irin yadin aka makale mata
shi daga tsakiyar daurin nata da pin. Takalminta mai tsini
da jaka duk kalar mayafin ne. Ango ma shaddarsa irin
mayafin nata ce amma fa ba mai kyalli ba. Ga hula har
wani dan karkacewa tayi. Asmau tana gama fitowa aka
fara daukar hotuna kamar me. Safiyya da Shemau ne
masu tsari suka jera su MC din taro S.Kilishi ita ce ta
sanar da shigowar ango da amarya. Suka taho suna taku
daidai. Wuri ya kaure da sowa.
_Qamshi qamshi yana tashi, 'yan mata zamu kamun
amarya_
_Yaune muke shirin kamu...amarya_
_Asmau amarya zo gamu...amarya_
_Ki hakuri da zancenmu, kinsan aure yana kanmu_
Kafin mai wakar ta karaso gaban ango da amarya tuni
'yan mata sun fito ana ta rausayawa. Jajimaji kenan, idan
ta bude baki ko Sangandali sai dai taja baya. Haka ta
cigaba da waka har amarya da ango suka zauna.
Bayan Hajiya YBK ta bude taro da addua aka shiga biki da
gaske. Su Bilkisu da tawagar gidan Hajiya Lubabatu da
'yan Jikamshi ankonsu iri daya ne da nasu Ainau. Ga su
Amatullah yau anyi kwalliya itama ta fito sosai. Yaran su
Shemau da nasu Sadiya 'yan uwan Abubakar kowa fa
yayi kyau.
An bukaci dangin ango su fito fesawa amarya turare sai
gasu mata biyar ne harda Mami kowacce da tsadadden
turare a hannunta suka zo a rinka fesawa. Biki yayi biki
mata sun sha rawa. A cikin taron mata 'yan taya ango da
amarya murna sun gwangwaje. Saboda yawansu ba
sunan kowa zaka iya kamawa ba. Akwai su Maman Afrah,
Tash, Jatma, Zahida, Mrs G, Sadiya Jegal, Ibtihal,
Shukriya, Ummu Rauda, Maman Sadiq, Ummu Aslam,
Mrs Ambursa, Hauwa Ag, Mum Little, Farha, Jammu,
Mardiya, Shafa, Ruqayya, Tafeesu, Ummi BK, Didi, Mjay,
Zahra BB, Biebie Isah, Temseey, Khadija Candy.....(wai
abin da yawa ni mai rubutu naji hannuna zai tsinke nace
wallahi sauran ma duk ina sonku har raina).
Taro kam ya kayatar. Anci an sha an kuma rausaya. Ana
cikin daukar hotuna ne Mama Yalwa tazo zasu dauka ita
da Asmau da ango. Suna hada ido da Asmau suka tuna
abu daya suka fara kuka lokaci guda. Duk wanda yasan
wadannan matan yasan kukan me suke yi. Allah Ya jikan
Abubakar, mutuwarsa ce tasa har aka zo rana irin
wannan. Suna yi ana tayasu har su Umma. Suwaiba
karamar kanwarsa ce ta iya daurewa tana basu baki. Col.
Ishaq duk kishi irin nasa ya dauke kai a yau. Abubakar
wani bangare ne na rayuwar Asmau da bazai gogu ba.
Haka aka kare taron kowa ya tafi gida cikin farinciki da
annashuwa. 'Yan gulma basu sami abin fada ba sai san
barka domin taro ya burge kowa.
*****
Washegari sai shabiyun rana zaa daura aure. Asmau tun
dare ta kasa baccin kirki. Yaushe zata manta ranar
aurenta na farko da ango ya rasu. Ji tayi gabadaya bata
da kuzari har gari ya waye.
Col. Ishaq kuwa jin kansa yake kamar anyi masa wani
albishir mai kyau. Farar shadda ya saka harda babbar
riga. Anyi mata aiki da zare ruwan goro saboda haka
hularsa da takalmi harda agogon hannunsa ruwan goron
ne. Masallacin Hotoro ya dauki jama'a wadanda suke
son shaida wannan babbar rana. Su Jafar da Yassar suna
kan gaba, ga Kawu Garzali da wani abin mamaki Kawu
Rabe yazo yana ta ra6e ra6e. Bisa amincewar Hajjo da
sauran 'yan uwansu Alh Adamu Matawalle shine waliyin
amarya. ASP Qasim ma gayya guda yazo da ita daga
abokan aiki zuwa makusantansa a Shanono. Ga su Sada
suma ba'a barsu a baya ba.
Ango sai faraa yake yana gaisawa da jama'a. Har hoto
suka yi da Qasim suka gaisa a mutunce. Shabiyu nayi
Liman ya bukaci wakilin angon da waliyin amarya. An
daura auren Col. Ishaq Muhammad Jikamshi da Asmau
Shu'aib Yahya akan sadaki dubu sittin.
*****
Asmau na zaune kowa yayi wanka ana ta shirin tafiya
gidan Umma inda zasu zauna saboda baki masu son
ganin amarya. Tamkar wadda aka zarewa laka haka take
jin jikinta. Ga faduwar gaba da ta kwana dashi. Tana
kwance text ya shigo wayarta ta dauka a firgice. Kalma
daya ta gani daga Jikamshi wadda ta saka ta kuka sosai.
*Alhamdulillah.*
Su Sabira suka zuba mata ido har dakin ya fara cika da
su Ainau da Zulaiha suna ta tambayarta me aka yi mata.
Shemau rai a bace tace "ku kyaleta tayi kukan nan. Tun
daren jiya take neman yinsa. Ni nayi mamaki ma da kika
jira sai yanzu. Ace mutum bashi da sana'a sai ta zubar da
hawaye."
Tana kukan tace "Anti Shemau an daura fa"
La'ila ha ilallah....shine abinda Shemau ke fada tana tafa
hannuwa.
"Amaryar zamani da kanta take sanar da aurenta"
Wani hawayen ne ya zubowa Asmau bata ji haushin
yayarta ba tace "na zata shima mutuwa zaiyi, tun jiya
gabana ke faduwa"
Jikin Shemau yayi sanyi bata san abinda ke ran kanwarta
ta ba kenan taje ta rungumeta. Ainau ma ta matso ta
rungumeta suka soma kuka. Sabira da Zulaiha aka bari
da rarrashinsu.
Sai da suka saka Asmau yin nafila godewa Allah sannan
tayi wanka ta shirya suka tafi. Shigarsu gidan ke da wuya
Yassar ya shigo yace ga ango a waje zasu dauki hoto da
amarya. Umma tana cikin mutane ta girgiza kai tana
murmushi. Wannan ango bashi da dama. Bare an daura
aure ai shikenan kuma.
Dakin da suke zaune da su Rashida Mimi taje ta kirawota.
Yawanci sallah masu rakata sukeyi sai ta nemi
takwararta Ma'u ta rakata. Mayafi tasa ta rufe fuska haka
suka fito. Ashe tawaga guda ce domin harda su Jafar da
Qasim. Ita dai duk kunya ta isheta haka akayi hotunan ta
kasa sakewa. Shima bai matsa mata ba. Ko don idon
mutane ya raga mata.
Qasim tun fitowarsu idanunsa suka fada kan Ma'u.
Yarinya ce kyakkyawa suna kama da Zulaiha sosai. Itama
ta kula da kallon da yake mata sai ta sunkuyar da kanta
cike da kunya. A take yaji wani abu a ransa game da ita.
Sun gaisa da Asmau zata shiga ciki ya kalli Col. Ishaq.
"Ango don Allah a bani dama zan roki amarya alfarma.
Ta dan daga kai suka hada ido da Jikamshi yace "bari na
matsa ga mutane can zamu gaisa. Idan kun gama sai
kuyi mana jagora mu dauka dasu Hajjo"
"Godiya nake yallabai, idan tarkona ya kama zan fada
maka don kune masu nema"
Col. Ishaq na matsawa Qasim ya tambayi Asmau game
da Ma'u. Tayi murna sosai ta masa bayani game da ita
harda bashi numbar waya. Tana tafiya wurinta ta fada
mata. Ma'u tayi murmushi kawai. Asmau tace alamun
nasara kenan.
Har cikin falo aka shigo da angwaye aka dauki hotuna da
iyaye da kakanni sannan suka tafi.
*****
Bayan magariba aka shirya tafiya Meena event centre
inda za'ayi Sword Crossing. Wasu sun saba yi ido na
ganin ido amma wannan karon tsarin na dare ne. Fili
suka kama ba hall ba saboda shi zai dace da irin abinda
suka shirya.
Kayan Asmau na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da
kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne
light green sosai. Riga da siket aka yi mata. A bisa
umarnin ango ita da Amatullah suka dinka kayan. Wani
irin dauri Najah mai kwalliya tayi mata da sauran
material din wanda ba'ayiwa shafi ba. Kowa sai cewa
yake tafi jiya yin kyau. Komai da ta saka ya dace da
kayan sai daukar ido take. Amatullah ma Najah sai da
tayi mata kwalliya kada da ta dace da yara aka daukesu
hoto da Umminta. Ana fara tafiya ango yazo daukar
amaryarsa. Drebansa ke jan motar sai wani abokinsa a
gaba. Ko kadan ba haka yaso ba amma wannan tsarin na
Mami ne. Kasa dena kallon

Please Login or Register in order to submit comment