Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma dai meye bazata bari
yayi nisan da zai shiga tsakaninsu iyaye ba. Wayarta ta
dauka ta kirashi. Tayi sa'a yana gida tace yazo tana son
ganinsa.
*****
Dakin Mama yaje ya fada mata Umma na kiransa. Plate
din da take shan kankana ta ture ta tashi.
"Jirani muje tare jiya naji Aina'u tana ta tari. Tun dazu
nake tunanin zuwa duba ta."
Tare suka tafi suna 'yar hira a hanya. Umma taji dadin
ganinsu su biyun. Sun dan taba hira ta kwalawa Asmau
kira.
Tana fitowa da taga Abubakar sai da gabanta ya fadi...ba
dai Umma kiransa tayi akan abinda ta fada ba?
A kasa ta zauna ta gaishe su. Umma ta lura tabbas bai
amsa ba. Kuma bai dade da gama tsokanar Aina'u ba.
Idon Umma akan Asmau tace "dazu da nace kije
Abubakar ya koya miki assignment me kika ce min"?
Cikinta har wani kullewa yayi ta daga kai suka hada ido
ya harareta. Da sauri ta sauke kanta
"Uhmm, uhmm, babu komai".
Mama ta kallesu duk su biyun. Asmau a tsorace,
Abubakar ya hade fuska.
"Ni kun batar dani Umma, me ya faru?"
Umma ta sanar da ita abinda Asmau ta fada da kuma
wanda ta kula dashi a wurin. Duk su biyun Abubakar
suka zubawa ido suna jiran amsarsa.
Dariya suka bashi ya mike tsaye " ni bata yi min komai
ba. Bari na koma gida dama aiki nake yi."
Mama ta daure fuska "kaga abokan wasanka a nan ne,
zauna ka fadi me ya hadaka da kanwarka. Ni bazan
lamunce da gaba cikin 'ya'yana ba. Ku da su Asmau duk
matsayinku daya a wurinmu."
Ita dai Asmau sai satar kallonsa take yi a tsorace.
"Mama kin tuna ranar da na sami attack har na kwanta a
asibiti? Yarinyar nan fa tana cikin masallacin. Na kasa
dauko inhaler a cikin aljihun wandona saboda yadda
nake ji nayi ta nuna mata kuma ta gane wai sai ta fita
kiranki. Da baki zo da wuri ba shikenan fa".
Umma da Mama sai dariya shi kuwa da gaske yaji haushi
ya dubi Asmau itama shi take kallo.
"Da na mutu a lokacin idan ba fatalwa zan rinka yi miki
ba."
Wannan karon itama sai da tayi murmushi ganin ya dan
saki fuska.
Mama ta janyota jikinta "Me yasa baki bashi inhaler din
ba Asmau?"
Idonta ne ya cicciko da hawaye. Umma tace " oh ni
Bara'atu yarinyar nan ko baure bazai nuna mata zuba
ba. Ke baki da aiki sai na kuka daga tambayar fatar baki."
Mama ce ta lallaba Asmau muryarta na rawa ta kalli
Umma.
"Ba cewa kika yi haramun bane mace ta taba namjin da
ba muharraminta ba. Har a islamiyya duk ana fada
mana. Da na taba shi nasan fada zaki yi min sannan a
rubuta min zunubi shiyasa na kira Mama".
A take Abubakar yaji wani irin yanayi game da Asmau.
Shi kan shi yasan bai dace ace yana fushi da ita ba amma
abinda ta fada yasa yaji ta sami wani matsayi a wurinsa.
Ashe abinda tayi, tayi shi ne don bin umarnin addininta.
A yadda yake matashi mai tsantseni wurin addini yana
son mutane masu kiyayewa.
Yanayin kallon da yake mata ya canza zuwa sakin fuska
"dauko littafin muje na koya miki kinji kanwata Idon
kuka."
Sai da suka dara gabadaya sannan Umma tace "Asmau
addinin musulunci yayi mana iyakokin da musulmin
kwarai bai dace ya tsallakesu ba. To amma akwai
sassauci akan abinda ya zama lalura. Kinga a lokacin da
ya sami attack bashi da wani mataimaki sai ke kadai a
wurin. Rashin taimakonsa kuskurene tunda yana cikin
mawuyacin hali. Da ace akwai wani namijin to dama bai
kamata ki taba shi ba. Komai na addininmu yana da
sauki. Duk abinda ya zama lalura wajibi ka taimaki
mutum koda kuwa baki sanshi ba. Ku tashi Allah Yayi
muku albarka".
Shi Abubakar har kunya yaji. Yarinya ta fishi hangen
nesa. Can gefe suka koma a cikin falon wurin wasu
kananan kujeru da dan tebur a tsakaninsu. Littafin ya
karba yace ta dauko text book dinta na P.N Okeke
Mama ce ta bisu da kallo har suka zauna sannan ta
maida hankalinta ga Umma.
"A gaskiya Umma ina yaba miki wurin kokari a
tarbiyantar da yaran nan. A zamanin nan da kananan
yara sun san meye mace ko namiji amma har a irin
wannan yanayin Asmau bata manta da hudubarki ba.
Allah Ya kara taimaka mana wurin basu tarbiya. Shiyasa
nake jinki kamar kanwata ta jini wallahi."
Murmushi kawai Umma tayi.
Mama ta cigaba da magana " inama dai yaran nan su
hada kansu? Wallahi ba karamin dadi zanji ba. Ji nayi
Asmau ta kara shiga raina. Ni daga yau ma ta kwace
matsayin auta Umar."
Wannan karon dariya Umma tayi.
"Anya wannan dan shagwabar zai yarda? Maganarki
kuma akan ita da Abubakar ba tun yau ba nima nake
sha'awar hakan. Allah Ya zaba mana abinda yafi alkhairi."
A can gefe inda suke yin aikin kuwa ko yaya suka hada
ido sai su sakarwa juna murmushi.
Wannan murmushin sai da ya zame musu jiki. Ko
karatun dare suka zo sai Abubakar yayi ta kallon Asmau
har sai sun hada ido anyi murmushin nan. Ita yanzu
kunyarsa take ji sosai. Shi kuma duk irin basarwar nan
tasa da rashin kula mutane indai suka taru suna hira ko a
gidan Mama ko gidan Umma to sai yasan yadda yayi
Asmau tasa baki.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽14
Batul Mamman💖
Kwance tashi babu wuya a wurin Allah. Anyi bikin
Suwaiba da Sadiya lokaci daya. Asmau kuma ana ta
shirin fara WAEC da NECO. Ita kuma Shemau tana aji
uku a jami'a sannan ansa bikinta wata hudu masu zuwa.
Asmau tayi murna don lokacin ta gama jarabawa.
Karatu take yi sosai saboda don cika burinta na zama
likita. Har gidan su Abubakar yaje da laptop dinsa yayi
mata registration din JAMB. Anan ne ya cike mata
medicine a matsayin zabin farko sai pharmacy a zabi na
biyu.
Duk abinda ya shige mata gaba tana tambayarsa ya koya
mata.
Gab da fara jarabar tasu ne posting din su Abubakar ya
fito an tura shi jihar Ebonyi bautar kasa. Da yaje fadawa
Umma yana kula da yadda fuskar Asmau ta nuna rashin
jindadi sosai. Shi kuwa hakan yayi masa don yanzu ya
tabbatar ba shi kadai ne zuciyarsa ta kamu da sonta ba.
Jira yake yi ta kammala makaranta sannan ya fada mata.
Watansa biyu da tafiya watarana tana dawowa daga
makaranta sun gama practical din food and nutrition
yamma tayi sosai wani saurayi ya tareta a hanya. Tunda
ta fito daga makaranta bayan sunyi sallama da Walida
kawarta yake binta a baya. Tsoro ne ya cika mata zuciya
bare da yayi mata sallama ya bukaci ta tsaya. Yana
bayyana mata soyayyarsa tace yayi hakuri tana da mijin
aure har ansa mata rana. Saurayin ya gamsu ya tafi. Ita
kuwa a ranta gani takeyi kamar taci amanar Abubakar ne
ma idan ta tsaya da wani duk da bai taba cewa yana
sonta ba.
Alhamdulillah sun gama jarabawarsu lafiya sai jiran
sakamako. Ranar da ta gama tana dawowa gida Umma
na kitchen ta kwala mata kira. Ko kayan makaranta bata
cire ba taje amsa kiran.
Umma na murmushi tace "Asmau yau an gama
jarabawa ko? To ki dage da addu'a kamar yadda kullum
nake yi muku. Allah Ya bada sa'a Yasa ku gama lafiya."
"Amin Ummana".
"Kije dakina akan gado duk abinda kika gani naki ne na
tayin murnar gama exams. Sauran kyauta sai naga result
mai kyau."
Dadi ya kama Asmau tana ta godiya ta ruga dakin
Umman.
Kwalin waya ta gani akan gadon hannunta har yana rawa
ta dauka tare da yin ihun murna.
Daga kitchen Umma tace "Asmau babu hamdala sai ihu
ko? Kin kyauta."
Dena ihun tayi ta fara godiya ga Allah sannan ta fito falo
wurinsu Jafar. Sun tayata murna Yassar yana rokonta ta
rinka bashi yana yin game. Shema'u da Jafar kayansu
baya tabuwa.
Jafar ya bude kwalin harda sabon sim na mtn. To dama
Umma yanzu ta kara samun matsayi don har mota ta
siya. Masu abu da abinsu. Duk wanda ta sayawa waya
dole yayi sim din mtn.
Suna gama murnarsu ta saka hijab ta fadawa Umma zata
je ta nunawa Mama. Umma tace "babu inda zaki sai kinyi
wanka kin canja kaya. Kin yini da uniform kuma kice
dasu zaki fita?"
Komawa tayi ciki tayi wanka ta canja kaya ta. Tare da
Aina'u da Yassar suka tafi. Umma ta girgiza kai kawai
tana dariya.
Da sallama ta shiga ganin Nasiba tayi a falon da danta
Amir. Asmau ta karasa ta rungume Nasiba tana murna
sannan ta karbi Amir.
"Tun dazu nazo fa, naje munsha hira da Umma tace kina
makaranta. To ya exams din?"
Maimakon amsa wayar ta mikowa Nasiba bakin nan yaki
rufuwa. Ta tayata murna suna duba wayar Mama ta fito
"yau Idon kuka ce take ta murna haka kamar an baki
takardar karatun likita."
"Haba Mama na dena fa. Kinga wayar da Umma ta bani."
"Masha Allah, Allah Ya tsare. A kula sosai don Allah banda
yin abinda bai dace ba kinji ko. Ni zaki fara bawa
numbar kuma" .
Dariya suka yi Umar yazo shima yana nacin a bashi ya
gani. Kamar daga sama aka ziro hannu aka karbe wayar
a hannun Umar. Da sauri tabi hannun da kallo.
Abubakar ne tsaye yana mata wannan murmushin. Yayi
kyau wata uku da rabi da bata ganshi ba har kiba yayi.
Ga gemu dan madaidaici ya tara shi. Fuskarsa sai tayi
mata kyau.
Nasiba ce tayi dan tarin gulma wanda yasa Asmau tayi
firgigit ta dauke idonta daga kansa. Mama sai ta basar
kamar bata gani ba ta tashi ta bar falon.
"Bazaki gaisheni bane?" Ya fada yana zama kusa da yar
uwarsa.
Kunya ta kama Asmau tace "ina wuni?"
"Tunda sai da na roka na yafe. Ni da na taho musamman
saboda tayaki murnar gama makaranta ".
Nasiba ta soma dariya ganin yadda Asmau tayi kamar
ace kyat ta tashi a guje. Mikewa tayi "bari naje na fara
shiri ana magriba Baban Amir yace zai zo daukana."
Aina'u ta kinkimi Amir tabi bayanta. Yassar da Umar ne
suka rage. Abubakar ya dan kallesu "baku da abinyi ne a
ciki kuka tsaya a nan?"
Ba shiri suka tashi suka bi bayan Nasiba. Itama Asmau
tashin tayi zata bisu taji muryar Abubakar yana mata
magana a hankali
"not so fast Mrs A.A Matawalle. Zance zamuyi. Ko kinfi so
nazo gida anjima?"
A kidime take sosai. Tana dago kai ya kashe mata ido
daya.
Yau kuma me ya sami Yaya Abubakar tayi tambayar a
zuciyarta.
"Soyayyarki ce ta sameni Asmy. Kuma nayi missing dinki
da yawa."
Hannu tasa ta rufe bakinta don bata san maganar ta fito
ba. Shi kuwa dariya ta bashi ma. Bata saba ganinsa yana
nishadi kamar haka ba, sai take ganinsa kamar ba wanda
ta sani ba. Duk ya canza.
Ya kula duk bata da nutsuwa kuma shima dai bazai sake
ba a falon gidansu inda ake ta shige da fice.
"Ki koma gida anjima zan zo in sha Allah."
Kanta a kasa tace to ta juya zata fita. A takure take dama
kamar wadda tayiwa sarki karya.
"Asmy..." sabon sunan da ya rada mata taji ya fada. A
hankali ta juyo amma bata iya daga kai ta kalle shi ba.
A tsaye yake shima "dama fuskarki nake son kara gani.
Sai na shigo anjima".
Bata iya yiwa kowa sallama ba ta fita da sauri. Ko
wayarta bata nema ba wadda tana kallo yasa a aljihun
wandonsa.
Har taje gida ta kasa gaskata maganganun Abubakar. Wai
ita ya kira Mrs A.A Matawalle. Murmushi ta saki saboda
sunan yayi dadi. Kai tsaye daki ta shige ta tarar Shema'u
ta dawo daga makaranta.
Itama murna ta fara taya kanwarta ta sannan tace ina
sabuwar wayar ta gani.
Asmau ta danyi yake "Yaya Abubakar ne ya karba zai
duba amma yace zai kawo min anjima."
Shema'u tace to Allah Ya kaimu. Daga nan hira suka
cigaba wadda duk akan shirye shiryen bikin Shema'un
ne.
Sai bayan sallar Isha Abubakar yazo. Dayake ranar babu
karatun dare saboda Malam Hadi ya danyi tafiya.
A falo ya same su suna cin tuwo ita da Aina'u a plate
daya. Yana sallama Asmau ta tsame hannunta don yadda
take jin kunyarsa yanzu ko kallon inda yake ta kasa. Binta
yayi da ido yana murmushi har ta shige kitchen.
Shema'u da Yassar suka yi masa sannu da zuwa ya
tambayi ina Umma. Yassar ne ya kirata suka gaisa tana
tambayarsa ya Ebonyi. Sun sha hira har yake fada mata
bazai koma ba sai bayan bikin Shema'u. Makarantar
secondary aka tura shi service kuma sun yi hutu.
Asmau tunda ta shiga kitchen ta kasa fitowa. Yana ta
kallon hanya yaji shiru. Gajiya yayi ya tashi yayi musu
sallama sannan yace Shema'u tazo zaiyu mata magana.
Wurin da Umma ke ajiye mota suka tsaya ya dan shafi
fuska "nifa wurin Asmau nazo amma na kasa sanarwa
Umma kamar yadda nayi niyya tun a gida."
Dariya Shemau tayi cike da jindadi "Allah Yayi lokaci
yayi. Mun dade muna jiran lokacin nan da zaku dena
satar kallon juna ayi kowa ya sani".
Ya dan daure fuska yana harararta "Ke nifa yayanki ne
kike min dariya. Amma seriously ke da waye 'yan sa
idon?"
"Tabdi, Yaya Abubakar kowa fa ya gano ka tuntuni. Su
Umma ma duk jira suke hasashensu ya zama gaskiya.
Yanzu ma da ka kalli kofar kitchen sai Umma tayi
murmushi."
Kunya yaji sosai "kice kawai na dena zuwa gidan nan. Ga
wayarta ki bata, ni yanzu kunyar ganin Umma nake yi
ma."
Shema'u dai dariya tayi ta masa da tsokana har ya tafi.
Tana shiga gida ta bawa Asmau wayarta sannan ta sanar
da Umma yadda suka yi da shi. Kasa boye farincikinta
tayi saboda sun jima suna jiran hakan ita da Mama.
Asmau ta kira ta bata izinin zata iya tsayawa da Abubakar
tunda ko yanzu za'a iya aurar da ita a shekara shabakwai.
Sannan ta ja mata kunne sosai game da kare mutumci
duk da dai ta yaba da tarbiyar Abubakar.
Asmau kamar ta shige kasa don kunya wai ita Umma ke
yiwa nasihar fara zance. Bayan ta koma daki missed calls
ta gani da numba an sa _Mine_. Duk tunaninta tasan
batayi saving numbar kowa da wannan sunan ba. Tana
kallon wayar aka sake bugowa ta dauka. Muryarsa taji
mai dadin sauraro musamman idan yana karatu. Ya ce
"My Asmy"
A hankali tayi magana "Yaya Abubakar?"
"Sunan da kika gani kenan da aka kira ki?"
"A'a" ta amsa tana dan murmushi
"Wane suna kika gani?"
Lallai ma Yaya Abubakar so yake ta fadi sunan da ta gani
yaji dadin cewa tayi rashin kunya. Shiru tayi har kusan
minti biyu babu wanda yayi magana.
Ya numfasa har tana jin sautin "idan na dameki ne bari
na ajiye wayar."
Da sauri ta ce ba damunta yayi ba.
"To ki fadi sunan da kika gani don shi kadai zan rinka
amsawa daga gareki idan har kin yarda nan gaba kadan
ki zama matata."
Wani irin dadi taji yana ratsa zuciyarta. Bata taba sanin
soyayya ba sai akansa. Muryarta kamar mai rada yaji ta
ja kalmar
"Mine"
Ji yayi kamar yafi kowa nishadi a wannan lokacin. Bai ja
ta da hira sosai ba sai dai duk abinda ya fada mai
tsayawa ne a rai. Da suka yi sallama wata hirarsu ta tuna
da Walida inda take ce mata babu wanda ya kai ustazai
wadanda suka koshi da boko kuma suka dauki koyarwar
Al'Qurani da hadisi a matsayin jagoran rayuwarsu iya
soyayya. Kafin tayi bacci yayi mata text ya kai biyar duk
na kalamai masu ratsa zuciya.
Cikin dan lokaci kowa ya san soyayyar Abubakar da
Asmau. Mama ta kara nuna mata so tamkar 'yar cikinta.
Duka gidajen biyu babu wanda alakarsu bata burge shi.
Ya zauna a Kano har akayi bikin Shema'u da sati daya
sannan ya koma Ebonyi. Waya kam shi da Asmau kullum
ne sai sunyi. Soyayya suke yi mai tsafta saboda dukkansu
sun fito daga gidan tarbiya. A can garin ma shine Amir
din Muslim Students' Society (MSS) dinsu suna kiransa
Young Ustaz.
*****
Admission ya fito Asmau bata sami medicine ba sai
pharmacy. Abubakar yace ta karba ta godewa Allah
domin zabinSa a kodayaushe shine alkhairi. Haka kowa
tayi registaration dinta tayi sa'a Walida ma shi aka bata
saboda haka kullum suna tare.
Yana dawowa Abdulhalim yayi aure Mama tace gidan
nata duk ya daye saura su biyu shi da Umar. Shima aiki
yake nema ido rufe saboda a fara maganar aurensa da
Asmau. Baba yayi musu gini duk su uku mazan a wuri
daya gate ne ya rabasu. Amma yace daga nan kuma
mutum ya nemi aiki ko sana'a sannan a fara batun aure.
Itama Umma a nata bangaren sai siyan kaya take tana
ajiyewa kada biki ya tashi batayi tanadi sosai ba. Da bikin
Shema'u dangin babansu na nesa sune suka bata
gudummawa. Hajjo da 'ya'yanta da suke makusantansu
babu abinda sukayi mata. Daurin aure dai Alh Rabe ne ya
karbi sadaki...su Rabe an zama Alhaji sakamakon
kujerar Makkah da shugabar kamfanin da yake aiki Haj
Rufaida ta biya masa. Shiyasa wannan karon Umma ta
kara dagewa don fita kunya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽9
Batul Mamman💖
Mal Yahaya dakansa ya rinka yiwa Hajjo fada amma ta
takura Bara'atu. Lokacin Shua'aibu yaje gyaran gidan da
zasu koma a Zaria. Yana dawowa ya tarar da mahaifinsa
a kwance shine suka kaishi asibiti shi da Rabe. Likita ya
duba shi aka ce malaria ke damunsa. Magunguna kawai
aka rubuta suka dawo gida.
A tsakar gida Hajjo tayiwa mijinta shimfida suka kwantar
dashi yana shan iska shi kuma Shu'aibu ya tafi siyan
magani. Fitarsa keda wuya Rabe ya karasa kusa da Hajjo
yace
"Hajjo likitan fa yace basu gane kan cutar dake damun
Baba ba. Idan bakiyi wani abu ba duk sai mayun nan sun
cinye mu."
Hankalin Hajjo ya kara tashi. Rabe yaji dadin hakan.
Bashi da burin da ya wuce asa dan uwansa ya saki
Bara'atu shi kuma ya aura. Tun farkon haduwarsu yaji
yana sonta. Duk wasu alamu ya nuna mata inda tayi
masa tatas shine ya koma zuga Hajjo suna muzguna
mata. A dalilin bata son hadashi da dan uwansa ne yasa
bata tona masa asiri ba tunda dama babu mai kaunarta
sai mijinta. Ko ta fada kila bazasu yarda ba.
A fusace Hajjo tace "Bara'atu fito nan muguwa mai
mugun nufi".
Bara'atu tana kitchen ta fito da sauri ta durkusa. Lokacin
bacci ya fara daukar Baba amma hayaniyar Hajjo tasa ya
farka.
Sai da ta gama harararta sannan ta dubi Rabe "fita ka
nemo min abokanka majiya karfi koda biyu ne"
Murmushin mugunta yayiwa Bara'atu sannan ya fita. Ba
jimawa suka dawo su uku. Hajjo ta tashi ta nuna musu
Bara'atu da Bintu "gasu nan, so nake ku sa su tsallake
Malam sau bakwai ko na samu su saki kurwarsa. Bari
naje na debo garwashi na kunna turaren mayu."
Bara'atu tayi matukar razana ta soma rokon Hajjo tayi
hakuri. Ko kallonsu bata sake yi ba tayi gaba abinta tana
masifa. Ganin haka yasa ta kama hannun Bintu zasu
shiga daki su rufe Rabe ya fizgota. Suna ihu da kuka ya
rike Bara'atu wani kato ya daga Bintu yana tsallaka
Malam Yahaya da ita a kafadarsa.
Mal Yahaya jiki babu kwari ya kasa tashi sai daga kwance
yake kokarin yi musu magana amma babu mai
sauraronsa.
Bayan sun gama da Bintu suka ajiyeta sannan Rabe da
dayan suka kama hannu da kafafun Bara'atu suna
shillata ta saman Malam. Kuka dai tayi har muryarta ta
dashe. A karo na biyar da shilla ta da suke yi Shu'aibu
yayi sallama ya shigo.
Abinda da ya ga kaninsa yana yiwa matarsa yasa yaji
wani mugun daci a wuya. Shi kanshi Rabe ba karamin
tsorata yayi ba suka yar da Bara'atu yayi ciki inda Hajjo
take tahowa da kasko fal garwashi.
Ko tunanin daga Bara'atu, Shu'aibu baiyi ba. Kan Rabe
yayi da gudu ya damko shi. Dukansa yake kamar ba
jininsa ba yana zaginsa. Hajjo tayi iya kokarinta amma
bai sake shi ba sai da ya gaji don kansa ya koma ya daga
matarsa yana haki.
Hajjo ta durkusa ta daga Rabe. Baki da hancinsa duk jini.
Rai a bace tace " yanzu saboda wannan yarinyar kayiwa
dan uwanka irin wannan dukan? Meye laifinsa don yana
son ceto rayuwar mahaifinsa. Kuma ni na saka shi".
"Yanzu saboda Allah Hajjo ko Bara'atu ba matata bace
abinda akayi mata yayi daidai kenan? Duk abinda akeyi
ina dauke kai darajar Baba amma na rantse duk wanda
ya sake shiga sabgar iyalina sai hukuma ce zata raba
mu."
Da hannu Mal Yahaya yayi masa alama ya durkusa a
gabansa. Hakuri baban nasu ya sake bashi da alkawarin
idan yaji sauki zai dauki mataki.
Bayan kwana uku ciwonsa ya kara tsanani suka je wani
asibitin aka ce typoid ce taci hanjinsa ma. Dama irin
abinda ake gudu kenan. A kai mutum asibiti babu gwaji
su hau dirka masa magani. Washegari Malam Yahaya ya
cika. Iyalinsa sun sha kuka sosai. Bayan wata daya
Shu'aibu ya hada nasa iyalin suka koma Zaria. Hajjo dai
ta kullaci Bara'atu don ta yarda dari bisa dari su suka
kama Malam.
Tunda suka koma Zaria suke samun budi. Bara'atu har
kiba ta soma yi kuma ya samar mata gurbin karatu a
ABU Zaria tana karanta Public Administration. Duk sati
Shu'aibu yake zuwa Kano amma baya tafiya dasu. Da tayi
magana yace babu amfani tunda ba kaunarta sukeyi ba.
Itama Hajjon don neman magana ta tambayeshi yace
hakan ya fiye musu kwanciyar hankali.
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah. Shekara bata
zagayo ba Bara'atu ta haifi Shema'u. Danginsu na
Wushishi sun zo sosai tunda mijinta yana bari taje ganin
gida. Daga Kano ma su Yaya Abu sun zo sai dai ba'a rabu
lafiya ba.
Bayan shekara daya da rabi ta haifi Jafar sannan Asmau.
Shu'aibu yana kula dasu sosai. A lokacin Bintu ta gama
secondary akayi bikinta.
Haka suke zamansu lafiya ga jari ya bawa Bara'atu tana
sayar da kayan sawa na mata a cikin gida. Sai lokacin
sallah kawai suke zuwa Kano ko idan wani abu ya faru.
Basu da wata matsala a lokacin. Asmau nada shekara
hudu aka haifi Yassar.
Wata rana da yamma Shu'aibu yana zaune a falo tare da
iyalinsa Rabe ya zo. Shi da matarsa ne Laraba da yaransa
biyu. Baraatu bata nuna wata damuwa ba tayi musu
tarba mai kyau. Laraba mace ce mai mutumci shiyasa
basu dauki lokaci ba suka saba a dan zuwan da suke yi
Kano.
A can falo kuma Rabe yake sanar da yayansa yazo ne
zasu dan kwana biyu shi da iyalinsa. Ko kadan Shu'aibu
bai so hakan ba sai dai ya kyale yaga iya gudun ruwansa.
Shiru basu da niyar tafiya ita kanta Laraba har kunya
take ji. A sati na uku Shu'aibu ya dawo daga makaranta
zai shiga dakinsa yaji muryar Rabe yana rokon Bara'atu
da ta amince masa wannan zuwan ma duk nata ne.
Daga murya tayi tana fada tace cikin kuka "idan baka fita
ba sai nayi maka tonon asirin da bazaka kara mutumci
ba a duniya. Matarka fa tana gidan nan. Ko don kaga
tuntuni ina rufa maka asiri?"
Murya kasa kasa yace "ki amince Bara ko ba a gidan nan
ba. Ni sau daya ma kawai ya isheni. Ki taimaka."
Ihu ta kurma a tsorace ganin yayo kanta Shu'aibu ya
bude kofar ya shigo. Yau ma iya karfinsa yasa yana duka
Rabe. Abu yayi tsanani har Laraba ta jiyo su ta fito.
Korarsu yayi a yamman yace ya fice masa daga gida.
Laraba na fahimtar abinda ke faruwa ta tattara ko
jiransa batayi ba ta kwashi yaranta suka tafi. Shu'aibu
yayi kukan bakinciki sosai sannan yayi mata fadan rashin
sanar dashi da wuri.
Washegari da safe yace mata zai je Kano ayi maganar a
gaban Hajjo don yasan Rabe yanzu yanzu zai juya zance.
Haka kuwa akayi Hajjo tace sai ya saki Bara'atu ko ta
tsine masa. Jiya Rabe ya dawo gidan jina-jina saboda
sharrin data kulla masa. Duk yadda Shu'aibu yayi Hajjo
taki yarda. Laraba ma data bada shaida akan Rabe a take
Hajjo tasa ya saketa.
A kan hanyarsa ta komawa ne Shu'aibu yayi hatsari.
Bacin rai ne ke damunsa saboda Hajjo tace idan har bai
saki Bara'atu ba sai dai ya sake wata uwar.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽10
Batul Mamman💖
www.fikrahwriters.blogspot.com
Bara'atu ta gama girkinta tayi wanka sannan tayiwa
yaranta. Albishir gareta ga maigidanta idan ya dawo
wanda take tunanin zai rage masa bacin rai. Ciki ne da ita
har wata biyu. Dayake ranar babu islamiyya su Jafar sai
wasansu suke yi a gida.
Sallamar maza taji a kofar gidan ta dauki mayafi ta fita.
Ga mamakinta har da 'yan sanda biyu. A tsorace ta gaisa
da su sannan guda cikin 'yan sandan ya miko mata ID
card ko ta gane wanda yake jiki.
Tana ganin hoton jikinta ya fara rawa "ku fada min
abinda ya same shi"
Wani mutum a gefe yace "Hajiya sai dai hakuri a hanyar
shiga gari muka ga motarsa yayi hatsari. Allah Yayi masa
rasuwa".
Kuka Bara'atu ta saka har yaranta suka fito. Ganin
Ummansu na kuka suma suka fara. Bare Shemau da
Jafar masu wayo sosai.
Cikin dan kankanin lokaci sauran abokan aikinsa suka zo.
Bintu da mijinta ma duk sun zo da makotansu. Karfe uku
suka kama hanyar Kano.
Basu tsaya ko'ina ba sai kofar gidan Marigayi Mal Yahaya
a unguwar kofar mazugal. Hajjo tayi kuka sosai na
rasuwar danta sai fadin irin halinsa na hakuri da kawaici
take yi. A nan aka yi masa sutura aka kaishi.
Bara'atu duk ta rame a cikin 'yan kwanakin nan saboda
tashin hankali. Saukinta daya shine canjin data gani a
tattare da Hajjo. Mutuwar ta daketa sosai shiyasa duk
tayi sanyi. Sabanin yadda ta saba yanzu tana jan su
Shemau a jiki. A da kuwa sai dai tace su dena kallonta da
kwala-kwalan idanunsu na mayu.
Bayan sati biyu da rasuwar gabadaya 'ya'yan Hajjo suka
taru da Kawun Bara'atu tare da wani malami da Rabe ya
kira akan rabon gado. Kafin malamin ya fara jawabi
Bara'atu ta sanar dasu cewa tana da ciki.
Ran Rabe yayi matukar baci ita kuwa Hajjo abin yayi
mata dadi. Dole aka hakura da rabon gado sai ta haihu.
Da amincewar Hajjo ta koma Zaria saboda makarantar
yara. Tausayin Bara'atu ne kawai ya kamata tun bayan
rasuwar Shu'aibu.
Bayan wata shida ta haifi 'yarta mace Hajjo da kanta ta
zaba mata suna Aina'u. Yarinyar duk tafi sauran 'yan
uwanta kama da mahaifinsu shiyasa ta shiga ran Hajjo
sosai. Kano suka dawo lokacin kafin tayi arbain. Kwana
goma da haihuwar Bara'atu Rabe ya sake dawowa da
Malamin rabon gado. An gabatar masa da dukkan
kadarar Shu'aibu wanda ya hada da motarsa guda daya
da kuma makeken gida da ya gama ginawa a unguwar
Hotoro sai 'yan kudade a banki da kuma wanda wurin
aikinsu suka bawa iyalinsa sai kuma wata gona a Zaria.
Malam ya gyara zama
"Tunda mamacin yana da 'ya'ya da mata sannan
mahaifiyarsa tana da rai duk 'yan uwansa basu da gadon
shi."
Rabe yaji kamar an kwada masa

Please Login or Register in order to submit comment