Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shima da ya
gaji fita kawai yayi daga dakin.
Likita yazo ya sake duba Asmau ya tabbatar musu cewa
zasu iya tafiya da ita gida. A haka suka tafi ko da suka iso
gate din gidansu Abubakar da yake shine a farko kafin
nasu wani kukan ta sake fashewa dashi. Mutanen da suka
zo daurin aure sun koma zaman makoki. Duk a nan suka
sauka suka shiga gidan. Gaban Asmau sai faduwa yake
balle da taji ana cewa ga amaryar nan ta shigo. Mutane
da dama suka taso ana kallonta. Kowa na fadin
albarkacin bakinsa na dangane da tausayawa gareta.
Bayan sun shiga gidan dakin Mama aka wuce da ita. Ko
zama batayi ba Umma tace mata taje tayi alwala saboda
batayi azahar da la'asar ba. Jiki kamar wadda bata da
laka haka ta shiga bandakin jiri na dibarta ta dauro
alwala tazo ta biya sallolin dake kanta. Tana sallar tana
zubar da hawaye. Bayan ta idar ta dade tana kuka da
addu'a.
Sadiya ta hado mata tea mai zafi ta mika mata. Kai ta
girgiza alamun bazata ta karba ba.
Kusa da ita Sadiyan ta zauna " ki daure ki sha ko yaya ne
sai kici abinci. Kowa da kika gani dauriya kawai yake yi
Asmau." Nata hawayen ta share sannan ta dubi Shema'u
tace "Anti Shema'u kisa baki ta sha ko kadan ne".
Taruwa akayi ana lallabata tasha tea din amma taki har
Umma da Mama suka dawo daga waje inda suka karbi
gaisuwar wasu maza 'yan unguwar. Suma suka saka baki
har Asmau ta karbi tea din. Bai fi rabin kofi tasha ba ta
fara kwara amai saboda tun jiya rabonta da abinci. Haka
ta rinka amai ta baki ta hanci abin tausayi.
Ta galabaita sosai. Bayan ta gama aman Nasiba ta dagata
zata shiga da ita bandaki ta gyara jikinta ta fadi kasa a
sume. Nan da nan aka taru a kanta ana mata fifita. Aka
shafa mata ruwa a fuska tare da sauke mata zip din
rigarta don tasha iska amma duk da haka bata tashi ba.
Mama tace aje a kirawo mata Baba a waje. Ita Umma
gefe kawai ta koma tana kuka. Gani take yi kamar
Asmaun ma ta cika.
Shi da wasu suka shigo suka ga halin da Asmau ke ciki.
Jafar aka kira da Abdulhalim suka sakata a mota aka
kaita wani asibitin mafi kusa dasu. Su Mama suka biyosu
a wata motar kowa bakinsa da addu'a.
Bayan an bata gado wata likita da nurse suka zo suka
tsaya a kanta ana ta kokarin ceto rayuwarta. Allurai kala
kala kam tasha su. Likitar tace jininta ne ya hau ga kuma
rashin kuzari a tare da ita. Gwajin jini ta umarci ayi mata
don su gani ko akwai wani ciwon a tare da ita.
Har wani likitan ne yazo suka taru ana ta abu daya
sannan suka samu ta farfado. Su Umma sai godiya suke
ga Allah. Mama na zaune a kusa da Asmau tana sake bata
baki akan tayi hakuri kuma duk da ana mata karin ruwa
ta daure taci abinci sai ga nurse din ta shigo.
Shema'u ta tashi da kyar Anti Bintu tace " kema kina
bukatar hutu tun dazu baki zauna ba. Kada kafarki ta
kumbura". Murmushi Shema'u tayi sannan ta tambayi
nurse din tana fata babu wata matsala a tare da Asmau.
Nurse Ngozi ta washe baki cikin hausarta irin da
inyamuran da suka zauna a Kano tace "babu wani
masala sai abin murna...." ta mayar da kallonta ga
Asmau "...congratulations ashe ciki ne yana baka
wahala."
Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da
yake motsi na wani dan lokaci har maganar nurse Ngozi
ta gama shiga kwakwalwarsu.
ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ4
Batul Mamman๐Ÿ’–
Kallon kallo suka fara yiwa juna. A wannan lokacin da
za'a sake auna jinin Asma'u ba karamin hawa ya sake yi
ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki.
Mama ce tayi karfin halin kallon Ngozi tace" 'yar jakar
uba bakinki ne cikin ai, dama Hausa bata gama zama ba
dole kiyi shirme. Bari likitan tazo da kanta muji daga
bakinta. Kila ma ciwon ciki kike son cewa kika ce ciki zaki
karasa tsorata mu."
Nurse Ngozi tace "Madam ina jin Hausa sosai fa.
Yarinyarki is pregnant zata haihu shine abinda nake
nufi."
Takardar hannunta Umma ta fizga tana karantawa jikinta
ya hau rawa. Shema'u ta karbi takardar suka hada kai ita
da Nasiba da Anti Bintu suka karanta. Gabadayansu
Asmau suka zubawa ido da tsantsar mamaki a
fuskokinsu. Mama dake tsaye a gefe ta zaro ido tana
tambayarsu me suka gani a takardar.
Jafar ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan inda
Abdulhalim yake tsaye tana masa bayanin magungunan
da aka rubutawa Asmau. Kamar wanda aka jeho haka ya
shiga office din ransa ya gama baci. Abdulhalim ya
tambaye shi ko jikin Asma'un ne. Jafar yace "ai gara ace
jikinta ne da abinda mahaukaciyar nurse dinnan ta
rubuta. Wai ciki? Asma'u ke da ciki kamar a tatsuniya...."
likitar ya kalla "...ki taso muje ki sake gwadata don kada
ku karasa gawar da ba taku ba."
A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya
cinye mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi
jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ta
karbi report din daga hannun Nasiba ta karanta. Ita ma
abin ya bata mamaki domin kuwa Abdulhalim yayi mata
bayanin dalilin suman Asmau. Ta bukaci kowa ya fita
suka fice babu musu. Sirinji ta dauko daga aljihun rigar
asibitinta ta sake daukar jinin Asmau. Bayan ta gama
tace "Asmau yaushe ne lokaci na karshe da kika ga
al'adarki?"
Tun dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da
take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan
tambayar. Hankali a tashi tace " biyu ga watan da ya
wuce na gama".
"Yanzu kuma gashi ana karshen wata na gabansa. Yau
kinga ashirin da takwas ga wata." Likitan ta fada tana
rubutu a wata takarda. Fuskarta na kan takardar tace " ki
fada min gaskiya kin taba tarayya da namiji?"
Kasa bada amsa tayi sai jikinta da ya kara mugun yin
sanyi. Fatan mutuwa kawai take yi akan bala'in da yake
tunkaro ta. Da taki magana likitan ta fita su Umma suka
dawo har yanzu babu mai cewa uffan kowa zuciyarsa na
sake-sake. A haka likitar ta dawo kana ganin fuskarta
kasan labarin da ta kawo bashi da dadi. Ita kanta ta
tausayawa mutanen ta dan sunkuyar da kai "a bisa
binciken da nayi da kuma amsar da Asmau ta bani ya
nuna tana da CIKI na kusan wata biyu."
La haula wala quwwata illa billah....a rana daya duk wani
farincikin gidajen biyu ya koma kishiyarsa. Umma tayi
kan Asmau wadda dama tasan haka zata faru.
"Asmau me nayi miki zaki yi min muguwar sakayya irin
wannan? Uban waye yayi miki ciki? Har kinsan ki kebe da
namiji ba tare da aure ba a tsakaninku?" Tana magana
tana dukan Asmau ko ta ina. Su Anti Bintu ne suka yi
kokarin riketa tana fada tana kuka.
Shema'u ma gefe ta koma tana nata kukan. Wane irin
abin kunya ne wannan Asmau ta janyo musu a wannan
halin da suke ciki?
Umma na dukanta duk da rashin lafiyar da take ciki
amma ta kasa yin kuka. Biyewa son zuciya na 'yan
mintuna ya wargaza dukkan wani farinciki da ta taba
sani a rayuwarta. Irin ABINDA AKE GUDU kenan. Yau
asirinta ya gama tonuwa. Sirrin boye ya fito fili bata da
abinyi sai yadda Allah Yayi da ita. Mama ta rike hannun
Umma da take shirin sake dukan Asmau "ba da duka
zamu tambayeta ba Bara'atu. Kada ki bari bacin rai yasa
kiyi aikin dana sani."
Muryar Umma har ta dashe tace "akwai wani dana sani
daya wuce haihuwar wannan yarinyar? Fyade aka yi miki
ko kwaya kika sha da har zaki yarda da namijin da ba
naki ba?"
A hankali Asmau ta sakko daga kan gadon har allurar da
ake yi mata karin ruwa ta fita daga hannunta bata sani
ba jini ya rinka zuba daga hannun. Ranar wanka ba'a
boyon cibi. Sai a lokacin ta soma kuka ta durkusa akan
gwiwoyinta a gabansu Umma.
"Tsautayi ne da sharrin shaidan. Don girman Allah ku
yafe mana. Wallahi sau daya ne kawai. Idan har ina da
ciki na Abubakar ne".
Cikin tsawa Mama tace "kin ma isa ki dora masa. Wallahi
nasan karya kike yi saboda kinga kasa ta rufe masa ido
shine zakiyi masa irin wannan mummunan kazafi?"
Magana take tana haki saboda bacin rai, sai kuma
hawaye.
"Yanzu kinyi masa adalci kenan? Ko kwana baiyi a
kabarinsa ba kike binsa da mummunar shaida bayan
kinsan mala'iku suna tsayawa karbar shaida akan
mamaci. Allah Ya isa tsakanina dake. Har yaushe kika ga
Abubakar din ma? Mutumin da sau biyu yake zuwa Kano
a wata. A can makarantarku dai kika hadu da wanda yayi
miki"
Anti Bintu ta kama hannun Asmau ta tayar da ita tsaye
cikin jin haushin maganar Mama gashi Umma taki cewa
komai "wannan magana bata asibiti bace. Mu bari idan
an sallameta sai ayi a gida. Amma kowa yasan bata da
wani saurayi bayan Abubakar."
"Babu wata magana da zamuyi a gida. Kai, ku wuce mu
tafi." ta fadawa Abdulhalim da Nasiba. Dukkaninsu an
rasa mai bakin magana. Tabbas Abubakar ne kadai
saurayin Asmau. To amma kowa yayi shaidarsa wurin
kyaun hali. Mutum ne mai kawaici da kunya. Ita kanta
Asma'un ba don a gabansu aka yi komai ba sai su
karyata saboda itama ko 'yan unguwa zasu shaideta da
kyaun hali.
Abdulhalim yaso ya tsaya domin a kare maganar a nan
Mama ta daka masa tsawa dole yabi bayanta suka fita
tana ta bambami. Bude kofar dakin kenan suka hadu da
mata sun kai shabiyar daga gidan rasuwar suke sun taho
jin halin da Asmau take ciki. Kana ganinsu kasan duk
abinda ake yi a cikin dakin sun gama ji. Mama ko kallo
basu isheta ba tayi gaba su Nasiba na bin bayanta. Matan
dai tunda har an gansu dakin suka shiga suna tambayar
ya mai jiki. Anti Bintu tace da sauki suka tashi ko minti
daya cikakke basu yi ba suka fice ana ta mayar da zance.
Bayan fitarsu Anti Bintu tace "Yaya Bara baki ce komai ba
kina jin abinda Maman Abubakar take fada."
"Me zance Bintu? Kin taba ganin cikin shege yayi uba kai
tsaye a kasar musulmi? Duk abinda Mama Yalwa ta fada
tayi min daidai. Nima da namijin ne nawa bazan yarda a
kakaba masa cikin shege ba." Hada ido suka yi da Asmau
Umma ta sakar mata wani mugun kallo. Abinda yafi
wannan ma tasan zata gani tunda haka ta faru. Kusa da
Umman ta dawo ta sake durkusawa a kasa ga wani irin
jiri da take ji, kirjinta kuma kamar ana hura wuta.
"Umma ki yafe min. Wallahi sharrin shaidan ne kuma
muna ta istigifari kullum. Wallahi bazan kara ba wannan
ma kaddara ce. Umma...."
Ture ta Umma tayi ta dubi inda Shema'u da Jafar suke
tsaye suna hawaye "Jafar fita ka samar mana abin hawa
mu koma gida."
"Asma'un fa?" Anti Bintu ta tambaya. Tamkar da dutse
tayi maganar haka Umma ta shareta. Bayan Jafar ya
dawo Umma ta rike hannun Shema'u saboda kafarta
data rike suka yi hanyar fita. Asmau na ganin haka ta
tashi tabi bayansu Anti Bintu na kiranta bata tsaya ba.
Haka suka fice daga asibitin ga dare suka shiga tasi din da
Jafar ya tsayar. Har suka isa gida babu mai magana a
cikinsu.
Abin mamaki nasu gidan a cike suka same shi bayan
tunda aka yi rasuwar aka koma gidansu Abubakar. Bacin
ran Umma ya sake karuwa don tasan labari ya riga ya
iske duka umguwar. Sai cewa akeyi ya jikin Asmau. Aka
rasa me amsa musu tunda sun san ainihin abinda ya
kawo su.
A cikin falo Umma zata wuce dakinta taji ance "Ke
Bara'atu dakata." Ta gane muryar mai maganar ta san ba
karamin rashin mutumci yazo yi mata ba. Alh Rabe ne
kanin marigayi. Kin tsayawa tayi sai da taji muryar Hajjo
mahaifiyar maigidanta sannan ta juyo. Kuka ne ya kwace
mata yadda taga duk 'yan uwan mijinta a wurin
mazansu da matansu ga kuma mahaifiyarsu. Allah Yasa
itama akwai nata 'yan uwan wadanda suka zo biki daga
Wushishi ta jihar Niger. Dangin mijinta basu taba
kaunarta ba gashi Asmau ta sake shafa mata kashin kaza.
Jafar ya juya ya matan dake binsu kamar jela yace duk
su fita. Surutai da gunaguni suka rinka yi har suka watse.
Aina'u da Yasar ma yace duk su tashi. Yasar baiso hakan
ba a ganinsa shima ya girma ransa a bace ya tura Aina'u
suka shige ciki.
Kowa a zaune banda Asmau dake rakube a jikin kofa. Alh
Rabe ya zare mata ido "munafuka algumguma ai sai kizo
ki zauna kin wani tsaya mana a ka kamar sa'anninki."
Da sauri ta zube a wurin da take tsaye ta dukar da kanta
hawaye na kwarara a kumatunta. Hajjo ta furzar da
goron bakinta a kan kafet tace "hankalinki ya kwanta ko
Bara'atu? 'Yarki ta janyo mana abin kunya ta bata mana
suna a gari. Tun rasuwar Shu'aibu babu yadda bamuyi
dake ba akan ki bari 'yan uwansa su raba 'ya'yan a
tsakaninsu kika ki amincewa. Yau wa gari ya waya
uhmm? Dama tarbiyar mace mai zaman kanta har wata
tarbiya ce." Hanci ta tsaya fyacewa tana kukan Bara'atu
ta cuce ta.
Umma tayi shiru kawai, tun dazu da aka aika musu da
rasuwar Abubakar babu wanda yazo cikinsu. Yinin bikin
ma cewa suka yi tayi a gidanta suma zasuyi nasu ko babu
amarya. Sai yanzu da wannan abu ya faru shine duk suka
taho. Harda Yaya Abu da babu abinda ta halarta na bikin
wai tana ciwon wuya.
Alh Rabe ya doka tsaki "dama me kike tsammani daga
mace irin wannan Hajjo? Saboda na taimaki rayuwar
'ya'yan dan uwana fa har shahada nayi nace zan aureta
duk da yadda nake kyamar mayu 'yan garinsu amma
taki. Yanzu ta fada muku shegen da ya dirka mata cikin
ko kuwa saboda samarin sunyi mata yawa bata san waye
uban ba?"
A kufale Jafar yace "Kawu nayi tunanin zama akayi na
maslaha akan matsalar nan ba bakaken maganganu ba."
Umma ta watsa masa harara don yayi shiru amma duk
da haka sai da Yaya Abu ta hado masa ashar ta kunduma
masa. Sannan ta dubi Asmau "to karuwar cikin gida
wadda ake nuna mana kunfi kowa tarbiya. Cikin na waye
don ko ni ban yarda na yaron nan bane Abubakar bawan
Allah. Gara da Yalwa taki karba zaku gurbata musu asali."
Jin batayi magana ba har Hajjo ma ta sake tambaya yasa
Kawu Rabe yayi kanta yana haurinta da kafa. Tun tana
zaune har sai da tayi kasa yana tattaka ta. 'Yan uwan
Umma suka tashi aka rike shi sannan suka janyeta.
Umma dai sai kukan zuci. Duk abinda aka yi musu a yau
Asmau ce ta janyo mata saboda haka bata da bakin
magana. Kallonsu take yi suka ci gaba da caba musu
bakaken maganganu 'yan uwanta suna karewa sannan
suka tashi. Hajjo tace "ki shirya sati mai zuwa ki turo min
Yasar da Aina'u gara nasa su a gabana don bazan bari
zuri'ar Shu'aibu ta gama lalacewa ba ina raye.
Ranar gidan Umma ansha kuka kala kala. Shema'u duk
yadda suke da kanwarta ko inda take taki kallo. Asmau ta
bata kunya sosai. Anyi ta tambayarta kuma taki magana
tunda sunki yarda cikin Abubakar ne. Abu dai har tsakar
dare suna dakin Umma ana ta magana daya. Asma'u
kuwa babu wanda ya shigo dakinta. Kawayenta da suke
gidan gabadayansu bata san inda suke ba har da
aminiyarta Walida wadda take ganin kamar bazata
gujeta ba a wannan yanayin.
ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ5
Batul Mamman๐Ÿ’–
Zaune take kan abin sallah tana addu'a tana zubar da
hawaye. Bata taba tsammanin ganin rana makamanciyar
wannan ba a rayuwarta. Babu Abubakar ga cikinsa a
jikinta batare da aure ba. Yau da cikin aure ne bata san
irin soyayya da gatan da Umma da Mama Yalwa zasu
nuna mata ba. Ashe haka ake ganin bambancin rayuwar
wadda aka shafa fatiha akanta da wadda ba'a shafa ba?
Gashi dai duk abu daya suka yi, amma mai aure sai ta
zama tauraruwa har idan batayi ciki ba ayi ta korafi ko
aji tausayinta. Ita gashi kuskure sau daya tak, tayi cikin
da bata bukata gashi hatta mahaifiyarta tana nuna mata
kyama. Aure ibada ne, zina kazanta ce. Wani kukan ne
yazo mata da taji cikinta na kukan yunwa. Yanzu idan
taci abinci abinda ke cikinta ma zai samu? A hankali ta
shafi cikin zuciyarta na kuna.
"Wayyo Allah, Ya Allah Ka jikan Abubakar Ka karbi
tubanmu" abinda ta fada kenan cikin raunanniyar
muryar da ta gama dashewa don kuka. Akan abin sallar
bacci ya saceta tana rungume da AlQur'ani.
Gari na wayewa ta rinka jin muryarsu Umma a kitchen
ana dafa abincin da ta fuskanci na sadaka ne da za'a kai
gidan Kwamishina. Tana son fita amma tana tsoron
abinda zai biyo baya. Duk wannan tashin hankalin wata
muguwar yunwa take ji sai dai ko zata mutu bazata fita
neman abinci ba.
Sai wurin karfe goma taji gidan ya danyi shiru. Tana nan
zaune Anti Bintu ta shigo dakin. Itama dai ba sakin fuska
tayi ba, ta shigo dauke da plate din abinci da ledar pure
water. A gaban Asmau ta ajiye ta juya ko gaisuwar da
take mata bata amsa ba.
Sai da ta fita ta fashe da kuka. Rana daya Asma'u ta zabge
idanu sunyi ciki kamar ta shekara a kwance. Tana jin
tausayinta sai dai dole a nuna mata kuskurenta. Abincin
da ta kai mata ma babu wanda yasan ta kai. Kuka tayi
sosai sannan tabi bayansu Umma da suka riga suka tafi
gidan rasuwar.
Su Umma zasu shiga gidan taji Mama Yalwa tana cewa
alajirin da ya kawo abincin ya mayar musu da abincinsu
bata so. Dama tasan tun faruwar al'amarin jiya dole
Mama ta canja mata. Sai dai mutuwa ta kori komai
shiyasa ta daure tazo. Sallama tayi suka shiga sai tayi
kamar bata ji abinda Mama ke fada ba. Itama kunyar
ganin Umman tayi sai ta bar gaban kulolin abincin. Haka
suka gaisa kowa fuskarsa a cunkushe su Umma suka
sami wuri suka zauna. Babu mai cewa komai dama gidan
rasuwa ne. Mutane 'yan kallo suka taru suka zuba musu
ido.
Haka ce ta kasance kullum Umma zatayi abincin sadaka
kuma su je gidan su zauna sai anyi la'asar su koma gida.
Tsakaninsu da Asmau kuwa ko kallonta batayi duk da
tana fitowa ta gaisheta. A rana ta shida ne da daddare
wata dattijuwa cikin 'yan uwan Umma tace ya kamata su
zauna suyi magana akan lamarin Asmau.
Umma tace "kayya dai Gwaggo, me ya rage mana kuma
banda zubewar mutumci."
Gwaggo tayi dan murmushi "Bara'atu nayi tunanin ke
mace ce mai hangen nesa da tawakkali. Me kike
tsammani ga yarinyar da take cikin yanayi na Asmau ace
kowa ya juya mata baya? Idan abin ya isheta dole tayi
tunanin nemawa kanta mafita koda kuwa mafitar halaka
ce fiye da halin da take ciki yanzu. A 'yan kwanakin nan
duk wanda ya kalleta yasan tana cikin damuwa kuma
muna fatan ta yi nadama. Kamata yayi a sake
tambayarta lallai ta fadi gaskiya game da cikin sai a san
matakin dauka."
Kowa a dakin yayi na'am da shawarar. Shema'u dama
mijinta yayi mata fada akan rashin kula Asmau da suke
yi ba shine mafita ba. Umma tace aje a kirawo Asma'un.
Gabanta na faduwa ta shiga dakin kowa ya zuba mata
ido. A can gefe ta zauna idonta a kasa.
Anti Bintu tace " Asmau ki dubi girman Allah da halin da
kike ciki ki fada mana gaskiya game da cikin jikinki."
Kai a sunkuye ta sake nanata musu cewa na Abubakar
ne. Ran Umma a bace tace ta tashi ta fita. Ji take inama
Asmau tace fin karfi aka yi mata. Da ta tausaya mata
amma da jin bayaninta kasan abin ba haka bane.
Shawara aka yanke jibi bayan anyi kwana bakwai da
rasuwar suje su sanar da iyayen Abubakar. Haka kuwa
akayi. Da yawan 'yan bikin sun koma Wushishi sai kadan
suka rage saboda abinda ya faru. Babu wanda ya sake
zuwa daga gidan Hajjo dama basu sa a ka ba.
Umma da Anti Bintu suka je sai Gwaggonsu da Asmau.
Mama na ganinsu ta hade rai Umma ta daure ta bukaci
ganinsu ita da Alh Adamu.
Harda Abdulhalim da Nasiba suka zauna a falon. Gwaggo
ta gabatar musu da dalilin zuwansu.
Alh Adamu yayi gyaran murya ya soma magana "duk
wannan bayanin naji shi tun a ranar da Abubakar ya
rasu. Ina sane nayi shiru har sai an share makoki. Bazan
boye miki ba Haj Bara'atu wannan labari yayi matukar
muni garemu baki daya. Sai dai kuma tsakani da Allah
wanda ake abin a kansa yanzu baya raye. Maganar
Asmau kadai bazata sa mu karbi cikin jikinta a matsayin
nasa ba. Yau da yana nan ne sai ya karba ko ya kare
kansa."
Tunda ya fara magana Umma ta soma zubar da hawaye..
" Alhaji duk mun shaida Asmau babu wanda take
sauraro sai Abubakar. Idan kuka gujemu a wannan
lokacin bansan inda zanyi ba. Dangin babansu dama ba
kaunar mu suke yi ba, kune dai a garin nan kuka tsaya
mana tamkar 'yan uwa....."
Mama ta katseta "maganar 'yan uwantaka da cikin shege
fa bata taso ba. Kamar yadda Baba ya fada da Abubakar
yana raye sai muji ta bakinsa. Amma babu yadda za'ayi
mu karbi cikin nan kawai don Asmau tace nasa ne."
"To a bari ta haihu mana sai a gwada a tabbatar da
zancenta." Abdulhalim ya fada yana kallon Asmau. Shi
tausayinta yake ji.
Mama tace " zanci mutuncinka wallahi. Idan an bari ta
haihu ya dace da dan uwanka zaka karba ka rike ne?
Shashasha tashi ka fita."
Baba yace "ina zaunen kike irin wannan abin Yalwa?..."
ya juya ga su Umma
"kiyi hakuri Haj Bara'atu amma babu yadda zamuyi
saboda babu kwakkwarar shaida. Idan har kina bukatar
taimako kinsan ni mai taimaka miki ne kodayaushe."
Yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki Mama tabi bayansa.
Nasiba ma ta tashi babu wata magana da suka ji mai
dadi.
Umma da Asmau sun sha kuka. Suka tashi suka tafi gida
jiki babu kwari. Asmau tana tausayin halin da ta jefa
mahaifiyarta. Suna zuwa gida hawan jinin Umma ya
tashi aka kaita asibiti. Kuka dai yaki karewa a gidan.
Kuma aka ki tafiya da Asma'un asibitin. Sai bayan isha
suka dawo Yasar yazo dakinsu Asmau ya kirata fuskarsa
babu walwala. Tana tashi yayi mata wani kallon banza "
idan kika kashe mana Umma wallahi sai nayi miki abinda
baki taba tsammani ba. "
A razane ta kalli yaron da ta bawa shekara hudu wanda
tsakaninta dashi kullum girmamawa ce. Indai Yasar zaiyi
mata haka kowa ma dole ya tsaneta. A sanyaye tabi
bayansa.
Yanayin da taga Umma ya bata tausayi sosai tace "Umma
yaya jikin?"
Maimakon ta amsa sai tace "munyi magana da wata
ma'aikaciyar asibiti tace gobe mu kaiki karfe goma na
safe a cire cikin".
A tsorace Asmau ta mike tsaye tana kuka "Umma kada
zunubin yayi min yawa. Ga laifin ciki ga na kisa. Don
Allah ki janye..."
Saukar mari taji mai zafi a kumatunta daga Jafar, marin
bai gama shigarta ba yace
"banza ana son taimakonki zakiyi mana shirme. Waye zai
sake kallonki idan aka bari kika haihu? Dubi yadda kika
tarwatsa mana gida Asmau. Ki bari a cire indai ba kuma
neman karasa zubar mana da kima kike son yi ba."
Shema'u ta taso ta rike kafadar Asmau
"cire cikin nan shi kadai ne maslaha garemu baki daya.
Waye zai dauki dawainiyarki data abinda zaki haifa? Haba
Asmau, ki bari muji da bakinciki daya mana."
"Ku kyaleta ta nuna min iyakata. Asmau da kinsan irin
radadin da nake ji a zuciyata da baki soma bude baki ba
ma. Wallahi nayi nadamar haihuwarki, ina ma barinki
nayi tun kafin ki zama mutum da dai naga irin wannan
bakar ranar a dalilinki." Umma ta fada kuka mai sauti.
Hankalin Asmau ya sake tashi sosai da jin abinda Umma
dake matukar kaunar 'ya'yanta take fada yanzu.
Durkusawa tayi a gabanta tana ta kuka da rokon ta yafe
mata. Anti Bintu mai jin tausayinta tace ta fita ta basu
wuri. Tana bakin kofar taji Jafar yana cewa ko ta karfin
tsiya sai sun kaita asibitin ko a kira likitan har gida a cire.
Umma dai bata sake magana ba amma sauran sun
amince. Har Gwaggo na cewa akwai wasu saiwoyi da
basu fada a asibitin ba sai tasa a kawo daga Wushishi a
bata tasha cikin zai zube.
Kasa tsayuwa tayi a bakin kofar ta koma daki. Ita da
Abubakar sunyi kuskure babba amma tabbas zubar da
cikin nan karin laifi ne. A yadda ta janyowa gidansu
bacin suna a duniya bazata so ta zama silar karin zunubi
a garesu ba a lahira. Da wannan tunanin ta janyo akwati
daya cikin na lefenta ta hada 'yan kayayakinta ta zuba a
ciki. Dan kudin da ta samu na biki da dan sauran
kudinta ta saka a jakar hannu mai girma sannan ta ciro
wasu sarka ,dankunne da awarwaron daga wata drawer
duk ta saka a ciki tare da wasu kayan kala uku. Ko kadan
bata runtsa ba a daren. Asubar fari Jafar da Yassar suka
bude gate suka tafi masallaci. Suna fita Asmau ta lallaba
ta fice daga gidan tayi hanyar titi.
ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ6
Batul Mamman๐Ÿ’–
Ta tsakanin gidaje ta rinka bi don kada ta hadu da idon
sani idan an idar da sallar asuba sun fito daga masallaci.
Ta jima tana tafiya zuciyarta cike da fargaba. Ba ita ta iso
titi ba sai da hasken rana ya fara bayyana. Jefi-jefi
ababen hawa suke wucewa don ma titin nasu na hotoro
wurin wucewar matafiya ne. Kusa da wani kanti da yake
rufe ta shimfida dankwalinta tayi sallah sannan ta koma
titi ta tare dan sahu.
Mutumin ya kare mata kallo sama da kasa sannan yayi
magana
"Hajiya ina zuwa?"
"Tasha zaka kaini." Ta amsa masa tana kara rungume
jakarta da akwati.
"Garin Kano kuma mai tasha da yawa sai ki fadi wadda
zaki je"
Sai da ta danyi tunani ta tuno sunan tasha daya
" kaini ta unguwa uku, nawa zan baka?"
Yadda dreban dan sahun ya kula ta matsu ta shiga yace
"kawo dari biyu tunda kinga yanzu safiya ce sosai"
Babu musu ta zuba kayanta ta shige tana kare rufe
fuskarta da hijabinta.
Sai da ta sauka ta fara rarraba idanu domin ko kadan
bata san inda zata je ba. Ummanta 'yar Niger state ce to
amma tasan zuwa yanzu duk 'yan uwanta sun gama jin
labarin komai, idan taje wurinsu ba ta tsira ba. Tana
cikin wannan tunanin taji ana cewa,
"Azare mutum daya
Azare mutum daya"
Ko dogon tunani

Please Login or Register in order to submit comment