Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farincikinsa.
Hajiya tace "to sarkin surutu. Ke da tace kada ki fada
masa sai da ya ganta kika fasa kwan saboda kina murna
mamanki zata zo ko?"
Bilkisu ta turo baki "kai Hajiya nifa ba haka nake nufi ba"
Col. Ishaq yace "Hajiyar tawa kike turawa baki. To na
mayar da goron albishir din banji abinda kika fada ba"
Tashi tayi ta bar dakin tana buga kafa yana mata dariya.
Ya juya ga Hajiya cikin murna "gara tazo taga yayarta
kuma kanwarta"
Mami ita ce 'yar Haj Lubabatu ta biyu. Shekara daya da
rabi Col. Ishaq ya bata. Ba karamin shakuwa suka yi ba
kamar ba sako da sako ba. Komai nasu tare suke yi.
Hatta zancen Asmau ya fada mata ya sami wadda yake
so amma sai tazo Kano ko shi yaje Jos din zasuyi
maganar sosai. Ita kanta murna da doki ya isheta saboda
ta matsu yayi aure. Tun bayan rabuwarsu da Badariyya
bata kara jin yayi zancen mace ba sai yanzu.
******
Washegari litinin su Asmau sun kwana a asibiti. Da
sassafe Umar yazo ya kai Mama gida ta yi wanka sai ya
taho da Ainau ta taya Asmau zama. Ko goma bata yi ba
suka ji sallamar Col. Ishaq. Asmau na jin muryarsa taji
wani irin dadi a ranta. Soyayyarta da Jikamshi kullum
jinta take sabuwa. Cikin khakinsa yake na sojoji yayi
kyau ta bishi da ido a lokacin da yake shafa kan
Amatullah dake kwance tana bacci. Ya amsa gaisuwar
Ainau sannan ya juya yana kallon Asmau. Saurin
sunkuyar da kai tayi tana jin kunyara tan cigaba da yiwa
Husna dake hannunwa wasa. Bai dauke idonsa daga
kanta ba yace
"Ainau dake ake shirin kai Matar Jikamshi gidan wani?"
Ainau ta zaro ido "wallahi babban yaya nima har kuka na
tayaka. Ba don kada kuga wautata ba sai nace asthmar
Amatullah tayi min daidai."
Wani wawan dundu Asmau ta kai mata harda harara.
Ainau tace "ba fa har raina naso ciwon ba." Ta dan juya "
kaga tana hararata ko"
Col. Ishaq ya karbi Husna daga hannun Asmau yana
dariya "nima harararki nayi a zuciya. Ya zaki ce asthma
tayi. Duk da dai na dauketa a matsayin tazo hanawa a
raba Jikamshi da matarsa"
Irin kallon da yake yiwa Asmau yana wani lumshe ido
yasa Ainau jin kunyar kasancewa a wurin. Sai murmushi
suke yiwa juna. A ranta tace ba dole Yaya Asmau taso shi
ba. Shi kuwa Yaya Qasim bata ga alamar ya iya nunawa
mace soyayya ba. "Allah Ya baku hakuri to. zan fadawa
Baba Amatullah ta warke ko gobe Yaya Qasim ya kawo
kudi"
"Kinga kina jego shiyasa nake tausayinki. Idan aka aura
mata wani ranar zaki kwana a guardroom don nasan
adduarki ce taci" Col Ishaq ya fada suka yi dariya sannan
ya yiwa Asmau alama da ta biyo shi.
Sai da suka je bakin motarsa yace "Matar Jikamshi kin
tashi lafiya, ya jikin princess dina?"
Tana kallon kasa saboda kunyar tunowa da yadda jiya ta
nuna masa tana sonsa tace "lafiya kalau Alhamdulillah"
"Yau 'yan kunyar sun zo ne zasu hana ace min I love
you" ya karashe maganar yana kwaikwayonta.
Bata san lokacin da ta soma dariya ba yace "jiya duk
bana cikin hayyacina ne sosai nima bance miki Matar
Jikamshi ina sonki ba. Amma yanzu na fada. Zan wuce
office sai an taso zan dawo ko kuma bayan magrib. Ki
kular min da matata da 'yata"
"Allah Ya tsare Ya bada sa'a kuma Ya kareka daga dukkan
sharri"
Kasa bude motar yayi ya kalleta "Matar Jikamshi"
"Naam Jikamshi _na_"
Yana murmushin jin dadi yace "komai naki ina sonsa, ki
rinka yi min adduar nan kullum don Allah. Kuma idan
zamu rabu ki kada ki rinka kirana Jikamshina. Sawa kike
naji kamar kada na tafi"
Tayi dariya ta sake cewa "Jikamshina"
Ya dan marairaice mata "don Allah ki bari"
Ta sake bude baki zata maimaita tana dariya yace "kina
fada zan wuce wurin Umma na fada mata irin kalaman
da kike yi min wanda yasa nake so a daura mana aure a
yau dinnan"
Ba shiri ta rufe bakinta. Ko dai bai fadi hakan ba tasan zai
iya kwatantawa. Dan gefe ta matsa ya shiga motar ya
dago mata hannu sannan yaja ya tafi.
Ciki ta koma Ainau tana yi mata tsiyar yadda duk su
biyun yanzu basa iya boye sirrin zukatansu a gaban juna.
Sai shabiyu su Umma suka zo ita da Hajjo da Mama. A
nan suka yini don likita yace sallama sai gobe idan
numfashin Amatullah ya daidaita yadda ake so"
*****
Daga wurin aiki gida Col. Ishaq ya wuce. Bazai iya zuwa
wurin Asmau ba sai yayi wanka ya canza kaya. Idan
Mami ta iso kuma su je da ita dasu Hajiya.
Tun a waje yaga motoci a cikin gidan na kannensa da
wata da yake tunanin a cikinta aka kawo Mami. Hakan ya
bashi tabbacin yau duk sun zo a tare. Mara motar dama
daya ce mai bin auta. Dadi yaji saboda yawanci suna
zuwa ne kafin ya taso aiki basu fiye haduwa ba. Ya shiga
falon yaji shiru sai daga dakin Hajiya yaji ana magana
ana daga murya. Karasawa yayi kofar dakin ya tsaya
yana karewa 'yan uwansa kallo.
Mami ke binsa sai Ismail, Dahiru, Safiyya da auta
Musaddiq.
Mami ce take magana cikin matsanancin bacin rai harda
hawaye a idonta "wallahi tallahi Hajiya bazamu yarda
Yaya ya bata mana suna ba."
Ismail yace "meye na rantsuwa Mami, kema kinsan babu
mai zuwa cikin su Kawu nema masa aurenta. Idan basu
san karuwa bace yarinyar ni...."
Tsawa mai karfi Col. Ishaq ya daka masa. Duk sai da suka
razana don sun san halinsa sarai. Kirjinsa ke bugu da
sauri da sauri saboda bacin rai "ko da wasa kada ka kara
kuskuren kiranta da wannan sunan"
Safiyya tace "ayi hakuri Yaya, Sayyada zamu kirata ko
ustaziyya?"
Dariya suka yi dukkansu banda Hajiya ta sha kunu "ban
taraku a nan don ku zagi Asmau ba. Yarinyar nan
kaddara ce ta fada mata wadda babu wanda ta wuce ta a
cikinku. Kuma ni ba amincewarku na nema ba. Na dai
fada muku tana da 'ya ne saboda bana son kananan
zance nan gaba"
Musaddiq yace "haba Hajiya wannan ai ba zancen da ya
kamata Yaya zo dashi bane ki karba. 'Yar shege da
uwarta bazasu sami karbuwa ba a danginmu."
Col. Ishaq yayi kansa ya cakumi wuyansa yana huci.
Musaddiq sai kakari yake yi don wahala. Hajiya tana ta
cewa ya sake shi amma yaki. Cikin zafin rai yace
"Musaddiq kada ka kaini bango. Dukkanku nan babu
zaman wanda nake yi. Idan na aureta don Allah kada
wanda yazo gidana."
"Dama waye zai zo" Safiyya ta fada cikin tsiwa. Ya juyo
kama ya mareta.
Daga nan suka tararwa yayansu ana ta musayar magana.
Hajiya taji babu dadi saboda yaranta akwai hadin kai.
Yau daya sai fadawa juna magana suke yi akan Asmau.
Ita da tayi laifi shekarun baya amma a yau sanadiyar
wannan kuskuren 'yan uwa duka magidanta suna fada.
Col. Ishaq yace "an fada muku duk matar da ta haihu ko
tayi ciki a waje karuwa ce jikinta ta sayar.?"
"Yaya ka fada mana gaskiya fyade aka mata ko me? Ni
wallahi gara ka auri gurguwa da wannan yarinyar. Kila
ma asiri tayi maka duk ka kasa fahimtar mu " cewar
Mami
Yau duka 'yan uwan nasa haushinsu yake ji "ba fyade aka
yi mata ba Mami. Idan su basu fahimce ni ba yakamata
ace kin gane inda na dosa."
"Tausayinta kake ji?" Dahiru ya tambaya
"ina jin tausayin Asmau saboda irin wannan abubuwan
naku ma tun farko taki amincewa da aure. Amma ba
don tausayi zan aureta ba. Sonta nake yi so you all
should better learn to live with that."
"Wai Yaya da kake maganar nan hala ka manta cewa
baka *haihuwa* ?"
Ismail ne yayi maganar wadda tasa kowa yayi shiru.
Hatta Col. Ishaq jikinsa yayi matukar sanyi. Hajiya ta taso
rai a bace "Ismail wace irin magana ce wannan? Dan
uwan naka kake fadawa magana haka" ta daga hannu
zata mare shi
Col. Ishaq ya rike hannun idanunsa sun kada sunyi
jawur. A sanyaye yake magana "Hajiya gaskiya ya fada.
Lokaci daya na manta ina da lalura har nake tunanin yin
aure."
Ya kalli kannensa daya bayan daya "in sha Allah daga yau
na bar zancen auren Asmau. Ismail nagode da ka tuna
min da waye Ishaq, ni mutum ne da Allah Ya tsarawa yin
rayuwa ba tare da naga nawa dan ba. Alhamdulillah
tunda duk kuna da yara bazan ce na rasa gabadaya ba.
Allah Yayi musu albarka. Bari na shiga nayi wanka zafi
nake ji"
Hankali a tashe Ismail yace "Yaya"
"Kada ka damu kasan gaskiya daci gareta. Na da dan
lokaci idan tayi aure zan manta da ita in sha Allah. Fatana
Allah Ya tabbatar da aurenta da Qasim ko wanda ya fishi
alkhairi gareta."
Yana fita yaci karo da Bilkisu. Hawaye take yi sosai ga
tray din abinci a hannunta. Tana jin shigowarsa taje ta
hada masa abinci don tasan tunda su Mami suka zo
bazai fito da wuri ba. Duk zantunkansu taji komai.
Ganinsa baisa ta tsorata ta bar wurin ba. Shima baiyi
mata magana ba ya wuce abinsa.
Tana nan tsaye taji Hajiya tace "kun bani kunya da
mamaki. Ban taba zaton zaku iya juyawa dan uwanku
baya ba. Ina cewa Asmau tana da 'ya kuka hau surutu
babu wanda ya tambayi garin yaya tayi cikin kafin aure."
Cikin nutsuwa ta basu labarin Asmau kamar yadda taji
kuma ta gani. Safiyya uwar tsiwa sai ta fara kuka
"Mun shiga uku. Hajiya kuji wata muguwar kaddara.
Allah Sarki"
Mami kuwa cewa tayi "duk da haka Hajiya ai bamu
tabbatar da cewa a garuruwan da ta zauna bata taba
karuwanci ba. Nima ta bani tausayi amma a bar
maganar auren tunda ya fasa shima. Kinsan shi baya
magana biyu"
Suna ta magana akan halin da Asmau ta tsinci kanta
wanda ya girgiza tunaninsu ya kuma basu tausayi. Ace
har rubutun cikin waya ya isa ya sa mutum aikata zina.
Abin da ban tsoro da firgici saboda babu wanda ya isa ya
tserewa kaddara sai dai komai akwai sila. Hajiya
Lubabatu tace tunda zata je dubo Amatullah tana so
dukkansu suyi mata rakiya.
Kukan Bilkisu suka ji Hajiya ta tashi da kanta sai dai kafin
ta fito Bilkisu ta koma dakinta tana kuka. Bata taba sanin
wannan labarin ba. A iya tunaninta baban Amatullah ya
rasu ne ko ya saki Asmau. Tsoro ne ya kamata saboda
akwai wani saurayinta da suke chatting a facebook. A
hankali ya fara sako mata zantukan banza tun bata
amsawa har ta dan fara sakewa yanzu. Wai har ya iya
tambayarta ta kwatanta masa kayan baccinta da
daddare. Tayi saurin dafe kirji, yanzu idan da abin yayi
nisa kila itama ta shiga sahun masu bawa samari jiki.
Kuka take sosai tana tausayawa Asmau kuma har ranta
tana fatan Uncle Ishaq ya aureta ko don ya rufawa
rayuwarta asiri. Sabon saurayin da suke dan satar kallon
juna dashi ta kira a waya tana sheshshekar kuka.
Numbar ma a wayar Uncle ta dauka batare da saninsa
ba. Da sallamarsa ya dauka cikin muryar da ta dashe da
kuka tace "Yassar ne?"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽45
Batul Mamman💖
Mamaki ne ya kama Yassar, kamar ya san muryar amma
bashi da tabbas.
"Da wa nake magana don Allah?"
"Bilkisu ce"
Tsorata yayi, shima yana neman numbarta amma yanzu
da ta kirashi da alamun kuka sai yaji hankalinsa ya tashi.
"Bilkisu me ya faru?"
To me kuma zata ce masa? Tausayin kawunta take yi
amma tana tsoron yi masa shishshigi. Uncle Ishaq yana
da dadin sha'ani amma babu mai son ganin bacin ransa.
Fasa maganar tayi na son ta roke shi ya lallaba yayarsa
kada ta ki Uncle dinta tace "babu komai, anjima zamu zo
duba Amatullah" tayi masa sallama ta ajiye wayar.
A ransa yasan don zasu zo ba shine dalilin kiran ba. Tashi
yayi ya shirya ya tafi asibitin. Zai jira su zo ya sami damar
tambayarta. Ko dai ta lura da yawan kallonta da yake yi
ne? Yayi murmushi, tun zuwansa gidansu na farko ranar
da kare ya biyo Asmau ya fara jin wani abu game da
Bilkisu. Sai dai duk hayaniya ta Yassar bai taba yin
budurwa ba. Ta nan bangaren tsoro ne dashi kamar
farar kura.
*****
Col. Ishaq na shiga dakinsa ya fada kan gado ko takalmi
bai tsaya cirewa ba. Kansa ne yake wani irin ciwo kamar
ana buga masa kusa. Ga zuciyarsa ta gama tafasa da
bacin rai. Wai yau shine kannensa har da Mussadiq dan
karamin cikinsu suke fada masa magana son ransu. A
gidansu akwai tsari na girmama na gaba sosai. Sun tashi
da so da kaunar juna. Lalurar kowa tare suka haduwa
suyi maganinta. 'Ya'yan Ismail biyar duka maza karamin
ma bai shekara ba. Amma saboda yadda suke bashi
girma duk shi yake sakawa yaran suna. Haka yaran
Dahiru guda uku. Gidansu gwanin sha'awa baka ce
babansu ya dade da rasuwa ba. Amma yau akan auren
Asmau duk sun ture wani girmamawa da shakuwa kowa
ya fadi son ransa. Da akanta kadai suka tsaya ya tabbatar
da har yanzu yana dakin suna cacar baki. Sai gashi
saboda irin rayuwar Asmau ta baya har gori Ismail yayi
masa. Gori da abinda yafi so a rayuwarsa, haihuwa. Shi
da kullum yake kwantarwa da yayansa hankali. Kafin
rabuwarsa da Badariyya ma yaransa biyu manyan a
wurinsa suke. Dumi yaji a idonsa yayi saurin mayar da
hawayen dake neman zubo masa. Duniya ta Allah ce
kuma ba wurin tabbatar bayi ba. Da ace babu lahira sai
yace rayuwar Asmau ta wuce abinda ake gudu domin
komai daren dadewa sai an ambaceta ko 'yarta a
matsayin mazinaciya ko 'yar zina. Ya tabbatar ko
shugabar malaman duniya Asmau ta zama sai kaji
mutane suna cewa
"Wance kamar ba ita ce tayi cikin shege ba"
"Ji yadda take nuna mana ita ta Allah ce kamar bamu san
tarihinta ba"
Amatullah kuwa ita ma bazata tsira ba. Komai kyawun
rayuwarta sai an ce "kaga wance kamar ba shegiya mara
uba ba" "wance fa da kuke gani babu aure aka haifeta"
Irin haka da maganganun da suka fisu zafi mutane zasu
fada a kansu. Babu ruwan kowa da yaya tsakaninta yake
da Allah. Shin ta tuba ko kuwa. Zina ta zama mugun
tabo mara gogewa.
Tashi yayi ya zauna tare da daga hannuwansa sama.
Hawayen da baya son yi ne suka zubo masa
"Ya Allah Ka karbi tuban baiwarKa Asmau da sauran
al'umma da suke cikin hali irin nata. Allah Ka basu
rayuwa mai albarka su ji dadin tuban da sukayi bisa
laifukansu, Ya Allah Ka bata miji nagari wanda zai zame
mata alkhairi kuma mai wanke mata bacin rai da bazata
taba dena fuskanta ba a dalilin kuskurenta na baya. Ya
Allah Ka karemu da sauran musulmi daga fadawa alfasha
kowace iri ce. Amin"
Sai yanzu yaji saukin kuncin zuciyarsa ya tashi zaiyi
wanka kafin a kira magariba. Abu daya ne a ransa yanzu,
shine hakuri da Asmau da zaiyi. Ba karamin so yake mata
ba amma dole ya barta ta auri wanda zata iya haihuwa
dashi. Zafin soyayya ya rufe masa ido har ya manta yana
da nakasa a rayuwarsa. Tunda baya haihuwa bazai cutar
da kuruciyarta ba ta zauna da 'ya daya.
Wanka ya shiga ya fito ya sanya riga da wando na yadi
mara nauyi. Ya saka hula kalar adon rigar ya sha turare
sai gashi ya fito a Jikamshinsa. Idan ka ganshi bazaka ce
yana da damuwa ba saboda tunda yayi adduar nan babu
abinda yake sai tasbihi ga Allah. Wannan ne ya saukaka
masa damuwarsa yaji kwarin gwiwar niyarsa ta rabuwa
da Asmau idan suka koma gida. Kafin ya fito text dinta ya
shigo wayarsa. Yaa budewa yaga ta rubuta _missing
Jikamshina_. Wani sabon sonta yaji ya ratsa shi. Kasa yi
mata reply yayi ya tura wayar a aljihu.
Yana fitowa ya tarar da kannensa jugum a falo domin
kuwa Hajiya tana gama basu labarin Asmau tace su fice
mata daga daki. Da ya fito duk da ransa babu dadi haka
ya basar ya dubi mazan
"Kuzo mu wuce masallaci"
Suka tashi jiki a sanyaye. Mami tace "Yaya don girman
Allah kayi hakuri da abinda Ismail ya fada. Wallahi duj
don bama so ka auro wadda zata gurbata mana dangi
ne"
Suma sauran suka soma bashi hakuri. Ismail kuwa ko
kallon yayansa ya kasa yi. Murmushi yayi wanda
dukkansu sun san irinsa yake idan ransa ya baci
"Magana ta wuce, bazan auri Asmau ba kamar yadda
kuke so. *Amma ba don kun nuna rashin amincewarku
bane, don baku isa ba*. Saboda kaddara ta fada mata ba
zan ce sai na aureta ba duk da ni din bana haihuwa ko
Ismail?"
Ismail ji yayi kamar yayi kuka. Idanunsa tuni sun canja
launi. Yayansu yana da kirki matuka, bai san yaya akayi
shaidan yaja shi yayi wannan katubarar ba.
"Yaya ka yafe min, wallahi Hajiya yau har zagina tayi
bayan fitarka. Yanzu ma cewa tayi zamu rakata asibiti
duba yarinyar Asma'un daga nan kowa ya fice mata daga
gida. Hatta Mami Hajiya tayi rantsuwa bazata kwana a
gidan nan ba."
Col. Ishaq ya kara murmusawa "to ai babu damuwa
Mami ga kannenki nan sai kibi daya daga cikinsu ki
kwana a gidansa"
Mami ta saki baki don batayi tunanin haka zai ce ba. Tayi
zaton zaije ya bawa Hajiya hakuri. Duk sun san bacin
ranta yafi karfi akan gorin haihuwar da aka yi masa ne.
"saboda Allah ya zaayi naje gidan kannena na kwana da
girmana"
"To bari mu dawo daga masallaci sai na baki key din
gidana. Babu datti sosai saboda karshen sati maigadi
yana min shara. Sai ki tafi da taki 'yar Bilkisu ta tayaki
kwana" yana gama magana yayi gaba kamar bashi ya
fada ba. Sun san sun tabo soja yau sai yadda ta yiwu
kuma. Bayan fitarsu masallaci Mami da Safiyya suka
zauna suna ta magana akan lamarin auren Asmau da
kuma karin laifin da Ismail ya janyo musu.
Bilkisu dai shiryawa tayi a daki ta fito ta zauna jiran zuwa
asibiti don tasan dole aje da ita tunda mai aikinsu bata
nan.
Tare suka dawo daga masallacin su Dahiru suna ta bashi
hakuri ya nuna musu komai ya wuce. Wurin Hajiya ya je
ta shirya ita ma tace motarsa zata shiga su tafi.
Suka fito falo Bilkisu tabi bayansu suma sauran suka fito.
Bilkisu na gaban motarsa Hajiya a baya Safiyya tazo ta
kama daya kofar zata bude ya juyo ya watsa mata harara
ba shiri ta saki kofar.
"Ki koma kibi motar 'yan uwanki masu haihuwa. Ni
Hajiya zan dauka da 'yata."
Tayi saroro tana kallonsa. Dahiru da yaji ya dan matso
wurin motar "Yaya don Allah kayi hakuri ka manta da
zancen nan. Kuma ka yarda ta biku ko Mami ta shigo.
Kaga sai ayi saving din mai mu tafi da mota biyu"
Col. Ishaq ya wani kankance ido ya kalli Bilkisu "toshe
kunnenki kinji mai gadon zinare" ta kuwa tura yatsu a
kunne tare da sunkuyar da kanta.
Hajiya tasan karshenta wata maganar mara dadi zai
yabawa kaninsa tace "a gaban 'yarku zaku nuna min hali
ko, kai kuma Dahiru kusan yadda zakuyi ku taho"
Col. Ishaq ya mayar da kansa ciki albarkacin Hajiya suka
ci. Dole mota biyu suka yi don daya zata matsesu saboda
Dahiru da Safiyya duk akwai jiki.
Yana soma tuki Hajiya tace "kai"
"Naam"
"Kayi hakuri da abinda suka yi maka don Allah kada kuyi
min gaba. Aure kuma da kaina zan sami kakar Asmau
muyi magana in sha Allahu. Tun farko na fada maka dole
zaka fuskanci kalubale ta ko'ina saboda wannan abu fa
ba wanda ake iya saurin kawar da kai bane a kansa. Ni
dai ina sonta kuma na baka goyon baya ka nemi aurenta.
Allah mai yawan gafara ne da jinkai. Idan bama iya
kawar da kai ga kuskuren mutane to bamu san da wane
laifi mu kuma Allah zai kamamu ba"
Allah Sarki Hajuyarsa akwai zurfin tunani.
"Hajiya nagode sosai amma ki bar maganar auren.
Asmau bata cancanci ta kare rayuwarta bata haihuwa
ba. Nima daga yanzu bana fatan kara neman aure. Mu
bari kawai tabi shawarar iyayenta a zauna lafiya."
Sosai Haj Lubabatu taji tausayin Ishaq. Duk sallah bata
fasa yi masa adduar samun rabo saboda yadda yake son
yara. Da suna kanana har goya masa kannensa tana yi
saboda yadda yake mata nacin zaiyi raino. Sai ayi goyon
ya zauna a falo ko baki tayi baya jin kunya.
"Dole kayi aure shine cikar dan Adam. Kayi addua kamar
yadda nake maka. Allah Ya kawo maka mace tagari" ya
amsa da amin amma ba don yana tunanin zai kara son
wata bayan Asmau ba. Shi fa bashi da raayin auren da
babu soyayya. Kuma soyayyarsa ta kare a wurin Matar
Jikamshi.
Ya kai hannu kan giya zai canja yaji Bilkisu ta dora nata a
saman nasa ta kankame. Ya dan kalleta ya kula kuka take
yi a hankali. Yace "nine ko, nasa Maminki kuka"
Muryarta na rawa tace "a'a Uncle don Allah kada kaki
auren Ummin Amatullah"
Murmushi kawai yayi yana kwanar shiga asibitin motar
Musaddiq tana bayansa.
"Allah Yayi miki albarka kinji. Ki cire duk abinda kika ji
dazu daga ranki.... Wai ma wa ya koya miki labe? Bari mu
dawo yau sai kinyi tsallen kwado"
Da guntun hawayenta tayi murmushi. Hajiya ma
murmushin tayi. Taji dadi da fushinsa bai shafi 'ya'ya ba.
Boot dinsa ya bude ya fito da ledoji biyu cike da
tarkacen kayan kwadayi na yara sai katon din ziza. Yana
tasowa daga office ya siyo kafin ya wuce gida. Bilkisu
tazo taya shi dauka sai ga su Ismail da sauri kowa ya
dauki abu daya cikin su mazan. Ya kawar da kansa gefe
don yasan suna neman shiri ne. Abinda bazasu samu
kenan a nan kusa ba.
*****
Shi da Hajiya ne a gaba sai Bilkisu da ta jero tare da
Mami da Safiyya tana tambayar Mamin kannenta. Sun
kusa zuwa dakin suka ga wata mace ta fito daga wani
daki da hijab dinta har gwiwa tana kuka. Col. Ishaq bai
san lokacin da ya isa gabanta ba da sauri ba hankali a
tashe yace "Matar Jikamshi menene?"
Asmau kuka take yi kawai "Amatullah ce ta sake samun
attack. Likita zan kira"
Shima a rude yake yace "koma wurinta bari na kira
likitan"
Kasa komawa dakin tayi tabi bayanshi da gudu tana ta
zubar da hawaye. Duk sunji tausayin Asmau da yadda ta
gigice. Dakin da suka ga ta fito Hajiya tace "mu shiga mu
jirasu"
Mami ta bude kofar suka shiga da sallama. Mama Yalwa
ce a tsaye kan Amatullah tana ta kakari. Safiyya na jin
yadda take kakarin ta matsa kusa da gadon da sauri tace
"wannan ba attack din asthma bane. Ba kuji yadda take
numfashin ba, majina ce a kirjinta"
Mama Yalwa tana jin haka ta saka bakinta a hancin
Amatullah ko kyama babu ta rinka zuke mata tana
tofarwa. Tana kaunar Safina fiye da sauran jikokinta
sosai saboda yarinya ce mai tattare da tabo mai muni a
rayuwarta. Bayan zina mace aka fi gani da nason
zunubin duk da cewa dole idan anyi akwai namijin da
suka yi tare. To amma namijin sai ya tsira daga
aibatawar mutane saboda shi ba'a ganewa a jikinsa. Idan
ya karyata babu yadda za'ayi dashi. Sharrin zuciya ya
cutar da Abubakar wanda yayi sanadin cutar da Asmau.
Gashi a karshe Safina ita ce abin ya kare a kanta. Mama
ta dan share hawayenta sai ga Amatullah ta ware saboda
hancinta ya bude.
Sai a lokacin suka gaisa dasu Haj Lubabatu. Mama tace
"Hajiya duk wadannan yaranki ne? Masha Allah"
Hajiya ta dan murmusa "ya mai jikin?"
Mama tace " gata nan duk ta ruda mu." Ta kalli Safiyya
"nagode miki kinji. Ya sunanki ne?"
Safiyya ta fadi sunanta kenan su Asmau suka shigo tare
da likita. Ga mamakinsu a zaune Amatullah take ta
jingina da pillow. Asmau taji wani sanyi a ranta sannan
ta matsa kusa da Amatullah tana mata sannu. Likitan ya
dubata ya tabbatar harda mura tayi mata mugun kamu.
Magunguna yace zai turo nurse ta kawo musu.
Bayan fitar likitan Asmau ta gaishe da su Mami. Cikin su
babu sa'anta duk sun girmeta. Sun amsa mata
fuskokinsu babu yabo babu fallasa. Col. Ishaq yana tsaye
daga wurin kofa. Idonsa kyam akan Asmau har 'yan
uwansa suka fuskanci yadda suke jifan juna da kallo. Ita
duk kunya ma take ji musamman saboda su Hajiya da
Mama.
Amatullah ce ta kurawa Ismail ido tace "kai da Babana
iyinku daya. Kaima sunanka Jikamshina?" saboda irin
kamaninsa da Ishaq.
Ya Salam, Asmau ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige.
Allah Ya taimaketa ma Amatullah bata ce irin yadda
Ummia ke fada ba. Don kadan daga aikinta ne yin
hakan.Col. Ishaq kansa yau yaji kunya karo na farko a
rayuwarsa game da fadin magana a gaban kowaye
batare da yaji komai ba.
Su Musaddiq sai kallon kallon kallo ana dan murmushi.
Ismail kuwa yace mata "nima babanki ne 'yan mata" ya
karasa wurin gadon da murmushinsa.
Ta kalli Col Ishaq tayi masa gwalo " Babana kaga nayi
sabon baba ko. Ni yanzu na dena yin baba da kai"
Yace "subhanallahi me nayiwa princess dina haka. Kai
Ismail tashi ka bani wuri mu sasanta ni da 'yata"
'Yar dramarsu tasa mutanen dakin dariya. Amatullah tayi
saurin rike hannun Ismail tace "yanzu baka wasa dani
sosai sai da Ummi na. Nima ga sabon Baba nayi"
Asmau ta rasa abin cewa. Tsiyar yaro mai surutu fa
kenan. Yau Amatullah ta gama bata kunya.
Safiyya tace "amma da baban nan naki da Ummi basu
kyauta ba. Yanzu ga sabo nan mun baki. Amma kiyi
hakuri Babanki so yake ku koma gidansa sai ku rinka
wasan tare kullum shiyasa yake yi da Umminki"
Kana gani kasan Amatullah taji dadin wannan zancen
tace "Ummi kuje kuyi wasa da Babana to idan kun gama
mu koma gidansa."
Yau kam ta kai karshen jin kunya, shi kuma Col. Ishaq
saboda shawarar da ya yanke ta rabuwa da ita shiyasa
yau bai bada amsar da zata karasa bata kunya ba.
Hajiya da Mama Yalwa sai sunkiyar da kai suke. Ita Mama
harda mamakin dama son Asmau sojan nan yake bata
sani ba.
Ismail ji yayi ta shiga ransa. Dama yana son 'ya mace
gashi duk maza gareshi.
"Ki kyale wancan Baban kawai kinga a gidana zan siyo
miki kayan wasa da alawa"
Tace "ai Ummi ma tana siya min. Ta hanani kwadayi.
Kuma bana yi sai tace min Allah Yayi miki albayka"
Yarinya karama sai basu sha'awa take yi. Mami kallon
Asmau take yi. Yanzu mace mai kamannin kamala irin
haka ace a waje ta haihu. Kai wannan duniya mai rudin
bayin Allah.
Amatullah ta sake cewa "sabon Babana in kayanta maka
Allahu?"
Dahiru yace mata "karatu ake cewa ba kayatu ba"
Tuni ta bata rai "kayatu fa nace ba kayatu ba"
Daki ya kaure da dariya. Col. Ishaq yana kallon yadda
'yan uwansa duk suka mayar da hankali gareta.
Murmushi yayi

Please Login or Register in order to submit comment