Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Asmau yayi tunda ta zauna.
Itama yayi mata kyau sosai domin kuwa korayen kayan
sojoji ne irin wanda suke sawa lokutan taro a jikinsa. Sai
yau ta kara jin soja yayi. Fuskar nan tasa ya gyara saje ya
kara haske da kyau. Ji yayi inama daga wurin dinner sai
gidansu. Ya mika hannu mai sanye da farar safar hannu
mai santsi zai riko nata da yasha lalle suka ji kukan
Amatullah. Kuka harda ajiyar zuciya wai Umminta da
Babanta zasu tafi su barta. Ana ta rarrashinta akan suma
can zasu je yarinya taki amincewa. Col. Ishaq yace a
miko masa ita. A tsakiyarsu ta zauna ta hana ruwa gudu
don har suka isa wurin surutu kawai take yi. Gata a
tsakiyar iyayenta duniya tayi mata dadi.
Da suka je wurin ya fara cika. Duk masu cewa zasu
sword crossing dinnan kowacce ta je. Gashi dai card
admit ne amma haka wurin ya cika sai san barka.
Iyaye ma ba'a barsu a baya ba. Hajjo da Yaya tagwai ma
duk tsufansu sunce basu taba ganin bikin sojoji ba dole
ne ayi dasu.
Tare da sauran yara aka hada Amatullah sannan MC ya
sanar kowa ya zauna ango da amarya zasu shigo. Yace a
zauna ne saboda a tsaye dogaye zasu karewa marasa
tsaho. Duk sojojin wurin cikin uniform din occassion
suke. Dole su burge mutane. Sannan babu hargitsi don
biki ne na manyan kasa da kowa baya son tsokano su.
Layi ne sojoji suka yi hagu da dama mutum goma goma.
Kowanne ya rike hularsa a hannu daya sannan suka hada
takubbansu ta sama inda amarya da angi zasu wuce.
Kida ne mai taushi yake tashi aka umarci amarya da
ango da su taho su wuce. Babu masu daukar hoto ta
waya don ance kowa ya zauna. Masu daukar hoto biyu
ne kawai wadanda aka hayo su suke binsu. Sun zo inda
zasu shiga karkashin takubban hularsa na makale a
hannunsa ya lankwasa hannun damansa yayi mata
alama da ta rike. Duk da tana jin kunya haka ta zura
hannunta ta cikin nasa suka fara tafiya. Jama'a kuwa sai
tafi har suka wuce suka zauna.
Duk taron da akayi da tsari dole ya bada sha'awa. Irin
wannan taron akayi a bikin Ishaq da Asmau. Tana daga
mazauninta ta hango Qasim table dinsu daya da Ma'u
suna ta hira. Ta nunawa Jikamshinta yayi murmushi
"Allah Yasa shima tashi Asmaun mace ce tagari kamar
tawa"
"Amin" ta amsa tana 'yar dariya masu hoto suka sami na
yi.
Yaya Tagwai tace da Hajjo "wai ku a bikin Kano tsufaffi
basa takawa ne? Tunda muka zo kidin yara ake sakawa
suna ta rawa."
Hajjo tayi dariya sosai sannan ta yafito Yassar da hannu
tace aje a saka wakar da zasu iya takawa kuma a fada
filin nasu ne tsufaffi. Ango da amarya dole su sauko.
Yassar ya rinka dariya yaje ya fadi sako amma don
shakiyanci wakar da yace a saka bata dace da Yaya
Tagwai da Hajjo ba da sauran irinsu masu kashin kafa
yayi laushi.
Sai da suka fito tsakiyar fili ga ango da amarya kawai aka
soma wakar Uban Duma ta Ali Dawayya. Hajjo ta
karkace itama Yaya Tagwai ta gotar da kafa daya zasu
fara taku suka ji sautin yafi karfinsu. Kunnen Yassar ta
jawo yace "wallahi Hajjo tsohuwar waka nace ya saka
kuma ita ya saka."
'Yan taro suna ta dariya Yaya Tagwai ta gwangwaje
abinta. Ango ma sai gashi yana juyi da abokai. Asmau dai
kunya ta hanata rawa sai dariyar tsufaffi dake cikinta.
Iyaye ma sunyi tasu da amarya da ango asa ta turanci
asa ta hausa. Da taro yazo karewa su Hajjo sunyi hanyar
fita aka saka Mata ku dau turame. Dafa juna sukayi ita da
Yaya Tagwai suka koma fili suka sha rawa. Su Ainau sun
sha dariya kamar cikinsu zai kulle. Hajjo tace ita ba don
amarya tayi ba. Dole ta taka idan aka ambaci sarki.
Sai wuraren shadaya da rabi wurin yayi saukin mutane
anata tafiya gida. Col. Ishaq ya dubi Asmau wadda duk ta
gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Drebansa yace ya bashi
key din mota ya bi wasu ya tafi gida. Abokinsa da suka zo
tare yana wurin yace "ango duk tsiyarka fa tare zamu
tafi. Naga kana sallamar dreba nasan ni zan biyo baya.
Kasan Mami...."
"Mamo ba Mami ba. Ka fita idona Captain. Wai Baraka ba
tazo ba. Don Allah ka dauketa ku tafi dare yayi"
Saluting dinsa yayi yana kyakyata dariya. "Na barku
lafiya angon Asmau."
A can gefe daya kuma su Mami ke neman Bilkisu a tafi
gida an rasa inda tayi. Tana can ita da Yassar a wurin
wasu kujeru. Abinci yake ci yunwa ta dame shi yaji
sallamarta. Har kusan kwarewa yayi don baiyi zaton
ganinta ba. Tayi murmushi ta zauna a kujerar dake
kallon tasa. Yassar ya ajiye cokalin yana kallonta. Tace "ci
abincinka mana"
"Bazan iya ba. Ni bana iya cin abinci a gaban mutane
shiyasa ma kika ganni a nan yanzu"
"Ni kuma kaga so nake kullum ka rinka ci a gabana"
Sauran abincin bakinsa ne yasa shi kwarewar da yake
gudu da yaji abinda tace. Tayi masa sannu amma tarin
yaki tsayawa. Da tayi magana sai ya sake yin tari.
Bilkisu ta dan harare shi "dama saboda ni kake tarin? To
aiki ya sameka don bazan dena yi maka magana ba"
Yassar ya rasa me zai ce mata. Haka yake da kunyar mata
tuntuni. Babu wanda zaice ga budurwarsa. Ta dan
sassauta kallonsa tace "ni na gaji da kallon kallo da muke
yi fa, sai yaushe zaka ce kana sona?"
Wannan karon da ya fara tari har sai da ya sauko daga
kan kujera. Yana dafe da kirji tana yi masa sannu yace
"ke haka danginku suke ne, basa jin kunyar magana"
Turo masa baki tayi "to ba wani bane a cikin 'yan biki
yace yana sona ba. Kuma har cewa yayi zaiyiwa Uncle
magana shima soja ne a karkashinsa yake"
Yassar ya ware ya koma ya zauna yana kallonta babu
zancen wasa "don Allah kada ki amsa masa. Nima zanyi
sojan nan har Yaya Ishaq ya karbo min takarda zanyi
short service"
"Uncle Ishaq nake ce masa fa" tana magana kamar zata
yi masa kuka
Duk ya rude da tayi zancen wani soja yace "to nima
Uncle Ishaq kinji"
Ta juya masa ido "to kana sona kenan na sallami
wancan"
Kai ya sunkuyar kasa da gaske kunyarta yake ji ya gyada
kai a hankali.
"Ni da baki zaka fada"
"Kiyi hakuri zanyi miki text ko na kiraki"
Shan kunu tayi "zan cewa wancan ya turo kawai"
Yassar ya sake rudewa "me yayi zafi kiyi hakuri. Ina sonki
mana ai ko ban fada ba kin sani"
Sai yanzu yaga alamu taji kunya ta rufe kuskarta da
mayafi ta tashi "bari naje nasan ana jirana. Don Allah ka
kirani fa"
Yayi murmushi "in sha Allah ina zuwa gida zaki ji wayata"
Sai da ta soma tafiya ta dan daga murya yadda zaiji tace
"Yassar"
Ya juyo yana kallonta "dama karya nake yi, so nake
kawai kace kana sona" daga haka ta tafi. Ya zauna yana
sosa keya. Yana tunanin ko dai soyayya a jinin dangin
Jikamshi take. Tasha fada kuwa a wurin Mami. To
bukatarta ta biya ko kadan ranta bai baci ba.
******
'Yan uwan Asmau sunyi gaba da harda yi mata tayin ko
zata bi motar Umar tunda Ainau ce kawai a ciki. Col.
Ishaq ya jefi Shemau da kallo harda harara ta kwashe da
dariya. Dama tsokanarsa tazo yi. Sai da yayi sallama da
abokansa sannan yazo ya sameta a inda yace ta jira shi.
Jikinta yayi sanyi tunda taga ya sallami 'yan motar tasu.
Har wani dan tsoronsa take ji. Ya kula da canjin
yanayinta a ransa yace baki ga komai ba.
Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar
yaki sakin hannun. Wani iri take ji daban don bata saba
ba. Idan ba bisa lalura ba tana iya rantsuwa banda
Abubakar babu wani namiji da ba muharraminta ba da
ya taba mata hannu. Shima jin hakan yake har ransa. Ya
dade yana jiran ranar da Asmau zata halatta gareshi ya
tabata batare da tsoron zunubi ba. Sai ma lada da zai
biyo baya.
Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna
wurin dreba. Ya tayar da motar sannan ya kamo
hannunta ya dora akan giyar. A haka ya saka giyar ya
soma tuki cikin nutsuwa. Zuciyar Asmau ta kusa ballo
kirjinta don tsoro.
"Tunanin me kike yi ne"
Ta dan rufe idonta ta bude "babu komai" muryar nan a
salihance take fita.
"Are you sure, har tunanin abinda zan iya yi miki daga
nan zuwa na kaiki gida bai zo kanki ba?"
Ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda dare ne
kuma titin babu motoci sai tsiraru shiyasa yake iya
kallon bangaren da take.
"Kinyi shiru, bari na fada miki abinda naji zuciyarki tana
cewa"
Kallonsa tayi tana jiran taji abinda zai ce. Shima sai da ya
dan juyo sannan ya mayar da ido sa ga titi.
"Zuciyarki tace yau dai gani ga Jikamshina a matsayin
maya da miji. Daga nan zuwa ya kaini gida zanyi kokari
ko kiss ne nayi masa"
"La'ila ha ilallahu, ni banyi wannan tunanin ba..." Asmau
ta fada tare da cukwikuye kanta cikin mayafinta. Kunya
taji har bazata iya misalta ta ba.
Shi kuwa dariya yake mata. Yana son wannan kunya ta
Asmau.
" ko kwana daya bamuyi da aure ba har kin fara karyata
ni?"
Ta dan dago kanta daga kan cinyarta da ta rufe "ba haka
nace ba fa"
Nishadi kawai yake ji gashi ga Asmai a matsayin
maaurata. Ya daga gira daya "to yaya, kin amince kinyi
wannan tunanin?"
Ta soma girgiza kai sai taga ya bata fuska. Tayi saurin
cewa "Allah Sarki banyi ba amma dai naji nayi tunda
haka kake so nace"
"Good girl, that means I will get one kafin mu rabu yau."
Ta turo baki don ta san idan ta sake magana wani abin
zai kuma fada. A hakan ma bata tsira ba ya kalli dan
bakin ya sha janbaki
"Mayar da lips din mana, ai ba yanzu za'ayi ba sai mun
isa gida. Naga alama kin fini zumudi".
Kwafa tayi tana tunanin me zatayi masa, tukinsa yake
hankali kwance. Tace "Jikamshina"
"Yes sweetheart. Kinsan fa yanzu duk wani suna da ake
kiran masoyi a duniya zan kiraki dashi"
"Zan rama ne."
Yayi dariya "dama haka nake so. In ce wani abu ki rama
yanzu?"
Ta gyada kai "I want to hug you"
Ta bata fuska a shagwabe "wallahi zan maka kuka"
Ya sami abinda yake so. Tana jinsa yana dariya ta ja
mayafi ta rufe fuska har suka isa gidan Jafar. Yaron
makota da yake masa gadi ya bude ga motarsa nan
alamun sun dawo.
Ta kama kofa zata bude taji ta a rufe. Yace mata
"Kiyi hakuri kiyi min magana please"
Ta noke kafada, ya ce "to shikenan ina zuwa. Umarni na
baki kada ki bude kofar nan"
Itama nata salon ramawar kenan yau duk abinsa bazata
yi masa magana ba har ya tafi. Tana kallo ya bude ya fita
ya zagayo ta gefenta ya bude mata. Sai da ta ziro
kafafunta waje kawai ya durkusa a gabanta ya kafa kafar
ya cire mata takalma yana bin yatsun kafar yana
matsawa. Kasa magana tayi saboda bata yi zaton abinda
zaiyi mata ba kenan. Ga kunya kamar tayi ihu. Har
fargaba take kada wani ya fito ya gansu. Ta dan ja kafar
ya rike sosai ya cigaba da matsawa yana magana a
hankali.
"Tun dazu kike dingishi kina tunanin zan bari ki shiga ciki
ne kice wata tayi miki tausa a kafa?"
"Don Allah ka dena kada yaya Jafar ya fito" tana magana
idonta na kan kofa.
"Matsoraciya bari kiga wani abu" bata ankara ba taji yayi
mata daukar jarirai. Abinka da dogon soja tashi yayi ya
nufi hanyar kofar gidan da ita.
Asmau ta gama tsurewa ga tsoro tasa hannuwanta biyu
ta kankame masa wuya "Ji...Jikamshi don Allah ka
saukeni"
"Anki din, ki sassauta rikon nan kin shake ni"
Ta dan marairaice "idan aka fito aka ganmu fa"
"Zaki sa na shiga dake har dakin da kike kwana idan
bakiyi shiru ba"
Shirun tayi don kada ta kara tunzura shi. Kanta a wurin
kafadarsa ya cigaba da tafiya ta lumshe idanu. Komai
nasa daban yake mata. Aure dadi aure lada yau ba
tsoron fada take yi ba idan da wani zai fito ya gansu. Ko
waye sai dai taji kunyarsa sabanin da wani namijin ne
kawai da babu aure a tsakaninsu. Taji tsoron a kamasu
sannan ta hada da lodin zunubi. Allah Ya kara karemu
daga soyayyar tabe tabe babu aure wadda wasu suke
yiwa kallon burgewa.
Tunaninta ya katse da taji ya ajiyeta a bakin kofa sannan
ya bata takakmanta. Ya daidaita fuskarsa da tata ta
hanyar rankwafowa ya rage tsaho suna jin numfashin
juna. Idonta a rufe don fargaba.
"Ina jin na cancanci wannan kiss din da kika yi tunani
dazu"
Bata bude idon ba taji ya hada bakinsa da nata.
Alhamdulillah cikakken farinciki yana tare da aure. Da da
yanzu ta kwatanta sai taji yanzu duk da tana jinta kamar
akan kaya kada wani ya fito kuma shima tana jin
kunyarsa amma yanzu ne hankalinta ya kwanta. Yanzu
ne taji nutsuwar kasancewa da namiji-mijinta.
Ya dan dago kansa yana karewa fuskarta kallo kamar
kada ya barta yace "saura ladan nauyi da na sha"
.
Tar ta bude idon "gaskiya bani da nauyi"
"Ba kiji yadda zuciyata ke bugu bane da na daukeki." Ya
dora hannuta daidai kirjinsa ya sake kissing dinta.
"Ke dai ba na nauyinki bane, tsabar dadin kasancewa
dake ne. Ba don ina jin kunyar Umma ba sai dai a biyoki
da kayanki gobe"
Kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rungumeta sosai a
kirjinsa zukatansu na kara son juna "yau zanyi bacci mai
dadi Matar Jikamshi. Ina fata kema zakiyi. Sai gobe idan
mun hadu a dakinki" a goshinta yayi mata wani kiss din
ya tafi ya barta a tsaye tana numfashi da kyar.ABIN DA AKE GUDU
Na Batul Mamman
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment