Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku rinka tunanin
lahirarku. Nagode sosai."
Daga haka ta lallaba ta karasa bakin gate din. Wannan
karon sai da Gaddafi yayi da gaske Annur ya ja motar
suka tafi.
Kasa daga kafarta tayi taji kamar zata fadi wata mata mai
uniform din masu shara da wanke bandaki ta tareta
daga baya tana yi mata sannu. Daga nan bata san da
yadda aka shigar da ita asibitin ba. Ko awa daya bata cika
ba Allah Ya taimaketa ta haihu.
Tana jin wannan kukan na jarirai taji gabadaya
damuwarta ta gushe burinta kawai taga abinda ta haifa.
Nurse din da ta karbi haihuwar tace mata kin sami 'ya
mace. Asmau tayi murmushi tare da dago kai ta kalli
kyautar da Allah Yayi mata tana hamdala. Gata da 'yar
Abubakar sai dai babu shi kuma babu iyayensu. Kaddara
ta riga fata a kansu. Ba don haka ba da yanzu iyayensu
za'a mikawa jaririyar.
A wani dan zani aka nade 'yar aka miko mata. Ta zuba
ido tana kallonta. Sai kuma kuka ya kwace mata da ta
tuna bata da wata hanyar kulawa da 'yar. Ko suturar da
zata saka mata bata da ita. Wannan mai sharar tayi mata
Allah Ya raya sannan ta fita daga dakin. Ba jimawa ta
dawo da wasu tsofaffin riga da zani amma a wanke ta
bawa Asmau fuskarta a sake.
"Ga wannan akwai ruwa a bandaki ki gyara jikinki sai ki
saka. Idan kin fito sai ki fadi wa za'a kirawo a danginki."
Asmau kamar kada ta bata yarinyar haka take ji. A
rayuwarta bata taba son wani kamar yadda take jin son
jaririyarta ba. Tayi godiya ta karbi kayan ta wuce
bandakin.
Bata dade ba ta fito aka kaita dakin hutu. Wani likita yazo
ya dubata yace babu wata matsala amma sai da safe
zasu sallameta. Ya bata takardar magungunan da zata
siya. Bayan fitarsa mai sharar ta kara dawowa wurinta ta
sake tambayarta ina 'yan uwanta saboda a bakin gate ta
ganta ita kadai. Ya kamata a sanar dasu ko don su kawo
mata abinci da kayan baby.
Asmau bata da amsar da ta wuce kuka. Matar sai ta
kyaleta ta koma bakin aikinta. Ita kuma ta cigaba da
kallon jaririyarta tana bacci. Ikon Allah, yarinyar kama
take yi da Mama Yalwa. Asmau sai ta rantse duk 'ya'yan
Mama babu mai kama da ita kamar wannan yarinyar.
Dama duk sunfi kama da Alh Adamu. Da namiji ta haifa
dama sunan Abubakar zata saka masa. Amma tunda
mace ce zata saka sunan mahaifiyarsa kamar yadda
suka yiwa juna alkawarin sai sun sakawa 'ya'yansu
sunayen iyayensu. Da wannan tunanin ta danyi
murmushi. Babbar matsalarta yanzu bata san ta ina
zata fara ba? Bata da komai bata da kowa. Sannan bata
san irin tarbar da za'ayi mata ba idan ta koma gidansu.
Wannan tunanin ya isheta ga kudin asibiti duk da na
gwamnati ne tasan ko yaya za'a bukaci ta biya kudin
wani abin. Hakan ne yasa tana ganin duhun dare yayi ga
cikinta kamar anyi mata yasa don yunwa ta kwance
dankwalinta ta goya jaririyar da shi sannan ta zura hijab
dinta tayi waje. Gara ta gudu tun kafin ace ta kawo kudin
da tasan bata da su. Ta kusa karshen barandar da zata
kaita bakin gate ne taji muryar mai sharar nan tace "ba
dai guduwa zakiyi ba".
*****
Hajjo ce ta farka daga bacci a gigice ta rinka juyi akan
gado har ta tabbatar dai a dakinta take. Hawaye ne
kwance a fuskarta sakamakon mafarkin da tayi da jikarta
Asmau. Kuka ta ganta tana yi tana kiran Hajjon da ta
taimaketa. Duk yadda taso ta kama hannun Asmau ya
gagara har ta farka. Jikinta sai karkarwa yake ta tashi ta
dauko mayafinta a gefen kujerar dakin ta tafi dakin
Garzali. Ko agogo bata duba ba tayi sa'a ta same shi yana
fesa turare da alama fita zaiyi.
Tsayuwar kirki ta kasa cikin tsawa tace yazo ya kama
karnukansa zata fita.
"Hajjo ina zaki je da yamman nan. Biyar da rabi fa".
Harararsa tayi fuska a murtuke don kada ya kawo mata
wargi "inda ka aike ni zani. Kaga kada ka bata min lokaci
wuce muje".
Suna fitowa yayiwa karnukan fito suka yo kansa Hajjo ta
samu ta fice. Don sauri kafarta har zafi take yi mata taji
takun mutum kamar ana binta da gudu. Duk da a
tsorace take haka ta dake bata juya ba take magana
"Rabe wallahi yau ko me zaka ce sai naje wurin Bara'atu.
Ba kai ka haifa min Shu'aibu ba shiyasa baka san ciwon
iyalinsa ba."
Garzali yayi yar dariya
"Ni ne Hajjo. Raka ki zanyi. Nima rashin mu'amala dasu
ba karamin damuna yake yi ba."
Tayi murmushi "Allah Yayi maka albarka" daga nan ta
bashi labarin mafarkin Asmau da tayi suna tafiya.
*****
Tun kafin azahar Zubaida ta iso garin Kano ta samu mai
tasi suna ta yawo a unguwar Hotoro basu gane gidan ba.
Gajiya yayi ya sauketa bayan ya karbi dubu biyu a
hannunta. Har zai tafi sai ya dawo saboda ta bashi
tausayi yace ta sami mai adaidaita sahu sunfi sanin
layukan cikin unguwa.
Tayi sa'a kuwa ta sami wani ta fada masa inda take
nema. Da ya kula bakuwa ce a garin ya tsula mata kudi
sai dai bata damu ba. Biyan bukata yafi dogon buri.
Kusan dubu talatin ta dauko a cikin kudin da Uwargida ta
bawa Yaya Babba.
A cikin layin mai adaidaita sahun ya nuna mata gidan
kwamishina. Tayi masa godiya ta bashi kudinsa. Daga
nan tasan Asmau tace gidansu babu nisa. Wata tsohuwa
ta hango da wani mutum a bakin gate din wani gida tayi
saurin karasawa kafin su shiga.
Sallama ta rinka yi musu suka juya suna kallonta a tare.
Riga da siket ne a jikinta sun dameta sosai ga katuwar
jakar kaya sai wani siririn mayafi da ta rataya a wuya. Da
murmushi a fuskarta ta dan rissina ta gaishesu sannan
tace "don Allah gidan Umma nake nema. Umman
Asmau".
Garzali ya sake kallon Zubaida sannan yace "nan ne".
Ko jiransu batayi ba ta shige ciki tana kwalawa Asmau
kira. Yassar da yake shanya ne ya fara ganinta bai san
lokacin da ya saki wandon da yake kokarin dorawa a
igiya a kasa ba ya nufota. Zubaida na ganinsa ta saki
murmushi.
"Tabbas nan ne gidan don naga kamarku. Kai ne Yasir
ko?"
Kallon rashin sani yake mata yace "a'a sunana Yassar"
Zubaida tace "hakane kaini wurin Asmau".
Hanyar falon ya nuna mata sai ya kula da Hajjo da Kawu
Garzali. Har dan tsorata yayi sai yaga Hajjo tana hawaye
"Zo nan Yassar, zo naji duminka a jikina"
Ji yayi kamar mafarki yake ya fara tunanin gudu Garzali
ya damko wuyan rigarsa ya hada shi da jikin Hajjo. Kuka
ta fashe dashi na takaicin yadda jikanta yake nuna tsoro
da fargabar ganinta har yana neman gudu. Tana rike da
hannuwansa tace "kuyi hakuri Yassar. Ku yafewa wannan
tsohuwar".
Shima kukan ne ya zo masa ya kankameta. Ashe akwai
ranar da Hajjo zata nuna masa so? Tana rike da
hannunsa suka shiga cikin falon.
Umma suka gani da Aina'u da kuma Jafar sun saka
Zubaida a gaba suna kallonta jin tace daga Azare tazo
wurin Asmau.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽25
Batul Mamman💖
Cikin matsanancin tsoro Asmau ta juyo tana kallon
matar. Hakuri ta soma bata murya na rawa ga hawaye
na wanke mata fuska tana sanar da ita bata da kudi
kuma bata kowa da zai taimaketa. Matar sai tayi
murmushi "kada ki damu ni ba wani abu zanyi miki
bane. Hasali ma na rasa dalilin da yasa tun da na shigo
dake cikin asibitin nan hankalina yake kanki. Amma dai
biyoni mu koma ciki".
Ba yadda ta iya haka tabi bayan matar suka tafi wurin
wata mai sharar. Matar babba ce don da gani zatayi sa'a
da Umma. Wadda ta biyo ta gaisheta cikin ladabi sannan
ta gabatar da Asmau a matsayin 'yar uwarta wadda bata
da komai. Rokonta tayi akan ta ranta mata kudi su biya a
sallameta ita kuma tayi alkawarin biyanta a hankali cikin
albashinta.
Babbar matar ta kalli Asmau tayi wuri wuri da ita tana
jijjiga goyonta. Da gani ma a tsorace take tace "kudin ba
wasu masu yawa bane Zulaiha, ga wannan kije ki biya.
Sai mu warware daga baya. Ki gaida mutan gidan."
Zulaiha tayi mata godiya itama Asmau ta saka baki suka
yi tare. Bayan sun fito ne Asmau ta rasa bakin godewa
wannan matar mai suna Zulaiha. Matar bazata girmeta
da yawa ba. Tuna mata take da Anti Rashidan Azare.
Bayanta tabi suka koma wurin likita aka sallameta duk da
yaso kwarai ta kai washegari.
Zulaiha tace "babu komai yiwa kai ne. Bari na canza kaya
nazo muje gidana tunda dare yayi".
Asmau sai mamaki take yi meyasa wannan matar ta
taimaketa alhali bata san komai a game da ita ba. Suna
fita daga asibitin bus suka hau maleji suka sauka a wata
unguwa da Asmau bata sani ba. Daga nan suka bi cikin
lunguna suka karasa wani gida mai karamin gate. Idan
kaga gidan dole zakayi tunani masu shi suna da rufin
asiri. Sai ka shiga zaka ga babu wasu abubuwan more
rayuwa. Yara ne har shida suka fito suna yi mata sannu
da zuwa ta amsa fuska a sake sannan suka gaishe da
Asmau. Zulaiha ta dauki karamin ciki da baifi shekara ba
ta soma shayar dashi. Falon da ta kai Asmau ko leda
babu ta dauko tabarma ta shimfida mata.
Yaran ta tambaya ko su kadai ne a gidan suka ce eh.
Babbar cikinsu mace ce da bata fi shekara tara ba sai
namiji dake binta. Duk yaran babu wata tazara
tsakaninsu. Ta dauko naira hamsin daga gefen zaninta ta
bawa namijin "Muhsin siyo mana kan kifi, ke kuma
Humaira dauko attaruhu hudu da rabin albasar nan ta
safe ki jajjaga min. Sannan ki dauko katuwar tukunyar
nan ki wanke a cikata da ruwa yanzu zan zo na dora"
Da murna yaran suka fita tunda suka ji batun kan kifi
sun san yau gidan za'a ci dadi. Asmau na nan zaune
Zulaiha ta kunna kyandir sannan ta tashi ta dora mata
ruwan wanka ita da baby ta kuma dora girki.
Wankan Zulaiha ta fara yiwa jaririyar itama Asmau tayi
da taimakonta dai. A ranta sai mamakin matar take yi.
Haka kawai daga haduwa sai taimako? Bayan tayi
wankan taji dadin jikinta tana zaune Zulaiha ta sakawa
jaririyar kayan karamin danta Ali irin wanda suka yi
masa kadan. Allah Sarki wannan jaririya ko kayan
sakawa bata dashi. Ta gama ta nado mata ita a zani ta
bata sannan aka kawo mata dafadukan taliya 'yar hausa
harda yaji da ruwa. Asmau ta zauna ta narki abincin nan
tana yi tana godiya. Sai da ta koshi sannan Zulaiha ta
tambayeta sunanta da kuma abinda ya fito da ita. A nan
Asmau ta soma kuka. Tana yi tana bawa Zulaiha labarinta
mai cike da ban tausayi da gargadi ga sauran mutane.
Sosai Zulaiha ta tausaya mata. Tace
" Tun da na ganki haka nan Allah Yasa naji ina son na
taimaka miki. Kinga nima ba wani abu gareni ba. Ganinki
da nayi sai ya tuna min da tawa rayuwar shiyasa na zabi
na taimakeki ko Allah zai kawo min sassauci a cikin
kuncin da nake ciki. Kinga dare yayi ki kwanta zuwa gobe
zaki san nawa labarin. Allah Yasa ki sami ruwan nono da
wuri kafin hakurin 'yar tamu ya soma karewa ta fara
kuka".
Murmushi Asmau tayi tana kallon fuskar 'yarta ta hasken
kyandir. Sun tashi Zulaiha zata nuna mata dakin da zata
kwanta don gidan akwai dakuna suka ji an shigo falon.
Wata dattijuwa ce rike da wani mutum yana ta tangal
tangal kamar zai fadi. Daga bakin kofa ta tsaya tana jifan
Zulaiha da harara "yau kuma wani sabon iskancin ne ya
tashi kina jina ina fama da Gidado bazaki zo ki taimaka
mu kaishi daki ba?"
Idonta ne ya sauka akan Asmau ta daure fuska
"Wannan kuma fa, daga ina?"
Zulaiha tana saka hannuwan mutumin a kafadarta tace "
'yar haya na samo dazu a asibiti. Zata karbi hayar daki
daya a gidan nan, kinga kudin ko cefane sai mu kara
dashi".
"Cefanen banza, ni zan rinka karba ina karawa a jari na."
Asmau ta dan duka ta gaishe da matar ko kallonta bata yi
ba ta fara tambayar ina abincinta. Shi kuwa mutumin da
Zulaiha ke ja surutai yake marasa kan gado. Da suka zo
wucewa ta gabanta wani irin wari yake fitarwa.
A falon ta jira Zulaiha ta kaishi daki sannan ta nuna mata
wurin da zata kwana. Tana kwance rungume da 'yarta
tana jin wannan dattijuwa tana masifar anyi kaza anyi
kaza ba daidai ba. Can kuma taji mutumin wanda ta
tabbatar mijin Zulaiha ne ya soma zage zage bata bashi
abincinsa ba zata kashe shi da yunwa. Har Asmau tayi
bacci babu abinda take ji yana fitowa daga bakin Zulaiha
sai "kuyi hakuri".
*****
A can Kano kuwa lokacin da Yassar ya shigo ciki rike da
hannun Hajjo sai da gaban Umma ya fadi. Aina'u tayi
saurin labewa a bayan Umma a tunaninta daukarsu tazo
yi.
Hankalin Umma ya bar Zubaida ya koma wurin Hajjo.
Cikin sanyin jiki ta gaisheta sai dai sabanin da sai taji
Hajjon ta amsa cikin kuka. Har inda Umma ke tsaye taje
ta kama hannuwanta tana hawaye "Bara'atu nasan ke
mai hakuri ce da kawaici. Ki dubi girman Allah ki yafewa
wannan tsohuwar banzar hakkinku da ta dauka."
Umma ta saki baki cike da mamaki. Me kunnenta yake
jiye mata ne? Hajjo ta cigaba da magana tana kuka "nayi
nadamar abinda nayi miki tsahon shekarun nan. Ni
kaina bansan dalilin yin hakan ba. Bakiyi min komai ba
na dora miki tsana da tsangwama."
"Alhamdulillah" Umma ta fada a fili itama da nata
hawayen. Hajjo ta cigaba da rokon gafara Umma tace ai
zuwanta kadai yasa komai ya wuce. Hajjo ta mika hannu
"zo nan autar Bara'atu. Taho wurin kakarki kinji 'yar
albarka. Jafaru baka ce komai ba. Ku yafeni ko don
darajar babanku"
A darare Aina'u ta matsa jikin Hajjo. Garzali ma a
kunyace ya gaishe da Umma ta amsa bakinta yaki
rufuwa don murna. Jafar ma murna yake yi sai dai
hankalinsa yafi karkata ga Zubaida dake tsaye tana kare
musu kallo.
Sai da aka dan sami nutsuwa a falon sannan Jafar yace
"Umma bakuwar nan fa tana jiranki"
Hakuri Umma ta bata ko wurin zama basu bata ba suna
farincikin fara daidaituwar al'amuran danginsu. Aina'u ta
kawowa Zubaida lemo da abinci tana ci suna kallonta.
Jira suke yi ta gama ta fada musu abinda ta sani game da
Asmau.
Da ta gama ne Umma ta fada mata Asmau tayi wata
bakwai rabonta da gida. Zubaida ta dan cije lebe fuskarta
ta nuna rashin jindadi "nayi tunanin gida da dawo da na
koma aka ce min bata nan. To ina ta tafi?"
Hajjo tace "kinga yarinya, bayani zakiyi mana yadda
zamu fahimceki sosai. A ina kika ga Asmau'un?"
Zubaida ta fada musu komai game da zamansu da
Asma'u. Umma da Hajjo sai kuka jin Asmau ta zauna a
gidan karuwai. Tace hatta yadda ta sami cikin duk ta fada
min.
Umma ta share hawaye
"Ta fada miki sunan wanda yayi mata cikin?"
"Eh tace sunansa Abubakar".
Umma ta toshe bakinta da hannu tana wani kukan.
Dama Qasim ya tabbatar musu cikin Abubakar ne amma
basu bawa wacce abin ya shafa damar bayani ba. Yassar
ta nuna "tashi maza kaje ka kira Mama Yalwa. Ka fada
mata bakuwa ce tazo daga Azare wadda tasan Asmau".
Ba'a dade ba sai ga Mama suka zauna Zubaida ta fada
musu duk labarin da Asmau ta bata na waya da yadda
al'amarin ya cigaba. Falon sai salati suke yi ana jimamin
wannan abu. Ace tarbiyar shekara da shekaru wasu can
da basa kishin addini suyi ta fito da samfurin yada
alfasha salo salo suna turawa 'ya'yan musulmi.
Hajjo tace "to shi shegen giruf (group) din aje a tarwatsa
mana kowa ya huta. Haka kawai an janyowa marainiya
fadawa mummunar rayuwa. Kada na kaiku da nisa ko
mu da babu waya a zamaninmu waye ya koya mana
yadda ake yi tsakanin mata da miji. Gashi mun rayu dasu
cikin kwanciyar hankali mutuwa ce ta raba. Duk wannan
shaidancin kuma da ake yadawa ai bai hana mutuwar
auren yara kanana ba."
Mama da batasan yadda akayi Hajjo ke nuna damuwarta
akan Asmau ba tace " ai group din a waya ake bude shi.
Ni abinda ya fi damuna bai wuce yadda zakiga yara da
matan aure a dauki waya tun safe har dare ki rasa me
ake gani. To ashe duk harkar lalacewa ce duk da dai ana
samun karuwa ta wani fannin. Yaranmu da sunyi waya
sai kiga basu da lokacin komai sai nata."
Zama sukayi ana ta mayar da zance kowa na tofa nasa.
Kawu Garzali a fusace yace "ita wacece wannan Walidar
ne? Tayi fatan kada mu hadu don wallahi sai nayi mata
rauni. Kawaye da abokan banza sunfi saurin lalata
tarbiya. Ni ba daga abokin bane muka kare a haka." Ya
dubi Jafar da Yassar
" yanzu kuna da uba saboda haka duk yaron da na gani
baiyi min ba kafin na kore shi ta kanku zan fara".
Umma tayi murmushin jindadi. Duk da tasan Garzalin
kansa baya sahun mutanen kirki amma dai taji dadin
kulawarsa ga 'ya'yan dan uwansa.
"Walida kawar Asmau ce tun primary. Kuma itama nata
mahaifin yana kokari. Don ranar da abin ya faru kafin
mu dawo daga asibiti yazo ya dauketa."
Hajjo taja tsaki wanda har Zubaida da Aina'u sai da suka
yi dariya "anyi ta baya ta rago. Shi da 'yarsa ta bata ta
wani ai ya jira nasa lokacin. In Allah Ya yarda sai ta
dauko masa abin...."
Mama da Umma suka dakatar da Hajjo daga yin
mummunar addua. Daga nan suka yanke shawarar
washegari da sassafe zasu tafi Azare neman Asmau. Anti
Bintu da Shemau duk an sanar dasu haka Abdulhalim da
Qasim.
*****
Annur da Gaddafi tunda suka isa masaukinsu ko abinci
sun kasa ci. Abokin da suka zo wurin party dinsa yayi ta
damunsu da su tashi suyi wanka a tafi sai su kalli juna su
sunkuyar da kawunansu kasa. Gabadayansu dana sanin
baro gidajensu suke yi. Sun baro iyayensu musamman
matan cikin tashin hankali domin sun san yanzu ana nan
ana nemansu. Yau da suka ga yadda mace ke wahala
wurin haihuwa kowannensu shiriya ta saukar masa.
Sannan ga adduar da tayi musu bayan taimakonta da
suka yi. Suna kallo aka shirya duk 'yan samari sa'aninsu
suka fice sai su kadai. Karshe ma shawara suka yanke
gobe zasu koma asibitin neman wannan matar daga n
[truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽26
Batul Mamman💖
Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora
ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta
shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume
da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi
"Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan
kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba".
Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa.
Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan.
Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta
mata rayuwa.
"Wane suna zaki saka mata?"
Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani.
"Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne".
Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina.
Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin
nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki
boye mata suna ne?"
"Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta
kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu."
Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi.
"Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar
radiyo yana nemanki".
Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau
jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana
kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji
muryarsa.
"Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a
aljihun wando yanzu na duba babu".
Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar
zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin
ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro
su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa.
"Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan
gida?"
Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace
"Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama
hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi."
Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai,
ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai
zan tambayeki na nawa za'a siyo?"
Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa
ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata.
Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada
kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar
dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya
fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye.
Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka
ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar
mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna
tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana
ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana
mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma
babu wanda ya kama kafarsa.
Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi
hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa
kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki."
Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan
hakan shine kike zaune dashi"?
"Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru
to sai dai hakuri."
Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda
kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar
Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da
kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan.
Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta
zauna bawa Asmau nata labarin.
"Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan
Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni
kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro
kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi
ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin
gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har
na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado.
Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne
shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko
Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru
mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo
daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar.
A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya.
Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani
sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji.
Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk
na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman
mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita
kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta.
Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya
dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana
Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na
gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke
wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata.
Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda
take sona ba."
Zulaiha ta share hawaye
"A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa
ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa
makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi
min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan
mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai
unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya
barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa.
Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan
shiga duniya."
A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai
"Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka
daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke
haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki
sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma
ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa
tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta
shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na
cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan
babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya
makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana.
Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya
auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada
akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai
daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne
kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya
zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina
da ya taba zuwa gidan nan."
Asmau taji tausayin Zulaiha sosai.
"Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran
mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka
ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya"
"Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi
dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a
makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu
zauna tare mu rufawa juna asiri".
Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma
dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma
abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi
ba.
*****
Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin
kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da
ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a
jiyan zai taho.
Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita.
Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo
basa nan.
Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami
wadda ta ga jikata Asmau."
Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa
"yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son
wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu
da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane
irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?"
"Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban
taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda
muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa.
Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada
kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba.
Kuma da kake cewa su ba wata tsiya

Please Login or Register in order to submit comment