Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

danna wayarsa aka turo masa wani
text da hoto. Da farko baiyi niyar bude hoton ba sai da
ya karanta labarin yarinyar a matsayin wadda mijinta ya
rasu ranar aure kuma aka gane tana da ciki. Tsaki yayi
sannan ya bude hoton don shi da Gaddafi yanzu karatu
suka saka a gaba.
Matar ya gani kyakkyawa da ita har ya ajiye wayar sai ya
sake daukowa ya duba hoton. Hannunsa na rawa ya
turawa Gaddafi yace ya duba ko ya gane ta. Ba jimawa
Gaddafi ya kira yace sai ya ga kamar matar nan mai ciki
da suka taimakawa mai suna Asmau. Matar da suka je
nema a asibiti basu sameta ba.
Tausayinta suka ji musamman da suka tuna halin da
suka tsinceta da irin nasiharta garesu. A cikin sati daya
suka yi ta bincike da tambaya ko akwai wanda ya santa
har suka dace da samun wani dan makarantarsu da yace
a unguwarsu abin ya faru a Kano. Yaron har gidan
Umma ya kaisu suka sanar da ita labarin haduwarsu dai
Asmau. A wannan ranar an sha kuka sannan Umma tace
ita ta hakura zata cigaba da yi mata addua. A duk inda
take Allah Ya tsareta kuma Yasa ta dawo gida da kafarta.
*BAYAN SHEKARA BIYAR*
Idan kaga Asmau bazaka ce itace tazo garin Jos a rame
da tsohon ciki ba. Duk da bata da jiki kamar da amma ta
dan samu nutsuwa. Ita da Zulaiha kuwa ko 'yan biyu
bazasu nuna musu kusanci ba. Tana tuka tuwo Zulaiha
na tsinke zogale taji sallamar Amatullah da Aliyu.
Da gudu Amatullah tazo ta rungumeta ta baya
"Ummina tuwo kike yi?"
Asmau ta bata rai "Ama so kike na kone zaki fado min
haka. Me ya dawo daku yanzu bayan ba'a tashi ba?"
Zulaiha tayi dariya "tunda kika ji ta kiraki da _Ummina_
kema kinsan akwai abinda take so".
Amatullah ta kama kasan dan hijab dinta tana wasa
dashi, Zulaiha ta dubi Ali "kai da kayi mata rakiya sai ka
fadi me ya dawo daku ai"
Ya ja baya da sauri "Umma nifa fitsari tace zata yi na
rako ta".
Asmau ta nuna hanyar bandaki "wuce kiyi kizo ku
koma".
Sum-sum Amatullah ta wuce bata dade ba ta dawo ta
sake tsayawa a bayan Asmau. Zulaiha ta kula akwai
abinda take so ta janyota jikinta
"Amatullah ta Ummi me kike so ne, fada min naji"
Dan turo baki tayi wanda duk lokacin da tayi sai Asmau
ta ga kamarta da babanta ta fito sosai Nabila ce take
shan kafi kaza kuma Ummi ta hanamu roko shine nazo
ta bani biyay na siyo".
Zulaiha ta kwashe da dariya "bakinki ne biyay din ai"
Amatullah ta dan buga kafa "Umma biyay nace fa ba
biyay ba".
Wannan karon Asmau ma tayi dariya. Amatullah bata iya
fadan duk kalma ma harafin *r*, idan ka fada yadda tayi
kuma tace sam ba haka ba.
Zulaiha ce ta basu naira biyar biyar ita da Ali suka tafi.
Asmau tace
" da baki basu ba. Sun baro makaranta takanas saboda
kwadayi. Yanzu gobe idan taga wani abin sake dawowa
zatayi."
"Na sani, rokon ne bana so tayi. Idan suka dawo sai a
kwabesu akan hakan. Amma da ban bayar ba karshenta
nan gaba bazamu sani ba sai da su roka a makarantar.
Asmau ta dage sosai kullum tana yiwa yaran lesson
musamman na turanci da larabci. Duk wanda yake da
homework zata zauna ta koya masa. A makarantunsu
'ya'yan gidan sun fita daban saboda kokarinsu. Ita kam
Zulaiha zuwan Asmau ya janyo mata alkhairi. Manyan
yaran Humaira, Muhsin, Amina da Habib duk
makarantar gwamnati suke yi. Anisa, Aliyu da Amatullah
kuwa a makarantar kudi mara tsada irin ta cikin unguwa
suke. Gabaday Asmau ta tattara hankalinta ga 'yarta.
Burinta a rayuwa yarinyar ta sami kulawa sosai ta kuma
san addininta don gujewa [truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽28
Batul Mamman💖
Da yamma Asmau ta dawo daga wurin aiki tun kafin ta
bude gate din taji kukan Amatullah. Ji tayi kamar an
tsikareta. A duniya babu abinda ta tsana kamar a taba
mata 'ya da rashin adalci domin kuwa indai Amatullah
tayi kuka a cikin gidannan baya wuce aikin Zinaru. Su
Humaira ji suke yi da ita balle tace anci zalinta. Da sauri
ta shiga ta sami Zinaru tsaye da bulala ta daga zata sake
dukan Amatullah ga Ali da Anisa a tsaye suna nasu
kukan. Asmau tayi saurin dauke 'yarta bulalar ta sauka a
bayanta. Don ma da mayafi amma ba karamin shigarta
tayi ba. Bata damu ba ta duba jikin Amatullah sai ga shati
lafcece a bayanta tana ta kuka da sheshsheka.
Kawar da kan da take yiwa Zinaru yazo karshe. Bazata
zuba ido a kashe mata 'ya ba. Cikin tsananin bacin rai ta
dago ido tana kallon Zinarun da ko a jikinta an kamata
tana dukan karamar yarinya haka.
"Me tayi miki kike mata irin wannan dukan?"
"Lallai Asamau wuyanki yayi kauri. Ni kike tsarewa da ido
haka kamar wata sa'arki. Ko zaki rama mata ne?"
Amatullah sai wani irin kuka take yi, Asmau ta tambayi
su Ali me suka yi.
Zinaru tace "jikokina babu abinda suka yi. Ba su nake
duka ba. Wannan afiruwar yarinyar da har yau ba'a san
ubanta ba ita na daka ehe. Na fada na sake nanatawa ta
dena kiran Gidadona da Baba taki ta dena. Kun zo kun
tare mana a gida kamar tare muka gina shi daku"
Rai a bace tace "akan wannan kike neman kashe min ita.
A iya zamanmu ban taba tanka miki ba idan kina cin
zalinta. Zulaiha ke shiga kullum. To ina so ki sani wallahi
kika kara taba min 'ya za'a ji kanmu dake. Na baki
girman da zan baki a matsayinki na uwa amma tunda
hakan baiyi miki ba zan zauna dake yadda kike so. Kuma
da kike cewa ba'a san babanta ba don Allah ki nuna
mana naki dangin ko na baban Gidado. Mtsww, gida
kuma yanzu na fara zama tunda kema ba naki bane."
Zinaru taji zafin maganganun Asmau "ni kike fadawa
haka saboda baki da mutumci. Ita Zulaihan ce ta fada
miki bamu da 'yan uwa?"
Asmau bata tsaya ta karasa sauraron Zinaru ba ta shige
daki. Da kyar ta rarrashi Amatullah tayi shiru har bacci
ya dauketa tana ta ajiyar zuciya. Kuka ne yazo mata da ta
tuna irin rayuwarta. Yau da a gidan aure ta haifi
Amatullah babu abinda zai fito da ita daga cikin danginta
har wani ya sami damar fada musu magana irin haka. Ta
tabbatar har ta mutu duniya bazata taba mantawa da
cewa a zina tayi cikin 'yarta ba. Ta cuci karamar yarinya
saboda soyayya.
Su Humaira sun dawo daga makaranta suma kannensu
ke fada musu abinda Zinaru tayiwa Amatullah. Duk sun
zo sun dubata har lokacin bacci take yi.
Bata farka ba sai bayan magriba da zazzabi mai zafi
jikinta sai rawa yake yi. Lokacin Asmau tana kan abin
sallah tana karatu taji fadowar Amatullah daga kan
katifarsu. Sauri tayi taje ta dagata taji jikinta yayi mugun
zafi. Hankalinta ya tashi ta rasa me zata yi mata. Da kuka
ta fito da ita a kafada ta tafi dakin Zulaiha wadda bata
dade da dawowa gidan ba. Har tana jin muryar Ali yana
fada mata Zinaru ta zane Amatullah. Ko sallama bata yi
ba ta shiga "Zulaiha taimakeni don Allah Amatullah zata
mutu."
Zulaiha ta bar kokarin cire kayan aikinta ta karbi
Amatullah tana salati. Kwantar da ita tayi akan katifa tana
ta karkarwa. Asmau ji take inama ciwon ya dawo gareta.
Ta matsa jikin bango ta jingina tana jira kawai ace mata
ta cika.
Amina ce ta shigo Zulaiha tace ta samo mata ruwa mai
kyau a roba da sauri. Asmau na kallo ta tubewa Amatulla
kayanta duk da sanyin da take ji da aka kawo ruwan ta
cire dankwalin kanta ta rinka guga mata ruwa a jikinta.
Kukan Asmau kai kace Amatullah ta rasu. Zulaiha tana
bata hakuri. Da taji zafin ya dan ragu tace bari ta cire
kayanta su tafi asibiti. Asmau ta dauki Amatullah ta
goyata suka fita. Yaran gidan duk jikinsu yayi sanyi. Kafin
su karasa asibitin da suke aiki numfashin Amatullah har
wani sama yake yi.
A asibitin emergency suka wuce likita da nurses suka
karbeta. Ana ta gwaje gwaje Asmau tana kuka kamar
ranta zai fita. Likitan ya fito ya bata takardar magani
sannan yace zazzabi ne mai zafi da kuma alamun
pneumonia(ciwon nemoniya ko sanyi da yake kama
kirjin yara).
Hankali a tashe Zulaiha ta karbi takardar da kudin
magani a hannun Asmau ta tafi ita kuma ta shiga dakin
da aka mayar da Amatullah. Idonta a bude sai dai ta fada
kamar ta dade babu lafiya. Tana ganin Asmau abinda ya
fara fitowa daga bakinta shine "Ummi ni waye Babana
ne? Zinayu tace Baba Gidado ba babana bane."
Wani kukan ne yazo wa Asmau. Yana daga cikin _abinda
ake gudu_ ki haifi yaro kafin aure ya tambayeka
mahaifinsa ki rasa amsar bayarwa. Tun farkon
haihuwarta take fargabar irin wannan lokacin. Ta
tabbatar idan Amatullah ta kara girma abin sai yafi haka.
Cike da nadama take tunanin da tana gidansu Yaya Jafar,
Yassar , Yaya Abdulhalim da Umar duk bazasu bar 'yarta
tayi maraici ba. Allah Sarki Abubakar ta fada a ranta. Yau
ga sakamakon rashin hakuri ta kusantar zina wanda ya
janyo musu fadawa ga yinta. Shekara biyar da faruwar
abin amma babu ranar da zata wayi gari bata tuna da
wannan yinin ba. Hawaye ta share ta kirkiro murmushin
dole "Ama babanki yana aljannah kinji ko. In sha Allah
yana can yana jiranmu. Kullum kika yi sallah kice Ya
Allah Ka yafewa babana Kasa shi a aljannah."
Ta zauna a kan gadon Amatullah tayi pillow da
cinyarta."Ummi yaushe zamu je aljannah wurin
babana? Ni yau nake son zuwa na fada masa Zinayu ta
dokeni. Sai ya yama min ko."
Asmau tace "zamu je watarana kinji. Amma ba yau ba
don Allah. Sai kin girma kin zama babbar malamar
addini kin tara yara da yawa".
Amatullah tayi dariyar jindadi "idan munje shine zai
kaini school. Ya siya min jaka mai kyau irin da takalmi.
Har kayan sallah fa." Kula tayi da hawayen da Asmau
take yi tace "Ummi ki dena kuka zai siya miki kema. Sai
mu tafi namu gidan ko?"
"Uhm" kadai ta iya cewa hankalinta yana wani wurin.
Yaya zata yi da Amatullah yarinya mai dan karen wayo.
Nan gaba kadan tasan zata sake tayar da zancen.
A haka Zulaiha tazo ta same su. An bawa Amatullah
maganinta da allurai sannan Zulaiha ta koma gida dauko
musu kayan kwana.
Cikin dan lokaci labari ya karade asbitin 'yar Asmau bata
da lafiya. Ma aikata da yawa suka rinka zo duba ta. Sai da
sawu ya dan dauke wata likita tazo tana yiwa Asmau
fadan irin dukan da take yiwa Amatullah wanda take
tunanin harda shi da kukan da tayi ya sa mata zazzabi.
Asmau ta tabbatar mata ba ita tayi dukan ba. Likita tace
to dai ta kiyaye don babu mai kular mata da 'ya kamar
ita kanta. Sannan dole a kula da hanata shiga sanyi da
kura don tana ganin alamun asthma gareta ba
pneumonia ba. Sake tsorata Asmau tayi. Tabbas
Abubakar yana da asthma ba abin mamaki bane idan
'yarsa tayi. Amma irin halin da taga yana shiga ga kashe
kudi wanda bata dasu sosai ya tayar mata da hankali.
Kwanansu uku sannan aka sallamesu. Kullum Zulaiha da
su Humaira indai ba aiki ba ko su suna makaranta a nan
suke zama sai dare su koma gida. Asmau kuwa taci
alwashin bazata sake yarda da Zinaru ta taba lafiyar
gudan jininta ba.
*****
Zinaru ce zaune a gaban wata kawarta da suke kasa kaya
a kasuwa take fada mata irin maganganun da Asmau ta
fada mata ranar da ta zane Amatullah
"Wato Kande maganganun sun kona min rai. Yarinya
kamar wannan ina ta kawar da kai duk da bana son
zamanta damu sai da ta kaini bango. Kuma ina ji lokuta
da dama tana ziga shegiyar nan Zulaiha akan ta rabu da
Gidado. Ni yanzu idan auren ya mutu ai ta tona min
asiri. Ina zamuje mu zauna. Gashi dan banzan yaron har
yau bai san ya girma ba. Daga shaye shaye sai neman
mata ya iya."
Kande ta tabe baki "tun farko ke kika yi sake. Ke da kike
da jari a hannu. Gidado ai *farar haihuwa* ne. Kina kalli
ya rasa matar aure sai Zulaiha ga 'ya'yan masu kudi a
gari. Kinsan mu da rauni akan mai kyau. Idan da hali kisa
ya saketa ita kuma bakuwar ku koreta ya auro sabuwa
'yar masu kudi".
"Kin kawo shawara Kande. Amma babbar matsalar shine
gidan nan nata ne. Ga yara har shida don bala'i haihuwa
kamar zomo. Don ma Allah Ya takaita mana ta tsaya.
Babbar fa zatayi shahudu yanzu. Kinsan auren kuruciya
suka yi."
"Duk wannan ba matsala bane. Ke dai ki samu yaron nan
ya dau saiti ya gyara kansa. Da kanki zaki bani labari. Kin
sanni da shige shige sai na tayaku neman mai maiko."
Tafawa suka yi sannan kowacce ta cigaba da ihun azo a
sayi kayanta.
*****
Kwanaki hudu a tsakani wurin karfe tara na dare Asmau
ta fito zata je bandaki taji Zinaru tana ambaton sunanta.
Tsayawa tayi taji abinda za'a ce tayi.
Daga cikin dakin Zinaru ke cewa Gidado "dole ne ka rabu
da Zulaiha hakan ne kawai zai sa Asamau ta bar gidan
nan. Zulaiha ma da dabara zaka saketa yadda zamu tsira
da gidan nan. Ka santa da son 'ya'ya sai ka ce mata ka
saketa amma tare da yaran zamu tafi. Nasan idan taji
haka zata bar maka gidan ita ta fita. Kande ta riga ta
samo mana 'yar wani kusa a gwamnati da zaka yi auren
jari da ita."
Gidado cikin muryar wanda giya bata gama sakinsa ba
yace "amma Zinaru idan muka yi haka kamar bamu
kyautawa Zulaiha ba. Kuma Asmaun nan na fada miki ita
ma sonta nake yi."
"Sakarai mara lissafi, Asama'un me. Ana maka zancen
'yar masu kudi. Yanzu dai ko da safe ne sai kayi yadda
nace."
Asmau ta jinjina bakin hali irin na Zinaru. Gashi Zulaiha
laulayi take yi babu wanda ya sani sai ita. Har kuka tayi
saboda bata son cigaba da haihuwa ga talauci da rashin
gata. Sauri tayi taje dakin Zubaida ta fada mata abinda
taji sai tayi tuntube da kwaftareren takalmin Gidado.
Zinaru ta fito da sauri taga ko waye suka hada ido da
Asmau. Ta dan ji tsoro da farko sai kuma ta dake ta
soma kwalawa Zulaiha kira.
Cikin bacci taji kiran da Zinaru ke yi mata ta fito tana
murza ido. Zinaru tace "munyi magana ne da Gidado
akan yadda Asamau ta raina ni da irin rashin jituwar
dake tsakaninmu shine yace zai koreta. Ni kuma sai na
tuna masa cewa gidan nan ba namu bane. To yanzu yake
fada min wai ko dai ki sallameta da kanki ko kuma ya
sakeki mu tafi mu bar miki gidan."
Zulaiha ta rude "me yayi zafi Gidado har da zancen saki?
Zinaru ki bashi baki don Allah."
Asmau tace "wallahi karya take yi Zulaiha. So take ya
sakeki ki bar musu gidan".
Zinaru ta kalli Gidado
"Ince dai kaga irin yadda take yi min. Ni bazan zauna a
gidan nan ana wulakanta ni ba".
"Zinaru kiyi hakuri indai Zulaiha ce yanzu zan saketa mu
tafi"
Yaransu duk suna kallo ita Asmau har ta soma jindadi
sai kawai Zulaiha ta durkusa a kasa ta rike masa kafa tana
kuka"ka rufa min asiri Gidado kada ka sakeni. Ina zani da
yaran nan."
Muhsin ya dagata tsaye "Umma kawai ki bari ya sakeki
kema kya huta da duka da wankin amai. Dama don ke
kike yi ne nake tayaki amma daga yau sai muga mai
wanke masa"
Bakin Muhsin din ta daka "waye ya saka bakinka. Ku bar
wurin nan kafin na bata muku rai."
Suna tafiya ta cigaba da rokonsu shi da babarsa. Zinaru
ma tasa kukan karya ita dole su bar gidan. Ganin haka
Asmau tace "indai saboda ni ne to in sha Allah da safe
zan tafi. Zulaiha ki tuna da gatan da Allah Yayi miki ki
koma gaban iyayenki. Gobe nima gidanmu zan tafi na
roki nawa iyayen gafara".
Daga haka ta bar wurin. Wannan wane irin so ne Zulaiha
ke yiwa Gidado. Tausayi take bata don wannan ba
karamar jarabawa bace. Mutum ya mayar da kai bolarsa
amma ka kasa rabuwa dashi.
Da kuka Zulaiha ta biyo bayan Asmau."kiyi hakuri Asmau
ki zauna gobe zan sake rokonsu."
"Zulaiha a kaina bazan so kiyi ta zubar da mutumcinki a
gaban su Humaira ba. Ni dai shawarata ki koma gida ki
roki gafarar su Inna".
Zulaiha tayi shiru. A yadda zuciyarta ta karaya bata jin
zata iya zuwa gaban iyayen da ta yiwa rashin kunya
harda kaisu kara.
*****
Karfe goma na safe Asmau ta gama hada 'yan kayanta da
na Amatullah. Tayi mata wanka suka shirya tafiya. Daga
kan Humaira har Ali kuka suke yi basa son tafiyarta.
Itama kukan take yi amma gara ta koma gida. Kewar
iyayenta ta dameta gashi duk inda ta zauna sai wani dalili
ya koreta.
Kamar bazasu rabu ba ita da Zulaiha kowa kuka ta rike
hannun Amatullah suka fita.
Tasha suka je bata dade ba motar Kano ta cika suka fito.
Sunyi tafiya mai dan nisa sun wuce wani gari Saminaka
ba jimawa suka ga wani mutum yana daga hannu
alamar neman taimako. Gefensa mace ce babba da
dogon hijab sai wata 'yar budurwa da bazata kai shekara
ashirin ba. Dreban farko kamar kada ya tsaya sai kuma
yaji tausayin dattijuwar suka tsaya. Motarsu ce ta lalace
ga makanike yana dubawa amma yace injin ya buga sai
an sauke shi. Su Asmau suka marmatsa matar da
yarinyar suka shigo. Aka bar dreban da makanike.
Sallama tayi musu suka gaisa tare da yi musu godiya.
Ta kalli Amatullah da ke zaune a cinyar Asmau tayi mata
murmushi.
"Yan mata yaya sunanki"
"Safinatu Abubakay. Amma Ummina Amatullah take ce
min ko Ummi"
Asmau tayi dan murmushi kawai. Fargabar zuwa gida ce
fal a zuciyarta. Ita kuwa dattijuwar tace "Safinatu
Abubakay ko Abubakar" tana yar dariya.
Amatullah tace "Abubakay nace ba Abubakay ba"
Mutane da yawa a motar sai dariya. Can ta dan taba
matar nan "kema aljannah zaki je? Ni da Ummi can
zamu wurin Babana. Ban taba ganinsa ba, Zinayu zai
zane saboda tana duka na."
Asmau ta dan kai mata duka saboda suruta sannan ta
share hawaye. Matar nan tana kallonsu sai taji tausayinta
ya kamata. A hankali yadda Asmau zata ji tace "Allah Ya
jikansa"
Asmau ta dago kai tace "Amin" wani hawayen yana fita a
idonta.
Sun iso Kano garin da hadari ga kura. Tana kokari daukar
kayansu ne ta ga Amatullah ta dafe kirji numfashi baya
sauka. A gigice ta saki jakar ta rungumota tana kuka. Yau
kam ta tabbatar asthma gareta saboda yadda take
kokarin numfashi yaki sauka.
Wannan matar da wasu maza suka taho wurinta. Dreban
da yazo daukar matar yana zuwa tace Asmau ta tashi su
tafi asibiti. Kuka take yi kawai ga Amatullah ta sandare.
Wani asibitin kudi suka je aka karbi Amatullah. Tana ji
matar tana waya tana sanar da wani inda suke.
Bayan kamar awa daya an samu Amatullah ta dawo
hayyacinta suna wani daki Asmau sai godiya take yiwa
matar taji an turo kofar dakin tare da sallama. Wani
daddadan kamshi ne ya mamaye dakin kafin ta kula da
mutumin da ya shigo cikin shigar sojoji masu babban
mukami.
Amatullah dake kwance ta tashi zumbur tace
" Ummi wannan ne baban nawa?".
ABINDA AKE GUDU🙆🏽29
Batul Mamman💖
Dan tsayawa yayi yana kallon kyakkyawar yarinyar. Tana
daga zaune harda ware hannuwa ta dan bata rai "Baba
bazaka yi min oyoyo ba? Nima bazanyi maka ba. Shine
ka taho aljannah ka barmu ni da Ummi."
Asmau kunya ta isheta ta kai hannu zata hana Amatullah
sai matar ta girgiza kai.
Taku yake mai cike da kamala da kuma kwarjini ya
karasa daya barin gadon ya zauna yana murmushi.
Asmau ta kasa daga ido ta kalle shi. A kan gadon ya
zauna ya janyo Amatullah ya dorata akan cinyarsa.
"Oyoyo baby din Baba. Kiyi hakuri bazan kara tafiya na
barki ba kinji"
Amatullah ta kankame shi ya dago kai ya kalli
mahaifiyarsa yana murmushi. Juyowa yayi inda Asmau
take zaune suka hada ido ba shiri ta kara sunkuyar da
kanta. Mutumin ba karamin kwarjini yayi mata ba. A
kalla zai kai shekara arbain. Kayan jikinsa sun kara masa
kyau. Shi kuwa mayar da hankalinsa yayi ga Amatullah
yana shafa mata kai. Girmansa da matsayinsa bai sa ya
kyamaceta ba. Muryarta ya sake ji tace "Baba idan anje
aljannah ba'a zuwa gida ne. Kullum ni da Ummi bamu
ganka ba. Kuma Zinayu sai tayi ta dukana baka zuwa ka
yama min".
Sake hada ido suka yi da Asmau ya kula da kwallar da ta
cika mata ido. Wani tausayinsu ne ya shige shi a lokaci
daya. Ko ba'a fada ba yasan baban yarinyar nan ya rasu.
Wannan ne dalilin da zaisa yarinyar ta rinka ambaton an
tafi aljannah an barsu.
Tana daga jikinsa yace "daga yau duk wanda ya sake
tabaki sai na rama miki kinji."
Matar da tayi masa waya tace "ai wannan Zinayu taga ta
kanta. Tun dazu ake kawo kararta."
Amatullah tace "Zinayu nace fa ba Zinayu ba".
Daga matar har danta sai da suka yi dariya sosai. Asmau
ta gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake yana kallon
Amatullah. Yarinyar ta shiga ransa lokaci guda.
Matar ya kallo yace "Hajiya gara kizo ku tafi gida nasan
kin kwaso gajiya da yunwa. Munyi waya da Falalu za'a
janyo motar gobe. Da kinyi min waya tun kuna hanyar ai
da na turo mota daga Jos din."
Murmushi tayi "kai babu komai fa. Na tura Bilkisu da
Shafiu a siyo musu abinci ne kafin mu tafi."
Ta dubi Asmau "kin kira 'yan uwanki kuwa? Ya kamata a
san halin da kuke ciki kada suji shiru"
Shiru Asmau tayi, to ita wa zata kira bayan yanzu bata da
numbar kowa a gidansu. Ta sunkuyar da kanta kasa
kawai ta sako karya "babu kudi ne a wayar, amma nasan
zasu kira idan suka ji shiru."
Hajiya ta dan bata rai "haba ke kuwa, me ya hana tun
dazu kiyi min magana da tuni an siyo ko na baki tawa ki
kira. Kai taimaka a samo mata kati ta kira gidansu. Wane
layi gareki?"
Ba karamar kunyar taji ba. Tayi karya sun dauka gaske
ne. Duk da dai kudin wayar dama bai wuce flashing ba
tace "MTN".
Cikin ladabi ya mike zai fita Amatullah ta riko masa riga
kamar zatayi kuka "Baba zan bi ka"
Wata waya da Asmau ta tabbatar mai tsada ce ya zaro
daga aljihunsa ya mika mata "gashi ki rike min yanzu zan
dawo"
Bata so ba haka ta sake shi ya fita. Kafin ya dawo Bilkisu
ta shigo dauke da ledojin take away na abinci. Shima
mutumin sai gashi ya dawo ya mikawa Hajiyarsa katin ta
bawa Asmau. Na dubu daya da dari biyar ne guda hudu
duka matar ta bata. Tayi ta godiya a son ranta daya ma
ya isa.
Bilkisu ta durkusa har kasa tace "Uncle ina wuni"
"Lafiya kalau, ya gajiyar hanya?"
Ta amsa masa da lafiya, ya shiga tambayarta kanwarsa
dake Jos wadda ta kasance mahaifiya ga Bilkisun.
Asmau dai kashe wayarta tayi sai tayi kamar ta saka katin
guda daya sannan ta tashi ta koma gefe kamar tana waya
don karfin hali harda kwatancen asibitin.
Bata san duk abinda take yi Soja na kallonta ba. Mamaki
ne ya kama shi da ya fuskanci me take yi. Tana juyowa
suka hada ido yayi mata wani irin kallo. Babu shiri ta
sauke nata idon ta basar duk da idanunsa sun tsorata ta.
Hajiya ta tashi "to mu zamu tafi ni sunana Hajiya
Lubabatu wannan jikata ce."
Bilkisu na dariya tace "Uncle kuma dan fari da ba'a fadar
sunansa"
Ya kai hannu zai rankwasheta "Hajiyar tawa kike tsokana
ko. Hajiyata kyaleni da wannan yarinyar zan miki
maganinta."
Kana ganin Haj Lubabatu kunya take ji bata son wasa da
dan nata.
Asmau tayi murmushi tace "ni sunana Asmau. Nagode
sosai Hajiya Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi"
"Amin, gobe in sha Allah zamu dawo don nasan dakyar a
sallameku. Idan mutan gidan sun zo ki gaishesu"
Asmau tace to ta tashi zata rakasu Haj Lubabatu ta dan
tsaya ta dauko wayarta daga jaka ta mikawa Bilkisu "bani
numbarki saboda kira ko da akwai wani abu."
Duk da ta gode da taimakon da matar nan tayi mata
amma bata so alakar tayi tsaho. So take yi ta koma gida
asirinta a rufe. Yanzu da Amatullah babu lafiya dai bazata
iya tafiya ba don bata san yaya zasu tarbeta ba, bai
kamata taje musu da lalurar 'yar da suka so a zubar da
cikinta ba. Number kawai ta kirkira da ka ta karanto
Bilkisu ta kwafa a wayar Hajiya.
Hajiya sai sake cewa tayi "yauwa to kirata sai ta samu
tawa numbar a wayarta ko."
Ji tayi cikinta ya murda kada asirinta ya tono. Sa'arta
daya ta kashe wayar tace "wayar ta mutu yanzu amma
zan saka chaji idan an kawo wuta"
Haj Lubabatu tayi murmushi "to babu komai. Ga abinci
nan ki tabbatar kin bata yanzu. Safinatu Allah Ya baki
lafiya kinji".
Daga haka Haj Lubabatu ta fita Asmau na binta da sakon
addua. Shima dan nata zai fita Amatullah ta dage shi zai
bata abinci ba Umminta ba. Da murmushi a fuskarsa
yace mata yanzu zai dawo ba nisa zaiyi ba. Yana dago kai
Asmau ya gani tana kallonsa don tabbatar da abinda
yace. Wannan karon murmushin da yayi mata mai nuni
da ta kiyayi dawowarsa sannan ya fita. Ai kuwa ta hau
Amatullah da fada akan me zata ce ya bata abinci.
Yarinya ta bare baki tana kuka, takaici duk ya ishi Asmau
don ta tabbatar zai dawo tunda ya sake barin wayarsa.
*****
Har bakin mota ya raka su Hajiya tana tambayarsa
yaushe zai tafi gida yace yana son lallaba yarinyar nan ne
saboda kada tayiwa mamanta rigima.
Haj Lubabatu tace "Allah Sarki ai nima ta bani tausayi.
Karshenta tana yarinya sosai uban ya rasu shiyasa ta
damu da ganinsa yanzu. Nasan dole hakan ya rinka
dagawa babarta hankali."
"Nima haka kawai naji ta shiga raina Hajiya"
Da alamun tausayi a fuskarta tace "ai na sani, kai da son
yara kuma. Bari mu wuce sai ka dawo"
Bai bar wurin ba har sai da motar ta fita daga gate din
asibitin sannan ya koma ciki. Hankalinsa sam bai kwanta
da Asmau ba. Yana tunanin ko dai irin matan nan ne
masu damfara ko kuma tana da sirrin da bata so a sani.
*****
Amatullah sai kuka take yi saboda irin fadan da Asmau
take yi mata.
"Idan baki rufe min baki ba nida ke ne. Haka kawai daga
ganin mutum sai ki dage shine babanki. To nan ba
aljannah bane kuma na fada miki yana can.

Please Login or Register in order to submit comment