Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

bane to a wurina
sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda
kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya
yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana
gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take
mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali.
Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar
Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma,
Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar
, Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi.
Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta
ba.
Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua
suke yi Allah Yasa su dace a sameta.
Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar
da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata
hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta.
Ai tunda matan gidan suka ga bakin dake shigowa tare
da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma
fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace
meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke
yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan
lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai,
kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai
barkwanci da yawan wasa.
Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata
ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri
ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma.
"Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min
ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan
fa?"
Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar
da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take"..
Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali.
Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To
nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar
da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar
Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba".
Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har
bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace
'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata
musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki
zanyi sai naga wanda ya tsaya miki."
Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na
basu hakuri.
Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake
sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga
Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta
gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta
da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya
aureta.
Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada
musu inda Asmau taje.
Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta
suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan
ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka
ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...."
Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida
tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama
suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi
iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin
da kayan Asmau suke.
Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara
tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari
sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi
kayan tana kuka.
Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya
tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya
santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata
wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida.
Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan
nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni
ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki
idan aka ji wacece ta haifeki."
Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita
tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba.
Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo
hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine
da goro suka fito.
"Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da
adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar
bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma
kinyi kin gama da yardar Allah."
Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga
kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta."
Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki.
Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da
bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya
kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti.
Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida
tayi iyaye da miji in ce dai shikenan."
Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa
bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga
nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar
kyautatawa Asmau.
*****
Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da
wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun
sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan
Sada.
Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama.
Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana
bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa.
"Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine
bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga
ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya
da gaskiya kun hau kun zauna."
Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan
zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...."
Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba.
Wayyo Allah na"
Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda
ya janyo shigowar sauran mazan.
Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?"
Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin
suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana
ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau.
Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru
da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace
"amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba."
Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini
tsufa"
Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora
bazasu fi goma ba"
Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da
tsufansu suke fadan shekaru.
Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru
don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace
ya ganta?"
Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu
bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare
har zuwa Jos ne.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽26
Batul Mamman💖
Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora
ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta
shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume
da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi
"Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan
kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba".
Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa.
Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan.
Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta
mata rayuwa.
"Wane suna zaki saka mata?"
Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani.
"Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne".
Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina.
Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin
nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki
boye mata suna ne?"
"Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta
kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu."
Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi.
"Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar
radiyo yana nemanki".
Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau
jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana
kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji
muryarsa.
"Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a
aljihun wando yanzu na duba babu".
Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar
zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin
ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro
su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa.
"Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan
gida?"
Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace
"Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama
hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi."
Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai,
ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai
zan tambayeki na nawa za'a siyo?"
Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa
ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata.
Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada
kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar
dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya
fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye.
Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka
ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar
mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna
tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana
ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana
mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma
babu wanda ya kama kafarsa.
Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi
hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa
kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki."
Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan
hakan shine kike zaune dashi"?
"Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru
to sai dai hakuri."
Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda
kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar
Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da
kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan.
Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta
zauna bawa Asmau nata labarin.
"Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan
Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni
kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro
kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi
ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin
gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har
na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado.
Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne
shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko
Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru
mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo
daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar.
A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya.
Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani
sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji.
Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk
na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman
mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita
kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta.
Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya
dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana
Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na
gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke
wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata.
Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda
take sona ba."
Zulaiha ta share hawaye
"A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa
ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa
makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi
min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan
mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai
unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya
barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa.
Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan
shiga duniya."
A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai
"Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka
daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke
haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki
sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma
ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa
tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta
shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na
cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan
babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya
makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana.
Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya
auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada
akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai
daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne
kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya
zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina
da ya taba zuwa gidan nan."
Asmau taji tausayin Zulaiha sosai.
"Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran
mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka
ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya"
"Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi
dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a
makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu
zauna tare mu rufawa juna asiri".
Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma
dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma
abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi
ba.
*****
Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin
kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da
ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a
jiyan zai taho.
Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita.
Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo
basa nan.
Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami
wadda ta ga jikata Asmau."
Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa
"yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son
wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu
da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane
irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?"
"Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban
taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda
muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa.
Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada
kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba.
Kuma da kake cewa su ba wata tsiya bane to a wurina
sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda
kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya
yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana
gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take
mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali.
Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar
Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma,
Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar
, Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi.
Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta
ba.
Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua
suke yi Allah Yasa su dace a sameta.
Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar
da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata
hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta.
Ai tunda matan gidan suka ga bakin dake shigowa tare
da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma
fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace
meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke
yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan
lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai,
kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai
barkwanci da yawan wasa.
Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata
ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri
ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma.
"Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min
ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan
fa?"
Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar
da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take"..
Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali.
Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To
nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar
da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar
Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba".
Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har
bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace
'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata
musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki
zanyi sai naga wanda ya tsaya miki."
Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na
basu hakuri.
Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake
sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga
Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta
gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta
da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya
aureta.
Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada
musu inda Asmau taje.
Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta
suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan
ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka
ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...."
Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida
tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama
suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi
iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin
da kayan Asmau suke.
Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara
tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari
sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi
kayan tana kuka.
Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya
tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya
santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata
wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida.
Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan
nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni
ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki
idan aka ji wacece ta haifeki."
Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita
tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba.
Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo
hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine
da goro suka fito.
"Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da
adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar
bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma
kinyi kin gama da yardar Allah."
Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga
kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta."
Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki.
Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da
bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya
kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti.
Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida
tayi iyaye da miji in ce dai shikenan."
Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa
bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga
nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar
kyautatawa Asmau.
*****
Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da
wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun
sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan
Sada.
Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama.
Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana
bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa.
"Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine
bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga
ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya
da gaskiya kun hau kun zauna."
Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan
zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...."
Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba.
Wayyo Allah na"
Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda
ya janyo shigowar sauran mazan.
Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?"
Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin
suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana
ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau.
Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru
da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace
"amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba."
Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini
tsufa"
Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora
bazasu fi goma ba"
Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da
tsufansu suke fadan shekaru.
Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru
don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace
ya ganta?"
Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu
bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare
har zuwa Jos ne.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽27
Batul Mamman💖
Qasim yayi alkawarin zuwa neman Asmau daga kauyen
farko har Jos din. A sanyaye suka koma gidan Sada
wadanda suke ganin sun zame musu 'yan uwa
sakamakon kyautatawar da suka yiwa Asmau. Duka
kayanta Rashida ta hada musu harda na jariran. Umma
dai tasha kuka har ta gode Allah. Su Anti Binta, Shema'u
da 'ya'yan Mama su Suwaiba duk sunyi ta kira su ji yaya
ake ciki.
Da zasu tafi har bakin mota Rashida da Sada suka yi
musu rakiya aka karbi numbar wayar juna.
Qasim ya cika alkawari wurin binciken Asmau sai dai
babu wani abin arziki da ya samu duk da haka bai
hakura ba. Duk inda yaji alamar anga mace da ta bata sai
ya duba ko za'a dace.
*****
Humaira babbar 'yar Zulaiha ke zaune gaban Asmau tana
jira ta gama sakawa Amatullah kaya a goya mata ita.
Zulaiha tace "Asmau kada ki goya mata ita kin santa da
rawar kai. Tsorona daya kada garin rashin nutsuwa su
fadi shiyasa idan tace na goya mata nake hanawa".
"Umma da gaske zan nutsu bazan yar da ita ba. Ni da har
girki nake yi miki amma sai ki hana ni goyo".
Asmau ta dauko zani cikin wanda Zulaiha ta bata "tashi
kinji babbar Yaya na goya miki ita. Ai nasan ko bakin
kofar gidan bazaki je ba a nan zaku zauna"
Duk yadda Zulaiha taso hanawa haka akayi goyon
Humaira ta fita tsakar gida tana murmushin jindadi.
Asmau ta sauke ajiyar zuciya. Watansu uku a gidan nan
lokaci yayi da ya kamata ta fara neman aikin yi ko don ta
ragewa Zulaiha nauyi. Ga Zinaru kullum tayi zancen
kudin haya sai Zulaiha tace mijin Asmau ne ba'a
samunsa ko da a waya. Gori kala kala take sha akan
abincin da suke bata wanda ba danta ke nema ba. Gyara
zama tayi yadda zata rinka hango Humaira da kyau
sannan tace da Zulaiha
"Nasan kina kokari sosai tun zuwana Allah Kadai zai baki
lada. Amma ya kamata na nemi aiki. Saboda Amatullah
dai nasan babu gidan da zasu daukeni kuma gashi bani
da wata takardar makaranta. Shine nayi tunanin ko zan
sami irin naki sai nayi".
Zulaiha ta katse ta "haba Asmau, yarinyar nan har nawa
take da zaki fara neman aiki? Ki bari ta kara kwari. Ni
zamanmu dake duk wahalar da zan sha ban dauketa
komai ba. Na dade ina rayuwar kunci da rashin
makusanci kafin zuwanki."
"Duk da haka gara nayi aikin ko don na taimaka miki. Ki
duba fa tunda nazo su Muhsin basu taba zuwa
makaranta ba saboda rashin kudi."
Zulaiha tasan gaskiya Asmau ke fada sai dai kuma tana
tunanin kankantar Amatullah. Shawara suka yanke
washegari da taje aiki ta sami makociyarsu wadda tayi
mata hanya. Da taimakon matar nan Allah Yasa Asmau ta
sami aikin itama.
Yanayin aikin nasu da wuya suje tare. Juya musu akeyi
idan wasu suka yi na safe wasu sai suyi da yamma.
Hakan yayi musu dadi kodayaushe akwai mai zama da
yaran a gida.
Asmau sai ta goya Amatullah ta tafi aikinta tunda bata isa
a fara barinta a gida ba. Da yake yarinyar akwai dariya ga
dan jiki sai tayi saurin shiga ran sauran ma'aikatan. Idan
Asmau zata wanke bandaki sai a rike mata ita taje tayi
aikin. Tunda ita mace ce mai ilimi sai ya zamto tafi
sauran mayar da hankali wurin tsaftace duk inda ta
gyara. Albashinta na farko kaya ta siyawa Amatullah har
kala biyar da Ali autan Zulaiha. Sauran kudin kuwa kayan
abinci ta siyo musu. Zulaiha sai godiya take yi mata har
tayi mamaki ita da ake ta dawainiya da ita.
Zamansu haka yayi ta tafiya cikin lumana da taimakon
juna. A hankali likitoci da dama suka san Asmau saboda
tsaftarta zance har wajen Chief Medical Director
(shugaban asibiti). Da yaji yadda ake yabonta da son
cigabanta tunda har turanci ta iya sosai ya canja mata
aiki daga shara zuwa bada kati. Ba karamar murna
sukayi ba saboda albashi ya karu. Ko kadan babu
hassada tsakaninta da Zulaiha. Karshe ma aka mayar da
ita bangaren bada sakamako idan anyiwa mutum gwaji a
asibitin. Dan ihsani kuwa daga nurses da likitoci tana
samu sosai a dalilin Amatullah.
Bata da wata matsala a lokacin sai Gidado da Zinaru.
Daga ita har Zulaiha basa jindadin zama dasu. Kudin
hayar daki kuwa taki bawa Zinaru a hannunta kamar
yadda take ta naci. Su Humaira aka mayar makaranta.
Shi kuma Gidado baya shakka ko a gaban Zulaiha baya
iya boye son da yake yiwa Asmau. Ya sha nemanta sai dai
taki bashi hadin kai kuma kullum haka ta faru sai ta
fadawa Zulaiha don gudun matsala. Tayi ta yiwa Zulaiha
nasihar rabuwa dashi sai dai tayi murmushi kawai.
Wannan ya tabbatar mata da cewa har yanzu Zulaiha na
son mijinta. Sai ta kyaleta suka cigaba da zamansu.
*****
Annur yana kwance a daki bayan ya dawo daga
makaranta yana dan

Please Login or Register in order to submit comment