Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwa. Allah Ka yafe mana baki
daya. Ka zaba mata miji nagari tsakanina da Ishaq. Idan
aurenta ba alkhairi bane garemu Ka kaita gidan da za'a
so ta dominKa."
Tashi yayi yayi shirin masallaci. Yana ganin janyewa
kawai zaiyi amma zai tsaya mata sosai idan ta tashi aure.
Dole mijin da zata aura ya kasance mutum da za'a iya
yarda dashi. Mai amana. Shi kadai yayi murmushi da ya
tuno irin kalaman da Col.Ishaq yake fadawa Asmau.
Hmmm dole ta so shi ma. Shi kam ya manta rabonsa da
tsara mace irin haka. Tun zamanin yana Qasim mai shafe
'yan mata. Rasuwar Abubakar tasa duk tunanin soyayya
ya fice masa a rai. Kila harda rashin wannan yasa Asmau
bata sauraron shi sosai. Mata da son soyayya kuma....
*****
Haj Lubabatu ke faman fifita an dauke wuta saboda
hadarin da ya hado. Ta kira Bilkisu da ke zaune wurin
taga tana ganin haske tana karanta littafinta na
makaranta saboda test da zatayi washegari.
"Bilkisu ina babanki ne? Na zata ya dawo amma naji shi
shiru tun dazu."
"Ya dawo Hajiya, na kai masa abinci ma"
"Duba min kiga me yake yi a ciki tun dazu. Kwanakin nan
sai kace wata amarya bashi da aiki sai zaman daki"
Dariya Bilkisu tayi "Hajiya ita amarya zaman daki take
yi?"
"Ban sani ba. Wuce ki duba ga magariba ta kawo kai."
Da sallama Bilkisu ta shiga dakin. Duhu ta gani duk
labulayen a sauke ga zafi. Daga kan gadon ta hango shi a
kwance ya rike kansa. Saurin karasawa tayi bakin gadon
"Uncle Ishaq" ta kira shi a hankali.
Da kyar Col. Ishaq ya iya bude idanunsa. Kansa ke masa
wani azababben ciwo kamar zai tsage. Kwana uku kenan
yana fama amma na yau yafi tsanani.
"Uncle baka da lafiya ne, bari na fadawa Hajiya."
Ta tashi zata fita wayarsa tayi ringing. Bata yi niyar dauka
ba sai da yace "dauki wayar nan Safiyya ce take kira tun
dazu. Idan kin amsa ki kasheta kawai. Ga dayar can a
kusa da tv itama ki kashe"
Muryarsa da kyar take fita. Hankalin Bilkisu a tashe ta
dauki wayar ta fita. Karawa tayi a kunnenta tace "Anti
Safiyya bashi da lafiya Uncle din. Kamar ciwon kan nan
da yake na bari..."
Gaban Asmau ne yayi mugun faduwa. Baki na rawa tace
"Bilkisu nice Asmau. Tun yaushe ne bashi da lafiyar?"
Dan sauke wayar Bilkisu tayi daga kunnenta ta duba
sunan. MJ ta gani wanda ta gane yana nufin Matar
Jikamshi saboda ta taba ji Uncle din nata ya fada.
"Anti Asmau yi hakuri ban san kece ba. Yanzu na shiga
dakinsa na ganshi a kwance. Zan fadawa Hajiya ne ko
za'a kai shi asibiti. Dama yana yi idan baya samun hutu
sosai."
Idanunta har sun ciko da kwalla , duk abinda tayi niyar
fada masa na bacin rai tuni ta manta. Sake rike wayar
tayi da kyau tace " Bilkisu don Allah ki kai masa wayar
kinji."
Ta san baya son komai idan yana wannan ciwon
musamman surutu. Amma kuma bazata iya cewa Asmau
a'a ba. Juyawa tayi ta koma dakin. Yana nan inda ta
barshi a kwance ta dan kara masa wayar a kunnensa tayi
saurin fita kafin yayi mata fada.
Asmau ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta tare dashi.
Allah sarki Jikamshinta. Ashe bashi da lafiya shiyasa
kwana biyu ta dena jinsa. Haushin kanta taji da har da
tayi niyar nuna masa fushinta saboda baya kiranta kuma
baije gidansu ba.
Yanayin canjin numfashin da take iya ji yasa ta gane an
bashi wayar. Mamakin karfin halin Bilkisu yake da ta
kawo masa a halin da yake ciki. Bari ya warke zata fada
musu. Rashin Asmau yasa shi shiga damuwa sai yayi ta
dadewa wurin aiki. Hakan ya tayar masa da ciwon kai.
Sai kuma ga text da tayi tana fada masa yadda suka yi da
Qasim akan zasu sake turowa. Tsabar kishi ne da rashin
sanin me ya kamata yayi ya kara kwantar dashi. Kamar
ba soja ba ya kasa daurewa zuciyarsa yaje ya fada mata
ya janye. Dena kiranta a waya din ma ba karamin juriya
yayi ba.
Muryarta mai sanyi yaji tace "Jikamshina me ya
sameka?"
Bugawa zuciyarsa tayi da karfi da yaji muryarta babu
zato babu tsammani. Ba karamin dadi yaji ba ya ratsa shi
har ya dan manta da ciwon kan na 'yan dakiku. Bai iya ce
mata komai ba sai manna wayar da ya sake yi a
kunnensa. Ita kuma ta sake rudewa ko ciwon yayi
tsanani ne
"Jikamshina nice, matarka ce, kayi min magana don
Allah."
Shiru da ta cigaba da ji ne ya sakata kuka. Dama kullum
haka take kamar tana jiran kiris.
Kukan nata murmushi ya saka shi babu shiru. Idon kuka
kenan ya fada a ransa kamar yadda yaji a gidansu.
"Its ok ki dena kukan"
Cikin shagwaba tace "Kaji sauki? Ina da ina ke yi maka
ciwo? Me yasa baka fada min ba kawai naji ka shiru"
Ta so saka shi dariya yadda yake jin muryarta a hankali
amma tana rawa alamun kukan nata bai kare ba
"I miss you too" taji yace a wahale saboda ciwo.
"Uhmm?"
"Duk wannan tambayoyin nan nasan abinda kike son
cewa kenan. Kinyi missing dina. But I miss you more
Matar Jikamshi. Kin hana Ishaq sukuni."
Jin kanta take kamar anyi mata wani babban albishir da
taji muryarsa har ya fara tsokana yadda ya saba. Ta kara
kashe murya
"Nima ka hana ni. Har dan wuya nayi. Kasa naji ina kara
....uhmm....na fasa fada"
Sautin dariyarsa taji. Dama Asmau ce ciwon kuma ita ce
maganin. Ajiyar zuciya yayi yana gyara kwanciya
"Yanzu ina kwance babu lafiya ma sai kinja min rai. Ki
tausayawa patient."
"Kasha magani ne?"
"No, muryarki kadai ta isheni magani. Yau ki shirya
zamuyi ta waya har sai kunnenki ya gaji"
Kamar yana gabanta tayi dan fari da ido "bana fatan
gajiya da kai Jikamshina. Baban Ama _da kannenta_"
Yaji dadin furucinta amma kalmar karshe ta dawo masa
da tunanin da yake addabar zuciyarsa.
"Matar Jikamshi ina son ganinki. Akwai magana mai
mahimmanci da zamuyi kinji"
Tunanin maganar aurensu ne yazo mata tace "to Allah Ya
kaimu. Ka bari sai kaji sauki sosai. Dama duk na damu ne
da naji ka shiru."
"Ki kular min da kanki." Ya iya cewa zuciyarsa babu dadi
ya ajiye wayar.
Motsi yaji a wurin kofa ya juya. Hajiya ce a tsaye bai san
tun yaushe take a wurin ba. Abin mamaki sai yaji 'yar
kunya kadan ba da yawa ba. Itama basarwa tayi ta shigo
ciki kamar bata ji komai ba.
"Zaka je asibitin ko kaji sauki? Ni a yadda Bilkisu ta fada
min na zata ciwon sosai ya kamaka"
"Sosai ne mana Hajiya. Kamar kan zai tsage haka nake ji"
Tayi dan murmushi kawai "ai naga kamar ka sami
magani."
Dariya ta bashi ya tashi zaiyi alwala. Fita tayi tace idan
anyi magriba lallai yaje asibiti don tasan ciwon kan baya
masa da wasa.
*****
Bayan isha Asmau da Amatullah suna gwada sabon
dinkinsu da Yassar ya karbo musu taji waya. Ringtone
din Jikamshi daban yake shiyasa ta gane shi. Da fara'a ta
dauka don tun wayarsu ta dazu hatta su Umma sun ga
canji a tare da ita. Kafin tayi magana yace "fito ina
jiranki"
Har wani faduwar gaba taji. Tayi kewarsa sosai amma
tana jin kunyar hada ido dashi kuma. A waya ta iya nuna
masa soyayya sai an hadu bakin ya mutu. Ga mamakin
zuwansa shi da bashi da lafiya. Amatullah ta tura wurin
Yassar tace ta fada masa suje babanta ya zo. Ita kuma ta
zauna ta gyara fuskarta ta sami mayafi ta yafa sannan
taje ta fadawa Umma. Addua tayi mata tace ta gaishe shi.
Da ta fita Umma tace ashe ga dalilin sauyin da ta gani a
tare da ita. Allah Yayi mata zabi mafi alkhairi. Mai son
naka dole ka so shi.
Tunda ta fito daga cikin gidan yake kallonta. Samun
kansa yayi da yin godiya ga Allah da ya hada jininsa da
Asmau. Yarinyar akwai nutsuwa da kamala. Tana bukatar
miji nagari saboda samin ingantacciyar rayuwa da
nutsuwar zuciya idan aka yi laakari da kaddarar da ta
fada mata. Kuma tana burge shi saboda ta karbi
jarabawarta hannu biyu. Har ta iso wurin da yake zaune
a gefen mota shi da Yassar da Amatullah kanta na kasa
tana murmushi.
Da sallama ta karaso ta dan rissina ta gaishe shi. Ya amsa
yana kare mata kallo. Tayi kyau sosai. Shi kuma ta lura ya
dan fada.
"Yassar ka shigo dashi falo"
Yace "kiji min mata, ni gurgu ne?"
Ita da Yassar suka yi dariya sannan suka koma falon. Da
kyar Yassar ya yiwa Amatullah wayo suka shige ciki.
Daga inda take zaune Asmau ta dan dago kai suka hada
ido da Jikamshi. Karuwa sonta yake a zuciyarsa amma
dole yayi abinda ya kawo shi. Tattaro duk nutsuwarsa
yayi yace......
ABINDA AKE GUDU🙆🏽48
Batul Mamman💖
Ta kagu sosai taji abinda zai fada shi kuma nauyin
maganar yake ji. Idan ya fada shikenan yayi musu
katanga daga wannan lokacin. Ganin babu amfani yayi ta
jan abin yasa yace
"Banda sunan sunan matata ta fari baki san komai game
da ita ba ko"?
Asmau ta dan turo baki kishi na cinta duk da bata san
matar ba.
"Ni sunan nata ma na manta. Kawai kazo bayan sama da
sati daya ka fara min da hirarta"
Yadda take hade rai ya bashi dariya. Ya gyada kai "kishi
gareki haka, mun dade da rabuwa fa har ma tayi aure".
"To ai kaine sai ka rasa hirar da zaka yi sai tata"
Ya gyara zama tare da harde kafafunsa "saboda abinda
zan fada miki yana da alaka da ita. Ina so ki saurareni da
kyau ki fahimci abinda zan fada miki."
Hankalin Asmau ya fara tashi. Wani abu ne ya darsu a
zuciyarta ta soma hawaye babu shiri tace cikin murya
mai nuna rauni "ba ma sai kace komai ba na gane
abinda kake son fada. Aurenta ya mutu zaka mayar da
ita ko. Babu komai zan iya zama da kishiya. Don Allah Ka
kwatanta adalci a tsakaninmu" ta kare tana jan hanci.
Col. Ishaq bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba.
Ita kuwa Asmau tayi kicin kicin da fuska. Hankici ya
dauko daga aljihun wandonsa ya bata "kinci sunanki
Idon kuka. Daga fara magana ji yadda fuskarki ta
kumbura. Ai dai kya bari na fadi abinda ya kawoni kafin
ki soma zubar da hawaye. Mata na gidan mijinta zaki
kashe mata aure da baki"
Dan sanyi taji a ranta kila ba abinda zai fada ba kenan.
Har tayi murmushi sai kuma wani tunanin yazo mata
"maganar aurenmu ne?"
Ya daga kai yana kallonta. Tausayinta yake ji sosai a
ransa.
Murmushi tayi mai ciwo "Hajiya bata amince ka aureni
ba ko? Dama nayi tunanin haka zata faru. Ba kowace
uwa bace zata iya daure zuciyarta ta bari danta ya auri
mace irina. Ko nice kila nayi sama da haka ma. Abinda
kayi mana na kyautatawa Allah Ya saka da alkhairi.
Nagode sosai wallahi. Ko a haka ma nagodewa Allah da
Ya hadani da kai har ka nuna min so ka zama cikin masu
nuna min na kara hakuri da kaddarar rayuwa"
Hawaye ke zubo mata tana magana bata ko tunanin tare
shi. Dago kansa yayi daga cikin kujerar ya dan matso
gaba.
"Ya Salaam, Matar Jikamshi haka kike? Lokaci daya duk
kin rikita kanki. Kada ki dauki alhakin Hajiyata wallahi ta
amince da aurenmu"
Jikinta duk da haka a sanyaye yake tace "sauran 'yan
uwanka ne basu amince ba?"
"A duniyar nan Hajiya ce kadai zata hanani aurenki na
hanu. Banda ita babu wanda ya isa. Yara kanana akeyiwa
haka ba ni ba. Kamata kowa yasan ina da hankalin da zan
san abinda ya dace da rayuwata. Ki saurareni da kyau kiji
abinda zan fada. Kamar yadda na fara magana kafin ki
katseni da dan bakin nan naki mai bani shaawa..." ya
fada yana kashe mata ido.
Kunya taji sosai harda rufe fuska da hannuwanta. Yayi
murmushi ya cigaba da magana "na taba aure,
shekarunmu shadaya da Badar babu haihuwa. Munje
asibitoci da dama ana cewa bamu da matsala. Har
maganin gargajiya mun sha. Daga karshe mahaifiyarta
tasa na saketa kuma cikin ikon Allah a shekarar da tayi
aure ta haihu"
Asmau ta dan girgiza kanta "Allah sarki, dama haihuwa ta
Allah ce. Wani baya haihuwar dan wani"
Kallonta yake da mamaki kamar bata fuskanci inda ya
dosa ba
"haihuwar Badar ya tabbatar min da inda matsalar take.
*Matar Jikamshi, bana haihuwa*. Saboda haka kiyi
hakuri da na bata miki lokaci amma na _janye maganar
aure a tsakaninmu_."
Tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi haka taji saukar
maganarsa ta karshe. Shiru tayi na dan lokaci yana ta
kallonta yana jiran ta fara kuka sai yaga idanunta ko
alamar hawaye babu banda wanda ta zubar dazu.
Shirunta tsorata shi yayi yace "kice wani abu mana."
Murmushi take yi kamar bata ji abinda ya fada ba ma.
"Jikamshina"
Jiran amsarta yake na nuna masa bacin rai da bai fada
mata tun da wuri ba.
"Lokacin da ka fara sona tausayina kake ji ko kuwa sona
kake fisabilillah"
"I love you Asmauna, and I will always do"
Tayi sassanyar ajiyar zuciya "duk macen arziki bata da
burin da ya wuce idan zatayi aure ta kai budurcinta
gidan miji. Jikamshina na rasa wannan damar har abada.
Na fada tarkon shaidan har ya zamana ina da shaidar da
duk wanda ya kalleta bazai manta da cewa Asmau ta
taba bayar da jikinta ga mutumin da babu aure a
tsakaninsu ba. Ni abar gudu ce da kyama a cikin
mutanenmu. Bani da sauran daraja da kima a idon
jama'a sai dai kawai ayi min kara. Da wannan ciwon
nake kwana nake tashi kuma dashi zan koma ga
Mahaliccina. Idan aka kallemu sai an sake. Ga wadda tayi
cikin shege nan. Amma duk da wannan nakasar ta
rayuwata kake sona saboda Allah. Ka rike 'yar da bata da
uba na aure a matsayin taka. Ka nuna min ina da sauran
darajar da zaka iya zama dani. Shine yanzu zaka ce zaka
barni saboda rashin haihuwa.?"
Sai da yayi tunanin haka zata iya faruwa. Ba yanzu yake
jiye musu ba. Kada ayi aure hakurinta ya kare
musamman da yake tana da kuruciya.
"Matar Jikamshi, haihuwa ba abin wasa bace nakasa ce
mai girma. rashinta ya kashe aure da yawa. Ya bata
soyayyar shekaru da dama. Ya hana zaman lafiya
tsakanin kishoyoyi"
Innalillahi wa inna ilahi rajiun take karantawa tun da ya
fadi maganar don ta sami kwarin gwiwar magana. Kada
tayi kuka ya tursasa mata amincewa da bukatarsa.
"Sayar da jiki a waje ko haihuwa babu aure shine babbar
nakasa a rayuwar musulmi. Amma rashin haihuwa ta
sunna ba nakasa bace. Jarabawa ce daga Allah
Madaukakin sarki. Shi kadai Yasan ladan da Ya tanadarwa
masu hakuri da rashi. Ita fa aba ce da duk kudin duniya
bazai siyeta ba kuma marasa ita su kadai suka san halin
da zukatansu ke ciki sai Allah. Amma mutuncina da ba
fin karfi akayi min ba wurin rabani dashi kaga bani da
uzuri. Taka jarabawar kenan, hakuri da ita sai yasa Allah
Ya yafe maka dukkan zubunanka Ya baka aljannah. Ni
kuwa fa? Ni na jawowa kaina. Bani da masaniya Allah Ya
yafe min ko kuwa...."
Sai yanzu ta soma kuka mai cin rai. Wayyo Allah son
zuciya. Babu wanda yayi musu dole ita da Abubakar suka
biyewa shaidan. A rayuwa bazata taba manta groups da
ake hira ko litattafan da ake rubutawa ba masu sanya
mace budurwa taji bukatar namiji, mai aure idan
mijinta na nesa taji ta kasa hakuri. Duk su biyun idan
shaidan na kusa ga kaddara sai su fada ga halaka. 'Yan
mata nawa ne a sanadiyar karamce karance irin wannan
suke burin samarinsu su dan taba wani bangare na
jikinsu ko don su rage musu shaawa? Da yawansu sun
koshi da tarbiya kuma suna kokarin kamewa. Rana daya
tsautsayi zai sa suci karo da irin wadannan masu yada
alfashar shikenan komai nasu sai ya lalace.
Col. Ishaq ji yake kamar ya tayata kuka. Tausayi tare da
son Asmau ke karuwa a zuciyarsa. Bude baki yayi zaiyi
mata magana ta riga shi
"Jikamshina idan kaki aurena saboda rashin haihuwarka
ka cutar dani kuma ka raina son da nake maka. Idan so
kake ka rabu dani saboda Allah zanyi hakuri. Amma idan
wannan ne dalilinka to ka sani *wallahi* bazan taba
rabuwa da kai ba. Har zaka iya son auren mace irina sai
nice kake tunanin zan gujeka"
Dafe kansa yayi saboda ta daure shi da zantukanta. Ya
kara yarda Asmau mace ce tagari wadda kaddara ta gifta
mata. Yana jin kukanta har ransa. Saukowa yayi daga kan
kujerar da yake ya zauna a kasa dan nesa kadan da ita.
"Look at me please"
Babu musu ta dago kanta. Wannan idan su Umma suka
ganta sai a zata wani mugun abin yayi mata ai.
"Har mamaki nake yadda kika shiga zuciyata Matar
Jikamshi. Ban taba jin zafin so da tsoron rabuwa kamar
akanki ba. Ina tsoron muyi aure ki kasa hakuri da lalura
ta. Kada son da muke wa juna ya koma zaman hakuri
kawai a nan gaba. Kada kiga kamar saboda abinda ya
wuce a baya dolenki ki zauna dani duk yadda nake. Kiyi
tunani sosai, bani da niyar cutar dake."
Idonta cikin nasa abinda bata yi ko bisa kuskure suka
hada ido tana saurin dauke nata.
"Gobe Baba yace yana son ganina kuma nasan so yake
yaji wa na zaba cikinku. In sha Allah sunanka zan fada
masa. Idan kaki amincewa zan hakura nasan Allah bai
kaddari aurenmu ba. Amma bazanyi aure ba har abada.
Bazan yarda na kara son wani ba balle na kara haduwa
da irin ciwon da nake ji a zuciyata yanzu."
Tana gama magana ta tashi tayi hanyar da yasan zata
kaita cikin gidan sosai. Kasa motsin kirki yayi sai daga
baya ya tashi duk jikinsa babu kwari. Wannan ciwon kan
ne ya sake dawo masa ya tashi jiri na dibarsa. Yana son
Asmau amma yana tsoron kada Allah Ya kamashi da
tauye mata hakki. Da kyar ya iya zuwa bakin motarsa.
Duhu duhun da yake gani yasa ya dauko wayarsa ya kira
Yassar.
Bai dade ba ya fito ya tsorata da halin da yaga Col. Ishaq.
Mukullin motar ya bashi yace don Allah Ya kaishi asibiti
daga nan ya ajiye shi a gida amma kada ya fadawa su
Umma balle Asmau. A rude Yassar yaje yace da Umma
zai raka Col. Ishaq unguwa tace to sai sun dawo.
Asmau kuwa daki ta wuce ta fada kan gado tana kuka.
Bata da abinda zata sakawa Jikamshi dashi sai aure da yi
masa tsantsar biyayya. Zata aure shi ta nuna masa
haihuwa ba ita kadai bace aure. Ita dai tana karawa
maaurata jindadi ne. Amma idan Allah Ya hanaka to bai
hanaka saurin jindadin rayuwa ba. Bai hanaka lafiya da
arzikin ibada ba. Ko yanzu kukanta na tsoron kada yaki
amincewa ne.
Da Umma taji shiru bata fito ba tace karshenta tana can
tana kuka Ishaq ya gaya mata ya fasa.
*****
Da Yassar ya kaishi gida yaso tambayarsa abinda ya faru
amma ya kasa saboda yanayin da yake ciki. Sunyi
sallama ya bashi kudin mota yaki karba ya tafi gida da
wasiwasi.
*****
Washegari Asmau tayi wanka da wuri tana jiran zuwan
Shemau da Jafar. Tun bayan asuba ta tura musu text
tana rokon su zo kafin taje gidan Baba. Umma dai addua
take yi mata a zuci da fatan Allah Ya kawo mafita cikin
sauki. Tayi mamakin ganinsu Shemau suka ce Asmau ce
ta neme su. Suma hankalinsu ya tashi.
Hajjo na bacci lokacin suka shiga dakin Umma bayan ta
hada Amatullah da kayan wasa don kada ta dame su.
Duk yadda sukayi da Col Ishaq ta fada musu. Babu
wanda yayi mamaki domin kuwa duk sunji komai a
wurin Umma. Maganarta ta karshe ce ta dauki
hankalinsu da tace shi zata cewa Baba ta amince ta aura.
Shemau tace "Asmau baki da hankali ne. Rashin haihuwa
da kuruciyarki ba abu bane da ya kamata ki bari soyayya
ta rufe miki ido a kai."
"Yaya Shemau ki tuna shi fa da 'yata ya ganni kuma yace
yaji ya gani. A irin rayuwata ko 'ya'ya yazo dasu yanzu ai
dole na hakura na aureshi tunda nima ina da ita. Duk
yarinyar da ta tafka kuskure irin nawa wallahi zabinta ya
zama ragagge a rayuwa. Dole idan tana son jindadi ta
hakura da wasu abubuwan. Sharrin zina kenan. Yanzu ko
auren mai duka nayi indai ina son rufawa kaina asiri dole
na hakura na zauna dashi ko na fito duniya ta zageni ace
kila ma halin da nayi a baya ya sake kamani dashi."
Umma tace "yanzu ke kina ganin zaki iya zama dashi a
hakan. Bai fiye miki ba ki amincewa Qasim."
"Umma ba karamar alfarma yayi mana ba da yace yana
sona. Babu wata alaqa da ta hadamu fa. Rana tsaka ya
ganni kuma yace yaji ya gani duk da abinda ya faru dani.
Sai nake ganin bai dace ba naki shi saboda rashin
haihuwa. Abinda bashi yayiwa kansa ba. Yaya Qasim
kuwa nafi alakanta da tausayinmu yake ji "
Jafar ji yayi Asmau ta burgeshi ba kadan ba. Kanwarsa ta
ga rayuwa ta kuma hankalta da ita. A yanzu tasan so ba
shine samu ba. Duk yadda ake son haihuwa a aure indai
tana son kanta da arziki dole ne ta ajiye son ranta ta
karbi abinda Allah Ya azurta dashi
"Umma ni dai ina ganin indai tana sonsa kuma ta amince
da lalurarsa a barta ta aureshi. Wallahi shi da Qasim
bazamu manta dasu ba har abada. Duk da sun san
komai game da ita suke son aurenta. Umma mu akayiwa
alfarma ba mune zamuyi musu ba. A matsayina na
yayan Asmau na bawa Col. Ishaq ita har abada" ya fada
da murmushi.
Shemau ma ta fahimci kanwarta yanzu ta kai masa duka
a baya "to sannu waliyyin Asmau. Ai dai akwai manya
gaba da kai"
Nasiha mai ratsa jiki Umma tayi mata tare da bata goyon
baya. A karshe tace "bamu ba wasu ma zasu hankalta
idan suka ji labarin rayuwarki Asmau. Auren Ishaq zai iya
rage miki gori da surutan mutane saboda wasu zasu ga
kema kinyi masa hallaci. Shi Qasim sai a bashi hakuri
tare da godiya domin ba karamin mutuntamu yayi ba.
Allah Yayi muku albarka. Allah Ya kara kare mana zuria
daga fadawa ga tarkon shaidan Ya yafe mana
kurakuranmu baki daya."
"Amin" suka amsa su uku. Bayan azahar kuwa da Asmau
taje gidan Baba bata yi nauyin baki ba ta sanar dashi
wanda ta amince wa. Sai da yayi ta tambayarta zata iya
zama dashi babu haihuwa. Amsarta ko sau daya bata
canja ba tace eh. Addua yayi mata shima da fatan
alkhairi. Da rayuwarta bata zama yadda take yanzu ba
bazasu yarda da wannan aure ba. To amma yanzu sun
san cewa ba karamin arziki Allah Yayi musu ba da ya
bata manemi kamar Col. Ishaq Muhammad Jikamshi. Zai
rufa mata asiri itama ta rufa masa. Allah Mai hikima ne
kuma Masani akan komai. Zuwa Shanono ya kama shi
dole zai je yasan irin dabarun da zaiyi a warware
maganar Qasim batare da zumunci ya sami rauni ba.
*****
Su Asmau na zaune a tsakar gidan Kawu Garzali suna
hira ta dauki waya ta turawa Jikamshi text.
_Na zabi Jikamshina a matsayin miji. Na yarda na bashi
amanar sauran rayuwata. Na amince babu wanda nake
so sai shi kadai. Ina fata zaka amince ka karbi soyayyata.
Kuma ina so ka sani cewa ba tausayinka nake ji ko auren
alfarma nake nema ba. So ne kawai, Matar Jikamshi sai
da Jikamshinta_
*****
Zaune yake gaban Hajiya tana yi masa nasiha saboda
damuwa da tayi masa yawa yaji shigowar text din. Yana
karantawa ya dago kai ya kalli Hajiyarsa yana murmushi
mai burgewa "Hajiya ki fadawa su Kawu su shirya zuwa
nema min auren Asmau"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽49
Batul Mamman💖
Bayan tayi text din duk da hira suke mintuna kadan sai ta
duba wayar ko ya aiko mata da reply. Ganin babu bai sa
taji komai ba. Naci zata kafa masa har sai ya amince don
dole. Wannan shine abinda ta yankewa kanta zata yi
masa. Haka kawai bazata bari Jikamshinta ya kasance
cikin bacin rai da sadaukarwa ba shi kadai saboda wata
lalura da bai isa ya yayewa kansa ba. Wani guntun
murmushi tayi ta sake daukan waya. Kafin ta fara rubuta
text din taji an kwashe mata da dariya. Shemau da su
Sabira ne a wurin. Asmau ta dago kai tana kallonsu.
Maijego Zubaida da Ainau shayar da yaransu suke amma
suna tayawa wurin yi mata dariya. Ta dan ware ido
"Me aka yi?"
Sabira tace "me kuwa akayi banda kallonki da muke yi.
Gaskiya wannan sojan ya cancanci a kira shi da gwarzon
namiji."
Ainau ta amshe "ai baku ga komai ba ma. Sai suna tare
wallahi, abin sai ya baki shaawa. Shiyasa tuni na canja
takuna wurin Yaya Umar. Muma mun zama Laila Majnu"
"Lallai yaran nan kun koshi, a gaban nawa ko" Shemau ta
fada amma fuskarta a sake.
Sai yanzu Asmau ta gano wai da ita suke dariyar. Ta
murmusa "to me nayi yanzu"
Wannan karon Zubaida ce tayi magana "ke kadai kike ta
kallon waya kina murmushi kamar yana kusa dake. Don
Allah a bawa Qasim hakuri idan ya rabaku karshenta ku
kamu da ciwon zuciya."
Aka sake yin dariya. Shemau tace "da dai Asmau akwai
kunya amma yanzu sai a hankali. Akan _Jikamshinta_bata
gane su waye a kusa. Allah Ya kaimu lokacin buki a kaiki
tun asuba kafin mu laluba muji amarya ta kai kanta.
Suna dariya Asmau ta turo baki "amma kun gama dani
wallahi. Kuma har yanzu da kunyata fa. Daga yau na
dena magana ma"
Sabira tace "Yi abinki Asmau, idan mutum na sonka
kaima ka nuna masa baka da tamkarsa. Bari nima na kira
Abban Abid mu dan taba hira. Yau tunda muka fito banji
muryarsa ba" sai da ta gama magana ta tuna da Shemau.
Tashi tayi da gudu ta shige daki. Tsakar gidan kuwa sai
dariyar su Asmau.
Sai yamma suka tashi tafiya gida. Hankalinta kwance
kamar an cire mata dutse a zuciyarta. Duk da bata ga
amsarsa ba ta gama yanke shawarar jurewa har sai ta
shawo kansa ya amince. Ainau da Shemau tare suka tafi.
Ita kuma ta bi Jafar da yazo daukar Sabira suka ajiyeta a
gida.
A bayan motar tana zaune da waya a hannu Amatullah
tana wasa da Abid. Text din da bata sami damar yi ba
dazu ta rubuta ta tura masa.
_Don Allah kace kana sona....zanyi kuka fa._
Daga bakin gate suka sauka don lokacin har anyi
magariba suna hanya. Tana tura gate din ta ga wata
bakuwar mota a kusa da ta Umma. Bata damu da sanin
mai motar ba ta shiga ciki tana sauri taje tayi sallah.
Amatullah tace "Ummina muyi yige yigen shiga falo"
Ta bi 'yarta

Please Login or Register in order to submit comment