Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batayi ba ta nufi motar da sauri. 'Yan
kamasho har sun fara baibayeta ana tambayarta ina zata
je. Da shigarta motar dreban yazo suka gama surutansu
da 'yan uwansu drebobi ya tada mota suka harbi titi.
*****
Har karfe tara babu motsin Asmau. Anti Bintu da Jafar ne
zasu kaita asibitin duk sun shirya. Umma tace aje a tashe
ta idan batayi wanka ba su tafi a haka ta yi idan sun
dawo.
Aina'u aka tura taje ta dawo tace bata ganta ba. Shema'u
tace kila tana bandaki kije kice mata tayi sauri ita ake
jira.
Da gudu Aina'u ta dawo tace "Anti na duba bata daki
kuma bandakin a bude yake".
Umma na jin haka tace a tashi a dubota karshenta buya
tayi saboda kada aje asibitin. Da farko Yassar da Aina'u
kadai ne suka duba dakunan da bayan gidan suka dawo
basu ganta ba. Hakan ya soma tsorata Umma kowa ya
tashi a rude suka shiga nemanta. Ganin babu alamun
za'a sameta a gida Shema'u ta kira wayarta. Tayi mamaki
jin muryar Walida. Bayan sun gaisa Walida tace wayar na
hannunta. Tun ranar da abin ya faru zance ya fara
bazuwa mahaifinta har gidan yazo ya dauketa da kansa
lokacin da aka sake mayar da Asma'u asibiti kuma ya
haramta mata sake zuwa gidan.
Shema'u tayi kasake har Walida ta gama bayani sannan
tace zata turo Yassar ya karbi wayar. Tana juyowa Umma
ta kalleta a tsorace
"Kada kice min an sace wayar ne".
"A'a Umma tana wurin Walida."
"To ina Asmau ta shiga, ni Bara'atu daga wannan sai
wannan".
Da gudu Jafar ya dawo falon da takarda a hannunsa
wadda ya gani a tsakiyar gadon dakin su Asmau. Jiki
babu kwari ya mikawa Umma ta karba hannu na rawa.
_Umma ina mai rokon gafararki a lokacin da kike
karanta wannan takardar nayi nisa da gida. Nayi nadama
da bakincikin halin da na saka ku na kuma jefa kaina. Sai
dai na dauki komai a matsayin kaddara. Na tafi ne
saboda bana son ku daukarwa kanku zunubin kashe rai.
Zan haifi abinda ke cikina da izinin Allah zan kula dashi
batare da na fada mummunar rayuwa ba. Ki yafe min
kuma ki cigaba da yimin addu'a. Allah Ya hadamu cikin
aminci. Sannan ina mai kar tabbatar muku cikin nan na
Abubakar ne. Ku yafe mana._
_Asmau_
Kuka mai sauti Umma ta saka wanda yasa Shema'u
saurin karbar takardar ta karanta. A take itama ta fashe
da kukan. Umma sai sumbatu take saboda tsabar tashin
hankali.
"Asma'u ki dawo wallahi babu mai cire miki cikin. Ki
dawo na yafe miki. Ina zaki je ke kadai a wannan duniyar
da amana tayi mana karanci?"
Duk wanda yake wurin sai ya tausayawa Umma. Dama
da mayafi a jikinta tace Jafar ya dauko mukullin motarta
yazo su fita neman Asma'u. Nan da nan kowa ya fita
suka fara karade unguwar. Daga nan sune gidajen
kawayenta da tashoshin mota tare da hoton Asmau suna
tambayar ko an ganta.
*****
Karfe goma na safe tayiwa Qasim a kofar shagon mai
gyaran waya. Mai shagon a wurin ya sameshi a ransa
yace dan anace ya iso. Allah Ya taimake shi ya gama
gyaran shiyasa da fara'arsa yace "ranka ya dade ai yanzu
nake shirin kiranka idan na bude shagon."
"Baka da abin da zaka fada min. Gyaran waya sati guda
kuma na biyaka. Kawai sai ka zauna kana ja min rai."
Gefe ya matsa mai shagon ya bude. A cikin wata drawer
ya dauko wayar Qasim wadda screen dinta ya fashe tun
ranar alhamis da ya iso garin Zamfara. Duba wayar yayi
ya tabbatar tayi sannan yayi sallama da mutumin ya fita.
Bakin titi ya koma inda ya ajiye motarsa. Yana shiga ya
kira mahaifiyarsa bayan sun gaisa ya sanar da ita wayar
ta gyaru zata rinka samunsa. Dama ta wani yake ara a
ofishinsu ya saka sim dinsa ya kira. Karamar wayarsa
tana wurin kanwarsa da ya bawa kafin ya taho.
Bayan yayi sallama da ita ya kira numbar Abubakar.
Kullum idan ya ari waya sai ya gwada amma a kashe
yake samunta. Dariya kawai yake yi yace ango ya dau
hutun waya kenan. Sai da aka fi kwana uku a haka ya
fara damuwa ko sace wayar aka yi. To da yake data aro
yake amfani shiyasa bai matsa ba sosai. Yau kuwa yayi
sa'a gwaji daya ta shiga. Sai da ta kusa tsinkewa yaji an
dauka. Ko magana bai jira anyi ba yace
"Haba mutumina, daga aure sai ka yar dani. Nayi ta kira
bana samu gashi tawa wayar ta lalace. Ya madam? Ina
fata duk kuna lafiya."
Shiru yayi saboda yaji ba'ayi magana ba.
"Hello, Abubakar ko baka jina ne?" Ya dan cire wayar
yana dubawa ko gyaran ne baiyi ba.
Daga daya bangaren yaji ance "Qasim".
Muryar tayi kama da ta Abubakar sai dai ya tabbatar
bashi din bane.
Rike wayar yayi yaji an sake kiran sunansa sannan ya
amsa
"Ango me ya sameka ne? Naji muryar taka taso ta canja
min."
Abdulhalim ya hadiyi yawu sannan ya shafa kansa yana
tunanin da yadda zai fadawa Qasim abinda ya faru.
"Qasim nine Abdulhalim, dama Abubakar ya fada min
anyi maka transfer a wurin aiki da karin girma".
Sai a lokacin Qasim yayi ajiyar zuciya da ya gane mai
maganar
"Wallahi kuwa baban Yaya. Kuma da yake ko wata ba'ayi
da bani query ba shiyasa dole na tafi kada nayi laifin da
za'a koreni. Daga karin girma ace na fara wasa da aiki"
Yana dariya yake maganar sannan ya tambayi ina
amininsa ango Abubakar.
Shiru Abdulhalim yayi na dan lokaci sannan yayi ajiyar
zuciya yace
"Qasim Allah Yayiwa Abubakar rasuwa a ranar daurin
aurensa".
Wani duhu-duhu Qasim ya fara gani da kyar ya iya cewa
"kai, karya ne Wallahi. Abubakar din? Abubakar fa nake
nema kaninka mai wannan layin".
Abdulhalim yasan za'a rina. Abubakar da Qasim abokai
ne tun aji daya a firamare. Cikin nutsuwa ya labartawa
Qasim abinda ya faru.
Tamkar karamin yaro haka Qasim ya rinka kuka. Har
wani zazzabi yaji ya kama shi a lokacin. Ya dan gyara
murya yace "ina Asmau?"
"Tana gidansu" Abdulhalim ya bashi amsa a takaice.
Qasim yayi alkawarin zuwa Kano a satin idan ogansa ya
bashi dama. Mahaifiyarsa bata sami zuwa bikin ba
saboda ciwon kafa kuma kanwarsa wadda su biyu ne
dama ita take jinyarta. Kila shiyasa basu ji zancen
rasuwar ba tunda a Shanono suke.
Daga nan suka ajiye wayar Qasim ya tafi office. Duk
wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali. Koda
yaje wurin ogansu da hawaye a fuskarsa ya fadi
bukatarsa. Labarin ya taba zuciyar ogan ya bashi damar
tafiya a ranar ya dawo wata lahadin.
Gidan da aka bashi yaje ya canja kaya cikin kankanin
lokaci ya kama hanyar Kano.
*****
A can Kano an bazama neman Asmau. Umma tayi kuka
har ta gaji. Hajjo da 'ya'yanta suka zo har gidan suka yi
mata abinda suka saba. Har cewa sukayi ita ta turata
yawon karuwanci.
Da zance ya kai kunnen Mama Yalwa ko kadan bata ji
dadi ba haka ma Baba da sauran 'ya'yan gidan. Sun
tausayawa Umma sosai Baba yace zai sa a bada cigiya a
kafafen yada labarai.
*****
Shiru Asmau na zaune a cikin mota banda addu'a babu
abinda bakinta yake ambato. Tana daga gefe ta ja hijab
dinta ta rufe rabin fuskarta. Sunyi nisa sosai taji wani
daga gaba yana tsaki da zage-zage. Na kusa dashi wanda
da alama abokinsa ne yace "ya dai kake tsaki kai kadai
Bala?"
Wanda aka kira Bala ya nuna masa wani hoto a wayarsa
"ka duba don Allah yadda ake rashin imani a duniyar
nan. Dubi fuskar yarinyar nan kai kace idan aka saka
mata hannu bazata ciza ba...."
Hankalin sauran 'yan motar ya koma jin jawabin Bala.
Shi kuwa ya cigaba da magana cikin bacin rai "....wai
yarinyar nan ce ranar aurenta ta kashe mijin saboda ya
gano tana da ciki kuma yace ba nasa bane. A cikin
gidansu fa aka tsinci gawar tasa a bandaki ta buga masa
guduma a keyarsa bayan an kai ta, ance a halin yanzu
tana hannun hukuma. Shegiya Allah Yasa su harbeta ma"
A hankali Asmau ta daga kai ta kallo hoton da duk 'yan
motar sai da suka karbi wayar suka gani. Gabanta ne ya
fadi sosai da taga hotonta ne. Cikin dan lokaci an canja
labarin gabadaya. Ba karamin mamaki tayi ba da taga
hoton da ita kanta yanzu bata dashi a wayarta. Mutane
kamar jira sukeyi abu ya faru sai ayita yayatawa ana ta
kara gishiri da maggi a zancen. Kafin ka ankara zancen ya
sauya daga ainihin yadda yake. Shiyasa ake so mutum ya
kiyaye me yake saurin turawa mutane a kafafen sada
zumunta (social media).
Sake rufe fuskarta tayi don kada su ganeta. Wani daga
kujerar baya yace "nima ina da wani hoton nata daban
da wannan harda mijin" wayar tasa ya miko shima da
hotonsu na dinner ita da Abubakar.
Mutumin ya cigaba da cewa "ni a yadda aka turo cewa
akayi kafin a daura auren aka tsinci gawarsa a bandakin
hotel shine aka kalawa yarinyar. Ana tunanin wata
yayiwa ciki ta kashe shi."
Har zuciyarta zancen yayi mata daci sai dai kafin a gama
ganin hoton wata tace itama taji labari amma cewa akayi
rasuwa yayi a gidansu kuma a ranar aka gane amarya
nada ciki. An rasa gane ko cikin waye nasa ne ko na
yayansa don amaryar tana bin maza.
Duk masu bayani na matar ne yayi kama da gaskiya.
Duniya kenan, kowa da abinda zai ce ba tare da yasan
gaskiyar lamari ba. Asmau tana ji motar ta kaure da tsine
mata ita da Abubakar ga wadanda suka yarda ciki yayiwa
wata. Rufe ido tayi kamar mai bacci tana kukan zuci har
suka shiga tashar Azare ta jihar Bauchin Yakubu.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽7
Batul Mamman💖
Ba karamin gudu Qasim yayi ba a hanya. Allah ne Ya
kawo shi Shanono lafiya. Kai tsaye gidansu ya nufa. Gida
ne irin ginin gargajiya amma yasha gyara ciki da waje ga
sabon fenti. Duk shiririta irinta Qasim baya wasa da
lamarin iyayensa. Shiyasa albashinsa duk wata a hidimar
gidan yake tafiya ko tunanin aure baya yi duk da shine
babba. Kanwarsa daya Jamila wadda ada yaso Abubakar
ya nemi aurenta.
A soro ya tarar da mahaifinsa Mal Musa zagaye da
dalibansa samari da magidanta wurin su goma. Da dai-
dai Qasim ya gaisa dasu sannan ya gaishe da mahaifinsa.
Yana durkusawa gaban Malam sai hawaye ya kufce
masa. Ganin haka daliban suka tashi gabadayansu suka
yi sallama da malaminsu.
Hankakin Mal Musa a tashe yace
"Baba wata matsalar ka sake samu a wurin aiki ne?"
Qasim ya girgiza kai. A lokacin Jamila ta fito zata je
makota inda Inna ta aiketa. Ganin yayanta yana hawaye
yasa ta koma ta sanar da Innar abinda ta gani. Kokarin
tashi tayi da kafarta daya da tasha dori sakamakon
karayar da ta samu a kafar bayan ta zame a bandaki.
Kafadar Jamila ta dafa ta kaita soron. Suna shiga suke jin
Qasim yana sanar da mahaifinsa mummunan labarin da
ya dawo dashi gida.
Inna ta saki kuka hade da salati "Abubakar din da na sani
ko dai wani kake nufi Baba".
Ido fal hawaye ya fada musu abinda ya sani dangane da
rasuwar amininsa. Inna da Jamila sai kuka. Ba tun yau
Abubakar yake dan gida a wurinsu ba. Yadda Qasim ke
zuwa Kano hutu haka Abubakar yake zuwa Shanono.
Lokacin da Mal Musa ya sami mutuwar barin jiki ba
karamar hidima iyalin Kwamishina Adamu suka yi musu
ba. Lalurar iyayensa da canjin aiki da ya samu yasa basu
je wurin bikin ba. A can Kano kuma tashin hankalin cikin
Asmau yasa basu tuna da sanar musu ba.
Bayan sun gama koke-kokensu suka shirya duk da
yamma tayi Qasim yasa kujerar guragun da ake tura
mahaifinsa a ciki a bayan mota sannan suka kama
hanyar Kano. Ana gab da magariba suka isa kofar gidan
Kwamishina. Maigadi ya sanar dasu cewa gabadaya 'yan
gidan suna makota wato gidansu Asmau. Gaba Qasim
yayi da motarsa suka karasa can gidan. Ya taimakawa
mahaifinsa ya fito jingine da jikinsa suka shiga gidan.
Jigum suka tarar da Umma da Mama Yalwa kamar basu
sami sabani sakamakon jin batun cikin ba. Baba
Kwamishina yana gefe shi da Abdulhalim suna ta bige
bigen waya. Kowa ka gani da abinda yake yi. Sallamar
Qasim ta sa hankalinsu ya koma ga kofa. Kuka sosai ya
zowa Mama saboda ganin Qasim. Shima bayan ya
zaunar da mahaifinsa gabanta ya koma yana kukan.
Mutuwar Abubakar ta dawo musu sabuwa. Da suka dan
nutsu ne Qasim yace " Umma ina Asmau ne?"
Kamar yace a fara wani kukan suka sake dasa sabo. A
gigice yace " ba dai itama ta rasu ba?"
Jafar ne ya bashi amsa da cewar ba'a ganta ba tun safe.
Qasim ya share kwalla "amma me yasa Asmau bazata yi
tawakkali ba. Ina ta tafi haka?"
Boye- boye bashi da amfani shiyasa Shema'u ta sanar
dasu abinda ya faru. Idan ma basu fada ba a waje wasu
zasu fada musu.
Labarin yayi matukar razana Qasim da iyayensa. Lallai
iyalan biyu suna cikin tashin hankali. Jikinsa duk babu
kuzari ya dubi wurin da Malam da Baba suke zaune "ko
da ba a gabana akayi ba, ni shaida ne cikin Asmau na
Abubakar ne."
Mama ta dago jajayen idanunta tana kallonsa " Qasim
abokinka fa ya rasu, yanzu ka kyauta kenan kana binsa
da wannan mummunar shaida".
"Mama na san inda yaje nima a ko wane lokaci zan iya
tafiya. Fadin gaskiya shine adalcin da zanyi masa." Daga
nan ya basu labarin abinda ya sani dangane da Abubakar
da Asmau wanda babu wani mutum da ya sani. Shi
kadai ne yasan wannan sirrin.
Falon ya sake rudewa da kyar Baba da Malam suka samu
aka yi shiru sannan suka ce a tashi ayi sallar magriba
zasu karasa maganar idan sun dawo daga masallaci.
*****
Tun kafin azahar mota ta sauke su Asmau a tasha. Kowa
na ciki ya dauki kayansa yayi gaba, ban ita. Sai yanzu take
tunanin inda zata je kuma bayan nan. Bata taba zuwa
Azare ba kuma bata san kowa ba. Wurin da taga an kebe
domin sallah taje tayi sallah sannan ta karasa wurin
masu abinci ta sayi wake da shinkafa da pure water.
Yunwa take ji sosai. A gefen wurin sallar ta zauna taci
abincin. Da akayi la'asar ta sake yin sallah ta kuma
samun wuri ta zauna. A nan dai magariba da isha suka
riske ta tayi sallolinta cikin fargaba. Ga dare yana yi gashi
bata da wurin zuwa.
Bayan tayi Isha ne hankalinta ya kai kan akwatinta. Dama
jakar na kafadarta. Akwati dai babu shi babu dalilinsa
wani ko wata ya dauke batare da ta sani ba. Bakin cikinta
ya karu ta soma kuka. Ita ga tsoro bare tayi cigiya. Tana
kallon yadda mata ke fada a cikin tashar da maza amma
bazata iya ba. Tayi sa'a ma akwatin babu kudi a ciki.
Tana wannan kukan ne taji muryar wani daga gefenta
yace
"Gani nazo sai kizo mu tafi."
"Mu tafi ina?" Ta fada a tsorace ga wurin babu wadatar
haske.
Wata dariya mutumin yayi. Babba ne don a kalla zai
shekara hamsin. Yasa riga da wando na yadi ga taba a
hannunsa. Bakinsa kuwa hakoran Makkah ne har biyu
daga sama. Tsoro ne ya sake shigarta ta dan matsa baya.
"Kinga ki kwantar da hankalinki yarinya kinzo gida.
Irinku sunfi a kirga da nake taimakawa a tashoshin garin
nan." Ya dan zuki tabar sannan ya sake kallonta. " ki taho
mu tafi idan ba a tashar nan kike son kwana ba 'yan
iskan gari su danneki anjima kadan.."
Asmau ta manne jikin bango zuciyarta na dukan uku-
uku
"Don Allah ni dai ka kyale ni."
Mutumin ya girgiza kai alamun ya saba jin irin haka.
"Kinga 'yata ta kaina. Ni dinnan da kike gani ba cutar
dake zanyi ba. Billahillazi masauki zan kaiki."
Cikin tsiwa tace "bazani ba"
Ya dan tabe baki "kinyiwa kanki, irinku- irinku yawa
garesu. Ku fito daga gidan iyayenku duk garin da kuka ga
mota zata kuje. Sai kun sauka a tasha kuke gane kunyi
kuskuren barin gida. Irina kuma sai mu nuna muku
cewa ku kadai zaku iya rayuwa batare da iyaye ba. Akwai
gida na mata zalla dama can nayi niyar kaiki saboda
kwanan tasha ga zukekiyar mace irinki ba karamin
hatsari bane."
Maganganunsa kara tsorata Asmau suke yi sai dai haka
kawai bazata bi mutumin da bata sani ba. Dauke kanta
tayi ya gaji da tsayuwa ya juya abinsa bayan ya bulbuleta
da hayakin taba.
Ajiyar zuciya ta saki bayan ya tafi sai dai kafin ta motsa
daga wurin da take taji wasu maza na tahowa wurin da
take. Tana jin su suna tattaunawa a tsakaninsu waye zai
fara amfani da ita. Abin nasu kamar fada mutum biyu
suka dage harda zage-zage. Kafin su karaso da sauri
Asmau tabi bayan mutumin da ya gama yi mata magana
dama baiyi nisa ba. Tana kankame da jakarta tace ya
tsaya zata bishi.
Wani shu'umin murmushi yayi yana kare mata kallo.
Shiyasa yake son aiki da su Shoki yaran da ya biya suka
tsorata ta.
Addu'a kawai take yi tabi bayansa suka mike wata hanya
da tayi kudu da tashar.
*****
Su Umma sun sake taruwa a falon gidanta inda Malam
Musa ya bada shawarar a dage da addu'a da binciken
mutanen da take da alaka dasu. A cewarsa babu wani
abu yanzu mai mahimmanci a gabansu sama da sanin
inda Asmau take. Sannan ya ce
" a gaskiya dukkanku kunyi kuskure akan yadda ku ka
karbi al'amarin yarinyar nan. Dukkan dan Adam ajizi ne,
Allah da Ya haliccemu mai gafara ne da jinkai. Idan
mutum ya aikata ba daidai ba musamman abu irin nata
dolene mu nuna mata kuskurenta sannan kuma mu jata
a jiki don gudun sake faruwar makamancinsa. Mu nuna
mata mahimmancin tuba da karbar kaddara. Amma
idan muka watsar da lamarin 'ya'yanmu saboda sunyi
laifi hakika muna tura su ne ga aikata wanda yafi shi.
Wani lokacin idan hantara da kyama tayi yawa sai kawai
yaro ya fandare gabadaya yace bari yayi ta laifin tunda
bashi da sauran gata.
Mu kula sosai idan mutum yayi laifi fada, nasiha da
jankunne yakamata muyi ba sharesu ba har su bi hanya
mara kyau. Allah ma muna masa laifi Ya yafe mana duk
girmansa indai ba shirka bane balle mu 'yan Adam. Wani
abin yana faruwa ne domin ya zama izina ga sauran
mutane.
Kuma na tabbatar yadda kuka nemi tilasta ta akan a cire
cikin shi ya koreta. Sannan ta fiku gaskiya domin cire ciki
ba tare da wata lalura ba bashi da muhalli a addininmu.
Allah Ya tsare mana ita a duk inda take."
Jikin kowa kuma sai yayi sanyi da jin bayanin Mal Musa
suka ce Amin.
Haj Bara'atu dai babu abinda ke damunta sai irin yadda
ta rinka fadar maganganu marasa dadi ga 'yarta cikin
bacin rai. Da ta sani bincikar ta tayi taji yadda al'amarin
ya faru domin a kiyaye faruwarsa ga sauran yara.
Bacin rai da fushi dole ne amma yin komai cikin hikima
da ilimi shine daidai. Da ta sani fada tayi mata wanda ta
tabbatar halin da take ciki ma ya isheta abin kunya. Daga
nan sai a kiyayi gaba,yanzu kuwa tana iya zuwa inda
rayuwarta zata iya gurbacewa gabadaya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽8
Batul Mamman💖
Tafiya su Asmau suke yi a inda tafi tunanin kasuwa ce
saboda yawan shaguna da ta gani da mutane suna kai
kawo kamar ba dare ba. A bakin kofar wani gida suka
tsaya mai kofa daya. Sai da suka shiga ta ga ashe gidan
yana da girma ta ciki. Dakuna ne birjik ta bangaren hagu
, dama da tsakiya. Ga 'yan mata kamar ba dare ba suna
ta bidirinsu babu mai shigar arziki. Harda masu daurin
kirji. Tun daga nan Asmau ta fara dana sanin biyo
mutumin.
'Yan matan taga suna gaisawa da mutumin da ta biyo
suna tambayarsa bakuwa ya kawo musu yace eh. Tafiya
suka cigaba da yi har sai da suka je kofar wani daki daga
gefe. Dan mukulli yasa ya buga kofar dakin wata
budurwa ta fito a fusace. Wani mugun kallo ta watsa
musu shi da Asmau sannan ta matsa gefe wata babbar
mata ta fito. Doguwa ce da gani shekaru sun ja, jikinta
kuma yayi jaja-jaja alamun anci bleaching lokacin da
ake ji da sauran kuruciya. Ganin su Asmau yasa ta washe
baki tana murmushi.
" Bulayi kaine a daren nan? Bakuwa ka samo mana ne?"
Shima murmushin yayi "a bamu wurin zama mana sai
muyi magana a nutse".
Yarinyar da take ta hararsa a kofar dakin matar ta kalla
ta koma ciki ta dauko musu tabarma aka shimfida a
wurin. Sauran 'yan matan gidan kowacce harkar gabanta
take yi.
Mutumin da ya amsa suna Bulayi yace
" ina shirin fita daga tasha nayi gamdakatar. Dubi
tsaleliyar da na gano. Ina ganinta nace wannan taki ce
don duk garin nan gidanki ne gidan kyawawa."
Matar ta maida kallonta ga Asmau " yarinya ina miki
barka da zuwa. Ni sunana Uwargida haka kowa yake
kirana. Kuma tunda kika zo gidan nan zamu taru mu
sharewa juna hawaye. Babu ruwana da abinda ya fito
dake bariki indai zaki kiyaye dokar gidana shikenan."
Asmau ta mike tsaye domin ta gano wane irin gida aka
kawota. Jakarta a hannu tace "Hajiya kiyi hakuri ni ba
yawon bariki na fito ba. Bazan iya zaman gidan nan ba.
Nagode".
Takalminta ta fara kokarin sakawa ta dan hada ido da
yarinyar dake tsaye a wurin. Ga mamakinta murmushi
sosai yarinyar tayi mata.
Uwargida tayi dariya sosai "duk yaran gidan nan da kika
gani babu wacce take yarda karuwanci ta fito yi sai babu
ta sakata a gaba. Ni bazan matsa miki ba. Akwai daki na
haya dubu goma duk wata. Idan kina so a jona injin
gidan nan dake ki rinka samun wuta idan babu a gari
duk sati zaki biya dari biyar. Ci, da sha da sutura kuma
kowa ta kansa yake yi. Zabi ya rage naki. Zaki zauna ne ko
zaki fita ki kwana a titi".
Shiru Asmau tayi tana tunani. Yanzu idan ta fita ina ta
nufa.
Matar ta katse mata tunani " bana tilasta mace tayi
sana'ar da bata so amma indai ba kina da jari ko wurin
zuwa fa to nan ne gidan da kowace 'ya da bakincikin
rayuwa ya korota zata kira gida."
Bulayi yace "kuma gata da jikin sana'ar ba. Fatarta har
wani sheki take yi tayi luwai-luwai. Ni da na matsa kusa
da ita ma har kamshi naji tana yi shiyasa nace da shirinta
ta fito."
Dan murmushi Uwargida tayi sannan ta zaunar da
Asmau a kusa da ita
" ke amarya ce ko?" Ta fada tana daga gira.
"Irinku yawanci mijin ne bakwa so sai ku gudu. Shiga
duniya ba da ka ake yinsa ba. Dole ki fara ta wani wurin.
Kamar yadda na fada miki ko wurin zama ki samu nan
gaba idan kika shafa kika ji babu abinda zaki ci nasan
zaki fara sana'ar da bata tsufa. A lokacin zan taimaka
miki da kayan aiki wato maganin mata sannan na hadaki
da kilayen(client). A tsarin gidan nan duk wadda tayi
ciniki a gida ko a waje zata bani kaso goma a ciki. Sauran
bayani dai sai kin shigo hannu. A lokacin kuma zan saka
miki suna. Ni nan babu ruwana da sunan kowace
yarinya na gaskiya."
Yarinyar dake tsaye a gefe tayi tsaki "haba Mama tace ba
abinda ya fito da ita ba kenan ko dole ne?"
Bulayi ya kalleta yana dariyar shakiyanci "ustaziya
Zubaida kenan, kina nan da halinki na korar mana
alheri".
Baki ta murguda masa Uwargida tace " yanzu ma fadan
da nake mata kenan ya kamata ta ajiye girman kai ta
rungumi sana'ar da na haifeta kuma na raineta a ciki
shine ta fara min rashin kunya na bige shegen bakin."
Asmau ta sake kallon yarinyar sai taji tana sonta.
Murmushi tayi mata yarinyar ta mayar sannan Uwargida
ta umarceta da ta nuna mata daki daya cikin wanda
babu kowa. Babu yadda Asmau ta iya dole ne ta nemi
muhalli kafin tasan yadda zata fara gudanar da rayuwa.
Shiyasa ta bi bayan Zubaida. Wani daki ta bude duk yayi
kura. Zubaida tace bari na kawo tsintsiya. Bata dade ba
ta dawo da yake akwai wutar nepa ta kunna fitilar dakin.
Sai da ta taya Asmau shara da goge kura suka karkade
yamushasshiyar katifar dakin da babu zanin gado. Bayan
sun gama Zubaida ta fita sai gata ta dawo da tuwo wanda
aka fara ci da ruwa a kofi.
Tana murmushi tace "Allah Yasa ki iya ci dazu na fara ci
Mama ta fara damuna na barshi. Don girman Allah da Ya
haliccemu kada kiyi karuwanci. Gidan nan har mace ta
nemi mace anayi."
Asmau ta karbi tuwon da murna taci tayiwa Zubaida
godiya sannan ta kara tabbatar mata da cewa da zarar
komai ya daidaita barin gidan ma zatayi.
Zubaida tace "idan babu damuwa ki fada min abinda ya
raboki da gidanku".
Ajiyar zuciya Asmau tayi "in sha Allahu gobe zan fada
miki tarihin rayuwata".
Zubaida sai murna take. Har ta fita ta dawo da sauri "ina
kara tuna miki kada kiyi sana'ar matan gidan nan. Mata
da yawa da farko haka suke cewa sai an kwana biyu su fi
kowa lalacewa. Ni ma ba don bani da wurin zuwa ba da
tuni na bar gidan nan."
A haka suka yi sallama. Da Zubaida ta koma dakinsu har
ta kwanta addu'a take yi Allah Yasa bakuwar nan kada
tayi halin matan gidan. Bata da wani ilimin addini amma
tasan cewa sana'ar da ta tashi taga mahaifiyarta tanayi
bata da kyau..
Washegari shayi da bredinta ta dauka zata fita daga
dakinsu Uwargida ta kalleta tayi murmushi.
"Zuby tawa kenan, da kinga bakuwa kin rinka rawar kafa
kenan ke a dole sai kinsa ta koma gidan iyayenta.
Rayuwar duniyar nan ta wuce tunaninki fa. Ki sani duk
wadda kika gani a nan to abinda ya korota yafi nan
muni."
Zubaida ta gallawa Uwargida harara ta fita. Kai tsaye
dakin Asmau ta wuce. 'Yan matan gidan suna ta mata
dariya don sun saba ganin irin haka a wurinta idan taga
bakuwa.
Da sallama ta shiga dakin. Asmau na gyangyadi a zaune.
Kyamar katifar yasa bata kwana a kai ba. Kusan kwana
tayi tana koke-koke da addu'o'i. Cike da farincikin ganin
Zubaida ta amsa mata sallama.
Zubaida na zama ta mika mata abincin ta karba da
godiya taci. Sannan ta tambayeta inda ake samun ruwa
domin taimama tayi da asuba tayi sallah.
"Meye kuma taimama?" Zubaida ta tambaya.
Asmau tayi mata bayani. Zubaida ta gamsu sannan ta
sanar da ita kowa a gidan siyan ruwa yake yi. Dole sai ta
siye duk wani abin amfani sannan ta tanadi kudin
hayarta domin anjima kadan Uwargida zata bukaci ta
kawosu. Bayan duk ta gama jin bayanin gidan ne
Zubaida tayi mata tuni akan alkawarinsu na

Please Login or Register in order to submit comment