Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana fatan ko nan gaba idan ya roki
alfarmar a bari tazo gidansu ta yini wurin Hajiya bazasu
yi mata gori ba. Ido suka hada da Asmau tayi murmushi
sai taga ya dan sunkuya kamar zai duba waya. Bata kawo
komai a ranta ba.
Ismail ya samu shiga wurin Amatullah yace "karanta min
a kunnena ni kadai kada su ji"
Ta fito da ido da mamaki "Ummi fa tace mai yada mai
yada dan wuta, mai ji mai ji kafiyi." Nan dariya aka yi
suka ce to sai ya kiyaye yarinya tasan rada babu kyau.
Daga kai yayi ya kalli Asmau ta danyi murmushin jin
kunyarsa. Su Mami suma mamakinta suke yi. Ga dai ta
yadda ta haifi 'yar nan amma ga dukkan alamu tana da
tarbiya sosai. Tunda ta bude baki ta fara karanto
sunayen Allah gudu biyar da tsallake. Musaddiq ji yayi
inama 'yarsa ce. Ga muryarta akwai dadi tana yi kamar
da addu'a
"YA RAHMANU YA ALLAH-AMIN
YA RAHIMU YA ALLAH-AMIN
YA MALIKU YA ALLAH-AMIN...."
Haka tayi ta yi har karshe. Mami ta y kurawa Asmau ido,
yarinyar bata da makusa sai abinda tayi a baya. Idan har
aurenta zai sa dan uwanta ya dawo mata kamar da, to
zata amince da auren nan. Sai dai fa dole su shirya da jin
surutu da gorin 'yan uwa da sauran mutane.
Copied By
ABINDA AKE GUDU🙆🏽46
Batul Mamman💖
Surutun Amatullah ke tashi a dakin da masu biye mata.
Tsakani da Allah ta shiga zuciyar Ismail. A ransa ji yake
ina ma yarinyar nan ta cika 'ya kamar kowa. Ta tashi har
karshen rayuwarta bazata taba jin wata magana mai
muni game da haihuwarta ba. Col. Ishaq kuwa Asmau
har ta gaji da kallon inda yake tsaye. Duk iya yinta ta kasa
yin sa'ar kallonsa a daidai lokacin da yake kallonta. Shi
kuma yana sane yake dauke kansa daga gareta idan yaga
ta dago nata kan. Duk son da yake mata dole ya rabu da
ita indai tsakaninsa da Allah yana son farincikinta. Duk
wani tanadi da yake yi mata da Amatullah maganar
Ismail ta rusa komai. Zaiyi kokarin taimakonta ta kowane
fanni na rayuwa musamman karatu da tace tana son
komawa. A shirye yake ya dauki nauyin hakan idan bazai
kawo matsala tsakaninta da wanda ta aura ba. Ko kawai
ya hada kudi ya bata a matsayin gudunmawar aure. Shi
kadai yake ta tunaninsa har su Umma suka shigo ita da
Anti Bintu da Shemau.
Ba haka su Mami suka tsammaci ganin dangin Asmau ba.
Gashi dai suna da rufin asiri sannan ga hadin kai. Wani
abin mamaki wai harda babar wanda yayiwa Asmau ciki
ake jinyar Amatullah. Mamakinsu bai karu ba sai da Alh
Adamu ya shigo. Mutum mai fara'a jan mutane a jiki. Ya
gaisa da kowa sannan ya zauna yana tsokanar Amatullah.
Lokacin dakin ya cika sosai shiyasa Haj Lubabatu tace su
tashi su tafi.
Tun daga kan Mami har Musaddiq sun yaba da 'yan
uwan Asmau. Kaddara kam babu inda bata giftawa.
Kuma idan ta ratso kamata yayi dukkan musulmin
kwarai ya karbeta hannu bibbiyu. Ashe ba daidai bane
idan 'yar mutum tayi ciki ko zina a kyamaceta a koreta.
Hakan ba komai zai kara musu ba sai bushewar zuciya
idan basuyi sa'a kamar ta Asmau ba. Ba'ace a nuna musu
sunfi kowa ba ko a shafe girman laifinsu a mayar dasu
kamar komai bai faru ba. Amma a jasu a jiki ta hanyar
nuna musu kuskurensu da wajibcin tuba da nesanta
daga aikin dana sani. Asmau ta zama babban misali. Duk
da iyayenta sun yafe mata kuma ta tuba amma fa har
abada da gaban abada idan akwai baza'a taba mantawa
ba. Ita da ta manta da haka a rayuwarta sai ranar da taji
ance *shiga aljannah cikin aminci*. Ya Allah Kasa mu
dace.
Ita da Anti Bintu suka fito rakiya. Sai a lokacin suka
hango Bilkisu da Yassar a wurin wani benci. Kusan kowa
ya manta dasu ma.
Duk abinda taji daga bakin iyayenta da kakarta ta
tambayi Yassar ya tabbatar mata da haka ne. Bilkisu tayi
kuka sosai taji tausayin Asmau. Ta fada masa shawarar
da kawunta ya yanke na rabuwa da Asmau saboda
matsalarsa. Nan fa hankalin Yassar ya tashi. Bai ga wanda
ya dace da yayarsa ba kamar Col. Ishaq. Suna wannan
tattaunawar ne suka hango fitowar su Ismail. Bilkisu ta
rasa inda zata saka kanta don kunya. Kada ayi zaton ko
Yassar saurayinta ne duk da kuwa hakan take fata.
Amma bata riga ta faru ba. Yanzu kokarin daidaita
Kawunta da yayarsa suke yi.
Allah Yasa hankalinsu baya wajen. Asmau da Anti Bintu
ne suka gansu. Anti Bintu sai ta tsaya wurin Col. Ishaq
saboda dama tana son ganinsa. Sauri zatayi suyi magana
kafin Hajiya ta fito don Alh Adamu dasu Umma sun dan
tsaya hira da ita. Ita kuma Asmau ta karasa wurin su
Bilkisu.
Suna hangota suka tashi sai dai ta kula da hawayen da
Bilkisu ke gogewa da sauri. Tsorota tayi ko Yassar yayi
mata wani mugun abin. Tsaresu tayi da ido tana kallonsu
daya bayan daya
"Me kuke yi a nan tun dazu?"
Yassar ya dan sosa kai yana murmushi "babu komai
Ummin Amatullah"
Tayi dan tsaki "Bilkisu fada min kinji. Me yayi miki kike
kuka?"
Itama murmushi tayi "Allah babu komai, abu ne ya
shigar min ido"
Ko kusa bata yarda dasu ba. Daga ganin yanayinsu tasan
basu da gaskiya.
"Tunda bazaku fada min ba bari na kira babanki, shi
nasan zaku fada masa"
Zata juya Yassar ya riko hannunta da sauri "don Allah
kada ma ki fara. Bari su tafi wallahi zan fada miki duk
abinda kike son ji.
Suna kallo motocin su Ismail da Dahiru suka fita daga
asibitin. Bilkisu tace "bari naje, Anti Asmau sai da safe."
Asmau ta dan bata rai cikin wasa "bazan amsa ba sai naji
bayani."
Murmushi kawai Bilkisu tayi ta kama hanyar motar Col.
Ishaq.
******
Tana karasawa taji Anti Bintu cikin tashin hankali tana
cewa "wace irin magana ce wannan Ishaq? Haihuwa ta
Allah ce. Yanzu saboda wannan zaka ce ka fasa. Wallahi
baka ga yadda na shiga damuwa ba da naji zancen
Qasim"
Rabin hankalinsa yana kan Asmau da yake hangowa suna
magana da Yassar. Ba a nan inda 'yarta ke kwance tana
jinya yake so taji zancen ba. Bilkisu ya kalla babu fara'a a
fuskarsa.
"Kin gama kai gulmar? To kije ki fada masa nace kada ya
kuskura ya fada mata komai yanzu"
Hanjin cikinta har wani kullewa yayi don tsoro ta koma
wurinsu da sauri sosai. Ya mayar da hankalinsa ga Anti
Bintu.
"Rashin haihuwa ba karamar matsala bace. Ke shaida ce
ina sonta amma yaushe zan tauye mata hakkinta ta
zauna dani babu haihuwa"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Asmau tana ganin
jarabawa kala kala a rayuwarta. Tunda ta dawo gida ban
taba ganin farincikinta ba kamar idan tana tare da kai.
Ishaq wallahi tana sonka. Kada kayi mata haka. Yarinyar
nan taga taskun rayuwa. Yanzu kuma zata rasa masoyi"
Anti Bintu tana magana ita kanta kamar zata yi kuka.
Ji yayi zuciyarsa har wani zafi take masa. A jiya ya yanke
shawarar ko me zai faru bazai rabu da ita ba. Amma
magana daya tasa ya tuno da rashin dacewarsa da ita.
*****
Kafin Bilkisu ta isa wurinsu Asmau tayo gaba. Yassar yayi
mata alkawarin sai sun koma gida zai fada mata komai,
ita duk tunaninta ma ko soyayya sukeyi a boye. Bata
matsa masa ba tace shikenan. Cikin nutsuwa ta taho
wurin da Jikamshi yake tsaye da Anti Bintu. Ita dai Anti
Bintun tana ganinta ta bar wurin zuciyarta tana kara
karaya. Bata san halin da Asmau zata shiga ba idan taji
abinda Ishaq yake tafe dashi. Gashi lamari na haihuwa
ba'a daukarsa da wasa. Ita bata isa tace dole ayi auren ba
tunda da kansa ya fada mata aurensa na fari shekarunsu
goma shadaya da matar. Gashi suna rabuwa ta haihu.
Da zata bar wurin suka hada ido da Asmau tayi saurin
sunkuyar da kai a kunyace. Shima ba dadewa zatayi a
wurinsa ba saboda kada Hajiya ta fito.
Yaji dadin ganinta amma yanayin da zuciyarsa take ciki
ya hana ya bayyana mata duk kokarinsa na boyewa. Da
murmushi a saman fuskarta ta gaishe shi.
"Matar Jikamshi"
"Uhmm"
"Yau nafi sonki akan kullum, ji nake kamar yau na fara
sonki ma" yadda yake furta kalamansa a hankali yasa taji
wani dadi a ranta.
Mukullin motar yake dan kadawa yace "baki amsa min
ba."
A zuciyarta tace zai fara sakata jin kunyar da ya saba.
Kasa take kallo tace "to me zan ce?"
"Au baki ma sani ba, to bari na fada miki tunda ni nake
son jin amsar. Ina ji idan baki fadi abinda nake so ba
bazan iya kaimu gida ba." jikinsa duk a sanyaye yake.
Daga yau baya jin zai kara furta mata kalmar so. Kallo
kuwa tamkar ya cinyeta da idonsa. Jin soyayyarta yake
sabuwa a zuciyarsa.
Dago kai tayi "don Allah ka dena fadin haka bana so"
"Nine bakya so ko maganar da nayi"
Kwabe masa fuska tayi tana shirin kuka yaji ta kara shiga
ransa"kasan me nake nufi. Ka dena cewa bazaka iya
zuwa gida ba"
Yayi dariyar karfin hali "to bani amsar da ta dace"
Rufe fuskarta tayi da mayafi sannan tace "I love you
Jikamshina" da sauri ta juya zata gudu ya dakatar da ita
ta tsaya amma bata juyo ba.
"Matar Jikamshi ki rike mijinki da gaskiya kinji ko. Allah
Ya albarkaci rayuwarki"
Duk ya kashe mata jiki da kalamansa amma ko kadan
bata kawo komai a ranta ba. Ita a zatonta shi yake nufi a
matsayin mijin nata shiyasa tace
"Amin" sannan ta shige cikin asibitin.
Allah Ya taimaketa domin kuwa a hanya ta hadu da
Umma da Mama sun rako Haj Lubabatu. Gashi babu
damar canja hanya haka tayi mata sallama ta wuce su
kuma suka rakata har mota.
Har su Umma suka zo tafiya Anti Bintu bata ga wani
sauyi a tare da Asmau ba. Wannan ya sa tayi tunanin
Ishaq bai riga ya fada mata ba. Duk su biyun tausayi suke
bata, zata saka su a addua don ita bata san wace shawara
zata basu ba.
*****
Bayan kwana biyu aka sallami Amatullah. Duk kwanakin
da Mami tayi a Kano a gidan Col. Ishaq tayi su don kuwa
da gaske Haj Lubabatu ta hanata kwana a gidanta. Ranar
da zata tafi suka taru ita da kanneta suka sake bawa
Hajiyan hakuri. Shi Col. Ishaq tuni ya ware dasu. Fushin
bazai kaishi ko'ina ba yanzu tunda akwai gaskiya a
maganarsu. Mami ta tafi akan duk shawarar da ya yanke
su duka zasu bashi goyon baya.
A wannan lokacin ya rage kiran Asmau. Idan ta kira sai
taji wayar a kashe. Nambobinsa biyu gareta duk bata
samunsa sosai sai idan shi ya kirata. Shima din hirarsa
tafi yawa da Amatullah. Idan ta karbi wayar daga
gaisuwa sai yace mata zaiyi aiki ko zai kwanta. Tun bata
dauki abin komai ba har dai ta fara tunanin akwai wata a
kasa.
A bangaren Qasim ya matsa mata sosai da waya yanzu.
Yazo sau daya ya koma bakin aikinsa. Nunawa yayi bai
san da maganar Col. Ishaq ba. Ita kuma taki sakar masa
jiki tana jira taji daga bakin Jikamshi tukunna.
*****
Haka tayi sati daya duk abubuwa sun cakude mata. Jafar
ya karbi takardunta na SSCE zai sake nema mata
admission. Amatullah tunda taji sauki Abdulhalim ya zo
wata litinin da safe ya tafi da ita makarantar da yaransa
suke yi. Makaranta ce mai tsada sosai domin kuwa ana
arabiya da boko tun bakwai da rabi sai hudu da rabi ake
tashin yara.
Ga karatun Qur'ani ba kama hannun yaro. Ita dai Asmau
sai son barka. Kowa na kokarin kyautata musu. Shemau
taso ace a makarantar da nata yaran suke zuwa aka saka
Amatullah. Da yake saura sati daya hutun makaranta
gwaji kawai aka yi mata suka bata aji, kayan makaranta
da litattafai. Karatu sai an dawo zata fara sosai.
Abdulhalim ya biya kudin komai. Alh Adamu ya kara
masa kudi don kada ya shiga matsi tunda yana da nasa
yaran. Amma yaki karba Amatullah 'yarsa ce baya
bukatar taimakon kowa.
Da ya dawo da ita gida kuwa an sha labarin sabuwar
makaranta. Tana ta zuba zance akwai lilo da wurin
computer irinta Uncle Yassar. Hajjo da Umma kadai ke
amsa mata. Asmau na rike da waya a hannu tana ta kiran
Jikamshi ta kasa samu. Bata jima da ajiye wayar Qasim
ba yace mata iyayensa suna so a sake basu ranar da zasu
dawo.
Umma ce ta lura da yadda take ta tsaki ga waya a hannu
tana ta dannawa.
"Asmau wa kike nema ne haka? Kinsan dai wani lokacin
network sai yaki dadi amma duk kinsa abin a ranki sai
tsaki kike faman yi."
Amatullah tayi caraf tace "kuma ni ta hana ni yi, wai
tsaka ce yake yi"
Ran Asmau yayi mugun baci ta kai mata duka ta sameta
a gefen fuska "ban hanaki idan manya na magana ki
saka baki ba. Tashi ki bar wurin nan kafin na kara miki"
Kuka sosai Amatullah take yi don har dankunnenta sai da
yayi tsalle. Umma da Hajjo har suna rige rigen janyota
jikinsu. Umma itama ta harzuka tace "wane irin rashin
hankali ne wannan Asmau. Daga tayi magana sai duka."
Hajjo tace "kuma dukan ma a fuska, tayi kuskure don
ba'a so a koyawa yara saka baki a zancen manya. Amma
ya zaki mata hukunci irin wannan. Ji yadda dankunne ya
karce ta"
Suna kokarin jan Amatullah amma taki tsayawa. Da
Hajjo ta saketa jikin Asmaun ta koma tana kuka "Ummi
kiyi hakuyi na dena"
Kuka Asmau ta saka, tasan bata kyauta ba don fushinta
ta saukewa Amatullah. Ga zuciyarta dama ta gama rauni.
Bata samun Jikamshi shima baya kira sosai sannan
Qasim yana jiran amsarta na ranar da zasu dawo.
Amatullah ta sake cewa "Ummina kin hakuya?"
Cikin kuka ta rungumeta sosai a jikinta "na hakura Ama"
"To ki dena kuka nima na dena"Amatullah ta fada tana
share hawayenta.
Wannan ya kara karyarwa Asmau zuciya ta cigaba da
kukanta bilhaqqi. Umma da Hajjo suka tsaya kallon ikon
Allah. Sai da tayi mai isarta ta dauki Amatullah suka shiga
ciki.
Suna tafiya Hajjo ta rike baki "Bara'atu anya yarinyar
nan bata da mutanen boye? 'yan kwanakin nan na lura
tana cikin damuwa. Wannan kukan ma da biyu ko uku
ma zance take yinsa."
"Nima haka nagani, bari naje naji ko menene"
*****
Dariyarsu Umma ta fara ji Asmau tana bin Amatullah
tana cewa zata shafa mata dettol a wurin da dankunne
ya karceta ita kuma tana zagaye gado da gudu. Umma ta
rike baki kawai. Asmau da Safinanta sai Allah. Tare suka
ga wahalar rayuwa shiyasa shakuwarsu take bawa
mutane sha'awa.
Sakin fuska tayi ta shiga ta daga Amatullah.
"Gudu wurin Hajjo kinji yarinyar kirki."
Ta fice kuwa a guje tana dariya. Asmau kunya ta kamata
ta ce "Umma kiyi hakuri don Allah".
"Bakiyi min komai ba Asmau. So nake ki fada min abinda
yake damunki. Ba'a so damuwa tasa iyaye su rinka
hucewa akan 'ya'yansu. Amatullah bata kyauta ba da tayi
magana amma ba da haka zaki tsawatar mata ba. Ko don
gaba ki kiyaye"
"In sha Allah Umma. Nagode"
Wuri Umma ta samu ta zauna tace "zauna Asmau,
magana zamuyi"
Murmushi ta kirkiro "babu komai fa Umma, haushi ta
bani ne"
"To na tashi kenan tunda kina da wanda zaki fadawa
matsalarki bayan ni"
Daga magana kamar ance fara kuka kawai ta kwantar da
kanta a cinyar Umma ta soma kuka. Tausayi ta bawa
Umman ta fara rarrashinta "komai yayi tsanani
maganinsa Allah. Yakamata ace kece mai fadawa wani
hakan. Wa kike nema a waya har abin ya bata miki rai
haka"
Muryarta har ta dan shake tace " idan mutum ya dena
nemanka a waya sosai alama ce ta ya hakura da kai ko,
ko kayi masa laifi"
Duk da Umma tasan wa Asmau ke so sai tace "waye baya
kiranki a waya"
Rufe bakinta tayi da sauri. Maganar ce take cinta amma
bata yi niyar fada ba.
Dan murmushi Umma tayi. Tun ranar da suka hadu da
su Hajiya a asibiti kafin Anti Bintu ta koma Zariya ta fada
mata yadda suka yi da Col. Ishaq. Ta sauke ajiyar zuciya
"Ishaq ne baya kiranki?"
Sake sunkuyar da kai tayi ta kasa amsawa. Umma tace
"ki yawaita addua da neman zabin Allah nima zan
tayaki."
Abinda yake ta cin ranta ta kasa boyewa "cewa yayi zaiyi
magana da Hajiya, ina jin saboda Amatullah bata amince
ba. *Umma nayi kuskure ne da ban zubar da cikin ba na
haifeta*?
Wannan karon Umma ma sai hawaye "ko kadan Asmau.
Haihuwarta shine maslaha gareki damu baki daya. Mun
so bin son zuciya da muka dage sai kin zubar da cikinta.
Ki duba ki gani yadda Allah Yayita mai kokari da ladabi.
Kema kinsan ba iyawarki bace kawai tasa kike da yarinya
mai tarbiya kamarta. Mata da yawa da iyayensu sukan
gujewa kunyar duniya su zubar da ciki ko a yar da jariri.
Sai anje lahira kuma ido ya raina fata. Ga laifin zina ga na
zubar da ciki ko kashe jinjiri. Ko ki sami miji ko kada ki
samu ki sani cewa rayuwarki ibada ce. Hakuri da
tawakkali shine ginshikin farincikin dan adam. Batun
Ishaq kuma kada ki damu zai nemeki da kansa ku kare
magana. Da shi da Qasim wanda duk Allah Ya zaba miki
ko waninsu sai mu ce Alhamdulillah.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽47
Batul Mamman💖
*Maman Farida mai Hanyar Ruwa. Ina gaisuwa da fatan
alkhairi. Ga naki shafin yar uwa*
*Amina Yau, Jikamshi yana gaisheki da kyau.*
*Shafaatu mai masaukin baki a gidan Batul ina godiya*
*Masu sakonnin gaisuwa bazan taba mantawa daku ba.
Allah Yayi mana jagora*
Sai yanzu Asmau ta dan sami nutsuwa a ranta. Tun da
Jikamshi ya dena kiranta sosai ta fara tunanin ko
Hajiyarsa ce bata amince ba. Amma yanzu Umma ta
kwantar mata da hankali. Zata sake nemansa daga yau
zuwa gobe. Idan taji shiru to zata bar komai ga iyayenta.
A yanzu dai Umma da Mama Yalwa sun riga sun san da
maganar Col. Ishaq. Mama har fada tayi da basu fada da
wuri ba sai a asibiti ta ganewa idonta. Asmau ta san
bazata bar maganar ba dole ta fadawa Baba.
Bayan fitar Umma tashi tayi ta dauko Al-Qur'ani tana
karantawa. Neman sauki kawai take a zuciyarta da ke
kitsa mata abubuwa da yawa. Adduarta bata wuce idan
Jikamshi bazai aureta ba zata mayar da hankali ga
karatu, idan kuma iyayenta sun zaba mata Qasim duk da
a yanzu sun san bata son shi to bazata yi musu ba.
Fatanta bai wuce ta sami juriya wurin karbar duk wata
jarabawa da tazo mata ba.
*****
Washegari Umma ta gama shirin zuwa gidan Mama suyi
magana ta karshe da Alh Adamu sai ga Garzali ya shigo
yana ta fara'a suka hadu a bakin kofa. Umma tace
"kanina mijin 'yata irin wannan fara'a haka. Ko dai
Zubaida ta haihu"
Yana murmushi yace "yanzu daga asibitin nake. Ko awa
daya bata yi ba. An sami namiji."
Umma sai murna ta koma ciki tana mita akan me bai
fada musu ba tun lokacin da suka tafi asibitin. Sai da
suka je dakin Hajjo bayan ta fada mata kyakkyawan
labari tace "ina kuka kai su Walid?"
"Kai Yaya Bara'atu sai faman fada kike yi. Tsakar dare fa
ta fara nakudar. A makota na ajiyesu muka tafi."
Asmau ce ta shigo dakin daga kitchen bayan taji muryar
Kawu Garzali. Tayi murna sosai tace bari ta dora ruwan
Asmau ce ta shigo dakin daga kitchen bayan taji muryar
Kawu Garzali. Tayi murna sosai tace bari ta dora ruwan
zafi sannan ta hada abinci. Kawu Garzali yace ta barshi
makociyarsu duk tayi wannan. Yana jin bazata dade ba
za'ayi sallama. Tace to bari tayi wanka sai su tafi. Tana
tafiya Umma ta soma fada masa halin da suke ciki ga
Qasim kuma da yake jira a sake basu lokaci. Hajjo tace
"Allah mai iko, wallahi idan aka ce min yarinyar nan zata
sami manemin aure sai in karyata. Gashi yanzu an samu
har an rasa na zabe. Ni dai shawarata kada ayi mata
dole. Yaron nan Qasim dan mutumci ne gaba da baya
amma bana son ayi auren dana sani. Asmau ba
kankanuwar yarinya bace da zaa ce bata san me take yi
ba. Kai Garzali mu zamu je asibitin. Kaje ka sami Alhaji
kuyi magana. Idan za'aji ta bakin Ishaq din ne ya kamata
a hanzarta. Idan kuma da Qasim din ne ma duk yadda
akayi babu matsala."
Umma ta dan sassauta murya tace "Bintu fa ta fada min
shi Ishaq din yace ya janye saboda baya haihuwa."
"Baya haihuwa?" Hajjo ta fada tana daga murya.
Umma tace "Asmau bata sani ba. Yace zai fada mata da
kansa. Nima ban nuna mata na san wani abu ba"
Kawu Garzali ya shiga jimami. Zubaida ta fada masa irin
yadda ta ga Col. Ishaq da Asmau suna son juna ranar da
taje yini a gidan. Anya akwai ranar da Asmau zata ga
haske a rayuwarta kuwa. Daga wannan matsalar sai
wannan.
"Wai ya taba aure ne ko tuzuru ne shi Ishaq din"
"Kaima dai Garzali in bai taba aure ba yaushe zai san da
matsalar rashin haihuwar. Shekararsa shadaya da
matarsa ta farko"
Gefen gado Hajjo ta samu ta zauna "ni dai kaina duk ya
kulle. Haihuwa ba abin wasa bace duk da mutum baya
bawa kansa amma kowa yana so. Muje dai wurin
maijegon, kai kuma duk yadda kuka yi da Alhajin ka fada
mana. Ai ita shawara tana da dadi. Bana son azo ana
cizon yatsa nan gaba shiyasa cikinsu babu wanda zan ce
lallai sai ta zabe shi."
*****
A nan suka bar zancen su Umma suka wuce asibiti
daukar Zubaida. Kawu Garzali ya tafi gidan Alh Adamu.
Bayan sun gaisa ne Alhajin yace "ina Hajiya Bara'atun?
Tace zata zo. Ashe tare ma kuke"
"Ni kadai ne Alhaji. Sun tafi asibiti mai dakina ta sauka
dazu bayan asuba"
Barka Alh Adamu yayi masa sannan suka fara tattauna
abinda yake gabansu. Zancen Col. Ishaq ma sai da Alh
Adamu yayi ya ce Mama ce ta fada masa. Ashe shiyasa
yaga shi da mahaifiyarsa da 'yan uwansa sun zo duba
Amatullah. Daga Shanono kuma jiya ya sami waya suna
bukatar a sake basu lokaci.
"Alhaji wannan abu duk mai sauki ne. Yanzu nake ji cewa
shi Ishaq din yace zai janye saboda yana da lalura ta
rashin haihuwa. Idan haka ne kaga Qasim ya kamata ta
aura"
"Banki taka ba Garzali. Duk abinda aka riga aka sani yafi
sauki idan za'a tunkare shi. Amma menene tabbacinmu
na cewa shi Qasim yana haihuwa ko ita Asmau zata sake
haihuwa? A zahiri nafi sonta da Qasim saboda
kusancinsa da Abubakar. Gani zanyi kamar dana ne ya
aureta. Sai dai kuma bana son mu saka son zuciya a cikin
al'amarin nan. Tana gida ne yanzu?"
"A'a tare suka fita dasu Hajjo" Garzali ya bashi amsa.
"Idan ta dawo kace ina nemanta jibi bayan azahar in sha
Allah. Zan je daurin aure ne gobe Gashua. Tambayarta
zanyi don kada abin yazo da daukar alhaki. Wanda ta
zaba sai mu duba mu kuma muga dacewar hakan. Aure
ai ba'a yi masa garaje. Rashin karasa karbar kudin
wancan karon ma daga Allah ne."
"Shikenan Alhaji, Allah Ya zaba mata mafi alkhairi." Daga
nan suka yi sallama Kawu Garzali ya tashi ya tafi.
*****
Inna mahaifiyar Qasim ce ta saka shi a gaba suna
magana akan aurensa.
"Baffanka yace sunyi magana da Alhaji Adamu yace a
dan kara musu lokaci zasu sanar da ranar da za'aje kai
kudi"
"Eh munyi maganar. Dama Asmau nace ta fada musu da
farko to ashe ma Baffa ya kira shi"
Rai a bace Inna tace "yanzu ita Asmaun har sai an bukaci
lokaci kafin ace an yarda a kai kudin? Naga dai ita ce ma
me abin bincike a kanta. Yarinyar da ta bar gidansu
tsahon shekara biyar."
Murmushi kawai yayi. Inna bata son auren nan nasa duk
irin yadda zaiyi mata bayani tace su rayuwarsu ba irin ta
birni bace. A nan duk wanda yaji Asmau tana da 'ya sai
ya tambaya mijinta rasuwa yayi ko sakinta yayi. Wasu
ma suyi ta cewa mai zai sa Qasim ya fara da auren
bazawara. Babu yadda za'ayi su boye gaskiyar lamari.
Wasu ma sun dade da sanin rasuwar abokin Qasim da
cikin da yayiwa budurwarsa. Gulma da kananan
maganganu sai yawo suke. Ko kadan Inna bata jin dadin
hakan duk da tana kokarin yiwa Malam biyayya ta nuna
ta amince da auren.
"Sai anyi magana kayi ta murmushi kamar wani
bazawari. Ya dai kamata kafin komai ya kankama kuje
ayi mata gwajin 'yan cututtukan nan na zamani
musamman kanjamau"
"Inna ba fa karuwanci taje tayi ba. Aikin asibiti tayi duk
tsahon lokacin nan"
Tabe baki tayi "haka dai ta fada muku ku kuma kuka hau
kuka zauna. Mace babu mai kwabarta ai sai ta mike kafa.
Ni dai ba wani abu nace ba. Ayi mata gwaji ko don taka
lafiyar. Gurbacewa ce dai ka gama gurbata mana dangi.
Ko me kuka haifa nan gaba sai ance yayarsu shegiya ce"
Har ransa Qasim baiji dadi ba. Innarsa ta lura da yadda
ya hade rai tayi murmushi "Baba kenan, kada ka daukeni
muguwar uwa wadda bata son danta yayi aikin neman
lada. Duk wata uwa komai shedancin danta tana son ya
auri mace tagari. Abubuwan da kaga suna ta faruwa da
yarinyar nab kadan ne daga *abinda ake gudu* a zina.
Bana muku fata amma wata rana idan kunyi aure zata
iya yin abu da zuciya daya amma saboda sanin da kayi
na rayuwarta ta baya kawai sai shaidan ya kitsa maka
zargi ka hau kai ka zauna. Karuwai da yawa sun yi aure.
Wasu ma a gidan mijin suke sheke ayarsu. An sani amma
da yake aure rai gareshi sai kaga ba'a sake su ba. Kasan
halina bana boye abinda yake raina. Idan ka auri Asmau
kayi mata halacci kuma ka rike amanar abokinka. Ka
gyara abinda ya bata. Sai dai bazan fasa nanata maka ba
ina so ka kara aure a gaba."
Duk maganar Inna yasan gaskiya ne. Idan Asmau zata
taba mantawa da juyin da rayuwarta ta samu sai dai
idan an goge wannan bakar ranar da tayi sanadiyar
tarwatsa mata rayuwa.
"Akwai wadda kike so na aura ne? Da niyata bazan kara
aure ba bayanta."
"Yo dan nan kasan me gobe zata haifar ne da zaka ce
haka? Zabin wata matar yana daga gareka don kada ma a
sami matsala nan gaba kace nice na zabo matar. Bari na
shiga wurin Malam naga la'asar ta kusa"
Da Inna ta tashi Qasim dogon tunani ya zauna yi game
da auren Asmau da ya takurawa kansa lallai sai yayi.
Burinsa ya kyautata rayuwarta ba ya zama sanadiyar
kunci da bacin ranta ba. A yadda ya fahimci hirarta da
Col. Ishaq kwanakin baya ba karamin so suke yiwa juna
ba. Addua ya rinka karantowa a zuciyarsa
"Ya Allah, na sani ina daga cikin mutanen da suka batawa
Asmau da Abubakar

Please Login or Register in order to submit comment