Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiya.
Asmau tayi murmushi mai ciwo sannan ta fara sanar da
Zubaida dalilin watsewar farincikinta.
*FARKON LABARI*
Alh Shu'abu Yahaya sunan mahaifinsu Asmau. Iyayensa
duk 'yan Kano ne kuma a nan cikin Kanon suka tashi. Su
biyar ne a gidansu shine na biyu. Babbar yayarsa suna
kiranta Yaya Abu sai shi sannan mai binsa Rabe sai Lami
da Garzali.
Babansu mazan kawai yake sawa a makaranta. Saboda
haka Shu'aibu yayi karatu har matakin digri inda ya
karanci Agric Science harkar aikin gona. Shi mutum ne
mai saukin kai da kirki shiyasa mahaifinsu yake ji dashi.
Sauran 'yan uwansa kuwa kusan duk halin Hajjo
mahaifiyarsu suka debo na fada da sa ido.
Lokacin bautar kasa aka tura shi makaranta a wata
karamar hukuma a jihar Niger mai suna Wushishi. A can
ya hadu da Bara'atu tana ajin karshe na sakandire.
Farkon haduwarsu duk da baya koyar da 'yan ajinsu
soyayya ta kullu a tsakaninsu. Abu kamar wasa har
lokacin komawarsa gida yayi inda yayi mata alkawarin
turo iyayensa. Dama a hannun kawunta take ita da
kanwarta Bintu marayu ne ko kadan basa jindadin zama
da matar kawun.
Da ya koma Kano ya sanar da iyayensa Hajjo ta dage
indai tana da rai danta bazai auri banufiya ba. Duk 'yan
Niger mayu ne a cewarta. Ita a son ranta ya auri 'yar
kanwarta. Akayi ta jan zance ita da mahaifinsu shi kuma
ya dage Shu'aibu sai ya auri wadda yake so. Rigima sosai
akayi sai bayan wata biyu iyayensa suka je Wushishi.
Lokacin Bara'atu har ta fitar da rai. Ba wani dogon lokaci
aka saka bikin ba gashi ko aiki bai fara ba. Wurin hada
lefe yasha wahala Bara'atu ta bashi kudi cikin kudin
gadonta ya cika ya siya mata kaya masu kyau. Haka aka
yi biki aka kawo amarya Kano ita da kanwarta Bintu
saboda bazata iya barin kanwar a hannun matar
kawunsu ba ta cigaba da azabtuwa.
Wani bangare aka gyara musu a cikin gidan iyayensa
suka tare a ciki. Zaman lafiya sosai suke yi da mijinta sai
dai a wurin Hajjo da 'yan uwansa tana ganin wulakanci
mara misaltuwa. Daga ita har kanwarta basu da sunan
da ya wuce Mayya. Gashi dama duk suna da idanuwa
Tubarakallah.
Duk wani aiki na gidan ya dawo wuyansu amma bata
taba korafi ba. Kullum Shu'aibu sai dai ya bata hakuri
lokacin yana ta fafutukar neman aiki. A haka ta samu ciki
har sau uku yana barewa saboda aikin wahala.
A karo na ukun ne da safe Hajjo ta shigo taga Bara'atu
bata sha kunu da kosan da ta aiko mata dashi ba wanda
babansu Shu'aibu ne ya tilasta mata dama.
Fuska babu walwala tace "Au baku karya ba har yanzu
saboda ki jawo min fada wurin Malam yace bana kula
dake?"
Daga kwance inda take saboda rashin kuzari Bara'atu
tace "Kiyi hakuri na koshi ne".
Hajjo tayi dariya "yo ba dole ki koshi ba, kunyi kalaci da
jikana ke da kanwarki. Ai Shu'aibu ya gama janyo mana
masifa. Nan gaba kadan ma mu zaku bi ku lamushe."
Bayan ta gama fadanta ta fita Bara'atu babu abinda take
yi sai kuka. A wannan yanayin Shu'aibu yazo ya sameta.
Hakuri ya bata kamar kullum tare da kyakkyawan
albishir na cewa ya sami aiki a jami'ar Ahmadu Bello ta
Zaria a matsayin lecturer matakin farko. Kuma har da
gida aka bashi. Murna a wurin Bara'atu ba'a magana.
Kafin su tattara su koma Zaria ne mahaifinsa ya fara cuta
yana ta ramewa. Hajjo tasha kuka tana rokon Bara'atu
akan ta sakar mata kurwar miji.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽12
Batul Mamman💖
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Anti Bintu tazo Kano wurin yayarta yawon arba'in. Tunda
tazo kullum sai sun fita kasuwa siyayyar kayan amfanin
gida. Duk wani kudin Bara'atu na albashi, kasuwanci da
abinda ta samu na gado ta hada shi a gini da zuba kayan
bukata a sabon gidan. A lokacin falo da dakuna biyu
kawai ta gama sai kitchen amma bahaushe yace da babu
gara ba dadi. Hatta sutura da Hajjo ke yi mata gorin bata
siyawa yaranta duk ta siya. Dama tara kudin take sai ta
gama da abinda yafi mahimmanci.
Sai da ta gama shirinta tsaf sannan wata juma'a bayan su
Asmau sun dawo daga makaranta tasa sukayi wanka duk
ta basu sababbin kaya sannan ta hada sauran 'yan
kayansu suka tafi dakin Hajjo. Duk yaran mamaki ya ishe
su ina Umma zata kaisu sun kwashe duka kaya.
Kwadon zogale take ci yaran Rabe suna zaune suna wasa
a gefenta tana dariya. Shigowar Bara'atu da 'ya'yanta
yasa ta hade rai.
Dan Rabe na biyu sarkin gulma ya ruga ya fadawa
babansa ga Anti Bara da su Jafar zasu fita yau sunyi
kwalliya. Daga shi sai dogon wando haka ya fito da sauri
jin kwaf.
Bara'atu na dauke da jaririyar Bintu tace
" Hajjo albarkacin zaman tare a yafemu Allah Yayi zamu
tashi"
Zaro ido sukayi ita da Rabe. Shi a son ransa idan Bara'atu
ta gaji da takurata da akeyi ta yarda da aurensu. A ranar
ma zai saki Sagira.
"Ina zaki kai min yaran da kike cewa zaku tashi? Idan
tafiya zakiyi ke kadai dai ga hanya nan."
"Ba nisa zanyi ba Hajjo, nan layin gidan sabon
kwamishinan 'yan sanda zan koma. Cikin ikon Allah na
kammala gini na."
Ashar Rabe ya fara saki sannan yace "kika kammala
wane ginin? Waye ya baki filin da kudin ginin?kada ki
raina mana wayo wani saurayin kika yi kuke zaman....."
Katse shi tayi kafin yayi barambarama gaban yara.
"Fili dai tare muka siya da wannan da kuke ciki ni da
babansu Yassar. Ina sana'a ina aiki. Allah Ya buda min
gashi nayi gidan kaina. Wannan da kuke ciki kuma har
abada ku sani cewa gidan marayu ne. Allah SWT kuma
Yace wanda yaci dukiyar marayu tamkar yana ciwa
cikinsa wuta ne."
Hajjo ta bata rai "nufinki mune 'yan wutan..Bara'atu ki
kiyayeni wallahi. Kuma idan kika fita da yaran nan to ki
sani babu ni babu su."
"Ai aikin gama ya gama. Yara dai ke kika haifi babansu
saboda haka jininki ne. In Allah Ya yarda zasu rinka zuwa
gaisheki tunda ba nisa mukayi ba."
Daga haka suka fice Rabe yana binsu a baya yana kiranta.
*****
*Sabuwar Rayuwa*
Wannan tashin nasu shine ya kara kiyayya tsakanin
iyalan mariyayi Shu'aibu da gidan Hajjo. Kamar yadda ta
fada duk juma'a bayan masallaci take tura yaran gaishe
da Hajjo. Manyan kullum sai sun dawo rai a bace ko da
hawaye a idonsu. Amma hakan baisa ta dena turasu ba
saboda tasan su din dai suka rage musu dangin uba.
Rayuwa sabuwa suke yi cike da 'yanci da jindadi.
Bara'atu ta dage wurin bawa yaranta tarbiya. Sannan
tana nuna musu soyayya irin wadda bazata sa su
sangarce ba. Shakuwa mai karfi ce a tsakaninta da
'ya'yanta.
Washegarin tarewarsu suka shiga makota domin gabatar
da kai. Lokacin da suka shiga gidan Kwamishina Mama
Yalwa tayi musu tarba ta karramawa. Dama sun saba da
Umma. Duk yaranta suna gida ta kirasu ta gabatar dasu
ga 'yan uwansu kamar yadda ta fada musu. Abdulhalim,
Nasiba da Abubakar dai duk sun girmesu amma suma
sunyi kokarin jansu a jiki.
Bayan 'yan kwanaki ne Mama Yalwa taje gidan Umma
take sanar da ita Baba yace ta rinka turo su Asmau ana
yin magariba masallacin gidansu akwai Malamin da yake
koyar dasu Sadiya karatun Qur'ani zuwa karfe tara.
Umma taji dadi sosai,duk da suna zuwa islamiyya amma
wannan ma zai taimaka kuma ba nisa suka yi da gida ba.
_Asmau S. Yahya_
Ranar farko da zasu je makarantar kowa yana doki
banda Asmau. Haka take da tsoron mutane. Duk gidansu
ita ce ta kasa sakewa da yaran Mama.
Kowa ya shirya ta kwanta ciwon cikin karya saboda taji
ance kowa karatunsa shi kadai malam zai biyawa. Yadda
zata yi karatu a gaban su Suwaiba ne yake kara tsorata
ta. Umma na ganinta tasan ciwon karya ne. Da rarrashi
ta lallabata suka tafi suna idar da sallar magriba.
Cikin gidan suka fara zuwa suka gaishe da Mama sannan
suka fito waje. Suwaiba 'yar Mama ta hudu ita ce kusan
sa'ar Shema'u amma duka ita da Sadiya sun zama
kawaye da Shema'un. Tare suka fito zuwa masallacin
Asmau na bin bayansu rike da hannun Aina'u.
Malam Hadi yana zaune tare da Abdulhalim, Abubakar
da Umar. Suna zuwa gaishe shi suka yi kowa ya sami
wurin zama. Sai da ya gama da manyan sannan yaji
karatun su Suwaiba. Daga nan ya fara jin inda su Asmau
suka tsaya yace kowa sai ya biya surar karshe inda ya
tsaya.
A nan ake yinta ana zuwa kan Asmau da ta fuskanci
idanu sun dawo kanta tana yin Bismillah sai hawaye.
Malam yace ta barshi ya gama da sauran .Shema'u tayi
tsaki tace " malam wallahi ko a islamiyya haka take yi sai
taji bulala take kawo hadda."
Murmushi yayi "ni bana duka kinji Ma'u. Bari na gama
da kannenki sai ki biya min."
Hatta Aina'u sai da ta karanta suratul Ikhlas amma ana
dawowa kan Asmau sai kuka. Jafar yace Ummansu tace a
zaneta idan bata yi karatu ba.
Tunda ta fara kukan farko Abubakar yake kallonta.
Dariya abin ya bashi sai da yaga taki denawa ta soma
bashi tausayi.
Malam Hadi yayi har ya gaji taki karatu sai kuka da rawar
murya. Yace kowa ya fita banda manyan yayye. Suna
tafiya ya nuna mata Abdulhalim da Abubakar
"Waye a cikinsu kika yarda zakiyi karatun a gabansa
tunda kin kasa a wurina."
Tana daga kai suka hada ido da Abdulhalim ya hade rai.
Da shine malamin zaneta zaiyi fes baya daukar rainin
hankali. Da sauri ta nuna Abubakar. Malam Hadi yace "to
Sadiq ka kwatanta gaskiya ka ji karatun. Ke kuma gobe ki
tabbatar zakiyi a gabana ko na samo bulala".
Da haka suka fita saura ita da Abubakar.
Fuskarsa a sake ya fara tambayarta "shekarunki nawa
Asmau?"
"Shahudu"
"Ashe ma kin girmeni da shekara takwas"
Ta dan saki fuska amma muryarta bata dena rawa ba "so
kake kace ka girmeni da shekara takwas dai"
Yayi murmushi dama so yake ta saki jikinta "Haka ne, ni
yanzu ina level two a BUK ina karanta computer science.
Ke fa?"
"SS1 nake a science class. Likita nake son zama" yadda
take maganar yasan ba karamin son hakan take ba.
"Very good, sai dai bakiyi kama da likita ba saboda tsoro
yayi miki yawa. Likitoci kuma basu da tsoro".
Yana kallon bata ji dadin maganarsa ba ya sake yin
murmushi.
"Kada ki damu akwai maganin tsoro. Shine ki daure ki
rinka magana a cikin mutane. Babu mai yanka ki. Iyaka
idan kinyi kuskure a gyara miki. Karatun Qur'ani karfin
zuciya yake sawa ba ragwanta ba."
Shiru tayi tana sauraronsa yana ta janta da zance. Sai
karshe yace ta biya masa yaji.
Da kyar ta daure hawaye wani na bin wani ta karanta.
Kafin tayi rabi kukan ya dauke sai karatun ake ji.
Tana kaiwa karshen surar yayi kabbara sannan ya sake
karfafa mata gwiwa wurin bude baki a gaban jamaa.
Da murmushi ta fito suka tafi gida ran Shema'u a bace
saboda tasa sun dade.
Tun daga wannan lokacin ko ta fara kukan idan
Abubakar yana masallacin sai ta daure. Karshe dai
sunanta ya koma Idon kuka saboda kullum sai tayi.
Gashi ta tsani sunan.
Haka rayuwa ta cigabar musu har lokacin bikin Nasiba.
Gidajen biyu suna ta shiri duk da su Umma basu fi
shekara daya a unguwar ba. Haka suka yi bikinsu lafiya
kalau kamar dangin juna.
Su Asmau an kara zama 'yan mata. Yanzu tana dan
sakewa har ayi hira da ita. Wani lokaci da Umma zata
Wushishi gashi basu yi hutu ba a nan gidan Mama Yalwa
ta barsu.
Abdulhalim ya tafi bautar kasa Jos yanzu Abubakar ne
babba a gidan. Duk da yanayin karatunsa bai hana shi
cigaba da zama daukar karatu a wurin malam Hadi ba.
Duk cikinsu yafi kowa mayar da hankali akan karatun
addini shiyasa Baba yake matukar ji dashi.
Watarana an gama karatu kowa ya fita daga masallacin
sai Asmau dake zaune tana kokarin kammala aikin da
malam ya bata na fitar da hukuncin (NUUN saakina) a
thumunin da ya biya mata ranar saboda washegari test
gareta a makaranta karatu take son yi. Abubakar yana
can wurin zaman liman yana tilawa aka soma iska mai
karfi alamun ruwa zai iya sakkowa a kowane lokaci.
Da dan gudunta ta tashi zata rufe tagogi kafin ta fita
saboda kurar dake shigowa. Har ta gama rufewa
Abubakar baiyi yunkurin tashi ba. A take kuma aka
dauke wuta saboda wata tsawa da akayi mai karfi. A dan
tsorace tace
"Yaya Abubakar kazo mu fita kafin ruwan nan ya sauko"
Shiru taji sai numfashinsa da ya kara karfi. Gabansa ta
karasa sai dai duhu yasa bata ganinsa sosai. Wayarsa da
ta taka ta dauka ta haska shi. Kwance yake numfashinsa
yana sama-sama da kyar yake fita. Hannunsa daya kuma
yana nuna mata aljihun wandonsa.
Asmau duk ta rikice ta kuma fahimci abu yake so ta
miko masa daga aljihunsa. To kuma Umma tayi musu
gargadi sosai akan taba maza wannan yasa ta kasa
tabashi ta fita da gudu a cikin ruwan ta shiga gidansu ta
fadawa Mama Yalwa.
Tare suka dawo har da Suwaiba dauke da irin filtilar nan
mai batir. A kwancen dai suka same shi ya hada gumi
idanunsa harda hawaye. Mama ta daga kansa ta dora a
cinyarta a rude tace "ina inhaler dinka?"
Aljihunsa yayi kokarin nuna mata. Tasa hannu ta dauko
ta shaka masa. Asmau da Suwaiba suna tsaye suna yi
masa sannu.
Duk da haka numfashin bai dawo daidai ba. Mama tace a
fadawa dreba yazo su tafi asibiti. Bayan fitarsu Asmau ta
tafi gida ta sanar da Umma abinda ya faru.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽11
Batul Mamman💖Rabe ne ya fito yasha sabuwar shadda sai kyalli take yi.
Idonsa a kan Bara'atu da yanayin da ta shiga yayi dariyar
mugunta. Don tsabar wulakanci yace
"A'a bazawara kune a garin? Ya hanya?"
Hawaye take yi wani na bin wani ta durkusa a gaban
Hajjo
"Nasan har mijina ya rasu baku taba kaunata ba amma
Hajjo wallahi cin dukiyar marayu haramun ne. Gidan
nan baku da hakki a kansa to a wane dalili zaku zo ku
tare batare da izini ba".
"Eh, lallai wuyanki ya isa yanka Bara'atu. Ni da gidan
dana kike gaya min maganar banza." Hajjo ta amsa
itama rai a bace.
"Ko kinki ko kinso zama dole muyi a gidan nan. Idan
bazaki iya zama damu ba sai ki bar min yaran ki kama
gabanki."
Yusuf mijin Anti Bintu yace "Anti kada ki sake cewa
komai. Ai basu fi karfin hukuma ba. Kuma rabon gado
ba hauka bane. Ki bari mu kwana yau gobe sai mu san
abinyi."
Mikewa tayi cikin zafin nama tana kallonsu daidai.
Garzali banda taba babu abinda yake busawa. Rabe da
amaryarsa suna tsaye suna mata kallon banza. Hannu
tasa ta share hawayenta
"Dama can saboda marigayi nake raga muku to amma
wallahi yanzu an wuce wurin. Mu zuba ni daku shege ka
fasa."
Yaranta ta dakawa tsawa duk suka tashi daga gaban
Hajjo suka bita cikin gidan.
Hajjo da su Rabe kowa yayi tsit suna mamakin wai yau
Bara'atu ke mayar musu da martani haka.
*****
A cikin gidan dakuna biyu ta samu a bude ita da Yusuf da
su Shemau suka rinka shiga da kayansu. Sai cikin dare
tana zaune tana kallon 'ya'yanta na bacci ta rinka kuka.
Washegari ko karyawa batayi ba suka fito ita da yaran
suka hadu da Yusuf zasu tafi ofishin 'yan sanda.
Rabe yana tsaye a waje yace " kinga basai kun wahala ba
a bayan layin nan akwai gidan wani babban dan sanda.
Maza ku tafi ku kai kara kada kuda ya rigaku."
Basu kula shi ba suka wuce. Duk wani bayani sun
gabatarwa 'yan sandan. Mutum hudu aka hado su dasu
suka zo aka bukaci su Rabe su fita.
Wannan muguwar dariyar yake yi ya dauko takardun
gida sai gashi sunansa ne dana Shu'aibu a jiki a matsayin
tare suka gina.
Kuka sosai Bara'atu take yi tana karyata shi. Sai dai kuma
bata da shaida. Bata san yadda akayi ya sami takardun
gidan ba wanda a hannunta suke har akayi canje canje
haka.
Dole 'yan sanda suka tafi domin basu da wata shaida.
Yusuf ya nemi ta bishi su koma Zaria daga nan ta koma
garinsu da zama.
Tana kuka tace "ko zasu kashemu babu inda zamu je.
Gidan nan namu ne kuma duk rintse sai ya dawo
hannun masu shi."
Babu yadda Yusuf ya iya dole ya tafi ya barta. A dakin
kwanansu ta sayi risho mai kai biyu da kayan abinci.
Kullum suna daki tana saka yadda zata bullo musu.
A karshen sati ne abokan marigayi biyu suka zo. Anyi ta
kai ruwa rana Hajjo da Rabe da sauran 'ya'yan gidan
suka hade musu kai. Magana dai har wurin dan sandan
dake bayan layinsu, Adamu Matawalle ashe abokin daya
daga cikinsu ne. Shima ya gamsu da bayanansu sai dai ga
shaida kurukuru suna gani gida na Rabe da Shu'aibu ne.
Shawara suka bata akan ta koma gida kawai tace babu
inda zata je.
Wani katon fili wanda gida daya ne tsakaninsa da gidan
dan sandan ta nuna musu. Rabi nata ne ta siya da kudin
kasuwancinta daya rabin kuma Shu'aibu ne ya siya mata.
Takardun ta bawa dan sandan ta roke shi ya rike mata
amana zata gina kayanta a hankali sannan su tashi daga
can gidan. Duk ta basu tausayi. Wani cikinsu ne yayi
cuku-cukun nema mata aiki a kamfanin sadarwa na MTN
, duk wannan abu batare da sanin su Rabe ba. Tayi musu
godiya kamar ta ari baki.
Cikin dan lokaci ta saba da iyalin Adamu sai dai kullum a
gida take barin 'ya'yanta idan zata je wurinsu. Tana
tsoron surutun yara kada su fada a gidan. Makaranta ta
samar musu a nan cikin unguwa. Saboda yanayin aikinta
ta koyawa Shemau da Jafar girki ko da bata dawo da
wuri ba. Zagi da surutu har su Hajjo sun gaji da yi wai
tana yawon bariki. Bata kula su ba sai dai bata bari
'ya'yanta sun raina kakarsu ba.
Wata rana ta fito suna sauri zata kai yara makaranta ta
wuce wurin aiki ta nemi motarta bata gani ba. Rai a bace
ta koma ciki ta tambayi Sagira. Sai da ta gama yaukinta
sannan tace ban sani ba. Itama Hajjo amsar data bata
kenan.
Tasan aikin Rabe ne sai tayi kamar ta hakura. Har wani
gadara yake yi yana cewa motarsa. Na tsawon sati biyu
ta dauke kanta daga kan motar sai dai a bayan idonsa ta
sami wani abokin aikinta ya samo mai siya.
Ranar Juma'a Rabe na kwance a daki mai siya yazo yaga
mota aka gama ciniki ta bashi mota da takardunta. Shi
kuma yayi alkawarin kawo kudin ranar litinin.
Sam Rabe bai san me ake ciki ba sai washegari ya gama
shirin zuwa daurin aure. Ganin babu motar kuma yasan
Bara'atu nada mukulli ya tafi kofar dakinta yana ta bugu
iya karfinsa. Yaranta duk bacci suke yi ta fito da dogon
hijab a jikinta tana murmushi don tasan me ya kawo shi.
"kinga ba wasa bane ya kawoni ina kika kai min mota"?
"Hmmm, karfin hali barawo da sallama." Ta fada tana
tafa hannuwa.
Hajjo da Sagira suka fito suka sakata a gaba.
Bara'atu ta yatsina fuska "mota dai tawa ce kuma na
sayar na cinye kudin. Shikenan ko."
Ran Rabe a bace ya zabga mata mari. Hajjo tace kayi min
daidai.
Bai ankara ba Bara'atu ta kwashe shi da mari shima tana
harararsa.
"Dani daku a gidan nan daga yau an shata layin rashin
mutumci. Na gaji na kai wuya duk abinda zakuyi kuyi.
Banda rashin tsoron Allah komai na gado sai mun raba
ni daku? To mota dai tawa ce ni kadai"
Tsaki taja ta shige dakin ta banko kofa.
Hajjo ta kalli Rabe a dan tsorace." Anya yarinyar nan
bata shan kwaya kuwa? Kada tasa a koremu fa."
Rabe ya dafe kunci "barni da ita Hajjo sai na nuna mata
bata da wayo". Sai dai har kasan ransa bazai iya ba
saboda son da yake mata.
Haka suka cigaba da zaman doya da manja a gidan.
Tsakanin Bara'atu da su sai kallo. Yaranta kuwa ta
wajabta musu zuwa gaishe da Hajjo safe da dare duk da
bata amsawa. A haka har suka shekara daya da rabi tana
ta gininta a hankali, sannan duk da tana aiki bata dena
kasuwanci ba.
Wata ranar lahadi tana daki ta jiyo hayaniya a falo. Yaya
Abu ce da Lami suka zo yini da 'ya'yansu. Su Shemau na
son zuwa wurin sauran yaran suna tsoron Ummansu.
Murmushi tayi tace su je amma banda tsokana.
Da gudu suka fice tunda da sauran kuruciya basu gama
bambamce masu sonsu ba. Iyayen dai babu wanda ya
amsa musu gaisuwa da 'yan uwansu yara suke ta wasa.
Kamilu babban dan Yaya Abu ne ya shigo ya soma
rungumar kannensa kamar yadda ya saba. Yana
rungume da Shema'u yana tsokanarta Bara'atu ta fito
idonta ya fada kansu. Mantawa tayi da mutane a wurin
tace
"Kamilu wane irin wasa ne wannan? Shema'u ban hanaki
wannan rungume rungumen ba?"
Dena hirar su Hajjo suka yi suka tsaya kallon Bara'atu
tana yiwa dansu fada.
Lami ta watso mata harara "To kinibabbiya kin fito ne ki
fara rashin da'ar taki? Menene aibu don ya taba
kanwarsa, yaro da muharramarsa ma sai an nuna musu
iyawa" mtws.
"Bani da matsala don Kamilu ya taba kanwarsa sai dai
Shema'u ba muharramarsa bace shiyasa na hana. Daga
shi har ita babu karamin yaron da ba'a budewa littafi
ba".
"Ya Sayyada manya....indai Yaya Shu'aibu ne uban
Shemau to baki isa ki rabata da Kamilu ba domin kuwa
iyayensu uwa daya uba daya suke. Kinga sun zama
muharraman juna".
Kallon Lami kawai Bara'atu tayi ta girgiza kai zata koma
ciki Hajjo ta dakatar da ita.
"Sai kin fada min dalilin son raba min kan jikoki tunda
kin gama fetsare kafafunki".
"Hajjo ni ba rashin kunya nazo yi miki ba. Wannan abu
ba fadata bace. Da yawa mutane muna jahiltar abinda
ake nufi da muharrami. A musulunce duk mutumin da
ko ku kadai kuka rage a duniya aure ya haramta
tsakaninku shine muharrami."
Yaya Abu tace "to ina kuma alakar jini da take
tsakaninsu? Ita kuma an datse ta kenan?"
Bara'atu ta fahimci neman kureta suke yi sai dai kuma
tana da hujja ba da ka tayi magana ba.
"Alakar jini bazata hana aure tsakaninsu ba wannan yasa
ya zama ba muharraminta ba. Mutanen da suka amsa
wannan suna a garemu sune kaka(namiji),'yan uwansa
wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma
banda 'ya'yansu. Haka kuma yake ga bangaren kaka
(mace), sai 'yan uwan uwa da na uba suma wanda suka
hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda
'ya'yansu. Sannan sai 'ya'yan kanne maza da mata.
Babban misali shine Sayyadina Ali RA kani ne ga Annabi
Muhammad SAW domin iyayensu wa da kani ne. Nana
Fadima bazata iya auren Abu Dalib ba saboda kawun
babanta ne amma ta auri dansa duk da cewa kani ne ga
mahaifinta.
Sannan ko a gidan nan Rabe da ya auri Sagira ai
kanwarsa ce tunda Hajjo da babar Sagira shakikan juna
ne.
Muna yawan yin kuskure sai muce 'ya'yanmu 'yan uwa
ne mu bari suna taba juna ko suna shiga dakin juna kai
tsaye da sunan 'yan uwan taka.( A labaranmu na soyayya
muna yin wannan kuskuren duk mu saka cousins ko
'ya'yan riko sun gama tabe taben jikin juna duk da
sunan 'yan uwan taka sannan daga baya mu kulla
soyayya tsakaninsu). Aya ta ashirin da uku a suratun
Nisa'i ta iyakance mana su waye muharramai. Kuma
_An karbo daga Ma'qal ibn Yassar yace Manzo SAW yace:
ya fiyewa dayanku a buga masa kusa a kansa da ya taba
jikin macen da ba muharramarsa ba.At-Tabarani ya
rawaito shi, Sheik Nasiruddeen Albani ya inganta shi a
Sahih Jaami'."_
Wani kallon raini suka rinka binta dashi tunda dai ga
hujja ta basu. Yaya Abu tace da Kamilu " Kai, daga yau
babu ku duka babu wadannan 'ya'yan gwal din."
Bara'atu dai kyalesu tayi ta wuce tana addua'ar kammala
gininta su huta da wannan masifa.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽13
Batul Mamman💖
Tare suka koma gidan Kwamishina sai dai su Mama har
sun wuce asibiti. Sai wuraren shadayan dare Mama ta
kira Umma bayan taga missed calls dinta take sanar da
ita an kwantar dasu asthma din Abubakar ce ta tashi.
Gari na wayewa Shemau ta hada abincin safe harda
mutanen asibiti. Ita da Umma suka tafi asibitin su Asmau
kuma suka wuce makaranta. Sai bayan la'asar da zasu
kai abincin dare duk da ana kaiwa daga nasu gidan
Umma ta hada 'ya'yanta gabadaya suka tafi asibitin.
Jikin Asmau a sanyaye suka shiga dakin saboda ba
karamin rudewa tayi ba da ganin halin da Abubakar ya
shiga. Bayan an gaisa kowa yayi masa sannu ya amsa
banda na Asmau. Da farko ta zata baiji ba ta sake
maimaitawa. Wannan karon harararta yayi amma ita
kadai ta kula da hakan. Bata gane dalilinsa na yin hakan
ba amma bata ji dadi ba har suka tafi bata sake magana
ba.
Sai da yamma aka sallame shi washegari. Nan ma da
suka zo karatu yana falo ta sake yi masa sannu yaki
amsawa har sai da Qasim yayi masa magana.
"Abubakar ana yi maka sannu baka ji ba"
Hamma yayi ya gyara kwanciya batare da ya amsawa
Qasim ba.
Da dan murmushi Qasim yace "jikin nasa da sauki . Ke
ce Asmau ko?"
Kanta a kasa saboda abinda Abubakar yayi mata tace
"eh" tare da mikewa ta tafi masallaci.
An shafe sama da wata biyu Abubakar baya amsa
gaisuwar Asmau. Dama can ba wata hira suke yi ba. Abin
yana matukar damunta sai dai ta kasa fadawa kowa.
Ranar lahadi da yamma tana dakinsu Yassar ya shigo ya
ganta tasa littafi a gaba tana kuka. Baice mata komai ba
ya fita ya fadawa Umma. Tasowa tayi ta shigo dakin da
kanta.
"Me ya sami Idon kukana kike sana'ar a daki ke kadai"
Littafinta ta mikowa Umma na Physics. Assignment ne
kuma duk lissafi ko daya bata yi ba.
"Tun dazu nake yi na kasa amsa ko daya. Kuma malamin
duka yake yi."
"To shine kike kuka kuma saboda kinfi kowa ruwan ido,
uhmm? Kinga ni da yayyenki babu wanda yayi physics.
Idan kuma kin amince na koya miki gobe kici kafi-zero
shikenan" ta fada da dariyarta.
Murmushi Asmau tayi tana sake duban littafin.
Umma tace "kije Abubakar ya koya miki shine dan
science a gidan Mama."
"Umma ai gara naci zero din. Ni da ko gaisuwata baya
amsawa idan naje nasan bazai kulani ba"
"Asmau bana son karya. Baban nawa ne baya amsa
gaisuwarki? Jiya da yazo ba ke nasa kika dafa masa
indomie ba. Ko dai wani laifin kika yi masa?"
"Kila kunyarki yaji amma da gaske tun kwanciyarsa a
asibiti ya tsaneni. Kuma ni banyi masa komai ba".
Umma ta dan kalli Asmau sannan ta fita. Abubakar yaron
kirki ne kila Asmau tayi masa laifi ne ko kuma dai wani
rashin fahimta suka samu. Ko

Please Login or Register in order to submit comment